Labari ne mai cike da...... *Tausayi* *Mugunta* *Zalinci* *Cin amana* *Yaudara

PAGE2️⃣1️⃣⏩2️⃣5️⃣

by @prettys01


E.P2️⃣1️⃣.



_____________________________________________________________Shuru ne ya ratsa babban parlourn da take zaune a ƙasa, tana jin abin da Uwar mai muƙami ke faɗa amma gaba hankali ya koma ga abin da ya faruwa daren jiya tsakanin ta da Unais. Da sauri ta rintse idanunta tana mai kuma ganin abin da ya faruwa a cikin kanta. ( Tabbas ta shi cikin ɗakin da ƙafafunta in da ta tsaya gaban mirrow tana kallon, dafa kanta ya yi dan jin yadda yake sara mata. A rayuwa Sopiyya ta tsana abin da zai dinga ɓa ta mata rai ko ya sanya ta damuwa balle ma sam ba ta saba da su ba. Ta rasa wannen ya faru a farko tsakanin shigowar Sarki Unais da yin ba ya da ta yi zama zuɓe. Duk da ba ta kai ƙasa ba domin cikin zafin nama ya taro ta sai ta faɗa jikinsa. Girgiza ta ya yi amma shuru dan haka ya kwantar da ita akan wannan kaifafa ya fice, bai jima ba ya dawo ɗauke ruwa, yayyafa mata ya yi amma shuru sai dai ya lura kaman tana neman iska dan yadda nunfashina ta ke fita a wani irin yanayi. Ji ya yi kansa ya ɗauke ba tsayawa tinanin komai ya fara aikata abin da kansa ya hasaso mai na wani film in da Actor ke busa ma Actress iska ta baki...... Hura mata iska ya shiga yi har ya ji numfashin ta ya dawo dai-dai, da sauri ya zame bakinsa yana mai rintse ido, sai ya buɗe take suka haɗa idanu amma na ta hawaye ne kwance a ciki, da sauri ya fita a ɗakin ba tare da ya ce komai ba....... A lokacin hatta notice ɗin kanta sun ƙawance dan ko motsi ba ta kuma yi ba a haka barci ya ɗauke, ko bayan da gari ya waye ba su haɗu da shi ba. Sannan tin bayan ta kammala shirita shine aka ƙawotai wajen Uwar mai muƙami. Ta gaida su sai dai Mama ce kawai ta amsa, a wajen ta zauna, amma ba ta da wani tunani sai daren jiya.......) 

“Sopiyya!.” da sauri ta ɗago kanta tana barin tinanin tare da kallon Uwar mai muƙami.

“Na'am.”

“Tinanin mai kike haka? Na ce maki yanzu mun zama ɗaya tunda kin yadda za ki mana biyayya. Da niyyata na cutar da ke amma a yanzu na yafe miki” murmushi da iyalansa kan leƙan ta ne ta yi tana mai faɗin.

“Godiya nake sosai.”

“Bakomai, ke ƴar Hamza Rasheed ce koh?.” Zaituna ta faɗa cikin matuƙar zullum jin amsar Sopiyya, ita kuwa Sopiyya shaf ta manta abin da Unais ya faɗa mata, cikin sauri ta furta.

“Eh ni ce Autarsa.” murmushi Zaituna ta yi tana cewa.

“Garinya kika ɓa ce? Banji ana cigiyarki ba.” wani yawu ta haɗiye sannan ta fara jero magana kaman irin ta tsaran nan.

“Bana ce ba, amma nasan dole su nemeni mayyuwa suna fara bincikan cikin jahar ne kafin akawo cibiya nan.” ta amsa na biyu ba tare da ta amsa ɗayar tambayan ba.

“Ƴar nan shiga ciki.” Mama ta faɗa, ba musu ta miƙa tare da barin wajen.

“Mu jira na wani lokaci har muji cigiyar ko?.”

“Eh Mama, zan jira. Wallahi da farin ciki nake kwana yanzu duk dan Sopiyya, kai Alhamdulillah.” Mama ta yi murmushi dan ta son ta ga Zaituna cikin nishaɗi.





_________________Shi kansa mamakin kansa yake, haka kuma tin bayan barin ɗakin ya tsinci kansa da sakar murmushi, har yau kuma har yanzu da yake zaune a faɗa, hatta zagayen da suka yi ya ƙi magana sai faman murmushi da taɓa leɓansa yake. Sai a yanzu ya luma mutanen da ke wajen kowa cikin tsoro-tsoro suke dan in yana murmushi to wani mugun aikin zai yi.

“Allah ya ja kwana, tin ɗazu wakilan Masarautar Sayyid ke jiranka.” sai ya buɗe baki ya yi magana duk da baya wani magana amma yau kam babu abin da ya ce.

“Ka faɗa ma shi kansa Sayyid ɗin, in ma ya gayyace mu ko Masarautar Shuraib. Amma idan su ya fara aikawa da saƙo to ya yi haƙuri ban iya zuwa taro ina ganin maƙiyi na.” yana faɗan haka ya miƙe tsaye tare da fara tafiya, da sauri masu take mai baya suka hau bin sa. 


        *Masarautar Sayyid Rasheed*

________________Ko da saƙo ya iso ma Sarki Sayyid Rasheed, sai ya yi murmushi sannan ya kalla Hamza dake harhaɗa rai ya ce.

“Unais ji yake da kansa kaman wani sa'ar mu bayan duk mun haifesa.”

“To wa ya buƙaci ya zo, shima yasan dole Sarki Arman za mu gayyata.” 

“Sosai ma kuwa, ya sha zaman sa dan dama na sauƙe haƙƙin da ke kaina ne. Dama ko angayyace mu ni kaɗai ke zuwa.” miƙewa Hamza ya yi yana faɗin.

“Kaji za ka iya ne Yaya.” girgiza kai kawai ya yi.



___________Yana shiga ya ɓangaren sa ya tadda Ayusha riƙe da kofi, yana kallon ta ta sakar mai da murmushi, a hankali ya ɗan rage damunsa da ya ɗibo.

“A kullum Ummi complain take min akan ni banda aiki sai yawo da takobi kamar kai, shine na shiga cikin na haɗa wannan, sha kaji.” amsa ya yi suna shiga cikin parlourn da ya ƙawatu irin na sarauta. Sai bayan da ya zauna ya aje takobin sa sannan ta kai baki, ba ɗanɗano ba tsari amma ya shanye tas.

“Auta wannan ai maƙura ne a daɗi, kema saura aure tunda kin iya haɗa....” sai ya yi shuru dan bai san da mai zai kira abin da ya sha ba.

“Ina bazan yi Aure ba, babbar mayaƙiya zan zama kamar kai, a yanzu na ƙware dan jiya mutum uku maza na zubar. Next yaƙi da ni za'a yi.” sai ya yi murmushi dan yana alfahari da ƙyarsa, yin bayan ta so warta ta wanke mai ciwon rashin haifan namiji Magaji shi da Sarki. Duk cikin yaran tana da zafi kaman Hamza haka kuma akwai ta ƙarfi da iya wasa da takobi. Idan ta fita cikin gari kowa bin ta yake dan yadda ta cire tuta, amma har yau babu wanda yasan fuskokin yaran gidan Sarki. Kullum cikin rufe fuska suke hatta a cikin gida wannan shine babban al'adar Sayyid Rasheed Dan mutanen garin mata sai yara su manta fuskar Mahaifiyarsu saboda kullum tana kulle. Hatta yanzu ɗin Niƙaf ne fuskar Ayusha sannan ta riƙe takobi.

“Ko zamu kwada wasan takobi.” ta faɗa tana kallon Hamza sai ya ce.

“Kar na ji miki ciwo.”

“Hahaha idan har ka yi galaba da ni to daga yau na bar zuwa filin yaƙi zan runguma kitchen.” murmushi ya yi yana mai alfahari da ita dan akwai ƙarfin hali. Mike wa ya yi tare janyo takobin sa...............✍️
END.

> PRETTY SK ce.............✍️🥀



***

****

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 




🌙🕌🌹⭐🕋اَلّٰلھُم  صَلِی عَلٰی مُحَمَّدٍ وَعَلٰی آلِ مُحَمَّدٍ کَماَصَلَّيتَ عَلٰی اِبْرَاھِيمَ وَعَلٰی آلِ اِبْرَاھِيمَ اِنَّكَ حَمِيدُ مَّجِيدُُ❤️🥰

*____________________________ PRETTYN JAJIRTATU ce...............✍️✍️✍️✍️✍️


E.P2️⃣2️⃣



*BAYAN KWANA UKU*

__________________________________________________________________________________ Fara'a kwance akan fuskar Uwar mai muƙami, cikin wani irin mamaki ta kalla Mama ta ce.

“Sai yau saƙon ɓatar ƴar Hamza ya iso, gaskiya na yi farin ciki da wannan maganar. Rashida.......” da Rashida dake zaune ta amsa.

“Na'am shuganata.”

“A isar ma Unais da saƙon ina son ganinsa bayan magrib.”

“Yanzu saƙon zai isa garesa.” ta faɗa haka tana ficewa.

“Zaituna mubi komai a hankali.” ta ɗaga wa Mama kai....................



________________Idanunta a kulle suke amma sai annuri ke fita tare da murmushin fuskarta ba komai take tinawa ba sai a cikin kwanaki ukun da suka wuce, wani al'amarin da ba za ta iya fassarawa wanda ke faruwa tsakaninta da Unais, tasan ta dage da addu'a, akan Allah ya sautatta zuciyar Unais da nuna mai hanya ta gaskiya, tun a yanzu ta fara ganin sauyi domin Unais mutum ne mai tausayi sai muguntan dake jininsa baya bari tausayin ya yi mai tasiri. Alhamdulillah ba laifi Sopiyya iya kwarkwado tasan haƙƙin aure da auren mecece.

“Sarauniya!.” jin yadda yake Mama Jakaddiya ta kira sunanata yasa ta buɗe idanunta da sauri tana kallonta.

“Menene lafiya kuwa!?.” sai ta zauna a gefe tana faɗin.

“Yanzu wasu suka kawo ma Sarki saƙo daga Hamza Rasheed akan yana cigiyar ƙyarsa mai suna Ayusha Hamza Rasheed.” zaro idanu Sopiyya ta yi tana faɗin. 

“Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un', shike nan.......”


“Me yasa baki faɗa mana ainiyin sunan ki ba?.” ganin Mama ba ta harbo jirgin ta ba yasa ta ce.

“Da suna biyu ake kirana.” 

“Dama wuce zanyi na ji ana shela, bara na amso miki saƙon.” ɗaga mata kai kawai ta yi tana mai zama da ƙyau. Shuru ta yi tana mai faɗin.

“Ɓata kuma! Garin ya!.”.................. 




_____________________Tinda aka faɗa mai saƙon Zaituna ya rage walwala ba dan komai ba sai dan a yanzu yana jin Sopiyya a cikin ransa, ya rasa ta ya ya amma harga Allah tana burgesa, sai abu mafi damunsa shine baya iya zama yana ganinta ba tare da ya ji yana son taɓa gashin kanta tare da son ƙara shan wannan pink lips na ta masu jan hankali. Sai dai sauƙin Zaituna ya ruguza komai..............


 *MASARAUTAR SHURAIB*

_______________Ji ya yi wasu hawaye na gangarowa daga cikin idanunsa, ba dan komai ba sai dan tunawa da Sopiyya, ɓata yarinya babu daɗi, amma kwanda shi yasan ta mutu ne amma shi Hamza fa?, A ranan bikin yaransa aka nemeta aka rasa, tin washegarin ranan sauƙin ɓatar ta ya iso gareshi. Kuma yaje amma har yanzu yana cikin damuwa da wannan al'amari.............



__________________Cikin wannnan kogon yake, a zaune yana mai tinanin nan da kwana biyu shike nan ya zama baban mai kuɗi daga nan zai shiga second target na son mallakan kujeran Arman, har ga Allah da biyu yake son Sopiyya saboda tana burgesa sannan yana son kujeran babanta, ya samu nasaran sace ta sai dai Allah ya nufa a ranan wani baban Zaki ya cinye ta, wanda shi kansa ya ga wannan zakin dan da ƙyar ya kuɓuta. Hannu yasa ya warware niƙaf ɗin take fuskar wacce ya sato, take gabansa ya buga dan ganin mace mai kama da Hamza Rasheed.
“Kar ace dai ita ce wacce naji ana cigiya, ƴar shugaban yaƙin masarautar Sayyid........” dafa kansa ya yi yana furzar da iskan bakinsa mai wuce............


*Masarautar Shuraib*

___________________Tin bayan tashi daga faɗa ɓangaren Zaituna ya nufa, bayan ya gaidasu sannan ya zauna akan kujera yana kallon Zaituna da ta fara ƙwararo zance. Tinda ta fara yake jin wani yanayi a cikin ransa.

“Unais lokaci ya yi, lokacin da nake jira ya yi domin ɗaukar fansa, a shirya yaƙi ya shirya babban aikin da ke gabanmu......... Da Sopiyya za mu yi amfani gurin mallakan gaba ɗaya masarautar Sayyid domin ta dawo ƙarƙashin namu. Wannan shine burina a rayuwa, idan ta kana har kan Sopiyya a fille domin aika ma Hamza Rasheed amma sai bayan kujeran ta dawo naka. Ina son naga hawaye na zuba a cikin idon Yayana Hamza Rasheed, zan tabbatar na cika ƴar halak ƴaga Rasheed, Zaituna Rasheed na ke har abada.............” ..................✍️
END.

> Jama'a kaina ya kulle. Mutane uku nake da tambayoyin da zan musu. Ke Uwar mai muƙami (Zaituna) ba fahimci komai ba. Haka Muhajid sai kai uban gayya Unais. Hmmmmmmm 🙄🙄🙄🙄🙄. PRETTYN JAJIRTATTU ✍️🥀.



***

****

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 



E.P2️⃣3️⃣


     *MASARAUTAR SAYYID RASHEED*


_____________________Tabba an ta ɓa raunin Hamza Rasheed, domin yadda yake ji da Ayusha, ba zai manta wunin ranar bikin ya ganta sau uku har lokacin da aka ɗauki amare amma daga nan bai kuma ganinta ba, an bincika an nema kuma yasan Ayusha jarumai ce sosai, domin ranan da suka yi faɗa a ranan ya ƙa tabbatar da cewa shekaru ba baya ba dan sau huɗu ta ci narasa a kansa shikam da ƙyar ya ci ɗaya duk da dama bai nuna mata ƙarfi ba. Ya na da yaƙinin sai dai wani abin aka mata domin dai face to face ba mai iya sace ta.

“Ƙanina! ka rage damuwa ka ji, insha Allah za'a ganta, mun tura cigiyar ta zuwa masarautun da muke kusa.” Sarki Sayyid ya kai ƙarshen maganar cikin alhini sosai.

“Allah Ameen, Yaya zuwa yanzu ban wani damuwa sai dai ina fatan ya sa duk in da take ta zama cikin ƙoshin lafiya.”

“Yau ƙanina, yanzu ka koma gida su Zulfa da suka kama hanya suka zo ma za angwaye su kwashe su su wuce *ƘIRAQ* Sannan a gaidamin Sarki Utubaddeen.”


“To Yaya.” daga haka Hamza ya miƙa ya bar faɗan.


 
   *MASARAUTAR QUMAIZ*

________________________“To shike nan, duk yadda kuka ce, na barku lafiya.” bayan gama jin dogon jawabinta ya bar ɓangaren ya na ji aka na farko da ƙyar ya iya aikata wannan aikin. Yana shiga part ɗin sa, ya kwanta a sofa dan ko bedroom ba zai iya shiga ba. ya jima a ƙwance yana kallon guri ɗaya ba tare da ƙyaf idanuba. Daga bisa kuma a kulle idanunsa. Take ya jiyo muryan Sopiyya tana faɗin.

“Sarki ka dawo.......lafiya kuwa?.” ta tambaya ganin yadda fuskarsa babu walwala. A hankali ya miƙe ya zauna tare da kallon ta. Sanye take da dogon hijab har ƙasa kalan dari blue, ba a hange kalan kayanta domin hijabi ɗin ya rufe komai fuskarta ta hannuta dake ɗan waje ta hannun hijab ɗin yake kalla. Hannunsa ya miƙa mata ba musu ta riƙe take wani abu mai kama da shork ya ratsa kowanne su.

“Are You okay?.” ta kuma faɗa tana da ga tsaye ɗin dai kuma har lokacin hannusa na tare da na juna.

“Zauna.” ya faɗa yana sakin hannunta. A yanzu ko ta zauna a ƙasa sai ya ce ta hau sama dan haka a gefansa ta zauna tana faɗin.

“Na kawo maka magani?.”

“A'a, zan tambaye ki ne.” ta ɗaga mai kai sai ya kuma cewa. “Na rasa me yasa ba ke jikinki a rai na, ban jin zan iya fille miki kai.......” waro idanunta ta yi sai ya ci gaba bayan ya ɗaga mata alamar tabbatar wa.

“Za ki iya fassaramin menene a zuciyata dangane take?.” murmushin gefan baki ta yi tana cewa.

“Bana ce ba, ka tambaya kanka.” 

“Okay, ina ga zan ɓatar da ke in yaso zan dawo da ke bayan burin mahaifiya ya cika akan babanki.”

“Mai kuke shirin aikata mai.” sai ya dake yace.

“Sarautar Yayan babanki zan ƙwace da ƙarfin tsiya, sannan na hau karagar mulkin, fille kanki yana cikin abin da zai haukata Hamza sai dai a madadin kanki nasa zan cire domin kawo ma Mamata, idan masarautar Shuraib ta shiga tsakani har ta kan Arman zan bi, ya zama gana ɗaya arewaci Sarki ɗaya ne.......”

“Shuru. Wai kai mutum ne!? Kisa! Kisa! Kisa! Kaman wani biscuit. Wai me yasa kake son mulki ne?.” ta kai nan har hawaye na zubo mota dan jin sunana mahaifinta a list ɗin sa.

“Saboda Izza, ji da kai.”

“Mai Babana ya muku haka da tsanani.”

“Hmmmmmmm Fansa ke ci a zuciyar mamata, dole na wanke mata da jinin Hamza Rasheed domin ramuwar gayya ta fi zafi.” rintse idanunta ta yi sai cikin ƙarfin hali ta ce.

“Mai aka mata.” sai da ya furzar da iska sannan ya ce.

“Ba yadda mutum zai so ace an kashe jininsa, haƙuri za ki yi domin ita wacce ta sani suma jinin ta ne. Sayyid da Hamza duk yayanin Mahaifiyarta ce, Uwa ɗaya uba ɗaya, yadda za ki ji idan sun mutu haka ita ma za ta ji, amma dole na ɗau mata fansa.” cikin mamaki da ke kallonsa tana faɗin.

“Uwa ɗaya Uba ɗaya! To mai ya kawo gaban nan!?.” sai da rintse idanunsa sannan ya buɗe take ta ɗan ja baya saboda kauninsu da suka sauya.

“Hmmmm banyi mamaki ba da ba ki san Mahaifiyarta Zaituna Rasheed a matsayin ƙanin babanki. Hmmmmmm labari ne mai tsayi mai ta ɓa zuciya sannan labari ne mai cike da buri, wanda har zuwa yau Mahaifiyata ta ce da burin ganin ta halaka Sayyid da Hamza ko da ƙarshe aikin da za ta aikata ne.........”...........✍️
END.

> Zaituna Rasheed!?🙄🥺.


***

****

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 




🌙🕌🌹⭐🕋اَلّٰلھُم  صَلِی عَلٰی مُحَمَّدٍ وَعَلٰی آلِ مُحَمَّدٍ کَماَصَلَّيتَ عَلٰی اِبْرَاھِيمَ وَعَلٰی آلِ اِبْرَاھِيمَ اِنَّكَ حَمِيدُ مَّجِيدُُ❤️🥰

*____________________________ PRETTYN JAJIRTATU ce...............✍️✍️✍️✍️✍️

Sakeenat Abdullahi 🥰
     *Pretty SK Noverlist....... ✍️*

      *THE SLAVE*
 Labari ne mai cike da......
*Tausayi* 
*Mugunta*
*Zalinci*
*Cin amana*
*Yaudara* da kuma...... *SOYAYYA 💘.* 
   
    ______ Labari ne na wasu ƙabilan Larabawa a zamin da. Ƙagaggen labari ne, ban yin dan cin zarafin kowa ba, idan kunga ya yi kama da rayuwarku, to ki yi haƙuri, sharrin alƙalami ne.


🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹






E.P2️⃣4️⃣.


   *YAKIN ƘIRAQ*
*Masarautar Afzar* ƙarƙashin mulkin *Attubaddeen Safraz*


______________Ƴam mata biyu ne zaune a wani ƙawataccan parlour, gaba ɗaya jikinsu a mace yake, ɗaya daga cikin hawaye ne ke zubowa daga idanunta. Gƴaran murya suka ji dan haka suka gyara zama tare da sanya ɗan natsuwa a tare da su. Bayan wannan dattijon ya zauna sai Zulfa ta ce.

“Allah ya ja kwana Sarkin mu mai muƙamin, dama saƙo ne daga Abba ya ce mu miƙa mai gaisuwa ta musamman gareka.”

“Ma sha Allah, na za ci sai dare za su kawo. Ku yi haƙuri insha Allah in rabo ce za'a ganta.” ɗaya ta amsa amma bangane Wacece ba dan kaman kuka. Nasiha ya ƙara musu sannan suka shiga ciki, har ransa yana farin ciki da samun su a matsayin sirikansa. yaransa uku maza Safraz wanda ake kira da Mahir saboda jarumta kuma sunan kakansa ya ci, shine mijin Nasiba, sai na biyu Ka'ab shi kuma shine ya aura Zulfa, sai autansu Malik wanda yake karatu. 


_________Massarauta ce babba mai wadatan komai, rayuwar ba takura da salama suke yi, akwai peace ana unity sosai, ta hangen fuskokin su za ka fahimci ba su da wani damuwa dan Allah yana su komai, a wannan lokacin idan ka rasa mayaƙa to karasa komai, suna da mayaƙa masu zafi ciki harda babban ɗansa da ƙaramin, na tsakiyan sai dai ya shiga tawaga amma Malik da Safraz suna shugabantar wajen yaƙi.




   *MASARAUTAR SHURAIM*

____________________Misalin 2:23am na dare, Muhajid ya miƙe daga kwanciyar da yake, a hankali ya fito parlour amma baya jin motsin kowa, yana isa bakin ƙafa har ya sanya hannu zai buɗe ya ji maganar Abu-Muhajid.

“Ina za ka je?.” cak ya tsaya tare da juyowa, sai ya fara kame-kame, dan Baban nasa ya hanasa zuwa wani masarautar domin ɗan hatsaniyar da ke faruwa.

“Zan.....zan duba abu ne.” a kallo ɗaya yana gane bai da gaskiya.

“Ina faɗa ma ka daka dinga jin tsoron Allah, na kan rasa mai yasa a cikin kwanakin nan in na hanka hankalina ke tashi, kamar akwai wani mugun abin da kake aikatawa.”

“A'a wallahi ni kuma, ban yin komai, na ma fasa fitan.” ya faɗa yana koma wa cikin ɗakinsa. Abu-muhajid ya girgiza kai sannan ya sanya ƙwado a ƙofar tare da ɓoye key ɗin. Yasa dalili amma yaga Muhajid ya sauya mai shi yasa in ya jima bai gansa ba sai ya sa an nemo sa, shi dai kawai ya dinga ganinsa a kusa. 


________Yana shiga ɗakin, ya kifa kansa akan katifa yana mai danne zuciyarsa.

“Badan da kai zan yi tirget akan Mulkan Sarautar Arman da na yi ajalinka domin zan iya aikata komai ba wanda zai ruguza min mafarki.



*MASARAUTAR QUMAIZ*


______________Shuru ne ya ratsa babban parlour, kowa da abin da yake tinani, shi ya na tunanin ai dole ya ɗau mataki ita kuma tana tunanin saboda abin da ya faru shine Zaituna take son ya ɗau mata fansa. A hankali ta janyota kusa da ita sannan ya ce.

“A karo na farko ina son na haɗa shimfiɗa da ke, ban sani ba ko yanayin da nake ji soyayya ce, amma a yau ina son na kasance da ke.......”

“Baiwa ba ta dace da Sarki ba.”

“Nasa ni, amma ƙaddara ta ce hakan, na zauna da Baiwa.” ganin kaman ya fara fita da hayyacinsa dan sai faman shinahina ƙamshin da ke fita a hijab ɗin ta yake. Da sauri ta miƙe tare da barin wajen ta shige room, tsayawa ta yi ƙarjinta na bugawa da ƙarfi, girgiza kai ta fara yi tana magana a hankali.

“Ban shirya zaman aure da kowa ba, ina son dai na sanya soyayyata a cikin ranka sannan na yi sauya tinaninka daga baya ka sake ni na koma gun Abbeey shi ya aurar da ni.”

'To idan ya nema haƙƙinsa ta ƙarfi ba!?' zuciyarta ta tambayeta sai ta zauna a ƙasa tana tattare hijab ɗin, kaman an tsunguleta ta haye katifa tare da shigewa duvet dan wani sanyi take ji na ratsa ta..................✍️
END.


> Au da gaske Sopiyya, nima zan so burin ki ya cika. *Muhajid* ina son na maka nasiha gaskiya. Yau ko Masarautar Sayyid ba mu leƙa ba ma🙄.


***

****

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 






E.P2️⃣5️⃣.


   *MASARAUTAR QUMAIZ*
_____________________________________________________________________________Sautin kimanta ne ke fita a hankali kamar tana rera waƙa, abubuwa.da yawa sun haɗe mata fiye lissafi ba kamo take tunawa ba sai daren jiya. Daren ya Unais ya mai da ita cikakkiyar matar aure, tabbas ba ta mai gaddama ba amma har ga Allah ba ta so faruwar wannan al'amarin ba. Wasu hawaye ne suka kuma gangaro mata, gaba ɗaya jikinta ya yi tsami har zazzaɓi take ji, a lokacin Mama ta shigo ɗauke da plask na ruwan zafi, haɗa mata tea ta yi da ƙyar Sopiyya ta sha.

“Sannu, ga maganin nan Sarki ya ce kisha.” ba musu ta sha tana kuma kwanciya. Har ga Allah Mama ta yi farin ciki da afkuwa sunna tsakaninsu. A kallo da ta ma Sopiyya ta gane haka, ita ta taimaka mata wajen gasa jikinta. 

“Yanzu zazzaɓin zai sauka insha Allah.” kai kawai Sopiyya ta ɗaya mata............


_____________Wani annashuwa ne yau ya tsinci kansa da a ciki, daga abubuwan da Sopiyya ta faɗa mai bayan ya matsa kusa da ita jiya.

“Bawai banson haɗa shimfiɗa da kai ba ne, kawai dai kai kanka kana buƙatar tsaftan ruhi.” a lokacin jinta kawai yake dan baya cikin wannan duniyar sai dai mai da yawa maganganun ta na cikin ransa. A karo na farko da ya fara afuwa ga mutane, duk wanda ya yi abu sai ya ce kubarshi. Ba wanda bai yi mamakin haka ba sai dai suka share dan babu mai iya tambayan dalili.

“Yallaɓai yanzu mai kai saƙo zai nufi kai saƙonka wajen Sarki Sayyid.” kai kawai ya ɗaga.



__________"Uwar mai muƙami, yanzu saƙon ya bar masarauta ya nufi wajen Sarki Sayyid Rasheed.” murmushi ta yi sannan ta ce.

“Yauwa saura muji amsarsa.” ta faɗa jiji da kai tare da tina baya........

    *Flasja back.*

Shekarun baya Masarautar Sayyid Rasheed, a lokacin Rasheed Zuhair ne ke Mulkan ƙasar, Rasheed mutum ne mugu mai mugunta, mulkin zalunci shine aƙidarsa, ba tausayi babu tausayawa haka yake aikata duk abin da ya so. Allah ya bashi yara uku, maza biyu mace ɗaya, Sayyid da Hamza sai ƙanwarsu Zaituna, sun taso ne tare cikin ƙaunar juna, sai dai tin bayan mallakan hankalin Sayyid da Hamza suka gane mahaifinsu ba akan dai-dai yake ba, sunyi ƙoƙarin sauya mai tunani amma hakan ya gaza, sannan Zaituna babu abin da ta bari na daga halin mahaifinsu, har Rasheed ya kan ji dama ita ce namijin su kuma maza. Faɗa ce - faɗa ce sosai ake yi a cikin gidan Sarki akan yanayin mulkin Rasheed, ganin haka Sarki ya sallama su tare da janyo Zaituna ita kaɗai a jiki. A ɓangaren su Sayyid shawara suka yi shi da Hamza, sannan suka yi amfani da wannan damar cikin sa'a suka yi nasara. Wannan shine mafarin komai da komai.


______________Bayan sun bar gidan sai suka dawo tare neman gafarar Rasheed, ba wani yi ja'inja da yawa ba yafe musu tare da dawo da su gida. Bayan sun kai wasu satittika a gidan suna zauna tare da shirya ma sarki zance, cikin farin ciki ya yi na'am da maganar su. Ba wasa aka sanya lokacin bikin Zainatu dan so suke su fara rabata da mahaifinsu. Wata rana, bayan Zaituna ta shirya cikin shigarsu da niƙaf ɗin su, dan ko da wasa ba sa fita babu hatta a cikin gida kuwa hmmmmm in ta ƙaice muku har tsakanin ƴan gidan sai dai in mata zalla ne kuma da daddare shine sukan cire, to an sama har barci yi suke da shi.


___________Ta zo dai-dai bakin ƙofar ɗakin mai martaba kawai ta tsaya cak dan jin abin da Sarki Rasheed ke faɗa cikin ɗaga murya.

“Na zaci kunyi hankali, ashe ba haka bane, to ku sani na yafe ku daga yarana sannan Zaituna ita na ba wa kujerar mulki, gobe zan sheda hakan ga kowa na ƙasar nan.” zaro idanu ta yi dan farin ciki ya mamaye ta.

“Baba mu ba wani abu mara ƙyau muke faɗa maka ba, kawai ana zalunci ne fiye da misali, haka ɗazu ka sanya ake wasu ba tare da ƙwarƙwaran dalili ba.” Sayyid ya faɗa cikin baƙin ciki sai Hamza shima ya ce.

“Haka ka ce?.”

“Eh haka ne ce kuma bazan canza ra'ayi na ba.”

“A'a Babanmu, kar na aikata abin da ba za ka so ba.” ganin hayaniya na tashi ya sa Zaituna shiga da sauri, da yake ba wani ƙaunar juna tsakanin su ta ce.

“Me kuke cewa? To wallahi in wani abu ya samu Mahaifina kune abin zargi.” Hamza dake tsaye ya zaro wuƙarsa yaƙi mai shegen ƙyalli ya ce.

“Idan har bai yadda da abin da muka ce ba to dole mu...... Hmmmmmm kun gane ai.” yakai maganar yana shafa wuƙan.

“Kar ka fara wannan tunanin, ba zamu yadda ba......” da sauri ta haɗiye sauran maganar ganin Hamza ya sanya wuƙan akan wiyar................✍️
END.


> 🙄