Labari ne mai cike da...... *Tausayi* *Mugunta* *Zalinci* *Cin amana* *Yaudara
PAGE2️⃣6️⃣⏩3️⃣0️⃣
by @prettys01
E.P2️⃣6️⃣
*MASARAUTAR QUMAIZ*
________________Da sauri Sayyid ya kasa da sauri dan Hamza akwai zuciya fiye da misali, a hankali ta kuma haɗiye wani miyau, dan a kan wutanta ya ɗaura wuƙan.
“Ki bi a hankali.” daga haka suka bar ɗakin, jiki a mace ta kalla Sarki Rasheed ta ce.
“Zuwa gobe zamu ɗau mataki akansu.” haka dai suka rabu a kan zuwa zasu kora su Hamza, sai dai abin mamaki zuwa wayewa gari Sarki ya mutu. Mutuwar da kusa haukata Zaituna, babu wanda ta hararo ya kashe Babanta sai *Hamza*, daga nan gabar ta so ma, daga jini ɗaya a ka komai maƙiyan juna. Haka dai kwanaki suka huce, lokacin na ɗin sabon Sarki ya yi ta ce ita ce za ta hau, a lokacin an sha rigima sosai dan haka ba ma ta sani ba Sayyid ya ɗaura mata aure tare sa a bar Jahar da ita, a lokacin haɗiyan zuciya ne kawai ba ta yi, sannan ta yi alƙawarin ɗaukan ma Babanta fansa da kuma Mulkan kujerarta. Bayan ta bar Jahar Sayyid Rasheed shi ya amsa bisa jajircewar Hamza. Kuma suka mai da wajen mai zaman lafiya da mulki na ƙwarai.
*Continuation of Zaintuna's Flash back*
*MASARAUTAR SAYYID RASHEED*
________________Zaune suke gaba ɗayansa a cikin fada a lokaci ne wanda aka aiko daga masarautar Qumaiz ya iso, bayan an gama gaisawa da shi sa'an nan ya mika wannan saƙon da aka aiko mai shi, bayan sarki ya umarta da a amsa ya saka a karanta mai cikin daga murya, ɗaya gada cikin na wajen ya amsa tare da buɗewa ya fara karatu kamar haka.
“Assalam salamu alaikum, wannan sako ne daga ni Sarki Unais, ban zo da sigar faɗa ba, haka zalika ban zo da siga roko ba kusan dai zan iya cewa umarni nake baku don ceton ranku da sauran mutanen cikin ƙasarku, nan da kwana biyar ina so ku bar wannan ƙasar ku bani kujeran mulkin ta domin ni na mulke gaba ɗaya, amma idan ba ku ji ba tofa,ku shirya wa yaƙi. Sako daga ni Sarkin Qumaiz Sarki Unais Abba Ali.” wani murmushi sarki Sayyid ya yi tare da uwarta a rubuta mai.
“Ba gudu ba ja da baya, lokacin ɗaukar fansar Zaituna ya yi amma ta sani da Allah muka dogara.” abin da ya faɗa shi aka rubuta tare da juyawa dan nufan Qumaiz, shuru ne ya ratsa faɗa, dan har ga Allah Qumaizawa sun fi su mayaƙa, da sauri Sarki ya kuma aika saƙo zuwa ga Arman.
*MASARAUTAR SHURAIM*
_______________Ko da saƙon Sayyid ya iso ma Sarki Arman, murmushi kawai ya yi dan dama wannan lokacin yake jira na ganin bayan Unais da duk masu baƙin hali a wannan tafiyar.
“Fatan mayaƙan mu na nan domin lokaci ya yi.”
“Eh Asalin Sarki.” daga haka suka dinga tattaunawa akan yadda tsarin yaƙin zai kasance. ɓangaren Abu-Mujahid kuwa ya hana shi fita baya zuwa ko ina kullum yana zaune a cikin gida domin har ga allah bai yarda da shi ba amma yanzu da aka yi maganan yaƙi dole ya barshi domin shima ya na ɗaya daga cikin mayakar da ake fita dashi dole a dinga bari yana fita don ɗaukan karin horon yaƙi.
________kwance yake a kan kujera amma tunani yake yi barkatai a cikin kanshi, yana tunanin izuwa yanzu ya kamata ace ya mallaka abin da yake maradi sai dai mahaifin shi yana ta kawo mai cikas, haƙuri kawai yake yi ba don ya so ba amma yan jiran haƙurin nashi ya cimma wani abu ne daga dangane da masarautar Shuraib. Dai-dai wannan lokacin mahaifinsa ya shigo gidan, bayan ya shigo ya zauna akan kujera yana sai tin kallonsa ya ce.
“Ka shirya zuwa gobe akwai fita domin fara horo za'a yaƙa masarautar Qumaiz don haka kamai da hankali kasan kana ɗaya daga cikin wadanda ake ji da su a cikin mayaƙa, dan Allah kamayar da hankali, na rasa mai yasa na ke ji kamar kana aikata wani abu a ɓoye haka ina ji a jikina baka aikata abin da ya kamata ka dai kula.” sannan ya tashi ya bar mai parlour, sai a lokacin ya buɗe idanuwansa ya saki murmushi da shi kaɗai yasan ma'anar sa, ɗakin sa ya koma yana kwanciya a kan kati.
Ji
“Da wannan ni zanyi amfani domin cimma buri na insha Allahu." Ya sa izuwa yanzu duk ƴan matan wajen nan sun galabaita matuka, yunwa ta gama kaddara su duk da ma dai yana ba musu kwayoyin bacci haka na taimaka ma jikinsu amma yasan duu sun yi weak sosai, yana fatanan nan da kwanaki biyu ya isa yankin Ƙiraq domin da kai su in da ya dace............✍️
END.
E.P2️⃣7️⃣.
*BAYAN WATA ƊAYA*
__________________Abubuwa sun faru da dama, na farko an tsaida lokacin yaƙi tsakanin Masarautar Sayyid Rasheed da Masarautar Qumaiz, sai dai shi Sarki Unais bai san cewa Sarki Arman da Sarki Sayyid sun haɗa kai ba haka kuma Sarkin Ƙiraq wato Sarki Utubbadden Safraz ya shirya taimaka musu ba. A yau ake da fita yaƙi sai dai mai Sopiyya ta shiga ransa, sannan ya mata alƙawarori wanda har ya fara cika mata wasu sune, rage zalunci da mugunta, dan dai wannan shine burin mahaifiyarsa da ya haƙura saboda Sopiyya. Tsaye yake cikin kayan yaƙi, sannan ya ɗauka doguwar takobin sa haka bayansa yana ɗauke da kwari da baka. Kallon juna suke yi kallo ne wanda kowa ke aiyana abubuwa a cikin ransa, Sopiyya dake tsaye gabansa tana ayyana kafin ya dawo daga yaƙi akwai gyaran da take son yi, domin a yanzu Zaituna ce kawai Mama ta mutu tun kwanakin baya.
“Ka kula.” ta faɗa tana juya sai ya riƙon hannunta tare da kiyo da ita.
“Kina so?.” ɗan murmushi ta yi dan tin da ya kamu da soyayyarta shike nan kullum cikin tambayanta amma sai ta ce sai ranar da ya sauya shi yasa yake ɗan rage zafi wa mutanen Jahar. Runguma juna suka yi na ɗan lokaci sannan ya sumbaci goshinta ya yi waje. Murmushi ne kwance a fuskarta har ya ɓace mata, take ta haɗe rai dan har ga Allah ko kaɗan ba ta jinsa a ranta. Tarko ta yi kuma ya kama ai shike nan.
_______________A filin gidan Sarautar ya tadda Uwar mai muƙami zaune ga bayi ne wasu ana musu hukunci da bulalan inji, yana isa mutanen wajen suka gaishesa, ya amsa sama-sama tare da ma Zaituna bankwana dan a ƙalla za su yi sati daya zuwa biyu.
“Ɗa na Ina maka fatan samun nasara, ka tawomin ƙoƙan kan Hamza.” jinjina mata kai ya yi sannan ya yi gaba, yana fatan kar Sopiyya ta fito ko da daga ɓangarensa ne domin umarnin Zaituna ne ya kasheta tare da tura gawarta, sai ya ce ya yi kawai, dan a yanzu ba ya jin zan iya kashe Sopiyya da duk wanda bai yi mai komai ba.
*MASARAUTAR SHURAIM*
____________________________Kallon Abu-muhajid ya yi tare da faɗin.
“Je ka kai mai abinci da ruwa.” Murmushi ya yi yana mai faɗin.
“Shugaba a ƙyalesa, ta yuma zuwa yanzu ya mutu.”
“A'a ɗan kane shi, ko yaye ne akwai wannan soyayya a cikin ranka, jeka duba shi.” jinjina kai ya yi tare da barin Sarki a tsaye a wajen dawakai. Shi harga Allah ya sallama Muhajid na har abada dan ko tausayin sam ba ya ji, ace mutum arziƙi ne zai yi sanadiyyar mutuwar ƴam mata 19. Tsaki ya ja yana mai tinawa da a ranan da ya uwarci Muhajid ya je filin yaƙi.
_________Yana lura da shi duk motsinsa na kan idon Abu-muhajid, wasa-wasa har Muhajid ya gudu, ba sanya Abu-muhajid ya dinga bin bayansa a ɓoye har zuwa wani waje da yaga ya shiga, bayan an jima ya fito, haka dai aka jera kwana Uku, a ranar na huɗu ne cikin dare ya fice wani leƙen doki na ɗaukan kayayyakin siyarwansa ya nufa wajen, sai dai ya duba yaga babu mace ko ɗaya a wajen, take hankalinsa ya yi mugun tashi, tana fitowa daga ciki ya tadda Jami'an Masarautar sun zagaye sa, babu ɓata lokaci aka kaisa wajen Sarki, tare da nuna mai ƴammatan 19 sun zama gawa ɗaya ce mai rai a ciki, daga nan ɗakin duhu aka kaisa in da anan zai ƙare rayuwarsa babu ci babu sha. Sai bayan da aka ɗauresa Abu-muhajid ya je wajen shine yake faɗa mai shine ya tona asirin sa. A ƙalla anyi sati biyu da faruwar haka, amma duk bayan kwana Sarki sai ya sa akai mai abinci. A karo na ba adadi ya kuma jan tsaki dan har Allah ba ya son ganin Muhajid.
_________Zaune yake cikin wani ɗaki mai shegen duhu, ba abin da yake yi, sai mafan ihu kaman mahaukaci, take haske ya gauraya ɗakin da sauri Muhajid ya kulle idanunsa dan ya jima bai ga haske ba, ganin mahaifinsa ta waje yasa ya miƙe da sauri yana magana da ƙyar.
“Abuna ka zo, kasan menene tintuni nake son ka zo dan na faɗa maka wani abu, ka naji?.” ya yi maganar cikin dasashshiyar murya. Girgiza kai Abu-muhajid ya yi yana kallon yadda Muhajid ya zama ƙaramin mahaukaci.
“So nake ka zama Sarki, ina so mu kashe Arma dan mu mulka tare, sai dai kaina ina so na kashe ka amma bazan iya ba saboda da kai zanyi amfani wajen kashe Arman, tinda na dubara ta farko ta rushe akan Sopiyya.” sai ya hau tari ganin Muhajid kaman bai san yana sakan layi ba yasa Abu-muhajid ya ce.
“Shine tintuni baka faɗa min ba, mai ka fara yi akan Sopiyya ɗin.” sai da Muhajid ya zauna sannan ya ce
“Sace ta nayi dan na aurenta tinda ka ƙi min hanyar auren ta, dama niyyata na aurenta dan na zama Sarki, sai akai rashin da ce ta ɓaci min a hanya, hmmmm.” Abu-muhajid ya dafe kansa yana kuma kallan ɗan sa ya zama dodo a fuskarsa.
“To su ƴam matan ina za ka kaisu dan samun kuɗin sai na kwashe su na kai su.” murmushi ya yi sannan ya ce.
“Ƙiraq, a wani mai suna Ibrahim Quraish, yana sai da kayan abin ci a kasuwar Lafti, shike siyan mata domin turasu wani waaaa.....waje....w.” sai da Abu-muhajid yana baya ganin take Muhajid ya hau shure-shure, da sauri ya yarda kwanan hannunsa ya buɗe wajen tare da shiga. Sai dai Muhajid ya mutu a lanƙwace kaman tantabara. Da sauri Abu-muhajid ya fice dan kiran masu tsaron wajen, tabbas ya mutu suka tabbatar mai da haka, zaman ƴan bori ya yi dan har ga Allah abubuwa suna tsaya mai rai tare da rasa menene mafita. Shuru ya yi ko magana ya kasa, duk wanda ya gansa sai yace saboda mutuwan ne amma shi ina abubuwan da ya faɗa suke mai yawo a cikin ransa..............✍️.
END
> PRETTYN JAJIRTATTU ✍️🥀.
E.P2️⃣8️⃣
*MASARAUTAR SHURAIM*
______________________________________________________________________________________________Tare da Sarki aka jagoranci sallace Muhajid, sai dai Abu-muhajid ya ki mai sallah, haka aka kai shi sannan suka dawo, a lokacin suka haye dawakai dan tafiya filin waƙi da ke can gabashi, wani babban fili wanda ake yaƙi a cikinsa. Tafiya suka yi suka bar Abu-muhajid, wanda har lokacin ya kasa ƙwararran motsi, sai bayan sun yi nisa tukun ya hau ta sa dokin tare da nufa wani waje.
__________A gidan sa kuwa, duk yadda mahaifiyar Muhajid ta so daurewa sai da ta yi kuka, haka Bintu, addu'a kawai suke mai na neman gafara. Zaune suke Sudan wasu ƴan uwansu larabawa, duk suna sanye da hijabai ne gajeru. Bintu ce ta miƙa jiki ba ƙwari ta shiga ɗalibta, kwance ta hanga wata mace kusan sa'ar ta, ƙara sawa ta yi tana kallon fuskarta yadda take barcin wahala.
“Allah sarki, ko a ina ya samomi oho.” ta faɗa tana gyara mata kwanciya tare da rufe mata ƙafafu.
*FILIN YAƘI*
________________Baka ganin komai sai na ɗaɗen ƙurar ƙafan dawakai, ɓangaren uku ne wanda ya haɗa hanyoyin masarautun, duk kuma suna ɗauke da tuta launin Jahar sa. Mamaki ne kwance akan fuskar Unais ganin tawagar Arman, bayan shi da su Sayyid kawai za su yi faɗa. Daɗinsa ɗaya tawarga suna da yawa amma idan wa'in can suka haɗu to dole acisu dan sun fisu yawa.
Mutum ɗaya Unais ya aika wajen Sayyi da takadda, ya na tsaye har ya dawo tare da faɗin.
“Sarkina ya karanta sai dai ya ce, na ce ma wannan shine tsarin, kawai mu shirya.” murmushi ya yi dan yasan ko ba su yi nasara ba zai yi ƙoƙarin cire kan Hamza tare da Sayyid, in ya so harda Arman ɗin tunda yasan kaf cikinsu babu mai iya kashe sa. Hatta Hamza kuwa........
*MASSARAUTAR QUMAIZ*
____________________Jin ta take a wani irin farin ciki mara misaltuwa, cikin izza da ɗagawa ta ke kewaye masarautar tana yadda take so. Take ta ji amsakuwar masarautar na fitar saƙo da ƙarfi wanda duk wanda yake Jahar dole ya ji.
“Ye kuwa jama'a, Sarauniya Sopiyya mata ga Sarkin mu, tana neman kowa, hatta ƴan kurkuku, kowa da kowa.” haka ya yi ta shela, baki ta buɗe tana faɗin
“Ba ta mutu ba?.” amma babu mai ba ta amsa dan haka ta nufi wajen da tabbas a can za'a yi taron. Da isarta ta ga mutane har sun kusa cika, dan ko mai mutum yake in aka yi wannan kiran to da gudu za ka ga mutane.
Zama ta yi a wajen da take, take Sopiyya ta bayya cikin wasu arnan kaya, doguwar riga ce wacce ta amsa sunan na Sarakai, ganin Sopiyya ya sa Uwar mai muƙami waro ido, dan ganin wacce ta sanya a kashe kuma a ce an kashe.
___________Babu ɓata lokaci ta matsa jikin mic ta fara gaisuwa tana mai fara kwararo zance.
“Sarki yaban riƙon ƙwarya, kuma nayi alƙawarin cike duk wani abubuwa da ya kasa cike wa. Ina kundin dokar da ake amfani da shi?.” ta yi tambayar tan kallon Zaituna da ke ƙoƙarin miƙewa sai Sopiyya ta ce.
“Karki tashi, ban kuma san ki ce komai, wannan Ni Sarauniya na ke faɗi.” Gyara zaman ta yi tana mai mata wani irin kallo. Babban littafi aka miƙa mata sannan ta amsa tana bawa na gefanta masu taka mata baya ta furta.
“Ashanar da na uwarci ka ɗauki, ma za ƙona.” mamaki da tsoro ya kuma kallon ta sai dai hannunsa rawa yake dan haka ta amsa ashanar ta ƙyesta ma ya hau ci, ba mutane kaɗai ba hatta ni sai da na waro idanu dan kowa na wajen ya tsorata sosai.
“Daga yau wannan dokar ce za ta fara aiki.” da sauri Mama Jakaddiya ta mike mata wani littafin doka wanda ta rubuta da hannunta. Miƙa wa ta yi sannan ta umarci da aka karanta musu. Wani ne ya zauna ya karanta tsaf duk da yawansa, karatu yake amma hawaye na zuba daga idanunsa badan komai sai dan wannan takarda opposite wanda aka ƙona ne. Take kuma aka fara aiki da dokan, wajen ta bari sannan ta nufi cikin unguwanni, in da take ta rabon abinci, tare da saura ma wasu muhalli, gaba dai a wunin ranar mutanen Qumaizawa sun samu sauyi wanda suke fatan ya ɗauke, da ya sun samu ƴanci, ta ƴanta wasu, ta yafe ma su laifukansu daga wajen huƙuba. Duk in da ta bi sai addu'a ake mata da Sarki dan ta ce shi ya ce ta yi duk abin da take yi. Sai yamma ta koma ɓangaren ta, tana shiga ta tadda Uwar mai muƙami zaune tana jiranta, bayan ta shiga, ta zauna kan kujera suna kallon juna.
“Fatan ba ki jima da nema na ba?.” Zaintuna da take gab ta ce.
“ *Baiwa* ce zan tsaya jira, na zo ne na nuna miki kinyi kuskure, wannan babban laifi kika aikata, sannan na yi mamakin ganinki dan na uwarci da aka yanke miki kai.”
“Au da na yi mene?.”
“Saboda ke ƴar Hamza Rasheed ce.” dariya Sopiyya ta yi sannan ta ce.
“Daga faɗa sai ku yarda, to ba haka bane, Ni da kike gani sunana Sopiyya Arman Shuraibawa ce, ɗaya ga sarki Arman, Gimbiya Sopiyya.” daga haka ta shige ɗakinta, da idanu Zaituna ta bi ta yana faɗin.
“Ko na yi kama da abar wasarta ce oho.” dan maganar a wasa ta mai da shi, daga haka ta bar ɗakin.
Washegari misalin 9:10pm, Sopiyya ta umarci duk mai buƙatar ya bi ta, subar masarautar to suje. An sha muharawa daga bisani ta ce.
“Ba da sanin Sarki Unais na aikata aikin jiya ba, ku yadda da ni, mubar mai masarautar nan, dan tsiratar da rayukan mu.” sai wani a cikin taddijai ya ce.
“Ƴar nan ina zamu to?.” murmushi ta yi sannan ta ce.
“ *Massarautar Shuraib*.”...........✍️
END.
E.P2️⃣9️⃣
____________________________Wannan filin babu kowa a ciki, haka nan babu alaman an yi wani hargitsi a wajen, sai dai sahun dawakai kawai dan hatta ƙura tashi take yi alaman ba'a jima da barin wajen ba.
> Toh fa ina suka je? 👇
________________________Bayan ya sha doguwar tafiya sai wajen yamma ya dawo masarautar a gajiye, harga Allah wani sanyi-sanyi yake ji a cikin ransa, bayan ya zauna Bintu ta kawo mai ruwa ya amsa tare da sha, lumshe idanunsa ya yi yana hasaso tafiyar da ya sha ' _Bayan ya fita bai tsaya a ko ina ba sai Jahar Ƙiraq - Masarautar Afzar, amma bai samu Sarki Attubaddeen Safraz ba, sai yaronsa Safraz, bai ɓata lokaci ba ya faɗa mai abin da ya kawo sa. A lokacin ya yi mamaki ganin Safraz ya cemai ai sun halakashi kwana biyu da ya wuce saboda asirinsa da ya tono. Ya ji daɗi dan haka bai jima ba ya ɗauko hanya, sai dai baiga kowa a filin yaƙi ba haka yanzu da ya dawo bai ga su Sarki ba. Harya kulle idanu ya ji hayaniya sosai daga waje, yasan shine babba tinda Sarki baya nan dan haka ya miƙa tare da fita, haka su Bintu na bayansa.
_____________Ganin mutane da mugun yawa a cikin masarautar kaman ƴan gudun hijira, yasa ya fara tambaya.
“Daga ina haka?.” sai dai babu wanda ya yi magana har ya isa tsakiyar su, take suka yi ido huɗu da Sarauniya Sopiyya, wacce take tsaye tana cikin shiga na alfarma, baki ya buɗe tare da zare idanu yana faɗin.
“So.....so.... Sopiyya.” da sauri ta rungumesa tana cewa.
“Abu-bintu na dawo.” Bintu ita ma dake gefe ta matso dan tabbatar da wanda idanunta ke gani. Irin shork ɗin da Bintu ta yi sai ka sha mamaki, sun jima ana ɗauki ta sosai tare da yin shela, sai a lokacin mutanen da suka zo suka fahimci wacece Sopiyya.
“Ye kuwa jama'a, ku fito ma za ku fito, Haske lantarkin masarautar Shuraib ta dawo....... Nace ɗiyar Sarkin mu mai adalci ta dawo bayan lokaci mai tsayi...........Gimbiya Sopiyya Arman.” mamaki ne ya cinye su uwa tawagan suna kallonta, sai ta uwarci da a bazu wajen kwana zuwa gobe kuma a neman musu muhalli domin gudun hijira muka yi.
Labari ta ba Abu-muhajid da mutanen da suke kallonsu, sun sha mamaki da ta ce daga masarautar Qumaiz ta fito lafiya. Murna ƙalilan ta yi dan har lokacin Sarki Arman basu dawo ba.
________________________________________________________________________________________________________Babu motsin komai a wajen sai kukan tsuntsaye da ke tashi a hankali, jama'a ne iya jama wajen, duk suna zazzaune, sai daga can gefe in da aka ƙawata shi tare da sanya tantina akan zagaye gefe da gefen, ba wani ɓata lokaci na nufi wajen kai na tsaye, tsayawa na yi cak dan ganin Sarki Sayyid Rasheed - Sarki Unais - Sarki Attubaddeen Safraz da Sarki Arman Yusuf da wasu mutum biyu wanda suma zance Sarakai ne domin shigarsu, daga gefe kuma Hamza Rasheed ne tsaye hannunsa ɗauke da takobi. Ban iya jin komai daga in da nake ba sai bayan da na isa kusa da su, take na ji muryan Sarki Attubaddeen Safraz yana faɗin.
“Mu baya a, yanzu za ta soma.” take naga ya sanya hannu akan table, ba wani ɓata lokaci, Sarakai biyun nan suka ɗauka nasu akan na Attubaddeen, sai shima Sarki Arnan Yusuf ya aza nasa, sai kuma ana ɗan tsagaita sai Sarki Sayyid shima ya ɗaura, ko a yanzu sun cinye sa, domin sun fisa yawa daya ɗauka da karya ɗaura doka dole ta zauna, hakan ya sa ya ɗago fararen hannunsa ya aja akan na yayar mahaifiyarsa, wani yanayi yaji na sanyi na ratsa shi, duk da a yanzu amfaɗan mai abubuwa da yawa amma abu ɗaye ke cikin ransa, ɗazu da Hamza ke ce mai.
“Shin ka ta ɓa ganin Ɗa ya kashe Ubansa, koda kuwa maƙiyan juna ne, duk bagune ko za su tsorota amma ina. Zaituna ta za ci nina kashe Babanmu, hmmmm ba cin wani hadimi ne, bawai ina faɗa ma bane dan ka tausaya min a'a, kawai ya kamata kai ka zama namiji ba komai ne zai shiga jikinka ba.” daga bai kuma ce mai komai ba, sai a lokacin shima Hamza ya ɗaura na sa hannu, domin an umarci da ya yi hakan. Take kuma aka cire wasu na murna wasu kuwa akasin haka ne. Tunanin abin da ya faru ɗazu a filin yaƙi ya yi wanda da hakan ba ta faru ba, da izuwa yanzu mutane da yawa sun mutu ciki har da Hamza Rasheed.
*Ɗazu*
___________Bayan kowani ɓangaren sunja da ga, sun shirya aikawa, tuta kawai suke jira suka wanda zai fara dawowa daga sama to shine zai fara kai farmaki, gaba ɗaya idanuwansu na kallon sama ne, take ba tsammani sai ga wasu jama'a daga gabashi kan cewan Sarkin _SUDAN_ Sarki Walid bin Khalid na neman tawagun yaƙi yanzu, ba yadda za su yi dan gaba da gabanta, bayan isarsu wajen shine suka tadda Sarki Attubaddeen Safraz dan shine ya kai ƙara. Sulhu aka yi tare da buga dokan tsagaita yaƙi na tsawon shekara 10. An musu faɗa sosai, kana shi da yafi kowa laifi, kowa da abin da yake faɗa akan sa, abin da duk ba su sani ba shine a yanzu akwai abubuwa da yawa da yake gani a matsayin kuskure yake yi, abin haushin dole sai zuwa gobe za su wuce, da ace yaƙin ne zai ɗauke su 1 week domin sai sun fara Mulkan jama'ar Hajar Sayyid ɗin. Furzar da iskan bakinsa ya yi yana mai Zaituna da Sopiyya, wanda in suka ji dole ɗaya ta yi murna ɗaya kuma su samu babban matsala a tsakaninsu..........✍️
END.
> Ammsar mai sauƙi ce, wacece za ta yi murna da faruwan haka? Zaituna 🥺 ko Sopiyya 🤗..
_LAST PAGE_
*GARGAƊI*
ban yadda ko da wasa yani ya sanya ma yaransa wani sunan cikin littafin nan ba, ba tare da neman ma'ana ba, toh na faɗa na fita haƙƙi.
E.P3️⃣0️⃣
*MASSARAUTAR QUMAIZ*
___________________ ya koma tamkar wani daji, saboda shuru ne ta ko ina, a ƙalla mutane a kashi 3, kashi 2 sun bi Sarauniya Sopiyya, tin safe labari ya rika Uwar mai muƙami sai dai a lokacin murmushi ta yi dan tasan dole su dawo, amma zuwa dare, wanda ta aika ya bisu ya dawo mata da wani labarin wai ita ƴar Sarki Arnan Yusuf ce, ana faɗa mata sai da ta wato idanu a lokacin domin mamaki. Haka da mamakin ta kwana, yau kam babu wanda take jira face in Unais bai dawo ba a bishi masarautar Sayyid ɗin, sai dai zuwa yamma gashi sun dawo da tawagar sa. Ji yake abubuwa da yawa na yawo a zuciyanshi, tin daga rayuwar sa yana yaro yake hasasowa, sai dai baya ganin komai sai tsabar mugunta da ya dasa harda kashe yayansa. Ko da yaji Uwar mai muƙami na nemansa bai jeba ɗakinsa ya nufa tare da kullewa, an ji juyun duniyar ya ƙi buɗe wa, a yanzu ji yake tamkar shi kansa najasane, kwana ya yi yana roƙon Allah tuba, dan ko ya kwanta jini kawai yake gani a cikin idanunsa, bai taɓa jin nadama ta sauka mai sai bayan wa'azin da ya sha ɗazu. Bashi ya fito ba sai washegari, a in da ya lura ba mutane sosai a cikin Massarautar, har zai nufi gurin Mahaifiyarsa sai ga ta dan haka ya zauna suka gaisa.
“Ka dawo, kuma yi kwanciyarka, ko dai su Sayyid sun ci galaba akan mune?.”. Sai ya ɗaga mata kai alaman eh. “Hmmmmmm" kawai ta faɗa tana gyara zama sannan ta koro mai zancen Sopiyya, shuru ya yi, sai kawai ya miƙe tare da barin Zaituna a wajen. Dokinsa ya nufa ya ja linzamin tare da barin haraban gidan.
*MASARAUTAR QUMAIZ*
Mutane ne ta ko ina ana harkoki, cike da walwala, hatta ɓaki duk sun saki ransu domin sarki ya yi na'am dasu, dan a jiya da za ka tambayake komai zai baka tsabar murnan ganin Sopiyya. Haka ya kwana da farin ciki mara misaltuwa, a gidan su Bintu ta kwana dan sun raba dare suna hira, anan ne ta ga Ayusha wacce ta ke buɗe idanu akai-akai.
A ɓangaren Sarki take zaune suna dasa hira, ya tambayeta ya aka yi ta ɓa ta, ta ce ba ta tuna komai ta dai san a ganta a cikin Massarautar Qumaiz, labari za ta bashi aka iso da saɓon Sarki wai Sarki Unais ya zo Massarautar. Abbeey ya miƙe ita kuma ta saki murmushi yana gyara kwanciyarta, bayan kaman minti 20, a ka zo neman ta, tasamo dama dan haka ta miƙa ta nufi fada, mutane ne manya-manyan a zazzaune suna bin ta kallo dan kowa ya yi farin ciki da dawowarta.
“Ranka shi daɗi gani.” ta faɗa tana zama gyefan Abu-muhajid, ta jin ƙwayar idanunsa aka ta amma ko gunsa ba ta kalla ba.
“Kinsan wannan?.” sai ta kalla Unais, shuru ta yi sai ta ɗaga kai.
“A ina?.”
“Qumaiz.”
“Waye shi?.” sai da ta yi shuru sannan ta ce.
“Sarki Unais mijina.” ba Sarki ba kowa na wajen sai da ya ji wani shork. Shi kuma Unais yaji wani sanyi a ransa. Labari ta ba sarki na komai da komai sannan ta ƙara da faɗin.
“Karka damu yanzu zai sake ni.” ta faɗa tana ɗage kai sama.
“Wai ma a ina aka ta ɓa irin wannan auren? To yanzu dai ka sake ta kawai, dan ko ni bazan yadda da wanan auran ba.” Sarki Arman ya faɗa yana jin wani iri in ya kalla Unais, ga dai namiji har namiji amma zuciya kamar da yahudawa. An jima ana musu akan ya sake ta shi kuma ya ƙi, ƙarshe dai ya hau dokinsa tare da barin garin.
Ganin ya wuce ta cigaba da walwalarta, a washegari kuma Ayusha ta miƙe harda ɗan yawonta tana zaga gidan, ganin haka sukan hau leƙen doki suke zaga gari.
Faɗa musu ta yi daga in da take, take fuskar Hamza ta haska ma Sopiyya, sai ta ce.
“Ayusha ko?.” cike da mamaki Ayusha da Bintu ke kallon Sopiyya.
“Ya kika san sunana?.”
“A kai mu faɗa.” abin da ta faɗa kenan sannan ak juya leƙen zuwa faɗa, ko bayar isarta, sai ta kuma ganin Unais tsaye daga wajen kallo ɗaya ta har ta zo sai tinsa sannan ta ce.
“Ka kawomin ƙaddan ne?.”
“Har abada ba za ki ko irin wannan paper ba.” tana jin haka ta ƙara gaba shi kuma ya saki murmushi, dan tunawa da jiya. Bayan yabar Massarautar, sai ya tsaya a hanya, a yanzu yasan kowa na masarautarsa a ƙasar suke kuma babu namiji bayan Ni. Take ya tuna kalaman Sayyid na ƙarahe.
“Mu ba yara band, kaje Allah ya shiya mana kai, idan kana buƙatar taimakon mu kawai ka aiko mana, yayen kane” tina hakan ya sa ya nufi wajen su, bayan sun ji ƙorafin shine suka shirya yau suka zo.
Ganin kaman maganar mai mahimmanci suke ya sa ta juya dan fita take ta hanga Hamza Rasheed, ai da sauti ta nufesa, ta ina ta tsugunna ta kai bakinta kunninsa ta raɗa mai abu, musu ya miƙe tare da bin ta. Ganin Ayusha zaune ta zuma ma ƙofar wajen ido yasa ya ɗan ja baya sai kuma ya kalla Sopiyya, ta ɗaga mai kai, hmmmmm faɗin reaction ɗin da Ayusha da Hamza Rasheed suka yi, abin sai ya ba mutum tausayi da nishaɗi. Daga nan al'amarin ya sauya, aka fara ta ya sa farin ciki hatta shi kansa Sarki Arman sai a yanzu ya ga mananninsu da yake kullum suna sanye da niƙaf ne.
*Bayan Wata biyu*
Shuru ne ya ratsa babban parlour Sarki Arman, sun ɗau lokaci a haka kafin muryar Sopiyya ya karaɗe wajen da faɗin.
“Na amince.” zan iya cewa akaro na farko kenan da Unais ya yi murmushi yin bayan tarewansa a Massarautar, dan ya ki koma wa, ita kuma Sopiyya ta ce sai ta ga ya sauya tukun, sai a yau bayan kwana 60 ta amince da su koma Massarautar Qumaiz, tun da har ga Allah Unais ya sauya fiye da misali, ya dawo tamkar maraya, haka dai kawai yake lallaɓa rayuwa badan ya so ba. Amma wannan amsa ta ta ya sanyaya ransa, sujjada ya yi tare yin addu'a mai tsawo.
A ranar kam suka koma ta su Massarautar tare da dukka mutanen da suka zo, ko bayan da suka je can, sun ga sauyi daban-daban, domin ya ɗaura wani riƙon ƙwarya ne akai. Haka aka kuma mai sabon naɗin a ranar, ba abin da yake mai zafi a yanzu sai na mutuwar Zaituna, wanda ta aiko ta ce tinda ya ƙi dawowa akan mace ko mutuwa ta yi kar ya tsaya kan gawarta. Da faruwar haka baifi sati ba ta rasu, dan haka bai jeba sai washegari ya je kabarin ya ma addu'a.
Ba laifi in nace muku Sopiyya ba ta ƙara girma da cikar halitta ba na muku ƙwarya, ta dawo wata babban mace, ƙyau, haske, ƙiba sai masha Allah, sai a lokacin na lura ashe akwai ciki a jikinta wanda ya fara bayya, kaf duniyar nan tana jira ne ta ga mai za ta haifa, dan ta najinsa a ranta.
Rayuwa suka dasa saɓanin na da, suna shan soyyaya tare da kula da juna, haka kuma ya na kiyaye dukkan sharaɗanta, da dokan da ta kafa da shi ake yake aiki. Hatta su Sarki Sayyid suna leƙosa dan a yanzu su ka ɗai yake gani a jininsa.
Haka suka raina cikin, har lokacin haihuwa ya yi, hmmmmmmm murna kaman ya kashe Unais da aka ce tweens maza ta haifa, ya ra ya zai yi da ransa dan murna. Ya ga yara amma a lokacin guda hawaye suka fara gangaro mai. Sopiyya da take ƙwacce ta sanya hannu tare da share mai..........
Ranar suna, an cika sosai a Massarautar, hatta su Hamza sun so dan a kafin ranar suka je ganin jikokinsu har Massarautar Afraz, Zulfa ta haifa sannan Hurara kuma Namiji. An sha an yi walima sosai, a wajen faɗin sunaye, Unais ya ce.
“Hassan - Sultan. Hussain - Muhajid.” take Abu-muhajid ta rintse idanunsa dan murna, ya tina a lokacin da Sopiyya ke tambayarsa sai akace mata ya rasu, a lokacin ta ji babu daɗi, yana ji tana faɗa ma Bintu.
“In dai Namiji na haifa to sunan sa zan sa insha Allah.” Gashi ta cika alƙawarin.
Taro bai watse ba zai yamma, in da Sopiyya ta fito dan gaida iyayenta. Ta yi kyau cikin wani haɗeɗɗen gown black mai aikin golding, cike da fara'a kowa ke amsa Haske Lantarkin Masarautar Quimaz, dan haka suke ce mata. Mai hoto ne ya ɗauke su gaba ɗaya kowa na murmushi. Hoton ya ɗauku dan haka mai hoton da kansa ya ce. “Wow ma sha Allah, Alhamdulillah”........ wanda nima da wannan kalman na kawo ƙarshen alƙawarin wannan littafin na _Baiwa_ Allah duk abin da n rubuta ba dai-dai ba ka yafe min.
Alhamdulillah.
Alhamdulillah.
Alhamdulillah.
END.
> PRETTYN JAJIRTATTU ✍️🥀😘🥰.