Chapter 5
by @reza12
TAZARA
© S-Reza ✍️
FCWA
MY WHASOP CHANNEL
Chapter 5️⃣
Tun ma kafin su buɗe masa motar Sadau ya bude da kansa ya nufi cikin gidan ransa a ɓace. A palo ya tsaya yana jiranta har ta ƙara so. Ta na zuwa kuwa ya tare ta da faɗin "Har yau dai ki sani kin sake cin darajar mahaifiyata ne, kuma har abada a haka nake kallonki muddin baki gyara hali ba". Ya faɗa yana nuna ta da hannu kamar zai tsokane mata ido. Ai kuwa kamar wacce take jira ta ce "Har kullum ba zamu taɓa haɗa hanya da Irin wannan ra'ayin naka ba, idan kai baka san ciwon kanka ba, to ni nasan nawa, ko Allah da ya halicce mu ya bambanta mu, ya ware mai hankali da mara hankali, kuma ya ware mai lafiya da mara lafiya, sannan ya ware baƙi da fari, haka zaluka ya ware talaka da mai kuɗi, wanda a cikin ikon sa ya gaddara cewar mu a layin masu kuɗin muke. Ko sokake mu chanja daga hakan?" Ta ƙara sa da ƙarfi har tana sakin jakar hannunta. Sadau ya zuba mata ido yana mamakin ta. Har cikin ransa yake jin ya tsani halinta, ta fice masa a rai gaba ɗaya, tabbas darajar Hajiya take ci badan haka ba ko me zai faru sai ya rabu da ita. Ya ce "Wannan tunaninki ne irin na marasa imani, amma a gurin Allah ba haka bane, tabbas shi yayi mai kuɗi da talaka, amma bai ce mai kuɗi ya dinga wulakanta wanda baida shi ne, kuma..." "Wa na wulakanta? Na ce wa na wulakanta? Kawai dan na nuna cewar a kwai tazara a tsakanin mu dasu shine wulaƙanci?" Ta katse shi da sauri. Sadau ya haura sama ba tare da ya sake cewa komai ba domin yasan ba zata taɓa ganewa ba. Duk da yasan a kwai nasa laifin tun farko amma tabbas zai iya cewa saboda halin Zinaru Allah ya hana shi mulkin garin Yalwa, domin kamar yadda Hajiya take faɗa ne, idan ba alkairi bane kar Allah ya ba shi mulkin al'umma, tabbas Zinaru itace ba alkairin ba a rayuwarsa, kuma zai samu mafita. A ranar Hajiya Zinaru ta haɗa miting ɗin gaggawa na manyan mata ƴan jam'iyar su domin ta ƙara jaddada musu ƙudurinta na wannan tafiyar. Tabbas wannan lokacin ta shirya tsaf, ko ma mai zai faru sai dai ya faru. Shi bai san duk wannan abun saboda shi yake yi ba. Bayan sun tashi daga miting ɗin ne kuma ta ɗauki waya ta kira malaminta ta faɗa masa cewar Sadau ya dawo da ita, yanzu menene abu na gaba. Malamin yayi dariya ya faɗa mata cewar ai Sadau ba zai iya yin ko kwana ɗaya ba tare da ita ba muddin mahaifiyarsa na raye, mulkin garin Yalwa kuwa Hajiya Zinaru kamar kunyi kun gama ne, kuma kece zaki zama shugabar al'umma. Zinaru tayi dariya ta ce "To Malam yanzu mai ya rage?" Ya ce "Sai dai goben idan kinzo. Amma idan son samu ne muna bukatar jinin baƙin kare, da jinin jariri sabuwar aihuwa wanda bai kai wata ɗaya ba Mace ko Namiji". Ta ce "Iya wannan sun isa Malam?" "Eh sun isa ayi wannan aikin kafin a dawo ɗayan". Ta ce "To an gama Malam, muna kan hanya gobe". Ta na sauke wayar ta nemo wata numbar ta danna kira. Ana ɗagawa ta ɗan yi kasa da murya duk da tasan babu mai jinta, kafin ta ce "Shaho, muna bukatar ɓakin kare da jinjiri sabuwar aihuwa a yau, ka tabbatar ya samu kafin safiya, zan faɗa maka gurin da zamu haɗu, zaka ga saƙo yanzu. Ta na faɗa ta kashe wayar bayan taji tabbacin za'a samu ɗin. Fitowa tayi tana kiran mai aikinta da ƙarfin ta.
****
Anty Hinde
A firgece ta tashi daga mafarkin da tayi, da sauri ta taɓa ƙasanta, sai kuwa taji laima alamun dai abun da ya faru a mafarkin da gaske ne. Ta kai kallonta ga Gali da yake ta barcin sa. Sai ta tashi ta shiga toilet ɗin ɗakin. Ta kai minti goma kafin ta fito ta na tunanin abun da ya faru a cikin mafarkin nata tsakanin ta da Saif. Sosai ganinsa ya dawo mata da tsohuwar soyayyar sa, ashe ganinsa da take yi a waya ma wani alkairi ne, sosai take shiga cikin ƙunci da damuwa tun lokacin da Gali ya kwace mata waya ya karya layin nata. Babu wanda zata yi wannan maganar da shi, gashi kuma kullum cikin damuwa take. Washegari da wuri ta shiga haɗa masa abun kari, har addu'a take ya fita daga gidan ta samu damar yin kuka. Da yake ba sabon abinci zata yi ba, ɗubame ne, yasa ta ɗaura sai ta tsaya a kitchen ɗin domin bata ma son fita su haɗu da shi kar ma tayi wani laifin. Tana tsaye a gurin ta faɗa tunanin lokacin da suke tare da Sulaiman. Bata san lokacin da ya shigo har ya kashe gass ɗin ba, sai da taji saukar mari kafin ta dawo cikin haitacinta. "Baki da hankali ne, Hinde abun naki har ya kai haka? Wato saboda na sakar miki fuska ko, gidan kike son ƙonawa ko me?" Ya Tambaye ta yana ƙara mata marin. Ta durƙushe a gurin tana kuka tana girgiza masa kai ta kasa magana, ga shi hancinta ya cika da ƙaurin kitchen ɗin wanda sai yanzu ma ta ankare da aika-aikan da taso yi. Hakan da tayi ya ƙara ɓata masa rai zuciyar sa har azarzala take, ya ɗagota ya wanka mata mari. Ya ce "Baki zaki buɗe kiyi magana dan uwar ki, mahaukiciya kawai, uban me kike tunani da har zaki ƙona min gida?" Cikin kuka ta ce "Kayi hakuri ban sani bane". Ya kamo hannunta yana janta har palo. Ya wurgar da ita a gurin kafin ya ce "Faɗa min abun da kika tunani da kika ƙona min abinci kuma kike shirin ƙona min gida?" Haka ta kasa magana tsabar kuka. Ya ce "Ko saboda wayar ki da na sayar ne? Okay saboda ban taƙura sai kin faɗa min a ina kika samu wayar ba ko?" Har lokacin kuka take ta kasa magana. Nan kuwa ya shiga dukanta da blet ɗin sa, sai da ya zane ta sosai kafin ya ce ta tashi ta sama masa abun da zata ci ya fita. Haka ta tashi da ƙyar ta nufi kitchen ta rasa ma me zata dafa masa domin duk a tsorace take. Sai kawai ta soya masa ƙwai da shayi ta kawo masa, nan ma sai da ya har haɗa mata kafin ya amsa yana ƙorafin wannan shine abincin da za'a ci, haka kawai dan gidadanci ta ƙona masa abinci. Ya sha ya bar gidan ba tare da ya sake bi ta kanta ba. Yana fita ta tashi ta ƙulle gidan domin yau bata jin zata iya tarɓar wani baƙo a gidan nata. A palo ta zauna ta sha kuka, kafin ta tashi lokacin duk jikinta yayi tsami ta haɗa ruwan zafi tayi wanka. Sai kuma ga zazzaɓi mai ƙarfi shima ya dirar mata. Tana hawa gadon da niyyar barci taji ana buga gidan. Bata san waye ba, gashi kuma ta kasa tashi, izuwa lokacin ma ita kanta zata so wani yazo domin ya taimaka mata ko magani a sayo mata. Lokaci ɗaya kuma tunanin ko dai shine ya dawo ya ɗarsu mata a rai. Ai lokaci ɗaya taji wani ɗan kuzari yazo mata, ta miƙe da ƙyar tayi hanyar palon. Haka take tafiya kamar ƴar kaciya ta buɗe gidan. Tsaye tayi a gurin tana binsu da kallon mamaki. Yara ne su biyu mata basu cika zuwa gidan nata ba saboda tsoro. Kafin ma tayi magana baƙar ta ce "Abida ce ta aiko mu, an kama Abbati yanzu a gida yayi sata ƴan sanda sun zo sun tafi da shi, shine tace wai muzo mu faɗa miki". Ta ƙarasa tana kallon Anty Hinde ɗin da tayi suman tsaye. Riƙe take da ƙofar palon amma ji take kamar zata fad'i, ga wani irin rawa na zazzaɓi da jikinta ke yi. Gashi ta kasa magana. Da ƙyar ta ce "Ku shigo". Ta faɗa tana sakin ƙofar domin basu hanya. Yaran suka kalli juna alamun tsoro. Kafin suce mai sai ga Anty Hinde a ƙasa ta zube zaɓar jikinta ba ƙwari. Haka suka ƙara sa suna kiran sunanta cikin ihu.
*****
GIDAN MARAYU
Kuɗaɗe ne sababbi ɗauri biyar a cikin jakar, sai agogo da kuma waya da ID da tarin takardu wanda basu san ko na meye ba. Wannan karan kam sun tsorata sosai ganin yawan kuɗaɗen har dubu ɗari biyar, domin basu taɓa samun kudaden haka ba. Abida ta ce "Abbati kuɗin nan fa sun fara bani tsoro anya ba zamu tsaya da satan nan haka ba?" Ya ce "Nima dai Abida naji tsoro, yanzu yaya za'ayi a mayar da jakar tukunna kafin musan abun yi?" "Amma dai ba yau ba ko?" Abbati ya ce "To a ina zamu ajiye ta, kar fa a ganta ne?" Abida ta karɓa ta cusa ta cikin ɗaya jakar wanda da kyar ta shiga. Haka suka bari akan gobe zasu mayar saboda gobe za'a dawo a cigaba da aikin kasancewar ba'a gama ba dalilin wannan satan da aka yi . A ranar suka fita gari aka ci dad'i da sauransu, wani abun ma sai sun mallaki gidan su tukunna kaman yadda suke faɗa. A daren a ɗakin su abbati ta kwana, kusan dukkanin su basu yi bacci mai kyau ba kasancewar jakar na gurinsu. Da safe kuwa taje ta amso abincin ta, mai yawa a gurin Mama Tani. Haka ta ci ta ƙoshi, Abbati kuwa cewa yayi hankalin sa ya ƙi kwanciya har sai ya ga an mayar da jakar. Jin haka yasa taje ta amso nasa ta ɓoye duk da yadda Abbati yace ta bawa wasu tunda ita ta ƙoshi amma ta cusa shi cen saman gadon nasu. Abbati ya girgiza kai kawai ya na kallonta. Ta ce "Kasan Allah akan dai na bawa wani gara ma ya lalace a haka, bare ma kuma ba zai lalace ba zuwa anjima zan dawo na ci". Ya ce "Yanzu fa bamu da matsalar abinci Abida, kuma Baba Manu ya ce ke abinci ma kullum daban yake, sannan kuma, sai ya ƙara maganar da ido ya ce ga kuɗi nan idan abinci ne sai su saya. Sai Itama ta mayar masa da ido cewar ai kuɗin ba na sayan abinci bane na sayan gida ne.
Daidai an fara taruwa a gurin yin katin zaɓen ne Abida ta ɗauki jakar zata mayar ya ce a'a shine zai mayar, haka ta bashi ya ɓoye ta a cikin rigarsa ya doshi gurin. Haka ya ƙara sa gurin yana fakar idon kowa kar wani ya ganshi. Yana fito da hannunsa daga cikin rigar suka yi ido huɗu da wacce aka sacewa jakar, kuma ga jakar a hannunsa. Ganin haka yasa ya saki jakar a ƙasa ya fashe da kukan tsoro, domin ya tsorata ganin irin kallon da take masa, kuma wannan shine karon farko da aka taɓa kama shi. Take kuwa ta kurma ihu tana faɗin ga ɓarawon jakar ta. Haka kuwa aka taru a gurin babu yadda ba'ayi da shi ba ya ce shima anan yaga jakar. Matar nan tace ba zata yarda ba, abokan aikin nata ma suka ce ba zasu yarda ba domin ai lokacin da aka zo za'a fara aikin babu jaka a gurin, kawai ya fito musu da jaka da kuɗin ciki. Sosai gidan marayu ya kacame ana ta abu ɗaya. Har saida Manu yazo gurin, babu irin tambaya da dukan da baayiwa Abbati ba amma ya kafe, ƙarshe Manu ya sa aka kira masa manyan gidan domin a yiwa Abbati dukan da har sai ya fito da kuɗin. Abida tazo itama tana ta rantsuwa akan ba shi ya ɗauka ba amma aka hada da ita gurin dukan suka ce bakin su ɗaya. Babu Manu ne ya ƙwaceta daga hannun su, Abbati kuwa aka cigaba da dukansa amma ya ce ba shi bane. Haka akai masa duka sannan suka kira ƴan sanda aka tafi da shi kasancewar yaki faɗin gaskiya. Abida ta biyo su har gurin motar tana kuka. Haka aka jefa shi a bayan motar Baba Manu na bada umarnin ayi masa duk abun da za'ayi masa ya fito musu da kuɗin su. Kafin mutar ta tashi suka yi nasarar yin magana da ido, duk da basu ƙara sa maganar ba motar ta tashi. Abida ta koma cikin gidan da gudu tana rusar kuka ta shiga ɗakin su Abbati ta kwashe gaba ɗaya kuɗaɗen ta bar dasu ɗakin, sannan ta fito da niyyar zuwa gidan Anty Hinde amma Baba Manu ya hana a barta ta fita. Hakan yasa ta bada saƙo bayan ta bawa yaran abincin da ta ajiye.
Koda aka ƙara sa da shi ofishin ƴan sanda farko ta laluba aka fara binsa ana lallaɓa shi, amma dai amsa ɗaya yake bayarwa. Babban police ɗin yasa aje da shi gidan msrayun a duba kayansa. Haka aka saka masa ankwa aka zo har cikin ɗakin su aka duba ko ina amma babu kuɗi. Gaba daya ɗakin ma aka duba babu komai. Haka aka koma da shi aka shigar da shi Sel. Har yamma babu wanda yazo gurinsa daga gidan marayu, gashi ko abinci babu wanda ya kawo masa. Yana zaune a cikin gurin zuciyarsa ta gama bushewa aka shigo da wasu mutum uku cikin gurin. Yunwa yake ji Sosai domin da safe bai karya ba. Minti biyu da shigan wannan mutanen sai ga Uncle Gali ya shigo gurin ya wuce gurin ƴan sandan. Bai dade ba sai gashi da ɗan sanda guda ɗaya an buɗe an fito da shi. Fuskar Gali a haɗe. Ya ce "Ina ne ka ajiye musu kuɗi?" Ya faɗa babu wasa. Abbati ya ce "Nifa ban ɗ..." Kafin ma ya ƙara sa ya ɗauke shi da mari. Ya ce "Kai kasan waye ni, wallahi zan iyar kakkaryaka a nan gurin idan baka faɗa min gaskiya ba?" Abbati da har bakinsa ya fashe, ya tofar da jinin yana bin Gali da wani irin kallo ba tare da ya ce masa komai ba. Gali da abun ya ƙara bashi mamaki ya ɗauke shi da wani marin ya kwashe shi, ya taka masa ruwan ciki, irin dukan da yake masa kai kace dama akwai wani abu a ƙasa. Ganin abun yayi yawa ne yasa ɗan sandan tsayar da Gali. Su da aka ce musu idan Gali yazo yayi masa magana zai fadi gaskiya sai kuma abun ya zama haka. Haka Gali ya fita ya na jaddada musu cewar su kulle shi har sai ya fadi inda kuɗin suke. Yana tafiya yana juyowa yana kallon yadda Abbatin yake masa irin wannan kallon da shine ya tunzura shi. Ana mayar da shi cikin sel ɗin wannan mutanen suka fara tambayar sa cewar wai wancen waye da ya tsaya yake masa irin wannan dukan, sannan ma laifin mai yayi. Sata ce ko fyade ko kisan kai ko kwacen waya ko kuma sharrin ƙwalawa ne?" Abbati ya cigaba da zubar da jinin bakinsa ba tare da ya tamka musu ba. A Cikin gurin yana tunanin rayuwa, shin suwaye iyayensa? Kuma haka zai rayuwa, shin da gaske yana da iyaye? Idan baiyi sata ba mai zaiyi, dole ne ya naimi kuɗi kota yaya ne ya samawa kansa ƴanci domin ya lura da cewar rayuwar duniyan nan sai da kuɗi ake zama lafiya, sai da kuɗi kake zama wani abu, Gali kuwa wallahi sai ya ɗau fansa a kansa. Washegari da safe kuwa sai ga Abida ta kawo masa abinci kasancewar babu nisa da gidan nasu, ko jiya saboda an hana ta fita ne. Sai da aka sa taci abincin kafin aka bashi ya ci. Ganin yadda bakinsa ya kumbura yasa ta fara kuka itama tana faɗa masa cewar jiya hanata zuwa a kayi. Abbati ya ce tayi shiru ya sani, haka suka ci abinci da wannan mutanen duk da abincin ba yawa, Abida kuwa sai kumfura take akan mai zai sa ya basu abincin da ko shi ba ƙoshi zaiyi ba. Abbati yayi murmushi, suma gayun sai da ta basu dariya. Bayan sun gama ne ta masa magana da ido.
Ta ce masa ko dai ta basu kuɗin ne a sake shi ganin yadda ya wahala. Jin haka yasa ya tafka mata gargadi akan ko me za'ayi masa karta fito da kuɗin, ko kashe shi za'ayi. Jin haka yasa ta sake fashewa da kuka jin batun mutuwa, ita to ai yafi mata kuɗin gara dai ya bayar da kuɗin a sakar mata shi akan dai ya mutu . Haka har kwana biyar Abbati na cikin gurin nan ana gana masa azaba, kullum kuwa sai ta kai masa abinci sau Uku a rana kuma tare suke ci da su. Sai a lokacin ya fahimci wadannan gayun ƴan duniya ne na gaske, suna ta zuga shi akan rayuwa, babu abun da basa yi daga kan shaye-shaye da fashi ƙwacen waya bangar siyasa da dai sauransu. Yaso ya yarda dasu amma ya nuna shi bai iya yin komai ba ko yanzu ma sharri akai masa, babban ya ce da shi, kar yaji komai muddin yana son yin rayuwa ya faɗa musu burinsa zasu taimake shi, ko yanzu a kwai wanda zai zo ya fitar da su, idan har ya yarda da su to za'a fitar da shi. Abbati yayi shiru kaman ya amince amma dai baya son ya haɗa tafiya da kowa, sannan shi har kar daba da sauransu basu dame shi ba, ga kuma Abida da komai zaiyi Sai da ita. Sai a kwana na bakwai ɗin ne aka fito da shi da sauran matasan. Ashe wai duk acikin aikin ƴan sandan ne suka saka wasu daga cikin ma'aikatan su akan su gwada shi. Abun ya bawa Abbati mamaki sosai domin bai taɓa kawo hakan ba. Haka aka sallame shi ya dawo gida. Koda ya dawo kuma sai ya fara ciwo, zazzaɓi da ciwon kai, har sai da ya kwanta. Babu wanda ya bi ta kansa sai ita take ta ɗawainiya da shi, gashi an saka musu ido yasa babu damar su yi amfani da kuɗi. Cikin kwana uku ya warke ya fara yawo a cikin gidan. A cikin kwana ukun nan Anty Hinde itama da take ta ciwo tazo ta duba shi har ta kawo masa magani da abinci mai kyau. Nan tai tai musu faɗa akan su sake kula, kuma ba ruwansu da kayan wani duk da ta san halinsun cewar ba zasu iya ɗaukar kayan wani ba. Anan take faɗa musu cewar tana da ciki. Take Abida tayi tsalle ta faɗa kanta ta na murna, sai kuma ta tsaya tana kallon Anty Hinde. Ta ce "Allah yasa kar yaron ko yarinyar tayi maka da Uncle Mugu...📝
S Reza