ABUNDA KE 'BOYE...

bonus

by @surayyahms

SURPLUS....Bonus

SARTUDAY 5.40am

yau yakansance babban ranar da ake jira na dawowar hajiya mairo mai tuwo daga can garin tudu wanda kusan kowa yake zumudin gani da dalilinsa na murnan dawowanta acikin ransa, rikita rikitan aiki da aka tashi da shi tun asubah tamkar wani ranar sallah, arnd 6:30am wokers na gidan har sun fara share share, at around 7.00am kuma masu aikin girke girke da akayi odern su na musmmn suka iso suma, saidai dake ammi karama ta riga tazare hannunta a batun girka main dishes kusan adan dole anty safeera ta katse baccinta ta fito waje ta same cookers din sukafara tsare tsare maganan shirya musu lafyyayen family

brkfast dan yau kowa anan zai karya.

acan ma su ammi babban sun gama shirinsu sunakan shirin tahowa sai har in anyi breakfast dinne kafin nan ayi maganan dora girki na tarban bakin hajiya daga na rana har ixuwa dinner, komi akay listing musmmn na sauran kananan fresh fresh abubuwa na girki da basu kammala ba, nan da nan aka ware ma cooks din family kitchen daketa can back yard nagidan anan duka workers din suka tare suka fara shirye shiryen abinci kai tsaye.

daga cikin dakin kulthum kuwa tunda suka farka da asubah sukay sallah su ukunsu sukaje suka gaida ammi karama suka dawo ayaanah ta koma bacci.

saka sleeping face dinta agaba da kallo kulthum tay tanata murmushi me sanyi tana shan mamakin yadda Allah ya bawa ayaanah wnn uban natural kyau na musmmn da kuma doguwar baqin suma mecika ga laushi ga yauqi kamr ba yar nigeria ba. sultana kuwa sai kan bata labarin shakuwarsu na ban mamaki takey dan babu tambay daga yanayin excitement dinsu akanta zaka san cewa ayaanah tagama samun wajen zama acikin zukatansu sosai.

ana daf kafin breakfast yagamu wata yar aiki ta kawo ma anty safeerah sabbin kayan dinkunsu a wani babban leda tasameta tana tsaye acikin lafiyayyen bedrom dinta atagaban gado iyakan farar bathrobe ne ajikinta bayan ta gama kwalliya tay kyau sosai

dama kuma kayan kawai takejira mai aiki tana miƙa mata batare da ta budesu ba maza maza ta sallemata ta fita dan bata san kowa yaga meyake ciki, wasu dan uban sun manyan atampopi ne sunkai kala goma da suka hada kudi suka siya tare da ita da ammi babba a asirrince badan komi ba saidan kullum sukaje kasuwa ko sukayi oder atampa aka kawo musu, toh idan sukazo sukaga wanda yake jikin ammi karama kuma sai duk suji hankalinsu ya tashi sabida ita awajen vendor guda daya talll take sayan kayanta da jeweries da lafaya wata shahariiyar hajiya ana ce mata hajiya zainab ceo na mum ramlat collection authentic clothing brand ne da aka riga akay registersa da gwamnati, babu wani social media da zaka duba bazaka same mum ramlat collection ba. kayansu sun aje reputation na quality na originality har kiga kamar bazaki taba samun irin kalar tasu a kasuwa ba (readers mum ramlat collection is real oo...inkema kinaso kaya na kece raini da luxury veils nd everything clothing u can imagine me mugun girgza zuciyar mahassadanki chat her asap ***)

Akwai laces kamansu hkg which is among the most expensive laces currently, Akwai mayun swarovski, voile laces manya Akwai Harish laces direct from Dubai suma very high quality ne kuma suna da kyau da tsada dede amare da hajiyoyi da uwargidaye masu capacity, Akwai kuma moderate ones irin su cotton laces haka,Swiss lace,applique atamfa wanda itafa har ordern su direct vendorn tana sakawa ayi, banda uwa uba very classy embroidery ankara da masu gold suma sun kai hawa biyar kowanne price ne kawai yake banbantasu, hakama kayan maza finest nd highest quality ba abarta abaya.

wnnn vendor itace tall acikin garin kano da take kawo ma ammi karama kowani irin kayansa sawa da veils da jeweries, wanda sai ammi karama tay makq shekara da shekaru ma bata san hanyar kasuwar kwari ba, duk sanda ta saka kayan ajikinta kuwa bakaramin girgiza zuciyar mahasadanta takeyi ba. barinma Ammi babba da abun yake cimata rai sosai shiyasa datagaji da jin kunya sai tatsiri saka hijabi musmn indan zasu zo family house kowani lokaci,

shigar yau ta rana ta musmn ce dan haka tun last week suka hadakai da anty safeerah taje tik tok ta kwakwalo musu mum ramlat collection din nan suma suka siyo wasu mayun atampopi suka dinka su suma aboye, yau za'a baza capacity uwar miji zata diro gari kowa so take agansa fesss kuma ace burge idon kowa fiye da ammi karama. tunda ta ciro ta raba kayan take ta xuba uban murmushi tana shafa laushin atamfar kankararru ne guda hudu nata, ammi babba kuwa guda bakwai cass tasiya ta dinka tsabar hadama kuma tafi kowa son kar aji zancen nan awaje dan kar ace tana copy copyn ammi karama..

Sharply anty safeera ta fara saka daya daga cikin kayan ajikinta babban aplique atampa ce royal blue colour aka mata dinkin maiduguri style gata fara soll siririya sai yamata wani irin mayen kyau da ke ita takware iya kwalisa da kwalliya. sumanta ta parke shi duka baya ta cakare da black ribbon tanakan fetsa turare agaban mirror sai ga nan sultana da kulthum sun shigo da sallama abakinsu

suna hade ido taga duk sun bude baki da alaman tq musu kyau wani dan uban murmushi tamusu nan suka fara gaisheta kusan atare ta amsasu tana mai cewa yanaga kamar bakuy wanka ba kunsan ynxun nan su ammi babba zasu iso duka ayi breakfast kuma babu wanda zaije mana table da tsamin jiki..

kulthum tace mama munyi wanka fa, sultana ne tace muzo mu gaishe ki kafin muje mu shirya..tace okay, ina ita kuma bakuwar naku? caraf sultana tace ynx ta farka mun barta acan tana wanka..tace ohhh inace dai batare kuka manna jiki kuka kwana akan gadon ba, nide i am cautiounin you guys about skin infections kunsan ai ance daga can kauyen fulani da buzayen nan tazo kuma suna da shanaye shanayen su suna da cutar kirshi da kazuwa abi u guys baku san ciwon nan bako? to wallah idan ya kama jikinku sai kun gwammaci borin jini sau dubu akansa ..sultana zata bude baki kulthum tay saurin cewa kai mama yanzu mune zamu guje kwanciya da ita ko itace ma zatace bazata hada jikinta da mu ba, kin ganta ne?..i told the girl looks exctly like a fallen angel, her skin is soo smooth, gata kyakkwa, kinga dogon bakin kashinta kuwa mama har kan waist dinta fa yake kwanciya?.

cikin yatsina fuska anty safeera tace kai enuf of this hype muje nikam inganta daga can ma sai muyi kwalliya zan zabar muku kayan da zaku saka dakaina kafin kuje kusaka wasu shirme hajiya mairo tazo ta tsigeni.

da murna suka juya suka fita a dakin anty safera ta sakosu agaba, suna zuwa kan stairs sultana tace mama barin je na dauko kayan da zamu saka nida ayaanah acan a dakin ammi... cikin gyada mata kai tace toh, nan da nan sultana ta sauka tay hanyar sashen ammi karama da sauri tama zuwa ta samu safiya ta musu firo dakayansu duk ta zubar a tsakar dakin...

anty safeera da yarta kulthum suka wuce dakin suka samu dede ayaanah ta fito a wanka kenan jikinta daure da oversize white towel ruwan showrr ya gama jika mata suman kanta tabi tazauna shiru agaban madubin tanata tsoron ta taɓa ma kulthum kayan shafe shafenta tuna cewa ibaad yariga ya hanata taɓa duk wani abunda banata ba

suna shigowa tundaga kofa anty safeera tay freezing in wowwww tanata kallon iya yawan suman ayaanahn kawai yadda yawani mannu akan fatarta yamata wani irin kyau ga fuskrta yay fresh sosai...

kulthum ta karaso da sauri suna kallon juna tana dan murmushi tace sis ya naga kin zauna shiru ko baki ga hair hair dryer bane? .ahankli ayaana tadago tace eh.. ji tay ance "masha Allah" muryan anty safeeran ne ya tsareta ta mike tsaye da tsoro sai kuma tay shiru ta zuba mata ido...

da wani irin baqar mamaki anty safeeera ta kalli kulthum tace wannan ne ayaanah?

kulthun ta fara dariya tace "mama ai nagaya miki toh ya kika ganta?

ahnkli anty safeerah tace ohh my God, but she is a goddess. atake ta wani riko hannun ayanahn da fara'a tace yan mata sannu da zuwa kinji, i am kulthum's mum, toh ya kike ya jiki kuma? ahnkl ayaana ta kalleta da murmushi me sanyi snn tace "da sauki, ina kwana mam..a..anty safeerahn tashafa kanta tace lafya my darling..toh zauna na bushar miki da kanki mana kar sanyi ya kamaki..

ayaana tana gyada kai har cikin ran anty safeera take cewa da tasan haka yarinyar take da mayen kyau duk tsiya ita ta karbeta tazauna agabanta ba ammi karama ba.

ayanaah tana zama agaban mirror anty safeera ta amshi kayan gyaran kai tay blowing mata suman ta gyara mata shi in a very well maintained style, ta shafa mata mayukan kai masu qamshi da tsada sann ta tattale gashin duka tay mata Ariana grande's pony tail hair style dashi jelar data nadeshi sau biyu haka ya zubo har kafadunta

the room was so lively sabida sake fuskan da anty safeera ta nuna ma ayaana sosai, sultana ta dawo musu da kaya dake ayaana bata da wani atampa they both decise to wear abaya kowa da kalan nasa, ayaana ta saka pure black cikin wanda ibaad ya siya mata, kulthum tasaka maroon sultana kuma ta saka kalar ruwan toka, anty safeera ta musu light make up, ayaanah ce karshe tanakan mata saiga safiya ta leko basuma lura ba tatsaya cak daga kofa ganin yadda duk suka tsaya akan ayaana suna gushing akan beautynta anty safeera tarike fuskrta da hannunta gently tana mata kwalliya yasa safiya ta kara jin tama tsane yarinyar sosai.

dama batay niyyar xuwa ba kadota ammi karama tay akan tazo ta bawa sultana hakuri akan wurgi data musu da kwatinsu ta zubar musu da kayansu a daki dazu.

tana ganin yanayin su ahaka ta juya sadaf abunta ta koma dan haryau bata gama jin haushin yadda sultana take yawan nanike ma amminta ba kawai kuma sai gashi wai ankawo wata me kama da aljanu.

ana gama ma ayaana make up mai aiki ta kira anty safeera akan ana nemanta a kitchen da gaggawa,lkcin kusan 8.40 ne tana fitowa harabar gidan kuwa suka ci karo da bataliyar bappa zaidu duk sun iso suma ko karyawa basuyi ba, as usual ammi babba ta sha wani irin bakin hijabi dogo har kasa. maheer da ibaad ne abayanta shikuma bappa zaidu ya tsaya a kofar masallaci tare da uncle mohammd suna tattaunawa a tsaye.

da fara'a ta tunkarosu tana cewa oyoyo ammi babba, both maheer da ibaad ne suka fara gaisheta ta amsa su sama sama dake suna sauri sauri zasu shiga ciki,"anty safeera tace aah ya haka? ammi babba tabi bayan su da mugun kallo taja tsaki "kyalesu zasuje kwadayi mana kinsan uwargijiyansu ai tana cikin gidan suna sauri sauri zasuje su fadi kasa su lashe kafarta tasaka musu albarka koda zasu ga haske a rayuwarsu.

karamar dariya anty safeera tay tace "kai ammi..just let them be ni wallah bakisan dadin ganinki danaji ba..

tace "kai safeerah nice dai zance haka, kinga kyan da kikayi kuwa?? lallai wann atampar ta dauke ki wallah.

anty safeera tay wani irin murmushi murya kasa kasa tace "ainagaya miki kayan wancan matar bawasa bace dinkin mun mq da safen nan duk aka kawo mana naki nacan daki wallah bakaramin kyau sukayi" da murna ammi babba tace Allah ki? toh muje mana in gani safeera bana son wancan yar rainin hanklin ta dau wanka ta fito ta ganni haka duk ban shirya kaina ba

..anty safeere tace " kai ammi gaskya bana tsammanin zata fito yanxu dan kinga chops small small local dishes, da sauran drinks da su salads duk ita takey a sashenta. its a lot of work gara da kikazo kar aikin da akabar mana ya lalace masu girkin suna can baya.

ammi babba tace hakane kuma muje kawai musaka ido akansu inga me sukeyi ince dai kin ean tsara musu abunda zasu dafa, anty safeera tace ehhh ynxu dai breakfast ne akan wuta suna saukewa zasu saka abincin karban baki

..abbansu mujaheed yace around 11-30-12 dai hajiyan zata iso kuma wai da baqi zatazo

ciikin yatsina fuska ammi babba tace hmm can mata, ni wallh tsohuwar bawai burgeni takeyi ba zatazo ne ta ishe jama'a da saka ido da gulma dama kuma kinsan tana da yar gaban goshinta sai abunda aka kitsa mata akanmu zata ji.

anty safeera batace komi ba har suka wuce backyard suka samu wokers din sunata aiki har an tafasa kaji ana soyawa anware na ppr chicken dana stew agefe, anbada hankli sosai ga breakfast suna kan soye soyen irish da kwaiyaye ana xubawa a platters da minced meat sauce.

ammi babba tana zuwa wajen ko amsa gaisuwar su batay ba ta hade fuska tafara bada oder ayi nan ayi nan dan tafiso ne suyi abunda suma za'a yabe su yau sosai...

9.00 on d dot kulthum da sultana da ta riko hannun ayaanah suka fito sashen ammi karama sam ayaanah taki ta daga fuskarta sabida make up din da anty safeerah ta mata wani bambamra kwai takejin kanta duk da yadda kawayen nata suke haba haba da ita..

wasu mugayen dadadan qamshin soye soye ne ya cika sashen ammi karaman sunayin sallama a falo suka samu ibaad da maheer ne kawai a zaune suna shan tea dayaji kayan yaji da madara yana baza tashen qamshin su citta.

nan take sultana tay kifi kifi da ido kirjin aayana na bugawa da karfi kamr zai faso waje, kulthum ne kadai ta tunkarasu da normal looking face inta daya sha make up ita tafara rusunawa tace "good morning yaa ibaad,.. good morning yaa maheer..kafin ibaad ya amsa maheer yay murmushi yace morning ummi kin tashi lafya? adan kunyace tace lafya,ya gyada mata kai, sultana tafara gaida ibaad kafin ta koma gefen maheer ta gaishesa, kan ayaana na kallon kasa itama ta gaishe da maheer yace wow prettyna kinyi kyau sosai fa,..kara boye fuskanta tay batace mishi komi ba snn ta dawo ta gefen ibaad da sanyin murya tace mishi "ina kwana ka tashi lafya? tea din dake hannunsa ya aje akan table saida yadau minti guda yanamai kare ma sunkuyayyen kantan kallo snn ya kyabe baki yace i am good'..ya jikinki? kafin ta amsa a miskile ya dube sultana yace "ke,..i hope u dint give her any cold water dis mrn,..da sauri sultana tace "aa yaa ibaad bamufa ci komi bama wanka kawai mukayi da ruwan zafi...yace toh ya isa haka toh kuje ciki mungode da gaisuwa.

..idon maheer nakan kulthum harta tamike tsaye tay kitchen din sultana tay saurin binta abaya, ayaanah na kkrin binsu da sauri ibaad yace "not you" wani garas taji ahnkli kuma ta koma ta zauna agafensa akasa a slow motion tay shiru.

dan karamin shirune ya ratsa wajen kafincan maheer yamike yanufi kitchen in shima aka barsu su biyunsu a zaune

..daukar fresh clean tea cup yay ya zuba shayin ya miƙa mata, dan dago kai datay zata karba da suka hade ido yaji wani abu ya tsarga masa yay loosing balance wanda tuni tea din ya dan zuba masa ahannu, dan gani da yay gabaki daya ta canza masa da make up dinnan, yay saurin kyabe baki tana karba ya ciro hankynsa daga aljihu yana goge inda tea din ya zuba masa itama nan take kallo batakai tea din baki ba harsaida ya gama sharewa suka kara hade ido girarsa na sama a dage ahnkli "what are u waiting for, ko sai nace miki kisha? ko kuma nabaki abaki? its almost nine bakici komi ba kinsaya kinata fenta fuskarki ko??toh ko kyau bai miki ba

dan shagwabe masa fuska tay daya kara narkan dashi batace masa komi ba, kurba daya tay ma tea din taga ya zuba mata ido yanakan kallonta, ahnki tare da kara shawgabe masa fuska tace bani nayi ba fa ai umman kulthum ne tamin"

yace "uhmm ni nace miki wani abu ne?..shanye kawao, kema kibisu ciki. shiru tay ta cigaba da shan tea din ahnkli tana satar kallonsa while yanakan latsa wayarsa, basu kara cewa komi ba awajen ba har saida ta gama snn ya sallemta yace taje kitchen din ta kira masa maheer tace ya samesa a daki dan su shirya ynxu..tana shiga kitchen din kuwa ta kalli maheer tacemai ibaad yana kiransa a can dakinsa ..

dambun kaza da ammi karama tay ya deba ahannunsa snn ya fita ya kyalesu anan sukadai

...ammi duk ta yabe kwalliyrsu tace sunyi kyau sosai sunata jin dadi.

Karfe 9am na cikawa duk aka fara hallara cikin main falo domin karyawa, da wuri ammi karama tace duka yaran nata sufita suyi gaisuwa kafin itama ta fito. dukansu hudu suka wuce main palon safiya ce ta fara sallama dake bata fiye son magana da su sultana ba, lkcin anty safeerah ce kawai mace a falon tana tsaye tana bada masu aiki su biyu oder ana jera breakfast din akan dinning ita kuma anmi babha tashiga dakin anty safeera canza kaya, daga bappa zaidu sai uncle moh da already kafin su ayaanan su shigowa falon anriga an kirasa a waya yafice cikin gaggawa dake shikam ma bai wani damu da yasan waye yarinyar ba existance dinta agidan baidamesa ba dan kwata kwata baison wani abunda zai takura ma rayuwarsa ko kadan

Dukansu yaran haka suka tsuguna suka gaishe da bappa zaidu cikin girmamawa, 10min past nine kowa ya fito aka zauna ammi babba ta wani cakare da jan atampa ta baza dauren ture kaga tsiya tana shan qamshi duk a tsammnta yadda suka ci kwaras hakama ammi karaman zata fito ta dau wankaz sai kuwa tabasu mamaki ta saka normal moroccan jallabiya dayaji dinkin zaren hannu golden colour all thru da mayafinsa

bata kuma yi kwalliya ba tabar natural beautynta a fili.

cikin girmamawa aka gama gaggaisawa kowa nakan table din face uncle moh da damsa mujaheed da already yake plane frm S.A.to nigeria bai iso ba tukuna.

lafya lafiya aka ci abinci karyawan, banda ammi babba dataki su ko irin gaisawa na fatar bakin nan da ammi karama, dan tana ganin irin kallon da bappa zaidu yake mata asace abunda yafarun jiyan ne kawai ya dinga fado mata arai tana jin tsananin kishi da kokontonsu akan ambatarta ta da mijinta yay da sunan fatima akan gadonsa jiya datake shafashi.

ana gama break fast bappa zaidu bai kula kallon kishi kishin da ake jefawa akansa ba ya fice, maheer da ibaad kuma suna cikin gida basuje koina ba suka zauna a dakin ibaad din suna kan wasu abubuwan dake gabansu time to time suke zagowa suzo su duba ammi karama a kitchen dan ita daya take abubuwanta ko yaran ma tahanasu su tayata

daga waje kuwa wani jiji dakai da iko ammi babba ta dingayi ma workers din, idan suka saka maggi tace sam su rage yay yawa, hakama zata bulbula ma abincin wuta fall fall yama ci tayita masofa tace wai sauri sukeyi ba sime sime ba...ta matsu sugama takoma daki ta sake canza kaya kafin hajy mairo su iso.

gidan yay shiru kowa na indah take, kafin 10:30am ammi karama tagama komi datake shiryawa nan tay packaging

dinsu drinks da chops din so lovely a wasu shegun bottles, classy glass, dispensers da wasu expensive luxury cheffing dish data sayasu duka ahannun uwargida collection tun daga garin kaduna...

tana gamawa ta bar komi anan kitchen din snn taje room inta batay wata wata ba ta fada wanka after a while ta fito ta ciro wata peach colour applique lace doguwar rigace me celeopatra neck ta saka

tay daurin daya rufe mata duka gashinta kanta sosai tay kyau bana kadan ba...

dacan har kamar zata fita ta duba ya su anty safeera suke ciki da girke girke sai kuma tafasa tay zamanta a daki dan tasani sarai ba wani abu me wuyane bane ammi babba ta gasa mata baqar magana acikin mutane.

har saida 11 yay kafin su ammi babba suka bar wajen girkin lokcin rabi ran masu aikin ya baci sabida yadda ta dinga kwaba musu aikin su da yawan bada oder. kai tsaye aka fara packaging abincin dana baki, dana hajya da nasu duk aka kai ciki, anyi coloured rice kala kala har guda uku, difrent kind of sauce da egg stews, ppr chicken da manyan manyan turkey da alalle daya ji cray fish, masa da miya, da kunun gyada dana tamba. ayayinda su ammo baban sukaje dakin anty safeera sake shiryawa nan wokers suka karasa kawo abincin babban sashen hajya mairo aka fara jeresu a kan dinning in falon within minutes harr angama komi gidan saiya dauka da wani irin shiruuu.

Da misalin 11:40am Wasu manyan manyan SUV jeeps guda biyu bakake kiriin masu fidda wata uban sheki suka shigo harabar gidan sukayi parking ayayin da driver yay saurin saukowa kasa ya bubbude musu kofofinsu Yana mai rusuna kansa akasa cikin yanayina tsantsar girmama wa, Wata dattijiwar mata ce wacce bazata wuce 60+yrs ba tafara sauka kasa cikin shigarta na mutunci tasha brown hijabi daba atula mai tarukucen design ajiki ba babban aminiyar hajya mairo kenan hajiya hajara wanda itama da safen tay sammako taje har tudu domin tadauko babban aminiyarta tadawo da ita gida dan tasan bazaimata sauki barin tudu ba yadda aka saba da taimkon bayin Allah datakey acan kowa baison hajy mairo tabar wajen..

tana sauka sauran baki guda uku mata da yarinya yar 12yr suka sauko suma amma su mataye ukun duk matasa ne basuda wani shekaru

driver su ne ya Taho da gudu ya amshi jakar hjy hajara ya rike mata har suka karaso Gaban dayan motan wanda har yanzu hajy mairo ce aciki amma bata sauka ba, tana karasowa gaban murfin motar taja ta tsaya tana kallonta kafafunta da hannunta Duk sunyi nauyi idanunta sunyi ciki ciki saboda tsabar gajiya, Wani dankareren medicated glass ne ta toshe kwayar idanun nata dashi Itakuma leshi ne ajikinta nata purple colour an mata dinkin buba da zani kafarta cikin wata flat shoe mai kama da Dunlop da kyar ta motsa jikinta sabida tana da Dan kauri.

hajiya hajaran ne ta riko hannunta domin ta taimaka mata zuwa kasa, kan kace Wani abu kusan duka rabin ma'akatan gidan sun kewaye su da gaisuwa hajya da bakinta duka duka mata hudu ne da maza matasa su biyu da yar yarinya

"Barkan ku da zuwa Hajiya mairo oyoyo hajiya Allah yasa anzo a lpya...kusan kowani ma'aikaci yana Miko musu gaisuwarsa cikin yanayin girmamawa da nuna farincikin sa da ganinsu

hajy mairo kmr wacce ta rude tafara washe baki kamr cele tana cewa "Sannunku dai"

Sannunku...Tana fada da kyar sabida kukan rabuwa da mutanen na tudu dataci harya shake mata murya tana yi tana dann waving dinsu dahannu tana baza murmushi...

hajy hajara data rikota tace An sameku lpya?duka Sukace lpya lau..Nan ta juya tana kallon driversu ta ciro kudi mai yawa ta basu tace sai ka babbasu na shan ruwa mungode Allah ya muku albarka

Da sauri Ya rusuna kai yace toh hajiya Allah kare ki angode, Duka sauran ma'aikatan dake washe baki suma suka bibbita da addua tuni wajen ya kaure da godiya da yabo kowa na washe baki

Itakam Bata kara ma kallonsu ba ta riko hannun kawarta suka nufi ciki A hankli suke tafiya sabida yanayin jiki sai an bita a hankli musamman ma da bata fiye son zaman waje daya ba.

Suna daf da bude kofar gidan sukaci Karo da bappa zaidu yafito fuskarsa dauke da kyakwan murmushi kallo daya zakamai kasan yana tsananin murna da isowarsun,da sauri sauri ya karaso da alamn an riga an sanar dashi labarin isowarsun ne, Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin shaddace a jikinsam wanda a ƙalla zaikai Darrikan kudi,ya ɗaura hula akansa ga wata gare datasha aiki sosai.

fuskarshin nan ta fito ras baqin sajenshi da gemunsa mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi

..Wajen hajiya mairo ya nufa da farinciki ya rikota ajikinshi ya rungumeta tsam wacce already tana Hade idanunta da nashi tafara sauke wasu maqudan hawaye, cikin muryanta da bai fitowa sosai

"tace'..zaidu? ashe zan ganka da idona..

Wani shafa kansa tayi a lalume tace Alhmdullahi,

saita juya ta kalli uncle mohammad daketa famar Murmushi cokin fashewa dakuka tace Alhamdull hajya hajara yau gani ga autana muhammadu kai masha Allah ashe haka kadawo gingimeme muhammadu?

..duka aka fara dariya itakam sai kuka takeyi jin yaranta duka sun rungumeta sosai

uncle moh yace "Ina matukar farincikin samun isowar ku hajya mama na yahanya.

Ta juyo cikin muryan kuka tace "Ohh nikam kalau nake ,toh Ina yayan naku, ya baka fitomin da suba?nima inga jikokin. Ohh Allah yajikan mahaifinku, Allah yasaka yana cikin inuwar Rahmanu ubangiji Allah yay muku albarka..

cikin tsantsar tausayinta da kaunarta dake mamaya aransu sukace "Allah ya kara miki tsawon rai hajya,in muna ganinki ai tamkar muna ganinsa ne Allah ya masa rahma..

matsanancin kukan ta kara fashewa da shi uncle moh ya rikota ajikinsa yanata lallashinta.

kafin nan suka fara sannu da zuwa suna gaisawa da sauran mutanen datazo dasu tareda su sun zama su takwas da yar yarinya karama,me suma ruthy itama age dinta kamar irinsu kulthum datazo da ita.

Cikin gidan bappa zaidu ya musu jagora tareda ma'aikatan gidan da suka shigo da kayan su da sauran abubuwan tsaraba da sukaxo dashi hilimi guda a buhuhuna

Daga cikin gidan kuwa kusan kowa shiri yake Dan yaga ya hallaro cikin babban katafaren falon sun on time,yau babu wanda bai haska yay kyau a shigarsa ba musamman ma ant safeera data sha Wani atampar again wann karon tasaka dark red in colour wanda ya amsheta shima kwarai dagske ,cikin wata golden atampa wax ammi babba ta fito suka sha dinkin su kowa da kalar nasa style din, shikuma maheer ya saka light brown shadda da dark coffee cap, ibaad ya saka sky blue colour voile marar nauyi wanda tsabr kyan data masa kamar ka cinyeshi.

har saida aka shigo da hajy mairo da bakinta kafin nan anty safeera tazo ita da ammi babba dasu ibaad , safiya da maheer cikinsu kowa ya rusuna cikin ladabi da girmamawa aka fara gaishe gaishe, ana cikin gaisuwar ne ammi babba ta fita domin duba su sultana, tasha baqar mamaki dataga ammi karama bata fito ba har yanxu...

gani tayi wnn ne perfect timr mata da zata baza gadara da ikonta a matsayinta na babban surkuwan gidan tunda ammi karaman taki fitowa akan lkci.

tana fitowa kuwa ta samu wata mai aiki da mopper tana share dattin kafar takalmn mutanen kauyr da suka shigo ciki musmn maza yan kauyen wokers din restaurant wanda basu da iyaye su biyu da hajya mairo ta rarumo su tazo da su birni

mai aikin tagama goge wajen kenan sukaji wani irin kwas kwas sautin takalmi mai shege tsini, zainab arifa ce sanye da wata iriyar english wears me fallen neck amma gown me dogon hannu red color ta daura vintage scarf taci wani uban kwalliya kamar zataje biki, ga wayarta ma dakyar take rikesa tsabar rigima, dede kan inda ynxn nan aka gama moppewa ko bushewa baiyi ba ta taka snn tabi ta zubar da bawon sweet din datake lasa akasa batama lura ba.

baki bude mai aikin tadinga kallonta, ita kuwa ko kallonta batay ba bare tace mata sannu kai tsaye ta nufi wajen ammi babba data daskare tana kallonta

tana isowa gabanta da wani irin rawan kai tare da over confidence tace "hi anty,. tay kmr zata fashe da dariya cikin gintsewa tace u look cool today da bakisa hijab ba.

..ammi babba dake washe baki tace thanks sannunki da zuwa zainab Arifah yasu mumnynki

zainab arifah na taunar cingam tace fine..umm anty kice ma wnn maid din taje car dina ta daukomin bag dina da wani gift bag i left the car open

..da rawan jiki tace okay my dear ki shiga ciki za'a'dauko.

yake kawai ta mata batako gode ba cikin wata mayyar catwalk ta wuce sashen datake jiyo surutun kai tsaye

babu sallama ta fado cikin falon tana wani irin murmushi me cike da shan qamshi like kana ganinta kasan kwata kwata ba'a bata dandanin tarbiya agidansu ba.

suna hade ido da anty safeera tace zainab karaso mana kizo ki gaishe da iyayenki

dakyar kai tsaye ta karaso ciki ta fara gaida su bappa zaidu dake uncle tace musu, sama sama ta gaida su maheer, sauran bakin kam batako kallesu ba taje jikin hajiya mairo ta mannu da ita tafara cikata da surutu tana cewa wai saida taje kauye tay baka kirin snn ne zata ta dawo musu??

..wasu nata mamakin rashin kunyatta wasu suka maida abun yaranta dake hajiya mairon ma cakka mata magana takey acikin wasan kaka da jika tana ce mata duk gidan ita ne bata gado kunya da hanklin kowa ba sai rashin hanklin ubanta zayyanu...

suna cikin haka saiga su kulthum da sultana da ayanan ce acan baya duk sun riko kayan small chops da ammi karama tay, suna ajewa duka sukaje suka rungume hajy mairo ta shafa kansu tana ta mamakin yadda taga ayaanah ta fesss saidai tun basu fara magana ba masu aiki suka karaso da sauran chops ammi karamar ce abayansu da katon tray na drinks da small chops da sanyin sallama ta shigo ciki kai tsaye taje har gaban hajy mairo ta durkusa snn ta aje tray din kayan tabawan tafara gaisheta cikin tsananin kewa da girmawa, hajy tuni ta mance da wata zainab arifah data makalkale mata ajiki ta riko hannum fatima

ayayinfa zainan tabi ta kafesu kulthum da sultana din da ido tanata kallonsu jin kmr yaran sun fara bata haushi ganin kwata kwata basa dokinta bare su gaisheta gabaki daya bata gama gane waye ayaanah ba dake akasa tabar kanta bata dago ba tukuna.

uncle moh ma sam bau gane waye ayaanah ba tukuna dan harga Allah ba haka yay tsammanin ganinta ba

da har zainab arifah zata tambaye safiya wacce wanncan din sai ga nan ammi babba takara shigowa fuskarta adan dore idonta stiff akan su.

hajya ta dan dafa kafadun fatima tana hawaye tana murnan ganinta, ammi karama duk ta juya gaban bakin hajya mairo tay musu gaisuwar mutunci ta saka masu aikin suka jejjera musu ruwan sha masu sanyi da kala kalan abubuwan sha agabansu wanda hakan barakamin batawa ammi babba rai yayi ba

tayama za'a ce sune suka fara tarban hajya amma daga zuwan fatima harta kawo musu ruwa da abun tabawa duk ganin hakan takey a matsayin makirici da neman gindin zama

hjy kuwa sai bayani take ma baqinta tana cewa ai wnan ita ce yata fatimar danake yawan gaya muku, daga nan tafara introducing kowa

hartazo kan ayaanah ta dan miƙa mata hannu ayaanah ta karaso kusa da ita, sai sann zainab arifah ta fara kare mata wani irin hamshakin kallon kwakkwafi dana maita bata taba ganin kyaun irin nata ba sai ji tay kirjinta na mata zafi

uncle mohd kuwa sai masha Allah masha Allah yake ta maimaitawa shima ya zuba idanunsa akan yarinya baya ko kiftawa

hajya ta jawo ayaanah jikinta tana hawaye sosai tace musu wannan ma jikata ce sunanta ayaanah, yar gidan yatace tacan tudu wato taawure...

anan duk bakin sukace Allahu akbar, Allah sarki itace wance addantta ta rasu ko?? atake idon ayaana ya ciko da ruwa, hjy mairo na hawaye tace eh wallh etace, Allah dai ya jikan inayah..hmm,.mutuwa bai bar kowa ba da babba da yaro intazo sai ka tafi...

da mamaki tafara tattaba jikin ayaanah tana share hawaye tana cewa masha Allah, kamr ba itace ke kula ba ta kalle ibaad daga can nesa fa karfi tace...Allahu akbr rayyanu ashe dai bazaka taɓa iya cin amanata ba..jibe yadda yarinya tay fess fesss..ohh ayaanah lallai toh mijinkin nan ya iya kiwo..

zainab arifa ta juyo tama ayanan wani irin kallo jin zuciyarta ya wani irin buga da karfin gaske duk dama taganta yarinyace...kuma taji kowa ya fara dariya.

...adan miskilance ibaad yace 'what, waime kike cewa ne? kin dawo kenan ko? tana harararsa tace yo bazan fadi gaskiya ba,..daga baka ajiyar yarinya harka mallaketa ka canza mata kamanni?

nan aka fara musu dariya yabi ya mugun hade ransa yana harararta yana cewa baya so itakuwa ..sai zuba takey abunta tana cewa sam batay tsammnin zata dawo taga ibaad yay kiwom ayaanah haka ba

ayaanah tay shiru kanta na kallon kasa jin duk falon anata dariyar jokes din hajy mairo kafin kace wani abu ibaad ya zame ya fita da wayarsa ahannunsa da alaman zai amsa waya awaje.

ana hirar maganan aure auren dangi duk dama wasa akeyi amma uncle moh ya fara dagewa da kawo batun lallai ayaanah acikin familyn nan kawai za'a bata mijinta dama bazata auri bare daga waje.

some feel it as joke amma hardaga zuciyarsa dagaske yakey dan aganinsa aima

ganganci ne a aurar da kyakkawar yarinya haka wa bare bayan gidansu bai koshi ba. he started to think for himself dan dama yana da burin kara auren amma bada wuri ba yasan kafin ayaana ta girma shim halaa yashirya

zainab arifah tafara kamar zata tashi ta bii ibaad waje sai caraf ayaanah ta miƙe ajikin hajy mairo zata koma wajensu sultana ta zauna wani dan uban kallon kurilla da zainab arifah takey ma fuskrtan Ayaanah tryn to look for one tiny or even the tiniesst Abu guda daya na tsabar madaran kyau datafi yarinyar dashi bata samu ba, duk kyan ayaanan sai yagama rudata taciki taji ta rasa nitsuwarta tabi ta saka mata ido sosai da sosai wanda yasa kafafunta suka fara harhadewa

tana wuceta kuwa taci tuntube suka dan gogi kafar juna ahnkli veil din kan ayaanahn ya zame kasa yafadi akan fuskar zainab Arifan ayaanah batama sani ba, zainab tana janye veil din taga wani irin pony tail mekyau da anty safeera tama ayaanan yanata warwarwa dakansa alaman dama veil din ne ya kamashi, baki bude mentally zainab arifah ta gwalo ido waje tareda dacewa ohhh wowwww ganin yadda tsantsin suman ya warware yabi bayanta yarrrrr. SURAYYAHMS

***