RUWA CIKIN COKALI

Chapter 19

by @mamanafrah3028

***



*RUWA CIKIN COKALI* 
(Ya ishi mai hankali wanka)
 
                  
                NA


         MAMAN AFRAH

 
.        *Daga marubuciyar* 
  *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* 
      *****

           BOOK 1

         PAGE 1️⃣9️⃣



                 *BABA* 
   Cikin sauri yana ɗauke da iccen ya nufi store ɗin Hafsat da take tsaye laɓe daga bakin ƙofa ta ciki, riƙe take da kwano wanda ta ciko da shinkafar, Baba babu tunanin komai ya nufi ɗakin tana jin yana dab da shigowa ta saki kwanon shinkfar ya faɗi, a bakin ƙofar suka ci karo amma sai Hafsat ta shammace shi  ta fita ba tare da ya kwala mata iccen ba, da gudu ta nufi wajen katangar gidan Baba ya rufa mata baya iccen yana rinjayarsa tana zuwa ta ɗare katangar dakyar kasancewar ba wani tsawo ne da ita ba Baba kuwa ganin za ta tsare kuma ba zai iya ɗagawa ta yadda zai rafka mata ba, don yau iya ganinsa sai ya rotsa kan ɓarawon shinkafarsa tun da dai har Allah ya nuna masa shi muraran.

 Ganin ba zai iya ɗaga iccen ba sai ya yi wurgi da shi saboda ƙarfin hali ya kama katangar shi ma ya ɗare don ya yi alƙawarin ko a shi ko a ɓarawon shinkafa.
 Hafsat ganin Baba ya hayo saman katangar sai gabanta ya shiga faɗuwa saboda kar ya je ya gane ta, duk da ta saka hular sanyi a kanta ba zai ga gashinta da zai nuna mace ba ce kuma ba lallai yadda yake a rikice ya yi la,akari da duk wani abu na jikinta da zai alamta masa ba namiji ba ne. Baba kuwa ganin ɓarawon zai dira sai ya miƙa hannu ya kama rigar Hafsat a zuciyarta ta ce

 "Shikenan na shiga uku yau in asirina ya tonu daidai yake da barina gidan nan ko makamancin haka, amma ba zan yarda ba duk sai na tona asirin kowa matuƙar nawa asirin ya tonu" Bismillah ta yi a zuciyarta ta saita ƙasa ta dira inda Baba ya riƙe a jikin rigarta kasancewar rigar yadin ya gama cin duniyarsa bashi da wani ƙarfi saboda tsufa kawai sai ta yage ya zamana gutsuren yana hannun Baba ita kuma ta dira waje.
  Baba ya kalli gutsuren rigar ɓarawon a hannunsa takaici y  ishe sa har zai dira sai ya hango ɓarawon ya zura da gudu, sannan ya hanga ya tabbatar tsakar dare ne ba ya hango kowa sai haushin karnuka, tunnainsa ɗaya kar ya bi bayan ɓarawon ya je ya shaƙe shi a banza a wofi wannan tsoron da ya ɗarsar masa a zuciya yana tunanin kar ma dai ko akwai wuƙa a aljihun ɓarawon kamar yadda mai napep ɗin da ya kai shi gidan Sadiya da zai mayar da ita ranar da Nasir ya dawo da ita ya shammace shi ya fito da wuƙa, bai yi wata-wata ba cikin sauri ya duro daga saman katangar ko ta kan iccen bai bi ba ya nufi ɗakinsa ko ɗakin shinkafar bai koma ba, yana shiga ɗakin duk sai wani tsoron ya ɗarsu a ransa yana tunanin da mai ya kai shi zai je ya bi bayan ɓarawo ya kashe shi ya kashe banza.

  Bai runtsa ba har asuba yana ta tunanin ɓarawon nan ashe dai zuwa yake yana ɗauka har yake zargin iyalansa ashe dai su hidima suke masa da kuɗinsu. Sai da aka shiga masallaci sannan ya fito ya yi alwalar ya buɗe ƙofar gidan ya fita, ita kuwa Hafsat tun lokacin da ya koma ɗaki da aka jima ta lallaɓo ta hayo katangar ta dawo gidan.
  Yana dawowa daga masallaci ya kewaya bayan gidan nasa yana duba sawun ɓarawo sai dai tun da daga gefen gidan ne kaɗai ƙasa da yake kuda da kwalta ne babu inda sawun ya je, haka ya haƙura ya dawo gidan.
  Yana zuwa ya shiga store ɗin ya ga yadda aka zubar da shinkafar nan ransa ya ɓaci a nasa ganin wannan ɓarawon ya ga makwancinsa. Haka ya sha masifa a gidan babu wanda ya kula shi a ƙarshe ya je ya siyo ƙaton kwaɗo ya datse ɗakin tun da ya ga ashe taƙadarin ɓarawon har mukullin gare shi tun da gashi yana buɗewa.


              BAFFA
             
    Rayuwa ta ci gaba da kaaancewa a gidansa har yanzu babu abin da ya dame shi da matsalar iyalinsa, Mamy kuma koyaushe cikin zulumi take dangane da yaran nata kowane yanzu abubuwan da yake ɓullowa da shi da ban, daga ta toshe waccan ɓarakar sai su fito da wata sabuwa. A ɓangaren Zalika yanzu kanta ya fashe domin kuwa na zaɓawa kanta rayuwa marar kyau da take ganin ita ce mafita a wajenta, rayuwar da wasu daga cikin ƴanmatan zamanjn nan suka zaɓawa kansu wanda ta biyewa shawarar ƙawarta Islam wacce tuni ta yi nisan da vata jin kira rayuwar siyar da mutunci wanda suke ganin holewa ne, bata yi la,akari da yadda mahaifiyarsu take ƙoƙarin inganta tarbiyarsu ba tun da mahaifinsu bai damu da tarbiyarsu ba ya sakarwa mahaifiyarsu ragamar komai.
    
        Zaune suke a wani wajen shaƙatawa su biyu sai wani baƙin Alhaji da mai ƙaton ciki ya gyara zama yana mai saka hannu a aljihu ya ciro waya yana cewa
    
    "Gaskiya islam baki da dama yanzu kuɗin shan ice cream ɗin ne har 500k" Ya faɗa yana ɗan dariya irin tasu ta manyan riƙaƙƙun ƴan duniya a ƙalla ya haife su amma ba ya tunanin abin da yake musu za a iya yi wa nasa ƴaƴan kawai duniyar ce a gabansa.
    
     Islam ta yi wani farrr da idanu ta ce
    "To kai Alaji 500k nawa take a wajenmu ai dama sai dai shan ice cream ɗin ka san dai mu manyan yara ne" Dariya ya yi ya kalli Zalika da take ɗan danna waya ya ce
    
    ",Wai haka ne?" ,Ya tambaya yana ɗaga gira ɗaya wani murmushi ta yi ta ce
    
    "Kai za ka ba kanka wannan amsar"
     
       A maimakon ya saka musu 500k sai ya tura musu 1m Islam tana ganin alert sai kawai ta karkaɗa kai tare da cewa
    "Yesss Alaji shi ya sa kake birgeni ka iya kyauta babu beb ɗin da za ta maka rowar komai tun da kana buɗe bakin aljihu" a faɗa tana mayar da kallonta kan Zalika da take darawa. Ji ya yi kansa ya fashe saboda haka sai kawai ya ce
     "Zalika mu mayar da Islam makaranta sai mu je hotel mu ɗan huta ko" Tana murmusawa ta tashi tsaye Islam ɗin ma ta miƙe tana musu tsiya cewa wato ƴar wariya ce. Sun kaita har cikin makarantar kafin ya karya kan motar suka wuce hotel Islam ta nufi cikin makarantar tana jin daɗin haɗuwa da Zalika kasancewar ita Islam ƴar talakawa ce kuma tana da son ƙarya da son abin duniya, inda ita kuma Zalika ba son abin duniya ne a gabanta ba kawai ta zaɓi wannan rayuwar ne da aka nuna mata ita ce mafita tun da tana ganin mahaifinta bai damu da su ba, sannan dama waje nan ne inda kowane uba zai sakawa ɗansu ido saɓanin ita uwa da take gida sai abin da ya zo kunenta na labari, don uban shi ne jagaban gida duk da uwa ma tana nuna tata bajintar domin dole a jinjinawa uwa ma wajen bada tarbiya.
    
    
       Sai dab da magriba ya ajiye ta a inda suka yj za su haɗu da Islam, kuɗin suka raba inda ta tari napep ta koma gidansu. Yanzu kam tana jin tashen balaga, don Mamy ta lura da sauyin Zalika kan dana shayinta ko jin tsoronta yanzu ko faɗa take mata ma sai ta ga dama za ta tanka bare har ta bata haƙuri. Kawai kamar rai bata ma son a mata faɗan don haka Mamy har ta yi faɗan ta gaji!.
      
     Da daddare misalin ƙarfe uku na dare Mamy ta tashi ta nufi ɗakin Zalika, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta mayar ta rufe, tana ta bacci hankali kwance, don ta ga shi ma Mubin sai wajen tara ya dawo dik abubuwa sun haɗe mata goma da ashirin. A hankali ta lallaɓa ta ɗauki jakar da Zalika ta fita da ita yau ta fito daga ɗakin ta rufe mata nata ɗakin ta nufa tana son a matsayinta na uwa ta fara binciken sirri ba tare da sanin Zalikar ba, tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar ta nufi bakin gado ta zauna gabanta sai faɗuwa yake, don dama ta duba wayarta jiya sai ta ga ta saka pswrd, tana son ta san abin da take aikatawa don tana jin zargi a ranta.

  Hannunta yana karkarwa ta buɗe jakar ta ciro komai na ciki ta birkice sai dai bata ga wani abu da ya danganci rashin gaskiya ba haka ta haƙura tana ɗn jin sanyi da sawaba a zuciyarta, tana dab da mayar da kayan saj ta ga ƙaramun zip daga ciki har za ta rufe jakar sai kawai wata zuciyar ta bata shawarar dubawa ko za ta samu wani abu da zai tabbatar mata wani abun. Tana zige zip ɗin abin da ta gani a ciki ya yi masifar faɗar mata da gaba, a take hankalinta ya tashi don bata san ma ta miƙe tsaye da abin a hannunta ba sai da ta ganta riƙe da abun tana tsaye a kan ƙafafunta cankarkar, jiri ya fara ɗaukanta....


              MEENAL

  Ko a jikinta yayin da take furucin Hajiya kuma cike da mamaki ta ce

"Meenal ko dai makuwa kika yi?" Meenal ta ce
"Ban gane ba Hajiya rass nake a cikin hanklina nake magana, yanzu ke idan su Husna ne suka yi aure a gidan mijinsu za ki so uwar miji ta takura musu? Ni ma nan gidan nawa mijin ne kuma wallahi abin da na ga dama zan yi babu mai taka min bare ya zubar" Tana kaiwa nan ta sauke wayar daga kunenta ta yanke kira ta koma kan kujera ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Nasir kallonta kawai yake jin ya rasa bakin magana ma Hajiya kuma sai ta saki baki tana bin su Husna da kallo wanda su ma ita suke kallo suna jiran ƙarin bayani duk da yanayinta ya so basu wata amsa amma basu fuskanta ba.

   Hibba ta ce

"Mene ne wai Hajiya?" Hajiya ta danne leɓe da haƙuri ta ce

"Ikon Allah wai ni ko dai aljannu sun hau kan wannan yarinyar ne a daren jiya? Gaskiya ba ƙalau take ba ina jin sai an nema mata magani wallahi ba Meenal ba ce" Su ma kalkonta suke nan ta shiga furta musu abin da ya wakana sai Husna ta ce

"Gaskiya abin fa da mamaki ai ko Sadiya da ba ma goyon bayanta bata yi wanna abin da Hajiya akwai dai abin da yake faruwa" Ajiyar zuciya ta sauke don sai yanzu ta ji daɗi da ta yi wannan tunanin amma in a ce gaske ne abin da yake faruwa to tabbas babu maraba akwai gagarumar matsala don ba za ta lamunta ba.

  Kiran wayar Nasir ta shiga yi amma ba a ɗauka ba har ta katse, Meenal cike da yatsina fuska ta ce
"Ko ka karɓi wayar ka ɗauki kiran ko ka kashe don i wallahi ba na son ƙara takura min yake" Kamar wani soko haka ya ga ya koma ya karɓi wayar kafin ya amsa kiran ta katse sai ta sake kira yana kara wayar a kunne ta cr

"Nasir lafiya dai ko, mene ne yake shirin faruwa" Kallon Meenal ya yi sai kuma ya ce

"Babu komai Hajiya" Hajiya ta ce

"Ban gane babu komai ba ko dai akwai matsala ka matsa daga kusa da ƴar tawa zan yi magana da kai" Da to ya amsa ya tashi ya nufi hanyar bedroom muryar Meenal ta katse shi da faɗin

"Wallahi duk wata ƙulla ƙulla da aka yi ba zan ɗauka ba don ni ba bauta na zo ba, in ban da ma ana son yin wata ƙullalleniya ya za a yi ina matarka sai ka matsa za a yi magana da kai" Bai tanka mata ba ya koma ɗaki Hajiya ta rage murya ta ce

"Nasiru wai daga jiya zuwa yau baka fahimci akwai sauyi a tare da yarinyar nan ba?" Nasir ya ce

"Eh na gani Hajiya wani abu ne"
 Hajiya ta ce

"Allah sarki Meenala ni wallahi na san ba ita ba ce yarinyar kirki me biyayya Allah sa ba jifanta aka yi ba wallahi ka san gidan kishiya" 

 Nasir ya ce
"Jifa kuma Hajiya daga zuwa sai a jefe ta, kum... Bai ƙarasa ba ta balbale shi da faɗa tana cewa ya je ya bata kulawa ya mata abin da take so ko ta takale shi da faɗa kar ya kulata don ba a hayyacinta take ba, ba don ya yarda ba ya amince kuma sai ya ji suna saka masa tsoronta a aransa.


  Yana zuwa falo ya ce

"Yanzu mai za ki ci" Ta wani rausaya idanu ta ce

"So nake ka je ka ce Sadiya ta soya min doya da dankali ta dafa min shayin goruba" Kallonta ya yi ya ce

"A gidan nan babu dankali ko ƙwaya ɗaya, bare doya Sadiya ai tuwo take yi dama kayan dankalin a gidan Hajiya suke shi ne nake ci a can kuma yanzu tun da ke ƴarta cw shi ne ta aiko har da ke amma Sadiya ko a cokali bata taɓa aiko mata dankali ba" Kamar daga sama sai ji ya yi ta ja tsaki da sauri ya ɗago ya kalle ta ya ce

"Wa kike wa tsaki" Banza ta masa ya buɗe ƙofar ya fita ba tare da ya ci abincin ba. Yana fitowa ya fice daga gidan dama ya ɗauka mukullin motarsa a falon yana zuwa ya tada mota, ita kuma ta koma ɗaki ta ɗauki waya ta kira ƙawarta ta ce

"Ƙawata" Daga ɗaya ɓangaren ƙawarta ta amsa da faɗi

"Inyee amarya ki ce ta waru, wato dai an dace an tsallake rijiya da baya, tun da na ji muryarki na gane ba matsala amma da ina nan cike da fargaba" Dariya ta fashe da ita ta ce

"Ai na faɗa miki komai ya yi daidai wallahi da bakinsa bai furta ba kuma bai nuna wata alama ba ke gabaɗaya babi wannan maganar fa" Ta faɗa suna ta darawa abin su

Safiyya ta ce
"Shikenan ƙawata sai ki sha sha,aninki gida naki" 

Meenal ta c

"Ai ki ƙaddarw ni kaɗai ce a gidan nan bani da kishiya kuma sai na koyawa kowa hankali"

 ,Safiyya ta ce

"Girmanki ne ai yanzu zan haɗo kan ƙawayenmu yuya guda mu zo" Nan ta bata labarin yadda suka ƙare da Hajiya tana kashewa ta kira Momi mahaifiyarta bayan sun gaisa Momi ta ce


"To ya kika ga yanayin zaman karki kuskura a rainaki matsawar dangin miji suka rainaki kowa kanki zai zuba shara da bola gwara a raba rani kowa ya ɗauka ko ita Hajoyar karki raga mata domin kowa kansa yake so ita ma duk yadda muke da ita ɗanta za ta fara so" Nan Momi take ɗora ta har tana faɗawa Meenal cewa za ta je wajen malamin ta ya dasa soyayyarta a zuciyar Nasir da kuma ƙin son rabuwa da ita duk runtsi!.


  Nasir yana fita ya nufi gidan Hajiya, ya samu Hajiya zaune suna ta magana da ƙannaensa Hajiya ta dube shi ta ce

"Wai Nasir ya na ganka duk a firgice kamar ba mai sabon aure ba" Nasir ya busar da iskar da ya cika bakinsa da ita ya ce

"Hajiya wasu halayya ne nake gani daba wajen Meenal duk abin ya ɗaure mini kai ... Tun kan ya kai aya ta tari numfashinsa da faɗin

"An faɗa maka ba cikin hayyainta take ba amma ni na san ƴata ba irin ƴnmatan zamani ba ce" Ya yi ɗan shiru ya ce


"Gabaɗaya ta sauya kamar ma ba sabuwar amarya ba"
 Nan Hajiya ta fara faɗin sai ta je ta samo mata magani wataƙila jifanta aka yi ko dai an yi mata wani abu da ya saiya mata tunani. Ko faɗawa ƙawarta mahaifiyar Meenal bata yi ba ta kama hanyar gidan malami ta ce ya bata karya tambaya bayan ta gama rattabo masa bayanin abin da yake faruwa ya bata tabbacin idan aka yi amfani da maganin komai zai warware.


   Lokacin da ta baro gidan malamin bata zame ko ina ba a napep sai gidan Nasir lokacin Nasir ya koma gidan ganin taron ƙawayenta sun cika falon wasu ma yana iya jiyo hayaniyarsu a bedroom, hakan ya sa ya faɗa mata zai ɗan fita bayan ya ɗakkowa Sadiya tsakuran abin da za ta dafa wanda ba zai isa ba ya bata. Shi a tunaninsa ƙawayen kawai ratsowa ne suka yi sai kawai Meenal ta ja shi gefe ta ce masa


"Nasir ina mukullin store" Da mamaki yake kallonta sai dai kuma ya danne mamakin ya ce

"Mukulli kuma?" Ta ce


"Tambaya kake ko neman sani?" Lafazin da ta yi ya so bashi mamaki don shi abubuwa ne sabbi a wajensa Sadiya bata taɓa masa tambaya ko bashi amsar rainin hankali komai cikinn girmamawa da mutuntawa matsayinsa na mijinta. Cike da mamakin dai ya ce

"Mai za ki yi da mukullin store?" 

 Ta ce 

"Wai ban gane ba shi mukullin store ɗin har wani abu ne da za ake tuhumar mutum don ya ce a bashi?" Hannu ya saka a lajihu ya fito da mukullin daga ciki da yake mukullayen suna da yawa a haɗe sai ya nuna mata wanda shi ne na store ɗin, tunaninsa ko zuwa za ta yi ta ga yanayin store ɗin sai kuma ya ga ta saka hannu ta cire mukullin daga jiki ta miƙa masa sauran, tsabagen mamaki ma ya kasa magana ko ƙara bi ta kansa bata yo ba ta yi gaba, duk abin da suke Sadiya tana kallonsu kasancewar labule windonta a ɗan ɗage yake sannan kuma tana iya hangon su.


  Wani murmushi ta yi a zuciyarta ta ce

"Mafari kenan" 

 Kicin ta wuce tana ƙarewa kicin ɗin kallo ta ga kayanta a gefe kayan Sadiya ma haka a wulaƙance take kallon kicin ɗin duk da a share yake tas a goge sai gawayi da yake gefe da Sadiya ta ɗora ruwan abinci a ƙaramar tukunya ita saboda ana zaluntar ta ma ko kuɗin mahaɗin ba a bata ba bare kuma a bata don mugunta saboda ya ga tana sana,ar mai, amma duk da haka bata ma tanka masa. Meenal ganan cooker gas ɗinta ta ƙarasa ta ga silindar gas ɗin babu komai ai kuwa da sauri ta fito tana ƙwala masa kira don har ya juya ya je zaure ya juyo ya dawo shi ya rasa ma mai ya sa ba ya mata tsawa ko kuma rainin hankalin da yake yi wa Sadiya wacce duk wani cin kashi yake saukewa a kanta.

Yana zuwa yake binta da kallon rashin fahimtar kiran da ta masa, yana ayyanawa a ransa wannan wace irin amarya ce da bata kara ko kunya a kwana ɗaya tak ta saki jikinta tana sha,anainta tamkar dai dama ta daɗe a gidan, ba ma wannan ba sai ya ga yanzu ta daina wannan tafiyar da take tana tale ƙafa. Wani farr ta yi da idanu ta ce

"Ka tafi da wannn silindar a sako gas" Ɗan dimm ya yi abu ne da bai saba ba shi har ya manta ma da ya sayi wani gas tun lokacin da Hajiya ta dakatar da ake sakawa Sadiya ta ce ta koma amfani da gawayi ai kuɗin ya yi wani amfanin da shi sai gashi kuma yanzu za a ɓallo masa ruwa, tunanin da yake kenan ita Meenal ɗin ba za ta yi amfani da gawayin ba ko yaya? Tunaninsa ya katse ne daga inda ta ce
"Amma fa karka sako mana have a ciko shi sosai" Da alamun tambaya a fuskarsa don ya kasa jurewa ya ce
"Dama ba a gidansu amarya ake ciko silinda ba?" Wani yatsin fuska ta yi ta ce

"Haba Alhaji Nasiru uwata ce za ta cika maka gas ɗin ma sai ka ce ita za a dafawa abincin" Bai tanka mata ba ya wuce ya ɗauki silindar ransa duk babu daɗi, yana kusa da ƙofar zaure ta ce

"Nasir ka siyowa ƙawayena snacks da drinks masu sanyi saboda yanzu rana ta yi idan suka ci sai su yj girki sun ce min basu karya ba, kuma iya sauran abin da muka ci da dare suka ci" Tsabar mamaki ma sai ya ji kamar ya wanka mata mari yana ta tunanin to ita bata da aiki sai kawo buƙata daga tarewarta jiya bayan sun kwaso yuya guda babu izininsa sun cika masa gidan sannan banda abincin da za su girka ake batun ya siyo wani bayan shi abincin ma bai samu natsuwar ci ba sai ma yake ga kamar bata damu da shi ba. 
  Ƙarfin hali ya yi ya ce

"Haba Meenal yanzu ƙawayen nan naki kusan rai goma duk ni zan siyo musu abu?" Tana masa kallon ko dai ka kasa ta ce

"Nasir su goma sha biyar ne fa, wasu ma don basu zo ba yadda nake da farin jinin ƙawaye ai baka ga komai ba wasu ma a gaba za suke kawo mini yini ka ga kuwa ai dole a tarɓe su don ni ba zan yi abin kunyar da ƙawayr za su yi gaba suna gulmata ba" Ta faɗa ba tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta shige falo sai shewarsu ya jiyo. Kai ya kaɗa ya fita ya buɗe but zai saka silindar tsayuwar napep ɗin Hajiya ya dakatar da shi, fitowa ta yi tana ba mai napep kuɗinsa.
  
  Bakin Hajiya kamar ƙofar gari haka yake a buɗe don tana miƙawa mai napep kuɗi ne amma idanuta suna a kan silindar gas. Da sauri ta juyo tana rufe bakin jakar hannunta ta ce

"Nasir mene ne wannan ? Ina za ka je da shi"
 Cikin sanyin murya ya ce

"Gas zan sako"

 Hajiya da mamaki ta ce

"Gas kuma Nasir na ɗauka ma siyar da silindae za a yi" Nasir ya ce

"Meenal ta ce in ciko musu da gas"
 Hajiya ta c


"Ka ciko musu kuma, yaushe yarinyar nan zuciyarta ta zama kare ya ɗauke yanzu har ta ɗauki kishiya wata tsiya da za ta ce a ciko musu gas, ni yanzu dama an saya mata kuka gas ne Meenal ɗin to mai ya hana a ciko mata da gas ɗin daga gida wannan ai ɗora nauyi ne ko zazzaɓin haɗa lefe bai bar aljihunka ba hallaw za a ɗora maka wahala" Ta faɗa tana kumfar baki Nasir ya ce


"Hajiya ba fa ita da Sadiya ba ƙawayenta ne fa a gidan suka zo za su yi girki" Har da dafe ƙirji ta ce


"Girki kuma? Ni ina tunanin abincin da na aiko da safe ya isa ku ci har rana kai da ita dai don cikinku kaɗai, shi ne yanzu za ta tsiro da girki bata san ni duk abin da zai hargitsa lissafin aljihunka ba so nake ba, su ƙawayen biyu ne ko uku, wannan ai tada mai gida tsaye ne ba don ba a hayyacinta take ba wallahi ba za a yi wannan rashin hankalin ba" Ta faɗa tana kumfar baki.


  Nasir ya ce

"Su goma sha biyar ne ƙawayen kuma ta ce in taho musu da snacks da drinks kafin a ɗora abinci" Haɓa ta riƙe tana nuna da sake amma babu mai nakasta mata aljihun ɗa fon haka sai ta ce ya je ya tafi za ta yi wa tufkar hanci don sai dai idan ya kawo snacks da drink ɗin kowacce shegiya ta ɗauka ta nufi gidan ubanta amma ba za a zauna a dafa musu abinci ba su masa ƙasa da tattalin abincinsa.


  Yana jan motar ita kuma tana shigewa gidan duk ranta a ɓace da a ce ba Meenal ba ce ta yi wannan ɗanyen aiki da sai ta saɓar mata, da sallama ta shigo Sadiya da za ta je ta duba tukunyarta ita ta amsa mata da fara,arta cike da girmamawa wani irin taɓe baki Hajiya ta yi a zuciyarta tana faɗin

'Gulmammiya uwar ƴan kissa" Ta juya ta kalli Kalifa ta masa magana tana mai ɗaga masa hannu ta ce

"Biyoni ɗakin ƴar gwal sabuwar uwarka ka ga ɗaki kamar a turai yarinya ta sha jere iya ganin mutum, duk hassadarsa sai ya yaba ko da a zuciyarsa ne ba a fili ba" Ta faɗi hakan ne dama don ta faɗawa Sadiya magana Sadiua kuwa bata ce komai ba sai ma ta
ce

"A fito lafiya" Shi dai Kalifa bai bita ba, tun kafin ta shige ɗakin take jin hayaniya da shewa irin na ƴan mata. Da sallama ta shuga amma tsabar surutun da suke basu amsa ba kuma ba wai don basu ji ba suna ji kawai ba za su iya katse hirar da suke ba.

   Har ta ƙarasa tsakiyar falon wasu a ƙasa a zaune wasu duk sun baje a kan kujerar wasu suna danna waya, sai wata da taee riƙe da plate tana cin dankalin daga cikin wanda suka ci na wajen Hajiya da ta aiko. Ran Hajiya ne ya ɓaci ita da take son a cancana abinci amma dai waɗannan sun zo za su yi almubazzaranci. Ganin babu wanda ya bata waje ta zauna irin cikin girmammawa a matsawa babba waje ya zauna ko a tashi a bashi wajen, sannan ta lura babu Meenal a falon hakan ya sa cike da nuna gadarar ta ita a dole uwar miji wato mamallakin gidan ta ce

"Wai ku babu manya a gidajenku, ya kuna ganina babu wacce ta mayar da ni mutum kowacce tana sabgar gabanta?" Tamkar tana magana da bango aikuwa ta harzuƙa cike da masifa take faɗin

"Yanzu za ku haɗa ya naku ya naku ku san na yi" Ta faɗa tana dosar bedroom ɗin da take jin wasu suna hanyaniya a inda take jin har da muryar Meenal ƴarta. Daga mai taɓe baki sai masu mata shewa. Tana shiga ta ga su huɗu ne kowacce ta waigo tana kallonta biyu a bakin gado a zaune kasancewar an sauya bedsheet ɗin sai dai babu wanda ya share don a cewar Meenal ma ɗakin bai ci a shere shi ba bashi da wani datti.

  Ɗaya tana tsaey gaban madubi tana shafa powder sai Meenal da take tsaye gaban gadon ta dafa kafaɗar ɗaya daga cikinsu suna magana, baki sake suke kallon Hajiya da Meenal ta ƙanƙance idanu saboda tsabar mamakin ganin uwar miji a ɗakinta ba ma falo ba, abun ya mata ciwo amma sai ta danne ta tsaya jin dalili don ta saka a ranta matuƙar tijara Hajiya za ta mata a kan maganar dankali da doya da ƙwai da kayan shayi sai ta yi wa Hajiya tass sai dai koma mai za a yi a yi don babu wani mahluƙi da zai taka mata birki dangane da cin kayan kowane abinci sai ta zaɓa ta darje.

  Hajiya ta kalle su a gadarance ta ce

"Ku bamu wuri za mu tattauna da ɗiyata" 

  Da kallo kawai suka bita sai Meenal cike da tsaurin ido na ƴanmatan zamani ta ce

"Hajiya ni da su duk ɗaya ne ai za ki iya faɗar komai a gabansu waɗanann shaƙiƙan aminai na ne ko baki faɗa a gabansu ba sai na faɗa musu gwara ma ki rage min aiki kin ga in suka ji a kan kunnensu ba sai na maimaita ba" Hajiya kaɗan jakar hannunta ta suɓuce tsabagen mamakin kalaman Meenal amma kuma tuno da cewa ba hayyacinta take ba sai ta ce

"Haba ke kuwa wanna  ai sirri ne tsakaninmu" Kafin Meenal ta ce wani abu ƙawarta Safiyya ta ce

"Ƙawata bari mu je waje bani mukullun store ɗin" Meenal ce ta miƙa mata mukullin ta ce

"Yawwa ku auno kayan abincin yadda zai isa, kun ga an jima wasu za su zo sannan da yamma ma ba za a rasa masu zuwa ba bana so abinci ya yanke in kuma za ku shiga kicin sau biyu to" Ta faɗa tana ƴar dariyar tsokanarsu don ta san ba za su yarda su shiga kicin sau biyu ba sai Safiyya ta 
ce


"Kema kin san ba za mu shiga kicin sau biyu ba sai dai mijin naki angonki ya siyowa sauran baƙin da za su zo abinci, amma dai yanzu za mu lodo isasshe wanda kowa zai isa sai a juye sauran a kuloli"

 Meenal ta ce

"Kuma za a kai gidanmu kun san akwai baƙin da basu tafi ba kuma ba na son Momi ta yi wahalar bada abinci tun da ina gidan miji kin ga ta huta" Juyawa suka yi suna mata na,am da maganrta Hajiya kuwa tun da suka fara tattunawa ta zama mutuntume, tamkar gunki haka ta koma, ta rasa ma abin faɗa tsabar mamaki wato mukullin store ne a hannun Meenal har take da damar ba ƙawaye su lodo ɗanyen abinci su dafa duk yawan ƙawayen nan a ce wai akwai wasu da za su zo, sannan ma wai har gidan mahaifiyarta za a kai don kar ta sha wahala wato ita nata ɗan ya wahala ya nemo tabbas da sake ko kima da badaƙala don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, dole ta magance matsalar nan ta hanyar maganin dawo da Meenala hayyacinta ta san abin da take ta dawo mai ladabi da sanin ya kamata kamar yadda ta aurawa ɗanta ita a farko!.



     Muryar Meenal ce ta katse ta da ta c

"Hajiya ina jinki" Ta faɗa wani gatsal babu sakayawa irin na girmamawar da ta saba tana mata, tana maida kallonta kan Meenal sai ta ga tana riƙe da ƙugu. Hajiya ta sassauta murya ta ce


"Ƴata Meenal" Sai Meenal ta ce


"Ashe dai arziƙi ne ya kawo ki ba tsiya ba ni wallahi na ɗauka maganar dankali ce ta kawo ki har na fara tanadar kalaman da zan mayar da martani, ah to in ce Hajiya an faɗi babu nauyi yanzu a ce a kan dankali ki taso tun daga gida" Ta faɗa tana ƴar dariya kamar a wasa. Abin ya baƙantawa Hajiya rai duk da tana tunanin ba cikin hayyacinta take ba.

   Danne zuciya ta yi ta ce

"Ba wannan ya kawo ni ba Meenala" Ta faɗa tana buɗe jakarta ta ɗakko wani ƙullin magani a leda fara da baƙa. Ta ce

"Wannan na farar ledar ki jiƙa a ruwa ki yi wanka, shi kuma na baƙar ledar sai ki sha a shayi" Ta faɗa tana bata amma bata karɓa ba ta jefe mata tamabayr

"Maganin mene ne?" Hajiya sai da ta ɗan waiwaiya gudun kar wata ta taho daga cikin ƙawayen ta ji ta juya tana fuskantar Meenal tana sassauta murya gudun ma kar Sadiya ta musu laɓe ta waje ta ce


"Maganin karayar asiri ne, da alama jifanji aka yi Meenal tun da safe bakya cikin hayyacinki" Wata bazawarar dariya Meenal ta yi ta ce


"A hayyacin wa nake to? Mai ma na yi?"

 Hajiya ta ce
  "Meenal maganganu karazube kike yi babu taunawa bayan ba haka kike ba duk kin sauya ko ni kina min magana kamar sa,arki, haka su Hibba da suka zo da safe ma kika ƙi ganinsu ina jin ma baki san sun zo ba saboda bakya cikin hayyacinki, dama zama da kishiya sai da takatsantsan babu abin da ba za ta yi ba din ganin ta dusashe haskenki a idanun mutane da na dangin miji, jin an ce kina da ladabi da biyayya da girmama na gaba da ke ta shiga ta fita za ta ɓata miki asali"

  Meenal ta ɗan lunshe idanu ta buɗe ta ce

"Bari ki ji in faɗa miki rasss nake, ke baki san a zamanin da ake ba ne yanzu? Ya za a yi kyakkyawa da ni yarinya ɗanya sharaf ƴar zamani in zauna miji ko uwar miji suna juyani kamar wata waina? Idan ma za ki ɗauke idanunki daga sabgar gidan ɗanki to ki kauda idanunki ki bar mu mu shaƙata mu more amma in kika ce za kike shiga sabgar da ba ruwanki ki yi uwa da makarɓiya wallahi hawan jini fa ciwon zuciya zai kashe ki" Meenal ta faɗa cikin halin ko in kula tana cikin faɗa wayarta ta yi ƙara ta duba ta ga Nasir ne sai da ta shawaɓe fuska alamar shagwaɓa ta kara wayar a kunne tana wani buga ƙafa kaɗan a ƙasa ta ce

"Baby ka je ka zauna ka barni da kewa" Hajiya neman mai Jijjigata take yi don ta tashi daga mafarkin da take don abin ya shallake tunaninta an barta riƙe da ledojin maganin da sai da ta zare naira na gugan naira har naira dubu goma aka bata, duk don a dakatar da rawar kan Meenal a dawo da ita hayyacinta take mata biyayya ya zamana ita take jan ragamar gidan ɗanta amma sai gashi Meenal tana tababtar mata cikin hayyacinta take da alama ma inda kunya take Meenal ko ta wajen bata bi ba.


  Daga ɗaya ɓangaren Nasir ya ji wani daɗi da ta masa magana shi dama ba ya son wannan gadarar da take masa hakan ya sa ya washe baki daidai nan Meenal ta danna handsfree Hajiya ta jiyo muryarsa yana faɗin


"An ciko gas ɗin taɓ kuwa amma ya ci kuɗi ko dama tsada yake ko don na daɗe ban saya ba na saba siyan buhun gawayi kuma Sadiya da adani sai ki ga ya daɗe tana amfani da shi" Hajiya jin an ce gas ya ci kuɗi ranta ya ɓaci ta fara tunanin yawan kuɗin kamar a aljihunta aka fitar tana tunanin yanzu idan hsr haka gidan Nasir zai ci gaba da kasancewa a hannun ƴan sari to ya za a yi da auren Hibba da Husna bayan shi ne komai nasu.

  Meenal bata amsa masa maganar wancan ba ta ce

"Sweet heart lemukan nan fa ba kala ɗaya za ka siyo ba ka haɗo kaloli, sannan ka ƙaro da mararsa sanyi kamar katan biyar sai a saka a frige saboda baƙi" Da to ya amsa mata sai da ta saci kallon Hajiya da take cike kamar za ta yi bindiga ta sassauta murya ta ce

"Ka taho min da fanadol jikina duk ya ɗau zafi saboda aikin da ka kwana kana yi

 Shi kuma ya ce

 Ai kam jiya na... Kafin Hajiya ta gama jin mai zai ce ta juya har tana haɗawa da gudu ta yi hanyar falo....


  MAMAN AFRAH
   ***