RIKITACCIYAR ALAƘA

3

by @diamondbhatool3

Ringing ɗin da wayarta ke yi yasa ta dakatar da zancen zucin tare da mayar da dubanta ga screen ɗin wayar. Ganin _SMFM_ yasa tayi picking tana murmushi.

“Hello my charming prince ” ta faɗa tana gyara kwanciyarta.

A ɗaya ɓangaren ya amsa da

“My charming princess... how's your day?, ɗazu na kira ki but your phone isn't reachable”

Murya ƙasa tace “Sorry my Man, mun je na sauya wayan ne ban kuma kai ga charging nata ba hala time ɗin da ka ƙira, how're you doing?”

“Fine babe, ki ce munyi waya, dama kince you're updating yours to the latest version, anyways dama kuɗin da zan tura Miki ne, I've been searching for the account details na rasa, perhaps ban san na goge ba Please ki ƙara texting min kinji?”

“Ok babu damuwa”

Daga haka tayi hanging out call ɗin sannan ta tura kamar yadda ya faɗa tana murmushi kamar wata mai aljanu.

Slowly tace “Talauci, God forbid! ko sunansa ban son naji an faɗi, Allah ka aurar da Ni wa mai kuɗi wanda zan yi facali da Naira ba tare da jin zafi ba”

*Imaan*

Tun lokacin da wayar Ihsan tayi ƙara ta farka daga baccinta sai dai tana tsoron tashi ta tarar da Bala'in Ihsan, ta San halinta sarai, ba mutunci gare ta ba sai ta nemi wulaƙanta ta a banza. Fitsarin da ya matsa ta yasa ta miƙe don ta je tayi ai kuwa caraf Ihsan ta dakatar da ita.

“Ke kuma jakar Company ba na hana ki yi min laɓe ba?” ɗauke da mamaki a fuskar Imaan ta dubi Ihsan Jin ta zo mata da wani sabon batu.

“Laɓen me kenan Ihsan?”

“Kinga Bana son zallar munafurci, Ni na faɗa miki da ki daina kiran sunana haka with this dirty mouth of yours, Haba shi talaka ko ina sai ya nuna halinsa, mtsss”.

Jijjiga kai kawai Imaan tayi ta fice ta barta tana bambaminta ita kaɗai.

Ta dawo zata wuce corner nata Ihsan tace “Ke dalla jakar Company dakata!” kamar wadda aka yi wa brake Imaan ta tsaya.

“Kin ji wayar da nayi ko?”

Cikin sanyin murya Imaan tace “Ya za a yi naji wayar da kike yi kuma?”

A hasale Ihsan ta miƙe tayo kan Imaan da USB a hannunta.

“Munafuka wallahi kinji, na faɗa miki tun ba yau ba ki daina min irin wannan laɓen naki na munafukai amma kin ƙi, wallahi yau mai raba mu sai Allah” kawai sai ta hau Imaan tana zuba mata USB cable ɗin. Ciki uku tayi mata kafin ta haƙura saboda ƙarar da wayarta tayi alamar shigowar saƙo, ita dai Imaan bata ce komai ba duk da cewa a girme ta girmi Ihsan ɗin Amma in da sabo ta saba da cin kashin da Ihsan ɗin ke mata gashi kuma babu damar ramawa tun da goyon baya ta samu na yin hakan..

****************

Ganin lokacin salla da yayi yasa ya miƙe tare da fitowa daga office nashi ya nufi masjid nasu da ke cikin Companyn. Bayan ya yi salla kuma ya dawo, nan ya tarar da su JK suna ta hayaniya, tsaki kawai yayi ya wuce bedroom nasa. Yana shiga yayi wanka, fitowar shi sanye da bathrobe da Kuma farin towel yana goge sumarsa yayin da jikinsa kuma ke fidda daddaɗan ƙamshin shower gel ɗin da yake amfani da shi, ya fara shafa creams ɗin da ke jere gaban dressing mirror ɗin da zaka yi tsammanin na wata hamshaƙiyar mace ce mai ji da kanta sai wayarsa tayi ƙara alamar neman agaji amma yayi ignoring, ƙiran wayarsa da aka ƙara yi a karo na biyu yasa ya miƙe da sauri ya ɗauko ta sannan ya dawo ya zauna kan stool ɗin da ke gaban mirror ɗin.

_Ummah_ ya gani rubuce, da sauri ya katse ƙiran don shi haka ɗabi'arsa take, baya taɓa bari yayi waya da credit ɗin iyayensa. Ƙara ƙira yayi, jin ta shiga yasa ya sauƙe ajiyar zuciya tare da kwantar da kansa yana lumshe idanuwansa.

Daga can ɓangaren aka yi sallama wanda ta sa ya ɗan buɗe ido a zabure alamar dai ya ɗan faɗa izuwa duniyar tunani ne.

Cikin daddaɗar muryarsa ya amsa sallamar yana faɗin “Ummah!”

Daga can ɓangaren Muryar matar ta ƙara faɗin

“Sweetheart!” sai kuma tayi murmushi mai sauti tana faɗin “Ka ga na ƙara ƙiranka though bamu daɗe da gama magana ba ko?”

Shima murmushi yayi wanda ya ƙara bayyana kyau da Allah yayi masa.

“Kai Ummah, don't tell me you're missing me so madly”

ƴar dariya ta ƙara yi ta ce “You guess it right son, I'm so eager to see you home shiyasa kaga na ƙara ƙira, Abie ɗinka ya ce you're coming home in three days time”

Murya shagwaɓe kamar ba wannan gwarzon ba ya ce “Kai Ummie, shine ki ka kasa mancewa? So kike ki sama kanki damuwa uhm?”

“No son” ta amsa masa “ just can't wait to see you, tun yanzu ka faɗa min me da me zan shirya maka!" Shiru tayi tana nazari can tace "Oh! I remember, your favourite?, zanyi maka snacks da yawa.”

Murmushi yayi ya lumshe idanuwansa sannan yace “You'll always be my best Ummah, Bari na gama shiri, yanzu na fito daga bathroom”

Da sauri Ummie ta ce “Alright, ka shirya, i love you” sai kuma ta yi masa kiss ta yadda zai iya jiyowa. Fuska sake shima yace “Love You too Ummah” sannan ya mayar mata da kiss ɗin.

Ita ta fara hanging call ɗin, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ajiye wayar kan dressing mirror sannan ya cigaba da rubbing creams ɗin da ke jere gabansa ɗaya bayan ɗaya har ya kammala. Jallabiya ya sanya sannan ya fesa turaruka har iri huɗu, _tom ford, kay Ali, coco noir, replica_ da kuma _Henry rose_ tuni suka bada wani irin sassanyan ƙamshi mai tsayawa a rai, yana gama fesawa ya ɗauki phone ɗinsa ya fito parlour. A nan ya tarar da su JK har lokacin suna zaune sai uban surutu yake da ƙaramin yaro.

Taɓe baki yayi wondering why is JK acting immaturely, ya rasa da wa zai yi surutun ma sai da Asim, 7years old child, Kai!. Haka dai ya ƙarasa wurinsu fuskarsa babu yabo babu fallasa. Yana zama cike da tsokala JK ya ce “Asim in munje ai zaka raka mu wurin budurwar tawa ko?” Asim yayi ƙasa da murya gudun kada ya taɓo AK ya ce “Da wa da wa za mu je?"

Cikin muryar da ya tabbatar AK ɗin zai ji shi ya ce “Da AK” ɗan zaro ido Asim yayi ya ɗan saci kallon Jalaal ɗin, ganin kamar hankalinsa ba ya wurin yasa ya sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da kallon Jahaan sai kuma ya kama bakinsa da hannayensa biyu yana zaro idanuwansa waje.

Ganin za su ɓata masa rai ne ya sa ya miƙe ya koma bedroom tare da kiran Ummah, hira suka yi sosai har take sanar da shi akwai suprise ɗin da za ta masa immediately ya dawo, he's super eager to see what's that thing.

*KUƊA ESTATE, BAUCHI, BAUCHI STATE*

Estate ne mai ɗauke da tsari gwanin burgewa, ba wani babba ba ne can kasancewar ba su da yawa sosai, amma tsarinsa kaɗai mutum ya gani zai so shima ya kasance cikinsu. Gini ne irin na zamani, ga kuma flowers bishiyoyi iri-iri waɗanda ke tafiyar da damuwa da sanyawa ruhi salama da aminci. A ɓangaren Alhaji Abubakar Kuɗa wanda ke ɗauke da sassa uku, Ummah ce ta fito daga nata sashen ta nufi sashen Ummie, kan Sallaya ta tarar da ita tana sallar walaha. Fuska sake ta zauna akan kujera tana faɗin "Tasalla Sarkin salla, Allah dai yasa muma kina tsunduma mu cikin sallar nan."

Sallama Ummie tayi sannan ta dubi Ummah tana murmushi, sai dai ba ta ce komai ba don tana son yin wasu zikirorin, itama Ummah ba ta ji komai da hakan, don in da wanda zai faɗi wace ce Ummie, to bayan ita ce, don rayuwar da suka yi, babu wani abu na Ummie da ba ta sani ba.

"Ummah!" Ummie ta faɗa tana miƙewa tare da naɗe sallaya ta dawo gefen Ummah ta zauna.

"Kin ji wai Jalaal zai zo nan da kwana biyu?"

Shiru Ummie tayi na ɗan wani lokaci kafin ta saki wani malalacin murmushi.

"To Ni ina zan sani Ummah Jalaal, nikam ai ƴar kallo ce."

"Kamar ya ƴar kallo kuma Chubaɗo?"

Wani murmushin Ummah ta ƙara yi sannan tace "To mana, idan ya zo na ganshi ai ko?"

"Hmm" Ummah ta gyara zama sannan tace "Lallai Fulani dai sai ku, ki haifi abun amma kina juya masa baya?, Ko dan, mu da Allah bai ba mu ba ai ga shi na kowa ma so muke"

Ajiyar zuciya Ummie tayi tana ƙara tausayawa Ummah bisa wannan jarrabawar ta rashin haihuwa da Allah ya jarabce ta tare da fatan Allah ya ba su ikon cinyewa. Cikin son danne rauninta tace "Ki daina faɗin haka Ummah Jalaal, haihuwa ta Allah ce, yana baiwa wanda ya so ne, bari na tunatar da ke, ita kanta haihuwar ga wasu ba Alkhairi ba ne, wasu sai ki ga Allah ya ba su, amma silar ƴaƴan sai su saki hanya, don haka, ki saka a ranki muƙaddari ne daga Allah hakan ma, ta wani wajen kuma ki ƙara gode masa da ya baki ɗa ɗaya tamkar da dubu, a kowanne lokaci sannan feelings ɗin ya tasar miki Ummah Jalaal, ki tuna da ɗanki Jalaal, don haifa miki shi kawai nayi, amma naki ne halak malak, na san ko bayan raina, zai kula da ke ko ba a matsayin matar uba ba, a matsayin wacce ta ceci mahaifiyarsa." Cikin cool and weak voice nata ta kammala maganar tare da goge wasu siraran hawaye da suka zubo mata sannan ta riƙo hannun Ummah, "Don Allah Ummah Jalaal, ki daina yi wa yaronki kuka, sai nake ganin kamar ya gaza miki ne"

Jijjiga kai kawai Ummah ke yi tana kuma ƙara jinjina girman sadaukarwar da Chubaɗo tayi mata, daga bisani ta iya furta "Na daina Chubaɗo, na daina kuka, tabbas ke ɗin ƴar halak ce, haka zalika Jalaal, ku ɗin na daban ne kasancewar ku kyauta ta Musamman daga Ubangiji zuwa gare Ni."

Hannu Ummie ta sa ta gogewa Ummah hawayen da ke kwance kan fuskarta.

A wannan yanayin maigidan nasu ya shigo, tun daga yanayin da ya tarar da su ya tabbatarwa kansa cewa labarin gizo ba zai wuce na koƙi ba, same time kuma yana ƙara jinjina irin soyayyar da ke tsakanin Chubaɗo da Zulaihat tare da fatan ko wacce kishiya ta rungumi abokiyar zamanta kwatankwacin yadda Chubaɗo da Zulaihat suka kasance. Ganin kamar ba su lura da shi ba yasa ya koma sashensa.

Bayan Wasu daƙiƙu Ummie ta dubi Ummah, don ganin ta kawar da damuwar da ke kan fuskar Ummah yasa tace

"Hala yanzu ma tashin ki daga barci Ummah Jalaal"

Ummah ta gyaɗa mata kai

"Za ki karya a nan ko kuma can za a kai miki?"

"Kawo min nan ɗin, bari na je nan wanke baki."

Ummie tace "To" daga haka ta wuce kitchen Ummah kuma ta wuce sashenta, few minutes later ta dawo. Bayan ta karya kuma a nan ta shantake, sai lokacin sallar zuhur ta koma nata sashen.

*******************************

*AZARE*

Imaan ce zaune da wata abokiyar aikin a SOHAAN bayan sun idar da Sallah a masallaci. Jamilah ta dubi Imaan tace "Imaan kin san me?" Imaan ta jijjiga kai. Har jamilah za ta ce wani abun sai kuma tayi shiru. Abun ka da gulmar da ke cin ɗan adam, can ta ƙara duban Imaan ɗin ta ce "Kika ce wai ba ki san me ake cewa a Companyn nan ba?"

Imaan ta amsa mata da "E, kin san ba kowa nake magana da shi ba bayan ke."

"Hmm"

"Me yake faruwa?"

"Ke me tunaninki ya kawo miki?"

"Babu komai Jamilah, wani abun ne hala?"

Jamilah ta gyara zamanta tace "Hmm, wai ki san Zuhra ta wajen beverages?"

"Zuhrah?" Imaan ta maimaita tana ɗan ɗaga kanta sama trying hard ta gano Zuhrah.

"Ok, wannan ƴar gayun?"

"Yauwa, ke ce ma ita."

"Me ya same ta?" Imaan ta tambaya tana mai lumshe Idanuwanta.

"To bari ki ji, an dakatar da ita aiki, MD da kansa yayi hakan, amma naji ƙishin-ƙishin ɗin cewa wai ta neme shi ne."

Idanuwa Imaan ta ware tana faɗin "What?"

"Abun da kika ji dai Imaan, kuma wallahi Ni na yadda, don wannan shigar banzar da Zuhrah ke yi in cewa aka yi ta nemi ko uban waye ba zan yi mamaki ba."

"Allah ya kyauta, tashi mu koma bakin aiki kafin Madam ta zazzage mu kin ji?"

"Ai kuwa dai, da Ni kadai ne na san babu abun da za ta yi, amma tun da da ke garanti sai ta tsige mu. Babba da ita amma tana haɗa ƙugu da yara, mtsss" da haka suka koma bakin aiki, cikin ikon Allah Madam ɗin mal ba ta nan.

Bayan sun tashi daga aiki, ta ɗebi nata snacks ɗin don wucewa, har ta ɗaga hannu za ta tsayar da ɗan sahu ta tuna yau babu kuɗi a hannunta, hakan yasa ta lumshe idanuwanta tare da fara takawa a hankali. Tana cikin tafiyar ne kuma wani mai mota ya tsayar da motarsa daf da ita, tsorata ma da farko tayi, a tunaninta ita ta kaucewa hanya, hakan yasa ta koma ta can gefe sannan ta ci gaba da tafiya with full caution.

Sai da ta kusa shiga layinsu karab ta ƙara ganin motar nan kusa da ita, da sauri ta dudduba don ganin ko dai ita ce yanzun ma ta kau layi, ganin dai ba ta hau hanya ba yasa ta ɗago da Idanuwanta, a wannan lokaci, mai motar ta sauƙe glass ɗin motar, ta ciki ya karaɗo sallama. Ta san hukuncin amsa sallama a addinance hakan yasa ta amsa daga haka ta ci gaba da tafiya tana Allah Allah ta shiga layinsu.

Kamar mutumin ya san me take faɗa cikin ranta ya fito daga motar ya bi bayanta, yana isowa saitinta ya ƙara yi mata sallama. A ɗan tsorace ta amsa ba tare da ta tsaya ba.

"Yi haƙuri ki ba Ni Ko minti uku ne ƴanmata, na san ba kima ko mutuncinki ba ne na tsayar da ke kan hanya, ki ba Ni lambar wayarki, daga nan sai na ƙaraso."

Ba tare da ta tsaya da tafiyar tata ba tace "Ba Ni da waya"

Mutumin yace "What?" While fuskarsa na nuna mamakin amsar tata.

"To don Allah ina ne gidanku?"

Da sauri tace "Ba a garin nan nake ba, hutu nazo"

Ƴar dariya yayi ganin yadda fuskarta ta sauya Lokaci guda alamar ba ta yi sabo da karya ba.

"To shi ke nan, gidan da kika zo za ki nuna min."

"Ai gidan malamai ne ba a zuwa, don Allah Yayana ka juya kar a gan Ni da kai."

The way she talks politely made him stop, sai ya ja ya tsaya yana mai bin ta da kallo, sai da ta ɓace masa tukun ya koma wurin da yayi packing motarsa ya ja ta cike da farin ciki.

A lokacin da ta koma gida Mami ta shiga ta gaisar, ba ta bi ta kan Dada ba kasancewar Dadan da kanta ta mata shamaki da hakan a faɗarta ba ta buƙatarta a rayuwarta, ta kuma yi wa kanta iyaka da ita don ba ta jin ita ɗin jininta ce sakamakon RIKITACCIYAR ALAƘAR da ta gifta tsakani.

Wanka tayi bayan ta fito ta ɗauko abincinta, sai da ta ci tukun ta lallaɓa ta kai wa Mami snacks ɗin, tana ba ta ta fito gudun kar Dada ta yi musu dirar mikiya. Babu jimawa Ihsan ta dawo, itama wankan tayi, Dada da kanta ta kawo mata abinci da ruwan leda, don ita ba ta shan ruwan gidan nasu.

Sai da tayi ƙyat tukun ta dubi Dada tace "Wallahi yau sosai na gaji Dada."

"Sannu Shalele, ki dai dage ki yi karatun nan, ki zama tauraruwa a zuri'armu don ke ce za ki zamo ta fari da ta fara yin boko."

Yamutsa fuska Ihsan tayi tace "To Dada, yanzu dai ba wannan ba, kuɗi ake buƙata a makarantar, kuma babu a wurina, Charity da ke taimaka min itama babu kwanan nan."

"To yanzu ya za a yi, har nawa ne kuɗin?"

"Dubu hamsin ne Dada"

Idanuwa waje Dada tace "dubu hamsin Shalele?"

"E Dada, nawa ne dubu hamsin ɗin wai? Ko albashin watan nan a karɓa min."

Fuska Dada ta saki tace "Au, ashe dai akwai albashi a gidan" sai kuma ta marairaice fuska

"Tun da wannan baƙar ashanar ta fara numfashi, daga nan duk wani farin cikinmu ya kau Shalele, wallahi babu ja in aka ce yar nan taki ba ƴar Muhammadu ba ne wallahi zan yadda."

Tura baki Ihsan tayi tana faɗin "Ni ki bar ce mata Yayata, wannan abar kunyar zan nuna matsayin Yayata? Tirrr"

Tana faɗin haka ta miƙe a fusace, Dada kuma ta fice tana faɗin "ko kin ce kina yinta ma Shalele ai ba sa'ar ki ba ce. Mutum kamar annoba?" Daga haka ita ma ta fice suka bar Imaan wacce jikinta ya gama yin sanyi da al'amarin kaka da kuma ƴar'uwarta, ba ta taɓa jin sha'awar dalilin wannan tsana da suke nuna mata ba sai yau, a yau kam ta ji buƙatar hakan domin ta san wane irin laifi ta aikata musu da ta cancanci irin kyata da tsanar da suke nuna mata, tana son sanin komai domin samar da daidaito tsakaninta da su.

Jikinta sanyaye ta miƙe itama ta bar ɗakin zuwa tsakar gida, a gindin bishiya ta zauna tare da lumshe Idanuwanta tana shaƙar iskar. Ba ita ta koma ɗaki ba sai lokacin sallar Magrib, bayan ta yi sallah ta buɗe Alqur'aninta tana karantawa a haka har lokacin ya Isha ya ƙarato, tana idar da ishar kuma ta kwanta tun da yau dai ba girkin dare aka yi a gidan ba, sai dai ga mamakinta baccin ya ƙi zuwa, har Ihsan ta yi nata baccin Imaan na kwance tana saƙawa da kwancewa kan zaren ƙullin RIKITACCIYAR ALAƘAR da ke tsakaninta da Dada da kuma Ihsan, a haka dai bacci ɓarawo ya sace ta.

_Let me get more reactions please, my group members ah beg lemme get more comments!, please fill my heart with ocean of happiness 😊, lemme feel that yes you're enjoying RIKITACCIYAR ALAƘA, love You loadi-loadi!_

_Diamond Bhatool Reading Club, RIKITACCIYAR ALAƘA FANS CLUB, I'm very grateful for you guys, ina godiya da ƙaunarku gare Ni, Diamond ce!_

Comment & Share this update please