RIKITACCIYAR ALAƘA

5

by @diamondbhatool3

Wani irin zafi ne ya ziyarci Imaan kasancewar ya zuba a idonta, runtse Idanuwanta tayi ta danne da hijabin jikinta. Dariyar mugunta Ihsan ta saki tare da hankaɗa ta ɓangarenta tana faɗin "Gobe ma ki ƙara kawo min abincin dabbobin nan, in ban da raini Ni?" Ta nuna ƙirjinta da yatsa cike da alfahari.

"Ni? The whole me naci garin kwaki, wallahi sai dai ku can ku ƙarata da ci, kuma bari ki ji ma, aure zan yi na bar muku tsiyarku, saurayin da yake sonki shi zan aura. Banza kawai."

Ta ja tsaki ta koma ta kaɗo duka garin da ya zube a sashenta zuwa na Imaan wacce ke zube akan shimfiɗarta Idanuwanta rufe. Abubuwa biyu ne suka taru mata, ba wai iya zafin yajin da idonta ke yi ba ne kaɗai, wulaƙanci da maganganun banzan da Ihsan ta mata ne.

Ta share kusan awa biyu a kwance ashe bacci ma ya kwashe ta, fitsarin da taji shi ya tayar da ita daga baccin har lokacin kuwa idanunta suna mata zafi, har za ta fice sai kuma karo na farko taji wani kwarin guiwa a tare da ita hakan yasa ta tsaya kan Ihsan da ke chat da wayarta. Cikin sassanyar muryarta tace "Ki daina alfahari Ihsan, don ba ki san me gobe za ta kawo ba." Galala Ihsan take kallonta don mamakin ganin yadda ta wani dake tana faɗa mata magana kamar ba yayarta Imaan da ta gama sakar mata ba. Ba ta gama tantance abun da ke faruwa ba sai da taji Imaan ɗin ta ci gaba da maganar ta.

"Dogon buri ba na ƴa mace ba ne, don ba ta san ina aure zai cilla ta ba."

Tana gama faɗar haka ta wuce waje, Hajiya Ihsan sai da Imaan ta fice tukunna ƙwaƙwalwarta ta gama fahimtar abun da Imaan ɗin ta faɗa. Hannayenta biyu ta sa ta tallafi kanta saboda tsantsar ɓacin rai, wani irin zazzafan huci ta sake tana mai jijjiga kanta har lokacin hannayenta na tallafe da kan.

"That's impossible!" Ta faɗa da ƙarfi daidai lokacin da Imaan ta shigo ɗakin, ai kuwa a fusace ta miƙe ta nufe ta kamar hasalalliyar damisa.

"Har ke waye da za ki faɗa min magana?"

Ihsan ta faɗa tana riƙe wuyan rigar Imaan wacce take bin ta da kallo.

"Magana nake miki fa! Ke wace ce da za ki faɗa min magana e?"

Ta ƙara maimaitawa cikin karaji.

Kai kawai Imaan ta jijjiga tana mai yi wa ƴar uwar tata fatan shiriya a zahiri kuma ta sa hannunta tana ƙoƙarin ɓanɓare hannun Ihsan da ke cakwame da wuyan rigarta.

Ƙara ƙanƙame rigar Ihsan tayi don zuwa yanzu zuciyarta ta kai ƙarshe wurin ɓaci, ji take a lokacin mai raba ta da Imaan sai Allah. Ganin dare ne kuma Imaan ɗin ba ta buƙatar tayar wa iyayensu hankula yasa tace "Look Ihsan, I'm sorry, dare ya yi ki bar Ni na kwanta."

Wani kallon raini Ihsan ta jefe ta da shi kasancewar akwai yalwatuwar haske a ɗakin ya ba wa Imaan damar ganin hakan, cikin ranta tace "Ba za ta taɓa canzawa ba."

"Da ke nake Miss Ihsan, matar future president."

Duk yadda ran Ihsan ya ɓaci yake kalaman Imaan suka sanyaya ruhinta, a hankali ta saki wuyan Imaan ɗin tana faɗin "Ko da zuciya ɗaya kika faɗa ko akasin hakan, ina fatan hakan ta kasance."

Imaan ta yi murmushi ta ba ta amsa da faɗin "Da zuciya ɗaya na faɗa, fatan fatanki ya zama gaske." Tana kai aya ta wuce sashenta.

A ɓangaren Ihsan sosai maganar Imaan ɗin ta mata daɗi, tsabar ruɗi irin na shaiɗan Kuma zuciyarta ta fara hasaso mata rayuwa a gidan shugaban ƙasa, hohoho, wani kaso na tsana da ta tashi da ita game da ƴar'uwar tata take da disashe, har tana jinta a yanzu a matsayin ƴar'uwarta. "Ko dai saboda ta so abun da na so ne a wannan karon?" Ta tambayi kanta da sauri. Take wani ɓangare na ziciyarta ya ba ta amsa da "Yea! Dalilin haka ne, dama tsanar da kike mata ai ba haka kawai ba ne, it's because she's always against you."

"And now she's with me!" Ta furta a saman laɓɓanta tana murmushi.

Wurin shimfiɗarta ta wuce tana ji a zuciyarta kamar an mata wata gagarumar kyauta.

*KUƊA ESTATE*

Ummah ce zaune a katafaren parlournta cikin shiga ta alfarma, zaune take tana zancen zuci, shigowar kyakkyawan Dattijo ciki yasa ta miƙe ta nufe shi fuska sake.

"Barka da dawowa Aba Jalaal!"

Shima a sake yace "Barka da gida Rabbatul-bait. Ba ki kwanta ba ke nan?"

"Ina na isa na kwanta bayan wani sashe na zuciyata ba ya kusa?"

Murmushi yayi yace "Lallai kam, soyayyarki ba ta tsufa Rabbatul-bait, kina sanya Zuciyata jinki kusa da Ni."

Itama murmusawa tayi tace "Ina matuƙar godiya Maigidana, yanzu dai ka samu ka watsa ruwa ko ka ji daɗi, da alama yau ma dai aiki kayi sosai, ya kamata ka fara hutawa zuwa yanzu Maigida, ka haifa fa, kuma shekarunka a yanzu sun kai ka samarwa kanka hutu, ka kuma samar mana da mu iyalinka lokaci na musamman da a baya ba mu samu ba."

Numfashi ga sauƙe tare da faɗin "In sha Allah Rabbatul-bait. Bari na samu na watsa ruwa na fito" sakinsa tayi ya wuce, ganin ya shiga ciki yasa ta rufe Idanuwanta kana ta buɗe su. Ƙasa-ƙasa ta furta "Ba zai taɓa canzawa ba, ba zan taɓa samun irin gurbin da Chubaɗo ta samu a zuciyarsa ba. Huh" ta furzar da iska tana ƙoƙarin ganin ta daidaita kanta.

Can babu jimawa Abie ya fito cikin wata jallabiya sai ƙamshi yake zubawa abunsa, ƙamshin da ta jiyo nasa yasa ta yamutsa fuska tana faɗin "Babu abun da Jalaal ya baro daga mahaifinsa, hatta rashin son hayaniyar!" Sai kuma ta miƙe ta tarbe shi, dining suka nufa tana ta masa surutu, sai dai ko A bai ce mata ba, hasali ma da ya zauna lumshe Idanuwansa yayi yana jiran tayi serving ɗinsa. Bayan sun ci tare suka dawo parlourn, ƙoƙari take na ganin ya ba ta lokacinsa sun yi wata muhimmiyar magana amma ya ƙi, sai ma remote da ya ɗauka ya mayar NTA don saurarar labarai, hakan ne ya hasala ta ma ta miƙe ta nufi ɗaki don ta saddaƙar ba za ta samu lokacin mai gidan nata ba.

Alhaji Abubakar Kuɗa ke nan! Dattijo kyakkyawa mai Kuma ji da kuɗi, sam ba ya son hayaniya ko wani disturbances a rayuwarsa, hatta ƙarar da kwano ke yi takan saka shi wani yanayi, sai dai duk da haka yana ƙoƙarin ganin ya sake da kowa, ba shi da girman kai ko kaɗan ba kuma ya ƙyamar waɗanda ke ƙasansa, yana ba wa kowa damar fadar ra'ayinsa kowanne lokaci sai dai kwarjini da haiba irin tasa ta hana mutum sakewa yayi magana da shi.

Alhaji Abubakar Kuɗa, wanda ake kira da Abie, ɗa ne na farko ga Alhaji Abdulmalik Kuɗa (Alhaji Kuɗa) da kuma Hajja Fatu, Abie ya kasance ɗa mafi soyuwa ga iyayensa kasancewarsa na daban a cikinsu, lokuta da dama idan yana tare da mahaifiyarsa Hajja tana yawan faɗin cewa "Babu abun da ya bari daga mahaifinsa, abu kaza, kamar mahaifinsa!"

Kamar sauran ƴan'uwansa, shi ma zaune yake da iyalinsa a cikin family estate ɗinsu. Yana da mata biyu, Ummah ita ce uwargida, auren soyayya suka yi da Abie duk da cewa ita ta fara nuna ra'ayinta akansa. Ummah mace ce mai son zuciya da kuma sanin makamar zama da mutane, zai yi wahala ko abun ɓacin rai ka mata ka fahimci wani sauyi a fuskarta, ta san makamar siyasar rayuwa shi yasa tun da Abie ya aure ta ba a taba samun wata matsala da ita ba a cikin danginsu duk da cewa haula ce sosai gare su, ba ma wannan ba, babu wani mahaluki da zai iya ja da maganarta a cikin dangin, hatta Hajja, banda Abie da wasu lokutan yakan tsawatar mata idan tayi ba daidai ba, Shekararsu goma da aure sai dai ko ɓatan wata Ummah ba ta taɓa yi ba, babu wanda ya taɓa magana tsawon wannan lokaci sai da ita da kanta ta magantu, da farko ta tuntuɓi Abie da batun ya ƙara aure shi kuma ya tubure kasancewar ba ta rage shi da komai ba, ganin hakan yasa ta tunkari Hajja da maganar, ai kuwa Hajja ta amince da batun da Ummah ta zo mata da shi, nan ta yi wa ɗan nata magana, da farko ƙi yayi sai da Baba Babba ya sa baki, amma ya buƙaci su ba shi lokaci don neman matar.

Ummah ce tace masa a'a, ita ta riga ta masa mata wacce take fata da kuma tabbaci a lokaci guda cewa zai so ta, babu yadda ya iya ta gabatar masa da ɗiyar mai aikinta Chubaɗo, kyakkyawar bafulatana wacce mahaifiyarta ke hidimtawa Ummah, ba a samu matsala da shi ba a wanna lokacin a cewarsa duk abun da Ummah ta zo da shi zai yi na'am da shi don ya san bayan Hajja da Baba Babba babu wani mahaluki da ke masa irin son da take masa. Ta ɓangaren su Hajja ma ba a samu matsala ba musamman da uwar yarinyar wacce ke ciwon ajali ta amince da hakan.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka sanya ranar aure, bayan aure kuwa da kwanaki mahaifiyar Chubaɗo ta rasu. A dai zamantakewarta ta zaman gidan miji sai dai tace alhamdulillah domin Ummah na ƙoƙarin ganin ta sake da gidan, takan ja ta a ciki, tana ƙara wayar mata da kai, wannan dalili yasa Chubaɗo (Ummie) sakewa da Ummah cikin ranta kuma tana jin ƙaunarta ɗari bisa ɗari saboda halaccin da tayi gare ta na haɗa ta da miji na gari, fatan Ummie ɗaya shi ne, Ubangiji ya yassare mata wata dama a rayuwa da za ta rama wannan halaccin da Ummah ta mata.

Ana cikin haka kwatsam ciki ya bayyana a jikin Chubaɗo, kar ku so ku gurna wurin kowa musamman su Hajja, Baba Babba, uwa uba kuma Abie da sai lokacin yasan cewa ashe ɗa ma cikon rayuwa ne, Hajiya Ummah ma sosai tayi farin ciki ganin burinta na rayuwa na gab da cika, haka ta danne kishinta ta fara ba wa Ummie kulawa ta musamman kamar ba kishiyarta ba, ɓangaren Abie shi ma yana kwatantawa don kuwa ba kaɗan ba a yanzu yake kaunar Chubaɗo, wannan dalilin ne ma yasa yake jin son abun da ke cikinta.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya har cikin Ummie ya kai watannin haihuwa, ranar wata Litinin kuwa naƙuda ta tashi, suka wuce asibiti, a nan ta haifi ɗa namiji, tun a asibitin take ganin ƙaunar yaron cikin ƴanuwa da abokan arziƙi don kuwa wannan na tafiya wannan zai zo, kowa sai faɗin ma sha Allah yake kasancewar yaron kyakkyawa mai kama da mahaifinsa sak, banbancinsu ɗaya shi ne kalar fata, don jaririn bai ɗauko duhun fatar mahifinsa ba sai ya ɗauko hasken uwarsa.

Ganin yadda Ummah ke nan da nan da yaron kamar ta haɗiye shi yasa Chubaɗo fara wani tunani cikin ranta, bayan sun koma gida Ummah ta ci gaba da kulawa da ita, ranar suna yaron yaci sunan mahaifin Ummah, Abduljalaal bisa roƙon da Chubaɗo tayi akan hakan. Ummah ta ji daɗi ƙwarai da hakan ta kuma tabbatar da cewa Chubaɗo ƴar halak ne. Haka ta ci gaba da shayar da yaron yayin da Ummah ke kula da komai nasa, Ummie kuwa ta nuna kara don ko sau ɗaya ba ta taɓa cewa a ba ta Jalaal ba idan yana hannun Ummah, a lokacin da Jalaal ya kai shekaru biyu cur a duniya, Ummie ta yaye shi tare da damƙa shi halak malak a hannun Ummah, a cewar ta wannan ita ce kaɗai abun da za ta iya yi wa Ummah don rama halaccinta gare ta. Wannan jihadi da ummie ta yi sosai ya ƙara mata ƙima da martaba wurin mijinta da kuma sirikanta, haka kuma wurin kishiyarta da ta maye mata wasu gurabe na rayuwa da ta rasa. Daga nan Jalaal ya dawo hannun Ummah, kulawa sosai take ba shi, tana kuma ƙoƙartawa wurin ganin ya san Mahaifiyarsa, a lokacin da ya fara magana kuma, da sunan mahaifiyarsa ya fara, ya kira ta da "Ummie"

Tun daga Jalaal kuma, Ummie ma ba ta ƙara haihuwa ba, kai ko ɓari ba ta ƙara yi ba.

Duk irin yadda take kawaici da ganin ta ɓoye ƙaunarta gare shi sai da ta zubar da ƙwalla. Tun daga wannan rana kuma shi da kansa yakan ɗebo ƙafa ya zo wurin Ummien nasa, sai dai ba ta sake masa ba don komai ba sai don ganin kada zuciya ta ɗebe ta ta karya alƙawarin da tayi tun ba a je ko'ina ba. Bayan wani lokaci ma sai ya janye jikinsa daga na Ummien, sai dai kuma time to time Ummah na kora shi yaje ya gaida Ummien.

Wannan a takaice ita ce rayuwar gidan Alhaji Abubakar Kuɗa.

Bayan Ummah ta wuce ɗakinta wayarta ta ɗauko ta kira ƴar'uwarta. Bayan ta ɗaga suka gaisa, cikin Muryar da ke nuna tsantsar damuwa Ummah tace "Yaya Zinatu ban san ya zan yi ba kuma, duk iya ƙoƙarina na ganin na yi magana da Aba Jalaal ya ƙi ba Ni dama kamar ya san me zan ce."

Ba a jin me ake faɗi a ɗaya ɓangaren, can kuma Ummah tace "To yanzu Ni ya zan yi? Ko kaɗan ba na son ƙudirirrikana su fara karyewa bayan na kusan cimma su."

"To, shi ke nan, e, gobe zai sauko garin, to zan ƙoƙarta."

Katse kiran Ummah tayi tana sakin wani zazzafan huci.

"Har zuwa yaushe ne ƙudirina zai cika Ni Asiya? Na gaji, na ƙosa komai ya kammala."

"Wane ƙudiri ne naki haka kike so ya kammala Rabbatul-bait?" Muryar Abie ta doki kunnen Ummah a ba zata.

Kanta ta jijjiga tana fatan dai Allah yasa bai ji wayar da tayi ba.

"Kin yi shiru?"

Murmushi ta ɗaura akan fuskarta tare da yafa abun da take lulluɓi da shi a duk lokacin da irin wannan al'amari ya tunkarota.

"A'a Aba Jalaal! Ba komai ba ne, kawai dai ina da ƙudirin ganin yaron nan Jalaal shima ya ajiye zuri'a, shekaru talatin da ɗauri a ce ko zancen mace ba ya yi?"

Ta ƙarashe cikin murya mai nuna tsantsar damuwa.

Janyota jikinsa yayi, cike da kulawa yace "Haba Ummah Jalaal" (kamar yadda shima yake kiranta wasu lokutan musamman kan al'amuran Jalaal ɗin.

"Ki kwantar da hankalinki, mu kanmu hakan yana damunmu, to amma shi aure lokaci ne in kin duba, ko Nima nan in kin duba lokacin da na aure ki na doshi arba'in. Don haka mu zuba ido mu ci gaba da addu'a har Allah ya kawo ta gari."

Sam ko kaɗan Ummah ba ta so jin hakan daga Abie ba, amma sai ta danne abun da take ji tace "Shi ke nan Aba Jalaal, amma dai mata na gari kan ai sun zo, sai dai fatan sun dawo."

Shiru Abie yayi a wannan lokacin ba tare da ya tankawa Ummah ba, ganin hakan yasa tace "Yanzu ga ƴar Yaya Zinatu nan Karimah, yarinyar nan kamar ta mutu a kan Jalaal, na nuna masa hakan amma yace shi ba ya son ta."

"To sai a bar shi, in ya fara son ta zai yi magana ai" Abie ya ba ta amsa a gajarce, shiru tayi da bakinta a wannan karon sanin cewa hannunka mai sanda ya mata, in ta ci gaba da maganar babu shakka zai iya cewa ma ya haramta masa auren Karimah, wanda hakan kuma tamkar tsonka igiyar da mutum ke bi ne a tsakiyar Teku, wannan igiyar kuwa ita ce burinta, idan har bai cika ba ke nan ta ɓata rabin rayuwarta ne a banza, a bauta, da kuma sarawa doki ciyawa, sam! Hakan ba zai yiwu ba.

*Bloordale village, Toronto.*

A yayin da ƙarfen agogon Najeriya ƙarami ya sauƙa akan lamba ta takwas (8:00pm), a birnin Toronto da ke ƙasar Canada, ƙarfe uku ne na rana (3pm).

Zaune AK Kuɗa yake a ofishinsa yana wasu muhimman ayyuka kasancewar katafaren kamfanin EL-MUBEEN jeweleries sun buƙaci haɗa hannun jari da su, wannan tabbas ƙarin nasara ne ga MLS, shi yasa ya maida hankalinsa ga aikin. Ƙarar da wayarsa tayi yasa ya dakata da sannan desktop computer da ke gabansa sannan ya kai kyakkyawan hannunsa da kallo ɗaya mai karatu zai masa yasan cewa hutu ya zauna. Wayar ya ɗaga ganin Uncle N, ƙanin mahaifinsa da yake matuƙar nuna masa soyayya, sallama yayi cikin muryarsa mai daɗin saurara sannan ya gaida Uncle N ɗin, amsawa yayi a nasa ɓangaren yana faɗin "Lallai son, wato yanzu dai ƙarfi da yaji so kake ka manta da Ni Ko?" Ya faɗa cikin sigar zolaya kasancewar dama akwai shaƙuwa ta musamman tsakaninsu, sau tari idan suna hira sai kayi tunanin sa'annin juna ne don shi Uncle N, mutum ne na mutane, wayewarsa yasa yake mu'amala da kowa a waye, yana matuƙar ji da ƙaunar AK, hakan yasa mutane da yawa a familyn sukan ce yana nuna wariya akan AK ɗin.

"Wane yaro ya manta da ubansa share kukansa?" AK ya ba shi amsa yana sakin fuskarsa kamar yana gabansa, take wani irin sihirtaccen kyau ya bayyana a tattare da AK ɗin, lumshe Idanuwansa yayi jin yadda Uncle N ɗin yake dariya

"Lallai wannan yaro ba dai wayo ba, wato dai ƙarfi da yaji wayo za ka yi babanka ko?"

Shima dariyar yayi mai ɗan sauti kana yace "Kaina ƙasa Babana, yaya gidan ya iyali?"

Uncle N ya amsa masa da "Lafiya ƙalau sai godiya, kai kam har yanzu ka ƙi ka ajiye iyalin ma."

Shiru AK yayi jin batun da Uncle N yazo masa, ganin shirun ya yi yawa yasa Uncle N murmusawa yace "Shirun dai shiru ko Son?"

Bai jira amsarsa ba ya ci gaba "Har yanzu ka gagara ajiye iyali bayan zuwa yanzu ya kamata a ce ka ajiye ɗin? Jalaal miye kake jira haka ne? Shekaru sun fara ja, daga kai har Jahaan babu wanda yayi wani yunƙuri and I don't know why sai dai ina kyautata zaton shi Jahaan ya yi shiru ne saboda kai."

"Jalaal" Uncle N ya kira sunansa a tausashe.

"Na'am Uncle"

"Kana ji na kuwa?"

Ƙasaƙasa yace "E Uncle."

"Ba ka ce komai ba kuma"

Ajiyar zuciya ya sauƙe yace "Uncle ban san me zan ce ba."

"Ya kamata kuwa ka san me za ka ce, daga kai har Jahaan ku yi wa kanku ƙiyamullaili ku yi tunani mai kyau, babu abun da kuka rasa bare a ce rashi ne, idan kyau ne Jalaal, duka family babu ya ku, idan kuɗi ne, shima kuna da shi, idan nasaba ce ma, Alhamdulillah, babu wata mace da za ta ce kuna da makusa, ina tunanin kawai shiryawa ne ba ku yi ba, amma ku sani shi lokaci ba ya jira ai."

Cikin sanyin jiki AK yace "Uncle in sha Allah za mu yi motsi."

Ƴar dariya Uncle yayi yace "Kar ma ku yi Jalaal, ban so ko Sabreen da Nimra zan ba ku ba."

Dariyar jin kunya AK yayi ya sosa kansa kamar yana gaban Uncle N ɗin. Shi kam Uncle dariya yayi yace "Dama shirun ne amsar taka ai na sani, in kuka yi kwantai dai babu ruwana, wallahi sadakarku zan bayar ga Nimra da Nihal." Ya ƙarasa cikin sigar tsokana.

Shima AK ɗin ƴar dariya yayi yace "Haba Uncle, ai ba sai an kai ga haka ba, ƴan yaran nan wa zai aure su yanzu?"

"Ku mana Jalaal" ya ba shi amsa kai tsaye "Ku ɗin dai, ba dai kuna ƙin ƴanmatan da ke son ku ba?"

A shagwaɓe wanna lokacin yace "Ba haka ba ne Uncle, matan ne duka babu na gari, babu masu son mutum tsakani da Allah, wollah Uncle duk mace da ta raɓe mu ba don Allah take son mu ba, abun hannun mu kawai suke hange, amma a kara mana haƙuri, in sha Allah wanan zuwan da za mu yi za mu ba ku mamaki."

Ba don Uncle N ya yadda ba yace "To a yi dai mu gani."

AK ya ba shi amsa da "In sha Allah za ku gani kuwa"

"Allah ya sa"

Cikin ransa ya amsa da "Amin" yana lumshe idanuwansa.

"Uhm, kaga gida ma zan shiga Ni kam."

"My regards to Aunty Dr (Uncle's wife) and Nihah, a'a, i mean baby Ayman"

Dariya Uncle N yayi yace "Hmm, shi ke nan za su ji, sai goben ko?" AK yace

"In sha Allah." Daga haka suka katse kiran.

Lumshe Idanuwansa yayi yana ƙara tariyo hirarsu da Uncle N, jinjina kai yayi yana shafa sumarsa da tayi luf-luf take sheƙi. Ajiye wayar yayi ya shafo sajensa, a hankali ya furta "Allah ka mana zaɓi mafi Alkhairi a rayuwa, ka haɗa mu da masu ƙaunarmu tsakani da Allah ba don wani abu da muke da shi ba."

Amsa addu'arsa yayi da kansa yana faɗin "Amin Ya Rabbi" sai kuma ya ci gaba da aikin da yake yi, so yake daga yanzu zuwa dare ya samu ya kammala komai, tunda Umar na nan sai ya bar komai a wurinsa, ya san zai yi abun da ya kamata, Fatansa a yanzu bai wuce ya buɗe idanuwansa ya ganshi a ƙasarsa ta haihuwa kamar yadda a can ma ake mararin a ganshi ɗin, dama already Jahaan yayi musu booking flights su ukun zuwa Jos.

Tabbas wannan tafiyar da zai yi ta kasance ta daban domin jikinsa da kuma zuciyarsa kansu sun fahimci hakan, a wannan hutu da zai yi, yana fatan samun abokiyar rayuwar da za ta dace da shi, zai bi duk wata hanya don ganin cewa ya haɗu da mai son shi tsakani da Allah, and he hopefully pray Allah ya ba shi ita. "Tabbas zan samu" ya ba wa zuciyarsa amsa cike da ƙarfin guiwa.

React, share and comment fisabilillah.

*Jazakumullah Khairan for those that share, Diamond Bhatool 🦋 really appreciate your efforts, Allah ya bar ƙauna.*