8
Asubar fari AK ya farka bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, ƙara lumshe Idanuwansa yayi kamar mai shirin komawa baccin yana ƙoƙarin tuna fuskar da ya gani a cikin mafarkinsa na yau, fuskar mace! Abun da bai taɓa mafarki da shi ba bayan Ummiensa. Me ke shirin faruwa da shi? Je asked himself "dreaming of a lady? Who's she and what's her intention towards me?" Ya furta cikin muryarsa da take dishe sakamakon baccin da yayi. Jin alamun shiga salla yasa ya mike da sauri ya diro daga kan bed ɗin nasa tare da nufar bayi, a gurguje ya watsa ruwa ya ɗauro alwala sannan ya fito ya sanya jallabiya ya ɗan fesa turare. Lokacin da ya isa ya tarar har an yi raka'a ɗaya, bayan an idar ya rama wacce ta kuɓuce masa sannan yayi azkar ɗinsa a cikin masallacin sai da ya gama ya fito, ganin shi kadai ne ya rage yasa ya wuce part ɗinsu kai tsaye, ko da ya koma bedroom nasa ya so ya koma bacci but baccin ya ƙi zuwa masa, gaba ɗaya yarinyar da yayi mafarki yau da ita ya gagara manta fuskarta, da ya rufe idanuwansa sai ya ga fuskarta cikin damuwa.
Ganin ya kasa cire ta cikin ransa yasa yayi tsaki ya miƙe ya ɗauko Alqur'ani ya fara karantawa, few minutes after ya fara jin bacci, hakan yasa ya ajiye Qur'anin akan bedside drawer, nan wani daddaɗan bacci ya kwashe shi shi ne har wuraren 10 bai fito ba, Ummah takan kewayo ta duba shi ganin bacci yake yasa take fitowa ba tare da tashinsa ba.
Wuraren 10:34am Jahaan ya shigo part ɗin nasu ganin shiru Jalaal ɗin bai fito ba tun da ya san cewa suna da appointment da Papa, not only papa, Daddy Abbie duka ba su haɗu ba bare su gaisa jiya.
Da Ummah ya ci karo a parlour, ya risina ya gaishe ta, ta amsa masa a daƙile, bai damu da hakan ba saboda ya saba da hakan, abu ɗaya shi ne bai san dalilin da yasa Ummah ke masa hakan ba, idan tare da Jalaal suka shigo za ta karɓe su hannu biyu tayi ta tarairayarsu har da wasa da dariya amma in shi ɗaya ya shigo to fa da ƙyar yake samu ta amsa gaisuwarsa ma, tun suna yara ya lura da hakan sai dai kasancewarsa mutum dai bai iya saka damuwar kowa a ransa ba yasa bai taɓa ko da baiyanawa wani ba, amma kuma tabbas akwai abun da yake hasashe tattare da hakan.
Kai tsaye ɗakin AK ya nufa, ya murɗa handle ɗin tare da shigewa ciki yana sallama, yadda ya tarar da shi hankali kwance yana bacci ga wani cool smile kan fuskarsa yasa ya zaro idamuwbsa with full excitement ya ƙarasa bakin gadon. Mutumin da in har aka taɓa handle ɗin ƙofa duk baccin da yake yake farkawa abun mamaki yau ga shi har sallama an yi amma shiru. Fatan Jahaan ɗaya, Allah ya sa hasashensa ya zamo gaskiya. A bakin gadon ya zauna tare da ɗago hannun AK ya saka hannunsa, sai kuma yayi amfani da ɗaya hannun nasa wuri tapping bayan AK ɗin yana faɗin "Wake up dude! Wake up!"
Kamar wanda aka zabura AK ya ce "Don't worry, I'm with you"
Mamaki ƙarara ne ya bayyana kan fuskar Jahaan ɗin jin abun da AK ya faɗa,take ƙwaƙwalwarsa ta hasaso masa abun da yake fata, ganin eyes ɗinsa a rufe yasa JK ƙara tapping bayansa yace "Oh yea, wake up dude! Papa na jiranmu fa." Wannan karon a zabure AK ya tashi ya zauna yana murza eyes ɗinsa.
Instead of seeing his dream girl sai yaga JK, wani dogon tsaki ya sake yana bin JK da mugun kallo wanda sosai ya ba shi dariya, kasa riƙe dariyar yayi ai kuwa ya fashe da ita har yana riƙe cikinsa. Ƙuluwa sosai AK yayi don haushin JK ɗin yake ji haka kawai, not only because ya katse masa mafarkinsa, but yadda yake wani masa dariya. Sai da JK yayi dariyarsa har ta ishe shi tukun ya dubi AK yace "tell me who's she, Who's that luckiest girl da tayi taking mind ɗin Mr. Perfect ɗinmu?"
Wannan karon iya ƙuluwa AK ya yi, hakan yasa ya ja tsaki tare da direwa daga kan bed ɗin ya shige toilet, dariya JK yayi yace "Za ka fito ka same Ni ne, amma na riga na gano ka kuma sai ka faɗa min who's she, yauwah."
Ko da AK ya shiga bayin maimakon yayi abun da ya kai shi sai ya samu wuri ya tsaya ya naɗe hannayhensa a ƙirji tare da lumshe Idanuwansa don son tariyo mafarkin yarinyar da ya ƙara yi da safe kuma, bai ga komai ba sai duhu, hakan ya sa ya ƙara jan wani tsaki yana faɗin "Why should I even mind about her?"
"Ki fita daga heart ɗina please,I'm not man of women ok?" Duk maganar da yake yi cikin zuciyarsa yake, haka kawai kuma bayan ya yi zancen zucin sai yake ganin kamar bai kyauta ba, da sauri zuciyarsa tace masa "Duk Jahaan ne ya jawo maka, You should have now asked her who's she amma ya katse maka baccinka." Tsaki ya ja tare da nufar heater, ya danna switch, sannan ya tara ruwa mai ɗan zafi cikin Jacuzzi. Bayan shafe lokaci can ya fito sanye da milk bathroom yana goge sumarsa da wani ƙaramin towel fari.
Kansa ya kawar gefe ganin har lokacin Jahaan na nan, dariya Jahaan ya kwashe da ita, take ransa ya ɓaci sai dai yayi controlling temper ɗin nasa ne ta hayan nufar mirror, mazauni yayi wa kansa da mirror stool ɗin tare da ci gaba da goge sunar tasa.
"Ko ma dai me za ka yi today you must tell me who's she" Jahaan ya faɗa sounding so naughty.
Bai kalle shi ba AK kam ya miƙe ya janyo trolley ɗin da ya zo da ita, kaya ne kala biyu a ciki sai gayyar turaruks da kuma mayukansa na shafawa. A hankali ya fito da su ɗaya bayan ɗaya ya jera kan dressing mirror ɗin har lokacin JK na nan ya kwanta kan bed.
Bayan ya gama fitar da komai na cikin trolley ɗin ya ɗaga ta tsaye sannan ya dawo gaban mirror, mayukansa ya shafa a Nutse sannan ya saka wata white soft t-shirt mai kyan gaske, bayanta an rubuta The young shall grow sai wani baƙin jeans da ya ɗan ƙama shi. Turarukansa ya fesa haka kawai ya tsinci kansa da kallon mirror, murmushi ya sake tare da shafa lallausar sumar kansa. Bai bi ta kan JK ɗin ba ya nufi hanyar fita, hakan ya sa JK dirowa daga kan gadon babu shiri ya yi tsalle ya cafko shi "Haba dude!"
Kallonsa AK ya tsaya yi ba tare da ya ce komai ba
"Kawai daga faɗan gaskiya?" Sau kuma ya sake shi, bai ko ƙara juyowa ya kalle shi ba ya fice, bayansa Jahaan ɗin ya biyo suka wuce dining. Ɗauke da mutmushi kan fuskarsa ya ƙarasa ganin Ummah na zaune tana karyawa.
"Yau dai kam an huce gajiya son, irin wannan bacci haka?"
Kansa ya kawar gefe tare da faɗin "Wallahi na gaji ne sosai, good morning Ummah"
"Morning my son, ka tashi lafiya?"
A taƙaice yace "Lafiya ƙala"
jajaanbne ya dube ta a mutunce yace "Ina kwana Ummah" Jahaan ɗin ta duba har tana jin kamar ta shaƙe shi sai dai yaya za ta yi? Murmushi ta yafa akan fuskarta tace "Lafiya ƙalau, Ya gidan naku"
"Lafiya lau" shi ma ya ba ta amsar fuskarsa babu yabo ba fallasa cikin ransa yana tunanin irin alternation na Ummah. Zuba musu girkin suka ci, bayan sun gama ta dube su ganin sun nufi hanyar waje tace "Ba dai fita za ku yi ba ko yarona?"
Dalatawa dukkansu suka yi, Jahaan ya sauƙe ajiyar zuciya don dama can jikinsa ya ba shi za a rina, ya rasa why Ummah ba ta don alaƙarsa da ɗan'uwansa, is it because of her selfish interest or something else Allah kaɗai ya san mata, shi dai zai ci gaba da haƙuri don ba ya jin zai wani ba ta damar tasiri cikin ƴan'uwantakarsu.
Amsar da Jalaal ɗin ya ba wa Ummah ne yasa ya Jahaan saurin ficewa don jiransa a waje.
"Yanzu Son ba za a huta ba? To shi ke nan, ka samu ka je ka dawo za mu yi magana ne."
"To Ummah"
"Kar ka daɗe ka ji?"
Ya gyaɗ mata kai sannan ya fice. A waje ya tarar da Jahaan, kai tsaye part ɗin Papa suka nufa Jahaan sai tsokanar AK yake shi kuma ya ƙi tanka masa.
Mammah suka fara gani a parlourn tana kallo, gaishe ta Jalaal yayi a mutunce ita kuma ta amsa masa fuska sake sannan tace "Ai dama na san can ka yi, to ga can breakfast ku je kuyi ko?"
Da sauri Jahaan yace "Mammah ai mun yi a wurin Ummah" fuskarta ta ɗan sauya kaɗan don har ga Allah ba ta wani son yarin nata yake cin abinci a sashen Ummahn. Ganin yadda fuskarta ya sauya yasa yayi saurin faɗin "Mammah don Allah ki ce wa Papa ga mu nan"
Ya yi hakan ne gudun kada AK ya fahimci wani abun. Ɗan murmushi tayi tace "Ai da ya fice abun sa, ya yi ta jiranku har ya gaji ya koma ɗakinsa bari na masa magana."
Tana faɗin haka ta wuce bedroom ɗin Papa babu jimawa sai ga shi ya fito cikin manyan kaya, tun da ya hangi yaran nasa ya saki fuska, da sauri Jalaal ya ƙarasa kusa da shi ya ba shi side hug yana faɗin "Good morning"
"Morning... Ka tashi lafiya"
Jalaal yace "Lafiya lau."
Zama suka yi a parlourn yayin da Jalaal ke zaune akan carpet daidai ƙafar Papa. Sake gaida shi Jahaan yayi ya amsa masa. Daga nan ya tambaye su ya aikin? Suka amsa da "Alhamdulillahil" Papa yace "Ai kun kusa ma Ku dawo Nigeria gaba ɗaya, we're about to relocate to our motherland, hakan zai ƙara ɗaukaka darajar ƙasarmu, masu son kayanmu kuma to, a yi abun da ya dace"
Mutmushi kawai suka yi gaba ɗayansu, Papa ya dube su yace "Ku dai har yanzu shiru, me kuke nufi ne?"
Kallon juna suka yi sannan suka sunkuyar da kayuwansu ƙasa.
"Magana nake fa, Jalaal, Jahaan, kun yi shiru"
Da ƙyar Jalaak yace "Papa a yi haƙuri"
Ju bbbbh cj
"Ai ba zancen a yi haƙuri ba ne Jalaal, ku ba kwa tunanin rayuwa ne? Haka kuke so ku ƙare taku rayuwar babu iyali ne?" Shiru suka yi ba tare da sun ce komai ba "Duk sa'anninku sun yi aure wasu har da yara ma amma kullum aka muku zancen sai ku yi shiru kuna sunkuyar da kai, to yau ku faɗa min meye matsalar, matan ne ba sa son ku ko kuwa dai dama w neman matan auren?"
Kunya ce ta kama Jalaal wanda yaji kamar ƙasa ta tsage ya shige ciki.
"Da ku nake fa kun sunkuyar da kai kamar kuna gaban sirikanku, to wallahi kafin ku tafi hutu ku tabbatar ko wannenku ya gabatar min da wacce yake so, don in za a biye ta Abbie ɗinku a haka za ku zauna, Gara a faɗa muku tun da ku ba ku san me ya dace ba."
"a yi hakuri Papa" suka faɗa cikin haɗin baki.
Papa yace "Na dai faɗa muku, in kuka ɓata min lokaci kuma duk wacce na samo muku Dole ku karɓa."
"In sha Allah za gabatar da matan kafin mu tafi ɗin"
"Kar ma ku gabatar ku ga abun da zan muku." Yana faɗin haka ya miƙe ya gota gefe ya wuce ɗakinsa ya bar su a zaune suna karanta wasiƙar jaki, suna wurin zaune babu wanda ya ce uffan har Papa ya fito, suka bi shi suka fita tare, wurin da motarsa ke fake suka raka shi ya hau sannan suka masa Allah ya kiyaye.
Sai da ya wuce Jahaan ya dubi Jalaal yace "Ka ga irin abun da ka jawo mana ko?"
Harararsa AK yayi yace "Na jawo mana kamar yaya? Kowa ya jawo wa kansa dai"
"Oh haka ma kace?" AK ya ɗage kafaɗa "Shi ke nan, wallahi Ni ka ga dama ina da wacce nake so, tun da ka ce kowa wa kansa ya jawowa wallahi Ni zan gabatar da ita kawai a yi abun da ya kamata, kai kuma in aka nemo maka wacce ba ta dace da kai ba kai ka sani."
"Mtss" AK ya ja tsaki "To sai me? An faɗa maka Ni ina da matsala ne? My dream girl is coming"
Jahaan ya zaro ido waje yace "Ba shakka, shi yasa yanzu kake dogon bacci ke nan, shi ke nan in Papa ya dawo sai na ce masa mu biyu duka mun shirya."
Jawo rigar Jahaan AK yayi yana jin kamar ya kai masa naushi "Ba na son shirmenka fa Jahaan"
"To Papa, yi haƙuri mana" ya ba shi amsa yana wani narke murya kamar yana magana da Papa, lokaci ɗaya kuma yace "Wai kai Jalaal da me kake nufi ne? Ni ne babban amma kai kake ji da girman? To Allah ya shirya."
"Ni zan wuce wurin Abbie, I no get your time"
Kafaɗarsa Jahaan ya buga yana faɗin "Ɗan rainin hankali, sai shegen faɗin rai kamar yafi kowa." AK bai kula shi ba suka nufi part ɗin Ummie, kamar kullum daga gauduwa da jin ya yake ba ta ƙara ce da shi komai ba, sun dai yi barkwancinsu da Jahaan, daga nan ya tambaye ta ko Abbie na nan, ta sanar da su ya wuce office. Hakan yasa suka mata sallama, da Nimrah suka ci karo wacce ta ci uwar kwalliya kamar mai fita biki. Murmushi tayi ta dubi Jahaan ta gaida shi sannan ta dubi AK tana wani narke murya tace "Ya Jalaal good morning."
A taƙaice yace "Morning " daga haka suka raba ta suka wuce. Haushi ne ya kama ta, but babu yadda zata yi tun da ita ke neme, kuma dama an ce mai nema shi ke samu, hakan yasa ta bi bayansu. Ganin sun nufi part ɗin Ummah yasa ta ɗan ja tsaki, ita fa wannan Ummahr wallahi ji take kamar ta shaƙe ta, in banda mugunta taba ganin yadda su ukun suke son auren AK ɗin amma ko kaɗan ba ta taɓa ƙoƙarin nuna masa hakan ba bayan kuma ta san ba zai ketare umarninta ba.
Babu jimawa sai ga su sun fito bayan Dramar da suka buga da Ummahta, parking lot suka nufa kai tsaye, da sauri Nimrah ta ƙarasa ta ɗan tsaya ta side ɗin da AK yake ta yi knocking glass, zugewa yayi yana bin ta da kallo, take ta diririce tace "Uhm Yaya Allah ya tsare hanya"
"Amin" kawai yace can ƙasan maƙoshi sannan ya mayar da glass ɗin hakan yasa ta sauƙe numfashi, tana gani suka fice har ta daina hango su. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin "Ya Allah ka ba Ni Yaya Jalaal, I alone Ya Rabb" sai kuma ta dafe saitin zuciyarta. A duniya babu wani ɗa namiji da take so irin ya Jalaal, tun suna yara lokacin ba su san kansu ba suke faɗa a kansa, fatanta dai Allah ya sa ta cinye wannan wasa tare da mallakarsa matsayin mijin aurenta.
Juyawa tayi don ta koma part ɗin su taci karo da Manal wacce itama ta sheƙa kwalliya sai ƙamshi take. Kallon banza suka aikawa juna, Nimrah ta wuce sashensu ta bar Manal ɗin da ta nufi part ɗin Ummah. Tana zuwa sashensu Nenne ta tare ta da faɗin "Kin samu kun yi magana dai ko?"
Bakinta ta tura tace "Kema Nenne kin sani ai, kin san halinsa, wallahi Ni tsoro ma yake ba Ni"
"Tsoro ko?" Nenne ta tambaye ta tana tsare ta da ido "A lokacin da kika rasa shi kika jin an ɗaura aurensa da Manal ko Safnah, lokacin za ki yi bayanin tsoronsa kike ji."
Wani ɗan Siririn hawaye ne ya zubo daga idonta ta share sannan tace "Nenne ke dai ki ci gaba da min addu'a, in Sha Allah Ya Jalaal nawa ne, nawa har abada."
Nenne tace "To Allah yasa, ba dai kin ƙi bin abubuwan da nace ba, ai da tuni an wuce gurin" ɓata fuska Nimra tayi kana tace "Ni dai ba zan yi abun da zai sa na rasa ƙima da mutunci ha, ba kuma zan yi abinda zai kaucewa hanya ba, Yes Nenne, I love ya Jalaal, ba wai don kuɗinsa ba, don Allah nake sonsa, idan har ba za ki min addu'ar na mallakesa ba shi ke nan, idan na mutu kema za ki yi rashi."
Tsaki Nenne tayi tare da faɗin "Ai in dai ba za ki yi abun da nace miki ba kina tare da wahala don masu farautar tasa suma ba haka suka bar shi ba." Takaicin halin mahaifiyar tata ne ga kama ta, hakan ya sa ta wuce ɗakinta ba tare da furta komai ba. Tsaki Nenne ta kara ja ganin yadda Nimra ta banko ƙofa sannan tace "Don ubanki idan ma ke ba ki yi ba Ni zan yi, wallahi dole a ci arziƙi da ke, dole na yi abun da ya kamata, ko don Haj. Asiya da ke wani nuna isa a kansa kamar ita ta haife shi, mtsss, sai na nuna mata cewa nawa salon ya wuce nata."
Hajiya Manal ko da ta shiga part ɗin Ummah a tunaninta Jalaal ɗin yana nan, ba ta samu fuska ba hakan yasa ta fito tana cin magani, karo ta ci da Karimah wacce saurayinta ya sauƙe ta yana ƙoƙarin fitar mata da kayanta daga Boot. Kallon banza ta aikawa Karimah ganin wata irin shiga da ta yi, ba ta san ta ba amma sam shigar ta yi baɗalanci da yawa.
"Yan mata ya dai? Irin wannan kallon kamar ba Mrs. Jalaal Kuɗa to be kike kallo ba?"
"What?" Manal ta tambaya cikin kaɗuwa.
Mutmushi irin na ƴan bariki Karimah ta yi tare da faɗin "Yesso! Yadda naga kin yi reacting prove me right that Kema son sa kike"
Kasa magana Manal tayi sakamakon wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi hakan ya ba Karimah damar faɗin "I guess it right abi? To ki ma cire ranki kan mijina don AK ba shi da wata mata sama da Ni, ban wuri." Tana gama faɗar haka ta banke Manal da takaici ya gama kashe ta sannan ta shige ciki, Nas ya shigo mata da trolleynta.
Da ido Manal ta bi su tana jin haushin kanta na rashin cin mutuncin Karimah ɗin, sai dai rashin sanin takamaimai wace ce yasa ta wuce part ɗin su zuciyarta babu daɗi, jikinta ne yayi sanyi kaɗan ganin sun ƙara yawa, hakan yasa ta ji cewa dole ta yi aiki tuƙuru in ba haka ba tana gani za su ƙwace shi daga gare ta musamman wannan mai zubin karuwan da ba ta ma san wace ce ita ba da har take wani jin kanta fiye da su jininsa. Tana shiga Aunty Salaha da ke kallo ta ce "Ya dai Manal?"
"Babu komai Maamah, kawai dai na je ne ban samu Ya Jalaal ɗin ba sai takaicin da na kwaso "
Mammah ta bi ta da kallon takaici kana tace "Ba dai na ce miki ki haƙura da Jalaal ɗin nan ba Aminatu kin ƙi ji? Kar ki ga tsakaninsa da Yayanki akwai alaƙa mai kyau, wallahi hakan ba zai sa ya karta miki rashin mutunci ba, uwa uba kuma Haj. Asiya da ke nuna tata isar a kansa, dama dai a ce uwar ce ke ƙafafa da shi na san Fulani ba za ta bari soyayyar ɗanta ya kashe jinina ba, she's been my favorite a familyn nan, amma Haj. Asiya hmm"
"Maamah ba ma Ummah ba ce damuwar, kin san me?"
Aunty Salaha ta jijjiga kai ba tare da ta kalli Manal ɗin ba don har ga Allah ita ba son wannan alaƙar ma take ba.
Kamar Manal za ta yi kuka tace "Maamah wata ce ta ci min mutunci wai na ma cire raina, Ya Jalaal nata ne" sai ga hawaye sun fara bin fuskarta. "Haba Manal! Wai akan namiji kike kuka haka? Haba Manal? Kin ga in ma za ki cire shi a ranki kamar yadda ta ce duk da ba san wace ce ba ki cire, ga samari nan a duniya da suka fi Jalaal kyau da dukiya, ko nan Sajid yana son ki kika ce a'a saboda jdanunki sun rufe akan Jalaal ɗin da ba lallai ki aure shi ba, shi fa bai ma san kuna haukarku ba daga ke har Safnahr da kuke faɗa da juna akansa kuma kin dai san ko auren zai yi ɗaya a cikinku zai aura, ga Nimrah ma ga kuma ita wacce kika ce ta miki kashedi. Ina jiye miki tafiyar dare ba mariki, don haka ki nutsu ki cire shi a ranki."
Ajiyar zuciya Manal ta saki tare da faɗin "Amma Maamah Ni ba don kuɗinsa ko kyansa nake sonsa ba you know."
"Sai ki same shi ki faɗa masa cewa kina sonsa daga nan kika idan ko amsa gaisuwarki zai yi" Aunty Salaha ta ba ta amsa a zafafe tana ture ta gefe ganin duk bayanin da ta gama yi mata ba ta gamsu da shi ba. Itama miƙewa tayi ta nufi bedroom ɗinta tana jin kamar ta cire zuciyarta ma gaba ɗaya ta huta, ita dai ta san cewa da so yana yin shawara da ba za ta bari na ta fara son Ya Jalaal ba, ta san ya fi ƙarfinta ta ko"ina to amma jarrabawa ce daga Allah, tana fatan cinta don zuwa yanzu itama so take ta ɗauki shawarar mahaifiyar tata da ke kan layi na gaskiya, idan kuma ta mutu silar ƙoƙarinta na fitar da son sa a zuciyarta ta shi ke nan."
*React and share fisabilillah.*
*Diamond Lady ce!*