RIKITACCIYAR ALAƘA

10

by @diamondbhatool3

A ɓangaren Ummah sai da Yamma ta fito, ta shiga kitchen don faɗawa masu aiki abincin da za a girka ta ci karo da tray ɗin abincin AK, tsintar kanta tayi da buɗe su, ganin ko taɓawa ba a yi ba yasa ta juya zuwa ɗakun Karimah don jin ko ba ta kai masa ba ne.

Karimah wacce ke chat Ummah ta duba tace "Karimah kin kai wa Jalaal abincin kuwa?"

Ta buɗe baki za ta faɗa mata abun da ya faru ta tuno da maganganun Mommynta bakan yasa ta narke fuska tace "Na kai masa Ummah, ya ce duk babu wanda ya masa a ciki, na ce ya faɗi me zan dafa masa ma ya ce na bar shi zai sha cornflakes."

"Shi ne ba za ki zo ki faɗa min ba kuma?"

"Kina bacci lokacin ai Ummah"

"Ke kuma ba ki san me ya kamata ki yi ba? Idan kika girka wani abun ai zai karɓa ya ci amma kika yi burus, kina tunanin hakan zai samar miki soyayyarsa ne?"

Shiru Karimah tayi tana nazaratar maganar Ummah ta kuma fahimci cewa tana kan layi sai dai me? Ita fa ba ta iya girka komai ba apart from Indomie, suna da mai musu abinci, wanke wanke da kuma shara, hatta gyaran ɗaki ita ba ma iyawa tayi ba.

Maganar Ummah ne ta dawo da ita daga duniyar da ta leƙa "Ki kula da kyau, ki yi amfani da dabarunki a matsayinki na mace ki tabbatar kin samu gurbi a zuciyarsa daga yanzu zuwa dare don gobe zai bar garin ma."

Karimah ta ƙwalalo ido tace "Ina zai ce Ummah?"

"Zai koma yadda ya fito mana, don haka ki yi yadda za ki yi na faɗa Miki, idan kin yi Sa'a to, zan ba ki numbersa ko Bayan tafiyarsa kike kiransa ki tabbatar kin samu kusanci da shi kin ji"

"To Ummah, I'll do all that's necessary."

"Da ya fi Miki".

Ɗakin AK ummah ta nufa kai tsaye sai dai ba ta same shi ba, hakan yasa ta fito parlour ta zauna tana jiran shigowarsa. Ganin har Magrib bai dawo ba yasa hankalinta ya ɗan tashi, fatanta dai kar yaje ya ci abinci a sashen mahaifiyarsa don kuwa in hakan ta faru zai iya daina cin abincin sashenta kamar dai mahaifinsa, shima tun da ya fara cin gurkin Ummie ya yi wa nata ƙaura sai yace wai sai dai ta girka masa da kanta ba wai masu aiki ba. Ita kuma Ummah, maganar gaskiya, ko lokacin da tana amarya ba ta girki, da mai aiki tazo tun lokacin da ta san cewa ɗan babban gida za ta aura. Tsaki Ummah ta ja tace "Wawuyar yarinya tana son lalata min plan, amma ba zan taɓa yin sake shekarun da na ɓata a baya ina aiki su ruguje ba, dole, dole ne Jalaal ka kasance ƙarƙashin iko da umarnina." Daga haka ta koma parlour ta zauna zaman jiran dawowarsa.

AK kam A nan part ɗin su Jahaan suka ƙarasa yininsu har dare, a nan ma suka ci abincin dare tukunna JK ya wuce part ɗinsu. Yana shiga Ummah ta tare shi fuskarta na nuna tashin hankali. "My son, where have you being, ina nan ina ta jiranka, Karimah ta ce ba yi Lunch ba, ga shi wayarka ba ta tafiya."

Cikin son kwantar mata da hankali yace "I'm sorry Ummah, wata ƙazamar Maid ce ta kawo and you know ba na son mata irinsu, why kika ɗauki irin wannan ƴan aikin?"

Janyo shi tayi ta zaunar da shi sannan tace "Son mace ƴar aiki?"

Ya gyaɗa mata kai yana wani yamutsa fuska don ko kaɗan ba ya ƙara ganin fuskar wannan ƴar aikin.

Shiru Ummah tayi tana tunani can dai tace may be Karimah ƙarya ta mata ta tura masa ƴar aiki, amma ya ce arniya ai, me hakan yake nufi? Kaf cikin masu aikin sashenta babu wata Christian bare yace wani abu. Ganin babu mai ba ta amsa yasa ta ƙudiri aniyar tambayar Karimah ɗin.

Kallonsa tayi cike da kulawa tace "yanzu dai mu je na ba ka abincin ka ci to"

Fuska ya yamutsa sannan yace "I'm already satisfied, na ci abinci babu jimawa."

"Is ok, ka yi haƙuri ka ji son"

Mutmushi yayi yace "Ki daina ba Ni haƙuri Ummahta, just tell who the so called Karimah is ta kula ko ma ki daina sa ta aiki tun da ba ta yin abun da kika sa ta."

"Shi ke nan my son"

Ɗakinta ta wuce ta bar shi a parlourn, tana shiga ta janyo wsyarta ta makawa Yaya Zinatu kira, bugun fari ta ɗaga bayan sun gaisa tace "Yaya akwai matsala fa"

"Matsalar me kuma Asiya?"

"Yaron nan zai koma Canada gobe Yaya kuma ga shi ba a tsayar da magana ba"

"To yanzu me ye abun yi?"

"Shi ne ma dalilin kiran naki ai"

"To gaskiya Asiya dole wannan karon ki zo nan Kaduna duk lokacin da ya kusa dawowa ko kuma ki zo nan babu jimawa, akwai wani boka da yake min aiki Asiya a birnin Gwari kuma gaskiya aikinsa na mugun ci, za a yi aiki kawai a kansa a yi a wuce wurin ko ba haka ba?"

Ajiyar zuciya Ummah ta sauƙe don ba ta son tonawa kanta asiri, amma bokaye babu irin wanda aminyarta ba ta raka ta ba har na ƙasashen kewaye amma amsa ɗaya suke ba ta na cewar "Ko an yi aiki a kansa ba zai yi tasiri ba, akwai garkuwa ta musamman a jikinsa"

"Kin yi shiru Asiya?"

"Shi ke nan Yaya, hakan kawai za a yi. Ki sa mana lokaci sai mu je"

"To shi ke nan, yanzu ita Karimah ɗin gobe ke nan za ta dawo?"

"Yadda dai ta ce, idan tana son zama a nan ɗin ai shi ke nan"

"To shi ke nan, sai an jima"

Suna katse kiran Ummah ta fito parlour, har lokacin AK na zaune yana kallon sport. Kujera ta samu ta zauna sannan ta kira sunansa. Ɗagowa yayi giving her his total attention.

"Jalaal yaushe ne za ka kawo min sirika ne?"

Tsintar kansa yayi da kumshe fararen idanuwansa trying hard to remember her face, that's his dream girl."

"Ka yi shiru son."

"Ummah ki ɗan ƙara jira kaɗan, in Sha Allah nan ba da jimawa ba ma."

Wani irin bugawa chest ɗin Ummah yayi jin amsar da ba ta yi tsammani ba, hakan yasa ta ƙago murmushi don kar ya gano wani abun tace "Ma sha Allah, amma dai kafin nan ina maka albishir da cewa na maka kyautar mata."

Babu shiri AK ya miƙe tsaye sai dai bai iya cewa komai ba sai kuma ya koma

"Shi ke nan, na fahimta ba ka so, kar ka damu mu bar zancen" ajiyar zuciya kawai ya sauƙe sannan yayi excusing kansa ya wuce ɗakinsa, available flights ya duba sai da babu na gobe sai jibi babu yadda zai yi kawai yayi booking seat biyu shi da Jahaan, bayan ya kammala ya fito parlourn, Abbie ya dawo lokacin hakan ya sa ya zauna suka yi hirarsu nan ya samar da shi cewa jibi za su koma, hakan bai yi wa Abbie daɗi ba saboda bai samu wani lokaci sosai da ɗan nasa ba saboda ayyukan da suka sha kansa amma yayi masa fatan Alkhairi daga nan ya fito ganin dare bai yi ba yaje ya gaida Ummie, a nan yake sanar da ita cewa zai wuce jibi, tace

"Ya kamata ka je Azare, ka gaida Baffa Malam, rabonka da shi tun yaushe?"

Kansa ya sosa cike da jin kunya yace "Kusan five years ke nan"

Ba tare da Ummie ta kalle shi ba tace "Ya rage naka kaje ko a'a, don na san kana ziyartar wadanda kake ganin sun dace a duk lokacin da ka zo, daga yau zuwa gida Baffa Malam wajibi ne a kanka duk lokacin da ka zo."

Cikin sanyin jiki yace "To Ummie" daga nan ta bi shi da fatan Alkhairi tana faɗin "Allah ya kai mu goben," ya amsa mata da "Amin" daga nan ya dawo ɗakinsa, wanka yayi kamar ko yaushe ya sauya kaya ya fesa turare sannan ya kwanta.

Tun daga ranar da Imaan ta yi shawara da su Ramcy daga nan ta rabu da saurayinta Uzair wanda ke mutuwar sonta kuma yake e, Allah sarki Uzair duk da haka bai kawo komai a ransa ba sai yayi tunanin ko hacking accounts ɗin nata aka yi, daga ƙarshe sai ya yanke shawarar zuwa gidansu su yi magana.

Imaan na zaune a tsakar gida yaro yayi sallama yace wai ana sallama da Ihsan, ba ta ba da amsa ba sai da ta nufi ɗakinsu ta dubi Ihsan ɗin da yanzu ba ta fiye zaginta ba tace "Ana sallama da ke a waje"

"Waye?"

Imaan tace "Ban sani ba"

A gadarance tace "Ki dubo min mai Mashin ne ko mota, in mai Mashin ne ma ki sallame shi in kuma mai mota ne ki tambaye shi waye."

Kamar wacce ake ba wa control Imaan ta fita waje, kyakkyawan saurayi ne jingine da motarsa, hakan yasa ta ƙarason don cika aikan nata. Tana isa Uzair ya miƙe tsaye y ƙaraso inda take "Haba Babe, why kike wahalar da Ni these days? I've been..."

Ba ta bari ya ƙarasa ba tace "I'm sorry, ba Ihsan ba ce, in ji waye za a ce mata?"

Kallon kin raina min hankali ya aika mata, shi dai iya saninsa Ihsan ita ɗaya ce a gidansu in fact ba ta taɓa ba shi labarin wani a gidansu ba hasali ma ce masa take yi ita kaɗai ce a gidansu. Marairaice fuska yayi kamar zai yi kuka yace "Haba Babe, don Allah in wani laifi na miki..."

"Ka ga malam, I'm not your babe, ka faɗi waye kai za ta fito ai"

Yanayin kalamanta ne yasa ya ɗan sha jinin jikinsa sai yace "Ok, ki ce mata Uzair ne" ya faɗa ba don ya gama yadda ba.

Ko da Imaan ta faɗawa Ihsan sunan mai kiranta ce mata tayi tace "Ba ta da lokacinsa"

Kasa tafiya tayi sai ta tsinci kanta da jin kunyar zuwa ta ce masa ƴaruwarta ba ta da lokacinsa, a dai yadda ta fahimta saurayinta ne kuma da alamu saboda sabon saurayin da tayi yasa ta daina sonsa, to amma meye laifinsa? Wai su samari me yasa ba sa gane mata mayaudara masu son abun hannunsu irin ƴaruwarta Ihsan ne?

Jiki sanyaye ta fita, cike da tausayawa ta ƙarasa wurin da yake tace "Bawan Allah ka yi haƙuri da Ihsan, mahaifinta ya hana ta tsayawa da kowanne namiji sannan kuma ya riga da ya yi mata miji ya ce kada ta ƙara tsayawa da wani. Don Allah ka yi haƙuri kar ka ƙara zuwa gudun fuskantar wulaƙanci."

Tana kai wa nan ta juya ciki abun ta.

Allah sarki Uzair, wani irin zafi sosai kalaman Imaan suka masa, ganin har ta shige gida ba tare da ya yi mata tambayoyin da yake buƙatar amsoshinsa ba yasa ya dafe kansa, da ƙarfi yace "Why Ihsan? Why me?" Naushi ya aikawa iska sannan ya wuce cikin motarsa kai tsaye.

*BAUCHI, BAUCHI STATE*

Washe gari da safe bayan ya karya direct part ɗin Mammah ya wuce, cikin Sa'a kuwa ya tarar da Papa bai fita ba, bayan sun gaisa ya sanar da shi cewa za su wuce ya kuma faɗa masa dalili. Murmusawa Papa kawai yayi yace "Duk tsallake-tsallakenku ku yi ku gama Abduljalaal, daga kai har Jahaan shekarar nan ba za ta wuce ba zan ɗaura muku aure, wannan shi ne magana."

Sosa kansa AK yayi yace "Afwan Papa, ba sai an kai wannan mataki na, in Sha Allah kwanan nan za mu yi magana, Ku dai yi mana addu'ar Allah yasa Alkhairi a ciki."

"To ameen Jalaal, ba lallai ina nan dawo ba lokacin tafiyarku da na miƙa ku airport"

"Laa babu komai Papa, Junaid zai miƙa mu ai"

Papa yace "To shi ke nan, Allah ya tsare ya ba da Sa'a kan abun da ake yi, ku kula da kanku, ina shi Jahaan ɗin?"

"Ga Ni nan Papa" ya faɗa yana ƙarasowa yadda suke, gaisge da Papa yayi bayan ya amsa Papa ya dube shi yace "Jahaan, ka kula da ƙanin nan naka, ka tabbatar next zuwan da za ku yi kun shirya wa aure da gaske" kansa ya shafa yace "In Sha Allah Papa"

"To Allah ya muku albarka, ya ƙara muku son junanku ya kuma kai ku lafiya."

"Amiin Papa" suka amsa bakinsu haɗe, daga nan yace "Za su iya wucewa" babu musu suka fice tare, dag bakin apartment ɗinsu suka tsaya, AK yace da JK ya shirya su ɗan zaga gari yau kam, hakan aka yi kuwa ya koma shi kuma ya wuce part ɗin su. Wanka yayi ya shirya cikin wani expensive boyel mai sheƙi da taushi white color wanda Ummmie ce da kanta ta ɗinka musu shi da Abbie shi yasa ma yake iya saka shi don shi ba ma'abocin shigar hausawa ba ne. Sosai kayan suka amshe shi, hular da aka sayi kayan da jta ya ɗaura kan baƙar lalllausar sumar kansa sannan ya ɗaura agogonsa silver color ƙirar MLS mai shegen kyau, daga nan ya feshe jikinsa da turarukansa masu bayar da ƙamshi mai sanyaya zuciya.

Akwai takalmin da aka haɗa kayan da shi shima dai launin fari ne, sakawa yayi take ya fito kamar wani Basarake, har ya nufi ƙofa ya tuna da wayarsa, komawa yayi ya ɗauko ta sannan yayi dialling numbern Jahaan tare da fitowa. Karimah ce zaune a parlourn tana latsa wayarta, daddaɗan ƙamshin da ya ziyarci hancinta yasa ta dakata tana jiran taga ta ina ne. Baki ta sake tana kallonsa shi kam bai ma san tana parlourn ba saboda wayar da yake da JK. Ji tayi kamar ta je ta rungume shi amma da ta tuna tsiyar da ya tsula mata jiya babu shiri ta kama kanta. Har bayan ficewarsa ƙamshinsa na nan a parlourn wanda ya sauƙarwa Karimah da kasala, take wata irin buƙata ta bijiro mata gashi kuma babu wani wanda ta sani a nan Bauchi, ganin dai ta kasa daurewa yasa ta yi wanka itama ta fice zuwa wani wurin da za ta shaƙata la'alla ko ta samu abokin harka.

AK na fita suka haɗu da Jahaan a bakin part ɗinsu, wata farar mota mai Shegen tsada suka nufa wacce jiya Abbie ya fita da ita. Daga nan kuma suka fice daga gidan. Jahan ne ya dubi AK da hankalinsa ke kwance idamuwansa lumshe yace "Ina muka nufa ne?"

Murya ƙasa AK yace "Ziyara, za mu gaida Ummieta (kakar JK) daga nan sai mu wuce Azare gidan Baffa Malam, Ummie ta fara sauƙowa Jahaan, har ta ce nake zuwa gidan Baffa Malam, ke nan da yiyuwar nan gaba ta sake da Ni Ko?"

Cike da tausayawa jahaan ɗin yace "Of course yes, Ni ka ga da ban yi tunanin ma zuwa gidan Ummieta ba saboda tafiyarmu jibi. Za kuwa ta ji daɗi na sani."

Kai tsaye wani katafaren sabon mall AK yace ya raka shi, AK ne da kansa yayi mata siyayyar atamfofi kusan goma, turaren jiki, turaren ɗaki da na banɗaki zuwa man shafawa, shi kam Jahaan kawai bin sa da kallo yake, AK mutum ne ba gama gari ba of course, shi ne gaba da shi amma ya fi shi hangen nesa, samun kansa yayi da shafa kansa daga nan ya koma mota ya jira shi, babu jimawa sai ga shi ya dawo bayan ya zuba kayan a back seat. Daga nan unguwar Ummieta suka nufa da ke Zongo, a bakin gate suka yi parking sannan AK ya ɗauko Babbar Jakar da ke shaƙe da kaya ya damƙawa Jahaan.

Kallonsa Jahaan yayi ba tare da ya karɓa alamun yana buƙatar ƙarin bayani.

"Take it mana."

JK yace "I'm not taking it, Kai da ka siya kai za ka bayar, mu je kawai."

Ganin ya ƙi karɓa yasa ya riƙe sannan suka shiga, tun kafin su isa ciki yara suka kaiwa Ummieta saƙon zuwan Yaya Jahaan da abokinsa balarabe. Ai kuwa Ummieta ta fito daga ɗakinta tana zaman jiran isowarsu bayan saka jikarta Shahada ta ɗauko musu ruwa da lemo a kitchen.

Da sallama suka shigo parlourn, Jahaan a gaba sai AK a bayansa. "Maraba Lale baƙin Canada, sai yau kuka tuna da ƴar kakar taku?"

AK da yake jin matar kamar kakarsa kasancewar shi ba shi da ko ɗaya yace "Haba Ummieta, ai kullum kina ranmu, gidanki ne gida na farko da muka ziyarta..."

"Ai shi yasa nake sonka Auduljalal, ka fi Jahaan hankali wallahi, wai hakan suna shi ne babba."

Takaici ne ya kama Jahaan yace "to shi ke nan, Ni bari na koma kayana"

Da sauri Ummieta tace "Haba Jahaan, ai kaima kana da hankalin, ku zauna maza, ke shahadah yi maza ki kawo musu ruwa"

Nan suka fara gaisawa a mutunce, Shahada ta kawo musu ruwa suka sha, Jahaan kam da kallo ya bi shahada yana tunanin ko ƴar waye ita Kuma don bai santa ba."

Suna cikin hirar Jahaan ya dubi Ummieta yace "Ni Ummieta wannan yarinyar shahada kam ban gane ta ba"

Ummieta tace "Ina kuwa za ka gane ta Jahaan kai da ba ka da zumunci, iyayensu ma da wuya ka gane su ai saboda zaman Turai"

Wani iri Jahaan yaji sai lokacin yake ganin rashin kyautawarsa cikin sanyin jiki AK yace "Allah sarki, Ummieta sai an haɗa da haƙuri, kin san yanayin aikin ne sai a hankali, amma in sha Allah za mu gyara."

Murmusawa Ummieta tayi tace "Kai dai na yarda da kai Auduljalal, na san ka da hankali don haka na yi haƙuri amma kuma yin zumunci Allah"

"In sha Allah" AK ya amsa mata "To ba ki faɗa masa Shahada ɗin waye ba ce Ummieta"

"Rabu da shi Auduljalal"

"Yi hakuri dai Ummieta ki faɗa masa kika san ko ƴar gida za a yi da ita?"

Ai ba shiri fara'ar Ummieta ta ƙaru da sauri tace "Ai kuwa da na yi farin ciki Auduljalal, watakila albarkacinta Jahaan zai ke yin zumunci da ƴan'uwan uwarsa."

AK yace "In Sha Allah" harararsa Jahaan yayi duk da cewa cikin ransa daɗi yaji da abun da AK ɗin yayi. Ummieta tace "Sai Shahada ɗiyar ƙanwar uwarsa Asma'u ce, wacce ke aure a Kaduna, yanzu ma hutu ta zo har Allah ya haɗa su, ke shahadah" Ummieta ta ƙwala mata kira, amsawa tayi ta zo tana faɗin "Ga Ni"

Ummieta tace "Ba ki sansu ba ko? Yayyenki ne" cike da jin kunya tace "Ummieta ai ban san su ba, ina yinin ku"

AK ya amsa mata da "Lafiya" a gajarce, yayin da Jahaan ya washe baki yace "Lafiya ƙalau Shahada"

Cikin jin daɗi Ummita tace "To madalla, wannan shi ne Jahaan" ta nuna JK da hannu "Wannan kuma Auduljalal" dariya Shahada tayi babu tsammani tace "Kai Ummieta Auduljalal kuma ai kin ɓata masa suna" shi kansa AK sai da ya murmusa, yanayin yarinyar ya burge shi, daga gani ba ta da rawar kai irin ta ƴanmatan yanzu kuma da alama tana da kunya kuma ta samu tarbiyya. Jahaan kam dariya yayi yace "Rabu da ita ƙanwata, Matso ta nan mu yi zumunci kafin mu kawo muku ziyararku daban."

Shahada ta dawo ta ɓangaren da suke tana faɗin "Allah ya ba ku iko" ya amsa da "Amin"

"To ya karatu kuma?"

"Alhamdulillah Yaya."

"A ina kike naki karatun?" Tace "KASU, shekara ta biyu, ina karantar microbiology"

"Wow, ma sha Allah, Allah ya taimaka ya sa albarka." Ta amsa masa da "Amin Yaya"

"Sai kuma maganar aure ke nan?"

Hannunta ta saka ta rufe fuskarta tare da faɗin "Kai Yaya" shima dariyar yayi yace "E mana, ko ba yanzu ba?"

Shiru ta yi masa har lokacin fuskarta na rufe da hannayenta.

Sosai AK yake kallonsu, sun matuƙar ba shi sha'awa, how he wish shima Ummiensa na da ƴan'uwan da suke da yara, da zai yi ƙoƙarin yin zumunci da su tun da bai samu kusanci da tasa mahaifiyar ba.

Yana gani Jahaan ya miƙa mata wayarsa ta saka mata numbersa, ya matuƙar jin daɗi haka kawai yana fatan wata alaƙar apart from ƴan'uwantaka ta ƙullu tsakanin ɗan'uwan nasa da kuma yarinya mai kunyar nan shi kuma yayi addu'ar Allah ya ba shi mai irin halayenta don ya gama nazartar yarinyar.

Ko da za su tafi ƴan sauran cash ɗin hannun AK ya damƙawa Shahada wacce ta karba a kunyace tana godiya, da kansa ya janyo yakar da ya ajiye a bayan kujera ya dire ta gaban Ummieta tare da "A yi haƙuri Ummieta babu yawa"

"Har da wahala haka?" In ji Ummieta "To Madalla Auduljalal Allah ya yi albarka ya ƙara buɗi, na gode sosai, ku gaida iyayen naku, don Allah kar ka manta ka gaida Fulani, ita kam ba ta zumunci irin naku."

AK ya amsa da "To za ta ji Ummieta, sai mun kwan biyu kuma"

Jahaan yace "Sai mun dawo kuma karo na gaba."

Ummita tace "Ke Shahada ki raka su mana"

Shahada tace "To" sannan ta raka su har ƙofar gida wurin da suka yi parking, sai da suka tafi ta dawo gida tana murmushi.

Ta rasa dalilin murmushin amma wannan ziyarar ta Ya Jahaan ta matuƙar burge ta. Da haka ta koma gida.

Daga gidan Ummieta Azare suka nufa gidan Baffa Malam kamar yadda suka tsara, a can ma sai da suka tsaya suka yi siyayya mai yawa wacce kusan duka kayan abinci ne ma sai kuma shaddodi kala goma da AK ɗin ya siyawa Baffa Malam ɗin. Shi kadai ne wani dangi na mahaifiyarsa da ya rage a dai yadda take faɗi don shi zai iya cewa bai san komai akan Ummien nasa ba sai ƴan abubuwa kaɗan da yake tsinta daga wurin Ummah.

Manta sunan unguwar yayi don rabonsa da gidan an jima, hakan yasa ya kira Ummie ya tambayeta, tana faɗa masa yayi tambaya aka nuna musu, daga nan kuma suka wuce, tun da Baffa Malam yaga ana shigo da buhuhunan shinkafa da katankatan ɗin taliya ya tabbatar da zuwan Abduljalaal, wasu hawaye ne suka zubo daga idon tsohon. Shigowar su AK kai tsaye ɗakin Baffa Malam ɗin yake aka kai su kai tsaye. Bayan sun gaisa haka suka yi ta hira abunsu. Jin sha'awar sanin wasu abubuwa game da Ummiensa yasa ya tambayi Baffa Malam ɗin. Sai dai ba wani abu da ya samu hakan yasa ya ƙara gaskata zancen zuciyarsa na cewa akwai wani ɓoyayyen abu da ba a so ya sani game da Ummien nasa, ba ma wannan ba, something fishy and twisted happened.