12
Washe gari da safe Imaan ta wuce wurin aikinta da wuri, kamar kullum ba ta shiga sabgar kowa ba in ka cire ƙawarta Jamilah da take replying zancenta time to time wasun kuma sai dai tayi murmushi. Bayan sun fita breakfast ne wata young lady ady da ke aiki a sashen beverages ta zo wurinsu Imaan tace "Among you people from snacks centre, The CEO is looking for is it Fatima Nadada ko me?"
Gaban Imaan ne ya buga tana fatan Allah ya sa ba laifi tayi ba. Jamilah ce ta amsa mata da faɗin "Ki ce tana zuwa" juyawa matar tayi, Jamilah ta dubi Imaan tace "Imaan me yake faruwa CEO yake nemanki?"
"Wallahi ban sani ba Nima, Allah dai yasa ba wani abun ne ya faru ba."
Jamila tace "Amin fa, ki samu ki je akan lokaci kada ki yi laifi."
Jiki a sanyaye Imaan ta miƙe sai dai ta kasa tafiyar, marairaice murya tayi tace "Please Jamilah ki raka Ni"
"Ni??" Jamilah ta tambaya tana zare ido
"Ke fa yake nema not me, ba ki ja min laifi ba ba ki jawowa kanki ba Gara ma ki wuce"
"Don Allah kawai rakiya za ki min"
"Geji zuwa bakin ƙofar office ɗin, daga nan zan tsaya"
Da sauri Imaan tace "E na yadda"
Jamilah ta miƙe suka tafi har bakin office ɗin CEO da ba kullum yake zuwa ba sai ya shafe dogon lokaci tukun, birki Jamilah ta ci, Imaan tayi knockong sannan ta saka kunnenta jikin ƙofar, daga ciki taji an ce "Yes"
Hakan yasa ta tura ta shiga a hankali, lumshe idanuwanta tayi jin wani sassanyan ƙamshi ya buge ta.
Gabansa ta tsaya kanta ƙasa sannan ta gaishe shi, da hannu ya nuna mata seat sannan yace "You can seat down miss" zama tayi duk ba a sake ba while kanta na ƙasa sai wasa take da yatsunta. Kalllonta CEO yayi yace "Are You Miss Fatima?" Ta gyaɗa kai yace "Talk to me, ba na son maganar kurame ok?"
Shiru yayi sai kuma yace "Are You?"
Tace "Yes sir?"
Envelope ya miƙo mata ta saka hannu ta karɓa, "bayan taro da wannan Company ya haɗa wanda ya ƙunshi executives ɗinsa an kawo wata muhimmiyar shawara na ba wa haziƙan ma'aikata damar ƙaro karatu ko don saboda ci gaban Companyn, gaba ɗaya executives na Company sun yi duba akan kowanne ma'aikaci da daga ƙarshe kuma sun yi matsaya akan cewa ke ce kika fi kowa ƙwazo da yin aiki me kyau. Da wannan nake taya ki murnar samun wannan dama, za ki sanar da iyayenki idan suka amince to in kuma a'a sai a ba wa wani damar."
Yana kai wa Aya ya mayar da kalkonsa ga Imaan wacce ta rungume envelope ɗin a ƙirjinta hawaye da rige-rigen sauƙa daga idanunta. Haka kawai ya tsinci kansa da faɗin "Ya kike kuka Miss Fatima?"
Goge hawayen kan fuskarta tayi sannan ta miƙa masa takardar tare da faɗin "Wannan takardar ba ta cancance Ni ba, a ba wa wani kawai" daga haka ta dire ta akan table ɗinsa ganin ya ƙi karɓa sannan ta fara takawa za ta fice. Har ta buɗe ƙofa taji ya ce "Miss Fatima"
Dakatawa tayi ba tare da ta juya ba
"Dawo ki zauna" sam ba ta so hakan ba sai dai babu yadda za ta yi, amma ta ƙudiri aniyar cewa ba za ma ta kai takardar gida ba gudun kada wani rikicin ya ɓarke, me ma ya kai ta in ba so take Dada ta nuna mata iyakarta ba?
Nazartarta CEO yayi kana yace "Miss Fatima, abun da kika yi bai kamata ba, you're making a mistake for your life because opportunity comes ones, idan har kika bar wannan damar ta kuɓuce Miki fa za ki yi nadama nan gaba musamman idan wasu daga cikin Companyn suka amfana da damar, za a ƙara musu matsayi, so also the pay, she ma za a ƙara musu. Ki yi tunani sannan ki kai takardar gidan, idan har iyayenki na su amince ba sai a ba wa wani slot ɗin."
Ajiyar zuciya Imaan ta sauƙe sannan tace "Na fi kowa farin ciki da wannan dama Sir amma ta fi karfina, ko na je da ita gida haka zan dawo da ita don ba abu ne da zai yiwu ba, saboda haka maganin a yi ma kar a fara."
"To Miss Fatima, ban katse miki hanzati ba, amma a rashin tayi akan bar araha, ba ki san ko iyayen naki su amince ba"
"Ba za su amince ba fa" ta maimaita cikin sigar da ke tabbatar da abun da aka faɗa.
CEO yace "na san ba hurumina ba ne hakan, amma ko za ki faɗa min dalili?"
Tace "Haka kawai" yace "To ki ba Ni dama Ni zan zo har gidan naku na yi magana da iyayen naki, I'm sure za su amince."
Numfashi ta sauƙe ganin CEO ya kasa fahimtarta, sai dai kuma ba za ta taɓa bari takardar nan ta isa gidansu ballantana a shiga wata wutar masifar. Trying hard to understand her CEO Sulaiman yace "Is ok, za ki iya tafiya miss" jiki sanyaye Imaan ta fice a office ɗin, ko da Jamilah tace ta tambaye ta dalilin kiran ce mata tayi babu komai, kawai CEO ya tambaye ta shawarwari ne kan yadda za su ƙara gyara kayansu and that's all, ba don Jamilah ta yadda ba ta yi shiru sanin halin ƙawar Tata na zurfin ciki.
Bayan sun tashi daga aiki Imaan ta koma gida tana ta roƙon Allah ya sa kada CEO yace zai zo gidan nan ya jaza mata bala'i, jiki sanyaye ta ƙarasa ranar, jin babu wanda yayi sallama a gidan har lokacin baccinta yasa ta ji daɗi maras misaltawa tana addu'ar Allah ya mantar da shi ma gaba ɗaya.
*Bloordale village.*
AK ne zaune a katafaren office ɗinsa yana ta aiki a system ɗin da ke gabansa, lokaci guda ya takawa kansa birki da danna keyboard ɗin tare da jinginar da kansa da jikin lalllausar kujerar da yake zaune, lumshe Idanuwansa yayi yana furta sunan Allah a saman laɓɓansa. Sumar kansa ya shafa zuwa kwantaccen sajen fuskarsa. Gaba ɗaya ya gagara aikin da yake son yi tun kwanaki biyu baya, tunanin da yayi wa zuciyarsa ƙawanya yasa yayi saving abun da yake yayi switching system ɗin off.
Wannan wanne irin yanayi ne yake tsintar kansa tun bayan fara mafarkin yarinyar nan? Who's she actually? Me ya shigo da ita rayuwarsa? Me yasa yake shiga cikin tunaninsa da mafarkinsa while bai ma santa ba, yana jin kamar su yi maganar da JK amma zuciyarsa na hana sa, he want that to be confidential, yana so alaƙarsa da dream girl ya zama sirri tsakaninsa da zuciyarsa har sai ya samarwa kansa mafita. Shigowar JK da ya zauna a ɗaya daga jikin kujerun da ke gabansa yasa ya dawo da hankalinsa gare shi.
"Are You not Alright bro?"
Jijjiga Kai AK yayi yace "No at all"
"You must not be alright I can see, me yake damunka ne?"
AK ya ba shi amsa a gajarce da fadin "Babu komai"
Cike da kulawa JK ya riƙo hannun AK yana faɗin "Idan har zan iya kasa gane walwalada kuma damuwarka ban ga amfanin alaƙarmu da kai ba AK, na san batun auren nan nan, don Allah kada ka saka komai a ranka, keep on praying, muma muna yi maka, so also Ummje I know, tana maka addu'a dude, why za ka damu kanka bayan zaɓin Allah kake nema? Look, in ma batun yarinyar wurin Ummah ne kada ka wani damu, she'll not do something that'll harm you, na san in ta fahimci you're not interested za ta janye because she truly love you and your happiness."
Kalaman JK sun yi matukar tasiri a zuciyarsa har yake jin kamar an rage masa damuwarsa, amma kuma still akwai matsala, sai dai yana hoping ta zo da sauƙi."
JK ne ya dube shi yace "yanzu muka gaisa da Ummieta da Shahada, sun ce a gaishe ka kuma a maka godiya Allah ya ƙara buɗi."
Kallon JK AK yayi yana faɗin "Wai har ka fara kiranta a waya?"
JK ya ɗage masa gira "Ko akwai matsala ne?"
AK yace "Akwai mana, akwai matsala mana za ka fara takurawa yarinya da halinka."
"To ya za ta yi tun da tana so na?"
"Did she propose?"
Jahaan ya ɗage gira "Da zarar Ni na yi na san za ta amince?"
AK yace "Will you?" jahaan ya gyaɗa masa kai yana murmushi.
AK ya harare shi yace "Girma dai ya faɗi"
Da sauri JK yace "Abi?, AK ya gyaɗa masa kai
"Lallai kana ruwa kuwa Jalaal, to in ban faɗa mata ba so kake ita ta faɗa min?"
"Yesso"
"Lallai ba ka da lafiya AK, wallah I'm eager to see lokacin da za ka yi felling ma wata, crying in front of her, pleading her to love you yuh! Kaiii" Ya wani yi shewa kamar mace. Wani mugun kallo AK ya aika masa yana faɗin "Over my dead body"
"Kar dai ka cika baki"
Tsaki AK yayi zai miƙa JK ya riƙo shi "Haba my man, daga ƴar ƙaramar magana sai ka yi fushi? To shi ke nan, a bar zancen, bari na ba ka wuri ka ci gaba da aikinka."
Daga haka ya zaunar da shi shi kuma ya fice Abunsa yana murmushi tare da fatan Allah sanyaya zuciyar ɗan'uwan nasa don kuwa irinsu soyayya ta fi ba su wahala.
Ganin JK ya fice yasa AK sauƙe ajiyar zuciya, wayarsa ya ɗauko ya fara dannawa jin hr lokacin mood ɗinsa bai sauya ba yasa ya ja dogon tsaki tare da ajiye wayar ya miƙe daga mazauninsa ya nufi jikin window, tsgwa yayi yana ƙarewa sararin samaniya kallo, ya jima yana karanta wasiƙar jaki don shi kansa ba zai iya cewa ga tunanin da yake yi ba, gaba ɗaya duniyar ta tsaya masa ba ya jin daɗinta.
Rashin maslaha da mafita yasa ya baro office tun ba a je ko'ina ba. Ko da lokacin tashinsu yayi jahaan da ya biyo masa don jin ko zai wuce ne ko kuma zai tsaya kamar yadda ya saba ya tarar da office ɗinsa locked, "ikon Allah" ya faɗa a ransa yana mamakin kasancewar hakan, zuciyarsa ce tayi saurin ba shi amsa da "May be ba ya jin daɗi ne"
Da wanna tunanin ya wuce zuwa apartment ɗinsu, bedroom ɗinsa ya nufa kai tsaye, turus ya tsaya yana bin ɗakin da kallo ganin yadda duka mayuka da turarukan da ke kan mirror a baje a ƙasa alamar zubar da su aka yi ga kuma pillows a zube a ƙasa haka bedsheet shima ya samu sabon matsuguni a ƙasa ga kuma flower vases da suka tarwatse a ƙasa so also the bedside lamp.
Cikin kaɗuwa Jahaan ke bin ko'ina da kallo yana mamakin abun da ya faru da ɗakin, kamar wadda aka tsikara ya shiga ciki tare da wawwaigawa, "Then wure is he?" Ya tambaya yana dudduba ko wane sashe na ɗakin.
Ƙofar bayin da ya gani yasa ya nufe ta da sauri tare da murɗawa, da sauri ya shiga ciki yana ƙwala kiran sunan AK ɗin cikin murya mai nuna tsantsar damuwa, "Ina kake ne? Kana ji na?" Jin shiri yasa ya ƙara faɗin "Idan wani abun kake lemme know, are you ok?"
Shiru a wannan karon ma yaji hakan yasa ya yanke shawarar ƙarasawa ciki. Birki ya taka a lokacin da ya shiga ciki ganin AK ɗin tsaye yana kallon mirror. Ɗan tsoro ne ya ɗarsu a ran Jahaan, cikin Wata murya mai yankewa yace "Dude"
AK kam bai juyo ba bai kuma masa ba, hakan yasa JK ƙarasawa Wurin da yake yana mai shirin kai hannunsa jikinsa. Da sauri ya janye hannun jin wata irin tsawa da AK ɗin ya buga masa yayin da jikinsa ya ɗau mazari.
Cikin ransa yake ambaton sunan Allah tare da faɗin "What's wrong Jalaal?" Kamar gunki haka AK ke tsaye. "Please AK tell me what's wrong"
Ganin ya ƙi amsa masa yasa ya lallaɓa a hankali ya tsaya a saitinsa tare da miƙa kansa ta gefen hannun AK ɗin don samun ganinsa cikin madubin kasancewar AK ya kere masa a tsaye.
Abun da idanuwansa ga gani yasa yayi saurin rungume AK ɗin ta baya yana faɗin "Na shiga uku, me ya faru da kai Bro"
Duk yadda AK yaso ƙwace jikinsa daga jikin Jahaan ya gagara coz yana buƙatar hakan, yana buƙatar jinsa a jikin wani don samun nutsuwa, sun jima a hakan daga bisani JK ya raba jikinsa da na AK ɗin ya tsagayo gabansa, cikin tashin hankali ya riƙo hannunsa yace "Your hand is bleeding AK, mu je clinic a tsayar da jinin"
AK bai ce komai ba kamar wawa haka yake bin JK da ido, ganin hakan yasa JK ɗin jansa suka fice daga toilet ɗin sannan ya nufi hanyar fita daga ɗakin, dakewa AK yayi ya hana damar hakan, cike da kulawa Jahaan yace "Mu je mana, kana zubar da jini fa"
Kai ya kauda gefen kafin ya iya furta "I'm going no where, ka bar Ni duka jinin ya zube"
"Why AK, wani abu ya faru ne? Don Allah mu je mana"
AK yace "Babu yadda zan je"
Rausayar da kai JK yayi sanin halin ɗan'uwan nasa na kaifi ɗaya, da sauri ya nufi closet ya janyo wani Siririn towel ya fito sannan ya riƙo hannun AK ya naɗa masa ya ɗaure. Jawosa yayi ya zaunar da shi bakin bed kana ya fara tattare abubuwan da ke zube a tsakar ɗakin, abubuwan da suka tashi daga aiki kuma fita yayi ya shigo da bin, yana tsaye ya kwashe su sannan ya fitar da su, bayan mintuna ya shigo hannunsa riƙe da glass cup mai ɗauke da lemu mai sanyi. Kai tsaye wurin da AK ɗin ke zaune ya ƙarasa tare da miƙa masa cup ɗin yace "Have this" karɓa yayi bayan ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya kafa kansa, tas ya shanye shi JK yayi saurin amsar cup ɗin gudun kada shi ma ya yasar, a gefensa ya ajiye sannan ya zauna kusa da AK ɗin.
Shiru ne ya wanzu na wani lokaci daga ƙarshe JK ya katse shirjn da kiran sunansa.
Bai ɗago ba bare ya sa ran zai amsa, amma dai ya tabbatar da ya ji, hakan yasa ya dafa shoulder dinsa yace "Dude, me yake faruwa ne?" Shiru yayi bai amsa masa ba har lokacin bugun zuciyarsa na fita da wani mugun sauri ga wani irin zazzafar iska da yake fitarwa. Wannan dalilin yasa Jahaan tsorata don zai iya cewa a zamansa ko kuma dai rayuwarsu da ɗan'uwan nasa a taƙaice bai taɓa ganinsa cikin yanayi kwatankwacin wannan ba, duk da cewa a baya ya yi jinya sosai akan yadda Ummie ta banzatar da shi har yana tunanin ko wani laifi ne ya aikata gare ta amma tun bayan da ya fahimci rayuwa ya watsar da komai ya samu lafiya duk da cewa dai har yanzu akwai burbushin wannan damuwa, Jahaan ya ɗauki hakan kuma a matsayin abun da zai iya faruwa da kowanne ɗa da uwarsa ta saddakar da shi ga wata uwar a wani babi wai shi na kara.
Matsawa kusa da shi sosai Jahaan yayi don ba ya manta lokutan baya da yayi ta fama da jinya, likitan da ke lura da shi yakan ce a yawaita samar da skin-to-skin contact da shi, hakan ka iya rage masa raɗaɗi da damuwar da yake ji.
A wannan yanayi sun shafe kimanin awa ɗaya kafin daga bisani Jahaan yaji jikin AK ɗin ya saki alamar bacci, tallafarsa yayi gudun kada ya faɗi sannan ya kwantar da shi kan bed ɗin shi kuma ya zauna yana kalkonsa tare da tausaya masa, yana kuma roƙon Ubangiji da ya azurta shi da mace ta ƙwarai wacce za ta maye masa wasu muhimman gurabu da yake da giɓinsu a rayuwa.
Tsawon awanni uku AK ya farka, ko da ya gana farkawa da tunanin me yake ya fara, ganin shi kwance yasa ya miƙe zaune yana bin ɗakin da kallo kafin daga bisani ya tsaida kallon nasa ga Jahaan da ke jingine da fuskar bed ɗin yana gyangyaɗi.
Idamuwansa ya lumshe tare da fara tariyo abubuwan da suka faru, tun daga lokacin da tunanin yarinyar da yayi wa laƙabi da dream girl ɗinsa ya addabe shi, zuwa tunanin gizon da ta masa a ranar da suka kai wa Baffa Malam ziyara, zuwa tunanin yadda zai ƙara tozali da ita ya kuma yi mata tambayoyin da yake da su tattare da ita tun daga kan dalilinta na shiga rayuwarsa ta kuma liƙewa tunaninsa da kuma rayuwarsa ga shi har yakan iya ajiye ayyukan da ke gabansa a dalilin tunaninta da ya addabj zuciya da ƙwaƙwalwarsa. Yana iya tuna lokacin da ya mike tsaye yana tunanin me zai aikata ya daina tunaninta ne ya fara jin kansa na sarawa, takamaimai ba zai iya tuna lokacin da ya bar office har ya dawo apartment ba, zuwa kuma yanzu.
A hankali ya ci gaba da bin ɗakin da kallo yana bin komai da komai na cikinsa, bedside lamp bai ga ba so also flowers ɗin da ke jere kan mirror ɗinsa, "what really happened?" Ya tambayi kansa, "ke nan dai ba mafarki ba ne? This girl is making me crazy and I don't know why" ya faɗa cikin zuciyarsa tare da ziraro ƙafafuwansa ƙasa, toilet ya shiga ya watsa ruwa, a nan ma ya ga sauyi sosai bayan ya fito ya sanya jallabiya ya yi ƙoƙarin tayar da Jahaan da baccin ya fara cin idonsa, a matuƙar firgice ya tashi hakan yasa ya dire ƙasa tare da tsayawa sannan ya dafo kafaɗar AK ɗin cikin kulawa yace "Man! Ka tashi, I'm worried about you, what all made you behave strange e?"
"Me kuma nayi?" He asked in his soft voice
Kallonsa Jahaan yayi yana ƙara nazartarsa, tabbas ya lura bai san abun da yayi ba, hakan yasa ya sauƙe hannunsa da ya ɗaura a shoulders ɗin AK ya ja hannunsa suka fita, kai tsaye bin ya nuna masa, broken pieces of bedside lamp, flower bases and kwalaben creams ɗinsa kusan bakwai.
Ɗauke da ayar tambaya ya dubi Jahaan ba tare da ya ce komai ba. Jahaan yace "Sit down first" babu musu kuwa ya zauna shima ya zauna next to him
"Ka ɗauke Ni a matsayin ɗan uwa?"
AK ya tsira masa ido ba tare da ya ce komai ba.
"Ka yi shiru?"
A hankali AK yace "Ban gane ba"
Jahaan yace "Ina nufin ina da matsayin ɗan'uwa a wurinka?" AK ya gyaɗa kai
"Babban aboki fa?" Ya ƙara gyaɗa masa kai
"Don Allah AK, Abduljalaal! Don Allah, idan har ina da waɗannan matsayin da ka ce Kada ka ɓoye min damuwarka"
AK yace "Tell me what happened first and I promised to tell you what's wrong with me"
"Deal?"
AK ya gyaɗa kai tare da faɗin "Deal"
Jahaan yace "na biya ta office naka to know if you're leaving sai mu tafi tare, sai na tarar closed, i was surprised saboda na san ba ka barin office before time hasali ma har da daddare kana iya zama ka yi wasu muhimman ayyukan, I rushed home to see if all is ok shi ne na..."
Nan ya labarta masa komai sannan yace "now you're promise"
Kamar AK ba zai ce komai ba can kuma yace "I'll ask you first, In ka amsa min zan yi amfani da amsoshin da ka bani domin na maka bayanin what's actually going"
Tsananin son sanin me ke damun AK ɗin yasa jahaan amincewa da batun AK.
Shiru suka yi can AK yace "Yaya ake gane feeling na so? Ina nufin ba irin wadda ke existing tsakani ɗa da kuma iyaye ba ko na ƴan'uwantaka?"
Juya idanuwa Jahaan yayi sannan yace "Are You too in love?"
Harararsa AK yayi sannan yace "Ba ka shirya jin damuwar tawa ba ke nan?"
Jahaan yayi saurin faɗin "Nooo" tare da jan ƙarshen "amma tambayar taka ce tayi confusing ɗina, tana da alaƙa da damuwar taka ne?"
"I don't know"
"Ok, keep on going ina jinka?"
"Should I?" AK ya tambaya "Ka amsa tawa tambayar ne?"
"Jahaan ya dafe Kai yana fatan shiriya ga ɗan'uwan nasa don ba kaɗan ba tun suna yara ma haka yake wahalar da Jahaan ɗin duk da shi ne babba sai dai sassanyan hali da yake da shi yana danne girman da yake da shi har wasu kan yi tunanin AK ɗin ne gaba da Jahaan.
AK "I'm all ears" cikin halin ko in kula
"To kaima dai ka san nima ban sani ba tun da I've never been in love"
"Ke nan i should tell Shahida or shahada the naked truth that you don't love her?"
Jahaan ya zaro ido tare da faɗin "Haba AK, ina ƙoƙarin in taimaka maka kana shirin ruguza Ni?"
"Then give me my amswey"
"Na faɗa maka nima ban sani ba, but we can Sulaiman to find out sai mu duka biyun mu samu ilimi"
Da sauri AK yace "You can call him alone, ni Kai na tambaya in ba ka sani ba fine sai a bar magabar ai ba dole ba ce.
Jahaan ya dafe kai yace "To ai shi ke nan"
Tunawa da illar rashin amsa tambayar yasa Jahaan faɗin zan kira shi idan ya so sai mu ji ilimin tare.
AK bai ce masa komai ba har ya Ciro phone ɗinsa yayi dialling numbern Sulaiman.