13
Suna zaune tare Jahaan ya kira Sulaiman, da farko bai ɗaga ba sai a kira na biyu don dama bai tsammanin hakan ba tun da dai dare ya yi. Ƙara jarrabawa Yayi a karo na biyu, cikin ikon Allah Sulaiman ya ɗaga, gaisawa suka yi har yana tsokanar Jahaan ɗin wai yau ya tuna da shi, ya tambaye shi ina AK yace ga shi a kusansa, sanin hali yasa bai ce ma a ba shi su gaisa ba, ai kuwa ko an bayar ɗin ba magana zai yi ba musamman yadda ya wani hakimce ya ɗaura ƙafarsa akan ɗaya.
Gyaran murya Jahaan yayi kana yace "Ka ga Sulaiman ƴar tambaya gare Ni"
"To ba damuwa ina jin ka"
Jahaan yace "Don Allah idam mutum ya kamu da soyayya ta yaya zai gane, wato yaya feeling ɗin soyayya yake?"
Dariya Sulaiman yayi a ɓangarensa kana yace "Ko dai ka zurma ne mutumina?"
Jahaan ya ɗago ya kalli AK shi kuma ya zabga masa harara. Dariya yayi ƙara-ƙasa sannan yace "Ni dai kawai ka faɗa min in ka sani"
Dariya Sulaiman yayi yace "Ai dole na fada maka kaji, idan ta tabbata mu samu mu aurar da ku, ƙawaye kowa ya yi aure amma banda ku, Allah dai ya kawo matan da za su kwashe mu kafin..."
"Ka ga Sulaiman, ba surutu nace ka min ba"
Jahaan ya faɗa saboda kallon da AK ɗin ya masa
"Tooo" shima ya ba shi amsa "Lallai na yarda zama da maɗaukakin kanwa shi ke kawo farin kai don kuwa ga shi kaima ka fara koyon halin Abduljalaal "
Tsaki Jahaan yayi don so yake AK yaji amsarsa shima ya faɗa masa damuwarsa
"Please ka ba Ni amsa in ka sani"
"Me ye ma tambayar taka?"
Jahaan yace "Nace ta yaya ake sanin an kamu da soyayya sannan ya feeling ɗin soyayya yake?"
Gyaran murya Sulaiman yayi yace "wato in na fahimce ka alamun kamuwa da so kafin an furtawa juna?"
Cike da takaicin yadda Sulaiman ke jan maganar yace "E haka"
Sulaiman yace "To Kamar yadda masu iya magana suka ce so ba ya boyuwa tabbas haka ne domin da zarar so yafara shiga zuciya sai kuma gangar jiki ta fara nuna wasu ɗabi'u da alamomin na so ko na amincewa, wasu daga cikin alamomin kamuwa da so kamar Burgewa, wato da zarar kaga budurwa tana burge ka haka kawai ko dan wani abu kamar ƙoƙarinta ,kyanta kwalliyarta, ko wani abu da ya shafe ta,.To hakan alama ce dake nuna cewa zuciyarka za ta iya amsar soyayyarta."
Jahaan yace "Ina jin ka"
Sulaiman ya ci gaba "Abu na biyu da ke nuna alamun cewa ka kamu da so akwai kallo, yawaita kallon abun da ka kamu da soyayar tasa ko da kuwa ba za ka iya hakan ba, da zarar so ya fara processing a zuciyar saurayi ko za ka ga ka fara jin kunyarta koda ba a furtawa juna kalmar so ba musamman ma idan ba ka taɓa soyayar ba, idan ka kalleta sai ma ji ka masa sakewa a kusa da ita har ka kasa iya haɗa ido da ita, idan kuma cikin rashin Sa'a ka kalleta ɗin kuka yi four eyes sai kaga ka kauda kai da wuri kana jin wani irin yanayi na fusgarka."
"Wata alama mai nuna tabbas akwai so ita ce jin fargaba idan an samu kusanci ko an ambaci ko da sunan abar ƙaunar ce ko kuma sauyin bugun zuciya idan an samu wani kusanci duk ƙanƙantarsa. Masu raunin zuciya a irin wannan yanayin suka rasa control musamman waɗanda kaɗaici ke ɗawainiya da su, hakan kuma zai iya sa su yi mummunan aiki kamar dukan wanda ke kusa da su saboda rashin gano ainihin me ke damunsu ko kuma su yi fa yin abu kamar masu taɓin hankali".
Shiru Sulaiman yayi tare da haɗiyar yawu. Cikin zaƙuwa Jahaan da ke jin kamar da shi ake yace "E ina jin ka"
Sulaiman yace "Na gaba, yawan tunaninta a ranka, Kaji kana so ake labari akanta ko kuma kai kanka kana son bayar da labarinta musamman ga makusantanka.."
"Da zarar so ya ƙullu yakan haifar wa da zuciya tunani sosai, wani lokacin tunanin ya haifar da farinciki domin zai raya ma ai waccce yake son za ta so shi don yana da kaza da kaza har sai ka gamsar da kanka zata soka sai kaji farinciki, a wani lokacin kuma so sai yasa ma tunani me zafi da shakkum anya kuwa za ta so ka? Anya wani bai dace zuciyarta ba this and that..."
"Daga nan fa?" jahaan ya tambaya cike da zaƙuwa
"Daga nan sai ka fara jin kana son ƙulla alaƙa da ita ko mutunci. Daga alaƙar ta ƙullu sai ka ji kana so. Kasancewa tare da ita a kowanne lokaci, yawan tunaninta, tausayi da kuma kyautatawa za su biyo baya, za ka ji cewa za ka iya kasancewa da ita a kowanne irin yanayi.
Rashin bayyanar da wannan saƙo saboda wani dalili na kunya ko wani abu kan iya haifar wa da mutum tunani maras yankewa a kowanne lokaci har mutum ya fara ji ya ƙosa da rayuwar in aka kai wani lokaci kuma wani ciwon ya kama mutum musamman na zuciya saboda rashin samar mata da nutsuwa da aka yi ba tare da an farga ba."
Wata irin ajiyar zuciya AK da ke sauraronsu yayi shi kuwa Jahaan gaba ɗaya ji yake ma kamar da shi ake, cikin ransa yace "Ke nan dai son Shahada nake?"
Maganar da Sulaiman yayi yasa ya tuna cewa bai yi disconnecting call ɗin ba
"Ya dai JK?"
Jahaan yace "Na gode ƙwarai Sulaiman."
Sulaiman yace "Allah yasa wata ce ta sace zuciyarka jahaan" dafe saitin chest ɗin sa yayi tare da kallo AK da fuskarsa ba ta wani bayyana wata alamar da za ka fahimci yanayin da yake ciki ba sannan yace "Ka saka Ni a addu'a kawai Allah ya ba Ni ita, sai da safe" ƙit ya katse kiran saboda sabon halin Sulaiman ɗin na yawan magana, ko shi kansa at times in suna tare da Sulaiman uzuri kawai yake masa bare kuma AK.
Kusa da AK ɗin Jahaan ya matsa sannan yace "To Man, ka cika alkawarinka"
"Wane alkawarin kuma?" Ya faɗa with his innocent face and look
"Wallahi ba ka isa ba Jalaal, dole ka faɗa min abun da ke damunka ko kuma na sanar da Abbie"
Da sauri AK yace "Behave maturedly mana, So kake ka daga masa hankali for no reason?"
jahaan yace "e! Haka nake so, ai gara ya san yanayin da kake ciki tunda Ni da nake kusa da kai ka ƙi fadamin after all ni tawa damuwar ba na iya ɓoye maka don Ni ina gudun abu ya wuce tunani a ga laifina"
Jikin AK ne yayi sanyi, ko ba a faɗa masa ba ya san Jahaan na daban ne gare shi kuma kyauta da Ubangiji ya ba shi mai tsananin daraja, tun yarinta suke tare, yake sadaukar masa da abubuwa da yawa ciki har da farin cikinsa domin nasa, je deserved to be treated well of course.
Sanyaya murya AK yayi yace "Zan faɗa maka, amma not now"
Jahaan bai ce masa komai ba ya fice daga ɗakin sannan ya nufi nasa ɗakin.
AK na ganin fitar Jahaan ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya miƙe ruwa ya watsa daga nan ya sauya kaya. Ji yayi kawai babu abun da yake buƙata fiye da Muryar mahaifiyarsa duk da ya riga ya san cewa ba wata maganar za ta yi da shi ba, amma duk da haka he still needs it.
Kiran fari Ummie ta daga, daga gaisuwa kuma babu wani abu da ta ƙara faɗi, haka suka share kusan mintuna sai ita ta kashe kiran. Numfashi ya sauƙe sannan ya kira Ummah, sosai suka gaisa tana ta ce masa tayi kewarsa this and that.
Sun sake suna hira abun su ta kawo masa zancen Karimah, da haka ya mata sallama da faɗin dare ya yi, babu yadda Ummah ta iya suka katse kiran tana sakin zazzafan huci. Bai bi ta kan Jahaan ba don ya riga ya san cewa zai ne shi, hakan yasa ya fice garden don shan iska da kuma ɗebe kewa.
*AZARE, BAUCHI STATE*
A ɓangaren Imaan tun da taga kwanaki biyu sun shuɗe wata wutar masifar ba ta ɓullo a gidan nasu ba ta tabbatar da cewa CEO Sulaiman ya riga ya janye batun tafiyarta ƙarin karatu, sosai kuma hakan ya mata daɗi yayin da Ihsan kuma komai ya ƙaru, ji da kai ya ƙaru haka ma dogon Buri sai abun da ba a ce komai ba, yanzu fantamawa take abunta don yanzu suturun da take ta'ammali da su, gyalalluka, Cosmetics da dai sauran kayan amfani duk sun fita daban don kusan duk tsoffin kayanta ta bar wa Imaan su duk da cewa dai English wears ne amma ta karɓa tun da dai hijabi ita take sakawa ba mayafi ba. Kayan maƙulashe kuwa kamar su buɗe baki su yi magana don yadda Barr. Junaid ke ajiye mata su niƙi niƙi wanda hakan ya mata matuƙar daɗi har tana jinta daban cikin duniyar baki ɗaya, ji take ta fi kowacce mace Sa'a a duniyar nan, abu mafi jin daɗi gare ta ma bai wuce yadda take juya Barr. Ɗin ba don kuwa duk abun da ta ce ba ya tsallakewa.
Shi dai ya gama kamuwa da soyayyar Ihsan fiye da kuma kuma har yanzu bai san cewa ba ita ce wannan yarinyar da zuciyarsa ta fara harbuwa da ƙaunarta ba kasancewarta ba, a yanzu ba shi da wani burin da ya wuce ya kyautatawa Ihsan tun da har a gidansu babu wanda ya nuna ƙinsa a kanta, sai dai abu ɗaya da yake ɗaga mas hankali shi ne duk yadda Ihsan ke nuna masa so da ƙauna ta ƙi ba shi damar isowarsa gida, a cewar ta ita sai ta kammala karatunta, to yaya zai yi tunda duk abun da take so shi ma yana so? Dole ya zubawa sarautar Allah ido har zuwa lokacin da Allah ya tsara musu zai yi.
Abu ɗaya da bai sani ba shine, Ihsan ba wai shi take so ba, kuɗin hannunsa kawai take ƙauna don ita a nata tsarin ko yau ta haɗu da wanda ya fi shi, babu jiran da za ta yi za ta rabu da shi ta auri wanda za ta zama abar nuni, ta zama ta musamman cikin mata ta yadda ko wacce mace za ta so irin daular da take ciki. To tun da ta rabu da Uzair gani take babu wani namijin da ba za ta iya barinsa ba idan ta samu wanda ya fi shi. Abu ɗaya kuma ya tsaya mata a rai da kuma ruhinta, ta kuma gagara cire shi, takan tsinci kanta cikin kewa da kuma tunanin halittar da ta yi wa kallo ɗaya tak a rayuwarta tare da fatan ina ma a ce wannan kyakkyawar fuskar Tata ita ce kwance a kan fuskar Junaid, to babu shakka ita mai amince masa ne su yi aure, sai dai fuskar nan ta gagara barin ruhi da ƙwaƙwalwarta, gani take kamar wannan fuska ita ce abokiyar rayuwarta, amma ta yaya? Ta yaya za ta ƙara ganin fuskar bayan ba ta san ta yadda za ta fara ba?
Ihsan ke nan, wannan dalili yasa ta fara tunanin ta yaya za ta samu wannan fuska ko kuma makamanciyarta? "dandalin sada zumunta!" Ta ba wa kanta amsa.
Tun daga yau kuma ta fara buɗe hajojinta a social media fatanta dai Allah ya sa ta dace, a yanzu dai facebook ne kawai Ihsan ta ƙi aminta da buɗe account a can don su Ramcy sun ce mata masu facebook faƙirai ne.
Washegari Imaan ta tashi da kewar Hajiya, kasancewar weekend nr yasa taji tana muradin zuwa gaida Hajiya ɗin. Misalin ƙarfe goma na safe ta shirya cikin wani Navy blue palazzo trouser da Ihsan ta ba ta, ta haɗa da rigarsa sannan ta shafa ƴar powder da kuma wet lips, sosai tayi kyau kamar me, abun ka da wadda bai saba ba dama an ce in ya yi ta fi yi masa kyau.
Baƙin takalminta ta saka da kuma baƙin Hijab sannan ta yi wa Mami sallama ta fice. Mai adaidaita ta tsayar, ta ce masa ya kai ta Filin pastor, bayan ya kai ta ta ba shi kuɗinsa sannan ta nufi gidan Hajiya. Gaishe da Baba Bala mai gadi ta yi ya amsa yana tsokanarta wai yau ta tuna da su, ɗauke da murmushi kan fuskarta tace "Haba Baba Bala, dama ban mance ku ba, yanayin aiki ne yasa ba na ziyartarku amma ai Hajiya tawa ce akwai amana'
"Allah Imani (kamar yadda yake kiranta)"
"Ta gyaɗa kai tare da faɗin "Bari na shiga wurin Hajiyar tawa "
"To shi ke nan, ki fito lafiya"
Kanta ta saka ta nufi sashen Hajiya, ɗauke da sallama a bakinta ta shiga, babu kowa a parlourn sai Yar matashiyar da ke goge-goge.
Gaishe da ita Imaan tayi itama ta mayar mata da gaisuwar tun da kusan a girme Imaan ɗin ta girme mata.
Kujera ta nunawa Imaan tace "Ki zauna, bari na yi wa Hajiyar Magana."
Imaan ta zauna tare da fadin "Na gode"
Free minutes sai ga mai aiki Hajiya na biye da ita, da saurin Imaan ta miƙe ta nufi Hajiyan tare da rungumeta tana jhun murna.
Itama Hajiyar dariya take tunda Imaan ɗin ta nufo ta. Cike da farin ciki Hajiya tace "irin wannan Oyoyo haka Imaan ai sai ki karya Ni"
Imaan ta janye jikinta tana ɗan tura baki
Hajiya tace "Yau ke ce a nan? To mu koma cikin kawai,. Sa'ade ki kawo mata wani abun"
Daga haka ta riƙo hannun imaan suka nufi ɗakinta.
A bakin gadi ta zaunar da Imaan tare da fadin "Ni fushi ma nake da ke Daughter, yanzu kin fara mantawa da Ni"
Imaan tace "Wane Ni in manta da Hajiyata? Wai haka Baba Bala ma yace na manta da ke bayan kuma ya san yanayin aikinmu "
Hajiya ta taɓe baki tace "E, aiki aiki kamar ke ce shugabar aiki, rabin ki da nan Imaan tun yaushe?'
Imaan tayi rolling Idanuwanta tace "Hajiya wata biyu ne fa kawai"
Hararar wasa Hajiyar ta aika mata tare da faɗin "Kawai ko? To ina ce dai yau ɗin kwanaki za ki mana?"
Zaro idanuwa Imaan tayi tare da faɗin "Kai Hajiya, iya kayan jikina ma nazo da shi, zan dai yini da yamma sai na tafi"
Hajiya ta zauna grfenta tace "Ban fa yarda ba Imaan, Mami ta rike min ke a gidanta ta hana Ni ke, gaskiya dai, to shi ke nan."
Imaan tace "Hmm, Hajiya ko gaisawa fa ba mu yi ba kike ta nemo mana magana"
"Oh? Maganar ma nemota nake?"
Imaan ta toshe bakinta da hannayenta kana tace "Ni dai Ina kwana, kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau Imaan, ya su Dada, Mami, Abba da ihsan?"
"Lafiyarsu ƙalau, Mami ta ce a gaida ki ma"
Fuska sake Hajiya tace "To ina amsawa kuwa, ya aikin naki? Ina fata dai kina jin dadinsa"
Imaan ta gyaɗa kai, Hajiya ta ce "Buɗe baki za ki yi ki faɗa min Imaan ba ki gyaɗa min kai ba,
Jiki sanyaye Imaan tace "Alhamdulillah, ina jin dadinsa sosai"
Nazartarta Hajiya ta yi kafin ta ce "Ma sha Allah" sai kuma ta yi shiru tana bin Imaan ɗin da kallo har sai da ta tsargu, can tace "Lallai Ikaan, to ya batun samari kuma? Ina ce yanzu dai akwai tsayayye"
Ɗan tura baki Imaan tayi tana faɗin "Ni fa babu kowa, na fi so ma na yi rayuwata a haka Hajiya"
Sakaka Hajiya tayi tana kallon Imaan har ta gama maganar kana tace "E lallai kam, biri ya yi kama da mutum, samarin ma kora su kike yi ke nan?"
Bakinta gaba tace "To Ni Hajiya ba zan yi aure ba, ko kina tunanin ma Dada za ta bari na yi aure ne bayan Ihsan tana gidan?"
"Ke da Ihsan ɗin waye gaba ne e? Wai har yanzu Dada ba ta sauya hali ba ne?"
Imaan kam ba ta amsa mata ba sai ajiyar zuciyar da ta sauƙe.
Hajiya tace "Shi ke nan, na fahimta Imaan, amma dai ki cire batun wata Ihsan a ranki duk da cewa na san ba iyawar za ki ba, ki fahimci rayuwa kuma ki sani, yanzu ne lokacin da tauraron yake haskawa, babu wata magana ta sai kin jira Ihsan, idan har kika yi wasa da damarki zuwa gaba ba lallai ne samarin ma suna kallonki ba sai an haɗa da addu'a."
"Don haka ki nutsu ki ji Ni ma, idan har don wannan ne kike korar samari to ki daina, idan har akwai Wanda ya zo kuma kika ji ya kwanta Miki sannan kika yi istikhara kika ji dai kika son hakan ki sanar da Ni first, don na ga in ta Maminki za a biye haka za ta ƙunshe baki ta ki magana, saboda haka ki fara faɗa min kin ji?"
Imaan ta gyaɗa kai yayin da hawaye ke zubo mata, share mata Hajiya tayi sannan tace "Yauwa, ki nutsu ki ki abun da na faɗa Miki kin ji yarinyata?" Still imaan didn't t say anything bayan gyaɗa kai da ta yi.
Ganin yadda ta suƙure saboda maganar da suka yi yasa Hajiya kawo mata wani zancen, ba a wani jima ba kuwa imaan ta sake suna hira abun su, abun mamaki kuma yadda suke hirar suna dariya tana wani shagwaɓa abun ta, hakan ya tabbatar da cewa ko wace ce wannan Hajiya tana da girma mai tsoka da muhalli babba cikin zuciyar Imaan tun da har ta iya sakewa suke hira, wannan suƙurarriyar Imaan ɗin kuma ta sauya zuwa wata daban.
Haka suka yini abun su, Hajiya sai ɗauko abubuwan motsa baki da ba ta gajiya da su take tana ba wa imaan ɗin ita kuma na sha, salla ce kawai take tayar da su, sai kuma gama abincin rana da aka yi suka ci. Wuraren ƙarfe biyar Hajiya ta yi baƙo wanda yayi silar tafiyar Imaan ɗin babu shiri bayan atamfofi kusan huɗu da Hajiyar ta haɗa ta da su da kuma kuɗin da ba ta san nawa ba ne sannan tace da ita kar tana jimawa da yawa ba tazo mata ba, sosai ta kuma ba wa imaan ɗin sakon gaisuwa ga Abba da Mami kana tace a gaida Dada ma. Bakkn nan kuwa ba kowa ba ne wannan baƙo sai CEO Sulaiman..
Tun da Imaan ta tafi take ta saƙawa da kwancewa cikin ranta tana mamakin me yazo yi gidan Hajiya? Sai dai kuma daɗin da ta ji shi ne shi bai ganta ba, fatanta Allah ya sa kar ya kawo batun karin karatun da company ya ba ta dama ta yi rejecting don abu mai sauƙi ne Hajiya tace za ta tsaya har Imaan ɗin ta tafi.
Bayan Imaan ta koma ta isar da saƙon gaisuwar Hajiya ga kowa sannan ta budewa Mami kayan da Hajiyar ta ba ta, ta ba wa Mami ɗaya ta kuma miƙa mata kudin tace ta biya kuɗin ɗinki sannan ta ajiye mata sauran, babu tsammani Dada ta shigo kamar aljana ta fizge kuɗin da Imaan ke mikawa Mami.
"Munafukan Allah ta'ala, wai Ni Rahanatu sai zuwa yashe ne za ki daina koyawa ƴar nan munafurci? Anya kuwa za ku shiga aljanna?"
Imaan da takaicin Dada ya cika ta tace "Dada Hajiyata ce fa ta ba Ni shi ne na ba wa Mamin..."
"Ungo nan munafuka!"
"Don ubanki Hajiyar taki sai tace ki ba wa uawarki kawai? Ko don dama can bakinku ɗaya itama ai munafukar ce, aikin banza da wofi" ta sa hannu ta tattaro atamfofi kana ta nufi hanyar waje tana faɗin "Na ga Ni da ku wai zai gaji ya bar wa wani don wallahi har abada ba zan mance da ku ba munafukai kawai"
Ajiyar zuciya suka sake a tare Mami kam haƙuri kawai take ba wa Imaan wacce ko kaɗan hakan bai wani dame ta ba sai ma mikewa tayi sannan ta nufi ɗakinsu
*Zuwa yanzu da yawa daga cikin masu karatu sun ƙosa su san wace irin Rikitacciyar alaƙa ne ke tsakanin Dada da kuma Mami har ma ta shafi Imaan, sannan da yawa na son sanin Matsayin Hajiya ga Imaan, to in sha Allah babu na gaba zai warware muku komai.*
*Kada ku manta saura kaɗan mu gama book one, book two kuma na kuɗi ne saboda haka ku ba da himma ku biya mu yi tafiyar tare da ku.*
***
*React and share fisabilillah

*Kada ku manta saura kaɗan mu gama book o

*Kada ku manta saura kaɗan mu gama book

Zuwa yanzu da yawa daga cikin masu karatu sun ƙosa su san wace irin Rikitacciyar alaƙa ne ke tsakanin Dada da kuma Mami har ma ta shafi Imaan, sannan da yawa na son sanin Matsayin Hajiya ga Imaan, to in sha Allah babu na gaba zai warware muku komai.
***