Kuncin zuci
by @bintuuu
Dan gajeran hutun su Na'ima ya qare suka fara shirye shiryen komawa makaranta, duk wani abu da zasu buqata 'yan qananu qananu na amfanin yau da kullum Mami ta hada musu, bawani shopping sukayi ba don acan din babu abunda suka rasa.
Dawowar da Na'ima taji bataso sai akasin hakan ya faru, batayi tsammanin zuwanta gidan zai saka mata nutsuwa mai tarin yawa ba wanda har zataji batason komawa England ba, sai dai tasani komawanta school din yazama dole shiyasa ta ke ture iren iren tunanin nan daga ranta.
Zaune suke a main falon gidan da yamma, Na'ima dake sanye cikin boubou mara nauyi tana zaune qasa a gefen Mami nan kan carpet tana tayata ware wasu kaya a leda da Mamin ta aiki driver ya siyo safiyar ranan, sai Mami ta ciro wani expensive air freshener ta miqawa Na'ima tace "Habibti sa muku wannan cikin kayanku zai muku amfani" karba Na'ima tayi tace "Toh" ta ajiyeshi gefenta a kan carpet, Nafisa ta dan dago daga kwancen da take akan kujera tace "Mami duk munadasu fa" sai Mami ta kalleta tace "Wai da nace ku qara akan nakun" Nafisa ta qarasa miqewa zaune tace "Mami kayan zasu mana yawa fa" Mami ta juya gun Na'ima tace "Habibti barshi toh" Na'ima tace "A'a Mami munaso, mungode" Mami tace "To ke kadai zaki rinqa amfani dashi kar naji kin bata, tunda ita ba'a mata gwaninta" sai Nafisa ta fara dariya tace "Kiyi hakuri Mami" tace "Ke kika sani, yauwa nasa Lantana ta siyo muku kuka da busasshen kubewa sannan ta hado da daddawa mai dadi dan nacan basa sarrafashi me kyau" bude baki Nafisa tayi saura kadan Na'ima ta kwashe da dariya sai ta dan kauda kanta tana murmushi, Nafisa tace "Mami daddawa fa..wallahi warinsa duk cikin jirgin nan sai kowa yaji" Mami tadan tsaya kallon Nafisan, dan turo baki Nafisa tayi alamun shagwaba ta koma ta kwanta akan kujeran tana gyara skin face mask din da ta saka, Mami ta juya ta kalli Na'ima tace "Bakwa yin tuwo ne Na'ima?" sai Na'ima tayi saurin jijjaga kai alaman A'a, tayi murmushi tana dan kallon gefen Nafisan tace "Munayi Mami"
Faruk ne ya shigo cikin qananun kaya bai dade da dawowa daga gurin aiki ba, ya zauna nan falon shima, bayan sun gaisa Nafisa tace "Yaya kaji wai daddawa Mami zata bamu mu sa cikin kaya mutafi dashi" Faruk ya danyi dariya yace "Daddawa kuma?" Na'ima tayi murmushi, sai Mami tace "Ni tambayata anan shine, basa dafa tuwo ne ko me?" Faruk yace "Mami inkinga fridge din yaran nan da naje last time, inaga sai kin kai hannu a kowaccensu, fast food kawai suke dirkawa cikinsu" Mami ta dan bude baki sai ta juya ta kalli Na'ima tace "Harda ke Habibti? naga kuma tuwon yana cikin favorite dishes dinki" Na'ima tayi saurin gyada kanta tace "Allah Mami muna dafawa time to time, amma miyan ganye" sai Mami ta kada kai tace "Ya muku kyau, nasan kuma Baby ce shugaba, da Abban ku ya siya muku mota kurinqa uzurirrika da ita bakwa zuwa shopping na kayan abincin ne ko me?" Nafisa tace "Wallahi muna zuwa shopping din Mami" Mami ta harareta tace "Na kayan kwalliya da fata ba, my friend shut up, kin wani maka leda a fuska" Faruk dake zaune ya kada kai shima yana murmushi sai Nafisa takai hannu tana gyara facial mask din nata tana dan dariya itama, Mami ta sake kallon Na'ima tace "Na'ima ku rinka yin abinci me kyau kunaci banason zama da yunwa, ko baby bataje siyo kayan ba ke kirinqa zuwa kina siyowa inyaso in kin dafa ma karki bata" Nafisa tayi dariya tace "Na'ima sarkin karatun kike bawa saqon nan Mami" Mami tace "Nidai na fada muku, meye kuma na rayuwa da fast food da lafiyanku da komai ku ba kutare ba, banason haka kuna jina ?" suka amsa da "Toh" sai Mami tace da Faruk "Kuma fa tsaf nake hadawa Al'ameen daddawan in qulle masa ya tafi da ita Toronto baya wani zancen wari" Faruk yace "Al'ameen kikace Mami ba mai bakin rezan nan ba" Nafisa da Na'ima suka kama dariya...
Ana gobe zasu tafi Na'ima na tsaye gaban madubi a dakin Nafisan tana tattare mata mayukan da zata koma dasu, wasu oil ta dauka ta juya gurin Nafisa dake zaune kan gado hannunta da waya, tace "Zaki koma da wannan?" Nafisa ta dago kai ta kalle ta tace "A'a inada irin wannan acan" sai ta maida kanta kan wayan ta cigaba da dannawa.
Deban wasu mayukan Na'ima tayi a hannunta ta nufi gurin akwatin Nafisan da take mata arranging kayan aciki tace "Har zamu koma baki hadu da Umar ba Nafee, meya faru ne?" Nafisa ta ajiye wayan hannunta tana kallon Na'iman tace "We broke up since" Na'ima na arranging kayan cikin akwati ta dago kai ta kalleta tace "You're taking a break dai, ba dai break up ba" Nafisa ta gyada kafada tace "Dagaske I'm done with that guy kuma, i need my sanity, it's high time infara prioritizing peace of mind dina nima" Na'ima dai sai kallonta take sanin it's a big decision for her, aranta tana ayyano yanda Nafisan keda kyau, gata, kudi amma sai Allah bai sa mata sa'a akan soyayya ba, namijin da bai kai ba yake juya zuciyar kawartata son ransa.. Miqewa tayi ta zauna kusada Nafisan cikin kwantar da murya tace "But are you okay with this decision?" Nafisa ta gyada kai tace "Tunda mukayi fadan nan nayi blocking dinsa, he makes no efforts akan gyara relationship din, zanyi ta bata lokaci na ne akan someone that will not make effort to have me neh Naima?" sai Na'ima tadan riqe hannunta tace "It's okay...Ina bayan duk abunda kikeso ko kikayi deciding..in Umar ba alkhairy bane a cikin rayuwanki a sannu Allah zai kawo wanda yafishi, the one that will make the most effort to love you earnestly" Nafisa tayi murmushi tana riqe da hannun Na'iman tace "Thank you sis, you know I'm grateful to have you in my life right?" Na'ima tayi murmushi tace "Me too Nafee" sai ta miqe ta kama kunkumi tafara bin dakin da kallo tace "Saura me kuma zan hada miki, banason sai mun koma ki fara mitan bakiga wasu abubuwanki ba" Nafisa tayi 'yar dariya ta koma ta kwanta tace "Toh mummy Na'ima,nkin sakamin inner wears din" Na'ima ta gyada kai ta sake komawa bakin madubi tana duban ko akwai abunda zata qara dauka...
Washegari ya kasance flight din sha dayan safe garesu, dawuri suka tashi kasancewan Na'ima anan dakin Nafisan ta kwana yasa bayan sun idarda sallah suka wuce dakin Mami tare.
Zaune suka sameta kan sallaya dan yawanci in Abba yatafi masallaci ita dakinta take dawowa tayi nata sallan..bayan sun gaisa Mami tace "Kun gama shirya kayan naku dai ko, dan banason mantuwa" Na'ima tace "Eh Mami in sha Allah" nan suka zauna tare da Mamin sukayi azhkar dinsu da karatun qur'ani, Mami na musu nasiha akan makarantan dazasu koma.....Karfe goma saura suka shiga falon Abba, sun sameshi zaune kan kujera hannunsa riqe da cup din tea yana hira ya samarin gidan, Na'ima ce ta fara zama a qasa nan kan carpet sannan Nafisa ta bi bayanta suka gaishe da Abban, yana murmushi ya amsa gaisuwan sannan yace "Yaran Abba kun shirya ko" suka amsa a sanyaye, Abba ya sake cewa "Toh, Allah ya kaiku lafiya, Allah ya bada sa'an karatu" suka amsa da Amin, Abba ya cigaba.."Banason wasa, ku maida hankali akan ibadunku da karatu, I'm very proud of how hard kuke maida hankali ga karatun amma ku qara himma, sannan a batun ibada kuma nasan indai akan tarbiyan da muka baku ne banida haufi akan kuna maida hankali, Amma tunda ba'a gabanmu kuke ba inason kuji tsoron Allah ku maida hankali akan sallolinku, Allah ya muku albarka.. we'll surely missed you" kasa amsawa Nafisa tayi ta miqe ta qarasa gurin Abban tafara kuka tana riqe hannunsa, ajiye tea cup din yayi ya bude mata hannunsa ta fada jikinsa tana kuka, yana dan bubbuga bayanta yace "Saura kadan ai daughter, besides zamuzo celebrating gamawanku ai" , idon Na'ima itama ya kawo hawaye tananan zaunen, Mami dake zaune kan kujera a gefe ta bude nata hannun tace "Zo Habibti" tashi Na'ima tayi ta qarasa gurin Mamin itama ta shige jikinta tana hawaye, barin jikin Abba Nafisa tayi ta koma jikin Mami itama tana sake wani kukan, Al'ameen da Abubakar suka koma gurin Mamin suka tsaya jikinsu duk yayi sanyi, Faruk yace "Kukan nan ya isa ku tashi mutafi kafin lokaci ya qure" suka dago daga jikin Mamin tana goge musu hawayen tace "Saura kadan fa yarana, ku maida hankali kunji, sannan ko menene yafaru ku kiramu, it's just a call away" suka amsa da "Toh Mami".
Haka su Na'ima sukayi sallama da iyayen nasu cikin sanyin jiki, Faruk ya tisa qeyarsu mota, maigadin gidan ne ya qaraso ya taya su Al'ameen saka kayansu a booth, tare suka tafi dasu Abubakar airport din suka bar Mamin da Abba nan tsaye bakin entrance din gidan suna daga musu hannu cikin sanyin jiki.
Zaune suke a waiting lounge na Airport din suna jiran lokacin tashin jirginsu yayi, Nafisa tace "Abu please siyo mana abun tabawa, banason zaman shiru" miqewa Abubakar yayi ta sake cewa "Iced coffee please" ya tambayeta flavor din da takeso ta fada masa sai ya juya gurin Na'ima itama ta fada masa kalan wanda takeso, miqewa Al'ameen yayi suka tafi siyowa tare.
Sunanan zaune Na'ima ta hango shigowar su Ahmad gurin shida Adam kafadarsa rataye da jaka while Adam jaye da qaramin akwati, sai Laila dake biye dasu itama, kauda kai Na'ima tayi daga kallonsu,
Faruk ne ya fara miqewa ya isa wajensun yana miqa musu hannu sukayi musabaha sannan su Na'iman suka miqe suma, Nafisa tace "Ita kuma wannan me kama da mayun ko meye na biyosu airport oho" Na'ima na jinta bata ce komai ba suka qarasa wajen da su Ahmad din suke tsaye, gaishesu sukayi Ahmad ya amsa yana kallon Na'ima wadda itama yau tayi nata jarumtar ta kallesa, amma baifi na few seconds ba ta dauke idonta jin yanayinta na canjawa sai ta juya tana kallon Laila dake kallonta itama, samun kanta tayi da qin saka mata gaisuwa ta kuma dauke kai... Adam yace "Yan makaranta, za'a koma kenan" Nafisa tace "Wallahi kuwa Yaya, kuma London din zaku je ne?" Adam ya nuna Ahmad daya maida hankalinsa kan waya yace "Ga mai tafiyan nan ai" Nafisa ta kalli Ahmad tace "Ashe flight dinmu daya Yaya" sai Ahmad ya dago kansa daga danna wayan, cikin nutsuwa yace "It seems so..kuma flight din 11 dinne?" Nafisa ta gyada kai tace "Eh" sannan ta juya ta na kallon Laila, in a mocking way tace "Hajiya Laila..kema London din kika nufa ne?" A daqile Laila tace "A'a" tana dan qara matsawa kusa da Ahmad, Na'ima na kallonsu... kallonta Ahmad yayi suka hada ido sai taga yadan matsa daga kusa da Laila still bai daina kallon idanunta ba, Na'ima ta kauda kanta jin zuciyarta namata wani iri sai ta koma kallon mutanen dake zirga zirga acikin Airport din.
Su Abubakar ne suka qaraso wajen hannunsu riqe da iced coffee din, Adam yace "Wannan kuma fa, nasu waye?" kafin Nafisa ta karba sai Laila ta rigata miqa hannu ta karbi duka cups biyun dake hannun Abubakar tace "Abunda naketa craving this days..thanks" Nafisa ta dan harari Lailan sannan ta karbi na hannun Al'ameen, Abubakar ne yace "Anty Laila ki riqe nawan amma vanilla flavor din na Anty Na'ima ne" Laila tace "Oh sorry" tareda miqawa Na'iman, sai Na'ima ta miqa hannu amma kafin ta karba Laila ta sake mata shi a jikin ta, nan iced coffee din ya kware gaba daya a jikin brown abayan Na'ima, baya tayi da sauri tace "Bismillah" ta riqe daidai gurin da ya zuban gashi har gyalenta ya taba, Faruk ya taka zai je gurinta sai ganin Ahmad yayi ya rigashi isa, kowa daskarewa yayi nan tsaye, Ahmad ya kamo dan bakin gyalen nata daidai inda shima ya tabun, cikin kwantar da murya yace "Are you Okay?" gyada kai kawai Na'ima tayi, sai Ahmad ya juyo ransa adan bace yace da Laila "Are you blind?" Laila ta wani juya kai tace "To ai bansani ba" Nafisa ta harareta sannan ta isa gurin Na'iman ta ciro hanky daga jakanta dake sakale a kafadanta ta fara goge mata jikin rigan..Sai sannan su Abubakar suka nufi gurin Na'ima suna mata sannu, Faruk dai na tsaye shida Adam.
Adam sai kallon abokin nasa yake da dan mamaki, Nafisa na goge wa Na'iman jiki tace "Muje restroom a dan wanke" ta kalli Ahmad tace "Yaya bari muje restroom kawai" Gyada kai Ahmad yayi ya sake bakin gyalen Na'ima suka wuce, Laila kaman ta fashe haka taji a wannan moment din, bata taba zaton Ahmad din zai nufi gurin Na'ima ba, atake abubuwa dayawa suka darsu mata acikin rai.....