AMNA DA SAFNA

Part 3-4

by @zahratulqalam51

بسم الله الرحمن الرحيم

اللَّهُمَّ صَلِّ وَ سَلِّمْ عَلَى نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ.

🖤AMNA DA SAFNA🖤

Part 0️⃣3️⃣▶️0️⃣4️⃣

📲 writing ✍🏼

Aisha G Umar

🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️

Ƴar harara Safna tayi mata ta ce, "nice miskila?" Dariya Raheena tayi, sannan ta ce "sorry my besty, yanzu dai muje ko." Murmushi kawai Safna tayi mata tana cigaba da tafiya, bin bayan ta tayi, suka jera suna cigaba da tafiya. Raheena ce takara faɗin "Besty ya lecture ɗin yau, wallahi ya cazamin brain sosai," hararan ta Safna ta ƙarayi akaro na biyu. "shiyasa kika manta dashi kika samu gurin surutu ai"

Raheena ta ce, "bama wannan ba ina zamu gida ne?" Karamar ajjiyar zuciya Safna ta sauke sannan ta ce "a ina kuwa zamu gida inba a adaidaita-sahu ba, hmm ni bansan lokacin da zaki zama mai ƴanci a gidan ku ba, mahaifin ki mai kuɗi amma yadda talakawa suke rayuwa haka kema kikeyi Safna"

murmushi mai ciwo Safna tayi daga bisani tac e, "Raheena kenan, kin riga da kin san komai ni ba kowa bace a gidan mu, Dady ne kawai mutumin dake ganin darajar mu, daga ni har Ammu na, itama da kanta tana buƙatan kulawa". Tafaɗi daidai fitowar su daga cikin makarantar. Raheena ta dafa ta haɗi da faɗin "hakane ƙawata ubangiji Allah yaba Ammu lafiya". "Ameen" suka ambata a tare.Taran adaidaita-sahu sukayi suka shiga.

Kafinsu zama ƙawaye an ɗau lokaci, domin Safna ta ɗauki Raheena me yawan surutu, da suka fahimci juna sai suka zama aminan juna na ƙwarai. Duk da Raheena bata iya zama shiru da Safna, haka za tayi ta zuba. Wani lokaci ta amsa mata ɗadɗaya. Ko kuma ta ce mata "uhmm ko a'a".

Daidai lokacin da aka kira Sallah. Safna aka fara saukewa a layinsu first GRA, sallama sukayi cike da kewan juna sai gobe kuma.

Tafiyarta tacigaba dayi cikin nutsuwa har izuwa ƙerarren gidan da ya ƙara shan gyara, ya ƙara haɗuwa fiye da da. ƙwanƙwasa wa ta fara, babu ɓata lokaci mai gadi ya buɗe gate ɗin.

Da murmushi à fiskarta ta gaishe da tsohon mai suna Hambali cikin ladabi. Shima amsawa yayi cikin fara a. Yarinyar tana da tarbiyya mai kyau, ita kaɗaice cikin yaran gidan take ganin darajar shi, sauran kuwa ko sannu basa ce masa, sai dai ma subishi da masifa inbai buɗe musu ƙofa yayin fita ko shigar da motan su ba, duk da tsoho ne shi, shiyasa yake bin Safna da fatan alkhairi a rayuwar ta.

Komawa gurin zamansa yayi, yayinda ita kuma ta nufi hanyar shiga ciki. Shigarta ƙayataccen falon keda wuya sai ji tayi an fincikota, gabaɗaya takardun dake hannunta suka zube, ɗaga ido tayi cikin firgita, tana duban wanda yayi mata wannan abu.

"Dama nace zaki dawo kisameni, wato harni zance ki kawomin tea da safe amma kiyi wucewanki saboda kin isa ko?" Ya ƙarasa faɗi yana saketa ƙasa, cikin firgita ta ce, "Yaya Marwan wallahi sai da na kawo maka before na tafi" tafaɗi da rawar murya. Zainab wacche suke kira da Hajiya ta sauko daga upstair, ƙarasowa inda muke tayi, da harara ta bini sannan ta ce, "Rabu da ita wurine ta samu saboda na ƙyaleta tana zuwa makarantar shiyasa, tana abinda takeso". Marwan yace "Hajiya nunawa take tafi kowa son makaranta, ko Ruki bata mai da hankali kamar yadda wawuyar nan takeyi, ince ta kaimin tea amma sai zuwa nayi naga cup emty". "Rabu da ita makarantar zan sa tabari, danni na daɗe da son ta bar zuwa, ta dawo aikin gida" hajiya tafaɗi haka.

"Ya Allah" Safna tafaɗi a zuciyarta, a fili kuwa ta ce,

"Wallahi na kai ban san wanda yasha ba", ɗakinsa ya wuce, hajiya kuma ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon. Batare da sun saurareta ba, kwashe takardun ta tayi, jiki a sanyaye ta nufi gefen ɗakin su. Tana share ƙananun hawayen da suka fito daga manyan idon ta.

Buɗe ƙofar tayi da sallama ta isa ciki. Tarar da Ammunta tayi zaune akan garduma da alama sallar La'asar ta idar, ajiye littafan hannunta da gyalenta tayi a kujerar dake ɗakin, sannan ta ƙaraso gun farincikinta, durƙusawa a gabanta tayi, hawayen da bataso fitan suba suka fara zubowa, Kwantar da kanta tayi a kan ƙafar Ammu, Ammun ma binta tayi da kallo cikin tausayawa, a hankali ta ɗaura hannunta a saman kan Safnan saboda yana yin jikinta,

"Meyasa hakan, ke faruwa da mu?, Shin ko munyiwa su Hajiya laifine, shiyasa suke yimana haka, Dady ne kawai ke sonmu?" Ta ƙarasa faɗi haɗi da matso ƙwallan da yacika mata idonta. Da ƙyar Ammu ta fara share mata hawaye, tana mai jin zafi a ranta, akan duk abinda ke faruwa, amma babu yadda ta iya.

Ganin hawaye yafara zuba daga idon mahaifiyar ta, tayi saurin ta shi cikin damuwa, hannu tasa ta share mata hawayen tana girgiza kai "no my Ammu don't cry, banaso inganki cikin damuwa bare inga hawayen ki. Bazan iya juran gani ba". Ta ƙarasa faɗi tana rungumeta.

Taimaka mata tayi ta kwantar da ita a kan gado. Ta ce, "Ammu bari inyi sallah sai inkawo miki abinci nasan kinajin yunwa," ta wuce toilet dan yin alwala.

Daddy na ɗawainiya da su iya ƙoƙarinsa. Ita kaɗai ce ke kula da mahaifiyar ta sosai. Babu me leƙo Ammu yaga ya take idan bata nan. Bayan masu gadi biyu da kuma masu gyaran flowers. Akwai masu girki huɗu, masu wanki mata biyu maza biyu. Sannan sai masu shara da goge-goge. Duk kansu kuma suna da ɗakunan su, amma fa Safna ko Ammu basu da iko dasu, iyaka dai Hajiya da 'ya'yanta kaɗai suke da iko akansu.

Bayan ta idar sallah kitchen ta nufa, saidai bata samu komi ba, illa jalof na taliya, ɗiba tayi a plate tayo ɗakin da shi, taso da Ammu tayi, ƙoƙarin kaimata tayi a baki amma ta kauda kai , idon Ammun ta gani sannan ta ce, "Nasan baki cika son spaghetti ba Ammu, amma ki daure kici saboda na sani kinajin yunwa."

Ƙara kau da kai tayi akaro na biyu, ajiye plate ɗin Safna tayi akan drawern gefen gado ta miƙe haɗi da faɗin "to bari inje na samo miki wani abun"

"A a Ammu bazan ɗaɗe ba, zan dafa mana ko kuskus ne, kin san bazan iya cin abinci ba in ke bakici ba" taƙara faɗi bayan taga idon Ammun nata,tsawon shekarun da tayi da mahaifiyar ta a haka, tana iya fahimtar abunda take ƙoƙarin faɗi ta ido, wucewa tayi don dafawa Ammu kuskus.

Bari mu leƙa garin Gombe.

Kyakykyawa ce na hango cikin wani Ƙaton shopping mai suna Haleem shoprite, tana matsakaicin tsawo, sannan kuma fara ce, wajen launin fata, ga shi tana da karan hanci sosai, wannan yasa ake mata laƙabi da wanke hannu kataɓa kawai. Manyan idanunta farare tas tas, glass ta sanya wanda yasa har ba a iya ganin kwayar idanunta, don baza kace idonta nada wani launi ba inka ganta. Sanye take da kayan kanti riga da wando, irin dogin rigunan da ake kiransu da gown, blue colour ta sanya, wacce ta sauƙa mata har gwiwar ta, sannan ta yafa ɗan gyalenta milk colour, wanda yazo dai dai colour ɗaya da flate shoes ɗinta. Ya nayin haɗuwarta da shigarta sai tabarkallah kawai.

Tsaye take agurin biyan kuɗi bayan ta zaɓo takalma black and red. Wani ɗan saurayi ne a gefenta da shekarunsu zai iya zuwa kusan ɗaya. Amma sai dai ɗan ɗara ta tsawo kaɗan. Shima kyakykyawa ne, Kusan 30 minute suke tsaye a gurin ga layin mutanen da ta tara a bayanta, akan takalma ɗaya da ta keson zaɓa tsakanin baƙi da ja.

Kallonta saurayin yayi cike da takaici yace "ke nifa nagaji haba, da yanzu ina gida ina cin daddaɗan girkin Ummee, amma kin jawoni nan tin ɗazu kina abu ɗaya, dan Allah kisai takalmin nan mu wuce, duba bayan ki fa mutane ne ke jira"

hararansa tayi, sannan ta juya ta dubi mutanen da suma cike suke da ita, taƙara juyowa ta dubeshi ta ce, "dama ba ce maka nayi kawuce ka ƙyaleni ba, harda cewa ƙafa ta-ƙafar ki, to ma mutum da kuɗinsa bazai zaɓa ya darje ba, ha'a" ta ƙarasa faɗi tana tattaɓe baƙin takalmin, Inta ɗaga jan sai ta girgiza kai, "a'a kamar wancan yafi kyau" sai ta ɗaga baƙi kuma.

"To ki zaɓa ɗin mana, kuma da kike cewa nace ƙafa ta-ƙafar ki ai kinsan wannan tsohuwar, dana koma ba tare da keba zata hanani sukuni", tafara faɗin, "kai Mubaraka ina kabaro min jika ta Aminatu, saboda Allah kataho kabar yarinyar da babu ruwan ta, in wani abu yasa meta fa, haka zatai ta min sababi, Mubarak ɗin ma bata iya faɗi in tana masifa sai ta kirani da sunan mace wai Mubaraka".

Bata tanka masa ba sai ma cigaba da abinda take tayi, gyaran murya yayi da alama ma shi ake biyan kuɗin a wurinsa, ɗago idanun ta dake cikin glashi tayi tana duban sa, shima kallonta yayi sannan yace "biwar Allah me kike nema ne anan, akan takalma biyu kike wasting time ɗin mutane, inba siya zakiyi ba kiba mutane wuri".

Kamar zata cire glass ɗin sai kuma ta fasa sannan ta ce, "kaga malam kuɗi zan bada fa, ko so kake in siya takalmin da bai da lasting, toma tinda bason ciniki kukeyi ba nafasa siya, ku sayar a wani" ta ajiye takalmin, tayi fitowar ta, take mutanen wurin suka hau surutu, haƙuri Mubarak ya basu, sannan ya biyota yana faɗin.

"Amma ke Amna ko, yanzu duk wasting time ɗin da mukayi ba ki siya komi ba". "Dama ce maka akayi siya zanyi?" ta furta hakan tana kwashewa da dariya. Yace "what me kike nufi, ba cemin kikayi kintara wasu kuɗi ba?" Amina ta ce, "ba wani kuɗin da natara, ƙure ƙaryan me ƙarya nayi, Zubi ce ke cewa "ai Haleem shoprite na manyan masu kuɗi ne, waini takewa bagu, shine nace yau zanzo in ƙure ƙarya"

Yace "wato shiyasa ta biyoki kenan?" "eh mana ba kaga tana ganin abin bana ƙare bane ta ware" ta kuma kwashewa da dariya. dariya yayi shima yace "kuma wai a haka mamma take cewa ba ruwanki, duk abinda zan faɗa mata sai taki yarda", Amina ta ce "kai kuma gashi baƙin ciki kakeji in ta faɗi hakan ba mai gulma" tafaɗi tana ɗan sa gudu-gudu, shima bin bayan ta yayi yana faɗin "nine magulmaci?"

🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️