💔NAUYIN BAKI👄💔 Na Uwar Batoorl
Page 19 _ 20
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
WANNAN SHAFI NAKI NE
Hafsat Umar.
🅿️ 19 _ 20
⭐️
Sadeeq ko da ya ji tayi shiru, kuma yana iya jiyo sautin numfashinta alaman ba wai ƙiran ya katse bane, sai ya busar da iska mai ɗumi a bakinshi, gani yake kamar laifi ya mata tayi shiru, may be ta fara fahimtan zai rusa mata farin cikinta ne, ko may be yanda yayi magana ya mata ba daɗi, sassauta muryarshi ya yi sosai yayi ƙasa sosai, kamar mai raɗa ya ce, "Fatan kina lafiya?"
Maganar Sadeeq shi ya dawo da Sadiya hayyacinta daga duniyar shauƙin yadda ya ƙira sunanta, murmushi ne ya yalwata sosai a fiskarta duk da yana ɗauke ne da rauni na tausayinshi da kewarshi, siririyar muryarta ta kwantar tare da cewa, "Alhamdulillah Yaayaana, fatan kai ma jikin ka da sauƙi?"
"Na ji sauƙi sosai Sa'adiyah", ya faɗi yana murmushi mara sauti wanda ya fi kuka ciwo, domin ya san sauƙin dai na farkawanshi ne, bayan farkawanshi ba wani sauƙi da yake ji a zuciyarshi game da ita.
"Alhamdulillahi ala kulli halin, mun gode wa Allah Yaayaana, naji daɗi sosai da kaji sauƙi, kuma na ji yanzu na nitsu, amma dai duk da haka ka dawo gida da wuri, ba za a barni na sake zuwa asibiti ba, kuma ba zan ji na nitsu sosai ba muddin ba ganinka nayi ana komai da kai ba, Yaayaana kai ne duniyata kai ne komai na, na fi jin ka a rai fiye da Yaya Umar wallahi, kwata-kwata ni bana son komai ya same ka, da kayi ciwo gwanda ma a ce ni nayi ya fi mini, dan Allah ka dawo gida Yaayaana, ina kewarka duk gidan ba daɗi."
Maganganun Sadiya daɗa ƙara karya wa Sadeeq zuciya suke bata sani ba, sosai maganganunta ke raunata mishi zuciya, wani irin abu yake ji yana kekketa mishi zuciya, muddin ya cigaba da sauraran Sadiya, rauninsa zai fito fili, ba zai iya cigaba da danne zuciyarshi ba, murya a ɗan dake ya ce, "It's my time to sleep, goodnight koh."
Idanuwan Sadiya ne suka ciko da ƙwalla, bata gaji da jin muryarshi ba, bata gaji da ƙiran sunanta da ya ke yi ya mata daɗi fiye da kowa ba, kai ita so take ma tayi turning phone call ɗin in to video call, tana son ta kalleshi, suyi hira sosai, ya bata labari ya sanyata dariya, tana da tabbacin indai Yaya Sadeeq zai yi haka to a yau za ta warke ta ji ƙarfin jikinta, cikin muryan rauni mai nuni da tana daf da fashe mishi da kuka ta ce, "Yaayaana!."
Sadeeq daga muryan Sadiya ya fahimci me take shirin yi, hakan ya sanya ya katse ƙiran ba tare da ya kuma ce mata komai ba, dole ya koya wa kanshi haƙuri da Sadiya, in ya cigaba da saurararta, to komai na gaf da faruwa.
Khalid da sauri ya taso ya ƙaraso ya amshi wayarshi da Sadeeq ke miƙa mishi, sannan ya koma gefen Umar ya zauna yana jin ya sauƙe nauyin alƙawarin da ya mata.
"Da wa yayi waya?", Umar ne ya jeho wa Khalid tambayar, idanuwanshi na a kan nashi wayar.
"Sadiya ce Yaya Umar."
Girar sama da ta ƙasa Umar ya haɗe tare da aika wa Khalid mugun kallo, ya ɗaura da cewa, "Wa ya baka go ahead ɗin haɗa su a waya?"
"Afuwan Yaya Umar, wallahi duk ta ban tausayi ne, kuma na yi alƙawari shiyasa."
"Next time ka kuma haɗa su a waya, ni da kai ne."
"Ba za a kuma ba babban Yaya."
Daga haka Khalid ya gyara yayi kwanciyarshi, Umar kuma ya cigaba da abinda yake yi a wayarshi.
Shiru-shiru har lokaci ya ja sosai, Khalid har yayi bacci saboda gajiyar da ke a tare da shi, a ɓangaren Sadeeq ma baccin ne ya fara fisgarshi, saboda shiru da yanayin jikin, kuma cikin magungunan shi akwai na bacci.
Umar sai da ya kammala duk abinda yake, sannan ya kulle datar shi yana mai kallon lokaci, wanda ke nuni da sha ɗaya saura, dare yayi sosai bai farga ba, locking na wayar yayi sannan ya sanya a aljihu ya miƙe daga bakin gadon ya ƙarasa gaban gadon da Sadeeq ke kwance, plastic chair ya jawo kusa da gadon sosai sannan ya zauna, cikin muryar da ke nuni da dukka hankalinshi na ga Sadeeq, kuma magana yake so su yi mai muhimmanci, ya ce, "I guess you're not off right?"
Sadeeq sarai baccin bai tafi da shi ba tukunna, tun motsawan Umar yana jin shi har yayi magana, bai bawa Umar amsa ba, domin bai da niyar bayarwa, sai haɗe fiskarshi da yayi.
Umar ya fahimci sarai idon Sadeeq biyu tunda ya zauna, saboda daga yanayin numfashin da yake yi, it doesn't sound like for someone who's asleep.
"Nasan idonka biyu, so kawai malam ka tashi muyi magana, dan in baka son kanka da lafiyarka to mu muna sonka muna son lafiyarka."
Gajeren tsaki Sadeeq ya ja saboda baccin da ya fara fisgarshi, ga Umar na son ƙara mishi ciwon kai akan na zuciya, a ƙufule ya ce, "Me damuwarka da ni? Waya ce taka kuma ka amsa sai dai hakan ai bai hana ni waya da ita ba, duka kuma in ka fasa taɓa ta, kai ka san ciwo ba zai hanani rama mata ba."
Guntun murmushi Umar yayi mara sauti tare da cewa, "Next time ko su Abba ba zan bari su haɗa ka da shirmammiyar nan ba."
"You should stop me from going to home idan aka yi discharge na, that'll be better dan haka ne kawai za ka samu abinda kake so."
"Ko ban hana ka komawa gida ba, ai nan da kwanaki za ta koma wani gidan."
Wani irin dogon tsaki Sadeeq ya ja a mugun ƙufule cike da kishi da haushin Umar, dan ji yake kaman da gangan Umar ke faɗa mishi wannan magana, kai ba Umar kawai ba, gani yake duk wanda zai yi maganar auren Sadiya a gabanshi to da gayya yake yi, da gangan ake so a ƙarasa kassara mishi zuciya, "Hmmn!", ya faɗi kawai, da kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, sai sake tamke fiska da yayi ya lumshe ido, yana neman bacci yayi gaba da shi tun kamun zuciyarshi ta kai bango, ya saki layi a gaban Umar, wanda kuma ba ya fatan haka, soyayyar Sadiya sirrin shi ne, and he'll keep on hiding it, saboda ta samu farin cikinta, he sacrifice his own happiness for her, yana mata fatan kasancewa cikin farin ciki da abinda take so.
Umar murmushi ya saki mai zurfi da sauti, saboda yana noticing wani abu ne wanda yake son gano wa, duk da abun dai ƙara ɗaure mishi kai yake, murya a sake ba yabo ba fallasa ya ce, "Barin kashi a ciki baya maganin yunwa, you better utter what's in you than ka ta humming kai ba mai naƙuda ba."
Sadeeq banza ya kuma yi da Umar, hakan ya sanya Umar ya ce, "Sannan maganar duka sai na kirɓa Sadiya, keep this on back of your mind, I'll make very sure that i deal with her, tana hauka ne za ta dinga yiwa mutane shiririta da yaranta, muna fama da addu'a ka warke sannan ta ke mayar wa mutane aiki baya, to in ka ji labarin na zane ta kayi zuciya ka warke ka dawo gida ka rama mata, I'll be very happy dan mun kwana biyu bamu gwada ƙwanji ba, sai naga da sauranka ko kuma ka zama rabi da rabi."
"Indai ba a gode mata ba ai ba za a zane ta ko a dake ta ba, batun gwada ƙwanji kuma you should try me and see."
"A gode mata a kan me? Akan shirme ko shiririta ko rashin hankali?"
"Duk wanda ka zaɓa, dan naga dai ni ta dama ba kai ba, kai ai ba ka da damuwa da hakan", faɗin Sadeeq cikin jin haushi, ga Umar ya tasa shi gaba da maganganun banza, kuma dama ko da ba zai yi surutu da kowa ba, to banda Aminin shi Umar, ko Sadiya, su yana iya wuni ya kwana magana da su ba tare da ya gaji ba.
Umar murmushin da shi kaɗai ya san ma'anarshi ya kuma saki sannan ya ce, "Ni kuwa nake da damuwa."
"Your problem is your problem, am not concern and i don't mind", faɗin Sadeeq yana taɓe baki saboda haushin Umar.
Ɗage kafaɗa Umar yayi irin ko kaɗan abinda Sadeeq ya ce bai dame shi ba, sannan ya ce, "Damuwana kai ne bro, kai ne damuwana wallahi, you were painted and unconscious, in ba dan Allah ya kiyaye ba, wa yasan abinda zai faru, kasan irin damuwan da muka shiga? Umma, Abba, Mama, Sa'ad da Khalid, dan ma an ɓoye wa Khausar, kai ka san da yanzu haka tana a asibitin nan tare da mu, duk da su Abba basu tambayeni akan abinda ke damunka ba, amma na tabbata suna mini kallon na san abinda ya faɗar da kai, i never expect this from you, wai ka ɓoye mini wani abu yana damunka, abinda har zai sa ka faɗi kaman mara numfashi a tattare da shi, i think there's no secret between us, ka san komai nawa na san komai naka, ashe am wrong, na fahimceka bai bai, yanda na ɗaukeka ba haka ka ɗauke ni ba, this is the last thing i never ever expect from you Sadeeq", Umar ya ƙarishe maganar cikin sautin da ke tabbatar da maƙurar rashin jin daɗin abinda Sadeeq ya mishi.
"Huh, ita ɗin da baka sako sunanta ba bata damu bane? Ko ita ba mutum ba ce? Umar meyasa kake wa Sadiya haka? Ƙanwarmu ce fa tana da wasu bayan mu ne?", Sadeeq ya faɗi cikin son kawar da maganan Umar, saboda tabbas Umar gaskiya ya faɗa, amma ya san sai ran Umar ya fi haka ɓacci muddin ya ji gaskiya, gaskiyanma wai na son Sadiya da ke a zuciyarshi, kuma ya ji daga lokacin da ya fara son ta.
Umar murmushi guntu yayi, na ganin yanda Sadeeq ke cigaba da son shashantar da shi, ba tare da damuwar komai ba ya ce, "Sadiya ba a lissafata a jerin mutane, and soon za ta samu wasu bayanmu, tana aure shikkenan kuma an wuce wajan, so in za ka faɗa mini abinda na tambaya ka faɗa mini kawai ka bar yi mini corner, me ke damunka? Menene damuwarka? Me kake so? Me kake ɓoye mana? Kai ne baka da kowa bayan mu, idan ka faɗa mana komai, we'll help and support you, ko da kuwa financially support ne, in kuma da addu'a ne we'll pray for u also, idan kuma muna da right akan abinda kake buƙata za mu samar maka da abin muddin bai fi ƙarfinmu ba, ko kuwa baj saɓa wa addini ba."
Maganganun Umar sun taɓa Sadeeq sosai, ya ji kaman ya faɗa abinda ke a ranshi, amma ba zai iya ba, ba zai taɓa faɗa ba, asali ma maganar Sadiya za ta yi aure ta samu wasu family, sake dulmiya mishi zuciya yayi cikin kogin ciwo da raunin rasa ta.
Daga haka duk abinda Umar ya kuma faɗa, Sadeeq bai ce komai ba, har Umar ya gaji ya tashi ya wuce ya je ya kwanta, Sadeeq ma ba jimawa bacci yayi gaba da shi.
Washe-gari bayan duk sun yi sallahn asuba, Umar ya ce da Khalid ya zauna wajan Sadeeq ɗin, shi zai je gida zai ya shirya, da kansa yau zai je wajan aikinsu, Khalid dan murna kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, dan da gaske yake ayyukan nan za su margaya shi, cikin jin daɗi ya ce, "Sai da kai Yaya Umar, a dawo lafiya, ina nan asibiti in ma ka ce kar na leƙa gida, to ba zan leƙa ba ina nan a asibiti."
Umar guntun murmushi yayi ya ce, "Allah ya shiryaka Khalid, idan Abba ya maka auren za mu ga wanda zai ke making kuɗi ya kular maka da matar da yaran da za ta haifa."
Jinjina kai Khalid yayi tare da cewa, "Abba, ai Abba ne ma zai ciyar da mu daga ni har ita har jikokinshi, ai ni cima zaune ne wallahi, ɗan zaman kashe trouser, in dai har aka mini aure a haka ai sai Abba ya ciyar da mu, ku ma da kuka goyawa Abba baya, sai kuke mana kayan sallah, maganan outing, kuɗin kashewa da sauransu, har Yaya Sa'ad sai yayi hidima da mu, Umma da Mama da Aunty Khausar da Sadiya kawai za mu ɗaga wa ƙafa, tun da su ma sai an basu suke samu."
Umar girgiza kai yayi yana ƴar dariya ya ce, "Allah ya taro ka, nikam na wuce ka kula sosai", yana gama faɗin haka ya juya ya fice ba tare da ya ce da Sadeeq komai ba, dan tun jiya da suka yi magana, to yau tun bayan gaisuwan da suka yi ya tambayeshi ya jikinshi, to bai sake mishi magana ba.
⭐️
RAYFIELD
SADIYA POV
***
Sadiya tana jin alamar Sadeeq ya katse ƙiran sai ta aje wayar, hawayene masu ɗumi suka fara zirya a kumatunta, ba ta ko tantama Yaya Umar ne amshi wayan ya datse ƙiran, "Ya ake so nayi da rayuwata?" Ta faɗa cikin karyayyiyar murya, mai nuni da rashin daɗin da take ji a zuciyarta.
Umma da ke tsaye tun shigowarta ta zuba wa Sadiya ido ta kuma kasa ƙarasowa ta zauna, sabboda tausayin Sadiya da kuma Sadeeq, dan ta fahimci da Sadeeq Sadiya ke waya, jin abinda Sadiya ta faɗi ne bayan ta dire wayan, ya sanya Umma ƙarasowa tana faɗin, "Ke da wa auta? Wa ya taɓa mini ke?"
Sadiya kwantar da kanta tayi a kafaɗan Umma da ta zauna a gefenta, cikin muryar kuka da sheshsheƙa ta ce, "Umma ba fa ni na ɗaura wa kaina lalurar zuwa asibiti ba, asalima kullum cikin son yaƙar hakan nake yi, dalilin da ya sa na ce zan karanci science kenan, amma Yaya Sadeeq ya hana ni kuma na hanu, Umma kowa fa ya san yanda na ɗauki Yaya Sadeeq, wallahi ko Yaya Umar ba na jin shi a rai tamkar yanda nake jin Yaya Sadeeq, Umma nasan ba za a barni na sake komawa asibiti ba, shiyasa na sanya wa rai da zuciyata salama, amma magana a waya ma a ce Yaya Umar ya hana ni yi da Yaya Sadeeq, hakan ya kyautu dan Allah?"
Umma hannunta ta kai take ɗan bubbuga bayan Sadiya alamar rarrashi, sannan ta ce, "Ki yi haƙuri Auta, ba a kyauta ba amma in sha Allah zan yiwa Umar magana, duk da ba ma fatan har biki ya zo Sadeeq bai dawo gida ba, amma in har Allah ya ƙaddari hakan ta faru, to ni da kai na zan kai ki asibitin wajanshi ya miki nasiha ko, amma fa duk haka zai faru ne akan yarjejeniya guda ɗaya."
"Menene yarjejeniyar Umma?" Murya a sanyaye ta yi tambaya.
Sai da Umma ta numfasa sannan ta ce, "Dole za ki sake kike walwala kamar yanda kike asali, za ki cire damuwar komai a zuciyarki ki saki ranki, hakan ne kawai zai sa kullum na haɗa ki da Sadeeq a waya ku gaisa kamun lokacin bikin idan Allah ya yi ya warke to, idan kuma bai warke ba sai na kai ki kaman yanda na ce in sha Allah."
"In Allah ya yarda Umma zan saki rai na, walwalanma zan ƙoƙarta dan dai Yaya Sadeeqna baya nan kam ba walwala, amma zan ƙoƙarta nayi, kuma in sha Allah zai warke ya dawo gida kamun lokacin bikin."
"Allah ya amince auta, Allah ya sa ya warke dan duk haka muke fata."
"Amin Umma."
"To maza ɗaga kanki ki fara cika yarjejeniyar tun yanzu, ki ci abinci sosai, kin ga duk kin bi kin faɗa, kuma dai bansan a wanne gari ake haka ba, amarya ba ci ba sha sai sanya wa zuciyarta damuwa, duk kin zama ba kyan gani kamar ba ke ba, so kike Haidar ya tuhume mu ko? To ki saki ranki tun kamun gwaggwaninki su iso su rufe Mamanku da faɗa kin san su sarai."
Ajiyan zuciya Sadiya ta sauƙe, sannan ta ɗage kanta a kafaɗan Umma ta ce, "Allah Umma na ci tuwo sosai a gidan Mama, har magani na sha, ki tambayi Yaya Khalid ko Mama."
Jinjina kai Umma tayi tare da cewa, "Shikkenan, Allah ƙara mana ƙoshi, tun da kin sha magani sai ki yi abinda za kiyi ki kwanta da wuri."
"To Umma, Allah tashe mu lafiya."
Da, "Amin", Umma ta amsa, sannan ta miƙe ta fice da plate da ta shigo da shi.
Sadiya tana ganin ficewan Umma, ta sauƙe wani nauyayyan numfashi, sai da ta lumshe idanuwanta na mintuna, sannan ta miƙe ta shige toilet, ruwa ta watsa ta fito tayi shirin bacci, cikin dogon riga na bacci, ruwan ɗorawa, saboda yellow ya kasance ɗaya daga cikin favourite colors na Sadiya.
Sai da ta kammala komai ta kwanta, sannan ta laluɓo layin Haidar ta aika mishi da ƙira, ringing guda yayi ya katse ƙiran ya ƙirata, tana sakin tattausan murmushi ta ɗauka tare da kara wa a kunnenta, "Umn rankashidaɗe na Halimatu."
⭐️
ALIYU HAIDAR POV
***
Haidar wuni yayi fama da ayyuka, a gefe guda kuwa yana ta gwada layin Sadiya baya samun ta, hakan ya sanya aikinshi ya ja lokaci sosai, ya so zuwa wajan Sadiya dan tabbatar da lafiya take, musamman da ya kwana da sanin za ta je asibiti, shiyasa hankalinshi bai kwanta ba, amma ba yanda ya iya don kuwa lokacin da ya fito da niyan zuwa wajan Sadiya, lokacin ne Hajiya ta dabaibaye shi da aikenta, bai ma dawo ba yana hanyan dawowan kenan ƙiran Sadiya ya iske shi, hakan ya sanya ya parker motarshi suka yi waya, sai da suka kammala ta ba shi uzurin Umma na mata magana, sannan shi ma ya ja motan ya ƙaraso gida, sai da ya parker motar sannan ya fito tare da locking nata, cikin ƙasaitacciyar tafiyarshi yake taku cike da gajiya, domin tabbas yau ya gaji matuƙa, tun safe har yanzu bai huta ba.
Lokaci guda ya kai hannunshi jikin ƙofan da zai sada shi da main palournsu, ya danna door bell kuma ya murɗa handle na ƙofan ya shige, bakinshi ɗauke da sallama ciki-ciki, ba a amsa mishi sallaman ba saboda main palourn ba kowa, dan daman bai sa ran samun amsan sallaman ba, kaman yanda bai sa tsammanin ganin kowa a palourn ba, wannan palour ne da iya baƙi ake iya samu a ciki time to time, babban palour ne sosai iya ganin mutum, mai ɗauke da set uku na kujeru mist color, palourn yayi matuƙar ƙayatuwa duk da ba wasu abubuwan hayaniya a ciki sosai, plasma ne babba da ya kusa rabin bango wanda mutum ya ɗauka ko majiƙi ne, sai dogayen home theatre da ke a gefe da gefen plasman, sannan sauran part's na bangon ɗakin an manne su da frame masu girma na zane mabambanta masu kyau sosai da ɗaukan hankali, ga isashshen centre carpet milk color a tsakiyan kujerun, duk set guda na kujera da nashi madaidaicin centre table, banda sansanyar ƙamshi da sanyin ac ba abinda ke tashi a palourn.
Haidar sai da ya ɗan shaƙi daddaɗan iskan main palourn, sannan ya cigaba da takawa, wani ƙofan ya kuma buɗewa inda ya sada shi da asalin palourn da masu gidan suke, wannan palourn ya fi palourn da ya wuce kyau da ƙayatuwa, sai dai bai kai wanda ya wuce da farko girma ba, wannan madaidaicine dan set na kujera ɗaya ne, a haka ma suna a manne da juna, saboda daga gefe akwai step's da zai sada mutum da upstairs inda ɗakunan yaran matan gidan yake, a ɗan gefen step's ɗin kuma ƙofan kitchen ne, a cikinshi akwai ƙofa biyu, ɗaya na store ɗaya kuma ƙofan baya ne, wanda in ka bi shi za ka fita compound na gidan ta baya ba tare da ka bi ta main palour ba, daga ɗaya gefen step's ɗin kuma ɗan corridor ne wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu, na Hajiya da kuma na Alhaji, wannan palourn ma kaman wancan dai ɗauke yake da tambatsetsen plasma da sauran abubuwa da ke ƙawata wajan zaman TV, ga showglass da ke ɗauke da mazubin turarukan wuta different type's with different scents, airfreshners, burner's, humidifier's da sauransu, sinadaran ƙamsasa gida, sannan a ko wanne ɓarayi na bangon palourn akwai frames, wani na Alhaji da Hajiya da yaran nasu duka, wani iya Alhaji da Hajiya, wani yaransu mata kawai, wani kuma duka yaran nasu, a side da ƙofan da zai sada ka da sashin Haidar, a nan ne frame na Haidar shi kaɗai ke manne, yana sanye da ƙananan kaya yayi masifaffen kyau, wannan ƙofan da ke a side ɗin ne idan ka shige shi zai sada ka da gajeren corridor sai palourn Haidar wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu, ɗaya normal ƙofa ne mai kyau da kuɗi, ɗaya kuma glass door ne, nan ne kuma bedroom na Haidar, sashin shi ma ya gaji da ƙayatuwa har bedroom nashi, sai dai ɗaya bedroom ɗin ba furniture a ciki, kuma wannan aikin Hajiya ce, ta ce ba za a sanya komai a ciki ba, daga shi har Alhaji ba wanda ya tamka mata a kan hakan, sun dai zuba mata ido ne su ga me take nufi da hakan, dan sun san duk tsawon lokaci dai dole abinda take nufi ya fito ko kuma idan Haidar ya tashi saka furniture ɗin ta ƙyale shi ya saka.
Da sallama ƙasa-ƙasa Haidar ya shigo wannan palourn ma, sai dai a nan kam jama'an da ke a palourn kaf sun amsa mishi, Hajiya, Nihal, Nimra da Husna, ƙannen nashi sannu da dawowa suka mishi bayan amsa sallaman, amma Haidar bai ko kallesu ba balle ya amsa, har ya ƙarasa gefen Hajiya da take zaune a kujera mai ɗaukan mutum uku, Husna ta yi matashin kai da cinyan Hajiyan.
Daga ɗaya gefen Hajiyan ya zauna tare da cewa, "Hajiya barka da dare."
Fiska ba yabo ba fallasa Hajiya ta ce, "Yauwa Haidar, sannunka da dawowa ko, fatan ka duba komai da komai lafiya?"
"Eh na duba komai ya iso yanda kika ba da lissafin."
Sai sannan Hajiya ta ɗan washe baki tare da cewa, "Ma sha Allah, nima gobe zan leƙa da yardan Allah, kwana biyu ban je ba tun da na amso list na abubuwan da ya kamata Nadiya ta shigo mana da su."
Haidar bai kuma cewa komai ba ya miƙe tare da nufan hanyan da zai sada shi da ƙofan sashin shi, maganan Hajiya ne ya dakatar da shi.
"Dinnern fa? A kawo maka sashinka ne?"
"No Hajiya am okay, Nihal ta kawo mini coffee kawai", yana gama faɗin haka ya murɗa handle na sashinsa ya shige, tun daga gajeren corridorn ya soma cire p-cap nashi da wristwatch nashi, da sallama ya shige palourn shi, kai tsaye ya wuce cikin ɗakinshi, a nan ya ƙarisa rage kayan jikinshi ya shige closet nashi ya wuce toilet, ya ɗan ɗau mintuna sannan ya fito sanye da rigan wanka(bathrobe), yana ƙoƙarin tsayawa tsane jikinshi ya sanya pyjamas sai ya jiyo sautin wayarshi, hakan ya sanya ya fito tare da ɗaukan wayan, katse ƙiran nata yayi ya ƙira ta, tana ɗauka ya ce, "Assalamu alaiki natsuwar ruhin Aliyu Haidar."
Lumshe idonshi yayi tare da sakin numfashi mai tattare da gajiya, lokaci guda kuma murmushi na mamaye haɗaɗɗen fiskarshi, saboda amsar da Sadiya ta ba shi a ɓangarenta.
"Haidar na Halimatu in ba da kai na a sare na je gida na ce da Alhajina faɗuwa kan yayi ko?", ya ƙarishe maganar da murmushi mai sauti yana ɗage gira guda kaman tana kallonshi.
***
A ɓangaren Sadiya dariya ƴar gajeriya tayi, amma irin dariya mara sauti kuma mai tafiyar da ƙunci da damuwan da ke a zuciya, sannan ta ce, "Ah abun bai kai har haka ba Al-Sad."
"Ya kai har ma ya fi", faɗin Haidar yana murmushi wanda ya kore mishi duk gajiyan da yake a ciki, da kuma damuwar wuni kewarta da yayi.
"Uhmn, to ya gajiyan ayyukan yau ɗin? Fatan gajiyan ya sake mini angon nan da ƴan kwanaki, ko kuwa dai sai an zane gajiya?"
"Nope, gajiya dai tun da ya jiyo muryarki yake ƙoƙarin ƙyale ni, amma dai da za a zane shi da tausa da zai fi tafiya da kyau."
Ƴar murmushi Sadiya ta yi bata ce komai ba, sai juyi da tayi a kan gadon Umma tana jin ƙaunar Haidar na sake huda duk wata magudanar jini, ruwa da numfashi na jikinta.
"Sweet Al-Sad...", maganan da yayi niyan yi ya katse saboda knocking ƙofarshi da ake yi, hakan ya sanya ya ce, "Excuse me sweet Al-Sad, bari na amshi coffee a wajan Nihal."
Gyaɗa kai Sadiya tayi tare da murmushi kaman yana kallonta, bata katse ƙiran ba saboda ya hana ta, muddin ba ita ta ɗau excuse na katse ƙira ba, ko shi da kan shi ya nemi ta katse ƙiran, to dan ya ce bari yayi wani abu to ya hana ta katse wa, haka ita ma indai abinda za ta yi ba wani na buƙatan ta katse ƙiran bane to bata katsewa zai jira ta har ta kammala sannan sa cigaba da wayarsu.
Haidar sanin Nihal ce ya ce ta kawo mishi coffee, sai bai damu da bathrobe da yake sanye da shi ba, kawai ya gyara zaman shi a kan kujeran da yake zaune wanda ke gefen gadonshi, wayan na maƙale a kunnenshi ya ce, "Hey Nihal come in."
Husna da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin Haidar ɗin, hannunta riƙe da tray na tangaran madaidaici mai ɗauke da coffee cup da murfinshi, fari tas mai yalƙi da ɗaukan ido, tiriri da ƙamshin coffee sai tashi suke suna dakar mata hanci, knocking guda tayi bayan mintuna ta ji ya ce ta shigo, sunan Nihal ta ji ya ƙira ba ita ba, hakan ya sanya jikinta ya ɗan kama kerma, dan ta san wannan ma wani hukuncin za ta amsa, na kawo abinda ba ita ya aika ba, balle kuma ita da ya hana ta shiga ɗakin shi, yanzu kuma ga shi ya ce ta shigo tunda a tunaninshi Nihal ce, rashin shigarta kuma wani bala'in ne a wajan Ya Haidar, idanuwanta ne suka ciko da ƙwalla.
"I said come in, ko ni zan taso na amsa? Ko sai ya huce tukunna za ki shigo?"
Maganar Haidar shi ya dawo da ita daga tunanin da take yi, sannan shi ya ƙara sanya wa ta daburce, amma sam hakan bai sanya ta yunƙura da niyar shiga ba.
Haidar da ranshi ke a ɓace na manna mishi hauka da Nihal tayi, a tsawace ya ce, "Don't let me come and meet you there."
Sanin halin Haidar ya sanya Husna yin saurin tura slice glass door ɗin, ta sanya ƙafanta ƙirjinta na bugun ɗari uku da tamanin, tana ambatan sunan Allah kawai, dan ta san yau sai ɗan buzunta.
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@UwarBatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
***
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# ***
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚