HAMAL Chapter 5
HAMAL
Arewabook@ayshadansabo
©️Ayshat Dansabo lemu
Chapter 5
WAIWAYE.....(Adon tafiya)
Alhaji Attaheer wani babban ƙusa ne a ƙasar tamu,kuma hamshaƙin ɗan kasuwa wanda ake damawa dashi a ƙasashe daban-daban.Ya mallaki matarsa ɗaya tilo wato Hajiya Ameena,kuma auren saurayi da budurwa sukai da juna.Aure ne aka yishi na so da tsananin shaƙuwa,dukkaninsu boko ya ratsasu matuƙa.A gefe guda kuma suna da sani na addini sosai,hakan yasa rayuwarsu ta zam abin sha'awa ƙwarai da gaske.Allah ya albarkacesu da yara guda biyar,Abdurraheem shine babba sai Abdallah,sai hassana da usaina wanda Allah karɓi rayuwarsu akan hanyarsu ta komawa skull.Daga su ne sai auta Fateemah wacce suke kira da Teemah,sosai Yaran suka sami tarbiya kwarai da gaske.Abdurraheem yayi karatunsa tun daga secondary skull har zuwa jami'a a ƙasar England,inda yayi karatun deegree ɗinsa akan Building Engineering wanda hope ɗinsa kenan dama tunda ya taso.Bai dawo ƙasarsa ta haihuwa ba saida ya haɗa masters ɗinsa,yanxu haka shekarunsa biyu da dawowa gida 9ja kenan.Dawowarsa gida kenan ya fara gudanar da ayyukansa cikin nasara,yana samun manyan kuɗaɗe kasancewarsa haziƙi kuma ƙwararre akan fannin nasa.Ba ƙananun kwangilolin gina-gine yake samu ba,daga shi sai Abdallah dake shekararsa ta ƙarshe sai auta Teemah wacce a yanzu take shirin shiga JS1 secondary school.Hajiya Ameena mace ce dake da matuƙar kula tare da saka ido akan Yaranta,ta jasu a jiki sosai ta yadda babu wani damuwarsu da suke iya ɓoye mata shi domin itace abokiyar shawararsu.Mahaifiyar Alhaji Attaheer tana raye Mahaifinsa ne ya daɗe da rasuwa,sosai Hajiya Ameena ke girmama sirikartata Hajiya Hajjo.Hajjo mace ce mai matuƙar sanyin hali da haƙuri,ta ɗauki son duniya ta ɗaurashi akan jikokin nata kasancewar suka ɗai take dasu.Alhaji Attaheer su biyu kacal Hajiya Hajjo ta haifa,daga shi sai ƙanwarsa wacce ta rasu bayan anyi mata aure.Ta rasu ne gurin haihuwa,kuma daga ita har abinda ta haifa Allah ya amshi rayuwarsu.Engr. AR Attaheer miskili ne matuƙa sam bashi da yawan hayaniya kuma baya ɗaukar raini ko kaɗan,a gefe guda kuma yakan taɓa barkwanci ga wanda yayi ra'ayi.A mafiya yawan lokuta inka ganshi yana yima toda kakarsa Hajjo ce,sai ko Momy da kuma abokanansa.Tun tasowarsa ya zama cikakken mutum,babu abinda yake ƙyama irin yaga mace ballagaza wacce bata da kamun kai,shiyasa har ya gama karatunsa a ƙasar turai yayi gogayya da matan turawa bai taɓa sakacin da yayi mu'amala da kowace mace ba inba a harkar karatu ba.shima kuma da an rabu shikenan,sam baya sha'awar ganin mace da shigar banza sam.A cewarsa duk wata macen kirki tana ƙoƙarin adana kanta da kwalliyarta ne ga mijin aurenta shi shi kaɗai,ba wai ta riƙa bayyana adonta a titi ba kamar yadda ƴan matanmu na yanzu suka ɗauki hakan a matsayin wayewa.Yana shekararsa na ƙarshe a ƙasar England wani dawowa da yayi hutu ya tarar Momy ta ɗakko riƙon Hafsat,Yarinyar ƙawarta ce data rasu ta barta tana budurwa.Don a lokacin har ta gama NCE ɗinta ma,Hafsat irin matannan ne marasa kamun kai gata da shigar banxa kamar ɗiyar arna,tana da ƙarancin kunya sosai ga taurin kai da rashin jin magana.sai dai kuma kyakykyawace sahun farko,domin ta mallaki komi da ɗiya mace za ta yi tinkaho dashi.Tunda ta ƙyalle ido taga Abduraheem taji ya sace zuciyarta baki ɗaya,wani irin so take masa na sha'awa zallah domin bata ƙi ya biyeta su dinga masha'aba koda bazai aureta ba.Kuma tunda Abdurraheem ya fahimci halayyar Hafsat gaba ɗaya yaji Yarinyar bata kwanta masa ba, tarbiyarta sam bai dace da irin turban dabyake so ɗiya mace ta kasance a kaiba.A ɗan zaman da yayi kafin komawarsa,Hafsa tayi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta cusawa Engr. Soyayyarta amma sam batai nasara ba,hasalima ƙara rura wutar tsanarta take a cikin zuciyar AR Attaheer take yi.Aɓangaren Hajiya Ameena kuwa tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta saita Hafsat akan turba nagari amma abin yaci tura,sai tayi kamar ta natsu sai kuma ta sake koma ma rayuwarta yadda take so.Hakan yasa daga Abdurraheem har ƙaninsa Abdallah basa ga maciji da Hafsat,ita kuma tasha alwashin saita mallaki AR Attaheer kota halin ƙaƙane ta biya buƙatarta a kansa ko yana so ko baya so.Tasha alwashin sai tayi amfani da duk wata kissa irin ta mata domin taga cewa burinta ya cika a kansa,ni dai Ayshat dake biye nace anya kuwa Hafsat za ki yi nasara akan AR kenan?Sam Engr. AR mata basa gabansa duk kuwa da cewa yana samun masu sonsa kamar suyi hauka,kasancewarsa haɗaɗɗe kuma ga masu gidan rana sun jiƙasa amma sam basa samun fuska daga gareshi.Halisama shi ba mazaunin guri guda bane,amma abin mamaki lokaci guda haɗuwarsa da Hamal Yarinya mai shekaru 17 ma'abociya kyawu da cikar halitta take ƙoƙarin sace zuciyar AR Attaheer ɗin.A ranar da suka haɗu shigowarsa Zaria kenan ya biya ta Samaru domin isar da wani saƙo,akan hanyarsa ta zuwa masaukinsa ne ya haɗu da zaratan ƴan matan uku wanda kansu yake a haɗe har Hamal tayi nasarar kama zuciyarsa.
********
Aɓangaren Hamal kuwa Mahaifinta Alhaji Abdulmutallab ɗan kasuwa wanda ake damawa dashi,kuma babu laifi yayi karatun boko tare da na addini daidai gwargwado.Allah ya azurtashi da auren matarsa ta farko Halimatu inda Allah ya basu arziƙin samun ƙaruwa suna shekaru biyu da yin aure ta haifa masa babban ɗansa mai suna Kamal,tun daga lokacin sai haihuwa ya yima Hajiya Halima ɗif,bayan wasu shekaru sai Allah ya sake haɗa Alhaji Abdulmutallab da Hajiya Bilki.Hajiya Bilki bazawara ce wacce ta fito daga gidan mijinta bata taɓa haihuwa ba,ba a ɗauki lokaci ba suka yi aure bayan Alhajin ya shawo kan Mahaifiyarsa ta amince da ƙyar domin a cewarta yana zaune da matarsa mai haƙuri da kirki me zaisa ya bijiro da zancen ƙara aure.Domin Hajiya goggo tana matuƙar son Halima da tilon ɗanta Kamal sosai,sai dai ganin yadda ya kafe akan yana son auren Hajiya Bilkin yasa ta haƙura ta bashi damar ƙara auren bayan ta lallashi Hajiya Halima akan tayi haƙuri ta kauda kai akan auren da mijin nata zai sake.Ta shawarceta da cewa kada ta nuna damuwa ko tace za ta canza akan irin biyayyar data saba masa,tace ta yawaita addu'a kurum Allah yasa matar ta shigo da alkhairi.Hakan ko aka yi domin sam Hajiya Halima bata nuna wa mijin nata komi akan ƙarin auren da zaiyi ba,bayan tarewar Hajiya Bilki da watanni shida ta samu ciki.Kuma tunda hakan ya faru lamura suka fara sauyawa,ya kasance Alhaji Mutallab ya maida kulawarsa kacokan akan Bilki da cikin jikinta kai kace
a lokacin ne za a fara yi masa haihuwa a gidan.Duk da cewa har zuwa lokacin bawai ya sauya akan irin matsanancinson Kamal da bashi duk wata kulawa bace,tun abin baya damun Hajiya Halima har ya fara taɓa zuciyarta ganin rawar kan da yake nunawa har yaso yayi yawa.Amma hakanan ta danne bata taɓa nuna komi ba,bayan haihuwar Bilki wacce ta haifi Muhibbah Alhaji Mutallab ya cigaba da basu kulawa a lokacin Kamal yana shekararsa ta karshe a secondary skull.Tazararsu da Muhibbah na da nisa sosai,Muhibbah nada 2 year's aka sake haihuwar Hauwa suna kiranta da Meemah.Nan fa Hajiya bilki ta miƙe ƙafa da rashin kirki,duk wani halinta na kirsa da makirci ta sake fito dashi fili.Bata da burin daya wuce ta buɗi ido taga cewa ta fitar da Hajiya Halima daga gidan aurenta,wanda hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Gwaggo yayi ba.Tana matuƙar tausayin Halimatu ƙwarai,hakan yasa wani zuwa da Alhaji Mutallab yayi ta zaunar dashi tana masa nasiha akan ya kula da gidansa ƙwarai,kada ya bari wata mace ta shiga tsakaninsa da matarsa ta kirki mai tsananin haƙuri.Domin idan har ya bari Bilki tayi nasarar rabashi da Halimatu to tabbas zaiyi wuya ya maida mace kamarta,sosai nasihar ya shigesa domin tabbas shima yasan Halimatu itace mace mafi biyayya da soyuwa a cikin ransa.A lokuta da dama ya kanyi danasanin auren Bilki sabida rashin kirkinta,domin ya daɗe da fahimtar cewa bata sami tarbiya ba.Idan ya kalli rabon dake tsakaninsuvne sai yaji cewa dole ne yayi haƙuri da ita kodan rabon yaran dake tsakaninsu,ana cikin haka ne Hajiya Halima ta samu ciki wanda bayan an rigada an fidda rai da cewa zata sake samun haihuwa.Sai dai shi Allah babu ruwansa ya kanyi ikon sane a lokacin da yaso ya kuma ga dama,tun daga samun cikin sai Alhaji Mutallab da goggo suka ɗauki kulawar duniya suka mayar kan Halimatu.Hakan ya ɗaga hankalin Hajiya Bilki,domin sam bata yi farin ciki da wannan tsananin rabo ba.Nan ta lashi takobin sai taga bayan cikin kota halin ƙaƙa ne,hakan yasa ta dinga sanya wa Hajiya Halimatu magunguna a cikin abinci amma sam bata ci.Tunda Gwaggo taga yadda Hajiya Bilki take nuna baƙin cikinta a fili,sai ta samu Halimatu tayi mata gargaɗin cewa duk abinda zai fito daga hannun Bilki kada ta sake taci.Duk da cewa sun dogara ga Allah ne amma kiyayewa daga maƙiyi yana da kyau,hakan ko aka yi domin sam Halimatu bata cin abincinta sai dai ta girka nata taci har zuwa lokacin data sauka lafiya ta sami Ƴarta mace.Yarinya mai tsananin baiwae kyawu matuƙa,duk wanda ya ganta sai ya tanka kyawunta.Tunda aka haifi Hamal ta shiga cikin zuciyar Mahaifinta ƙwarai da gaske,tana da shekaru huɗu a duniya ciwo ya kama Halimatu kuma bata ɗauki lokaci ba tace ga garinku nan.Wannan mutuwa ya girgiza mijinta da Mahaifiyarsa matuƙa,inda Alhaji Mutallab saida aka dinga haɗa masa da addu'a sannan ya dawo nutsuwarsa yasa dangana a cikin ransa.Kuma gaba ɗaya sai ya maida duk wani soyayyar da yake wa Halimatu akan Hamal da Kamal,domin yana matuƙar tausayin Hamal sosai.Gwaggo taci burin ɗaukar Hamal ta riƙeta amma sai Hajiya Bilki ta nuna cewa ita za ta kula da ita kamar yadda za ta kula da su Meemah,hakanan Gwaggo tasa haƙuri ba don ranta yaso ba.Shekaran Halimatu biyu da rasuwa Hajiya Bilki ta sake haihuwar Nadeeya,wanda taci burin dama namiji ne ta haifa.A lokacin Hamal ta shiga primary skull,sosai Hajiya Bilki ke basu kulawa sam bata nuna wa Hamal wani mummunar hali hakan yasa Yarinyar ta saki jiki da ita matuƙa.Hamal irin gifted ɗinnan ce,ta taso da kaifin ƙwaƙwalwa ba kaɗan ba kuma a ɓangaren boko da Islamiyyah,Mallamai na matuƙar ƙaunarta suna alfahari da ita,girma take yi kullum kyawunta da natsuwarta na ƙaruwa.Bata da hayaniya sam in ka ɗauke shagwaɓarta da rigima,abu kaɗan ke saurin sata hawaye.Waɗannan halaye nata da baiwar ƙoƙarinta ba ƙaramin ƙona ran Hajiya Bilki suke ba,wacce suke kira da Mami amma sam a zahiri da gaban Abbah da Gwaggo bata nuna komi illa ma ta riƙa biye shagwaɓar Hamal ɗin.Hamal nada shekaru 10 ta wuce secondary school kasancewar tana da matukar ƙoƙari,a lokacin duk su Muhibbah sunyi nisa suma a karatunsu.Tun daga lokacin da Hajiya Bilki ta fahimci cewa lokaci yayi da za ta fara cin moriyar Hamal ɗin,sai ta fito da munanan halayyarta akan Hamal ta shiga cusawa Yaranta tsanar Hamal ɗin.Tun basa ɗauka har suka fara hantarar ƙanwar tasu,sannu ahankali suka juyawa Hamal baya tsakaninta da Hajiya Bilki sai zagi da kuma hantara.Uwa uba duk wani aiki na wahala aka fara sakarma Hamal ɗin,da zaran ta dawo gida bata da wani hutu sai bauta.Ita ne wankin undies da kayan Nadeey, har takai an fara sakar mata aikin girki a lokacin tana JS3 kenan.Duk wani alamun ƴan matanci sun fara bayyana a jikinta,kullum ƙara kyau take yi wanda hakan ke ƙara dasa tsanarta a cikin zuciyar Mami Bilki.Duk waɗannan mugayen halayen sam Hajiya Bilkisu bata nuna su a gaban Mahaifinsu,kasancewarsa ba mazauni bane haka shima Yaya Kamal baya zama yana yawan tafiye-tafiye tare da Abbansu akan harkokin kasuwancin Abban.Tun Hamal tana kuka tana damuwa akan halin data tsinci kanta a ciki har ta sanya haƙuri tare da juriya,duk da haka bata rage komi akan ƙoƙarinta da maida hankali akan karatu ba.In kaga tana walwala to a boko ne ko islamiya,da zaran ta shigo gidan Ubanta za ta cigaba da fuskantar takura da matsi haɗi da zagi da hantarar Bilki da Yaranta.A haka shekaru suka ƙara ja watanni suka shuɗe,Hamal na fuskantar matsi da takura.Sannu-sannu har takai SS2 a skull kuma a shekarar ta zana weac domin fita.Zuwa lokacin ne Abba ya fara laƙantar halin da ƴar tasa take ciki,bayan ya keɓe da ita yana mata tambayoyi.Wani ta bashi amsa wani kuma ta ɓoye masa,Ya Kamal kaɗai take faɗi ma damuwarta da irin halin da take ciki a gidan.Hakan na matuƙar kona ransa amma bashi da yadda zaiyi,sai dai a kullum abu daya yake faɗa mata idan takai masa kokenta shine,"Hamal kiyi haƙuri ki ƙara haƙuri,ki sani komi da kika gani a duniya baya dawwama,a sannu komi zai zama tarihi,Allah yana sane damu kinji ko?"A lokacin sai dai ta gyaɗa kai ta share hawayenta.Sosai take ƙaunarsa a matsayinsa na Yaya a gareta wanda suka fito ciki ɗaya,shi kaɗai ke rungumeta ya lallasheta tare da yi mata nasiha har taji cewa ta gamsu ta kuma samu ƙwarin guiwar sake jurema halin data tsinci kanta a ciki na maraicin rashin Uwa uwa.Duk dawowar da zasu yi shi da Abba suna ƙoƙarin ganin sun wadatata da abubuwan sha'awa na mata tunda daga kan suturu zuwa kayan kwalliya,daga ita har su Muhibbah ba a banbantasu in dai har Abba ne zai yi musu ko ko Ya Kamal ɗin.Amma ita Hajiya Bilki a kullum burinta shine taga Hamal ta zama koma baya a cikin su Hibbah,cikin nasara Hamal taci jarabawarta taci jamb ɗinta tare da duk wani matakin da za a bi wajen ta shiga jami'a ta tsallakesu cikin nasara.Cikin taimakon Allah ta samu addimision a ABU Samaru aka bata course ɗin data zaɓa wato Chemistry,kuma a ranar data amso addimision ɗinta cike take da farin ciki marar misaltuwa.Suna shigowa parking lot na cikin gidan nasu ta hango motar uncle Areef ƙanin Hajiya Bilki wanda suka fito ciki guda taji zuciyarta ta ɓaci,domin
Areef tantirin ɗan iska ne na gaske.Manemin mata ne ƙwarai ga shaye-shaye,tunda ya ƙyalla ido yaga Hamal ta fara zama budurwa sonta ya ɗarsu a cikin zuciyarsa yayi ma Yayar nasa magana amma sai Hajiya Bilki tayi saurin ce masa kada ya kuskura ya fito da son fili ya jira har lokaci yazo.Lokacin da za ta saka Abbah ya mallaka masa ita,hakan ba ƙaramin faranta ran Areef yayi ba kuma
tun daga lokacin yake yawan zuwa gidan domin ya dinga ganin kyakykyawar fuskar Hamal ɗin.Duk randa yazo Hamal bata da sauran sakewa,haka Areef zai tasata a gaba da mayataccen kallonsa shine sata ɗakko masa wancan,dafa mishi abinci da sauran hidima kala-kala.Hakan yasa Hamal tayi mugun tsanarsa,gashi kaf mugayen halayensa babu wadda bata sani ba.Domin a banza ma za ta ji mamin nasu na zagin halinsa,lokuta da dama haka zai tsareta saita zauna sunyi hira wanda a ƙarshe zai ɓige da neman rungumarta ko ya dinga nema lallai sai ya shafata.Wannan yasa ko yaxo take ƙauracewa zaman falon sam,sai dai Mami ta gama zaginta amma tafi jure hakan akan ta fito tayi hira da Areef.Shiyasa tun shigowarsu taga motarsa ta nemi farin cikin da take ciki ta rasa,fuskarta a haɗe ta doshi falon bakin ta ɗauke da sallama.Mami ta gani zaune a cikin falon Areef na daga gefenta,kallo suke yi yayin da Nadeey ke kwance akan cinyar Hajiya bilki tana zuba shagwaɓa.Sallamar da Hamal tayi ne ya janyo hankulansu zuwa ga ƙofar shigowa falon,babu wanda ya amsa sallamar nata inka ɗauke Uncle Areef daya kafeta da mayataccen kallonsa yana ayyanawa a cikin ransa cewa gaskiya Hamal ta haɗu matuƙa ko wani shiga tayi birgesa takeyi.Ahankali ta janyo ƙafa ta shigo cikin falon,risinawa tayi ta gaidashi idonsa ƙyar a kanta.Juyawa tayi tana faɗin,"Mami na dawo kinga addimision ɗin na amso." Ta ƙare maganar tana fiddo takardar addimision letter ɗin ta miƙawa Hajiya Bilki wacce tayi saurin kawar dakai,tare da dakatar da Hamal ɗin ta hanyar faɗin,"Barshi basai na gani ba,burinki ya cika tunda an samu abinda ake so,saura aje ana rabama lacturers abin suna kwasar gara,don ni na daɗe da karantar shegun idanuwanki na jarababbun mata ne,sai dai a yau inaso kisani baki da mijin aure sai Areef,kin gansa nan tun kina ƙwaila yake faman dakon sonki,kinko ga bazai tashi a banza ba,tunda na gida naso ai yafi ki kwaso wani gantalallan nan gaba kice shine zaɓinki."Tunda Hajiya Bilki ta soma magana jikin Hamal ya ɗauki rawa,sosai kalaman Mami suka doki ƙahon zuciyarta lokaci guda wani azababben kuka ya ƙwace mata.Cikin muryar kukan take faɗin,"Mami kiyi min rai ni wallahi ba aure nake so ba karatu zanyi,kuma ai nayi ƙanƙanta da maganar aure ma a yanzu, please Mami ki daina wannan zancen don Allah."Tana kai ƙarshen kalamanta Hajiya Bilki na wanketa da wani lafiyayyen mari,cikin masifa take faɗin,"Keh! Har ni zaki kalla kice zaki tsarawa zance,kina nufin kinfi ƙarfin ki aury Areef ne?Da kike maganar ƙanƙanta don Uwarki toni ina JS3 ma aka ɗauramin auren fari,kafin in fito in auri Ubanki,wato kin kawo ƙarfi za ki sa ƙafa a babbar makaranta,har kin fara faɗa ina faɗa to mu zuba ni da ke ne,kuma ki ɓacemin da gani shashasha! Mai kama da zubin aljanu,kuma saura inji maganarnan a bakin tsohon naki wallahi saina illataki shegiya mai zubin karuwai." Hajiya Bilki ta ƙare kalamanta cike da tsawa da tsanar Hamal ɗin.Da gudu hamal ta nufi ɗakinta ta zube akan gado tana rizgar kuka,tofa! Ga ƙoshi ga kwanan yunwa kenan? Ana wata ga wata kenan? Haka Hamal ke faɗi a ranta zuciyarta na tsananin zafi tausayin kanta na sake rufeta.Babu yadda za'ayi ace za a liƙa mata auren Areef,hasalima ita karatu take da burin yi ana haka sai ga kiran Ya kamal ya shigo wayarta.Cikin azama ta miƙe zaune tare da share hawayenta,tana faɗin,"Hello Ya Kamal."
Ya amsa da,"Hamal ya naji muryarki wani iri meke faruwa ne?"Ai kamar jira take ta sake rushewa da kuka,wanda hakan ya tashi hankalin Kamal sosai, faɗi yake,"Hamal kiyi min magana meke faruwa ne?" Cikin kukan ta kora masa yadda suka yi da Mami,ta ƙare maganar da faɗin,"Don Allah Ya Kamal kada ka bari suyi nasara a kaina, wallahi ni karatu nake so shine burina,kuma imma auren ne kai kanka kasan Areef bai dace dani ba."Sosai ran kamal yakai ƙololuwa gurin ɓaci, ahankali yake lallashinta da kalamai masu daɗi tare da bata tabbacin cewa ƙaryar Hajiya Bilki ya sha karya domin bazai taɓa bari suyi nasarar ruguza rayuwar ƙanwarsa ba.Ya cigaba da faɗin,"Hamal ki kwantar da hankalinki zan sami Abbah in faɗa masa duk halin da kike ciki,domin koda sun je masa da maganar yasan yadda zaima tufkar hanci."Sai a lokacin Hamal taji nutsuwa tare da yi masa albishir da samun addimison ɗinta,sosai ya nuna farin cikinsa tare da yi mata nasiha data kama kanta yana mai faɗin,"Hamal kisani jami'a ba irin sauran makarantun da kika gama bane,a yanzu ne ake da buƙatar ki sake zama Kamila,ki tsare mutuncin kanki ki zama mai matuƙar yin taka-tsantsan,kisan irin ƙawayen da za ki yi mu'amala dasu Hamal,abinda ya kaiki shi kaɗai za ki yi kinji ko? Jibi In sha Allah ina hanyar dawowa ki kwantar da hankalinki Mami kuma ki nuna mata komi ya wuce kada ki sake nuna wata damuwa akan zancen Areef." Daga haka ya dinga janta da hira har sai da yaga ta samu nutsuwa,har tana ƙyalƙyala dariya sannan suka yi sallama da juna.Kuma kamar yadda kamal ya sanar da Hamal yana tafe,hakan ce ta kasance kuma bayan dawowarsa ne ya taimaka ta gama registration ta kammala komi nata sai shirin fara attending lactures kaɗai ya rage mata.Abbah ya tanadar musu wata sabuwar mota domin a riƙa kaisu skull,kuma duk wacce take da lacture da wuri ita ake fara kaiwa musamman Hamal dake zuwa Samaru.Hakan yasa su Muhibbah ke ganin an takurasu duk da cewa sune suka fita kusa da makarantunsu, Hajiya Bilki ce ta ɗaure gindinsu ta kuma mara musu baya aka daina kai Hamal skull a motar koda za ta makara ne sai dai ta hau napep ta tafi.Lokuta da dama tasha rasa lactures ɗinta,amma haka nan take haƙuri gashi da zaran ta dawo komin gajiyar dake tare da ita haka nan zata shiga kitchen tayi girki wataran ana kiran magrib zata shigo gidan tana aje hijab ba za a bari ko sallah tayi ta huta ba zata faɗa kitchen.Wannan kuma umurnin Mami ce duk da cewa tana da masu aiki har guda 2,su kansu su Iya na matukar tausayin Yarinyar tare da ganin matuƙar juriya da haƙurinta.Hamal department ɗinsu ɗaya ne dasu Badeeya da Afnan,course ɗinsu ɗaya da Hamal ɗin kuma suma sun kasance Yara masu natsuwa da kamin kai gasu da ƙoƙari matuƙa hakan yasa Hamal sakin jiki dasu har sukai wani irin shaƙuwa taban mamaki.Da sun fito daga lecture zaka samesu tare suna ƙarawa junansu sani,tare da tattauna rayuwar yau da kullum.Dukkaninsu a cikin congo gidajensu yake suna maƙwaftaka da Juna,sunyi suna a department ɗinsu baki ɗaya kowa ya sansu sabida ƙoƙarinsu domin sune kan gaba a koda yaushe idan anyi exam.Sosai ake matuƙar respecting Yaran yayin da wasu ke hassadarsu da kira musu girman kai, sabida basu kula kowa abinda ya kaisu kawai suke.Har kawo yanzu da suke level 2 ba a taɓa ganin saɓani ya shiga a tsakaninsu da juna ba,kuma zuwa lokacin su Badeeya sun daɗe da fuskantar halin da Hamal take ciki na takura da matsi daga kishiyar Uwa,suna kuma bata shawara tare da ƙarfafa mata guiwa akan ta cigaba da haƙuri.
CIGABAN LABARI...
yau da Abba yayi mata albishir na amincewa da komawarta hostel sai ya sakata cikin matuƙar farin ciki har tana jin cewa a yanzu ne za ta sami lokaci ta sake maida hankali akan abinda ya kaita gabanta,tana jin a yanzu ne za ta sami ƴanci daga matsi da takurar Mami da take fuskanta a baya.Tana ji a cikin kanta cewa a yanzu ne zata sami natsuwar zuciya gurin ganin mafarkinta ya tabbata na samun ilimi,hakan yasa suna fitowa daga lacture ta dubi ƙawayen nata domin yi musu albishir bayan sun isa inda suka saba zama gaba kaɗan da department ɗinsu.Guri ne mai ni'ima da daɗin zama sosai,Afnan ta fara duba tana fadin.........✍🏻