✦ 𝘿𝘼𝙍𝙀 Ɗ𝘼𝙔𝘼 ✦* _ 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂𝒏𝒚𝒊 𝒃𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆._ Soyayya 💔💔😍
LAST FREE PAGE'S 1️⃣6️⃣⏩1️⃣8️⃣
by @prettys01
*LAST FREE PAGE.*
PAGE 1️⃣7⃣⏩1️⃣8⃣.
_______Ya fi hour a kwance kafin ya farka, ganin har drip an ɗaura mai, iskar ya furzar sannan ya fizge ruwan da aka sa mai, yana zaune amma ya tafi wani duniyar, ji yake kaman komai a mafarki, ace wai su Ruhaima sun mutu, mutuwa fa, girgiza kai ya fara yi, sai a lokacin ya ji sautin ringing ɗin sa, ya janyo wayar kiran na kashe wa, kuma 3 missed call, kafin ya yi wani yunƙuri aka kuma kiransa, pecking ya yi badan yasan ko zai iya magana ba.
“Khaleed......Kana ina?." Ya ji muryan wani babban mutum cike da damuwa. A hankali ya buɗe bakinsa.
“Mustashfa (hospital)."
“Alhaji fa? Kuna tare?.”
“Eh."
“Wani asibiti ne." Besan waye ba amma yana zaton dan uwan Alhajin ne, address ya bashi, yana kashe wayan ya miƙe, zuwa lokacin har asibitin ya samu sauƙin mutane, ɗakin da aka shiga da Alhajin ya shiga, har lokacin yana kwance, ruwa na shiga jikinsa, sai wasu hawaye ke fita daga idanunsa. Jin shima hawayen na gangarowa daga nasa ido ya sa hannu ya share, tare da nufan Alhajin, hannusa ɗaya ya riƙe a cikin nasa, take hawayen suka ci gaba da zuwa kan hannun Alhaji.
Ba zai ce yasan iya lokaci da ya ɗauka a haka ba, jiya yi kawai an dafa shi ta baya. Da sauri ya ɗago yana share hawaye.
Ganin babban mutum, shima hawayen yake yi, sai ya rungumesa dan aladarsu ce.
Sun jima kafin ya sake sa, sai ya matsa kusa Alhaji, numfashi yake saukewa a wahale, girgiza kai ya yi cike da alhini.
“Zan tafi da shi, yana buƙatar masu kula dashi sosai, yana buƙatar ya jin ɗinmin mu, yana buƙatar rarrashi." Ɗaga mai kai kawai Khaleed ya yi.
Cikin minti 20 aka sallame su, sai Airport, a ciki aka sanya Alhaji dake kan gadon asibiti.
“An ce sun ƙone sosai, ko gawarsu ba zamu iya ba, malamai dai sun sa a haƙa babban rami wanda zai sanya wasu da part ɗin su ya tsaya, an kashe hanyar gaba ɗaya, ka dai musu addu'a, insha Allah da Alhaji ya samu sauƙi zai dawo, ka kula mai da gidansa, harkokin aikinsa kuma zan san abin yi." Har lokacin hawaye kawai yake sauka daga idanunsa. Da haka wannan mutum ya shiga Jirgin sama, yana shiga jirgin ta fara tafiya sai sararin samaniya. Ganin haka ya bar waje jiki duk a mace, sai da ya yi sallar isha'i, sannan ya nufa Station ɗin motar Alhaji ya ɗauka ya mai da gida, sannan ya kuma dawowa ya ɗau wanda yake driving zuwa gida.
Daga shi har Yà Rasheed babu wanda ya yi magana haka suka zauna su biyu na tsawon lokaci kowa yana tinanin su Ummi. Mace mai mutumci, mai daraja , mai murmushi, ga kyautatawa, wai ita ce yau ta rasu da yaranta har uku. Abin ya musu girma akai sosai.....
________Cikin ikon Allah, zuwa 10:00pm na dare suka iso lafiya, sannan a babban asibiti aka ba Alhaji gado, zuwa lokacin har Noor ta dawo cikin hayyacinta sai dai kuka da take yi, ganin Alhaji na kwance kaman matacce yasa ta kuma rushewa da matsanancin kuka mai shiga kai.
A wannan ranar mutane da yawa ba suyi barci ba, wanda suka yi kuma sun yi ne bana daɗin rai ba, domin gobar nan ta raunana zuƙata da mugun yawa. Ciki har da su Ammeey, da su Khaleed, dan yarda suka ga rana haka suka ga dare.
*BAYAN SATI BIYAR*
sai a lokacin Alhaji ya dawo cikin hankalinsa, aka sallamoshi da ga asibiti, sai a ranar yasan ya har Kuwait City. A haka suka koma gida suka masu jin ɗan daɗi ganin Allah ya tada kafaɗar Alhaji, sai dai baya magana, amma doctor ya ce zai fara magana su bashi kwana biyu.
Abinci Noor ta haɗa mai ta bashi, ba musu ya amsa ya kuma ci amma ko aleef bece ba. Haka dai suka ci gaba da hurɗoɗinsu cikin rashin walwala.
________Tun washegari ranar ya shiga babban falon shi da mai aiki, Zuwaira, komai suka kintsa sannan ya kulle ɓangaren. Gidansu ya koma amma kullum sai ya leƙa ya duba lafiyar gidan, dan duk ya sallame su, akan idan Alhaji zai dawo duk zasu dawo kan bakin aikinsu.
Dama be da yawan magana tun faruwar abin ya kuma zama silent sosai dan ma yana jin ana samun ci gaba da jikin Alhaji, dan suna waya da Abbeey.
______Haka rayuwa ta ci gaba Alhaji yana ƙara warware wa sosai, a yanzu har magana yake yi, sai dai cikin zuciyarsa tunanin familynsa yana addabar sa amma da taimakon addu'oi da nasiha akan tawakkali yasa ya samu sassauci. Yana magana wani lokacin harda murmushi, amma da ya yi sai ciwon dake cinsa a cikin ransa ya ƙara tado mai.
Shi ƙadai ne zaune a falon ya lula duniyar tunaninsu, da irin hirar rakinsu na ƙarshe.
“Da kun dawo zan baki a baki, dan girkin ya yi daɗi.” sai ta ce mai.
“Hmmmm nasan ka fa, turomin da hoton gani." Kafin ya ce wani abu Ruhaima ta amsa wayar.
“Abba na ƙosa mu dawo na nuna maka agogon da Aunty Noor ta shiya naka da kuma....” Abdulraheem ya fizge wayar.
“Abba, ka zo ɗaukan mu zan siya maka abu a hanya, na yi kuɗi."
“Waya baka kuɗi?.” ya faɗa.
“Aunty Noor."
“Abbana, Abbana, ni zan rage maka duk abin da na ci.” faɗin Abdulrahman. Haka dai suka sha hira ashe shine hirar su ga ƙarshe.
Lumshe idanunsa ya yi sai kuma ya buɗe, Ammeey da ta iso falon ta faɗa ɗa murmushi.
“Ammeey Barka da fitowa."
“Yauwa Alhaji, ya ƙarfin jikin?."
“Sai dai na ce Alhamdulillah kawai, sona ke zuwa jibi na koma Ƙuwait.”
“Masha Allah ai haka muke so, Allah ya kaimu."
“Ameen."
“Assalamu alaikum.” a tare suka kalla Noor wacce ta shigo, fuskarta a haɗe yake wanda daga muryarta suka fahimci haka, tana iso ta kallesu ta ce.
“Ammeey, sannu da gida, Akeena." Sai ya yi mata murmushi kafin ya ce.
“Uktheey waya taɓa min ke ne naga sai kumbura kike yi.” sai ta zauna a kusa da Ammeey tana furzar da iska daga bakinta.
“Wani ne ya ɓata min rai a hanyar dawowa." Ammeey da Alhaji suka kalla juna suna ɗan murmushi dan sun san komai, kafin Ammeey ta yi magana Abbeey ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, suka amsa, zama ya yi yana cewa.
“Lafiya kuka zuba ma Noor ɗita ido?.”
“Abbeey kai ma kasanta, yanzu ta shigo muke tambayarta ba'asi.” faɗin Ammeey.
“Noor me ya faru?." Zuba mata ido suka yi, sai ga hawaye ya zubo daga cikin idanunta, abin da ba ɗabi'ar ta bane, ko da me mutum zai mata.
“Subuhanalla, Noor lafiya." Ya faɗa tare da miƙe ya isa kusa da ita, yana ma Noor kallon ƙanwarsa ta jini ne. A hankali cikin kuka ta fara cewa.
“Nace banson soyayya, banso! Banso!! Su dena kulani, zafi hakan ke min, ace kullum sai ance ana sona..... Abbeey na gaji, na ce banso." Sai ta kuma fashewa da wani kukan, ta jima tana rerawa, su kuma duk suka zuba mata ido, Abbeey dai jinjina kai kawai yake. Tana gama kukan Alhaji dake gefanta ya ce.
“Noor idan ba ki yi aure ba hankalin mu ba zai kwanta ba, kuma ba muson miki auren dole......" Da sauri ta katsesa.
“Akee, wallahi ko waye zan aura muddin ba zai takura min da sunan soyayya ba, Ni Ko Baba me gadi ne wallahi ku aura min, amma banson kowa.”
“Noor ki natsu, aure ba wasa bane, aure ba wajen zuwa bane ki dawo, rayuwa ce ta har abada...."
“Ammeeyna na sani, na san da haka, kawai ni......”
“NOOR!!!!!." yarda Abbeey ya kira sunanta ya sa ta natsuwa kuma ta zuba mai ido haka sauran, sai ya furzar da iskar bakinsa sannan ya ce.
“Ko waye na aura miki ya yi?." Da sauri ta amsa.
“Eh." Baki Ammeey ta taɓe dan kallon Noor take a mara hankali.
“Tambaya ta ƙarshe, kowaye kin amince?."
“Abbeey ko tsoho ne na yarda." Sai ya rufe idanunsa sannan ya buɗe yana kallon Alhaji da shima yake kallonsa.
“Za ki aura Yayanki, Alhaji?.” A tare Ammeey da Alhaji suka kalla juna da zare ido, ba su gama mamaki ba balle su tambaya Alhaji dalilin haka su ka ji ta ce.
“Wallahi! Wallahi!! WALLAHI!!! Ni Noor na amince, na yarda, ai dana yi auren shi kenan ba wanda zai kuma furta yana sona." Hatta Abbeey da ya yi tambayar sai sakankance ta kallonta. Da haka ta miƙa tsaye tana kallon Alhaji.
“Akeena na san yasan Ni, zan kula da shi yarda ya dace, ba buƙatar dogon zance domin yasan halina kuma zai zauna da ni, Ammeeyna....Abbeeyna kun min zaɓi na gari Allah ya biya ku." Da haka ta juya ranta sake zuciyarta fes ta nufi part ɗinta.
Bayan shigarta duk sunyi jigum-jigum, kowa sai kallon juna suke.
“Abbeey, ina ga mu neman ma Noor magani ko tana da iska, kaman ba ta cikin hankalinta.”
“Hmmmm Akee, hankalinta lau yake, haka Allah ya yi ta, ba wani iska, kawai ina dai roƙanka abu ɗaya ne tak.........”
“Abbeey tsakani na da kai babu roƙo ai, faɗa min kawai." Sai Abbeey ya ɗaga mai kai.
“Za ka aura Noor?.”
“Hmmm ƙanwata ce, ba zan iya aurenta sam....."
“Akee! Ni da nake uwa a wanta jima ina roƙanka dan Allah dan Allah.....” da sauri Alhaji ya riƙe hannu Ammeey.
“Ammeey kuna ɗaure ni da jijiyoyin jikina, Noor fa..... A'a dai, na yi alƙawarin ba zan sake aure ba, gaba ɗaya Ni yanzu lallaɓa rayuwa nake, kullum cikin tunawa nake da iyalai na, bazan iya aure ba dan ba zan iya ba mace kulawa ba, ku shaida da ne akan yadda nake yanzu.” ya kai maganar ciki da rauni, su kansu duk sai jikinsu ya yi sanyi.
“Alhamdullah ai hakan ya yi, haɗin zai yi, irin yarda Noor nake so kenan, dan Allah Akee.....” da sauri ya matsa kusa da Abbeey.
“Kaifa kaman uba kake a wajensa, na amince.” ya faɗa yana jin babu daɗi. Rungumesa Abbeey ya yi yana kuma cewa.
“Nagode Akee, Allah ya biya ka, dama ina so na maka aure kafin ka bar JIDDARH, dan rayuwa kai kaɗai ba zai ma daɗi ba, kana buƙatar wani a kusa da kai, na gode.”
“Abbeey ba komai.” da haka suka tsaida washegari za'a ɗaura musu aure, sai jibi su nufa *KUWAIT* .
_______Murmushi ya saki a natse, yana ji a jikinsa ya kusa haɗuwa da gimbiyarsa, kawai a jikinsa yake jin haka, yana so ya cika ma Ammaa burin ta, ya yi aure da haifan mata jika. Tashi ya yi daga kwancen yana shafa tarin lallausar gashin gemunsa, sai ya ji wayarsa yana ringing, ɗauka ya yi bayan ya ga sunan Alhaji na yawo akan screen ɗin.
“Alhaji Barka da wannan lokaci.” ya faɗa bayan sun gaisa da shi, ba ƙaramin daɗi ya ji ba da Alhaji ya samu lafiya, sannan a jiya duk masu aiki sun dawo bakin aikinsu dan a satin nan ya ce zai dawo.
“Lafiya lau."
“Ya ƙarfin jikin?.”
“Alhamdullah, gobe insha Allah ina nan tafe, fatan komai yana tafiya dai-dai.”
“Eh Alhaji, Allah ya kaimu."
“Yauwa Ameeen, sannan ka sanar ma mutanen dake kusa, akwai walima idan na dawo, dan zuwa anjima kaɗan za'a ɗaura min aure." Ya faɗa cikin wani irin yanayi, harga Allah har cikin ran Yá Khaleed ya ji daɗin haka, dan kuwa yasan yadda mutuwar nan ta yi mai dafi ƙwando ko ya ya ne idan akwai mace a kusa da shi.
“Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi, gaskiya na taya ka murna."
“Hmmm ka shirya dan kuwa dana dawo kai ma dole ka fito da wacce ka ke so, ni zan ɗauki nauyin komai.” murmushi ya yi ya kuma shafo kashin kansa.
“To Alhaji, Allah ya ƙara ma dukiya albarka."
“Ameen." Da haka suka yi sallama, aje wayan ya yi yana kuma sakin wani murmushi.
“Ya Allah ina roƙanka ka haɗani da macen da za ta dace da rayuwata, da za ta soni fiye da misali, ta ƙaunace dangina. Allah Ameen." Da haka ya tashi yana mai fita compound din gidan dan ya duba flawers dake buƙatar kula, sannan ta ɓangaren Swimming pool Alhaji ya zuba kifaye wanda shi ke kula da su.
“Rayuwa kenan, wa'inna saboda su Ruhaima na so ne Alhaji ya sa, Allah ya jiƙansa, haka Allah ya so." Ya faɗa yana tunawa da su, dan kuwa Alhaji duk abin da yake nema na duniyar nan duk saboda yaran ne, ashe ba su da rabon cin wannan uban dukiyar.....✍️
END
> *Allahu Akbar 😓, dama haka rayuwa take, yau kai ne gobe wanin ka, mudai yi fatan gamawa da duniya lafiya. Allah ya jiƙan wa'inna suka rigamu gidan gaskiya, yasa suna aljanna suna dakon isowarmu, ya sa idan muma tamu ta zo mu cika da kyau da imani 🙏😓😓😓*
*THE LAST FREE PAGE'S*
Ga duk mai son ci gaba, da ganin irin dramer da zai biyo baya ya kasance a kashi na gaba tare da PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️.
_₦300 shiga privet group Wanda zan ci gaba da posting, idan kuma na gama ₦500 ne Complete. ga duk mai so kawai ya min magana already wasu sun fara biya, Allah ya ba da ikon biya. Ameen._
```
1. Za su ko ku ji shin auren zai yiwu ko yaya?
2. Idan an yi auren ya rayuwar NOOR za ta kasance?
3. Ko dai ma baza a yi ba?
4. Karku manta tauraron littafin shine Driver, na gidan Alhaji, hmmmmm za dai muga yadda al'amarin zai wakana.
5. Yã Khaleed yana son mace wacce za ta so shi fiye da misali, hmmmmm zai samu ko yaya ne?```
*Mu dai haɗu a can, 500 ne only*