28
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE 💫
Arewabooks@surayyahms.
⏯️2️⃣8️⃣
miƙewa uncle moh yayi dakansa ya bude ma anty safeerahn kofa ta karaso ciki ahankli tana takallonsa da mamakin ganin twel ne akugunsa kuma ko mai bai shafa a fatarsa ba gashi ita taci kwalliya tay mugun kyau tasaka lavender colour silk nity, tanakan kallonsan ta karaso ciki da yangataccen muryanta me dadi tace"babe ya naganka haka, ko mai fa baka shafa ba..wani irin riko waist dinta yay abazata tareda sakin karamin sexy smirks mai dauke da sigar rashin gaskiya dake tattare dashi a zuci yana sakin wata yaudarriyar murmushi harsaida ya ga ya matsota jikinsa yakankameta sosai yanamai shakarrrrrr dadaddar qamshin jikinta a mugun kasale snn yace"i am feeling lazy ne sarautar mata, dama ke naketa jira kixo kidan taya ni shafaman ki sosa mai har tsakiyan bayana, yana fadin hakan ya sakar mata wata erotic kiss agefen wuyarta wanda yasaka saida ta dauke numfashinta cakkkk idanunta a limshe sann tajuyo tagabansa tarike hannunsa cikin nata tana masa wani irin murmushi me sanyi tace toh ai tunda nazo sai muje ko?kafin ya amsa taja shi gaban mirror ta zaunar dashi snn ta dauki lotion din ta zuba a hannunta ta mulmula shi dakaau tafara shafa mai a kirjinshi har zuwa hannunsa da gadon bayansa ta dawo har fuskansa tana masa yawo dashi shikuma yana lullumshe ido yana sakin karuwar nishi yana murmushi
wanda duk tadauka tsabar dadin abunda take mishin yasaka ya gama sakar mata jiki bata san haryanxu tunanin maganan sa da alhaj ameer yakei akan posbiltynsa na samun ayaanah a matsayin future wife insa ba,.
sosai abun yafara shigewa ransa dan shikansa har mamakin kansa yakeji dayau yau kawai yaga yarinya amma duk ya birkice gabaki daya yakasa samun nitsuwa, har ji yake inbe sameta ba da wuya ne ma ya kara aure nan gaba bcos ayaanahn has a perfect age calculation for his future life nd sexual enjoyment, shi dama duniyar nan bai dauketa wajen shan wahala ba yaxo duniya ne yanemi azirki iya arziji snn ya kashe kudinsa ya aure kyawawan mata tsirara yan gayu wanda zasu haifa masa kyawawan yara
ynx lokcine dayake ji da damshin kuruciyarsa kuma yana kan morar soyayya da kulawar safeera, nd by the time ayaanah is riped yasan dole ne ace safeera ta fara gajiya ko kuma tsufa kyanta da dadinta akan gado duk ya ragu, shikuma by then ya kara age yagama riƙa ya zamo cikakken namiji sai kawai ya dora shagalin rayuwar jin dadinsa da sabuwar jini,inyaso sai itama ayanahn ta haifa masa kyawawan yara kuma yasan zai more jikinta sosai harya tsufa..
slowly anty safeerah ta tsuguna agabansa da moisturizing lotion din tana mai shafamasa akan farare sol din cinyarsa wani yarrr kawai yakeji ajikinsa yana ash ashhh baima barta tama gama ba ya wani sungumeta cak ya haura da ita kan babbn gadonsu ya fara wani irin romancing dinta tare da lular da ita duniyar ma'aurata...
Durzanta yay dakyau har saida bacci ya kwaceta ahannunsa kafin nan shima yabi yakwanta agefe da ita basuda farkawa ba sai can wajajen asubahi shiya fara tashi yay wanka ya fita masallaci kafin nan itama ta mike tay wanka tay sallahn fajr har saida ta gyara masa dakin tsaf ta saka qamshi snn ta fito tawuce dakinta domin shiryawa.
dake mujaheed yay latti yau sai baije masjid ba uncle moh yana idar da nashi sallahn kai tsaye yanufi wajen mahaifyar sa hajiya mairo, zuwa yay ya sameta akan sallahya tasha wani babban hijabi da carbi a hannunta tanata addua already ammi karama hartazo ta kawo tray na kayan shayi ta aje mata ta fita. haryaxo yazauna akan soft one seater leda chair hjiya mairo tanakan adduarta tana idarwa kuwa tay salati tashafa a fuskarta kafin nan sukafara gaisawa
cikin nitsuwa ya kara mata gaisuwar gajiyan hanya daga nan kuma kafin kace wani abu ta jawo tray din shayin ta deba masa hadadden tea din shima suna fara sha tafara jan sa acikin hirararrki
shiru yay yanajinta harta gama kafin ya fara mata tambaya akan iyayen ayaanahn wanda kamar jira take tafara bashi labarin tragedy na abunda ya faru dasu tun farko wanda duk dama bata wani toni asirin rayuwarsu deep deep ba amma cikin jimami ta sanar dashi cewa mahaifin ayaanah ba mutumin kirki bane, uwarta ce mutuniyar arziki kuma sanadiyar muguntansa ne ma har aka yanke hukuncin kawo ayanan birni bayan da ciwon appendix me tsanani yasaka yar uwarta inaayah ta rasu...
bai nuna mata komi a fuskarsa ba face tausayi, sai kawai yay shiru yana amsa tada jimamin shima tareda tabbatar mata cewa duk suna tare da ita
akan ayaanah, kuma zasu dauketa tamkr jininsu agidan nan, in yana raye ayaana bazata rasa komi na duniya ba...
cikin jin dadin furucinsa hjy mairo ta dinga saka masa albarka suna yi suna shan shayinsu atare cikin jin dadi
6:00am dot mujaheed ya farka daga bacci da kyar shima sabida alarm din gefen gadonshi ne daya damesa da kara yatadashi tashi yayi ya shiga bathroom dinsa, yadade aciki kafin yafito cikin wani white bathrobe wanda ta amshe kalar fatar jikinshi dats so white nd soft kamar wani baby, zama yayi abakin gadonsa ya shiga shafa moisturixing creams da hand cream dinsa mai kamshi sabida shi asali farin fatarsa me haske sosaine kominsa ahankli yakeyi yana bin ko inan sa a tsanake
Can sannan yatashi ya nufi wardrobe dinshi yaje yabude yaciro wani lv underwears da wata baqar logo print t-shirt na parco rabanne yasaka da damammen wandon jean baki dayan bangaren rigunan sanyin shi ya duba yana tunanin wanda zai saka kafin yajawo wata long field coat wanda yasaka ta akan rigan cikinshi tazauna ajikinshin tamai kyau sosai
designers pefs dinsa ta original Creed aventus ya ferfesa sannan ya shimfida dadduma yay salla yana sallamewa yaji kamar ana bugamai kofa..
Wani yatsine fuskarsa yayi sanin bazai wuce mum dinsa ba dan yasan tafi kowa son ya dawo sabida make up busines inta datake kkrin tadawa
da kyar cikin kasaita yace "come in" bude kofa akayi da mamki yaga sultana snn yaga kulthum abayanta da wata creature data sakashi miƙewa tsaye batare da ya shirya ba.
dukansu english wear ne ajikinsu sultana ta saka riga da wando, kulthum da ayaana duk skirt ne ajikinsu da decent long sleeve shirt na sanyi da hular sanyin shima...sultana tace yaa MJ can we come in?? idonsa nakan ayaanahn data ke baya baya ta sunkuyar dakai kusan a rude da kyaunta yace "uhh..aha..,kushigo mana yan matana sai ku gayamin jiya ina kuka je harnazo gidan nan ban ganku ba. kulthum tana karasawo ciki da gudu tana dan murmshi ta rungumesa tace "i missed you" ya dagata sama yace miss u too sis
..yana ajeta suka sha hannu da sultana cheerfully tace good morning yaa MJ nd i hope u bot us a gift? yana dariya yace sure miss chop chop..idonsa nakan ayaanah yace wann kuma wacece? waving mata hannunsa yay ganin ta kasa motsi da alama kmr kayan ne kwata kwata bata saba dashi ba
yace "Hi...kulthum ta jawota har gabansa tace hey ayaanah wann fa yaya mujaheed din mi yana miki magana ki amsashi.
dakyar ta daga ido ta kallesshi
bai iya contrlng kansa ba yace wowwwwwww.
kulthum tace she is our ayaanah..she is our new sister.
ahnki yace "really? wow wow
ya miƙa ma ayaanah hannu sai yaga bata bashi nata ba, ahnkli ta kallesa tace "sannu yaaya"
kwato hannunta yay abazata ya dora acikin nashi snn yace "cool face nd cool voice!.. nd ohh soft skin, sanunnki softie!
su sultanah suka fara dariya.
yace ayaanah ure so beautiful kinsan da haka? tay shiru tana ta kallonsa yace"beautiful and soft..daga yau softie zan na ce miki kinji ko..
itade kallonsa kawai takey fuskarta ba yabo ba fallasa har suka gama surutunsu bai sake mata hannu ba face har saida yazo ciro musu gift din duk ya raba musu manya manyan fancy fancy packs na candies da chokolates daya siyo all the way frm south africa.
suna karba suka masa godiya kulthum tace masa yaa MJ zamuje daki musaka kaya kafin breakfast kar mama tazo taga bamu shirya ba
yace.."tohm kuje nima zanje sashen mammyn ne ynxu..
daga haka suka bar dakin ya bisu daddaya ya musu peg agefen kuncinsu daga ganin murmushinsu zakasan they loved him so much dan duk yayunsu bamai sake musu fuska sosai face shi, har suka bace a dakin baidena satar kallon ayanaah ba.
suna barin sashen shima ya fito kai tsaye ya wuce room din mum dinsa qamshin turaren wuta mai shegen dadi ya baɗe koina yay sallama cikin sanyin murya yasamu dede ta gama saka kaya kenan taci kwalliya tay kyau tana gaban madubi tana daura dankwali
cikin ladabi ya karaso ya rungumeta ta baya jin yadda muryansa yake ratsata yasata ta lunshe idon yace "good morning queen mother" da murmushi tace "mrn my prince..harka tashi?amma yau dai bakaje sallahn fajr bako?
yace yeah yeah i am tired mama, wlh nagaji sosai ko hutun schl banyi ba fa naje games din nan..
da tausayinshi a muryanta tace yeah i know..shiyasa ma ban je dakinka na tashe ka ba ai dama yakamata wann satin gabaki daya ka huta bfr ur final exams and all that stuff dat will start.
dan sake hannunta yay yana kallonta harya jingina kusa da mirror yana cewa hmm ina naga wani hutu agidan nan bayan keda kanki kinfi kowa matsuwa na dawo gida muci gaba da aikin kin nan. tace "karka ga laifi na fa mujaheed, inban dage ba make up brand dinnan wallah bazai tashi da wuri ba, and all my friends are far far ahead of me ni natsaya inata rainonku banyi komi makaina ba..cikin kyabe baki yace but i am here for you, nd in sha Allah naki brand din sai yafi na kowa saurin karbuwa karki damu
..tana murmushi tace thank you mujaheed ure alwys kind with ur words to me..wai kunma hadu da kulthum kuwa?hmm kulthum anacan anata kawaye nikaina bata son kulani sosai..
yace eh yanxu nan fa sukazo daki na
sighing a pause yace mama dama wai yarinyr kauyen da hajiyan take magana akai kenan? damn, bansan ko idona bane but she looks..i mean her beauty is so calm nd eatheral..
..Dariya me sanyi tay tace' i know ryt..nima da naganta a farko saida nayi dana sani da ban karbeta agidan nan ba
..she wud have been the perfect face for my make up brand ko ya kagani? dama bana son images din A.I dinnan nafison real face. inda kuma ace su ammi karama zasu bani dama...
cikin katseta mujaheed yace cant we ask them, she is part of this family now ryt? ajiyan zuciya tay tace"yes, amma kuma karka manta yarinyace tunda ba ahannun mu take ba ai bamusan plans din da suke shirya ma ryuwarta ba amma inda ace zasu bani dama with ayaana's face i can click a very big start..
gyaran muryan da sukaji ya saka dukan su dagowa uncle moh ne ya shigo dakin da black jallabiya ajikinsa fusknsa babu yabo babu fallasa yay sallama suka amsshi kusan atare
mujaheed yay kansa kasa cike da ladabi yace"..ina kwana baba..kallonsa yay snn ya amsa ya kalli anty safeerahn da murmushi yace maganan me kukeyi hakan naji sunan yarinyan nan aciki
tace ohh dama wai suggesting fa mukeyi ko in hajiya zata amince inyi amfani da fuskrta wa sabon brand dina kaga insun amince kawai sai amata make up da photo shot ta zama face of the brand
karkada kansa yay yanamai kyabe baki a cikin yanayinda dukan su basu gane ba yace
"this is a joke ryt???
mujaheed zai magana ya daga masa hannu cikin katseshi yace wann ai maganan banza ce safeerah. ynxu ke akace ki saka fuskar yarki a internet kina yawo dashi kina tallan kyanta wa dubbanan mutane zaki so?
zatai magana yace look safee, this little girl need to be protected not advertised..her beauty shud be for the benefit of this house nd in sha Allah agidan nan fa zamu aurar da ita.. haba da Allah kuyi amfani da senses dinku mana.. daga zarar kunfara tallata idon duniya maza ne dayawa zasu fara jin sha'awar shigowa ciki
kawai..kubar wnn mgnan banzan ni banason ma naji wann batu yafita a dakin nan
yana gama furta hakan ya kama hanyarsa ya fita anty safeerah data tsaya cak da mamaki ta dinga bin bayansa da ido har saida ya bace mata kafin ta dawo daidai..
cikin kyabe baki tace kome ya sameshi ooho tunda yarinyar nan tazo yake ta ce wa su hajiya lallai agidan nan zasu aurar da ita, toh in ba'a agidan nan Allah ya aje mata mijin qaddararta ba fa?..ynxu ni ina zan samu me perfect face irinnata.
dafa kafadunta mujaheed yay gently yace" karki damu, i think he has a point. kawai kibari zan ma ibaad magana in ya amince akwai wata fine babe datake mutuwar sonsa a schl dinmu sunanta shakira if he can ask her for ur sake wallah zatay sabida kyakkwa ce sosai kuma tama fi wnn girma.
cikin zare ido tace hmm ibaad din ko? ohh pls mujaheed just forget abt it kawai ...anan fa zainab arifah da kyanta da kwalisarta ga kudi tace tana sonshi amma yayi zuciya ya dau bulala ya zaneta har saida yasata ciwo...nide ka rufa min asiri da lamarin ibaad wallah kafin kaje ka jawomin babban case awaje...
yace toh saidai ayi na A.I in kenan, sounding pissed tace yeah! what ever. sigar lallashi yace haba mama karki fushi
wayasan ma nine zan aure ayaanahn kinga inta dawo matata kuma surkuwanki wallah har kyautarta zan baki kiyi duk abunda kikeso da ita.
Dariyar bazata ya kufce mata tace"naji,Allah yasa ka auretan koma ace ka aure wacce ta fita kyau da dogon gashi..
..murmushi yay da mamaki a voice nashi yace "seriously u wont mind in na auri ayaana?
tace 'yeah toh meye aciki aikaine ma kayi daidai da ita
..age gap dinku will be jst lit...
dariya yay har da sosai keyansa sai yaji abun ya mugun tsaya masa aransa sosai...
jiranta yay ta kammala duk wani abunda zatayi kafin su fito daga sashen uncle moh ma har yagama shirinsa ya saka coffer brown shadda yaci kwalliya ya fito, kusan duka aka hadu a ashen hajiya mairo. wajen yabi ya cika da surutu sabida tunda su ayaana suka shirya kansu suka fito gaishe da ammi karama anan wajen hajiya mairon kawai suka tare dukansu jikoki mata suna ta surutunsu har sauran mutanen gidan suka karaso, anan ne su ayaanah suka gaishe da uncle moh da anty safeerah, cikin su duk bata gane wayafi sake mata fuska ba. duk sai taji daban, tuna gidan su sultana tunda taje hantara da sharri kawai ta karba awajen ammi babba amma nan gidan sai taga kamar kowa da kowa yana haba haba da ita ana mata kirki sosai..
ammi karama ce ta harhada musu family breakfast yau sunday dakanta tay komi dan haka kafin 8:30am duk tagama ta shirya abincin da dan yawa sabida tariga da san bappa zaidu yace mata zaizo shima
aikuwa tun ba agama zama a dinning ba saiga shinan shida maheer da ibaad ammi babba ce kawai bata biyosu ba haka duk yaran suka rusuna sukayi gaisuwa akaci abincin cikin lumana da jin dadi, sede tunda mujaheed ya zauna banda tunanin maganan mamansa akan ayaanah babu abunda ya cika mind insa, saidai bai sano ba ayadda yakekan satar kallonta da wann burin aransa hakanan ma ubansa yake sakawa aransa aboye....
ana kammala cin abinci ba akira masu aiki ba su ayaanahn kawai ammi karama ta umarcesu akan da su kwashe komi sukai kitchen wa masu wanke wanke.
Dukansu hudun haka suka tashi suka kwashe saidai haryanxu safiya ce kawai agidan batama ayaanah magana snn koyaushe suka hade ido sai ta watsa mata harara mai zafi.
yaran suna watsewa ammi babba ta karaso tasako jan abaya ta caccaba fuskarta da kwalliya tazo ta gaida hajy mairo, nan aka bar zallan manyan gidan tare da zallan yara mazan kawai a tsakiya
da mujaheed, maheer da ibaad kowa kansa na kallon kasa ayayinda bappa zaidu yay dan fadakarwa da jan hankli akan karfafa zumunci da kaunar juna, shide uncle moh baiya cewa komi sai dai yay noding
har hajy mairo ta fara mata magana..itama nasiha ta musu me ratsa jiki, acikin salo mai sanyi tahau tunashesu yadda mutuwa ya ɗeiɗeita rayuwar yarta taawure nd how she is forced to run away witout her kids, tana magann tana kallon ammi baba tana cewa "Duk wata macen data walakanta yaran wasu a duniya toh tasani itama wata rana zata iya mutuwa tabar duniyan nan, kuma bazata taba sanin awani hannu yaranta zasu fada ba ..
duk dai ta gama wa'azinta tace musu tasan duk ita ce mai daura musu nauyi amma suyi hakuri duniyan nan ma nawa take da zaka zuba ido yaran wasu su lalace... duk dai ta musu waazi akan akula da taimakon juna da kuma mutanen waje. acewarta Allah ya basu daukaka da arziki ne badan su ci sukadai ba dan haka dolene su hada hannu ataimaka ma alumman dake neman taimako awaje.
duk wann wa'azika masu dumbin shiga jiki da akeyi a baibai ammi babba take fassarasu aranta.
take takawo tunanin ko har ammi karama ce takai gulmanta awajen hjy mairo wanda har yasaka aketa mata habaici akan yadda ta rike ayaanah .ita kadai sai hararar kowa takey, guilt nata cinta acikin zuciyarta har hajy mairon ta gama waa'zinta bappa zaidu da uncle moh suka fita duba wokers estate din atare dan su duba lfyar baƙin hajiya kuma dama sun saba sukanje ziyara da suka saba zuwa ran sundays wajen wasu tsofin manyan aminan mahaifinsu dasuke raye hr yanxu.
wasunsu sukai musu sadaqa wasu kuma masu mulkine da dukiya sune ma sukekan bude musu hanyar samun businss connection kala kala, dan haryau dan uwansu na ciki daya wato prof zayyanu babu ruwansa da taimakon uban kowa acikinsu inbawai a bashi zai musu taimakon ba.
ficewarsu bada jimawa ba ammi babba tabi anty safeera sashenta har uwar daki suka shiga bata zaunana ta dinga masifa tana zage zage tana tambayar anty safeerah wai ta gaya mata gaskiya kawai ko fatima takai gulman ta ne hajy mairo ta dage da wa'azi akan tausayi da taimakon yara da marayu tana kallon ta kamar da ita kadai akeyi..
babu bayanin da anty safeerah bata mata ba amma taki sam tace dole dole ammi karama ce tay reporting dinta, ahaka har saida anty safeerah taji dukkan wasu labarin kaf rashin mutuncin da ammi babban tama ayaanah
baki bude ta dinga kallon ammi babban jin wai har ankoret daga gidan miji duk akan ayaanah daga hmm sai hhmmm take amsa mata hirar dashi.
mujaheed da maheer suna dakin ammi karama sunakan mata kwadayin abinci, iyaka ibaad ne kawai akabarsa da hajiya mairon asashenta suna zaune su biyu
bayan har sun gama fadansu da suka saba, ya mugun hade ransa yahau zare mata ido yace mata shide kar ta sake kiran sunansa acikin mutane tanacewa wai ayaana matarsa ce dan bayason abunda da zaina jawo masa kananan magana da raini agidan nan
ita kuwa ko ajikin ta da masifarsan amma ta tubure iyaka ma tsokanarsa take kan karayi tana cewa bazata ma bashi auren ayaanahn ba koda kuwa yazo yana so daga baya
..karshe shiru kawai ya mata tanata tsokanarsa, har sai da dataga kamar bazai biye mata ba snn ta kyabe baki ta mike ta shiga dakin baccinta ta dauko wani takarda tana zuwa ta bashi snn tace masa taawure ne ta rubuta masa wasika ta aiko musu ranar da zasu taho.
Ajiyan zuciya ya sauke cikin dedeta makansa nitsuwa kai tsaye ya bude wasikar yay shiru yana karantawa har saida idanunshi ya tara ruwan hawaye bai daga ido akai ba harsaida ya gama karantawa tass
yafi 2 min idonsa na kallon rubutun harsaida yagama shanye ruwan hawayensa ciki snn ya nade takardan ya jefa aljihun wandonsa yay shiru baikuma ce komi ba.
hanklin hajy mairo duk ya tashi tabi ta zuba uban tagumi takuma kuresa da ido tanata jira taji ya hau mata bayanin abinda yake cikin wasikan dan ta samu na fashewa da kuka sai taga ko kallonta baiyi ba.
duk iya ture bakin datake baiko kulata ba face ma kara hade ransa da yay
kkrin mikewa yay kmr zai fita tarigasa mikewa da muryan raki tana cewa "a'a ah ah haba rayyanu meye haka, wai tafiya zakayi bamu gama magana ba? da wani irin deep voice yace "wani magana? tace maganan wasika manaz yanzu fisabillah sai inma dakon sako tundaga tudu kazo gabana ka karance shi tsaf shine kuma ni bazaka gayamin abunda kuke ciki da surkuwan naka ba.?
hmmm, to yau naji ikon Allah, nida yata taawure za'a nuna min izza akanta to ai kayi a banza, ni dakake ganin nan taawure fa bata boye min komi. cikin katseta yace"toh ai nasan da hakan ne yasaka bazan gaya miki ba, kodama can rainin wayo ne yasaka kikeso nakara miki bayani akan abunda already kika sani?
tace o, o oo..nide bance maka nasan wanann ba wnn ai tsakaninka ne da ita da yarta amma tunda bazaku sakani aciki ba ai shiknann dama ai naga ka iya raino..basai na tsoma maka baki ba.
komawa yay ya zauna yana kallonta yace "babu abunda zan gaya miki. maganin me son gulma kenan, bake kince dole saikinji kome ba?to wallah bazakiji wnn ba.
a mugun masife ta kalleshi toh ni karka dakeni wallah gidan ƴayana nake saina saka suma shegen duka..
yay karamin tsaki cikin saka serious tone yace yaushe xaki fara fita shagon naki.."tagumi tay kmr bazata amsashi ba tace" nan da sati biyu zuwa uku dan zaidu yace min ya gama komi, a cikin satin nan ma nakeso muje da du safeera da fatima da yaran nan sai muga wajen..da muryan kuka tace Allah dai ya ma zaidu da muhammadu albarka yaran nan suna dawainiya dani...
har zata kara fashewa da kuka yatare ta da masifa yace "haba ke kuwa hajiya ya isa haka mana kefa kinfiyeson kuka kina cikamin kunne wallah..
regardless of masifan daya matan ta kara fashe masa da kuka har takama bakin xaninta tana matse hawayenta dashi tana cewa toh shikenan sai bazan sakaalbarka wa yara ba? amfanin auren wuri kenan, inace kwanan kaima aka maka auren wurin a can majiya haka kazo kasani agaba saida aka kwance auren nan, amma da ba akwance ba danan da wasu yan shekaru yaranka zasu tashi suma su saka maka da dumbin alheri irin wnda zaidu yake min sai asnn zaka san menakeji araina yanxu
...kallonta yake kamr xai hadiyeta da harara ahnkli yace toh naji, sun kyauta, saiki mana shiru ko?
babu musu ta share hawayen tare da makalkale wuya tana kallonsa murya gwanin tausayi da salon yaudara tace ayya rayyanu yanxu bazaka gaya min abunda yake cikin sakon nan na tayaka kuka ba?inafa kallonka da gefen idona yadda kayi kifi kifi da idanu kmr zakay kuka kaima..
cikin lumshe ido da budewa yace bazan fada ba kinaji ko?kedai abu daya nakeso kimin ynxu, kinga session na schll yay nisa duk exms zasu fara upper week kuma ana bada hutun sati uku ne kawai. ki kira yarinyan nan pls kuyi magana akan karatunta, intana da wani matsala dake damunta tagaya miki saike kisanar dani dan wallah nasaka a schl taje tay wasa harke ma sai kinji ba dadi .
....da wani irin masiffafen ido ta tsaresa da harara baki bude tace ikon Allah toh wallah karya kakey rayyanu, baka isa ba kace harni bazanji dadi ba, akan me? ubana ne kai? kaifa
duk wani muguntan ka ya kare akan yaran nan amma ni mairo yar gidan malam nafi karfin ka.
mikewa tsaye yay yana kyabe baki har saida ya tsaya snn ya kalleta da gentler tone yace hajiya i am serious abt this, pls u need to have this cnvrsation with her as soon as possible, ni bazata gayamin wasu abubuwan dake yawan damunta aranta ba, amma nasan ke xata iya gaya miki komi kinsan kuma bazaiyu bata gama warwarewa daga grieve ba atura schll.. ask her throughly dan Allah...kinji yar kyakkwan hajiyata?
yadda yay maganan da salon sanyi da yaudara yasa ta amsashi batare da gardama ba haka kuwa har yafice a sashen bai gaya mata abunda yake cikin wasikar ba.
******
bayan kamar kwana biyar kusan duk wani doki da marmari da akey na zuwan hajya ya fara gushewa, ayaana tun tana dar dar agidan har soyayyar datake samu ta kowani angle inta juya yasa ciwon ta ya fara mancewa da ita cos ever since ta dawo family house is always fun nd lovely moments.
haryau anty safeera tana mata kirki sosai tanajin dadi da suke kwana da kulthum a dakinta. musmn ma da taga ammi karama batace komi ba ta kyalesu, sabida ita kanta ammin tanasone ayaana ta zama tana cikin companyn yan uwanta mata da zasuna debe mata kewa. acikin mazajen gidan maheer ne kawai ta lura kamr ya canza mata kadan, dan insunzo gidan gaisawa kawai sukeyi talura kamr anan gidansun yafi bada kulthum kulawa amma bata wani damu ba cos mujaheed is all over her ever since dat day daya ganta kowani safiya shiyake xuwa ya tashe su bacci, tun yanakiranta da "softie" bata amsawa har ta haqura ta fara amsashi sabida tsabar son wasansa da saukin halinsa da kirkinsa da yadda taga har safiya ma tana balain son sakewa da mujaheed din sosai.
kullum da yamma yana zama a falon su haka dukansu zasu fito su mamayeshi suyita masa surutu yana basu game suna bugawa yanamusu kyautar kudi
gidan was fun for ayaanah, ga samun kulawa ga soyayyar kowa da kowa, wanda har saima taje wajen hajy mairo ne take iya tunowa da raywarta na baya, abu daya ne kacal ke yawan tada mata hankli,wanda shine in arana bataga ibaad yaxo gidan ba, amma daga ance mata yaxo kuma toh shikenan sai taji sanyi duk dama baifiye son janta jikinsa yanxu kamr dacan ba.
cikin kwanakin nan babu yadda anty safeera batay da uncle moh akan batun saka fuskar ayaana akan brand inta ba amma yaki mata sam, saima bata kudi dayayi me uban yawa wai saidai tayi investing wajen kara bude wani wajen koyarda makeup sabida idan su ayaanan sun kara girma shidakansa ma xai biyata kudi tana koya musu yadda ake kwalliya da saka kaya.
ita duk bata dau hakan akomi ba murna ma tay dake taji duk kudin goro yay ma yaran bai ware ayaanan ita daya ba,
daga cikin ransa kuwa tanadi kawai yake kanyi makansa yana so lallai safeera tazama itace zata koya ma future wife dinsa kwalisa da kwalliya irin wanda ta iya sosai. ita kuwa tunda ta caske kudi tabi ta mance da zancen fuskar ayaanah and she focuses on building the brand ,in ya tashi yay suna shikenan sai ta fara bude classes din kamar yadda ya fada.
time to time su ibaad suke xuwa ammi babba kam tun ranar da aka musu nasiha taji haushi bata kara zuwa ba kullum kuma hanklinta tashe yake dake kowani safiya ya zama kamr dolene ya zame ma mijinta yana zuwa family house yana duba mahaifyarsa, ita babbann dsmuwarta ba gaisuwar bane baifi yadda zaina kallon fuskar fatima kullum da safe inyaje gidan ba
ahujajan tafara tunanin yadda zatay maza maza adawo da hajiya gidanta, tunda akwai sashe na musmn da ake mata agidan itama
ranar da hajy mairo ta cika kwana bakwai da dawowa birni dukan matayen gidan suka shirya sukaje aka dudduba sabon shago
luxurious traditional local food spot ne da aka narka naira wajen kerashi yayi shegen kyau harma fiye da yadda kowannensu yay tsammani. akwai sashe sashe, da food nd drink compartmt kala kala inda ake saida abincin gargajiya a zamanince, dana zamanin ma da kuma inda akeyin chops da local drink harda tea spot ga wajen barbaque..
sabbin maai'katanta kowa da sabon unform dinsa dark blue nd white colour, iyaka manyan wokers din sukanxo ayita prep ma kananan harda su ruthy acikin wanda ake horasu, duk dai anata shirye shiryen budewa tare da grand openin ceremony next week sunday, sun bada kudade a manyan SM blogs anata musu social media makerting promotions da sauransu, ga office din ceo hajiya mairo me tuwo babba harda lumtsa luntsan kujerun zama, waje dai masha Allah, kowa yay mata murna suka dan dauke hoto as usual ammi babba ne kawai acikin matan bata zo wajen yau ba
dakyar ruthy ta rabu da su ayaanah sabida sukadai kawai ta sani a kano ynxu, duk tabi ta damu musmn ma dataga ayaanahn harta samu masu debe mata kewa sosai. tun anan tay ta rokon ayaana akan taroki hajiya kawai suyi aikin restaurant din atare, wanda tun ayaanah tana ja baya hartace mata xata ma hjy magana
da yamma suka dawo gida can bayan angama cin abincin kowa ya watse ya kwanta
sassafe bayan sunxo gaisuwa ayaana taxo ta lafe ajikinta tanamai sanar da ita yadda sukay da ruthyn akan aikin restaurant..
hajiy tace au har kin gama warkewa kinaso kiyi aiki ko?? da sanyin murya tace mata "ai satin nan sulthana zata tafi gidansu, kuma kulthum tana xuwa makarnta data zauna ita daya gara itama tana zuwa shagon.
cikin kyabe baki hajya tace toh ayaanaj nide bazan hanaki aikin nan ba amma fa dolene sai in ibaad yaxo nagaya masa ya amince.. sabida kinga ahannun mu dukanmu ni dashi uwarki ta mikawa amanar rayuwarki ban isa na yanke miki hukunci nikadai ba.
ayaanah tay shiru batace komi ba, itama hajya tay gum bata gayamata sakon ibaad din ba dan aganinta ai tunda ayaana ta fara tunanin aiki a shago to hala taji lafyarta kalau kenan.
ranar asabar na satin ma zagowa hakanan kowa yaxo family house wekdns yauma asashen anty safeerah zainab arifah yau ta wuni, wani irin xpensive human hair taje ta saka mai tsayi kuma baki kirin irinna ayaanah dan itama tay kyau ta burge kowa dan har ynxu batasan cewa gashin kan ayaanahn natural bane ta dauka duk fixing mata shi akayi dan ta kara kyau
taxo da jiji dakanta saidai tunda taje dakin mujaheed taga gifts din expensive turare da watch data bawa ibaad duk sune akan madubin MJ sai taji ranta ya sosu sosai abun bai mata dadi ba
gashi bata iya boye emotions dinta ba kusan wuni tay dashi
a dakin tana jero masa hilimin complain akan attitude in ibaad musmn yadda yake basar da ita, snn duk abunda ta bashi sai taga yay kyauta dashi
sosai mujaheed ya tausaya mata ganin tana maganan har tana hawaye, gata da wani irin raini dan gane take kmar ai bawani shegen ratan shekaru bane tsakanin su da ibaad din dahar yake jan mata aji haka sosai, shikansa MJ yaji babu dadi, dan harga Allah dayasan cewa special lovers gifts ne atsakanin su kuma ibaad ya dauka ya bashi da bai karba ba
babu irin lallashinta da baiyi akan ta karbi abunta shi baiso ba cikin jin tafi karfin tay kyauta adawo mata dashi taqi sam tace masa ya rike kawai hala rabonsa ne
wkends din gabaki daya bai ma zainab arifah dadi ba gashi yau bata samu cikakken dman magana da ibaad din bama bare ta nuna masa bacin ranta har yamma yay aka watse kowa ya wuce gida
washe gari sunday gidan yay wani irin shiru lokacin kowa yana dakinsa duk any sallahn su ayanah kam har ankoma bacci.. at around 6.30am ibaad yazo gidan, bappa zaidu ne ya aiko sa ya kawo ma ammi karama wasu files daya mata aikin review akai na foundation inta, har ya shigo gidan babu wanda ya sani kai tsaye yana zuwa sashenta ya samu bata nan da sauri ya dawo sashsn hajya mairo yakuwa samu suna zaune suna shan shayi atare sunata hira kamar uwa da ya.
ibaad yay sallama da ladabi ayanayinsa ya tsuguna ya gaishesu snn ya miƙa mata aikan tareda ce mata yana sauri zai koma gida bappa yace yaje yadawo yanxun nan.
duk da ya ambace hakan bai hana hajya dakatar dashi ba.
tace sam ya zauna tunda su uku ne anan zata musu magana ne akan rayuwar ayaanah
adan dolensa ya nemi waje ya zauna duka suka zuba mata ido tanata kame kamenta wai tana jin tausayin rayuwar ayaanah kai harta fito mai fili da maganan cewa ai ayaanah tace mata tana son tay aikin restaurant da su ruthy.
duk tay tunanin dayake mata tambayoyi cikin lumana akan hakan agaban mahaifyarsa bazai masifeta bane
tunda ta furta masa cewa aima batama ayaanah zancen schll din ba ya hade rai ya hau balbaleta yace kawai tace masa zata daure ma ayaanah gindi takiyi makarnta taje mata talla sabida abunda ta saba dashi kenan acan
yayita mata masifa tay shiru tana ta kallon uwarsa koda zata saka baki ammi taki cewa komi ta kyalesu
duk bayaninta yaki ji ya bata ransa yace sam bai Amince da zancen nan ba, kuma kartama kara cewa ayaanah zata mata aiki a restaurant kawai karatu zatayi, snn inhar ayaanah taki yin karatun toh wallh shi dakansa zaikai kararta wajen su bappa zaidu zaice itace ta zuga yarinya tay tallaa taki yin karatu...yana masifar hajiya mairo duk bakintan nan haka tay shiru ta zuba masa ido
irin seriousness dayasa ka akan maganan har saida taji dama bata gaya masa haka ba, da kuma haushintan ya kama hanyarsa ya fita bata sake ganin kafarsa a gidan ba.
ata fanninsa kuwa daren ranan tunani kawai yay akan irin future dayake so ya bawa ayaanah,tunda ya lura kamr hajy mairo zata sako goyon sakalci aciki sai kawai ya aje komi na jan aji dayakeji aransa yazage cikin daren yadau paper da biro ya gama tsara komi, islamiya ,boko, lessons da komi.
washe gari monday suna ficewa agidan ya aje maheer a schl shikuma yay U turn yawuce asibitin da ammi karama take kai ayanah check up, direct yay making enquiries as her quardian he took it upon himself zaiy tracking duk wani cigaban da ake samu a lafyar jikinta na satin, inhar yasamu wani gamsashen report na cewa she is physically and mentally okay register kawai zai mata a can makarantrsu sultanah dan tafara catching up da karatun ta baiso ma ya hadata dasu kulthum bare wata rana yaji labarin cewa hajiya mairo tajata taje saida abinci a kasuwa bataje schll ba..
satin gabaki daya baije gidan ba, duk saida suka damu, tracking health inta kawai ya dingayi na one full week result din na fitowa kai tsaye ya same bappa zaidu dashi colim nitsuwa ya masa bayanin komi
shikansa bappa zaidun yaji dadi dayaji ibaad yace ahada ayaana da sultana a schl daya kawai tunda sultana ita daya take zuwa atleast zata samu yar uwa acan. bappa zaidu ya bashi kudin da zai covering duka registration da uniforms dinta almost 3.4million zai kashe dake private school ne mekyau sosai, haka suka tsaida maganan, ibaad ya bar wajen bai gaya ma kowa ba hatta maheer baisani ba, cikin ruwan sanyi yaje school din ya biya kudin komi aka bashi 2 pairs of new uniforms da 2 shoes da duk wani school stationaries, da text books, babu wani abu na yar gata da schl din suke siyarwa wanda baisaya mata ba. jakar schll ne kawai yasiya mata me kyau da tsada a kasuwa... komi ya saka a booth yanakan jira gobe sartuday ne zaije gidan dan ranar monday yake so ayaanah tafara zuwa makarantar itama...
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025