KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Tsaye suke a restroom din gaban sink me madubi, Nafisa ta kunna famfo ta tara hanky din sannan ta cigaba da goge jikin rigan Na'ima, itadai Na'ima ta riqe rigan tana kallon yanda Nafisan ke goge mata, ranta in yayi dubu to ya baci a wannan lokacin, dan itadai tasan miqa hannun da tayi beci ace hannunta ne beyi reaching to Laila ba har coffee din ya kware mata a jiki, tarasa me ta tsarewa yarinyar da ta fara sakota a gaba haka, tana cikin wannan tunanin taji Nafisa tayi tsuka me karfi tace "Narasa ta ina Laila ke tunani wani lokaci, ita duk wani abu da zatayi cikin rashin da'a yinsa take kamar ba mace ba, dan ko kaffara bazan yi ba da gangan ta juye miki a jiki, kuma wallahi kinji nayi rantsuwa..bashi taci"
Na'ima tadanyi murmushi da iyakacin sa leban ta tace "Ki barta Nafisa, yaushe ma zata sake ganina?" sai Nafisa ta dago ta kalli Na'iman tace "Ai batada hankali ne shiyasa zan koya mata" Na'ima ta girgiza kai tace "A'a wallahi ki barta Nafisa" Ahaka suka gama goge gurin da coffee din ya taba suka fito tare daga restroom din.
Komawansu gurin 'yan'uwan nasu basu samu Laila ba a wajen sai mazan dake tsaye still, dan barinsu Na'ima wajen takaici ya ishi Laila anan tsaye ta musu sallama inda ba wanda ya kulata cikin su sai Adam da Al'ameen, haka ta juya cikin qunan rai ta bar gurin ta koma gida..
Isowarsu Na'ima gurin Faruk ya dan matso garesu yace da ita "Are you sure you're okay Na'ima?" tayi murmushi ta gyada kanta tace "Ya gogu ai Yaya" Faruk yace "But you're drenched ai, ko zaki koma a chanja kayan" Na'ima ta sake girgiza kai tace "A'a babu komai zai bushe a hankali" Ahmad dai dan kallonsu yake baice komai ba, Adam yace "Sorry Na'ima" ta gyada kai tana murmushi tace "Laa bakomai dai Yaya"... iced coffee din da kowa bai sha ba kenan aka barshi anan waiting area kan kujera.
Sunanan tsaye bada jimawa ba akayi calling jirginsu, sallama suka farayi da juna, Nafisa tayi hugging siblings din nata da daddaya, Na'ima na tsaye tana kallonsu jikinta duk a sanyaye, kasa daurewa Abubakar yayi sai da ya matso gurinta yayi mata hug din, yace "Anty na..we will miss you" tadan shafa bayansa tana dan dariyan qarfin hali ta kasa magana.
Ahaka sukayi sallama Ahmad yayi gaba su Na'ima na biye dashi a baya janye da boxes dinsu, shigarsu cikin jirgin suka ga shi yayi hanyan kofan da zai sada mutum da first class, qarasawa seat dinsu suka yi dake business class..bayan sun ajiye kayan nasu a sama Na'ima ta zauna a seat din jikin window ta fara maqala seatbelt dinta..
Basuyi nisa da tashi ba wata waitress tazo seat dinsu ta tsaya ta kalli Na'ima tace "Are you Na'ima?" dan gyada kai Na'ima tayi tana yiwa waitress din kallon tambaya while Nafisa ta amsa da "Yes..she is" sai ta miqo wa Na'ima jacket din hannunta wanda qamshinsa duk saida ya cika musu hanci, tace "Here...someome from other side of the plane send me to give you this" kallon waitress din Na'ima ta tsaya yi bata karbi jacket din ba, sanin Ahmad ne ya aiko wa Na'iman jacket din jikinsa ganin jikinta a dan jiqe earlier yasa Nafisa karban jacket din daga hannun waitress din, tayi murmushi tace "Thank you Miss" murmushi waitress din tayi ta juya tabar gurin su, Na'ima ta juya kanta tana kallon window batace komai, kawai ji tayi Nafisa na lulluba mata jacket din a jikinta sai tayi saurin juyawa tana kallon Nafisan dake murmushi kamar bakin ta ze yanke, hannunta tasa tafara ture jacket din daga jikinta itama tace "Ni nace miki inaso ne, ke ki lullaba ajikin naki mana" dan dariya Nafisa tayi tace "To ai bani na jiqe ba Baby Na'ima" sai Na'ima ta harareta tace "Wace babyn?" Nafisa ta dan daga gira tace "Ke mana... gashinan saboda riganki ya jiqe ana lallabaki harda jacket" kawai Na'ima ta tsaya kallonta takasa magana ma, dariya Nafisa tayi itama tana kallon nata tace "Kinga wani instinct dana gani gurin yaya Ahmad yau, girl you have alot to gist me and i mean everything" sai Na'ima ta sake juya kanta tace "Kin shiga uku da wannan mind din naki Nafisa, ni babu komai tsakaninmu" Nafisa ta cigaba da lullaba mata jacket din tace "Naji..yanzu dai let's get you warm baby" Na'ima ta sake buge hannunta tana dan murmushi tace "Zan miki ba dadi Nafisa" 
Nafisa na dariya ta sake cewa "Baby" 
Haka ta hakura Nafisa ta lulluba mata jacket din a jikinta qamshin rigan na cika mata hanci, ahaka bacci ya dauke ta zuciyarta na saqa mata abubuwa daban daban...

Sai shida saura jirginsu ya isa London, bayan anyi announcing fitan su, Na'ima ta sauqe jacket din daga jikinta ta miqa kan cinyan Nafisa tafara shirin miqewa, dan ware Ido Nafisa tayi tafara dariya tace "lallai ma yarinyar nan, ni na lulluba dashi ne?" Na'ima ta miqe tana gyara squeezing din riganta tace "Ke kika karba daga hannun wadda ta kawo ai" kawai dariya Nafisa tayi ta dan gyada kanta...Fitarsu basu gamu da Ahmad ba suka fara tafiya Nafisa nata waige waigen inda zata hangoshi suka shiga cikin Airport din, saida suka wuce arrivals Nafisa ta ciro wayanta daga jaka ta fara kiransa, bayan ya dauka sun gama magana Nafisa tace da Na'ima "Muje sis" .
A wajen airport din suka samesa tsaye da jaka a rataye cikin white t-shirt mai dan kauri, jacket dinsa dake rataye hannun Nafisa ta miqa masa tace "Gashi Yaya mungode" karba yayi ya kalli Na'ima dake tsaye, bude bakinta tayi a hankali tace "Thank you"  ya gyada kansa yace musu "The driver is on his way"  sannan yafara saka jacket din a jikinsa, Nafisa tace "Toh Yaya" 
Dayake spring season ya danyi nisa sai ya zamto garin babu wani sanyi sosai....suna nan tsaye wata sleek ride tayi parking a gabansu wani bature yafito yana gaisheda da Ahmad ya amsa masa, sai drivern ya gaisa dasu Nafisa sannan yafara diban kayansu yana sakawa a booth Ahmad din na tayashi..bayan sunyi settling acikin motan Ahmad na gaba ya fadawa drivern unguwar Anty Amnah suka dauki hanya.

Isarsu gidan Anty Amnah bayan driver ya sauqo musu da kayan nasu suka wuce bakin entrance din Nafisa ta danna door bell din, basu jima anan tsaye ba Anty Amnah ta bude, cikin fara'a tayi hugging dinsu tace "Oyoyo 'yan makaranta sun dawo" ta jasu suka shige cikin gidan nata mai kyau dake screaming luxury, twins basa nan suntafi makaranta shikuma Abbansu yana asibiti, kafin su zauna Nafisa ta wuce gurin dining area ta dauko musu bottle water data gani a gurin ta dawo falon tana miqawa Na'iman daya tace "Anty tare muke da Yaya Ahmad fa" sai Anty Amnah ta dan ware ido kafin tayi magana taji an danna door bell din again, miqewa tayi ta je ta bude Ahmad yace "Momma kin rufeni a waje" tayi dariya tareda riqo hannunsa suka shigo cikin gidan tana cewa "Na isa son, kaida ganinka yayi tsada a London ma" zama shima yayi nan falon Anty Amnah tasake cewa "Kasan ban kawo araina tare kuke bane wallahi" Ahmad yadanyi murmushi kawai..miqewa Anty Amnah tayi ta debo musu drinks harda snacks, da kuma abinci tace "Za kuci yanzu ko sai kun huta?" Na'ima batace komai ba sai Nafisa ce tace "A'a Anty zamu huta tukunna, sai munyi changing ma" sai Anty Amnah tace "Toh" Nafisa ta juya gurin Na'ima tace "Muje sis" suka miqe tare suka nufi dakinsu dasuke sauqa in sunzo gidan suka bar Anty Amnah ta miqa refreshments din nan gaban Ahmad.

Bayan su Na'ima sunyi wanka sun dan nutsu, komawa sukayi falon amma basu tadda Ahmad ba Anty Amnah tace musu ya wuce gidansa, dining area suka nufa suka fara cin abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon sannan suka fara hira da anty Amnah.

Haka su Na'ima sukayi zamansu nan gidan Anty Amnah suna hutawa akan sai Sunday zasu koma Oxford, Kuma sun fada mata hakan ta amince.

Ranan Saturday da safe Nafisa tayi waya da kawarta Lauren akan tashigo London, haka ta shirya akan zasu hadu a wani Cafe tace da Na'ima suje amma tace baza taje ba..
Wunin ranan Na'ima da twins tayi sa dan su Anty Amnah da Mijinta ma basanan sunje asibiti sunada shift, ta tafi kitchen da twins ta hau yi musu cake, dan Nafisa ce ta koya mata yanda akeyin cake din farkon zuwansu Oxford harta koya sosai, twins sai hira suke mata tana biye musu, sunyi having fun sosai dan twins suna sonta sosai indai tazo gidan kuma sunanan to bini bini duk inda Na'ima tasa qafa suna biye da ita kaman dama tun can sun santa tun tashinsu.

Daren ranan Na'ima na zaune dakinsu ta jingina bayanta da fuskan gadon tana kallo a laptop dinta, gefenta plate ne dauke da sauran cake dinta tayi, kwance Jafar yake a dayan gefenta yayi bacci shima...Nafisa ce ta shigo dakin Na'ima ta dan dago ta kalleta, Nafisa tace "Sannu uwar twins, sudai yafe mamansu suke yi ma in kika zo" Na'ima tayi murmushi tayi pausing kallon nata tace "Kin dawo?" zama Nafisa tayi a bakin gadon ta dauki cake daya dake plate nan kusa da Na'iman takai baki tace "Duk na gaji ma" sai Na'ima tace "Ina da Ina kuka je haka?"  ta amsa da "Ashe housewarming party Lauren tazo attending garinnan da kuma yin content akan gurin partyn....sis akwai masu kudi a London, waiii.." Na'ima tayi murmushi tace "Kijiki sai kace bakisan kudi ba" Nafisa tadan ware Ido tace "Banda irin wannan kudin Bobo" sai Na'ima ta dan jijjaga kai tayi playing kallonta, Nafisa ta dan gyara zama ta cigaba da magana "Guy dinda ya sayi Mansion din ashe cousin din Lauren ne....kawai sai gani ga Yaya Ahmad, na zagaya wajen pool din gidan naganshi zaune da wasu friends dinsa" Na'ima ta dan dago ta kalleta tace "Allah sarki" Nafisa dake lura da expression din Na'iman tace "Kinsan ya tambayeni yakike" maida idonta kan kallon Na'ima tayi cikin sanyin murya tace "Ayya, ya yake shima?" sai Nafisa tace "Lafiyansa lau, narasa ina yake haduwa da friends irin wa'inda nagansu tare yau, they all scream money" Na'ima bata ce komai ba Nafisa ta sake cewa "Kinsan Yaya Ahmad yasha creating apps da sukayi gaining global reach" sai sannan Na'ima ta dago kanta tace "He's a programmer?" Nafisa ta amsa da "Babba ma kuwa, bayan aikinsa na company da Baba ya dora shi Head ai yana programing manya manyan Apps, zuwansa da yayi this time ma maqasudin zuwan ashe saida wata App din yazo yi gurin investors, ina tsaye kusa dasu naji yana maganan da wani white friend dinsa" sai Na'ima ta gyada kai kawai batace komai ba, Nafisa dake son cusa mata maganan Ahmad din ta sake cewa "Dan dai ba shaquwa nayi dashi bane, saboda sai nayi shekara abu bai hadoni dashi ba kuma shi bayason arinqa shige masa cikin al'amuransa kai tsaye, dana jaki watarana munje gidansa dake nan London" Na'ima tace "To ma tayaya zamu kwashi kafa muje gidansa Nafisa..akan wane dalili?" miqewa Nafisa tayi tafara rage kayan jikinta tace "Ha'a muda yayanmu..yanada kirki fa kawai ba komai zaki gansa yasa kansa aciki ba kamar Yaya Adam" Na'ima jijjaga kai tace "Ai bance baida kirki ba kawai bazan je bane" cikin son kawar da zancen yasa ta sake cewa "Bayan celebrities dinda Lauren din keyin content akansu, yanzu ta koma yi har a gurin housewarming party ne? Ko bada ita kukaje yin content gurin movie premiere ba kwanaki?" Nafisa tace "Wannan babu inda bata tabawa indai akazo batun content, da celebrities din, Entrepreneurs, business tycoons duka ko ina ma" Na'ima ta gyada kai sannan ta cigaba da kallonta.

Washegari Sunday ya kasance ranar komawarsu Oxford, da wuri suka shirya komai nasu bayan sun idar da sallan safe, sannan suka tafi kitchen girka nasu breakfast din dan yau Sunday su Anty Amnah yawanci suna yin dogon bacci na hutu.
Bayan sun gama hada komai nan dining sannan suka zauna suka fara ci, Anty Amnah ce tafito sanye cikin long pajamas, gaisheta sukayi ta amsa sannan taja kujera ta zauna tace "Sannunku...kun gama shirya kayan naku dai ko" Nafisa tace "tun tashinmu" Na'ima na sipping tea din hannunta tace "Twins basu tashi bane Anty?" madadin Anty Amnah ta amsa sai tace "Meya samu muryanki daughter? Mura ne?" sai Na'ima tayi gyaran murya kadan tace "Nadan tashi da tari ne Anty" Anty Amnah tace "Sannu dear, akwai magani a cikin first aid box, zaki gani a study room din Abbansu, ko bari idan natashi zan dauko miki" Na'ima ta gyada kai tace "Toh Anty nagode"
Nan sukayi breakfast din da Anty Amnah suna hiransu, bayan sun gama suka koma daki sukayi wanka suna cikin shirin Anty Amnah ta shigo dakin tace musu "Ku fito yayanku yazo daukanku" sannan ta fita.
Na'ima ta juya ta kalli Nafee tace "Wani Yayan?" Nafisa na zipping riganta ta danyi murmushi tace "Yaya Ahmad mana, I told him yesterday akan yau zamu koma da safe" sai Na'ima ta dan tsaya kallonta can kuma ta juya ta cigaba da saka kananun kayayyakinta a qaramin jakanta batace komai ba.
Fito da kayansu suka fara yi Abban twins ya tayasu daukan wasu ya fita waje dasu, bin bayansa su Na'ima sukayi dauke da wasu kayan a hannunsu Anty Amnah ma haka.