ABUNDA KE 'BOYE...

29

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahms

⏯️2️⃣9️⃣

8:30am sartuday mrn

yau tun bayan da suka dawo daga sallahn fajr maheer ya biyo ibaad dakinsa yazauna akan reading table din ibaad din yana harhada wata assigmnt dinsa, bai jima da farawa sanyi yasaka ibaad yakoma bacci wanda bai farka daga barcin ba saida 8.30am ya cika on d dot, a hankli ya bude idanunsa da Sukayi Wani irin ciki ciki tmkar ba baccin yay ba ya budesu yanajin wata muguwar azaban kasala da gajiya a dukkan gabobin jikinsa ga wani azazzaben nauyi da ciwo da kansa yashigayi, agogon dake gefe ya kalla ganin 8.30 yasashi mikewa a firgit yadan zauna a tsakiyar gadon can sann ya juya yakalle maheer dake famar sharar baccinsa shima rungume da katon book dinsu na shaharrern authors din nan Okonkwo & Naish Criminal Law in Nigeria da ake ma taken "the bible of criminal law, a very notoriously hard course, cikin baccin maheer ya rungume book din ya Kuma sake jikinsa ayanayin da baisaba ganinsa ahaka ba

..leka fuskansa yay ahnkli ya tsaya akansa yanata kallon yadda yake sakin numfashi is like he is inhaling his fears into some of the core core words da ke cikin book din, things like homicide Sexual offences, Inchoate offences, Corporate criminal liability,Burden of proof complicated defences..

ibaad yay saurin kyabe baki jin Kansan dake masa Wani irin ciwo yafara juyayi ya rike kan cikin kasa iya gane abunda yakeji, Wani wahallalen tsaki ce ta kufce masa yashiga takune fuskan sa dats so smooth fresh and yellowish fair da succulent blush pink redish lips dinsa,cikin rasa nayi yay miƙa yana mai mikewa tsaye tsar namiji dan daga shi Babu komi ajikinsan face doguwar wando sai zaratan jijiyoyin sa da sukadan fara girma suna hargitsowa suka mimmike tuni yahau langwasasu qas qas cikin yanayin son ya warware kasusuwan jikinsan dayake masa tsami tsami Dana kwankwason sa da yakeji Kamar duka akayi masa awajen yana daddana su da palms dinsa Koda ma zaiji dama dama..

bayan Nan bai yi wata wata ba ya fada cikin bathrum ya saki cool shower akansa to help him relax his nerves and muscles shiyasa ma Bai yi amfani da ruwan dumi kwata kwata ba, agurguje ya fito bayan ya kammala wanka Duk hanklin sa naga kan lokaci dan yasan atata izuwa 9.30 am zasu bar gidan suje family house yana kuwa fitowa yasamu dakin wayam da alamn har maheer ya farka shima ya fita shiryawa.

littafansa na law daya barbaza yabar masa awajen all scattered ya kwashe masa ya aje su neatly agefe kafin nan ya shiga kimtsa kansa ya kuma gyara dakinsa tsaf ya goge yasaka qamshi kamar yadda ya saba kullum within 20-30 minutes kowa ya gama shirinsa ya fito tea kawai suka sha suka bar gidan duka atare.

**********10am as usual babban family house dinsun sosai yacika makil da hayaniyar surkunaye da jikokin hajya mairo me tuwo, ƙamshin abinci kala kala da kuma hira mai cike da annashuwa har aka gama ciye ciyen duk aka watse yara yara yan matan gidan suna ta yawo a tsakar gida, manya kuma mafi akasari suna zaune ne a falon hajiya mairo ana hira da dariya.

sai can wajajen bayan azahar kafin zainab arifah ta karaso tana shigowa asassarfe cikin wani irin takun dayafi karfin na me shekarunta wani irin jan aji take tana basarwa kamar wata ƙaramar sarauniya. doguwar riga ta saka designers irin me transparent net din nan, da rabin net din akayi kasan da kuma saman kirjin kayan, rabin jikinta ne da hannun ta kawai arufe saiya kasance daga can can nesa ma zaka iya hango

saman nononta da kuma sawun kafafunta tacikin rigar, dan kwalin doguwar rigan ta yafa shi half way a saman fixed expensive human hair data sakashi shima dogo ne baki haryana taɓa mata duwawunta wanda daga ganinsa kasan ba nata bane na sawa ne.

tana shigowa falon hajy mairo tun bata gama gaishar da su ba hajy mairo tajuyar da idonta baki bude tanata kallonsu bappa zaidu tanajira ko zasuma zainab fada akan suturarta sai taga duk basu ce mata uffan ba karshe tashi ma bappa zaidu yay ya dan fice waje.

kasa hakuri tay adan mmknce ta mike ta kamo hannunta kusa da ita tana dada kare mata kallo tace “haba jama'a ku duba min wannan yarinya sekace wata arniya? "ke wai waye yake baki wann kayan arna ne ehhh zainabu?

zainab arifah tay rau da idanu tace "excuse me hajiya Meye kuma kaya na ya miki daddy na ne fa yasaya min..tana fadin hakan tadan kwace hannunta a mugun sakalce ta zauna abunta da alaman ita bataga wani abun magana akan dresing inta bama,hajiya tay kifi kifi da ido tace"ikon Allah,waye kuma daddy? ina miki magann tsaraici kina kiramin wani dady ke kinci uwarki da daddyn.

turo baki kawai zainab din tay ta zuba mata ido da alaman batasan ma me zatace mata ba

da rikicin tsufa hajiya ta juyo kansu ammi dasu uncle moh muryanta kamr zatay musu kuka tace kai muhammadu yanxu saiku zuba ido Arifah tana fita kamar babu tarbiyya a gidan nan ni wallah tallah to Ku gayawa mahaifiyarta muba yan iska bane, bamuyi gadon nuna tsiraci ba, maza maza ta canza ma yarinyar nan sutura tun kafin na harzuka na ɗora mata tawul in rufe mata gwiwa da kirji ynx fisbillah meye kuma wannan???

Uncle moh ya dan girgiza kai his voice was calm ya kalle zainab arifah gently speaking yace"Yarinyar daddy baki san kin girma bako?” ɗaya ya ce hakanne zainab tabar turo bakin ta juya da shagwaba tana dan jan tsaki taciki a mugun sakalce tace "uncle amma hajiya fa ta daɗe a duniyan nan, she doesn’t even understand fashion.

cikin katseta ammi karama tace "its okay, ya isa..tashi kije cikin yan uwanki mungode da gaisuwa u can go now..

dake tana jin shakkar Ammi karaman sai batace uffan ta miƙe tana girgiza gashinta har tafita duka suka bita da kallo

tana ficewa hajiya ta fara masifa kmar zata daga cikin falo..

bakinta har na kawo kumfa tace "ke safeera fita waje ynxun nan kije ki kiramin zaidu..inshi zayyanun baida hankli sai ku duk ku zuba ido kuna kallo yana lalata yarsa, waallah bakumin adalci ba, zainab din har nawa take da zata fara yawo gantsal gantsan da kirji awaje tana nunawa maza kwailayen nono mai kama da yayan gujiya wai ahakane zaku yi zumuncin bakwa gayawa kanku gaskiya?...

tunda tafara surutun batay shiru ba, cikin su kuwa babu wanda ya katse ta har saida bappa zaidu yazo sann wani sabon tashin hankalin ya fara a falon tafara masa fada kamar ma shine zayyanun,

shiru kawai yay dan tun zainab bata kai haka ba yay iya bakin kkrinsa danyaga ya shiga rayuwarta ya saitata amma duk magana inya taso prof zayyanu yazo yay zage zage hajiya sai tay ta kuka tana zage zage amma bazata taɓa masa fada ba haka laifin zai dawo kansu kullum abu daya,

kowa yasani, prof zayyanu is very sensitive and over reactive akan yarsa zainab arifah gani yake kamar gwal ce daga sama Allah ya sauko masa dashi, yanzu ko tsawa kama Zainab arifah taje gida tana kuka sai ya zamo muku babban case da shi, da suka gaji da irin cin mutunci da baqaqen magana dayke fetsa musu idan sun mata gyara yasa kowa ya ja baya da ma zainab din gyara aka bar masa yarsa msmn ma dayasha gaya ma bappa zaidun cewa duk sanda ya takura ma yarsa da wa'azin karya wallah sai ya kulleshi.

infact haryau zarginsu yake da cewa tunda Allah ya bashi yarsa suke neman hanyar da zasu rabashi da ita dan inya mutu a kwashe arzikinsa akawo musu..

Duk da rakin hajiya haka bappa zaidu ya dakatar mata yafara tuna mata wayannan maganganun saida tay shiru

yace mata duk cikinsu babu wanda yake son yay fama da kazafi da zargi, ynxu qaddara wani abu yaje ya same zainab a gidan nan toh dole ne su zaa kama a kulle, kuma faɗar da gaban cikin gida ne, ..babu abunda zai jawo musu face zubewar kima da mutunci awaje, tunda yace abar masa yarsa saidai in ita zata iya masa mgn bazasu hanata ba...

atsakiya hajy mairon ta sakasu tanata bori cewarta babu abunda zai hanata itade ta gayawa zayyanu gaskiy bayan sunsan yanxu kusan shekara bakwai kenan basuy waya dashi ba

Bangaren zainab din kuwa tana saukowa daga kan steps nacikin babban palourn gidan ta miqe Inda taga Babu kowa

Dan tsayuwa tayi cikin nazarin Inda zata soma duruwa Can saiga sautin saukowar maheer ahnkli yake saukowa he is wearing dis calm coffee-brown T-shirt da Khaki trousers da sneakers sanye da wireless ear piece a kunnensa yana amsa waya, tana ganinsa da sauri ta taho tanamai tareshi

Shikuwa sanda ya Gama amsa wayarsa tsaf sann yaji kmr zai saurareta suna hade ido tahau murmushi tana kankance voice tace "whats up Big bro",

maheer ya hade rai,tana dan murmushi tace pls tmbya nake ko kaga Inda sauran mutanen gidan nan sukayi?..cos I came down here but no one is available..Idanunshi nakan wayarsa a hnkli yace "I don't know...

Kallon sa ta cigaba dayi shikuma baisan yawan kallo

yace Asali Wai wakike nema ne? bude baki tayi kamar zata amsa taci Karo da fararen idanunsa masu asalin kyau da daukar hnkli, wani kafeshi tay da ido tsaban yadda taji wani maqudan bugun zuciya na taso mata in her mind she was like dis guy is damnn hot too har wani kama taga ykeyi da dad inta musmn inya hade ransa, too many hot choices around here saidai haryau bataga wanda yazo mata kusa da irin kyauwu da ajin ibaad ba ji take har duniyarta yanade bazata ga wanda yakai ibaad ba

jin ta bace shiru yasashi dagowa ahnkli yace in su hajiya kike nema Suna can dakinta, And U can check out the rest atacan sashen anty safeera..Da Dan Murmushin ta tace mai ok thanks, shareta yy kamr badashi tayi ba ya juya kansa abunsa, ta kyabe baki batama jira ba ta bar wajen tanufi falon ahnkli tana takawa Kan matakalar da zai sadaka da ta wajen cikin sauki

Dan madaidacin falon sama ne mai Dan uban kyau da tsari wanda ba acika mai tarkacen kwalliya ba daga yan flawowi sai sofas da na asalin round glass table Wanda aka kawata shi da fararen kujeru masu dauke hankli

Wani salon taku take tana Jin yadda iskan Acn wajen ke famar hudata saidai harta karaso wajen su fuskrta ba asake ba ganin yadda yaran gidan gabakiya suka mamaye mujaheed ya sake yana zabga dariya acikin yar hirarsu da su sultana da su ayaanah safiya ce kawai ta kafe idonta a tv tana kallon indian series a star life da alama ko jinsu bayi takeyi ba..

Tana shigowa wajensu ayaanah tayi shiru ta yanke hirar da sukeyi har Arifahn ta soma masa magana cikin kayataccen salon data shirya tazo dashi, yadda bata musu sallama ba yasa sauran yaran duk basu daga ido sun kalleta ba kowa yay shiru face khultum datake da taurin kai ta cigaba da maganarta abunta kmr bata san wata ta shigo wajen ba

zainab arifah dake Kansu tana tsaye cikin yar sautin murmushinta mai tafe da yaudararren salo tace ma mujaheed "mjay can I sit with u guys? yace ok. ta karaso cikin tafiyar yanganta mai sanyi ta zauna ata dayan bangaren Agefe dashi kowa na satar kallon kalar shigarta amma ita ayaana kawai take kallo..

Da dan Jin haushin yaran aranta musman nakin basu waje tace"I hope I'm not interupting anytin? da Basu amsata ba ta cigaba, tace"..so Mr south africa Wani hirar akeyi bandamu kaifa kamata yayi ace hutawa kakeyi ba surutu ba,..right girls?Ta mayar da tambayar Kansu sultana Wanda suka dago cikin sauri suka mata kallon raini..

A hnkli ayaanah ta miqe kamar zata bar wajen ya mata Ido akan karta tashi

Sosai Hakan ya bawa zainab arifahn haushi dan ji take kamr jininta sam bai hadu da yarinyr ba amma a fuska murmushi kawai take tamkar bahakan take rayawa aranta ba,gyaran muryan sa daya fito a hnkli yasata bada hanklinta kanshi..

wasu irin damning question tafara masa akan ayaanah

musmn ma akan kauyensu waye babanta, tana so dai ta dawo da batun kmr almajira aka dauko musu aka kawo

feeling iritated da hirar yasa kulthum ta miqe tsaye tana kallonsu ayaana tace i think I'm gonna go inside inkun Gama hirar Kusameni aciki..

tun basu amsata ba mujaheed ya ganota cikin hade rai yace aa, babu inda zakije zauna kawai baga wata antyn taku tazo tayaku hira ba

..Hade rai kulthum tayi batace uffan ba ta zauna kusa da ayanah tana mata alama da ido akan kartay fushi, sama sama ake hira, har saida aka aje talla style life sann safiya tajuyo ta gaishe da zainab arifa ta amsa ta a dakile dan sosai ta lura da yaran gidan kmr suna da raini sosai .

satar kallon ayanah take trying to figure her out taga dai fatar jikin a wanke yake da haske irinna buzaye but with this unique smooth like Ethiopian looks, idonta manya, gashinta idonta dogon gaske bataga dai alamann wani extension ba nd she cant just get enuf of her sai ta tuna ashe ance daga kauye ma hajiya mairo tazo da ita hala bata iya turanci ba.

wani abu taji yana dan motsa mata a zuciya ta fetsar da numfashi me cika da isa tana kallon Ayanah sama da ƙasa.

suna hade ido tace “you… what’s your name?dagan gan ta yi magana da harshen turanci cos she just want to embrass ayanah awajen nd make fun of her.

Ayanah ta juyo kaɗan tay shiru jin kowa yay shiru saita kalle xainab din cikin idonta tace “My name is Ayanah,”ta amsa cikin smooth clear English.

Zainab Arifah tay jim dan tayi tsamanin yarinya daga ƙauye haka ai ba za ta iya sanin haka ba but anyways dats a simple one

Ta kalli dogon gashinta ta ɗan ja igiyar jelarsa a hankali tace “is your real hair? Or is it attachment?” ta na jan jelar ayaanahn faɗa da murmushin rainin wayo....wanda ko safiya ma barin kallonta tay ta juyo tana kallonsu tana Allah Allah ayaanah ta kwafsa ta fashe mata da dariya

Ahankli ayaanah ta janye jelar gashintan daga hannun zainab Arifah tabari ya sauko bayanta kamar an sake ruwa sabida yana da yauqi irin silkness na korean hair in nan acikin kwanciyar hankali tace malamin mu yace mana "attachments is haram acan garinmu kowa ai yana da gashinsa..

kulthum tay smirks ganin yanda zainab din tay wani iri da fuska tace “so, its REAL?”

da azarbabi sultana ta janye small veil din ayana ta kara warware mata gashin tace "yeah it is u want to feel it?

dagangan ta warba mata ajiki

tay saurin yarfawa Yaran suka yi dariya kaɗan. anty Zainab yakikaji laushi? hararar sultanan tay tayi shiru da alaman taji haushi, Hankalinta ya fara tashi sosai cikin basar da batun gashin ta kalli ayanah "well, i am just quiet suprise u speak good English..innocently Ayanah tace “Yes. I go to school. har wannan lokacin kallon ayaanah mujaheed yake tay yanajin ta burgesa ganin sunata fafatawa confidently take amsa zainab batare da tsoro ba.

can dayaga zata fara mata slangs yay sauri yace “Zainab, ke fa ba size ɗinta ba ce. Ki yi halin manyan mana ki kyaleta

zuciyarta na tafarfasa taciki tace "ure ryt, i think i just lost my drive to talk barinje dakin anty safee i need to be alone tana fadin hakan ta mike ta haura sama, wani dan uban karar dariyar su kulthum da sultana taji nabibiyarta abaya

safiya ma sosai taji mugun haushi saita bata shiru a falon ta kara kafe tv da ido

surutu ne ya kaure sultana ta rike kafadun ayana tana dariya tace i knew u knw how to speak english, duk na miki magana da turanci kina jina shine mu baki taba mana bako? kulthum tana kyalkyala dariya tace "gashi yau tay a inda yake da amfani,.yaa mujaheed amma kasan anty zainab dai tana mata turancin ne danta kunyartar da ita ko??

dariya kawai yakey yaki ce musu komi..yabarsu sunata making fun din abun har saida sukaji sallamn maherr kafin nan suka nitsu

daga nan har akaci abincin rana zainab arifah tana can sama bata kara fitowa ba har saida yamma yay aka kusa zuwa daukar ta snn ta fito ko kallon su batay ba taje neman ibaad, a kofar masjid ta samesa suka gaisa sama sama he notices how her eyes was a bit red sabida ɓata mata rai da akayii agidan yau amma dake abune da bai shafasa ba sai baice mata komi ba har drivernta yazo ko sallama batama hajiya mairo ba ta wuce gida abunta, bayan tafiyar zainab arifah gidan was calm nd quiet for a while, can wajajen bayan magrib kulthum ta fito daga wajen maheer da qur'ani hannunta tana isowa falonsun ta tsinci koina shiru batayi wata wata ba tahaura sama dakinsu ta same both ayaana da sultana suna kkrin idar da sallah atare

kallon sultana tayi daga kan sallaya ta budi baki a mamaknce tace"..oh my god siss wato ke sallah ma kikeyi bakima shirya tafiya bako? toh wallah kinsan yaa ibaad bazai juri jiranki kuma nasan anayin isha zaa ce ki fito kutafi gida.

..sultanah batace uffan ba taƙare mata kallo dan bakaramin kyau yau kuthum din tayi ba musmn dataje wajen maheer ta sauya kaya tasaka pure atamfa dinkin fitted na riga da sket takuma yi lullubi tafito zak arewa beauty masha Allah.

cikin kif kifta ido da kankance murya tace "toh nikuma shirin me zanyi bayan next week ma zamu kara zuwa kinga ni wallhy gidanmun nan ya ishe kamar karna tafi, ayanaah dai batace musu komi ba kulthum tana ta kallon bakin sultana datake turowa gaba gaba cikin mita batasan sanda tyi dariya ba"sis wallhy ure sooo funny ke kenan kullum zaki tafi gidanku kinta fushi kenan ko toh ki shirya dai yaa ibaad ne zai jaku a mota..kuma kinsan dai kika batamai mood yau ba kyaleki zaiyi ba dan wallh bakiga daukar wankan da yay bane yay wani fresh yay kyau, keeeee!! wata mayyar Plain black polo yasaka with this Ash-grey pants da wata irin blck sneakers da Silver wrist watch, mehnnn gashi ta dan kamashi guys kuzo kuga wankan swags, wallh nikaina saida naji kamar in sace shi, he is damn hot....

tuntuni su ayaanah sai kallon ta sukeyi tana rau rau da ido can sultana tace sis are u okay kuwa?ko kinsha wani abu a hanya ne yaa ibaad fa is always gushing hot kowa ya sani

tace "yeah i know" ta ai naga mutumiyarsa ta gudu gida ne, ayaana ta kunyata sheigya..ta fada kan gado tana dariya..

sultana ma tafara dariya Dan Allah dagaske kike ya shirya?

tace..."ohh u think im crazy, okay ki dan leka side din ammi karama ki tabbatar ma idanun ki..

cikin yarfa hannu sultanah tace niki kyaleni kar yaje ya wanka min mari kinsan dai daga ganin irin wannn wankansa anty zainab taje shagala taje takamo da sonsa kuma ai kinga karshen ta baiyu kyau a hannunsa ba...mugun haushi take bani tana wani abu kamar wata kucaka innine shi har abada bazan so ta ba

atare suka fashe da wata muguwar dariya ganin ayaanah bata saka bki a hirar ba da muryan tsokana kulthum ta jawo sumanta ahnkli cikin kwaiwakyon zainab arifah tace "hey. is ur hair real? or is it attachment? sanda ayaanah ta fara dariya ma bata sani ba

sultana ma tafara mimicking

sukaci dariya

tace"i dont knw what her problem is oo nifa na lura kamar tazo ne tay embrasiing dinki ayaanah, ...ahanki ayaanah tace toh ai ni bansanta ba..

quiet seriously kulthim tace ai kuwa yanxu zan baki labarinta ta kama hannun sultana tay da ita gaban mirror tace toh zauna na gyara miki hair dinki saiki fara shiryawa nikuma ina bawa ayaana kanun labarai

suna farawa kulthum ta kalle ayaanah tace yaya ibaad, yaya ibaad, hmm yaya ibaad the dangerous mupper. majinan bango ahauka a zame kahau mutum kazauna dai dai wani uban dariya suka fashi

dashi mai ƙarfi harda tafawa ita da sultana.

nn ta kalli ayaanah tace sis ingaya baƙaramin drama akayi a gidan nan ranar ba, nikaina naci dariya kamar inyi yaya amma fa saida naje harr schl dinmu nayi dariyan indan

a gidan nan ne da bakizo kin sameni ahakan ba hala da an kaƙƙarya ni.

ayaanah tace why meyafaru? dariya ya riga yaci ƙarfin kulthum amma hakanan ta fara bawa ayaana labari tace anty zaina ce mana da uban rawan kanta ranar bansan wani shaidan ne ya shiga jikinta taje ta cewa yaa ibaad wai tana sonshi....haba mana

daga nan sultana ta saka baki suka fara bata labarin irin tsuge zainab din da akayi da wayar wuta, word to word har kukan datayi yadda kulthum take mimicking wayyo Allah daddy kazo ka ceceni yasaka abun ya zama so funny

....magana kawai takeyi amma tuni idanun ayaana already ya cikko da ruwan hawaye tsabar taci dariya dan har ƙasa taga su sultana sukakai tare suna kyakyatawa kamar wasu sabbin mahaukata.

sai can da kulthum tsagaita tace wow u guys are really fun to be with zan masifar missing dinku wayyyo kamr karki tafi

sultana tace sis ya isa haka karki yaudare ne.. snn yakamata mubar hirar nan haka kar wata rana yajimu yace muna gulman shi a mana ciki da bai irinnna anty zainabuuuu..kara kwashewa da dariya sukayi

tace thank God sunzo sun dan shirya yanxu but rlship dinsu is so weird nd funny yana son fushi ita kuma shegen naciya

..gata da iya barazana hargara ynxu ma naga yana tsayawa ya kulata amma dacan hmm ko gaisawa baya shiga tsknsu

...sultana tace "maybe fa ansashi sun sasanta ne, dan ranar babanta ne ya aika aka kirashi yaje gidansu daga nan kuma naga ta dawo da rawar kanta tanakan bibiyarsa kamr wata jela har ynxu..

wannan hirar suka dingayi tun ana raha ana dariya har abun yafara sakama ayaanah tashin hankli acikin ranta batare da tasan dalili ba.

musmn dataji sultana tafara kawo magann ai iyayen ne sukeso su hada su aure hala shiyasa yaa ibaad yanzu baice mata komi yake kyaleta

within no time har kulthm tagama tayata shiryawa ta tattara kayanta duka suka shirya tsaf ta saka black abayah mai mugun daukar ido da mayafinshi nayin rolling..

ayaana kuma wani designer turkish skirt ne ajikinta da riga mai dogon hannu ba wani design mai yawa bane ajikin shi face golden beats da stripes da akayi striping tawajen wuya da hannun rigar din dashi aka zagaye shi da stones fari masu kyalli, kwalliyar ta nayau was more lighter than ever kwalli kawai ta saka a idanunta kulthum tay working mata eyes dinta da ghost shades lines idon ya zama so sexy nd natural,eye balls dinta suka fiffito suka bada yanayin luiiii shape din tamkar kuma nata ne na asali, man bakin data shafa was very shiny hakan ya saka tayi lining dinshi da pitch lipstick so her face was shining bright and fresh as hell.. suka fetsa perf ana kirar isha suka jero sukayi isha'in su atare.

suna idarwa suka fara parting junansu with goodbye speech dan babu karya cikin kwanaki sha hudun nan da sukayi tare a dakin kulthum bakaramin shakuwa da junansu suka kara yi ba musmn ma ayaanah da ta fara sabawa dasu sosai

cikin salo kulthum ta riko hannun ayaana ahankli tace sis, i am very proud of u for speaking up agaban anty zainab arifah karki bari dan anaga kinzo daga kauye ana rainaki, snn karkiga muna ma anty zainab arifah ki rainata dariya wallah daurin gindi take dashi ko su baba basu iyawa da ita, saishi wanda take so din wato yaa ibaad..duk gidan nan shine kawai yake mata abunda yaga dama kuma still kiga tana binshi..but dont be scared of her. if not walalh zata ci miki mutunci ai kinga abunda taso ta miki yau. da sanyin murya ayaanah tace hakane, duk dama ni bansan haka take nufi dani ba amma nagode sosai sis.. feeling sober sultana ta dafata tace "i will leave u in good hands ga kulthum zamu na waya da phone inta you guys shud stick togethr har sai sartuday in nazo.

suna ciki wann maganar aka wani bangaje kofar da karfi

suna daga ido suka ga safiya da blue hijabi atsaye tahade ranta sosai kamr zatay kuka

haushi ya kama sultana tace ke kuma meye haka.

da mugun rashin kunya ta harare sultanan tace toh ana kiranku wai inji hajiya waiku maza maza ku fito.

da sauri sultana ta miƙe ta cakomota cikin dakin kamr zasuyi dambe tace "toh mu sa oinki ne da bazaki mana sallama ki gaya mana aikan ahankalce ba saikizo kan mutane kina musu gatsale wallah kika kara murguda min baki saina fasa miki baki

batace komi ta fauce hannunta ta fita a dakin da gudu tana bambami

masifa sultana take tana cewa nifa rainin yarinyar nan ya fara isata ba kuma dan taga muna mata shiru ne shiyasa take kara hawa kai..but i wll show her dat i am not her mate

..mtwss. suna cikin fadin lefin safiya suka lura da yadda ayaanah tay shiru

kulthum ta dafata tace "what? kema safiyan tamiki wani abu ko? i saw the way she look at u sumtimes kamr wani zata dake ki

ayanah tace "aa, bata min komi ba. kawai ranarne naji ammin sultana nacewa wai ku aikun girme ni safiya itace age mate dina ka fa wata rana nay wani abu nima kuce ina raina ku..i dnt want us to fight kunga bansan kowa anan garin ba.

sunajin haka suka gane me take nufi da tausayi a idonsa suka dawo jikinta suka zauna dukansu kusa da ita sosai sigar lallashi

sultana tace" damu da safiya we all sisters ayaanah, nd yes akwai age gap tsakaninmu sosai, aiko kulthum na girme ta da watanni amma it doenst mean dat zamu taware junanmu base on silly age gap issures saidai base on charcters, ke kanki kinga bhvrs din safiya, in ana right ita tana left, is like she just hate every body, asalin ta fitinanniya

ce...nd ure nothing like her dats why i choose u to be our forever friend, kituna kin rufa min asiri nd u took blames for me...nd u even agree to sleep here with us a dakin kulthum for her sake duk dama baki gama saninta ba..kinga ai bazaki hade halinki dana safiya ba...

abunka da yaranta dan hakan da suka gaggaya mata sai taji hanklinta ya kara kwanciya da su sosai. daga nan suka rungume juna nd they promise each other to be friends nd sisters forever.

suna gama maganan suka tattashi suka kimtsa kowacce tay kyau snn suka dauki kayan sultanan sukaje sukay sallama ma anty safeera har daki kafin nan suka sauko sashen ammi karama suka maida kayan duka a akwatin sultanan ammi karama ta rako su har waje tabawa sultana cookies da su dambun nama dayawa acikin take away roba.

bayan anyi sallama da kowa ammi babba ta nace saida bappa zaidu ya dauketa ita daya a motarsa suka wuce

kulthum ma bata wani tsaya sosai ba tunda maheer yace taje tay karatu sai ta koma ciki, ya rage daga ammi karama sai ayaanah da sultana da mujaheed

har mota suka sakata suna mata bye snn dukansu suka juya ciki mujaheed yaja ayaana suka koma dakin kulthum suka same ta harta fara karatun su kuma suka zauna agefe akan sofa still yanata mmkin yadda akay ta iya smooth turanci

tambayoyi ya dinga mata da english tana bashi amsa har yazo ya gane cewa inganttcun malamai da coppers daga kudu ake yawan kai musu chan kuma dama basuda yawa amma dake tasaka bokon aranta shiyasa ma ta dage har ta iya turanci harma fiye da addanta inayah

daga harabar gidan kuwa maheer na zama agaban motar ibaad ya zago ya miƙa masa key yace masa suje gidan kawai shi sai gobe da safe zaizo kuma ya riga ya gayawa bappa zaidu har kuma ya amince..

jin hakan yasa saida maheer ya fito, suka tsaye agefe yafara matsa masa yagaya masa dalili duk ya dauka wani issures aka samu da ammi babba, dakyar snn ya sanar da shi cewa yana so ne yay magana da hajiya akan karatun ayaana nd he want it to be privtely shiyasa ma zai kwana.

da maheer har ya budi baki zai tambayesa why privately tunda sun saba komi atare sukeyi

saidai sanin cewa asali yay niyyar bazai gaya masan bane kawai yasa yay shiru, dan yasan da inda yana da niyyar fada masa plan dinsa akan ayaana da tuntuni sunyi mgn da shi an wuce wajen

,..gyada kansa yay yace masa babu komi sede daga ganin yadda ya bawa ibaad din amsar cikin attitude kasan har ransa baiji dadin hakan ba, da wani abu aransa ya koma motar daga shi sai sultana suka wuce gida kai tsaye

Direct ibaad ya koma cikin gida bai tsaya a ko inaba sai cikin personal room dinsa dake sashen maman nasa yana zama yafara cike ciken forms da files yanabi yana saka hannu nd reading tru each rules nd schdule throuhly daga na bokon harna islamiyan.

yana gamawa ya ajesu akan desk dinsa snn ya rage kayan jikinsa ya zauna yay karatu for like 3 good hrs both na club dana asalin schll wajajen 11.30p. na dare ya gama yashiga bayi yay wanka ya hado da alwala, yana dawowa dakin yazo ya samu mamansa har ta aje masa hot herbal tea aka desk dinsa, murmushi me sanyi yay kafin ya dauka yay bismilla ya zauna ya shanye kafin nan ya kimtsa kansa cikin pjamas me kyau ya kwanta kafin kace wani abu bacci ya daukesa.

tsabar doguwar hira da english da ayaanah sukayi da mujaheed yasa still anan dakin kulthum din ta kara bingerewa da bacci suka sha baccin su atare.

washe gari da sasafe suka tashi sukayi ibaadansu har sukay karatun qur'ani saidai haryau irin wnn momnt na dago mata tashin hankali sosai musmn inta y wani abu data saba yinsa sa inaayah sai taji gabaki daya zafin mutuwar ya kara dawowa mata sabuwa

kusan abunda ya saka ta tsiri yin baccin safiya kenan duk dama dacan bata saba ba dake yau sunday dama rnr hutu ne babu wanda yazo ya leka dakinsu sai MJ shima sama sama ya lekesa da asban snn ya wuce room dinsa daga nan basu kara ganinsa ayaana tafara bacci sosai harda minshari

dagata bangaren maheer kuwa har saida suka idar da sallahn frh da babansa snn ya same sa da complain dinsa akan yadda ibaad yafara waresa akan magann rywar ayanah

bappa zaidu yay shiru yana jinsa har saida ya gama complain dinsa snn acikin lumana yafara warware masa abunda ake ciki...

yace masa ayaana ai ba marainiya bace, kuma bawai an basu ita kyauta bace. shiyasa komi acikin tsari zasu bishi dan kar wata rana asamu bacin rana, snn tunda hajiya tace musu mahfiyarta acan tazabi ibaad din yay ma yarta jagora arayuwrta ai kamata yay su suzage suna bashi goyon baya bawai duka ataru ana rarraba masa hanklinsa

kashi kashi ba, .he told him alot of things da bai sani akan case din ayaanah ba, musmn part din baqin halin babanta ayadda haj mairo ta gaggaya musu, har dai yazo ya fahimce shi sosai.

Sai wajajen 9am su ayaana suka farka a bacci as usual sukayi wankansu fess sunje gaishar da anty safeera ta kamasu adakinta ta musu kwalliya mai kyau harda shafa musu jan baki. ayaanah slwys feels awkwad da abun amma zuciyar yaro data ga anty safeera tana son mata kwalliya sai abun yafara shiga ranta kadan kadan duk dama bata saba dashi ba. wani irin gyara mata gashinta tay da gel ta mata donut me kyau tasa mata kwalli da lip gloss akan pink lipstick she looks very fine har ta musu hoto.

dama can sultana ke zuwa dauko musu kaya dake yau bata nan tun ahanyar dawowa daga dakin anty safeeran sukay sallama da kulthum akan zata koma wajen ammi karaman kawai

kulthum ta rakota har kofa snn ta koma, sashen was soo quiet nd cold banda uban qamshin tureren wuta masu sanyaya zuciya bakajin komi

kai tsaye ta wuce dakin su da safiya, ta samu safiyar tana matse akan sofar dakin tanata karatun qur'ani kana kallonta kasan na dole akasata idonta ya cika da ruwa ita dayane a dakin amma ayaana ta lura jikinta na rawa rawa. kallon kallo sukama junansu batare da sunyi magana ba ayaana ta cire hijabin kulthum dake jikinta ta jawo akwatinta ta fara cire kayan sawa half gown da wandonsa me dan fadi ta saka already anty safeera ta tattale mata sumanta da pins da ribbons sai batasha wahalan yafa gyalen kayan akanta ba.

ganin yadda tay kyau sosai yasa safiya taja mata wata arniyar tsaki me kara itade batace mata uffan ba ta shafa turarenta sama sama yadda taga su sultana sukeyi ta kama hanya ta fita gaishe da ammi karama.

tana fita ko dakinta bata karasa ba ta sameta kitchen tana kan soya kayan miya zatay musu spagheti

Sallama tay da sanyin murya suna hade ido da ammi karama ta karaso ciki da wani irin sanyin ladabi tabita durkusa kasa kanta na kallon can can kasa tace"ina kwana ammi..ammi tay murmushi me sanyi tace "lafya.. ayaana kin tashi lafya? tace lafya kalau, uhm..akwai aikin da zan taya ki dashi ne?

murmushi ammi ta karayi tace "tashi akasan nan tukuna,. mikewa tay tsaye snn ammi tace mata ga waje can kije ki zauna,, tana zama akan chair ammi ta kawo mata tea me masifar kauri ta bata tace mata tasha, duk irin kunyar ayaana da sauri ta karba sabid wani irin qamshin dadi da tea din yakeyi

tafara sha kenan ammi tace" ayaana, i knw u will be lonely sultana ta koma gida amma karki damu akwai safiya da kulthum. they are ur sisters. u can play with them suma yan uwanki ne,..snn zuwa anjima idan munyi breakfast zanxo dakin naku sai kema k shirya kayanki a wardrob dinki dake da safiya will be sharing the room, amma zanso ace kowa yana kulawa da kayansa

..banda kuma kazanta banda fada ku zauna lafya da juna kinji ko? acikin ladabi ayaanah tace naji in sha Allah zany duk abunda kikace din ammi na murmshi tace good girl gashi kin sha kyau safeera tana ji daku fa..karamin murmushi tay tun batace wani abu safiya ta karaso kitchen din haway faca faca a face dinta ta kalle ayanaah da tsawa

tace "keeee...wai kijje yanxun nan yaa ibaad yana kiranki a dakin sa tana fadin haka ta rushe da wani irin kuka bakinta harna fitar da jini..

sosai gaban ayaana ya fadi taji tsoro ya rike mata zuciya ....

ammi tama ayaanan ido akan tashi tatafi waajensa kawai ayaanah bata kuwa bata lkci ba ta mike tafita a kitchen din da wani irin fargaban ibaad din a zuciyarta sosai...

tana ficewa ammi ta kalle safiya tace ke kuma meya hadaki dashi again??.......zata yi magana ammi ta kara kai mata duka tace koma miyene maganin ki kenan bake kin zama shedaniya baki tashi kiy sallahn asubah ba?ai dagangan naki gaya miki cewa xai kwana agidan nan tunda ke bakijin maganan uban kowa, bakima tsoron Allah sai tsoron yayanki ko? toh aiko kasheki agidan nan zaiyi bazan kara hanashi ba..just see the way u're talking to this girl now, ure so mannerless...kina wani mata tsawa kina hantararta ke din uwartace..uban metake miki ehh?dada rushewa da kuka safiya tay cikin sheshska tace ammi dan Allah dan Allah kiy hakuri kibashi haquri wallah bazan kara kin tashi sallah ba...

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025