ABUNDA KE 'BOYE...

30

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE.💫

arewabooks@surayyahms

⏯️3️⃣0️⃣

ammi taja tsaki tace Da Allah tafican sau nawa kina sani ina rokonsa cewa zaki canza hali haryau kin canza ne?toh wallah safiya ki shiga hankalinki, dan babu ruwana a case dinki da ibaad kuma wallah yau bazan karbeki awajensa ba..kawai ki fita kiban waje..

Da wani irin kuka ta juya tafita da sanyin jiki saidai tana kaiwa kofarsa ta hadiye kukan tay shiru ta tsaya cak tanata kkrin share hawayenta dan tasan inta shiga masa da kukan banza zai iya tattakata.

ata bangaren ayaana kuwa already a tsorace da ganin yanayin daya fasa bakin safiyan ta taho tunda tay sallama gabanta yake faduwa sosai.

kanta na kallon kasa ta shigo cikin niimtaccen dakin wanda ko kadan bazakay tsammanin wai safiya bane dan wani irin tattalashi da akayi da tsafta, koina is sparkling clean, raɓar Ac dana turaren wuta daya qama sashen ya gaurayu da tsadadden turarensa xerjoff naxos har wani bacci bacci rairaiyi raitayi taji atmosphern dakin yana neman sakata.

tunda suka hade ido ya amsa sallamarta ko sake kallonta baiyi ba, ita kuwa harta karaso kallonsa take yadda ya mugun tafiya da imanin ta id just past nine amma har ya cancanda kwalliya wata calm Burgundy short-sleeve shirt ne da Black jeans da classy black men Bracelet a hannunsa yana zaune akan kujera akame kmr dan sarki..

tamkar wacce bata mumfashi ta taho gabansa ta tsuguna

asanyaye tanamai hana kanta jin wann uban feeling din dake janta atacikin ranta duk dama batasan na meye bane amma sai take jin matsanancin tsoro kar ta shagala itama abunda ya faru anty zainab arifah ya faru da ita.

cikin tattaro makanta nitsuwa da wani irin sanyin murna tace "ina kwana??....bai amsa ba saida yaja minti biyu snn yace "you dont knw my name?kara fadi gaban ta yay tay shiru, muryan sa a dakile yace"ki sake memeta abunda kika ce wann karon karki kara gaisheni kamar wani masinjanki... tana budan baki taji muryanta na rawa rawa hawaye taji zasu xubo mata tay saurin shanyewa ahnkli tace uhmmm iina kwana" idonsa ya zaro yace ina kwana what?i dont have a name in dis ur tiny little mouth wato dan nace miki kidena cemin me mota shine kike neman rainimin hankli ko?

da sauri ta girgiza kai tace "aa fah,...yace okay say my name'

hawayen datake dannewa ya zuba mata ta kara sunkuyar kai snn tace ina kwana... yaya..i..i...tay shiru,"saida ta runtse ido tace yaa ibaad"

..yaja tsaki a masife yace "Ohhh dama kinsan sunana kike zuwa gabama gatsau kice min ina kwana? kika kara cemin uhmmm, ko ina kwana zakiga abunda zan miki..

batace mishi komi ba ta cigaba da hawayenta har ya miƙe tsaye ya dauko duka papers din yazo ya zauna agaban ta tare da su

karamin shiru ne ya ratsa wajen har saida ya tabbata tagama share hawynta ta nitsu kai tsaye yace"...yau sunday gobe monday kishirya zanxo nakai ki interview a sabuwar school dinki

wani irin garas taji saukar maganan ji datay yazo mata a kunneta kamar doka da oder.

yacigaba da cewa a new schedules dinki akwai zuwa islamiya, da lessons 4 times a week the remaining 3 days zaki amfani dasu ki huta snn kiy revising me kika karanta..

yana kaiwa nan ya miƙa mata papers din da biron sa ya nuna mata inda zatay signing one after d other tana gamawa yayi kasa da idonsa suna kallon juna with more gentler but no nonsense voice yace.."ai ynzu kingane me nake gayamiki ko?

tsabar rudewa duk dama ta ganen amma ta girgiza kai tace aa bangane ba yaaya..

..gyara zamansa yay yace dago ki kalleni,babu shiri ta dago idonta ta zuba anashi suna hade idon yace zan sakaki a makaranta domin ki cigaba da karatunki anan, mmnki ta rubuta sako aciki duk gayamin dede inda kika tsaya akaratu, baza a maidake baya ba anan zaki cigaba ne daga dede inda kika tsaya shiyasa ma zaa miki interview me tsauri gobe...,kobakici ba kuma dolene zakiy wani makarntar daban..dan haka kisani der no time for jokes arnd here dan nan bakamar can garinku bane,zaki hadu da kalubale dayawa but i dont care..you must produce the best result to ur ability inbadai dama karya malamnku nacan sukeyi suna biye dolancinki ba..if ure truly smart like they said then prove it here, duk gidan nan babu dolo..so..u eida come first or nothing. doka ta na farko dake kenan tunda har naji cewa kike zakiy talla dan tsabar sakalci da rashin tunani wato yarke innan harkin manta da alkwarin da kika ma mamanki da addanki ko? toh in sha Allah kika sake kika kawomin batun talla ko wasa akarantunki ranar na lahira sai yafiki jin dadi agidan nan..ahnkli yake magn amma bakaramin rawa jikinta yakeyi ba hawaye na zubowa a idonta kamar ruwa ta rasa abunda yake mata dadi..

muryansa na fita ahankli yace "u can cry a u want amma bazaki saida wani abinci agarin nan ba snn kuma na riga da nagaya miki sauran dokokin tun acan gidan so once kika fara schl kowani rana nazo zan iya tambarki abunda kikay aji, inba baki gaya min gaskiya ba ina da lambar kowani malmnku zan kirasu awaya inji, no watching tvs or using any gadjet untill ur home work are complte. ur lesson is very compusory..nd at end of the week zaki gaya min me dame kika koya..pls do not test my patience. da sauri ta gyada masa kai

yace gobe idan mun fita zakiga drivernki, kuma ai kinsan fuskokin yan gidan nan duka ko? ahnkli tace ehh yace toh inba daya acikinmu bane yazo daukarki a schll karda ki sake kice musu kinsanshi koda kuwa yace miki nina aikosa koda ya ambace sunanki dana mamanki da babanki dont u eve follow him.

cikin sanyin jiki tace toh nagode yaa Allah ya saka da alheri, naji abunda kace zanyi karatun..

daga nan yay shiru baice mata komi ba can ya dan jingina bayansa da kujera ya zuba mata duka idanunsa yana jin wani irin rauni rauni da kasala musmmn yadda fuskarta dayaji ssnyar kwalliyar yay caba caba da ruwan hawaye harsuna ɗiga akan dan karamin cute lips dinta like a molten ice, cikin lumshe ido da budewa yace give me those papers...

miƙewa tay jikinta a mugun sanyaye ta fara isowa kurkussa dashi qamshin turarensa yana wani irin bugar da ita ga wani irin dan iskan kallon dayake mata dats piercing direct into her small heart, idonta na kallon kasa ta iso gabansa tana kuwa miƙa masa pprs din taji ya kamo harda hannunta izuwa anshi ya fixgota jikin shi lkcin ji take kamr zata saki fitsari sai taga yaciro hankynsa me kyau

yakai karamin bakin ta ya goge lipstick da duk wani make up dake wajen ya rarrage mata powder wanda tsabar tsoro suna kallon juna amma ji take kamar zata shide yadda ya mannata a jikinshi a sosai

muryn sa na fita ahnkli yace

"ranar bana cemiki wnn abun fuskarkin baya miki kyau ba? in kuma neman maza zakiyi kigayamin saina maidake kauyenku kije kiyi aure acan, but not now..kibari se kin girma kinsan me kikeyi nd if u truly want to seduce me to marry you saikita sakawa..

wani kuka me tafe da kunya da batasan daga ina ya fito ba ta fashe masa dashi dan batay tsammnin zai furta mata haka cikin shagbabben kukan tace "yaa, ammin kulthum ne fa takemin ni bance inaso ba ai banma iya ba..yana kallon idonta yace "amma ai kinsan zaki iya kuma ai kina so toh kiyi hakuri bayanxu ba sabida bazai amfaneki da komi ba. this make up thing isnt even for children inde baneman maza kike ba toh duk sanda tace zata miki kice mata kinfison fuskarki ahaka..

da sauri ta gyada masa kai da hankyn still ya goge mata hawayenta tass tana kkrin sauka ajikin shin caraf safiya ta bude musu kofar har saida ta shigo snn ta mannu a bango da rawan murya tace salam alaikum warahmatullah

Da sauri yabi ya daga ayaanah ajikinsa yanamai doka ma safiyar harara zatay magana kenan yanuna mata hanyar wajen a mugun tsawace yace" sheigiya..fita..ure banned frm entring dis room...kije kijirani awaje naga alaman baki daku bane..

tana fita ya kalle ayaanan yace "ke kuma ga duka kayan schl dinki acan ki kitattara su kije can kinunawa ammi zata nuna miki yadda ake amfani dasu

..nd dont forget if u need anything kigyamin ko ki gaya ma ammi zata gayamin kinji ko..

cikin ladabi ayaana ta amsashi da toh yaya.. kyaleta yay anan ya fice ya samu safiya akofa

batasan me yace ma safiyar ba, tana fitowa da kayan kofa taga safiya ta hau karba tana tayata kwashewa suna kaiwa tare wa ammi karama

suna kaiwa duka kayan ammi tace su bari sai anyi breakfst an dawo tukuna zasu bude su gaggani. har kuwa akaje aka ci abincin safe a sashen hajiya mairo ayana bata nuna wa kowa alaman tay kuka ba banda make up da ya zama babu a fuskan ta yanzu.

immidietly ana gama breakfst din ibaad ya fice agidan abunsa..

tun bayan fitarsa su ammi suka tattaro kayan karatun ayaana sukaxo falon hajiya dashi daga ita sai safiya da ayaanahn aka fara bude kayan daya bayan daya wanda tun daga kan uniform suka gane a schl dinsu sultana akasa ayaanah.

hajy ta gama bambaminya tay shiru tana mitar waimesa ba asaka ta tare da safiya anan kawai ba, dakyar ammi ta ganar da ita ai nasu safiya da kulthum ba ahade yake da courses din islamiya ba shiyasa..kominta na yar gayu yar gata masha Allah, sosai safiya ta kasa boye kishinta ta dinga bori ma hajya wai itama saidai asaya mata irin jaka da takalmin ayaana kuma ai bata da stationriees na zamani da yawa haka..tun abun be dara ayaanah but dataga borin da safiya tay tasan cewa lallai bakarmin kashe mata kudi akayi ba...

wani irin dadi taji aranta na hudata asihirince haka su ammi suka sakata ta gwada komi ajikinta, masha Allah sun masa chass chass sai can da yamma bayan ammi tay mata arranging kayanta a wadrobe kafin kulthum tazo ayaanah ta nunna mata sabhin abubuwan schl inta duk dama bataso da akce ayaana batare da su zatay schl ba.

dake tun da ibaad ya fice da safe bai dawo gidan ba hanklin kowa akwance yay bacci akan kayan schll din nan har yanxu safiya taki ta mata magana

early morning 5;30 on d dot suna tsaka da bacci sukaji an buga musu kofa jin muryan ibaad yasaka safiya tay wani irin firgitaccen tashi..

tana jin muryansa ta kalle ayaanah datake kkrin farkwa da kyar, da karfi ta zage ta maka mata mari ayaanah tana mikewa zaune tace "Allah ya isa min munafuka kawai aida bakizo gidan nan ba da yaa ibaad bazaina zuwa yana takura ma rayuwa na wallah sai kin bar gidan nan..

Hanklin ayaana sai ya kara tashi dataga yadda safiya take kukan tun daga kasar zuciyarta harta sauka akan gadon cikin toshe muryan kukan da karfi tace yaa fa mun tashi..tanaji yaja tsaki yace start geting ready for school

...hawaye na zuba a idonta tace tohh ...yana barin wajen ta kalli ayaanah ta kara fashewa da kuka tace Allah ya isa..ni wallh sai kin barmin dakina..ai nan ba gidan ubanki bane zaki jawoshi yazo yay ta takura ma mutum shiken bazan yi bacci ba

itade ayaanah batace mata komi ba, tana zaune akan gadon har safiya ta gama wanka ta fito tafara salla,itama sai ta tashi tashiga tay wanka taga babu sabulu sabida gabaki daya safiya ta kwashe abubuwanta ta boyesu tsabar baqin hali, tana gama watsa ruwan ta doro har da alwala

zaman kurmaye sukayi a dakin kowa na abunda ke gabansa can ayaana ta bude wani waje ta hau tattaro nata sabulan da su man da ibaad ya tsiya mata safiya nata kallonta har takai wajen wanka ta ajesu agefe ta jerasu

confidence din yarinyar da saurin gane abu har mamaki yke bata har cikin aranta tasan dai duk tsiya bazata jima tana mata isknci ba duk alama yanuna mata cewa yarinyar nan zata waye ta kuma bude ido da wuri badajimawa

jim kadan suka gama duk wani shiryawan da zasuyi zuwan kulthum dakin dan ta dubata yasa ayaanah taji hanklinta ya dan kwanta dan wani irin tunanin addanta take yi aranta haryanxu, she cant belive it cewa zata koma karatu kuma a binni amma babu addanta inayah atare da ita,.she deeply hides her tears in her heart sabida batason tafara kuka akan haka ibaad yaji haushi ya mata fada agaban mutane, kusan tare suka fito wajen cin breafst da kulthum kowa yay kyau acikin unform dinsa na su ayaanah cambridge grey ne da fari nasu sultana kuma turquoise da fari, hanklinta duk atashe yake har aka gama gaisuwa aka ci breakfs kowa yana ma ayaana murna da nasiha wanda duk bama jin me suke cewa tay ba, her heart was busy drenching with grieve yawan surutun hajy mairo tare da kara sako mata zancen ummanta da ayaanah saiya zamana rauni ya riketa ataciki sosai.

har anty safeera da su mujaheed suka gama mata hotonan first day at schll da wayoyin su basu gane kanta ba, they all tot dat shirmen yara ne najin tsoron first day at schll dinsu kusan babu kalar rarrashin ta da mujaheed baiyi ba amma batace masa komi ba sai gyada kai har ya gaji da surutun yay shiru

uncle moh ne bai wani ji dadin abun aransa ba sai bai nuna ma kowa ba har saida ibaad ya taso yaran agaba kowa ya wuce makaranta

shidakansa ya dauke ayaanah, driver kuma ya aje su kulthum da safiya. bayan wucewr su bada jimawa ba uncle moh ya taho kamar xai same hajia da maganan sai kuma yay wani tunani ya fasa, in his imagine slight yaso ace asa ayaanah a schl din da matarsa safeera ta tay dacan, which is one of the loudest british schools a kano wanda yaran yan karya ne aciki sai kuma ya tuna cewa in yay hakan baida wani kwakkwaran dalili da zai gaya ma hajy mairo na saka ayaanah a schl din dayafi na sauran yaran gidan tsada sosai tunda kowa yasan duk salon koyarwn dayane wancan din dai suna yake dashi sosai har kasar waje...one of the few reason dayaji yana son safeera kenn sabida duk wani abu datay a rayuwarta na gani na fada ne na krya na nuna arziki, safera first class slay queen ce he is proud dat she attended the best schlls, travel abroads dai duk rayuwar karyan nan tay su datake karama nd he sumhow want to push ayaana to the same fate sabida tay matching level dinsa sai yaga kamr hakan kuma bazaiyu ba

share batun yay ya wuce wajen aikinsa kafin kace wani abu gidan ya dauka da shiru

dataga fannin su ayana kuwa suna isa gate din schll din taga ibaad ya tsaya daga gefe basu shiga ba yay parking a bakin hanya wayarsa yana kara sauka ya barta aciki yaje ya same wani mutum suna magana dacan har ta dauke kanta sai kuma taga kamar tagane mutumin sosai...

kara saka idonta tay ta madubin motar taga ashe malamin science dinsu nacan anguwar tudu, duk sai taji mamaki ya cikata tanata tunanin a ina ibaad yasanshi

batace uffan ba har ibaad din ya sallamesa ya dawo motar da wani farar takarda snn ya karasa da su cikin makaranta da bata taɓa ganin irinsa a fadi da girma da kyau ba dan ko da suka sauka ji tay kamar wani duniya nadaban take tsaya..

gaba yay da jaka abayansa tana bibiyarsa abaya baya har suka shiga wani katon building dake gidan sama ne security ne yamusu jagora inda ake interview duk taji ta rude dataga har da turawa kowa yana latsa computersa kuma duk turanci akeyi awajen babu hausa

wajen zama aka bata ta zauna ibaad kuma ya shige cikin wani office 10 mins later wata mata sanye da dark blue uniform tazo da murmushi da harshen turanci tace ma ayaanah tabiyota suje ciki .. ayaanah taki motsi ta zuba mata ido, matar tana murmushi ta mika mata hannu tace "haba yan mata muje ciki..karkiji tsoro ure safe here. da sanijn murya ta girgixa kai ssn tace yayana yace min karna biki ko ina ai bansanki ba.."Dariya matar tay tace" very good girl hmm ure security cautious.. to shkna badmuwa bari naje na kirashi"

ayaanah ta gyada kai, sai can data gansa tare da matar snn ta jawo jakarta tazo ta samesu suka karasa cikin office din atare..

tunda tazauna kusa da ibaad yabon wayon ta kawai mai interview din yakeyi sosai

..already bappa zaidu ya nema musu alfarma againts the normal school protocals dan basu daukar dalibi haka kawai musm ma daga kaskantaccen mkrnt na kauyr suyi admiting dinsa kuma a ajin daya baro. dakyar da ɓarin kudinsu snn suka samu duk wata alfarma wa ayaanah dan kar a maidata can can baya

Dan haka ne ma yasa ibaad yay going thru nooks nd cranies har saida yay tracing ya same number malamin science din su na tudu yabiya kudi aka bashi previous duk wani info da result transcripts da recomendations na duka perfomances inta na karatu abaya.

mai inteview yana ta mamki yadda taga komi na boko tanaci sosai babu faduwa islamiyan ne take baya bata yi nisa sosai ba kuma bata kkri akansa kamr na bokon

da can exams zai mata sai ya fasa, da turanci ya mata few question akan english, elmntary science,mathematic, civic education, da few other topics yaga ta amsasu sosai with her clean village girl english babu wani slang ajiki yadda ake koya musu haka takeyinshi corectly nd smoothly kuma confidntly

basu yi 20 minutes ba ya gamsu da potential inta sosai, yace za'a saka ta ne on trial admission idan akaga ta miƙe tay kkri wann sesssion din

kawai za'a kyaleta ne ta cigaba. islamiya ne aka mata repeating aji daya aka buga musu acceptance letter da rules da schll ajiki dayan matar ta karanta ma ayaana komi ta mata bayaninsu sosai snn aka sata tay signing. she was a bit okay face saida taga ibaad ya fara musu sallama zai tafi tafara jin hanklinta ya tashi

shiru tay har aka gama komi suka bar wajen interview suka sauko ya damkata ahannun caretaker dinsun wacce itace zata kai ayaana class.

yana juyawa kuwa ayaanah tafashe da kuka sosai matar ta kasa gane mata tun ibaad baikai ga tada motarsa ba tay gudu har tana haki takirawosa.

kirjinsa na buga ya biyota duk ya dauka wani abu ne, zuwa yay yasamu ayaanah ta zauna akasa tanata kuka dan guntun masifar daya taso masan ya danne acki ya karaso gabanta yace "me aka miki kike kuka??

shiru tay ya saka hannun ya fizgota tsaye yajata gefe yace

"Bakison makrntar ne?asanyaye ta girgiza kai a masife yace "then what? da muryan kuka tace "nifa tsoro nakeji, ai kace zanga sultana anan kuma banganta ba.

cikin lunshe ido da budewa yace dama dan ita kikazo karatun? tace aa..yace "ke bani son sakalci. waye kikaga yana kuka anan dan ankawo sa makaranta.. wato kin saka talla aranki ko? da shagon hajy nakaiki yanxu zakiy kuka ne?hawayen na zuba tace a'a kawai nifa tsoro nakeji..cikin harara yace "kinzo a tsakiyar term, kuma kinji sunce miki ure on trial admission..ayaanah idan baki dage wann karon ba zasu maidake ajin baya kuma shine zakice min kinajin tsoro..did u want me to slap you? a sanyaye tace "no, da muryan kukan daya kara zuwa mata bazata tace..toh dan Allah kayahakuri mana yaaya ai gani nay zaka tafi kabarni

..ajyn zucy ya sauke cikin sasauto da muryansa ya kara riko hannunta cikin nashi suna kallon juna cikin salon yaudara da lallami ya fara tuna mata wahalar da ummanta zatasha in bata nitsu tay karatu ba, kuma yace mata ta tana tuna addanta, she shud read to make them proud. haka ya dinga lallabata har saida yaga ta nitsu sosai snn ya rakasu ita da care takern har bakin ajin ta shiga ta zauna akan seat dinta

snn ya juya ya wuce schll da sauri dan bakaramin latti ta sashi yayi yau ba.

half of the time a schl din she was just thinking about his words in her head taga dai bata da wani mafita na jin rauni kasancewarta ita daya anan binni dolene tay karatun sosai.

gashi yan ajin sai kallonta kowa yakeyi dan seat dinta ita daya aka bata batada seat mate duk da yawan kallo sai batace ma kowa komi ba dan abune data saba dashi tun tuna kauye ake mata irin wnn kallon

kwata kwata schll din bai mata dadi ba har saida aka tashi break suka hadu da sultana dadi kamar zai kashe ta she was soo happy dataji wai schl dinsu daya da ayaanah, altho she is one class ahead of her tunda aka fito a break taje ta nuna mata wajaje acikin schl din har kamar karsu rabu

ata fannin ibaad kuwa har saida ya fito sallhn azhr kafin suka hadu da maheer acikin masallci maher bai kuwa boye masa fushinsa ba ya kuma gaya masa abunda bappa zaidu ya gaggaya masa.. ibaad baice masa komi ba face har sanda suka kama hanyar zuwa dauko su sultanan a schl snn yake sanar dashi labarin duk abunda ya faru dashi a tudu da duk wani abunda ya samu ayaanah,...

wa shi kawai ya gaya wa abunda ke cikin takardan wasikan tawuure, hannun maheer haka ya dinga rawa akan steering dan bai tabaji irin wann abun arayuwarsa ba..

jiki a sanyaye ibaad yace kafin ayaana taga mahaifyrta zai dau lokaci sosai dan acikin wasikar taawure ta gaya masa cewa matsafan majiya sun mata mummunn jefar daya fi karfin tsarin dayake jikinta, wanda ba ciwo ya sakamata ba amma duk inda taje zata zauna dan ataimaketa baqaqn aljanu zasu kona wajen da wuta kurmus

tace masa gidan kawun ta dataje a jigawa kwana uku kawai tay gobara ya kama gidan ya cinye musu gidansu kurmus, da suka gane ajikinta ne sihirin shine suke koreta. ynxu haka ta shiga wani duniya na neman maganin wn sihiri har saita samu taimako snn zata dawo wa yarta ayaanah

ynxu haka bazata iya muamala dakowa ba face har sai aljanun wutan nan sun dena bibiyarta inba haka ba duk wanda ya taimketa wuta zai masa asarar dukiyarsa ko rai, yan daidaikon abubuwa ne acikin wasiqar bai gaya ma maheer ba sabida ya shafi privacy tsakaninsu

..

gabaki daya jikinsu duka yay sanyi jikin maheer din na rawa banda salati babu abunda yake furtawa

sai yanxu yagane cewa babu shakka safetyn ayaana ya danganta ne da zama datakey a karkashin kulawan ibaad dan in har zasu iya ma taawure da tsafi zai ita yuwa suna lura da rayuwar ayaanah.

altho taawure ta gaya masa nan da shekara zasu iya dauke idonsu akansa inhar bai batar da ayaanah to bazasu sake nemansa ba..

hakuri maheer ya dinga bashi da judging dinsa da yayi har suka isa schl din hanklinsu duka tashe jikin maheer kuma bai bar rawa rawa ba.

dayaga ayaanah sai ya dada jin tausayinta ya mugun kamashi dakyar ya iya shanye hawayen sa suka kai su gida sharply sultana aka fara saukewa, snn suka kai ayaana gida ta samu ma har su kulthum sun rigata dawowa ranar hirar schl suka dingayi a dakin hajiya ayayinda ita kuma ta fara batun hidimar komawa shagonta da zasuy wnan asabar din

tsakanin ayaana da sultana monday friday ne kawai basu islamiya 1, 12. haka suke tashi a normal schl hours, but tues wed thur duk sai karfe 3 ake tashin su su dawo gida suyi lesson 4:30 to 5.30pm agida amma malaminsu daban daban.

farko da bata saba da kowa bakaramin hawaye ta dingayi yi ba,duk tabi ta dagawa mai kulawa da ajinsu hankli,yara yan uwanta sai kallon shirmen ta sukeyi.

Aranar harsanda aka kaita gaban shugaban makaranta

,dake mace ce harta dauka ko ayaanahn batada lpyane take yawan kuka, amma daga tace zata kira ibaad saitaga tayi shiru ta nitsu..

Tunda shugaban makranta ta fahimce hakan, ana zuwa da case din cewa ayaanah tana kukan banza da wurwuri zatazo da waya tace zata kira ibaaaf shikenan kuma anyi maganinta Ahaka haka harta zo ta sake jiki tayi abokai a ajin ta saba da karatunta ta mance da batun kuka kullum a break suna tare da sultana kamar yan uwan jini haka suka shaku da juna

After 2 months.

Fara zuwan makarantar ayaanah sosai yafara sauya mata hali tadawo bata ma da kwakkwaran lokacin hira da su kulthum agidan dake ibaad was on her neck duk da baida lokacin kansa amma haka yake takurawa don yaga ayaanah ta nitsu tay karatu, acikin wata biyun nan kusan kullum saiya xo gidan ya zakwalota ta masa bitan karatun da tayi a makarnta

...both islamiya da boko, gashi tana bala'in jin tsoronsa bata iya yin garaje musmmn ganin yadda yake casa safiya da bulala kamar jaka.

...within no time halayyar ayaanah gabaki daya suka soma sauyawa suka dawo masu kyau gwanin ban sha'awa, duk son ta da su mujaheed da anty safera haka taja baya dasu, bata sakewa amata kwalliya inba ranar asabar da kowa yake nan ba.. basirarta da ilminta da tarbiya da nitsuwarta kuwa sosai suke dada fallasuwa tareda karfin jajircewan ammi karama akan tarbiyanta sosai

yanzu haka inkaje gidan zaka dauka ayaanah ce asalin yar cikin ammi karama, tana mata biyayya sosai bata da kwuiwa koda ammi tahanata aiki zaka ga tazo ta nace sai ta tayata ahaka ahaka har take ganin yadda ammin take abinci abin yana bata sha'awa sosai saidai bata da lkcin koya sosai..

GOBE SASSAFE ZAN TURO WANI PAGE INNAGA COMENT

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025