GIDAN Y'AN BARIKI

Gidan y'an Bariki Chapter 3

by @pinkyjay


*PAGE*  5️⃣▶️6️⃣


Kamal kuwa suna gama waya number Suhana ya fara kira amma bata ɗauka ba, sai text ya tura mata amma ba amsa, Suhana kuwa bata duba wayarta ba sai da ƙarfe huɗu na yamma nan ta ga kiran Kamal da text ɗin da ya tura mata, kiransa tayi bayan sun gaisa yace "Hana Baby wani aiki ne ya samu na kuɗi." 


nan ya gaya mata abinda Sultan yake buƙata tace zata yanke shawara zuwa gobe zata kirasa, tunani ta fara idan tayi aure burinta fa na gina gidan kanta ta saka mai suna GIDAN ƳAN BARIKI, wata zuciyar tace ai auren da wani lokaci ne ba jimawa zakiyi ba, kafin ma a ayi auren zaki iya fara ginin gidan da wannan tunani ta tsaida shawara,


zatayi auren saboda ko ba komai zata samu kuɗin da zata kula da rayuwarta da sauran ƙayenta, cikin washegari ta kira Kamal ta shaida mai ta amince amma matsalar, ina iyayensa zasu zo neman auren ta Kamal ya tambaye ta, tace "Kamal nima abinda nike tunani kenan." 


Yace "Yanzu dai ki shirya zaku haɗu a taraka hotel, zanzo na ɗauke ki." Ta ce Okey sukayi sallama ƙarfi biyar na yamma kamal ya zo ɗaukarta lokacin Jamal ya fita, zuwa gidansu, suka wuce taraka hotel, sun isa room 30 suka shiga kai tsaye, wani ƙamshin turare ne ya dake hancinta, mai sanyaya zuciya, 

saida ta lumshe idanu, Kamal na gaba tana bayansa, har suka ƙarasa parlo zama sukayi kana ya kira wayar Sultan, sai ringing ɗinta yaji kan kujerar da Suhana take zaune, yace "Ashe yana kusa ma ina zuwa." Yacewa Suhana kana ya fita parlon Bar ya nufa dake cikin hotel ɗin a chan ya same shi zaune yana shan maltina, 


Kamal yace "Sultan mun ƙaraso tana ciki." beyi magana ba sai da ya kammala abinda yake yi kana ya tashi yana gaba Kamal na bayansa har suka shiga ciki lokacin Suhana ta ɗauko wayarta tana waya da Jamal ya dawo be sameta ba sai rigima sukeyi sai ta faɗa mai inda taje ya zo ya sameta, 


faɗa sukayi sosai ta kashe wayarta, Sultan kuwa zama ya yi kan kujera ya ɗora ƙafarsa kan teburin dake parlon, ya rufe idanunsa, yana jiran suyi magana Suhana kuwa sai lokacin ta kula da Sultan ne, wani dukan uku-uku ƙirjinta ya yi, amma ta basar kamar bata san shi ba , saboda ta kula ɗan jan aji ne,


Kamal ne ya ga shirun ya yi yawa kana yace "Sultan ga Suhana munyi magana da ita nayi mata bayanin komai , yanzu sai ku tattauna akan yadda za'a yi auren." Shiru Sultan ya yi na lokaci kafin ya buɗe baki da kyar kamar wanda akayiwa dole ya fara magana cikin muryarsa mai daɗin sauraro, 


yace "kamar yadda Kamal ya miki bayani inason yin aure na wani lokaci maybe na shekara ɗaya ko wata uku zuwa 7 mouth, ki faɗi ko nawa kike so zan biyaki duk abinda kike so zan yi miki, amma fa dole kiyi min biyayya, duk abinda nikeso shi zakiyi, cikin gidanmu zan ajeki, nan kowa da kowa yake, 

banaso ki ragawa duk wanda ke cikin gidan kiyi duk abinda kikeso duk wanda ya taka ki kema ki taka shi ko wanene ban ɗauke miki kowa ba, karki yarda da kowa duk yadda akayi karki aminta da ko ɗaya,  abinda na saka ki shi zakiyi, idan lokacin da na ɗiba ya cika zan sakeki.!" 

shiru Suhana tayi saida Kamal yace "Hana kiyi magana." Kana tace "Ni yanzu matsalata shine bansan inda iyayenka zasuje neman aurena ba saboda banda kowa!."  Sultan yace "Okey Kamal ka kaita gidanku, wurin Umma, saina zo anjima zamu yi magana yanzu ku tafi ta tattara kayanta gaba ɗaya, 


ku wuce bana son a samu matsala, gobe da safe zan turo ILiya ya zo ya kwashe kayanku zaku koma cikin gidana guda dake Unguwar, baifas." Cikin jindaɗi Kamal yace "Badamuwa yadda kace haka za'ayi." Sultan be koma magana ba, sai ma tashi da ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya riga su fita, 


Suhana kuwa tace "Kamal yanzu ya zanyi da Jamal wallahi idan yaji wannan zance bazai taɓa bari ayi auren nan ba.!?" Kamal yace "Ai wannan mai sauƙi ne, yanzu idan muka tafi ki kwashe komai naki kosu Lili da Afiya karki gaya ma wannan zance sai bayan aure, ki sanar da su, anjima zan siyo miki sabon sim card,


ki cire wannan, kega babu yadda za'a yi Jamal ya gano inda kike." Suhana tace "Kamal baka san waye Jamal bane amma bazan ƙi shawarar ka, yanzu dai mu tafi, nasan yanzu haka ya fita zuwa GIDAN ƳAN BARIKI yana jiran dawowa ta." Kamal yace "mutafi." 


haka suka tafi ta kwashe kayanta gaba ɗaya, suka wuce gidansu Kamal zaune suka tarar da Umma tana jan chalbi, saida ta kammala kana Suhana ta gaida ta cikin girmamawa, Umma ta amsa cikin sakin fuska, gyara zama Kamal ya yi kana yace "Umma Sultan ne yace na kawo miki ita ki kula mai da ita, 


matar da zai aure ce bata da Iyaye gidan marayu ya ɗauko ta kesan na gaya miki matslar gidansu da halin da yake ciki, shine ya ce don Allah ki riƙe mai ita a matsayin ƴar ki, gobe Yaronsa zai zo ya kaimu gidansa dake baifas, nan zamu ci-gaba da zama har lokacin da za'a yi auren." 


Umma tace "Ai ko kare Sultan ya kawo a gidan nan dole na kula da shi bale yarinyar da zai aure, gaskiya naji daɗin wannan labari ashe ina da rabon ganin auren Sultan, Allah ya kaimu lokaci lafiya, ya sa iyakar wahalar da yashi kenan!." Kamal yace "Amin Umma." 

sunjima suna hira kafin Kamal ya fita, Umma kuwa sai Jan Suhana takeyi ajiki har sun saba da juna, Umma najin Suhana kamar ƴar da ta haifa, Kamal ne kawai ɗan da Allah ya bata, shine kuma yanzu Allah ya saka mata ƙaunar Suhana,  


Jamal kuwa ya yi ta kiran wayar Suhana a kashe haka ya gaji da zama gidan ƴan barki ya koma gidansa da tunanin ta dawo amma shiru, ko da ya duba babu kayanta da ke gidan ko tsinke bata bari ba, hankalinsa ne ya yi masifar tashi to ina Suhana ta tafi kar dai gudawa tayi ta bi wani, 


fita ya koma yi wurinsa Afiya idan sun san inda Suhana take amma shiru sosai suka shiga ruɗani ina taje gashi wayarta a kashe ba'a samu, haka ya yi ta yawo a gari duk inda yasan tana zuwa sai da yaje amma babu labarinta, washegari, da safe 



Writer ✍️ *Bey PINKY DARLING MRS JAY*