Chapter thirty seven: Sabuwar soyayya
by @autum17
𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17
𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡ℎ𝑖𝑟𝑡𝑦 𝑠𝑒𝑣𝑒𝑛: 𝑆𝑎𝑏𝑢𝑤𝑎𝑟 𝑠𝑜𝑦𝑎𝑦𝑦𝑎....
Lokacin da Salamatu taji abinda xue yao ta faɗa hankalin ta ya tashi,amma sai ta danne ta kalli xue yao ido cikin ido tace '' Give it your best '' tayi maganar tare da juyawa ta fara tafiya taku biyu ta ƙara juyowa tana kallon xue yao that looked like she was about to explode tace '' har gaba da Abada, Aliyu bazai taɓa son ki ba so chill.'' tana kaiwa nan ta fita daga kitchen ɗin, xue yao fuskar ta tayi ja kamar tumatur jikin ta sai rawa yake ranta yayi mugun ɓaci. Furzar da iska mai zafi tayi tana faɗin '' zakiyi nadama'' kafin ta ɗauki coffee ɗin data haɗa ta fito daga kitchen ɗin,yau ma tazo gidan su game da project ɗin da aka basu ita da Aliyu, kamar ko yaushe wata shegiyar riga body hug ce ajikin ta da ya bayyana shape ɗin ta mai ɗaukar hankali amma banda Aliyu da ya rigada ya mace akan matar sa,he sees no one else. Duk yanda zata bi don ta ja hankalin sa abin yaci tura she felt so frustrated.
Dawo wa parlorn tayi ta iske salamatu zaune kusa da Aliyu tana hawaye,Aliyu duk ya bi ya birkice sai tambayar ta yake mai ya faru,xue yao gritted her teeth tana isowa inda suke tana bin Salamatu da wani shegen kallo ido suka haɗa Salamatu ta sakar mata wani arnen murmushi wanda Aliyu bai gani ba.
Sai ta kalli Aliyu tana kuka shaɓe shaɓe tace '' ciki na ciwo yake, ka kaini ɗaki pls'' tayi maganar tana ƙara riƙe cikin ta tare da shigewa jikin Aliyu, ɗaukar ta Aliyu yayi ya wuce da ita ɗakin su duk yabi ya daburce.
Xue yao da zuciyar ta ta kawo ƙirji,ji tayi kamar ta haɗiye zuciya tsabar baƙin ciki. Now she was more than sure dole tayi aiki da plan ɗin Irene
Jakar ta ta fisga ta fita daga gidan gaba ɗaya.
'' Are You sure kada a kira likita?" Aliyu ya tambayi Salamatu with so much care. Jinjina kanta tayi sai kuma ta jawo shi ya kwanta gefen ta,ta aza kanta a ƙirjin sa,he could hear her heart beat,ɗago ta yayi yana kallon fuskar ta yace '' faɗa min '' itama tana kallon shi tace '' me?" Yace ''what happened tsakanin ki da ita a kitchen?" Murmushi salamatu tayi tace '' it's between us kada ka damu, let's sleep '' tayi maganar with a final tone bata so su cigaba da wannan zancen, ciwon cikin ma ƙaryar sa tayi she was fine,kawai so take ta kori xue yao.
Aliyu bai sake magana ba ya kwanta kamar yanda ta buƙata.
NEW YEAR EVE.....
Ranar gabaki ɗaya ma'aikatan chan group kowa zaka gani,on their faces it's written they were extremely happy, kowa ya ƙule adaka,masu mata sun zo da matan su masu maza sun zo da mazan su. Hall ɗin ya cika da mutane, sannan mutane were still coming,Hall ɗin ƙato ne da kayi decorating ɗin sa da wasu Crystal like ice, ƙasan kuma wasu a marvel floor, Hasken wurin bai da haske can can amma kuma ba duhu bane can can shima, infact wurin yayi kamar wani kogon ƙanƙara hasken wurin yayi kamar light blue irin na ƙanƙara dai haka.
Sai kuma kujeru da aka lulluɓe da farin yadi sai table daga tsakiya. Ga counter idan mutum na buƙatar drink kowane iri,akwai alcoholic wine and non alcoholic,sai kuma soft drinks. Waiters at your service
Wurin kowa sai murna ake, they were standing in groups suna chatting,
Bayan ma'aikatan har da elites ɗin China aka gayyato dan chan group of company's is a big company, mutane sai zuwa suke suna gaisawa da ELITEs ɗin ƙasar China idan anyi recognizing ɗin ka,toh kakar ka ta yanke saƙa.
Ga yan ƙalilan daga cikin yan jarida da aka bari suka shigo,sai ɗaukar hotuna suke . Can na hango Park ɗin su Aliyu,Shang min yasa wata Black tuxedo days bala'in yi masa kyau ya sa ma gashin sa felt, daga gefen sa wata mata sanye da flared up gown she looked so beautiful,matar sa ce,sai wata mai suna Anna Lee ,da sauran yan group ɗin nasu,duka sunyi kyau sai hira suke.
Wata roles Royce Ce ta tsaya at the entrance and all eyes turned, driver ne yazo da saurin shi ya buɗe ƙofar dake hannun dama, Zuro doguwar farar ƙafar ta dake sanye cikin wasu tsinannun high heels sky blue color anyi adorning ɗin saman su da Crystal kamar ice, sai kuma ta zuro ɗayar kafin ta fito completely,It was Irene she looked beautiful.
Saye take da wata arniyar riga body hug itama sky blue da ko rabin cinyar ta bata kai ba,rigar ta mugun mugun matse ta, especially daga ƙirji da hips accentuating her curves,daga waist ɗinta na gefen dama kuma buɗe yake, hakan yasa farar fatar ta ke nunawa. Baƙin gashin ta anyi sa in a wavy style sai aka sa pearls from each side. Fuskar ta tasha kwalliya irin tasu ta yan China kamar ba irene ba.
Hannun ta riƙe da purse itama sky blue da take daddaɓe da stones suma sky blue sai ƙyalli suke. Ga wani irin ƙamshi da take zuba, tafiya ta fara yi ɗaya ɗaya duk inda ta wulga sai kawuna sun juyo ataƙaice dai ta sace sport light and dama da gangan tayi wannan shigar,tasan dama mutane zasuyi ta kallon ta dama akwai ta da iya shigar ɗaukar hankali, most importantly tayi don ta ja hankalin Aliyu she was sure kamar yanda kowa yakasa cire idon sa, shima Aliyu won't be able to.
Mutane suka fara zuwa especially maza suna mata magana ita ko tana wani basar wa,ƙawayen ta ne suka zo suka fara koɗa ta akan Aliyu dai yau dolen sa ya rusuna cuz Babu wanda zai ganta a haka bai ji ya ƙyasa ba. And dagaske mazan dake wurin mafiyawancin su sai haɗiyar yawu suke lustfully, her fair soft skin, dogayen ƙafafunta,her small waist,her flat stomach ba kowa zai iya kalla yace bai ji komai ba.
Almost immediately wata mota ya ƙara tsayawa and it was xue yao, fitowa tayi daga motar da aka buɗe mata cikin wata yar iskar riga irin ta Irene,Amma ta xue yao baƙa ce, wasu baƙaƙen stones ne masu shegen kyau akayi adorning ɗin ta dasu, ƙafafunta sanye cikin high heels jajaye, hannun ta riƙe da purse irinta Irene itama black color,gashin ta anyi styling ɗinsa in soft curls, ornaments ɗin dake jikin ta baƙaƙe and expensive, itama tayi wani smoky make up she looked stunning.
Sai ƙamshi take, baƙaƙen kayan sun hau da fatar ta sosai kasancewar she has pale skin, da sauri yan jarida suka yo kanta dan yar babban mutum ce, securities dake wurin daƙyar suka iya hana yan jaridar isa inda take.
Tun da ta shigo kowa ya manta da Irene all eyes turned to xue yao dake tafiya ɗaya ɗaya kamar she is on the red carpet
Mutane sai magana ake
• Is she a model?
•Isnt she the young mistress of the xue family?
•She looks expensive!
•Zan so in ɗaga dogayen ƙafafun Nan sama
•Isnt she prettier than Irene?
• Irene tafi ta kyau
• ji kayan da suka sa kamar karuwai
Haka maganganun suka ci-gaba da shiga kunnen xue yao but she didn't care, haushi ma take ji idan ana comparing ɗinta da Irene seriously, rolling ɗin idanun ta tayi.
wani gungun tsofaffin mutane ne zaune suna kallon yan matan suna analysing wacce tafi kyau,dukan su tsofaffin banza ne,wani daga cikin su da tunda Irene ta shigo yake bin ƙafafunta da kallo ne yace '' I will definitely have her tonight '' dariya sukayi su duka wani yace '' kai dai kama gaban ka,wannan tafi ƙarfin ka'' suna tsaka da magana sai ga xue yao tazo,
Almost immediately dukan su suka koma kallon ta, wani daga cikin su dake kallon xue yao cike da sha'awa, wani irin mummuna da shi,ga ƙaton cikin sa kamar mai cikin wata tara ya miƙe yana kiran '' yao yao '' Xue yao dake kalle kallen inda zata ga Aliyu taji ankira ta,juyowa tayi suka haɗa ido ,she really hates this pot bellied old man Xue sheng, style fuska tayi batare da tayi ƙoƙarin isa inda yake ba.
Kurɓar wine ɗin dake hannun sa yayi kafin ya fara takowa inda take,the other men suka bisa da kallo, mutanen wurin kuma suka bisu da ido bayan ya ƙara so yayi mata wani arnen kallo kafin yace '' You look so dashing ''
'' I know '' ta faɗa smugly, Murmushi tsohon ya sake yi yace '' Are You free tonight?" Tafiya zuwa yao ta fara swaying her hips shiko sai kallo yake lustfully tana faɗin '' i Don't ''
Komawa tsohon yayi ya zauna,he really has to have her.
Daga nan xue yao ta isa wurin Irene suka fara magana game da plan ɗin su akan Aliyu.
Har mutane sun cire ran Aliyu zai zo when out of the blue Aliyu ya fito daga wata Lexus,saye yake cikin baƙin yadi da aka yiwa aikin embroidery irin na maza,kansa da hula baƙa itama, ƙafafun sa cikin Black cover shoe sai shining suke, hannun sa saye da wani tsadadden agogo ,fuskar sa tayi wani haske duk da ba wani abu yayi ba out of the usual, ga wani azababben ƙamshi da yake zubawa he looked irresistibly handsome, the people staring lost their breathes,zagayawa yayi to the other end ya buɗe ma Salamatu ƙofa, ya miƙa mata hannun sa,amsa tayi ta fito daga motar, Itama ba baya ba,baƙar abaya tasa wadda bata da design ko ɗaya( to avoid tabarruj)tayi rolling ɗin veil ɗin, duk da bata yi kwalliya ba she looked breath takingly hot. 🥵
Ƙamshin turaren ta mai sanyi ba mai tashi ba, her eyes as bright as the moon, sai lip gloss da ta shafa, hannun ta riƙe da purse fara mai dogon igiya itama. Ƙafafun ta sanye da shoes flat farare. Murmushi ta sakar ma Aliyu as she rose to her feet daya sa numfashin sa tsayawa ya kafe ta da ido kawai,jan kumatun sa Salamatu tayi playfully tana faɗin '' ɗan samari ya dai?" Ba kunya Aliyu yace '' ji nake kamar in ɗauke ki mu koma ɗakin mu'' ƙasa Salamatu tayi da kanta jin abinda yake faɗa,kai! Could he not say such? Ganin tayi ƙasa da kanta yace '' Nifa ba wani abu nake nufi ba, kada Mrs Lee ta fassara magana ta'' Rufe fuskar ta tayi da hannun ta yayi dariya.
'' Shall we.'' ya faɗa yana miƙa mata hannun sa, saƙala hannunta tayi cikin nasa holding his arm suka fara tafiya,mutane aka saki baki da hanci da ido ana binsu da kallo,they together looked Ethereal
Ganin yanda ake kalle masa mata,Aliyu yaji wani abu ya tsaya masa a maƙoshi,but still he managed a fake smile.
Itako Salamatu Abinda yasa ta yarda ta biyo Aliyu was solely because bata yarda da su xue yao ba,tunda Aliyu yace xue yao zata zo itama tace sai taje.
Yao da Irene kuwa sumar wucin gaɗi sukayi ganin irin Kyan da Aliyu yayi,sun ɗauka his usual look was all but today he looks extra, zuciyoyin su sukayi baƙi Lokacin da suka ga Salamatu by his side *damnnn* *the* witch !!!
Dole koda yaushe sai ta kasance tare da shi?
Zuciyoyin su sun kusa bugawa lokacin da wurin ya kaure da claps,ppl were clapping for them shit!
Aliyu sai murmushi yake ita ko salamatu tayi ƙasa da kanta, the light blue lights making them appear more ethereal Aliyu na ƙarasowa suka fara zolayar sa, ita dai Salamatu ta kasa ko ɗagowa kanta ƙasa, Itama har da ita suke zolayar.
Mutanen dake wurin mafiyawancin aka juyo ana kallon couples ɗin like what's so special about them?
Baƙin ciki kamar ya kashe su Irene, after a while groups ɗin manyan mutane ne suka shigo ciki harda Mr ma, sai ƙusƙus ake ganin elites ɗin ƙasar China. Mutane were going over to Introduce them selves harda group ɗin wa'yannan tsofaffin banzan. Mr ma yai scanning ɗin wurin kafin idon sa landed on Aliyu murmushi yayi kafin yayi ma wani waiter dake wucewa ta wurin alamun ya kira masa Aliyu.
'' excuse me,sir's calling '' yayi maganar yana nuna Mr ma,
Shang min yace '' wato lambar ka ta fito ko?"
Wata tace '' mu dai kada a manta damu incase ''
Shidai Aliyu murmushi kawai yake as they went on, Salamatu ko sai raba ido take bata so ya barta.
Riƙe da hannun ta yabar wurin zuwa wurin su mr ma, tsofaffin nan sai kallon Salamatu suke duk da bata wani sa abinda zai nuna jikin ta ba,her simple dressing made her stand out cikin su dayawa and you know natural looks is a big turn on for men, Sai kallon ta suke lustfully her beauty effortlessly stood out.
Ganin kallon da suke yi ma matar sa ba ƙaramin ɓaci ran Aliyu yayi ba, tuni ya tsuke fuska kamar bai san yanda ake dariya ba,ita kuma Salamatu she was nervous like hell.
Mr Ma da murmushi ya tarbe su yana faɗin '' meet my boy,Aleeyeyouahh, and his wife'' yayi maganar yana tapping shoulder ɗin Aliyu da bai yi ƙoƙarin canja yanayin sa ba, especially daya ga mr ma na musu magana yet They weren't paying attention ELITEs ɗin da mr ma ya shigo tare dasu kaɗai ne sukayi ƙoƙarin yima Aliyu magana after hearing what mr ma said
Shima mr ma yaga abinda ke faruwa girgiɗa kansa kawai yayi this people will never change
Hannu ELITEs suke ba Aliyu Dan suyi shaking bayan sunyi masa yan tambayoyi ya basu amsa, ita Salamatu sai kalle kalle take her eyes jammed Xue yao's and Irene's. Sukayi mata wani murmushin makirci but she didn't falter.
Kowa na bama Aliyu hannu suyi shaking banda tsofaffin nan da directly suka miƙa ma Salamatu hannu wai suyi shaking, Aliyu ya kusa fashewa saboda kishi,he had never felt as jealous kamar yau. Slowly Salamatu ta juyo da foxy eyes ɗinta ta kalle su biyar ɗin duka ta kalli Aliyu da shima ita yake kallo,kafin slowly ta kalli mr ma da sauran elites ɗin da yazo da su, su biyar ɗin sai wani murmushi suke suna lasar baki
Batare da ta kalle su ba tace '' Shake my husband not me, addini na ya hana'' slowly suka ajiye hannun su by their sides feeling embarrassed,Mr ma yace '' ina ba Mrs Lee haƙuri a maimakon su'' Jinjina kanta Salamatu tayi tana matse hannun Aliyu dake cikin nata,
Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke sannan yayi ma su mr ma sallama suka bar wurin, Zuciyar Aliyu cike da baƙin ciki.
Bayan wani lokaci CEO Chan ya iso, wani Middle aged man,saye cikin suits baƙaƙe. Mutanen dake zaune tuni suka miƙe paying him respect
Mutane kuma suna zuwa suna gaida shi paying him respect.
Hawa stage yayi hakan yasa mutane suka taru aka fara sauraron jawabin shi, ya rufe jawabinsa da faɗin '' Happy new year to All,and enjoy your selves to the fullest'' wurin aka fara clapping anayi masa happy new year shima.
Kafin mutane suka fara dissipating, dozens of chefs suka shigo wurin with intercontinental foods duk abinda mutum ke so yaci kawai. Harda abincin Hausawa, Salamatu tayi mamaki sosai Aliyu yace'' ki dena mamaki,ai Hausa yanzu kuma ta zama one of the recognized languages in the world '' Abincin suka nufa duk da basu ci ba, rather sun tabbatar mutanen dake wurin kusan kowa sai da yaci sai praising ɗin Abincin ake su Aliyu sun yi farin ciki sosai (nima I'm proud) Su Aliyu suna tsaka da magana,Xue yao da Irene suka iso, wurin yayi shiru cuz daga gani ba alkhair ya kawo su ba, aiko Xue yao didn't fail to disappoint lokacin da tafara kunshe kayan Salamatu mutane sai defending suke, Aliyu ya riƙe hannun Salamatu gam anasa, '' wayan nan kayan ko yan aikin gidan mu sun fi ƙarfinsu amma ke baki koji Kunyar fita dasu ba'' Xue yao tayi maganar tana girgiza kanta in disdain,
Irene dai batace komai ba,ta shagala da kallon Aliyu ji take kamar taje ta yakice Salamatu daga jikin sa ta maye gurbin ta, kwantar da kanta Salamatu tayi a shoulders ɗin Aliyu ta wani juya idon ta tana faɗin '' mai zai sa inji kunya? Na yi sata ne? Na roƙi wani akan ya bani?" Shiru Xue yao tayi tana bin Salamatu da shegen kallo, smirk Salamatu tayi tace '' kaya na sunfi naki sau dubu, atleast sun rufe Ni banyi kama da karuwa ba'' wani irin yunƙorowa Xue yao tayi Aliyu yace '' touch her and you will see my bad side '' dunƙule hannunta Xue yao tayi tana barin wurin Irene na take mata baya duk da taso ta tsaya,amma idan ta tsaya what about their plan?
Abokan aikin Aliyu suka ba Aliyu da Salamatu haƙuri kafin su ci-gaba da sha'anin su
Other ppl around kowa sai sha'anin sa yake,ga waiters dake zagaye wurin da juice a plates ɗin su incase if you need
Gefe Irene taja Xue yao kusa da counter tana faɗin '' lokacin plan ɗin mu yayi '' tayi maganar tare da ciro wani magani kamar capsules guda biyu farare daga purse ɗin ta, ta miƙa ma Xue yao, kallon maganin xue yao tayi ta tace '' wannan fa?" Tayi maganar batareda ta karɓa ba, rolling ɗin idanun ta Irene tayi ta jawo hannun ta ta sakamata aciki tana faɗin '' Aphrodisiac '' waro ido Xue yao tayi tace '' biyu yayi yawa mana" tsuke fuska Irene tayi tace "idan yayi yawa wa zai ji daɗi? Idan baki so bani abu na!!" Tayi maganar cike da jin haushi. Kanta ta sauke kasa Xue yao kafin tace '' ya za'ayi ya sha maganin?" Irene tace ''wait and see''
Wani waiter da yazo wuce wa ta wurin su Irene ta tsayaar, ɗaukar wani red wine tayi ta miƙa ma yao karɓa yao tayi itakuma Irene stylishly ta juya ma yao baya incase in kamata zata ce ba tare suke ba. Maganin Xue yao tasa cikin juice ɗin ta ɗauko kuɗi ta miƙa ma waiter ɗin tana nuna Aliyu tace '' kai masa '' jin jina kansa waiter ɗin yayi bayan ya ɗauke kuɗin, ɗaukar cups biyu na juice yao tayi sannan waiter ɗin ya bar wurin. Kofi ɗaya ta ba irene ta ɗauki ɗaya.
Gaban su waiter ɗin yaba Aliyu wine ɗin ya karɓa. Murmushi suka sakarwa juna '' mission successful '' inji Xue yao