TAZARA

Chapter 9

by @reza12

TAZARA!

©By S-reza✍️

FCWA

Whasop Chanal

Chapter 9️⃣

Ya na ɗaga wa aka ce masa yanzu-yanzu yazo ana nemansa a jam'iyyar su. Haka kuwa bai tsaya sanarwa Zinaru ba ya fita da sauri. Sai da yaje zai shiga mota ya tuna babu hula a kansa, hakan yasa ya dawo gidan da sauri yana jin yadda Zinaru take amsa waya tana kuka da ƙarfi kaman wanda aka yi mutuwa. Sosai wannan videon ya tada ƙura a cikin garin na Yalwa mutane ke ta yin sharhi akan maganar da yayi. Ɓangaren Saif kuwa hankalinsa kwance sai dai ya na ta samun suka daga abokansa da kuma ƴan uwa, hakan yasa ya ƙulle layinsa gaba, sai lokacin ne ya ke jin ya ɗan samu sauƙi daga abun da akai masa, suma su ɗanɗani irin abun da yaji idan a kwai dad'i, babban burinsa ma sai anyi zaɓe sun faɗi zai haɗa ƙwarya-ƙwaryan biki tare da abokansa kuma ya gayyaci ƴan jaridu a chashe ayi shagali. Sannan ranar zaɓe zai tabbatar musu da abun da ya faɗa ta hanyar yin video a lokacin da yaje zai dangwala wa Alh Madu. Sai dai Saif bai san cewa wannan abun da yayi kuskure ne mai girman gaske ba, wanda har shi sai ya shafa ba zuwa gaba ba. Lokacin da Alh Madu yaga wannan labarin kuwa farinciki kamar yayi hauka, hakan yasa a nemo masa duk inda Saif yake tabbas za'ayi wannan tafiyar da shi, kuma duk abun da yake so ya faɗa zai masa.

*****

ANTY HINDE

Haka ta dinga sawa ana kira mata wanda taga ya dace ta bawa jari a cikin ƴan gidan. Kowacce idan ta zo ta bata sai tayi kuka da murna da godiya, sannan ta mata fatan sauƙa lafiya domin kusan kowa yasan tana da ciki. Sai da ta tabbatar da ta gama da kowa kuma sannan ta fara tunanin yadda zata yi da su abbati, domin dai su take son ta bawa atm ɗin nan kar taje tsutsayi yasa Gali ya gani tasan ta shiga goma ba tara ba. Kasancewar tun a gurin da ta sayi wayar an saita mata komai domin sai da ya buɗe mata YouTube a gurin ta tabbatar sannan tasa aka saka mata kati. Jikinta har rawa yake ta ƙulle gidan yadda duk wanda zai shigo sai ta sani. Ta shiga kitchen ta buɗe YouTube. Sunan gidan talabijin din da ta gama haddacewa ta rubuta haɗi da sunan Saif. Da mamaki sai taga wani sabon video ɗin nasa ba wanda take nema ba. Da sauri ta latsa kan sa, sannan ta kafe shi da ido. Ta na kallon videon gabanta na faɗuwa da sauri da sauri, kusan minti goma amma sai da ta sake maimaita shi. Babu abun da take yi sai salati domin ta fahimci komai. Kenan Saif ɗan gidan Sadau ne abokin takarar Madu? Ita bata taɓa sani ba, eh tabbas a kwai tazara a tsakanin su kaman yadda mahaifiyar sa ta faɗa mata. To kenan tun wannan lokacin baya shiri da su kenan ko yaya? To saboda me? Nan zuciyarta ta bata amsa da cewar saboda ke!. Ai take ta tsayar da kallon tana girgiza kai kuma tana cewa a'a ba haka bane. Sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin "Please Saif iyaye ba abun wasa bane, Saif kazo na faɗa maka illar rashin iyaye a rayuwar mutum, kar kai min haka, dan Allah ka dakata daga abun da kake yi. Sosai take kuka har cikin zuciyarta take tausayin sa, to ita da tasan ma shi ɗan masu kuɗi ne haka mai ma zai sa ta fara soyayya da shi, ita dai ba a matsayin mai kuɗi yazo mata ba, haka kuma ba gidan masu kuɗi ya Kaita ba lokacin da zasu je gidan su, to wai me ke faruwa, ƙarya kenan yayi mata ko kuma dai yaya, amma tasan Saif ba zai mata ƙarya ba domin baya son ƙarya. Babu abun da take ganin zai kawo masalaha kaman ta haɗu da shi kafin wannan zaɓen, to amma ta yaya, bata ma san ta ina zata fara ba. Anan wani tunani yazo mata ta karanta sunan sa da aka rubuta a jikin videon. Saif Sadau Inuwa. Hakan yasa taje ta sauƙe fecbok app domin dama tafi ƙwarewa a shi. Ta mayar da tsohon account ɗin ta, ta fara binciken sunan. Sai dai ta samu account da yawa masu irin wannan sunan, kuma kowanne hotunsa ne akai, da alamu dai irin mutanen da suke ƙirƙirar account da sunan wani sanannene. Haka dai duk mai irin wannan sunan sai tayi adding ɗin sa.  Sai kuma wata dabara ta sake zuwar mata. Ta rubuta sunan wannan gidan talabijin ɗin, aikuwa sai ga shi, ta shiga tayi following ɗin su. Sai kuwa ga video ɗin nan a sama. Comments section ɗin kawai ta shiga anan ne taga asalin account ɗin na domin mutane nata taging ɗin sa, wasu su zage shi wasu kuma suyi ta saka masa albarka akan yadda ya fito ya fad'i gaskiya. Irin maganun da mutane kiye yasa ita da kanta ma take ganin ai koda Saif bai fito yayi wannan abun ba to fa al'umma sun fi son Alh Madu, kasancewar yana da kirki kaman yadda ake faɗa a ƙasan a wannan video ɗin. Shi kuwa mahaifin Saif bata ma taɓa ganinsa ba sai a hoto, amma haka kawai taji shi take so kawai saboda shi ɗin mahaifin Saif ne. Kai tsaye account ɗin nasa ta shiga, sai taga rabon sa da hawa online ma yau kwana biyu. Sai kawai tai masa sallama sannan ta fita. Ta shiga cikin profayal ɗin sa tana duba posting ɗin sa da kuma hotunan sa. Ta na cikin kallo taji ana buga gidan nata da ƙarfi. Hakan yasa ta fita da sauri ta kashe wayar ta je ta ɓoye ta. Sai lokacin ma ta kula da yadda lokaci yaja gashi ko gidan bata gyra ba bare ayi maganar abinci. Addu'a take Ubangiji yasa ba shi bane ya dawo a irin Wannan lokacin ba. Ta na buɗewa ta same shi tsaye ya jingina da bangon gidan yana jiranta. Kafin ma tayi magana ya ce "Wai me yasa yanzu kika tsri rufe gida ne kullum sai na zo nai ta bugawa har sai lokacin da kika ga dama zaki buɗe? Ko gidan na ubanki ne? Ko mun haɗa kuɗi mun saya dake ne?" Tayi shiru tana Addu'ar kar ya shiga gidan. Ya ce "Dalla gafara min a hanya wawiya kawai mara hankali, Allah yasa na sake dawowa gidan nan da rana irin haka naga gidan a rufe wallahi sai na tattaka ki ƴar ƙauye kawai, ko uwar me ma zai sa ki rufe gida da ranar Allah oho". Ya bangaje ta ya wuce. Ta juyo ta biyo bayan sa kamar mara gaskiya. Dakinsa ya wuce itakuma ta fara sauri tana ɗan kawar da wasu abubuwan domin ta kula Kamar dai sauri yake hankalinsa bai ga gidan ba, domin ba laifi Gali a kwai tsafta ko yaya yaga abu na dadti to fa sai yasa ta kawar, kuma ko a jikinsa ta tabbatar yana da tsafta. Ya ɗan dade a ɗakin lokacin har ta gama gyara palon sannan ya fito. Har zai fita sai kuma ya dawo da baya ya kalleta tsaye ta taƙura guri guda hannayenta a baya kamar wata baiwa. Duk da dama yawanci idan yana gidan haka take yi, amma sai na yau ɗin ya ɗan sha banban. Hakan yasa ya ce "Hinde baki da gaskiya, mai keke ɓoye min?" Ya faɗa da tsawa ya na dosar ta. Sai ta fara girgiza kai kawai ta kasa magana. Ya je har gabanta ya zagaye ta yana duba jikinta ko zai ga ta ɓoye wani abun, ya finciko hannunta yaga ba komai ya ɗage rigar ta har sama, nan ma bai ga komai ba. Ita dai tana tsaye kamar an dasa ta. Sai kuma ya juya zai fita ya sake juyowa ya ce "Kin gama abinci?" Take hantar cikinta ta juya daga sama zuwa ƙasa. Ta girgiza masa kai a hankali. Yaja tsaki kawai ya bar gidan ya na banko mata ƙofa. Yana fita ta sauke ajiyar zuciyar da ta tsaya mata tun ɗazu. Ai kuwa tayi sauri ta shiga kitchen ta ɗora ruwan zafi. Idan ta bangaren abinci ne to alhamdu lillaha basu da matsala domin komai suna da shi, kasancewar Gali yana tare da ƴan siyasa, sannan kuma yana da ɗan ƙaramin shago a kasuwa ba sayar da su zanin gado da labileye harda zannuwa, kuma shi ya bar mata ragamar dafa duk abun da take so, domin shi bai da zaɓin abinci komai yana ci, tun farkon sauransu da take tambayarsa abun da za'a dafa ya ce mata ta daina, amma ta kasa dainawa sai da ta sha mari kafin ta tabbatar, shi yasa yanzu ko da wasa bata taɓa tambayarsa komai, koda abu ne ya ƙare kamar wani maye sai dai taga ya sayo domin bata iya faɗa masa. haka itama tana yin kitso na kuɗi sosai, kuma mutane suna zuwar mata, dan ma bata samun lokaci sosai, kuma bai taɓa hana ta ba, sai dai fa idan sake yaga gashi a abinci, ko ya dawo gidan yaga gashi a ranar zata gane Allah da girma yake.

Tana cikin aikin yara kusan shida ƴan mata suka zo gidan dukkanin su zasu yi Sa'a da Abida, hakan yasa duk ta raba musu aikin gidan itama ta cigaba da yin wani. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka gama ta zuba musu a faranti, sannan ta basu wanda zasu tafiwa da su Abbati. Kafin ayi sallar magriba ya dawo gidan rike da manyan ledoji guda uku. Lokacin tayi wanka ta gyra ko ina tana zaune ta kunna tv tana sauraron azkar ɗin maraice ya turo ya shigo babu ko sallama kaman dai yadda ya saba. Ta miƙe da sauri tana masa maraba. Ya ajiye ledojin a tsakiyar falon ya zauna a kan kujera. Ita kuma tana tsaye ƙiƙam!. "Kawo min ruwa". Ya faɗa da wata murya ta da ban ba wacce ya saba magana da ita ba. Sai da ta kalleshe kafin ta ɗauko masa ruwa ta ba shi. Ya daga bai ajiye ba sai da ya gama da shi. Ta zuba masa ido ganin yana zufa. "Zo nan". Ya faɗa yana yakutota da hannu. Ai kuwa ta fara takowa a hankali har gabansa. Ya nuna mata kusa da shi ya ce "Zauna" ya sake faɗa yana buɗe ledojin da ya shigo da su. Hinde ta zauna tana jin ta a takure fiye da kullum, ita bata ma saba zama kusa da shi haka kaman jikinsu zai haɗu ba, shi yasa taji gaba ɗaya palon yayi musu kaɗan. Ya ciro wata farar leda ya jefa mata ya ce "Buɗe nan" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Sannan yaci gaba da buɗe sauran ledojin. Anty Hinde hannunta har rawa suke ta fito da abun dake cikin ledar tana ta mamaki, ganin kwali yasa ta shiga buɗe shi sai ga waya sabuwa android ƙarama. Tayi jim kaɗan kuma bata ce komai ba. Ya sake jofo mata wata ledar nan ma ta ɗauko ta ɗan saci kallonsa taga yana ta ƙoƙarin kwance wata leda mai ƴar girma. Jama'a wani ya tada Hinde daga barci, haka take ta faɗa a zuciyarta, domin dai bata yarda a zahiri bane wannan lamarin, har wani zufa ne na rashin dalili ke karyo mata. Sai da ta ɗan sauke ajiyar zuciya kafin ta fara buɗe ɗaya ledar. Wannan karan kam bata san lokacin da ta ɗago kai ta kalleshi ba ganin abun busar da kai da, wanda yau din nan take ta nazarin yadda za'ayi ta saya koda ya gani ba zai gane ita ce ta saya ba. Gaba ɗaya ta manta da wannan tsoron nasa kasancewar ya bata mamaki. Ɗagowa tayi suka haɗa ido, sai kuwa ta kawar da bata idon hawaye na zubo mata. A ranta tana mamakin dama Gali yana mata kallon mutum da har zai iya girmamawa har haka, dama yasan ita ma mutum ce kamar kowa. Ganin tana kuka ya ce "Ke wai wacce irin bagidajiya ne, yanzu ɗin ma wata uwar nai miki, ko dan kawai kin mai da kuka ba komai ba?" Sai kuwa ta fashe da kukan mai ƙarfi har tana kifa kanta. Tunda take a rayuwa ba'a taba mata kyauta ba idan ba Saif ba, sai kuma Alh Madu idan ya zo, kuma bata taɓa jin tana son mutum kamar ta mutu irin sai ba, tun lokacin da Gali ya aureta ta kuma yake yin irin wannan rayuwar da ita ta rashin ƴanci tayi sallama da wani abu mai suna jin dad'i ko farinciki. "Dawo min da kaya na dan uwarki tunda baki so, kuma idan baki daina wannan kukan ba zakiyi mai dalili yanzu" ya faɗa yana miƙewa ya shiga ɗaki. Lokacin da ya fito ta share hawaye domin kuwa tsaf za tayi mai dalili ɗin. Nan dai ya faɗa mata cewar ya saya mata waya ne ba dan komai ba dan ya sayar mata da tata, kuma kar yaji kar ya gani, sai abun busar da gashin da kuma kayan sha na gida. A hankali ta ce "Na gode Allah ya ƙara buɗi da wadata". Ya amsa da amin ya na barin gurin. Kafin ya fito ta kawo masa abinci da ruwa, ta koma ɗaki ta ajiye kayan, sannan ta fito lokacin baya nan. Wayar itama har chaja, hakan yasa ta saka ta a chaji tana ta murna.

*****

GIDAN YAKUBU

Ya na tafiya a hanya sai murmushi yake shi ɗaya har ya iso gidan nasa. Da sallama ya shiga palon Yusra ta amsa masa tana kallon yadda fuskarsa ta cika da annuri. Ya zauna a kusa da ita ya na murmushi. Ta ce "Lafiya kuwa irin wannan kallo kamar ka warke daga makanta?" Ya ce "Yusra ba warkewa nayi ba, na san gaskiyar da kuke ɓoye min ne, ina ita Saddiƙar to ta fito yau na gano gaskiyar. Yusra dai ta cika da mamaki duk da gabanta na ɗan faɗuwa amma dai tunda yaga murmushi a fuskarsa tasan dai ba abun da take tunani bane. Saddiƙa ce ta fito daga ɗaki ta na tambayar lafiya dai ake mata irin wannan kiran. Yusra ta nuna mata shi ta ce "Ga shi nan dai, yazo ban gane mai yake cewa ba. Yakubu ya ce "Gaskiya na gano wacce kuke ɓoye min, kuma daga yau komai yazo ƙarshe zan fara lissafi da kaina. Har yanzu dai basu fahimci ina ya dosa ba, sai kallon juna suke. Saddiƙa da tafi rashin hakuri ta ce "Wai wacce gaskiya ce duk ka ɗaya mamu hankali fisabilahi?" "Gaskiyar wannan jinin naku na priyord nan kuka ce min duk kwana biyu ko huɗu a keyi ashe ba haka ba ne karya ne ma gaba ɗaya kwana ɗaya zuwa biyu yake yi, kuma a shekara ma sau biyu yake zuwar ma mace". Ya faɗa yana yin fasali da hannu. Yusra ta kwashe da dariya, ita kuwa Saddiƙa bata ma ga abun dariya anan ba banda zarlar jahilci da wawanci. A fusace ta ce "Waye ya faɗa maka haka?" Ya miƙa tsaye shima ya ce "Haka ne mana, har sai wani ya faɗa min, to abun hauka ne da za'a ce duk bayan kwana biyu, kenan kullum a cikin ƙazanta kuke kuma kuke zuwa aiki?" Sai yanzu ta sake tabbatar da wa suke aure, shi yasa mana Yusra ta ce duk mazan gidan marayu shi kaɗai zasu iya aura su cigaba da yin rayuwarsu ba tare da wata matsala ba, domin ba shi da saiti, to tabbas ya ta tabbatar. Ta ce "Wai kai Yakubu menene matsalar ka ne?" Ta na rufe baki ya ce "Hakkina nake so ku dinga bani na aure, ba zai sabu ba, ace mata har biyu amma baka da maraba da muzuru, ai tuxuru". Yayi mistake kuma ya dawo ya gyara kayansa. Yusra dai sai dariya take abun ta. Saddiƙa tai masa wani kallo daga sama zuwa ƙasa, sai kuma ta koma kan Yusra ta ce "Wai ke wannan ma abun dariya kika mayar da shi ko?" Ya ce "Ki kyale ta, Saddiƙa, dama ta gama raina ni, kuma wallahi zan dawo kanta, amma yanzu ba ta ita nake ba, tunda dai yau kice da kwana, ina fatan dai lafiya?" Saddiƙa ta ce "Ina priyord" ta faɗa kuma da gaske ne shi din take yi. Yakubu ya wawaso wata rantsuwa ya dire akan sam bai yarda ba. Ita kuwa tayi hanyar ɗaki sai kuwa ya biyota. Tana shiga ya shigo ta juyo a ce "Wai me kuke nufi ne, to wallahi zan kai karar ku gidan Anty Hinde, wannan ai rainin hankali ne. Ya na rufe baki Yusra ta shigo ɗakin ta na faɗin "Malam Yakubu Namiji fa baya cika Namiji a gidan har sai ya sauke gaba ɗaya nauyin iyalansa a kansa, kaga na farko baka ciyar da mu, baka tufatar da mu, sannan shi kansa gidan mallakin mu ne, to a hakan kake so ka samu komai, to wallahi bari ma kaji daga yau muddin kana so a dinga cin abinci da kai sau uku a gidan to ka manta da wannan maganar har sai lokacin da muka so yin hakan". Saddiƙa ta kara da "Idan kuma so kake a janye maka tallafin kuma to?" Yayi shiru jikinsa ya mutu ya kasa magana. Sai cen ya ce "To Saddiƙa Yusra Meye amfanin auran idan babu wancen abun?" Saddiƙa ta ce "Ciyar da kai da kuma kwana a kan ƙatuwar katima, da kuma ganin ka da ƙima da mutunci da ake yi a unguwa da gari mana". Yusra ta ce "Ko kuwa so kake mu fito mu nuna duniya cewar gidan da muke ciki namu ne, sannan mune muke ciyar da kan mu, kuma ko lokacin aure kusan mune mu kaiwa kan mu komai?" Yakubu ya kasa magana, domin tabbas sai yanzu ya sake tabbatarwa wannan auran dama ba saboda da Allah a kayi shi ba, idan ba haka ba Meye na kawo duk wannan batutuwan. Sai cen ya ce "Yanzu haka zamu cigaba da zama a haka kullum mu kwana mu tashi a cikin gida ɗaya amma babu komai?" Ya faɗa kamar wani mara gata sai su ɗin. Saddiƙa ta ce "To dai zaka koma kwana a waje ko palo ne?" Da sauri ya girgiza kai ya juya ya bar ɗakin. Yazo Palo ya zauna yana tunani. Gashi kuma gidan marayu ba'a kaiwa ƙara to shi yanzu idan ma ya kai ai asirinsa ne zai tonu, to ko Anty Hinde ɗin ma ya fasa faɗa mata, kawai dai zai naimi abun yi, ya dage ya riƙe gidan nasa, ko kuma dai ya san abun da zaiyi. Shiru-shiru basu fito ba gashi yana jin yunwa, sai kawai ya fara kiran su. A tare suka fito, ya bisu da kallo ganin kamar wanka suka yi. Ya kasa haƙura ya ce "Wai ni tare kuke yin wanka ne dan Allah?" Ya tambaya yana jin wani takaici, abun da ya kamata ace shi suke yiwa. Yusra ta ce "Ko baka so ne?" Ya ce "Wanka tare da kishiya idan ba rashin wayo ba, a ina aka taɓa haka?" Ya faɗa kamar dai abun ya ƙona masa rai sosai, kuma da alamun yaji haushi. Yusra ta ce "Mai zai sa muyi wanka tare, kawai dai tayi ne ta bani guri nayi, amma mai ka gani?" Ya ce "Ai ni yadda na sani kishiya abokiyar faɗa ce, Bama a yarda a shiga dakin ta bare har ma a zauna ana shiri, ke nifa yadda na sani har dambe ana yi sai dai miji ya dinga yin rabiya wallahi, amma ku saboda baku san illar da ke a cikin kishiya ba kun haɗa kai". Yusra ta ce "Ai mu ba kishiyiyi muka ɗauki juna ba, domin babu ɗa namijin da zai iya saka mu faɗa a kan sa, dan haka ka kwantar da hankalin ka Yakubu". Yakubu ya girkiza kai kawai ya fara cin abinci domin har Saddiƙa ta zuba masa, kuma ta zuba nasu, suna ci suna hira shi kuma ya ta gyaɗa kai alamun dai maganar na masa yawo...📝