Kuncin zuci
by @bintuuu
Hankali suka maida sosai akan karatunsu, basa wani samun lokacin kansu kuma yawanci a gida suke yin researches din nasu kasancewar sunzo wannan gandun, gidan Anty Amnah ma saida sukayi wata guda tukunna suka je shima waya ta kira ta rinqa mita sannan suka je, zuwa yanzu Na'ima ta dan cire tunanin Ahmad daga ranta ganin babu inda tunanin zai kaita, tana jin time to time yana gaisawa da Nafisa tun tana expecting zai tambayi ya take har ta hakura ganin yayi keeping boundaries dinsan yasa itama ta dan ajiye batunsa a gefe dan harga Allah batason abunda zuciyanta keji a duk lokacin da idanunta sukayi tozali dashi, Nafisa ma bata sake zancen suje gidansa ba wanda daman Na'ima batada niyan zuwa koda Nafisa ta nemi hakan.
Watarana suna zaune a falo da daddare Na'ima na typing abu cikin laptop dinta, Nafisa dake kwance gefenta tace "Kin fara dissertation din ki kuwa?" sai Na'ima ta bar abunda takeyi ta juyo tace "Kin tuna course mate dita dinnan wanda nace miki sunanta Zara?" Nafisa ta gyada kai tace "Yar Lebanon dinnan, Na'ima ta cigaba "Ita..jiya ta tambayeni ko zan amince mu hada study group da ita akan dissertation din" sai Nafisa tace "Dama bakida writing buddy kedin?" Na'ima ta gyada kai tace "I thought zan iya ne, kuma naga yamin wahala sosai yanzu" Nafisa tadan jijjaga kai tace "Kinada matsala Na'ima, ai dole sai kin samu group mates daman a irin situation haka, yanzu me kika cewa zaran" Na'ima ta amsa da "Na amince ai tun jiyan tace zamu rinqa ware lokacin shiga school din" sai Nafisa tace "Hakan yafi ai, namu fa study group din munkai takwas" Na'ima ta juya ta cigaba da typing tace "Naku da maza ai naganku ranan" dariya Nafisa tayi tace "Ke kuma sune abun gudunki, sis many men don't bite" Na'ima batace komai ba ta cigaba da aikin gabanta..
Ranan wata talata bayan sun gama baccinsu da hidimominsu Nafisa ta jasu suka tafi shopping abubuwansu da sukayi qasa, sai da sukayi sallahn la'asar sannan suka shirya suka tafi, kaya suka siyo dayawa na abinci dana qananun buqatunsu, bayan sun gama jera kayayyakin a kitchen suka fito Na'ima ta zauna nan kan kujera a falon ta fara ware kayan toiletries din nasu da na skin cares din, Nafisa ma ta zauna ta ciro wayanta tafara dannawa, shiganta cikin IG taga saqo a DM dinta dauke da sunan da ko cikin magagin bacci zata gane waye, dan gyara zama tayi daga zaunen ta dan dago ta kalli Na'ima da hankalinta ke kan duba kayayyakin gabanta bata dago ba, miqewa Nafisa tayi asannu ta shige dakinta ta rufo qofan sannan ta sake kallon message din me dauke da rubutu kamar haka.
Bilal Dabo: Saqo na ke son ki isar wa kawarki, tunda alamu sun nuna batasan ma'anan space dinda na bata ba and she's taking it too far, Tell her "it is not Over until i said so" ta dawo da kafarta , karta bari inzo daukanta dan lamarin bazai mana dadi ba, AUREn mu kuma na maidashi....
Saboda wasu dalilai ne kawai yasa nafisa bata maida masa da amsan zagi ba, dan ko jahili yasan auren da ya mutu kusan wata goma baya, bazai maidu ba sama taka, sanin cewa ko weed dince ta motsa masa yasa Nafisa qin maida masa martani, atake kuma taji duk wani
kuzari na jikinta ya bace, bata san ma me zata fara tunani ba, a wannan lokacin kuma babu abunda take tunani irin kwanciyar hankalina Na'ima, she can't know about this and there's no way she's telling Mami saboda tsaf zata iya aiko Faruk yayi wasu cike cike a school ya koma mata da Na'ima saboda nutsuwan Na'ima yafi komai a wajenta, ji tayi jikinta yayi sanyi sai tafara safa da marwa a dakin abubuwa dayawa suna dawo mata, in ta tuna ranar da Na'ima tazo gurinta da dare zuciyanta qara karyewa yake, ji tayi hawaye na kawowa idonta takai hannu tana sharewa.
Tana nan tsaye a dakin ta kasa zama Naima ta shigo hannunta riqe da laundry basket zata debi kayan Nafisan dazata wanke mata, juyowa Nafisa tayi suka hada ido a take taji zuciyanta ya kuma karye wa, ta daure tace "Har kin gama ware kayan" Na'ima dake dan lura da yanayinta ta jijjaga kai tace "Eh ga naki ma" gyada kai Nafisa tayi ta juya a sanyaye ta zauna bakin gado tana dan kallon Na'iman, wuceta Na'ima tayi ta qarasa gurin madubi ta debo wasu mayuka daga cikin basket din tafara jerawa sannan ta wuce toilet takai sauran, dawowa tayi gaban wardrobe din Nafisan ta bude zata debi kaya ta ajiye basket din a qasa ta fara duba kayan, sai kuma ta juyo a nutse tace da Nafisan "Akwai wasu kaya dana ware anan Ina kika kaisu kuma"
Nafisa tace "Kamar yana qasa ai" duqawa tayi ta fara bincikawa nan qasan tana mita "Haba Nafee nafa waresu ne zan wanke kika hadesu guri daya da masu kyau" qunquni takeyi Nafisa na kallonta tana dan murmushi mai ciwo, aranta tana ayyana how kind and innocent Na'ima is, Allah kuma ya jarabceta da wasu irin mutane zagaye da ita sukayi amfani da shirunta da kuma haqurinta wajen cutar da ita.
Inaaa...ai bazata taba bari Bilal ya samu haduwa da Na'ima a qasar nan ba, dan guntun nutsuwan da suka samu Na'ima tadawo cikinsa duk zai wargaza komai, ya kuma hanata karatunta da yazama saura kadan ta gama,
Miqewa Na'ima tayi bayan ta gama zuba kayan a basket ta kalli Nafisa, sai ta samu kanta da tsayawa tana nazarinta tace "Nafee meya faru ne?" Saurin jijjaga kai Nafisa tayi tace "Babu komai, me kika gani?" sai Na'ima ta matso kusada ita ta ajiye basket din ta zauna tace "Naganki kinyi sanyi ne all of a sudden, Dan Allah me ya sameki?" dariyan qarfin hali Nafisan tayi tace "Gani uwar surutu kullum, kawai kaina ke ciwo" Na'ima tace "Ayya sannu" sai ta dauki basket din ta fice daga dakin Nafisa na kallonta, tashi tayi ta rufe kofan sannan ta qara daukan wayan tafara dialing numbern Anty Amnahn..
Bayan ta dauka suka gaisa Nafisa ta fara mata bayanin saqon da tagani a wayanta, dayake Anty Amnah tasan almost everything gameda Na'iman yasa ta fahimta, itama tace kada Nafisan ta kira Mamin dan sai hankalinta yafi na Na'ima tashi in ta sani.
Na'ima ce ta dawo dakin dauke da maganin ciwon kai da ruwa ta balla ta miqawa Nafisan, karba tayi amma bata sha ba sai tace "Sis tunda bama shiga school din yanzu, why not mu koma gidan Anty Amnah toh" dan hararanta Na'ima tayi tace "Keda kike mitan gajiyan zuwa shine kuma all of a sudden zakice muje" Nafisa tace "Ji nake kaman banida lafiya ne sis, kafin yayi nisa gwara muje ta dubani" sai Na'ima ta dan bata fuska tace "To ki bari mana kigani, may be ma stress din fitan nan da mukayi ne" ganin kamar ba yarda zatayi ba yasa Nafisan gyada kai tace "Toh shikenan" ta juya ta kwanta Na'ima ta miqe ta dauki qaramin blanket din gadon ta lullaba mata tace "Sannu" sannan ta fice daga dakin.
Ranan anan dakin kusada Nafisan ita Na'iman ta kwana, Nafee sai tunanin uzurin da zata bullo dashi take, wanda zai sa Na'ima ta yarda su koma gidan Anty Amnah in yaso sai su rinqa zuwa school din daga can din jefi jefi tunda ba wani activities suke gudanar wa a school din ba yanzu.
Washegari ma Nafisa qin fita tayi suyi breakfast sai Na'iman ce ta biyota dashi nan dakin tana mata sannu, kadan Nafisa taci abincin tayi wani laushin qarya duk acikin batada lafiyan, ita kuwa baiwar Allah Na'ima sai hankalinta yafara tashi kuma tace "Sis ko zamu je asibiti to" Nafisa tadan koma ta kwanta tace "A'a kam, ai nadan fara jin dama dama" shiru Na'ima tayi batace komai ba....
Yammacin ranan Na'ima na zaune anan falon aka danna musu door bell, dan tsayawa tayi da duba wani takarda dake hannunta tana son qara tabbatar da kofan su ne ake dannawan kuwa, qara ringing din akayi kafin ta miqe sai ga Nafisa ta fito daga dakinta cikin sauri ta nufi qofan kamar zata fadi, bin ta da kallon Na'ima tayi tana dan mamakin firgicin nata itama ta miqe, ganin Nafisan tayi nan bakin kofan bata bude ba tana leqa peephole din jikin kofan, sai tace "Nafisa waye ne?" Juyowa Nafisa tayi kamar mara gaskiya tace "Order nayi mana na pizza sai na zata mai delivery dinne ya qaraso" Na'ima na kallonta ta gyada kai tace "Toh bude mana muga waye" budewa Nafisan tayi su kaga ashe Lauren ce , hugging din juna sukayi itada Nafisa cikin fara'a suka wuce ciki Na'ima tabi bayansu, zama tayi nan gurinsu a falo bayan sun kawo mata abun sha..
Nan Lauren tafara zuba musu surutu, itadai Nafisa tanason ta zage suyi hiran dayake kawar surutun ta ce amma babu hali saboda tayi qaryan rashin lafiya, ga Na'ima kuma zaune gurinsu itama, sai kawai ta rinqa amsawa sama sama har se da Lauren din ta tambayeta ko lafiyan ta, Na'ima ce ta amsa da "She's sick"...
Sai dare lauren ta tafi, bayan tafiyanta Nafisa ta koma daki ta kwanta, abinci Na'ima ta dafa musu bayan ta gama ta debi na Nafisan ta bita dakinta dashi, duqe ta sameta ajikin gado, dasauri ta ajiye abincin ta qarasa gurinta ta dagota tana tambayanta "Meya faru" Nafisa ta amsa da "Amai nayi sis", sannu ta fara mata sai ta dagata ta zaunar da ita akan gadon cikin damuwa tace "Sis bari in fara hada mana kayan mu mukoma gurin Anty Amnah din gobe, this is getting worse, sannu" gyada kai Nafisa tayi tanajin dadi aranta, dama abunda takeso kenan.
Kayan Nafisan tafara hadawa cikin babban akwati sannan ta wuce dakinta dan hada nata kayan itama, bayan ta gama tace da Nafisa "Yanzu yaya zamuyi sis, ko bus zamu hau, dan kinga ni hannu na bai fada sosai ba a driving din, kuma kema babu lafiya" tace "Nakira Yaya Ahmad yanzu yace yana gari, zaizo ya kaimu goben" sai Na'ima tadan bata rai tace "Ba ga bus ko train ba Nafisa" Nafisa tace "Sis gwara dai shidin yakaimu" shiru Na'ima tayi tana jin wani iri, tarasa ma ita fushi zuciyanta keyi dashi ko kuma son ganinsa takeyi oho..... dan har yanzu bata manta da maganganun da ta kyaba masa ba ranan, ta kuma quduri niyyan zata bashi hakuri akan hakan.
Ranan ma sake kwana Na'ima tayi a dakin Nafisan washegari bayan sunyi sallah da sassafen ta fara tattare gidan, kayan abincin da suka siyo jiyan ta ware wanda tasan zasu baci ta maidasu leda zasu tafi dasu can gidan Anty Amnahn, bayan ta gama tayi wanka ta gyara gashinta into dough ta shirya cikin wani sky blue din abaya tayi rolling gyalen, lip balm ta shafa har da mascara sai kuma ta tsaya kallon kanta a madubin, aranta tana dariyan meyasa take saka effort gurin kwalliya kuma, tananan tsaye ta jiyo door bell dinsu yayi qara...