Kamar da wasa pg 2
by @mrsomar
KAMAR DA WASA...💘
Fatima Isah
(Mrs Umar)
Page 2
FCT ABUJA🥰
A hankali yake taka steps ɗin Flight da ya sauke su yanzu nan bada jimawa ba a filin jirgin Nnamdi Azikiwe International Airport da ki cikin babban birnin tarayya Abuja. Duk da yana cikin tashin hankali amma natsuwar shi da kamalar shi bai sa sun nuna a gangar jikin shi ba. Zamu iya cewa shine farkon fitowa daga cikin jirgin kafin mai take mashi baya ya biyo shi da sauri yana binsa inda ya nufa. Jeren motoci ne a wajan an jera su gwanin sha'awa komai na airport ɗin a kan tsari suke gudanar dashi tun kafin su kara so da sauri matasa biyu suka fito daga cikin motar da suke ciki kirar Luxury rental Landrover army green gaban ta an saka mata tambarin wuka da taurare a jiki sai ɗaukar ido take salute ɗin shi suka yi kafin wanda suka iso wajan tare ya yi saurin buɗe mashi mota. ina kyautata zaton shine P.A ɗinshi wanda suke tare da drivern motan da sauri ya bar wajan ya nufi ɗaya daga cikin motocin sojojin da suka zo ɗaukar shi shi kuma P.A ya shiga cikin wanda ya buɗewa ogan nashi. Babu ɓata lokaci suka tayar da motocin suka fara tafiya gwanin sha'awar saboda convoy da suka yiwa motocin kallo ɗaya zaka yiwa motocin ka gane ba karamin soja bane a ciki.
Sai da suka fita daga area airport É—in kafin P.A É—in ya juyo cike da girmawa ya ce.
"Sir gida zamu je ka yi wanka ka huta?"
Wani irin kallo ya watsa mashi wanda shi kadai ya isa amsar da yake bukata da sauri ya juya ga drivern ya ce.
"Ade just go straight to the hospital"
"Ok"
Wani abu ya ɗauka kamar waya ya danna babu ɓata lokaci ya kara a kunnensa umarni ya bada inda zasu je haka ya tabbatar da motocin gaba yake magana. Babu ɓata lokaci suka isa babban asibitin Babindo Centre hospital ( Allah jikan mahaifina da mahaifiyata) dake cikin unguwar mabushi. Masha Allah kallo ɗaya zaka yiwa asibitin kasan tabbas kuɗi masu sunan kuɗi suka ginata. Dan tabbas ta tafi da imanina. A yanzu kam tun kafin P.A ya buɗe mashi mota ya buɗe da kansa ya fito da sauri tamkar zai tashi sama da sauri ya nufi cikin asibitin ganin shi yasa Anas dake tsaye isowa wajan shi da sauri tare ta yin salute ɗin shi ya ce.
"Welcome Sir"
"Anas me ake ciki wane hali take ciki yanzu i hope ta tashi yanzu tasan wanda ke kanta Anas just tell me the truth idan matata ta mutu ka daina min wani hanya hanya ko faÉ—a min gaskiya"
A yanda ya karasa maganan cikin daga murya duk sai da suka tsorata, dan yana tafe suna binshi a baya har suka iso wajan. Kai Anas ya girgiza cike da girmamawa ya ce.
"I'm sorry Sir tana raye yanzu haka ba'a barin shiga wajan ta mu ƙarasa dan doctor Shuraim na wajan ta yanzu nan ya shiga"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da jan ƙafaffunshi da suka yi masa nauyi suka isa ɗakin da take daidai doctor zai fito suka ci karo da sauri duk suka tsaya doctor Shuraim ya washe baki tare da miƙa mashi hannu yana faɗi
"S.Y Shattima saukar yaushe?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kirkiro murmushin ƙarfin hali ya aro jarumta ya ɗaurawa kansa ya ce.
"Wallahi yanzu nan na sauka Galadanci ya jikin matata"
"Da sauki yanzu nan fitowar da na yi zan tambaya yaushe zaka iso dan tun data farka sunan ka kawai take kira, so mu shiga daga ciki"
Babu musu doctor Shuraim Galadanci ya juya ciki shi kuma yana take mashi baya. Babu wanda ya yi yunkurin binsu daga cikin yaran nashi sai duk sunyi tsaye bakin kofar É—akin tamkar samudawa, sojojin dake da kaki a jikin da bindiga ko duk sun rabu ko wanne da wajan da yake tsaye sanye da bakar bulletproof.
Tunda ya shiga cikin É—akin idonshi na kanta kwance take kamar gawa ga na'urar lumfashi a hancinta da bakinta, babu tantama ita ke taimaka mata wajan lumfashin
A hankali ya karasa jikin gadon da take kwance dakyar ya iya É—aga hannun shi ya É—aura saman kanta yana shafawa a hankali tare da rankwafowa dai dai saitin kunnenta ya fara faÉ—in.
"Jamilah Please open ur eyes I want to see your eyes open"
Kamar jira take taji muryar shi ta wani zabura tare da buɗe idanunta lokaci ɗaya ta sauke su saman fuskar shi. Sai kuma a hankali ta fara ƙoƙarin rufewa da sauri ya furta.
"Please don't"
Wasu hawaye ne masu zafi suka gangara gefen fuskarta a hankali ta daga ɗaya hannun ta da ƙarin ruwa baya jiki ta fara ƙoƙarin cire oxygen. Da sauri ya taimake ta ta cire tana wani jan lumfashi da sauri da sauri daka kalla kasan bana lafiya bane ta fara magana can ƙasan makoshi har sai daya kai kunnen shi jikin bakinta yaji me take faɗa.
"Rahati I'm sorry wannan ciwon nawa na tabbata bana tashi bane ka gafarce ni ina boye maka abubuwa da dama na so ka fahimta amma ina abin ya gagara. Ina mai rokonka idan na mutu dan Allah kada ka barmin yara wajan kowa ka rike su a hannun ka, ka kula min dasu kada ka bari su yi kukan rashin mahaifiya. Iman na bukatar kulawar ka fiye da ta Milal tunda ita tana da lafiya. Ka saka ido sosai a mutanen nan da ke..t.."
Inaa ta gagara karasawa saboda lumfashi ta dake fisga, da sauri doctor Shuraim Galadanci ya ƙara so wajan gadon yana ƙoƙarin mayar mata da oxygen sai dai ina mai faruwa ta faru yana dai dai saka mata rai na halin shi idanunta suka yi sama.
"Innalillahi wai nna ilaihi raji un"
Abinda doctor Shuraim Galadanci ya faÉ—a kenan tare da saka hannu ya rufe mata idanu yana jan mayafin da aka rufe mata daga kafafun ta zuwa kugu ya ida rufe mata har fuska sai lokacin. S.Y Shattima ya samu damar kawo lumfashi tare da rike mashi hannu yana faÉ—in.
"Galadanci don't tell me that matata ta rasu?"
ÆŠagowa ya yi yasa hannu ya É—an bubbuga kafaÉ—an shi ya ce.
"I'm sorry ta riga mu gidan gaskiya sai hakuri addu'ar ka take buƙata"
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji un. Ya rabbi ka kawo min sauki a zuciya ta"
Abinda kawai ya iya faÉ—a kenan ya dafe kanshi saboda juya mashi da yake yi. Fahimtan halin da yake ciki ya saka doctor Shuraim Galadanci kama shi ya zaunar kan kujera yaci gaba da mashi nasiha mai shiga jiki. Hawayen kan fuskarshi ya goge tare da cewa.
"Nagode Galadanci ina so yanzu a bani ita mu wuce gida dan bana so a ɓata lokaci gara ayi mata sutura kawai"
"No problem za'a iya yin haka"
Daga haka ya mike ya fita.
"Me yasa jamcy baki faÉ—a min abinda ke faruwa dake ba sai da lokaci ya kure, kin tafi kin barni cikin duhu ta ina zan fara ni Shamsu oh ya rabbi"
Hannun shi yasa yana murza goshin shi da sauri da sauri saboda yanda zuciyarsa ke bugawa.
Tun a bakin kofar fita doctor Shuraim Galadanci ya faɗawa su Anas matar ogan nasu fa babu ita ai kam take hankalinsu ya tashi matuƙa.
Kamar yanda S.Y Shattima ya bukata babu ɓata lokaci aka yi komi aka gama dama sis ɗinta Naana ke tare da ita to doctor yace ba'a son ganin kowa wajanta shi yasa taje gida ta dawo.
Ƙarar kamar kukan jiniyan mota yasa basu kawo komi a ransu ba suka ɗauka S.Y Shattima ne yazo gidan kamar yanda ya saba. Sai dai ganin aunty amarya ta shigo ɓangaren da gudu tana kuka yasa gaban mafi yawan da suke zaune a falon mahaifiyar S.Y Shattima wanda suke kira da Dada duk kansu mikewa sukayi suna tambayar ta lafiya.
#son zuciya
#makirci
#yaudara
#soyayya