FreeArewaPen original
KAMAR DA WASA
- 1views
- 67chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Suna Fatima Isa Ni marubuciya ce kuma har kasuwa ina sha'awa karatun littattafan Hausa shi yasa na zama daya daga cikin marubuta yanar gizo da ake taka rawar gani dasu. Ku kasance dani Ni kuma zan cigaba da nishadatar daku haɗi da fadakarwa
Sample · Kamar da wasa page 1
KAMAR DA WASA..💘 Fatima Isah Page 1 *GARGAƊI* Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne. Ba nayi shi ba ne dan cin fuskar wani ko wata ba, ko cin zarafinsu ba, na yi shi ne kawai dan nishaɗi haɗi da fadakarwa. Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ko da kalma ɗaya. Dan haka a kiyaye. ADDU'A Ya Ubangiji sammai da ƙassai ina mai tawassali da sunayenka tsarkaka kajiqan mahaifiyata da mahaifina Allah kasa aljannah firdausi ce makomarsu da dukkan Musulmi baki ɗaya************* Tun ina ƙaramata na tashi da rashin ji bana barin ko ta kwana. Saboda rashin ji na yasa mutane da yawa ke kirana marar kunya dan duk girman mace duk shekarunta ta shiga gonata tabbas sai na wanke ta soso da sabulu ko a jikina. Na kan samu goyon baya wajen mahaifina dan shima mutum ne da baya barin sai ta kwana saboda halin shi yasa babu wanda bai sanshi ba. Saɓanin mahaifiyata da macece babu ruwan ta, in dan ita ne da duniya bata tashi ba, mutane da yawa na ganin girmanta, sometimes akan dinga tunanin anya Ummiy ita ce ta haife ni anya ba musanya aka yi mata ba? Amma tsananin kamar da muke yasa mutane da yawa ke ɗaukar lamari ne na Ubangiji Allah mai yanda yaso farin tukunya mai fifda baqin tuwo. Lokacin baya mutane na ɗaukar lamarina harda kuruciya idan na girma zan bari amma ina sai abinda ya qaru har zuwa yanzu da nake mizanin shekaru 22 babu abinda ya sauya dan na zamewa matan layin mu ƙadangaren bakin tulu.Rashin wutar da ake ta fama dashi kwana biyu yasa mu fita neman ruwa ni da yan uwana. Ahmad da Sadiq tunda muka taho babu tsiyar da suke taimaka min sai saka ni ciwon baki har muka zo soldiers club wajen da dole sai sun taimaka min baron zata wuce saboda jarka goma sha biyu ce a cikin kuma babu wanda babu ruwa. Tsawar dana daka masu ce yasa suka dawo cikin hayaccin su dan hatta su suna jin tsoron masifata. "Banzaye kawai to idan baku kama min ba ubanwa zai kama danma kun samu na taimake ku shine zaku dinga min iskanci, kada ku kama mu wuce nan kuga aiki da cikawa" Murmushi kawai Ahmad ya yi dan shi mutum ne da baya son tashin hankali zan iya cewa duk halin Ummiy ya biyo saɓanin Sadiq da Amina da halin mu ke kamanceceniya dana juna. Ni ce babba sai Ahmad na bi min sannan Sadiq Amina ita ce auta. A wahale muka iso layin mu dake jerin dogon layi mai ɗauke da ɗakuna goma cikinsu babu wanda babu mutane a ciki. Zan iya cewa wannan Block namu ya yi suna a Barrack dan babu wanda bai san da zaman shi ba,in dai wajen faɗa ne da gulma to wannan layi namu shine number one. Kamar ko yanda muka tafi muka barsu haka muka samesu a bakin bishiyar dogon yaro, suna gulma wanda basa nan da kuma maganar abinda ke faruwa da gidan auren ko waccensu. Ko kallo basu ishe ni ba na wuce su sai su Ahmad ne suka gaida su cike da girma...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.