RUWA CIKIN COKALI

chapter 23

by @mamanafrah3028

***



*RUWA CIKIN COKALI* 
(Ya ishi mai hankali wanka)
 
                  
                NA


         MAMAN AFRAH

 
.        *Daga marubuciyar* 
  *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* 
      *****

           BOOK 1

         PAGE 2️⃣2️⃣



ALIYA 

   Da tsananin faɗuwar gaba ta ƙarasa hawa saman benen ko fargabar ɗaya daga cikinsu bata yi ya zo ya ganta. Sai da ta gama hawa ta je ta rasa ma wace ƙofa ce za ta buɗe inda za ta ga inda aka ajiye abincin ta canja cokalin tana rarraba ido duk ta rikice burinta kawai ta aikata abin da fa kawo ta sai dai bata san ya za ya yi abin ya tabbata ba tare da wata matsala ta biyo bayan hakan ba.
  A hanzarce ta yi hanyar ƙofar ɗaya ta tura ta shige saboda ƙarfin hali har da karo ƙofar sai dai kash sai bayan ta shiga ta gane ba ɗakin da take nema ba ne don babu alamar wani abinci a ɗakin.Da sauri ta fito tana ta tunanin rashin nuysuwar da take da shi wanda ya sa bata gane inda za ta shiga ba sai dai ta san dama ba za ta samu nutsuwa ba saboda kawai tunaninta ya ta,allaƙa ne ga samun cikar burinta wato canja cokalin ne kawai a gabanta wanda take tunanin daga shi burinta na duniya ya cika.

  Ɗaya ƙofar ta tura a nan ne wani farinciki ya baibaye zuciyarte, domin tana buɗewa ta yi arba da system da kayan abincin da Jidda ta kai sannan uwa uba cokalin da yake kan plate ɗin tabbas shi ne dai wanda bokanyan ta yi aiki a kansa, wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Aliya maimakon ma ta yi abin da ya kaita sai ta tsaya ta ƙarea ɗakin kallo tana ƙiyasta nan da wasu kwanaki da basu taka kara sun karya ba ɗakin zai zama ya dawo ƙarƙashinta wato ita take iko da shi.
  Ƙarasawa ta yi ta tsugunna a gaban plate ɗin ta saka hannu ta ɗauke cokalin kan plate ɗin ta ɗora na hannunta wanda ta zo da shi, sannan sai ta ɗaga bra ɗinta ta saka wanda ta ɗauke wancan ɗin. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta samun nasara.

  Baki ta taɓe tana tashi tsaye har hango ta take yi tana zuba ƙasaita sai motar da ta ga dama kuma ta yi ra,ayi za a ta shiga hatta dangi da ƴan uwan Ibrahim ɗin ma kansa sai sun dawo ƙarƙashinta. Dama Abba ne matsalarta to gashi an ce aikin da aka yi mai gabaɗaya ne wato kowa da kowa.

   A zuciyarta ta ce

"Uhmm Aliya rufawa kanki asiri ki koma ƙasa ki zauna ki naɗe ƙafa kamar baki motsa daga wajen ba, tun da dai Allah ya ida nufi kin canja cokalin' Ta faɗa tana zuwa ta miƙa hannu za ta buɗe ƙofar, kamar abin almara kawai sai ta fara jiyo ƙaran takun takalmi alamar ana hayowa saman, idanu ta zaro ƙirjinta yana fatfat waiga bayanta ta yi tana jin faɗuwar gabanta yana tsananta a take ta shiga tunanin waye a cikinsu yake ƙoƙarin hayowa saman shin Jidda ce ko kuma shi mai gabaɗayan ne wato Ibrahim. 

A fili kuma a hankali ta furta
"Na shiga uku asirina yana dab da tonuwa" Ta faɗa tana haɗiye wani yawu muƙut.
  Tunani ta fara shin idan Ibrahim ne ya same ta a ɗakin nan wane zargi zai yi mata da wane idon ma za ta kalle shi ko da a ce a saman ya same ta ba ma a ɗakin ba mai ya kaita ɗakinsa a lokacin da shi da Jidda basa wajen. A gefe ɗaya tana tunanin idan Jiddar ce kuma fa? Wace amsa za ta bata shin mai Jidda za ta ɗauka dangane da sauya akalar tsanarta zuwa tsantsar ƙaunar ƙarya da suka yi don kawai ta auri mai dukiya, tabbas ta san duk wanda ya yi ido huɗu da ita yanzu to haƙiƙa sai ya mata kallon tuhuma domin gabaɗaya alamomin rashin gaskiya sun bayyana ƙiri-ƙiri a tare da ita.
 Jin takun yana matsowa dab alama ce ta mai hayowar ya kusa ƙare tako matakalar da sauri ta koma ta shiga waige waige tana son gano inda za ta ɓuya ta gwammace ta kwana a ɓoye idan har hakan zai yiwu a kan a ganta zargi marar adadi ya hau kanta!.

    Abin da yake kai kawo aranta shi ne idan kuma Jidda ce dole ai za ta ga bata falon sannan komanta tana falon ita cw bata nan mai za ta ce mata kai abin ya haɗe mata goma da ashirin. Amma hakan ba zai sanya ta karaya ba don cikar burinra da na Ummarta ya fi komai a halin yanzu. Kaf ɗakin bata ga wajen da za ta ɓoye ba tare da an ganta ba hakan ya sa ta yi wajen drower za ta shiga tsakanin drower da bango ta takure ko Allah zai tseratar da ita kar a ganta, sai daj tana zuwa ta ga wajen ya yi mata kaɗan ta shige domin dole za a hango ta a kiɗime ta fito ganin babu mafaka sannan sirinta yana dab da tonuwa sai kawai ta buɗe ƙofar banɗaki ta shige tana shiga ta mayar da ƙofar ta rufe. Jikinta har karkarwa yake da ta ji an turo ƙofar ɗaki ta shiga fargabar sa sai take jin tamkar ko numfashi ta yi sai an ji.

 A ɗarare ta samu wata tula a jikin ƙofar ta leƙa taakar ɗakin gabanta ya bada sautin dimmmm ganin Ibrahim ne ya shiga a nan ta tabbatar kashin ta ya bushe domin ta san tun da ya dawo ɗakin dole Jidda ma ta yi wa ɗakin kutse. Yana shigowa ya ajiye wayoyinsa a kan gadon ya hau cire rigar jikinsa a take Aliya ta yi wa idanunta masauki a kan kyakkyawar lallausar fatarsa kasancwar ya bata baya nw yana juyowa sai da ta kusa zaucewa ganin kyakkyawan gargasa shimfiɗe a faffaɗan ƙirjinsa ya kwanta lifet kallon tsari na kyawun halittar da Allah ya masa kawai take a take ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin lallai Jidda ta more da samun kyakkyawa kuma nagartaccen miji kowacce mace ta samu miji irin wannan tana ganin a duniya an sallame ta ta wannn ɓangaren.

  Gaban ta ne ya buga da ƙarfi da ta yi wani tunani cewa ko dai wanka zai yi a take ta ji shagalar da ta yi da kallon nasa tana yaba kyawunsa ta ji ya ɓace mata yawun bakinta ya ƙafa ta ji bakin ya bushe. Jikinta ne shiga karkarwa tana hangowa cewa idan ya buɗe banɗakin ya same ta ya za ta yi tana cikin wannan tunanin sai ta ga ya juya ya nufi wajen drower ya buɗe ya ɗakko wasu kayan ƙanana ya saka coffe ɗin wando da wata farar riga mai hoton damisa coffe a jiki a hanzarce ya ɗauki wayoyinsa tana jin yana waya ya buɗe ƙofar ya fita.


   Bayanta ta juya ta jingina a jikin ƙofar bayan ta rufe idanunta tana sauke ajiyar zuciyar tsalllake rijiya da baya, yanzu abin da ya rage sai ta bari idan ya ɗan jima da fita sai ta fito ta lallaɓa ta koma falon ƙasa.

  A haka ta lallaɓo ta fito tana sauri sai da ta leƙa daga jikin ƙofar ta ga tana hango step ɗin na benen alamar Ibrahim ya fita sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito kamar wanda aka jefo Jidda haka Aliya ta hango ta gashi ta riga ta fito daga ɗakin har ta rufe ƙofae babu damar ta koma hakan zai sa Jiddar ta ji ƙaran ƙofa da hanzari Aliya ta ji gefen jikin bangon da yake gefe ta laɓe, haka Jidda ta hayo tana sanye da wata doguwar riga mai tattara a hannun wacce gabaɗaya rigar kamar an halitta ta a jikinta yadda ta kama jikinta dole kowane namiji mai lafiya ya kalleta ba zai iya ɗauke idanunsa ba sannan dole sai wani abu ya ɗarsar masa a zuciya, tana riƙe da fulas ɗin tuwon don dama na miyar ne ta kai da plate da cokulan.
 Addu,a take a zuciyarta kada Allah ya sa Jiddar ta waiwayo bayanta don tana juyowa za ta ganta sai dai Jidda da hankalinta yake a gaba bata waiwayo ba ta wuce tana takunta ta nutsuwa wanda gabaɗaya rigar da ta kamata duk takun da za ta yi sassan jikinta suna rausayawa. Tana tura ƙofar ta rufe ta nufi inda ya cire kayansa ya ajiye ta shiga linkewa za ta saka a kayan wanki don ita al,adarta ce kaya ko na wanki ne saj ta linkeshi. 

   Aliya tana shirin kama gabanta ta sauka ƙasa sai kawai ta ji ƙaran takalmi ana hayowa sama, idanu ta zaro da sauri ta lallaɓa ta tura ƙofar ɗaya ɗakin a hankali ba tare da ƙofar ta yi ƙara ba ta shige ta rufo gabaɗaya ta haɗa gumi tana leƙowa ta hango Ibrahim yana hayowa, duk ta haɗe gumi na tsurewar da ta yi,. ta ji lokacin da ya tura ƙofar ɗakin Jim kaɗan ta ji an sake buɗewa sai ta fara jin maganarsa yana cewa

"Ba jimawa zan yi ba ina ɗakko saƙon zan dawo na yi tunanin ma a mota na bar shi amma da na duba ban gani ba na san yana office" 

  Sai ta ji Jidda cikin wata sassanyar murya mai tafiyar da nutsuwar miji tana cewa

"Yanzu wannan tuwon da ka sa na maka haka zai yi ta jiranka" Ta faɗa ta karashe tana wani yin kamar ƙaramar yarinya ta ji lokacin da ya ce

"Kin san dai wannan tuwo dole ne ma in ce ai har ɗumame zaki min da safe ko Jiddana?" Ya faɗa cikin sigar wasa da lallashi. Wani daɗi a cika ran Aliya jin yana batun cin tuwon sai kuma ta ji Jidda ta ce

"To ni dai karka daɗe ka ji" Ya kalle ta yana dariya ya ce

"Idan na daɗe tsallan kwaɗo za ki saka ni" Tana kumbura baki ta ce

"Kuka zan yi" Hannunsa ya saka a bakinsa yana ɗorawa a kan laɓɓansa guda biyu ya ce

"Karki yi min kuka da wannan idanun naki in ba haka ba zan rama da tsakiyar dare" Da hannu biyu ta rufe fuskarta tana jin yadda koyaushe son Ibrahim yake ƙaruwa a zuxiyarta saboda ya iya tafikar da mace ya san kalamai da ayyukan da zai yi mace ta so shi tabbas Ibrahim ya iya koyawa mace yadda za ta so shi.


   Aliya duk da bata ganinsu amma tana jin yadda tattaunawar tasu take gudana haka nan kuma ranta yana ƙuna da abin da suke faɗa, sai dai ta sa duk ihu ne bayan hari, sannan saura ƙiris tarayya da alaƙarsu ta zama tarihi babu abin da ya fi faranta mata irin da ta ji ya ce sai ya ci tuwon nan har da ɗumame da safe ai kuwa ta san shikenan burinta ya cika!.

   Tana jin yana mata sallama har yana cewa da dare za su je su gaishe da Mummy duk don ya farwntawa Jiddan tun da ya san tana ƙaunar Mummy ita ma Mummy tana ƙaunarta. Tana jin ƙaran saukarsa daga benen sannan ta ji lokacin da Jidda ta koma ɗakin ta rufo. Aliya tana maƙale a ɗakin a jikin ƙofa kamar wata ƙadangaruwa, sai da aka ɗan jima ta tabbatar yanzu Ibrahim ya bar falon ƙasa wato ya fita kafin ma ta gama wani tunani ta jiyo ƙaran buɗe get ɗin gidan haka ya bata tabbacin ya fita ma.


  Yanzu ne take so ta shammaci Jidda ta fito ta yi saurin sauka ƙasa tun da ta tabbatar yanzu Jidda ta san bata falon thn da ta fito ta ga bata ganta ba, saboda haka dole ta tanadi hujjar da za ta kare kanta da ita duk da wannan ba matsalarta ba ce a halin yanzu matsalarta ta fi karkata ga sauka daga saman wannan kafin asirinta ya tonu. Juyawa ta yi tana kallon ɗakin da take ciki tana ƙiyastawa a ranta yanzu haka Jidda gyaran ɗaki take ta san kuwa abu ne mawuyaci ta kasa shigowa ɗakin da Aliyar take ta gyara.

  A zuciyarta ta ce
"Uwar shegiyar tsaftar jaraba, dama wannan bata dace da ƴan aiki ba ni ce na fi dacewa a kawowa ƴan aiki wannan kalar ma,aikata ce ba kalar hutu ba ma,aikatan ma ƴan wanke-wanke' Ta faɗa tana jan ƙaramin tsaki.

  Cikin sanɗa ta buɗe ƙofar a hankali ta mayar ta rufe ta fara lallaɓawa tana takawa a hankali sai da ta je tsakiyar benen kawai ta ji ta yi wa ƙafarta masauki a cikin lema, kafin ta tantance sai ji ta yi suuuuuu ta yi wata uwar sufer da ta ganta zaune jaɓar tana gangarawa bata yi masauki ba sai a step na ƙarashe jin ƙaran buɗe ƙofa a sama ya sa ko hutawa bata yi daga gangarowar ba ta tashi da sassarfa ta tashi jin ƙugunta ya riƙe ta miƙa hannu ta riƙe tsantsa tana takawa dakyar da sauro ta yi tsakiyar falon Saude da take haɗa kayan wanke wanke a kicin tana ganin abin da yake faruwa a idonta ta shiga dariya marar sauti har da riƙe ciki.

  Aliya kuma sai ta shiga sauri-sauri gudu-gudu ta yi hanyar ɗakin da yake kusa da wanda Jidda ta shiga yin wanka, tana wani cangala ƙafa kamar kwaɗo, don tafiyar kamar tsalle haka take tana shigewa ɗakin ta rufo. Saude kuwa har lokacin tana ta dariya duk da bata san dalilin da ya kai Aliya saman ba amma kuma dai ta san ba wani abin kirki ba ne tun da babu yadda za a yi take sauri tana son guduwa alamun bata so a ganta duk da faɗuwar da ta hanga ta yi daga saman benen amma ko fatsarwa bata yi da jin ciwon ta tashi tana tafiya kamar wata sabuwar yar shayi tana tale ƙafa tana riƙe ƙugu ga wani ɗan tsalle da take tana cangala ƙafa.

  Akiya tana shiga ɗaki kawai sai ta kwanta a ƙasa sa,arta ɗaya ma kafet ɗin ɗaki da yake da laushi sosai, birgima take tana ambaton wayyo a hankali ji take kamar ta yi ihu amma babu hali don gwiwar hannunta ma da ta bugu ciwo take mata. Haka ta daure ta shiga banɗaki ta wanke ƙafa sai fuskarta ta fito sai da ta ɗan ji jikin nata ya ɗan koma daidai ta buɗe ƙofar ta fito tana ƙoƙarin gyara ɗankwalin kanta. Jidda kuma tana ɗakin bayan ta ɗan ƙara ɗame gadon duk da shimfiɗar bata waji ɓaci ba. Dama cikin zannuwan gadon da Mummy ta aiko mata ranar nan ne wanda ta ce a wajen MAMAN AFRAH marubuciya ta saya domin babu abin da bata sayarwa, guda huɗu ta bata zanjuwan gadon da mai haɗe da labulaye da mai bargo sai mai filo huɗu dukka na ɗinkawa ne sai kuma wani lumtsumeme shi kuma na kamfani ne. Sun yi kyau sosai don da ta kira Mummy tana mata godiya sai ta ce za ta bata lambar MAMAN AFRAR ko za ta saya wani abu saboda kayanta suna da inganci tana siyar da labulaye zannuwan gado, takalman yara da manya, kayannyara ɗinkakku da na kamfani mayafai atamfofi lace abaya hijabai tutaren wuta, magungunan mata maganin sanyi, kayan sanyi, kayan kicin da sauransu.
  Tana cikin gyarawar ne ta ji rigif alamar faɗuwar wani abu dalilin da ya sa ta fito kenan sai dai abin mamakin tun daga can saman take waige -waige har ta zo ƙasa bata ga alamar komai ba, sai dai ta ji ta taka lema da bata san ya aka yi hakan ta faru ba. Tana zuwa tsakiyar falon hakan ya yi daidai da zuwan Aliya ma sai kawai Jidda ta kalle ta ta ce

"Wai ina kika shige ne ni wallahi na ɗauka ma fita wajen kika yi ko saƙo aka kawo miki" Tambayar nan ta sake saka Saude a shakku don yanzu ta ƙara tabbayarwa Jidda bata san da zuwan Aliya sama ba, hakan ya sa ta fara hasashen dama ko sho dalilin da ya saka ta taho a gaggauce har tana faɗowa daga matakalar, don dama ita ta taho daga ƙofar da take sada ta da falon Jidda idan aka taho daga ɓangaren su na ƴan aiki lokacin sa ta yi wa falon tsinke ta hangi wulgin Aliya ta yi sama to duk tunaninta Jidda ma tana saman, sai bayan tana kicin kuma ta ga fitowar Jidda daga ɗaki ita ma ta zo ta nufi saman, don ta ji lokacin da Jidda take cewa Aliya ina ta yi kuma. Dama ita Saude tana zargin Aliya da wani abu na rashin gaskiya don yanayin da ta ganta ranar nan a kicin ma rashin gaskiya ne ɓaro ɓaro iya nazari da tunaninnta tana ganin tsantsar tsana da kuma ƙyashi a idanun Aliya da take yi wa Jidda.

  Da gangan ta ɗauki ruwa ta je ta zuba a matakalar don ta san tun da har Jidda bata san ta hau saman ba bayan a can turakar mai gidan take to ta san tabbas akwai wata maƙarƙashiya. Shi ya sa ta zuba tuwan domin ta san tun da Jidda ta hau samn to Aliya za ta yi ƙoƙarib kuɓuta, bayan ta zuba ne kuma ta ga Ibrahim ya dawo ga hau saman tana ta addu,ar Allah ya sa kar ya ga ruwan ko kuma ya taka, duk da ma akwai takalmi a ƙafarsa ba lallai santsin ya kwashe shi ba, bayan ya fito ne kuma sai ta ga ma yanayin yadda Aliya ta taho kaɗai ya isa ta gangaro idan ta samu kufcewar take matakala sai kuma Allah ya sa ta taka ruwan ta faɗo. Ta so a ce Jidda ta ganta sai dai kash an samu akasin lissafi.
  Amsar da Aliya ta ba Jidda ya ƙara saka Saude a tarkon mamaki domin cewa ta yi

"Dama na san idan baki ganni ba sai kin tambaye ni cikina ne ya hautsina min, ganin kina banɗakin wancan ɗakin shi ne na je na shiga na wancan ɗakin" Ta faɗa tana ƴar dariya Jidda ma dariyar ta yi ta matsa kusa da Aliyar ta ce

"Ki ce rage ciki kika tafi, Allah sarki har na tuna rayuwarmu ta yarinta idan na je gidan Umma daga na ce ina jin kashi sai ke ma ki ce kina ji, in riga ki shigewa banɗaki kike ta cewa in yi sauri karki yi a wando" ,Ta faɗa tana dariya sosai, Aliya ma daeiyar take duk da hannun Jidda da ya taɓa kafaɗarta ji take tamkar an ɗora mata garwashi saboda tsantsar tsanar Jiddar da take ji amma babu halin nunawa.

 Aliya ta ce

"Umma sai ta ce ku dama kamar ƴan biyu ɗaya ba zai yi abu ba sai ɗayan ma ya ce zai yi Allah na tuba kashi dai ba a matse shi ba sai a ce ana ji idan ɗaya ya ce zai yi wa ya sani ma ko da kanku kuke ƙwaƙulowa" Aliya ta maimaita maganar cikin kwaikwayar muryar Umma suke dariya.

  Kan kujera suka ƙarasa har lokacin hannun Jidda rataye a wuyan Aliya kamar yadda suke dafa kuna lokacin da suke yaran, Jidda tana jin wani daɗi da farincikin ganin sauyawar rayuwarta a ƙanƙanin lokacj, wato a da ta rasa duk kulawa da soyayyar ƴan uwantaka da ta ƙawance tsakaninta da Aliyarta uwa uba tsantsar tsana daga Umma amma yanzu gashi komai ya shiga littafin tarihi.

  Suna zama Jidda ta ɗauke hannunta tana cewa

"Ni wai har alwala kika yi ne " Ta faɗa ta sigar wasa dariya Aliya ta yi don dama da gayya ta wanke ƙafa da fuska don ta cirewa Jidda shakku a kan cewa daga banɗaki take sai da ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce
"Kawai dai fuska tw ce na wanke"
 Saude an barta da tsantsar mamaki tana tunanin makirce da ƙarya irin na Aliya hakan yansa ta ɗarsa zargin akwai wani abu da ya kai Aliya saman wanda kuma bata jin alkaiti ne don ta san dai ai Aliya bata ce zuwa ta yi kawai don ta ga saman ba idan har ganin saman take son yi ai ba sai a ɓoye ba sai dai za ta yi amfani da hankali da basira don ta gane inda Akiya ta dosa sannan ta yi alƙawarin duk wani abu da Aliya za ta yi ga uwar ɗakinta Jidda to ba za ta bari ba matuƙar tana numfashi sai dai abu wanda yake dama Allah ya rubuta a littafin Jidda wanda yake ƙaddara ne ita kuma ƙaddara duk runtsi babi mai guje mata.

  Ƙaran wayar Aliya ne ya katse tana ɗago wayar ta ga sunan Kasim dimm ta ji faɗuwar gaba don bata san dalilin kiran ba, sai kuma ta maje don kar Jidda ta fahimci wani abu tun da dai ta faɗa mata baya gari duk da shi bata faɗa masa za ta fitan ba sai kuma wani tunani ya faɗo mata tana jin Allah ya sa tana ɗaga wayar ta ji muryar wani daban wato a ce mata mai wayar sun yi haɗari ya mutu, shikenan ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da ƙuda.
 
  Tana ɗagawa ta kara a kunne tare da yin shiru tana jiran jin labarin mutuwar Kasim

  Sai ta ji muryar wani yana cewa

 "Ai abin babu kyan gani gabaɗaya babu wanda ya tsira a motar duk sun mutu" 

  Aliya bata san lokacin da ta ce

"Alhamdulillahi ba" Don tsabar son ta ji sanarwar mutuwar Kasim bata gane cewa wani ne a gefe yake maganar ba, ba wai a wayar da aka kira ta ake maganar ba, Jidda kuma idanu ta zuba mata jin ta jero hamdala.
 amma sai ta ji muryarsa rangaɗaɗau yana faɗin

"Hlo Aliya tawa mai aka samu ne na alkairi ake hamdala haka" ,Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare ta har sai da Jidda ta ga ɓacin rai ya bayyana a fuskarta sai kuma ta ƙirƙiri murmushi ta ce

"Kawai dai jin muryarka kana lafiya shi ya sa na yi hamdala, tun ɗazu nake son kiranka in ji ya hanya sai nake sha,afa"

 Kasim ya ce

"Hanya Alhamdulillahi ai gamu nan mun kusa zuwa ma ashe ma garin ba wani nisa ne da shi sosai ba kuma mun samu lafiyayar mota don ana ɗaurawa ma muka juyo ki dafa min jallof na taliya mai ruwa ruwa" 

  Aliya ta amsa da to ba don ranta ya so ba kuma gashi a kan kunnen Jidda ya ce ta masa girki, gashi tana son cikar burinta wato ganin Ibrahim ya ci abinci da cokalin da bokanya ta gama asircewa.
 Tana sauke wayar ta ce
"Kin ji wai ya taho ma yana faɗin in masa girki gashi la,asar lis ma ta yi" Jidda ta ce
"Ya fasa kwanan kenan" Aliya ta ce

"Eh ya fasa kawai ina hira da ƴar uwata zai katse min " Ta faɗa cikin kissa Jidda tw ce.

"Ai ni ma zan kawo miki wuni" Aliya a fili ta ce

"Amma ranar da na ji daɗi"

  Ji

A zuciyarta ta ce

'Yarinya daga yau za ki yi bankwana da kwanciyar hankali da nutsuwar da har za ki yi tunanin kai wa wani ziyara"

Jidda ta ce

"In sha Allah"

  Ɗan ƙaran ƙofar kicin ne da Saude ta buɗe ta fito don dama a karawa ta yi take tsegumin da take yi shi ya ankarar da su da akwai mutum Jidda ta juya ta ce

"Saude dama kina kicin?" Saude ta.ce

"Eh ina ciki ina ware kayan saman kanta da suka yi ƙura ina gogewa ina jera su" Gaban Aliya ne ya faɗi ta fara tunanin shin tun yaushe Sauden take kicin? Ba dai tana kicin ta faɗo daga saman bene be? Ko dai lokacin da ta shige ɗaki ta shiga bamɗaki tana wanke fuska ta zo ta shiga, gaban Aliya ne ya faɗi don ta ji yanayin yadda aka buɗe ƙofar kicin ɗin bai yi kama da cewa ƙofar a rufe take ba ya fi alama da dama ƙofar ba a rufe take duka ba.

  Kallon tuhuma ta fara jifan Saude da shi bayan ta fakaici idanun Jidda, ita dama ta tsani Sauden nan don ta lura ruwan munafukai ne da it, ita kuma Saude sai ta ɗauke idanunta ta fara takawa za ta bar falon don ko alama bata ma nuna ta san Aliya tana aika mata saƙon harara ba.
 Ta kama hanyar fita sai ta ji Jidda ta ce

"Saude zo ki bamu kunun gyaɗa" Da to ta amsa ta juya ta shiga kicin ɗin, ita kuma Jidda sai ta ce tana zuwa ta tashi ta shiga ɗaki jin wayarta tana ƙara, tana shiga ta ga Salama ce suka ɓige da hira.

 A falo Aliya ta tashi sai ta sunkuya za ta ɗauki jakarta, a daidai nan Saude da take ɗauke da kofuna biyu da cokali a cikin kowanne ta zo za ta ajiye kawai sai idanunta ya sauke a ƙirjin Aliya nan ta hangi cokali kane-kane a cikin bireziyar Aliya, idanu ta zaro gabanta yana faɗuwa da sauri ta kawar da idanunta ta ajiye kufunan ta juya za ta bar wajen daidai nan Aliya da ta ɗauki jakar tata ta ɗago cikin kaushin murya ta ce

"Keee!" Amma Saude ko gizau bata yi ba bare ta juyo ma ko nunawa bata yi akwai wata halitta a wajenta ba ta yi tafiyar ta tana dab da shiga kicin Aliya ta sake cewa

"Ke Saude aba da ke nake magana ba" Juyowa ta yi cike da nuna rainin hankali ta ce

"Au wai dama da ni kike? Ai na ji kin ce kee ni kuma da aka yanka rago Saude aka raɗa mini" Ran Aliya ne ya ɓaci hakan yansa ta yi jifa da jakar a kan kujera ta nufi Saude a fusace tana zuwa ta damƙi rigar Saude daga kafaɗa ta ce

"Ke ni kike faɗawa hakan?" Saude ta yi shiru batance komai ba don dama fitsararriya ce ta ajin ƙrshe don ta ga aiki take shi ya sa bata zaƙewa. Aliya ta kalle ta cike da tuhuma ta ce

"Tun yaushe kike cikin kicin" A fili ta ce

"Lokacin da Aunty Jidda ta dafa kafaɗarki kuna tsaye a can lokacin ne na zo na shiga" Ta faɗa tana nunawa Aliya inda suka tsaya ɗazu sai Aliya ta ji daɗi don hakan ya nuna bata ganta ba a zuciyarta ta ce

'Tun lokacin da kika haye sama' 

  A daidai nan Jidda ta fito daga ɗaki sai Aliya ta ƙirƙiri dariya tare da sakin riƙon da ta yi wa Saude ta ɗan buga kafaɗar Sauden da wasa tana cewa

"Kina birgeni Saude" Saude ganin barikin da Aliya ta yi sai ita ma ta yj dariya tana cewa

"Na kuwa gode Aunty Aliya bari na kawo muku sugar" Juyowa ta yi ta dawo falon Jidsa tana riƙe da wayarta tana dariya don ita sai ta ga sun birgeta tana ta mamakin sakkowar Aliya yanzu ta zama mai sauƙin kai sai take ganin hakan ne ya dace domin dama duniyar kanta nawa take da mutum zai ke ɗagawa da girman kai.


  Ko da ta kawo musu sugar suka sha kunun Aliya ta ce tafiya za ta yi Jidda ta saka direba ya kaita gidan, tun da ta san Jidda ta ji Kasim ya kira ya kusa dawowa sannan kuma tun da bata faɗawa Kasim ta fita ba duk da ta san idan ma ya san ta fita ɗin ba wani abu zai mata ba amma kuma dai tun da lallaɓawa take ta samu cikar burinta za ta daure ta kuma cije!.

 Ta haɗa mata sha tara ta arziƙi tana cewa sai ta kawo mata nata wunin, ko da ta rako ta bakin motar bayan ta saka dogon hijabia sai Aliya ta ƙame a gefe ta ce direba ya fito daga mazaunin direna ya buɗe mata haka ya fito ya buɗe ta shiga ya rufe wani daɗi take ji lalai mulkar wani akwai daɗi dole ta baza iko iya iko idan ta karɓi ragamar gidan Ibrahim. Da suka zo wucea mai gadi ya buɗe musu get sai da ta buɗe glass ta wurga masa uwar harara.

  Ana kiran magriba direba ya kaita ƙofar gidanta ya buɗe mata ta fito tana wani shan ƙamshi tana riƙe da ledar da Jidda ta bata wanda bata ma san mene ne a ciki ba sai kuma jakarta, tana jin ranta fari ƙal don ta yi aikin da ya kaita gidan.

  Tana shiga suka ringa waya da Amatullahi suna ta murna Amatullahi har da guɗa Aliya za ta zama matar manya, sai dai kuma sai ta ji tana baƙincikin cewa Aliya ta yi aure ta barta a gida sannan yanzu za ta ƙara yin wani auren ta shiga gidan arziƙi ita tana nan samarin kullum ta ce su fito sai su fita da gudu.


  A gidan Ibrahim yana shigowa gidan shi ma ana kiran magriba alwala ya yi ya wuce masalaci, lokacin da ya dawo suka haura sama ya ce Jidda ta zuba masa abincin haja ta zuba masa yana cewa

"Idan na cinye sai kin ƙara mini domin kin san ina son tuwo" Dariya ta yi ta ce


"Ai idan ka cinye na fulas ɗin ma sai a ƙaro maka a kicin" Dariya ya yi ya ce

"Mai kika sanya mini idan na cinye?"
 Tana kallonsa ido cikin ido ta ce

"Mai kake so in sanya maka kuɗi ko mota?"
  Ɗan ɓata rai ya yi ya ce

"Kuɗi abin so ne, saboda da su ne ake abubuwa na rayuwar yau da kullum, mota kuma wani abu ne na ƙawa a duniya sai dai ba dole sai da ita ake rayuwa ba, kamata ya yi ki saka mini abu mai muhimmancin da ya fi wannan" Da alamar mamaki take kallonsa ta ce

"Kamar me?" Kafe ta ya yi da idanunsa wanda take jin suna yawo a duka jikinta tamkar yadda jinin jikinta yake zagayawa a cikin jijiyoyinta ya ce


"Jiddarh,?" Ta ce

"Na'am"

 Ya ce
"Kamata ya yi ki bani kyautar kanki ina nufin ki saka mini kanki a cin abincin nan sai na fi ci da yawan da zan baki mamaki" Wani murmushi ne ya ƙwace mata wanda bata yi zato ko tsammani ba ta ce

",Banda abinka ni dama ai taka ce"

 Hanunsa biyu ya miƙa ya tallafo gefen fuskarta ya ce

"Na sani Jidda dama ke tawa ce amma ki ce za ki rayuwa da ni za ki kasance da ni rayuwa ta har abada, za ki zauna da ni a runtsi da duk wuya, duk halin da na tsinci kaina ba za ki taɓa guje min ba Jidda, da ke nake rayuwa kr ce sanyin idaniyata na faɗawa Mummy ke ar aljanna ce Jidda na faɗa mata in har miji ne yake ɗaga ƙafa matarsa ta shiga aljanna Jidda ki saka kanki cikin sahun matan aljanna, aljannar ma firdausi" Ƙwalla ce ta taru a idanunta kafin ta cika idanun sai kawainta gangaro saman kumatunta da sauri ya saka manyan yatsunsa ya goge hawayen don ba ya son ganin kukan Jidda.
 Muryarsa ce t bayyana cikin rauni ya ce
"Mai ya sa kike kuka Jidda? Wallahi ba na son zubar hawayenki" ,Ƙasa ta yi da idanunta don ta ga damuwa ƙarara a fuskarsa sannan idanunsa sun yi ja, tana ta tunanjn duk da ana cewa a farkon aure ana bada kulawa da nuna damuwa sai tafiya ta yi tafiya zama ya yi zama sannan zaman ya koma zaman haƙuri amma gaskiya a yadda Ibrahim yake nuna mata soyayya da kulawa bata jin har iya numfashin sa zai canja mata.

  Muryarta tana rawa ta ce

"Na ji kana min kalamai ne wanda suke nuna kamar kana mini ban kwana ne tamkar dai kalamai ne masu alamta kana mini sallama sai dai ban san wace irin sallama ba ce" 

 Murmushi ya yi don kauda damuwar fuskarta wacce har ta sa ta zubar masa da hawayenta ya ce

"Kawai dai ina nuna miki girma da muhimmancin Jidda a rayuwar Ibrahim ne" Ɗagowa ta yi ta kalle shi ya gyaɗa mata kai alamar gaskata maganar.
 Idanunta ta juya ta ce

"Muhimmancinka a zuciyar Jidda tamkar alaƙar gangar jiki da numfashi ne, idan aka cire rai a jikin gangar jiki to gangar jiki ta zama gawa ba za ta amfanu ba sai cikin ƙasa wato kabari haka kake da girma a zuciyar Jidda" Yana kallonta shi ma ya ce

"Allah ya dawwamar da soyayya da ƙaunar junana har abada ina fatan na riga ki barin wannan duniyar domin idan kika fara tafiya Allah ya sani ni dai rayuwata za ta tagayyara ne"

 Jidda ta ce

"Ni ma hakan take" Hannuwansa ya ɗauke daga fuskarta ya mayar wuyanta tare da kai fuskarsa ya ɗora goshinsa a kan tana goshin hancinsa yana kan nata hancin ya ce

"Tare za mu rayu kuma tare za mu mutu, don sanarwar mutuwar ɗayanmu shi zai sa zuciyar ɗayar ta buga shi ma a take ya bi ɗan uwansa sai a sakamu a kabari ɗaya" Su duka suka ƙyalƙyale da dariya don wannan ne buri da fatansu kar ɗaya ya mutu ya bar ɗaya baka jin komai a ɗakin sai sautin dariyar su sannan ya koma ya zauna.

 Plate ɗin ta tura masa gabansa ya ɗauki cokalin yana gyara zamansa, gutsiro tuwon ya yi a cokalin ya ya saka miya tare d ambaton


"Bismillah" Nufar bakinsa ya yi da tuwon sai dai ƙaran wayarsa ya katse masa Jidda da wayar take kusa da ita ta furta

"Mummy ce take kira" Ta faɗa tana ɗakko wayar ta miƙa masa. Da hannun hagu ya karɓi wayar hannunsa na dama yana riƙe da tuwon a cokalin, ya danna ok tarw da kai wayar kunnensa.

  Kukan Mummy ne ya saka ya saki cokalin hannunsa tare da tashi tsaye yana faɗin
 
 "Mummy lafiya?" Jidda ma tsaye ta tashi gabanta yana faɗuwa ganin hankalinsa ya tashi...
     

     *Na muku promo na kayan maganin mata a zo a mini ciniki* 💃💃💃💃💃

*🎉 PROMO NA ƘARSHEN SHEKARA GA MATA! 🎉*  
*Ki bar tsohon shekara da matsala, ki shiga sabuwa da gyara!*
  
  Mun yi sabbin kaya don nuna soyayya da kulawa ga wanda suke son mallakar ɗaya daga cikin waɗannn abubuwan ko kuma duka.

*Ga kayanmu masu inganci da kike bukata:*

1️⃣ *Maganin Matsi Gam-Gam*  Don matsi 1500 maimakon 2500 
2️⃣ *Maganin Sanyi*  Yana kawar da dukkan nau’in infection da wari, ƙaiƙayi, ƙuraje rikicewar al,ada 2500 maimakon 4k.
3️⃣ *Sabaya 3 in 1* Gyara breast, hips sannan tana gyara jiki 5k maimakon 7k. 
4️⃣ *Maganin Gyaran Breast*  Yana ciko da breast, ga masu shirin yin yaye da kuma wanda breast nasu yake buƙatar gyara 3k maimakon 4500.
5️⃣ *Daka* Tushen ni’ima 1500 maimakon 2500.

🎁 PROMO NA MUSAMMA
Ranar ƙarshe 31 ga Disamba, 2025 

Ki gyara jikinki, ki faranta ran mijinki, ki shiga sabuwar shekara da armashi.


***