ABUNDA KE 'BOYE...

32

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE💫
Arewabook@surayyahms.

⏯️3️⃣2️⃣

Ayaanah ta ji zuciyarta ta tsaya cak lokacin da Mujahīd ya furta come fast din..sai Kafin ta ce komai, Kulthum ta kama hannunta cikin murna, Ammi karama kuma na murmushi, hanklin Ayaanah da zuciyarta gabaki daya baya jikinta duk murna da jin dadin sakamakon nan da akayi kalmar da ta tsaya mata a kunne guda ce “First… or nothing wanda ta san batakai ba,Sharadi ne, kuma ka’idarsa ce.

satar kallonsa takey har ya karaso ciki Kamar kullum, shigowarsa na ɗauke da nutsuwa da kamiya babu hayaniya, qamshin turarensa me tsada atake take ya mamaye wajen da sanyin dadinsa.

idonta na kallon kasa ayayinda kulthum ke rike da hannunta A hankali sukace mai "sannu da shigowa yaa."kallo daya yay musu ya amsa da kai snn ya wuce dakinsa, asulale suka bi bayan mujaheed kai tsaye suka wuce sashen anty safeera wanda bata saka komi aranta face harsaida suka isa..

mujaheed dake shirin wucewa dakin anty safeera yace "kuje falonsa a sama ki sameshi, kulthum zata raka ki..cikin sanyn nitsuwa ayaanah tace "toh" kulthum ta rakatan kuwa har sama cikin karamin falonsa da sallama me sanyi suka bude wata shirgegen green labulen ayaanah tay maza ta ɓoye fuskarta ata bayan kulthum jin yadda uncl moh ya kira sunanta da "ayaanah Dear" da wani irin fara'a tun kan su karaso..

suna gabatowa ta lura da akwai wani baƙon abu a tare da shi wanda box ne madaidaici an nannade shi da ribbon mai launin ruwan toka.
Baiwani tsaya ba bai kuma kalli kowa sosai ba sai Ayaanah.

tana dan dago kai Idanuwansu suka haɗu dajuna na ɗan daƙiƙa kaɗan, ganin tana jin nauyinsa da kunyarsa yasa ya ɗan kauda kai yana murmushi tamkar nawanda yake jin mugun tausayinta tareda jin daɗi alokaci ɗaya.

Har zata zauna kasa tafara gaishesa yace "aa karki zauna kasa zauna anan mana dear .ya mata nuni da soft chair da ke kurkusa danashi, respcfully ta zauna kanta na kasa ahnkli tace uncle ga ni nan naji kace na zo,kulthum ta matsa gefe, yana mai dan murmushi ya turo box din gaban ayaana" Ki buɗe,” kawai ya faɗa. ta kalle shi da mamki sai taga kulthum tana dan noding mata kai, hannunta na rawa ta bude gift box din ahnkli taga wani hadadden fancy set ne na Art supplies  kmr colours, sketchbook, glitter pens da wani irin tsadadden Cute hair accessories da small girlish puzzle game aciki da wata nice hoodie dark red colour shima acikinn fancy kwalinsa.

..abunka da zucyar yaro tuni taji abun ya bala'in burgeta ta dago kai da sauri ta kalleshi taga yana murmushi ahnkli yace congratulations my dear result dinku ya fito ko? ahnkli tace eh amma...cikin katseta yace ai ni ban damu da nasara ajikin takarda ba, dake kawai na damu dan haka Ki kula da kanki snn ki ƙara dagewa kifi haka..ahnkli yace "kina da daraja fiye da wannan my dear.

shiru tay cikin rasa sanin me xatace mai dan ji tay kamar maganan nasa sun mata nauyi sosai, can ta dago da ladabi da jin nauyinsa a muryanta tace uncle nagode sosai Allah ya saka da alheri,in sha Allah zany kkri sosai nan gaba

yana murmushi...yace"nine da godiya..ya kalle yarsa dake tsaye yace nd you too baby kin yi kkri ko, i neva daubted you ure the best amma wnn karon gift na ayaanah ne ita kadai. da murmushin jin dadin kalamansa kulthum tace thank you soo much baba ai tay kkri mid term taje fa. ,yace yes she tried baby, dan shiru ne ya ratsa wajen after a while kafin nan ya sallamesu..

duka suka fito suna murna dakin kulthum suka nufa suka zauna akan gado suka hau bubbude gifts din for a while harta mance fargaban ibaad dake damun kwakwalrta suka kira sultana a waya sunata surutu kowa yay ma ayaana murna sukasa taji cewa ai bakaramin kkri tay ba haka ta rarraba musu wasu abubuwa daga ciki amma tace sai ta nuna ma ammi kafin ta kawo musu kowa tabashi, kulthum tana ta murna dan dama jan rigar sanyin ne yafi tsole mata ido kuma shi ayaana ta bata kyauta,.

harsaida suka gama kallon duka gifts din duka snn ta tarkatasu duka ta dawo dashi sashen ammi karama. xuwa tay ta samu ammi na zaune a falo ita daya da tulin murnan ta tazo da box din tace "Ammi..Ammi kigani uncle ne ya bani yace wai nay kkri...da fara'a ammi tace masha Allah ahh uncle dinkun nan ya kyauta mugani, da murna ta mika mata, ammi ta bude ta gaggani tace masha Allah, ayaana u tried, in sha Allah anjima zan miki abu me dadi kici ina fata kuma next time Allah yasa ki fi haka kkri, dan kwanciya tay ajikin ammin da murmushi me yawa tace Ameen ammi nagode in sha Allah zanzo first" daga nan ammi tajata suka je wajen hajya mairo dake kan shiri gobe jumaa zata kwana agidan bappa zaidu ana nuna mata result itama tay murna harsaida tasa ayaana kuka tana ce mata ai da tudu kike da ba haka ba..kinyi kkri sosai ayaana am, waye ma zaiyi tunanin zaki rayu batare da yar uwarki da mahaifyarki ba
..haka tasaka ayana tafara hawaye dakyr ammi karama ta rarrasheta, ana daf za'a kira magrib suka rakata kofa drivern bappa zaidu yazo ya dauketa ta wuce can gidan su ammi babba.

dawowarsu ciki bada jimawa ba tazo ta dauki rigar sanyin takai ma kulthum har dakinta acan tay sallahn magrib da isha suka sha nutella da cookie suna ta hira can kafin tafara tunanin gamuwarta da ibaad sai taji atake komi ya tsaya mata cak

mikewa tay tace ma kulthum zata tafi kawai sai gobe, agurguje ta sauka cikin sauri ta dawo sashensu dan karya kasance bayan isha zai tafi gida...

gabanta na wani irin faduwa ta shigo jin babu motsin kowa a sashen yasa fargaban ta ya karu tana kuwa lekowa ta kofarsa ta tsaya cak jin kamar an danna mata remote, ganin safiya tay a kasa a kofarsa ta waje tanakan kneeling tsabar tagaji hannun sai reto yakey a sama tanata matse hawaye

da saurin fargaba ta juya zata gudu taje wajen ammi karama
tana juyawa kuwa taji sautin muryansa frm no where...a adake yace"kee, ina zaki je.., a kangare ta juyo jikinta na rawa ganin fuskrsa ne kawai ya leko

suna hade ido yace" what are u doing here"..bakin ta na rawa rawa tace dama..dama..nazo
ince...ince..."cikin katseta da tsaki yace "just come in"..Da sauri ta gyada kai ta karaso da tsananin fargaba ta bude kofarsa a karo na farko dataga saman table dinsa a wargaje
ya aje katon white A4 ppers yana drawing wasu abubuwa ajiki

jikinta na rawa rawa ta taho dan tasan na biyu safiya tazo, ahnkli tabi ta tsare sa da ido baiko kalleta ba sai har da ya aje pencil din snn suka hade ido yace "what? cikin hadiyar yawu ta rusuna kadan da sanyin murya tace "Dama kulthum ne taxo dazu tace min wai result dinmu ya fito..yace "and so? kmr zatayi kuka tace "shine nazo na gaya maka" yace okay...did u come first?.
maqudan hawayen datake dannewa ya sauka a raunace tace "a'a..i came fourth"yace "hmm 4th, shine akace kizo kimin kuka? xatay mgnan cikin katseta yace.. naji.. naji.."uve tried. but not enuf to receive a congratulation from me

..adan shagwabe tace but i will try hard next time i promise.

girarsa na sama adage yace karma kiymin alkwarin da bazaki iya dauka ba i told u, u were not dat smart saidai a can kauyenku , u came mid term nikuma i came 2 weeks to exams in my schll but i came first, kije ammi zata nuna miki ai zaki gani..kinzo kin same wanda suka fiki ilimi ko? hmmm uve a long way to go yarinya...hawaye na kan zuba a idonta cikin turomai baki tace"i will try next time... yace okay, then dont come to my room nd cry again untill u come first i dnt walk with not sooo smart ppl.

duk da serious face din dayasa har ranta she knw he is just teasing her...saidai sosai mgn nasa yasaka takarajin dolene ma ta dage ta zo na daya kodan ta kureshi...

shirun datay tana kan raya hakan aranta yasa ya juyo suna hade ido yace "inkuka kikazo yi anan ki tashi ki tafi kiban waje...dama uban  waye yaje miki kije kizo na hudun

mikewa tay jiki a sanyaye taxo daf dashi da wani irin sihirtacn narkakken murya tace toh kay hqri mana yaaya..ainace zan gyara. 

yace 'naji"..ya dauki hankynsa ya bata yace "share hawayenki sai ki tayani tattara wannn papers din saiki tafi .

hakan dayafada yasa taji zuciyarta yay sanyi sosai, dan tagama tsammnin tsawa da hukunci me tsauri zai dauka akanta  sai taga ba haka ba, duk gidan ma shine kawai yasaka taji kmr she is deeply challenged to do better next time sosai tasa aranta zatay kkri nan gaba. tana gama share hawaye da hankyn taji gabaki daya ta dawo tana qamshi irin nasa.

cikin sanyin nutsuwa tafara tayashi tattara drawing dinsan kallonta yakeyi amma bazaka taba sanin kallonta yake ba, her cute eye balls were fixed on his bold italic fine hand writing dinsa wanda da alama ya dauke mata hankalinta sosai...

har saida suka gama snn ta daga ido suka kalle juna sai kuma taji bakinta yay mata nauyi tana son tagaya masa abunda uncle moh ya bata amma tsoron me zaice mata yasa ta kasa iya bude baki. har ya dauke idonsa akanta ya tattara jakarsa yazauna ya saka takalminsa ya gyara room din sharply ya kamo hannunta suka fice atare..

suna bude kofa safiya dake kneeling ta dinga satar kallonsu baki bude dan tagama daukawa yau zaiy ma ayaana dukan tsiya,sai taga har wani kama hannunta yay suka fito atare, wani gulluton baqin ciki taji ya rike mata wuya, ita fa na biyu taci akasata kneeling din nan bayan uban masifa da zungurin data sha. ko kallonta baiy ba kuwa suka wuce ta da ayaanan, suna kaiwa falon ammi ya sake mata hannu ahnkli yace "go to bed" ni zanje gida, hawaye taji na nemn cika mata ido sai ta shanye tace "okay..gud nite.. cikin kwayar idonta ya kalla yace "thanks" kafin ta dauke idonta anashi sukaji motsin ammi da sauri ta juya ta wuce daki har ammi ta karaso sukay bankwana da shi ya wuce ya tafi.....

tun bayan tafiyarsa harta koma dakinsun ta kwanta tunanin kalamnsa da fuskansa kawai takeyi jin wani birkitaccen shauqin yadda zuciyarta ya riƙeshi da muhimmaci wanda ita kanta bata san ya zata fassarashi ba batamasan meye takeji ba
...har tay bacci safiya bata shigo ba sai wajen around 11;30 na dare da ammi tazo ta sameta a tsugune dan tsabar tsoron ibaad datake ji har yanxu tanakan gyangydi wajen datake kneeling din bata tashi ba fitowar ammin ne yasa ta fatattaketa ta wuce daki taje ta kwanta

da tsaki ta shigo dakin dan tsabar haushin ayaanah datakeji haryau bata taɓa bari sun kwana kurkusa da juna ba kowa baccin sa yakeyi acan can edge din gado da safe ma suka tashi basuce ma junansu komi ba inba wani rikici ne ya hadasu ba. yau sosai tsanan datake mata yakara zafafa dan haryau batagama jin haushin yadda sultana take makalkale ma uwarta ba yet ayaana is just another pain in her ass, sai takeji kmar ma gara sultana, soyayyr uwarta kawai ta karbe mata, lamarin ayaana yafi ci mata rai cos it pains her alot to deeply feel in her heart that yaa ibaad yana bala'in fifita ayaana fiye da kowa, inba haka ba ranarfa ta musu laɓe taji duk sharudan daya saka mata akan karatu, amma yama za'ay ta karya sharadinsa na zuwa first snn ace bai dake ta ba harma ya wani kamo hnnunta su fito waje tare...wann abun sosai yayi ma safiya zafi har saida tay kukan baqin cikin ayaana kafin tay bcci.

bayan faruwar haka gidan bai kara zama lively ba sai ranar asabar tunda ayaana da kulthum da sultana suka hadu duniya yay dadi. gashi ranar ne aka kawo sabbin dinkuna na atamfofi da laces 20 pieces masu shegen kyau da tsada da ammi karama tay odersu wajen mum ramlat collection duka aka dinka ma ayaana

ranar asabar din tamkar ranar sallah haka taji aranta ganin yadda kawayenta suka mamayeta suna ta gwada sabbin kayanta a dakin ammi karama kowa yana mata murna suna dariya kmr sun mugun jimawa da sanin juna. she bacome so overwhelmed with joy da dan uban gatan da ammi karama ta nuna mata. wknd din yay ma su ayaana dadi, kowa yazo anci abinci anyi raha zainab arifah ne kadai haryau bata zago ba wanda hakan sosai ya fara sosa ma hjy mairo zuciya duk ta dauka ko akan ayaana ne zainab din tay fushi.

haka ta tursasa anty safeera ta kira mata ita awaya wanda dakyar ma ta dauka suka dan yi magana ta dinga ja mata aji amma ko ajikin ta tsohuwar nan tay ta bata haquri akan karta yanke zumuncin su sabida abunda ya faru tsakaninta da ayaana, bata kuwa wani bata kwakkwran amsa ba har suka gama wayar

monday nayi kowa ya shirya aka wuce schll wanda ya kasance sabuwar yanayi ga ayana dan da wani irin karfin gwiwa tafara wnn term din duba da har anyi aproaving admission inta within next four month zata samu sabuwar uniform na jss class itama. suna farawa ta dukufa tare da bada hanklinta kawayenta na schl din ma tafara baya baya dasu sai in ayi break su hadu da sultana kawai suci abinci.

satin gabaki daya was fun face saida sultana tabata labari cewa ai uncle moh yakama kulthum da hoodie data bata kuma ya mata fada sosai yace kar ya sake bawa ayaanan kyauta snn yagani ajikinsu..

bakaramin sanyin jiki hakan ya bawa ayanah  anar suna komawa da driver ko sashen ammi karama bata wuce ba ta nufi bangaren anty safeera

samu tay dukansu biyu suna zaune kulthum tanacin abinci da alama itama shigowartan kenan, tunda ayaana tay sallama ta gaishe da anty safeera duk sai ta rasa me zata gayawa kulthum, face saida kulthum din ta haura sama taje ta dauko mata red hoodie in da sakin fuska tace "dama innay wanka ne zanxo
nakawo miki rigarki kiy haqri baba na yace min kar ya sake baki abu na karba..muryan ayana kmr na wanda zatay kuka tace "kai kulthum amma ai kyauta na baki meyasa bakigaya masa haka ba dazu
hakama fa sultana ta dawo min da ribbons dina wai baku so, tana fadin haka hawayenta ya fara xuba a idonta.....cikin sakin murmushi anty safeera ta jawo hannunta tace "haba ayaana, karki dauki abun haka mana  meye na kuka, ai bawai sunki abunki bane nima fa ina bayan babansun this gift is specially for you...su ai anjima ana siya musu, bekamata su karbi naki ba shiyasa ma yace musu su dawo miki dashi...

jiki a sanyaye kulthum ta dafata, ganin ayaanan na hawaye sosai tace haba ayana na ai zan dinga sawa aro kinji! fadin hakan da kulthum tay yasa ayaana taji dama dama tace toh shikenan zan aje miki

shafa kanta anty safeera tay cikin lallashi tace "ure very kind my dear...yanxu kije ki cire uniform kici abincinki karki damu babu komi kinji? hawayenta ta share ahnkli tace toh anty sai anjima..ta gyada kai,suka bata red hoodie in ta karba..da kallo suka bita tana wucewa saiga mujaheed ya sauko ganin yadda sukay zugum da tausayin ayaana ya saka ya tambayesu what is going on, anty safeera ta hau gaya masa, kyabe baki yay baice komi ba cos if feels odd for him da babansu yafara behving haka, dan gaskyr shine ko su yayansa baiya saya musu kyauta..saidai dake suna zuwa first din kowani lkc yakan bada anty safeera kudi ta saya musu duk abunda suke so amma bai taba shida kansa yaje kasuwa ya siyo musu kyauta ba. da tausayi anty safeera tace musu ai ayana tamkr marainiya ce tunda babu uwa babu uba ynxu atare da  ita, tace hala shiyasa babansu yake son yamata abubuwa da zaisaka taji kamr ba a wareta agidan ba,..da wann furucintan yaranta duka suka kara fhimtar haka aka bari acewa tausayi ne da kuma taimako yasaka yncle moh yake ma ayaana abubuwa nadaban.


after few days komi ya dawo normal ata ko wani bangare, karatun ibaad yanamai kara zafafawa, har ya kaiga an fara rage musu hours da sukeyi a private club dinsun dan ya dinga samun cikakken nutsuwa. basu kara jin duriyar zainab arifah agidan ba har saida tacika wata daya har da sati snn ta shirya ta sako wata abaya me kyau na mutunci taxo gidan wkends daga ita sai driver, tun ahanya ta dinga kkrin kawo duka tunanin irin magnganun da suke yi da ruqayya insunje makaranta wanda  badan ruqayya tayta bata shawara yadda zatay ta dawo da mutuncinta agidan ba da kwata kwata bata san ya zatay ba.

mahaifyar ruqayyar yar siyasa ce babba,gata dai yar 14 going to 15yr amma tunanin manya ne da ita sosai tafi nala nesa bakusa ba dan nala banbamcinsu da zainab Arifah kawai dan gata ne da kuma albarkan daukaka da karfin power da sunan familyn al-mansur suke dauke dashi, al-mansur kusan suna ne dayake iya bude kowani irin kofar, snn ya durkusar da kowani irin sarki, hakama yan kasuwa da yan siyasa mahaifin zainab arifah yana da wani irin strong ties da international gvnt nd secret organisations saikaga mutum komin ikonsa da kudinsa ba son shiga harkansa bare ayi wasa dashi shiyasa golden dotersa zainab aarifah ta zama sananniya acikin makarntar wanda  haryau shugabannin ta da malamnan cikinta gani suke kmr babban alfarma prof zayyanu yay da ya kawo yarsa karatu dasu...


yau shigar mutunci tay kamr yadda ruqayya ta gindaya mata, sashen hajy mairo ta wuce direct ta samu kowa ya taru yaran ne kawai ba sa wajen kowa nata mamkin ganinta hjy mairo ta rungumeta tana murna ahh ahhh zainabu  lale marhaba kaga yarinyar kirki ashe ba xuciya da mu kikayi ba, murmushi kawai tay bata amsa ta ba ta wani narke ajikinta d shigar sakarci ta gaishe su da bappa zaidu da sauran matanen," su ammi babba sai shige shige suke mata duk dama ta balain basu mamaki da sukaji tace ai bada hakuri tazo ta bawa su ayaanah tace ai kawarta nala ce ta shirya komi ita babu ruwan ta aciki shiyasa ma zata basu hquri. falon ya cika da kace kacen mata kowa yana yabon ta anty safeera kuwa abun bedaina bata mamaki ba.

can dai suka nufi sashenta tasamu su kulthum suna zaune a regular spot dinsu a falo su da yayansu mujaheed  yasaka musu puzzle game duk wanda yaci zai bashi kudi ayanah ce kawai bata wajen taje debo musu ruwa marar sanyi

yaran suna ganinta suka harxuka zasu bar wajen anty safeera tace musu aa suzauna, a tsomare suka zauna suna watsa mata harar kasa kasa zainab arifah duk ta daure ta sharesu dan ruqayya ta gaya mata tadinga tuna cewa in bata daure tay hakan ba duk bazata samu kan ibaad ta sauki ba, nd ji take kmr zata iyayin komi inde ibaad zai yafe mata su dawo suna magana kmr dacan dan dakayr tay surviving kwana biyun nan data basanya shi a kwayar idonta ba

da wani irin makircitacn salo ta kalle su sultana tace" hi sisters..suka amsa ta ciki ciki, confidently da wani irin rigima tace "girls, abunda ya faru lets put it behind us tunda nazo nabaku hquri yau. by d way, it was all my frnds idea so i hope dai ya wuce...shiru suka mata jin yadda take kan laka komi akan kawarta basuce komi ba saiga nan ayaanah tana dawowa da goran ruwa
guda biyu a hannu

suna hade ido da zainab arifah din ta tsaya daga can gefe zainab din tafara mata wani irin murmushi kafin ta mata magana ayaana ta aje ruwan akan table agaban mujaheed da sauri ta doshi kofar waje ta kama hnyar sashen ammi karama da sauri duka suka bita da kallo...

anty safeera har ta budi baki  zata kwala mata kira akan ta dawo zainab arifah tace

"its okay, karki damu
anty safee..ai zanje sashen nasu.

ta kalle su sultana tace "so, guys are we cool ryt now? tun basu amsa ba anty safeera tace haba dont mind them they are cool, ai suma da lefinsu tunda kema ai elder sis dinsu suke rainaki..

cikin hade rai tace kulthum sultana oya kuma kubata haqri maganan nan ya wuce haka itace babba kuma taxo ta baku haqri ai sai kuyi hakuri...kusan atare suka ce "ya wuce anty zainab ..we are sorry too..dan karamin murmushi mujaheed yay yace good girls toh kusha hannu,abasu so suna qi haka ya saka duka suka sha hannu da zainab arifah kafin nan tabi anty safeera sama kowa na mamakinta, anty safee babu yadda bataso dan tasha cikin zainab Arifah ba amma tay kyam taki gaya mata komi

tace bata so ne kawai babanta yaji maganan na ya hanata zuwa cikin yan uwanta kuma nd she is bored na zama agida..she refuse to admit sabida ibaad ta dawo bada hqri amma sosai anty safeera ta ganeta.

nasiha ta mata akan ta rika kama kanta da shiga harkan yaran msnm ma ayanaah da kowa yake jin tausayin ta ana taimaka ma rayuwarta, anty safeera tay ta bawa zainab arifah labarin yadda ayaanah ta taso, har mutuwar sisternta inaya, da rabuwarta iyayenta da zuwanta nan birni da duk wani temakon da su ammi babba suke mata kai har kayan da aka siya mata da kudin da su ammi karama da bappa zaidu suke ɓatawa akan lafyarta da welfare inta da wanda ibaad yake kashewa akan karatun ta da komi sai data warware ma zainab a tunaninta wann bayanin is enuf to make zainab arifah sympathetic nd to understand the situation of ayaana agidan fully, danta dafa gane cewa yarinyace datake bukatar kulawa da taimako da gata sosai bawai haka kawai ake mata abubuwa ba..

saidai anty safee batay tsammanin a baibai zainab take jin labarin ayana datake batan ba all she hears is a story of a helpless, poor, sick village girl with broken parents dataxo cin arzikin ibaad dinta..
dan dai bataga dalili da za'ace dan mahaifyr yarinya ta damka yarnya a hannun ibad shikenan kuma sai yazamo tamkar ubanta ba.

amemakon taji imani da tausayi sai taji matsancin kishi da haushi dan bakaramin irritating inta labarin ayaanahn yay ba..

har anty safeera tagama mata bayanin kom batace uffan ba sai ayyah, eyyyah, so sad..so sad... ko nuna wani alaman wani abu aranta batay ba har suka gama maganan ta sauko kasa direct ta wuce sashen ammi karama, lkcin ayanaa tana kitchen tare da maheer tana nuna masa inda coconut juice din ammi yake ibaad ne kawai a falo ya gama cin irin tsiren tsinken nan kenan sai gata nan ta shigo .

tunda ta yaye labulen ta kallesa taji duniyarta gabaki daya yay haske tamkar wanda dacan acikin duhu take ynxu ne dare ya waye, dan tabbas wann maqudan son datakeji akan ibaad bata tunanin natural ne, ji take kamar Allah ne dakansa ya diga mata kaunar ibaad aranta, tunda ta dora idanunta akansa taji duka jijyin xuciyarta sun tsaya cak

ganin irin dressing din dake jikinsa oh my god irin mayun american urban fitters dinn ne
simple shirt creame colour, da wata matured suade tailored trousers he look old money classic, very smart nd groomed, tsaftarsa duk yafi tafiya da ita.

mancewa tay ana sallama ta shigo da dan rawan jiki da murmushi me sanyi tace "hi,ganin ya daga ido da sauri alamn baisan da shigowartan ba yasa tace ohhh..my bad
"salam...wani irin kallo ya mata a dake yace "wasalam
and who are u looking for?
..dan kadan ta lumshe ido tace "no one". cikin dauke kai yace "okay..daga nan ya cigaba da abun da yaky baikara kulataba, har tagama tsayuwarta ta taho ta zauna a kusa dashi cikin sauke ajiyan zuciya ahnkli tace "ive come to apologise..i am sooo sorry for what i did to ur sisters ibaad. it was childish dan Allah kay hakuri, suma na basu hakuri..i just want u to give a scnd chance kaima fa kasan ba hali bane, wallh baran kara bari wata kawa ta zugani ba...pls lets put this behind us..

yana jinta har ta gama tay shiru baice komi ba har ya gama tauna naman dake bakinsa ya dauki ruwa yasha snn ya dau tissure ya goge bakinsa  da hannunsa he used almost 10 pieces of sheet na tissure, wajen ya dauke da wani irin shiru,shi be kalleta ba baikuma ce mata uffan ba, har tafara kokonton ko ma baiji me tace bane amma kuma taga kusan daf da chair dinsa take zaune

hawaye taji ya cika mata ido kirjinta yay nauyi ta kara juyowa ta kallesa taga kmr wayarsa ma yake shirin dauka muryanta na rawa na rawa tace are u listening to me at all?saida yaja kadan snn yace "yeah, apology ryt?toh, good for you!! now what? kallonsa take bata ko kiftawa dan duk duniya babu wanda yake bata mugun wahalar sha'ani kmr ibaad, the way yadda yake basar da ita yake ja mata aji da sauran su is deeply killing her, cos all her life ppl are made to worship, and serve her, rana daya kaje gidan su kaga yadda ake mata duk wasu hidiman rayuwanta acikin tsananin biyayya da nuna gata da sakalci har abada bazakay tsamanin zainab arifah zata taɓa budan baki tabawa wasu haquri dan kawai ta samu attention dinsa ba, bata dena kallonsa ba face saida taji hawayenta ya kusa zubowa ahnkli tace "are we cool now?? dede nan su ayaana suka fito tana daga idon ta kalle ayaana cikin dauke kai ta dafashi da wani irin shagwabben murya tace ibaad, i...missd you, nd i am sorry..pls say sumtin. mamaki ya cikashi kafin yace wani abu ta miƙe tana wani irin hawaye batace ma maheer komi ba ta kamo hannun ayaana da karfi ta jawota gabansa tana makalkale wuya tace "you see i wll apologise to her now..nide dan Allah ibaad kayi haquri wallh bazamu sake ba..

akaro na farko da ayaana tafara jin wani irin abu na rike mata zuciya zainab arifah ta fara kallonta tace hey little girl kiyi hquri kinji? i wll neva do that to u again kingama  ai agaban quardian inki na fada
toh ki mance da komi kinji

kafin ayaanah tafara sakin hawayenta yace musu ya isa haka..just let her go..anji ..ni wnn surutun na damu na. ta ki sake hannun ayaana, da tsaki ya sa hannunsa ya raba yace ma ayaana "leave. da sauri ta wuce ciki ta wuce dakinsu bata kara lekowa ba, itama znab din zatamai magana cikin daga mata hannu yace 'its okay..just leave. thanks! cikin lumshe ido da budewa ta mike ta dauki jakrta ta fita da fushi..

maheer ya girgiza kai ya karaso har saida ya zauna snn yace"..yarinyar nan fa dagaske ne take sonka..

runtse idonsa yay alaman baison jin wann maganan
ahnkli yace "maheer kaina yanamin ciwo wallh..virus inda ta samin a brain ina ma kabarni dasu is enuf

maheer yana murmushi yace hmm wata rana zakace na fada maka dan abunda zaisa zainab tazo ta bada haquri ai babban abu ne.

ibaad yace ohonta, kaga ni bawai na gama yarda da ita bane... i knw she is upto sumting kawai dai abarsa ahaka but will defnatly keep my eyes on her...

dariya maheer yay baice komi ba har suka bar maganan ya wuce haka, jim kadan yamma yay, bappa zaidu yace sam yau magrib ma agida zasuyi dan haka kawai kowa ya fito su wuce. yay tsammnin ayaanah zata fito kmr kullum suyi bye amma sai yaga har sukabbar gidan tun bayan data shiga dakin bata kara fitowa ba.


Bayan faruwar haka bada jimawa sosai ba rayuwa ya dawo normal tun suna dar dar da zainab arifah har suka saki jiki suna respcting inta normal, babu wani hayaniya..tunda ta lura kmr intana gefen ibaad ayaana bata magana yasata tafara wasu sabbin over caring bhrvs akan ayaanan masu ban haushi.

tay tay ibaad ya budi baki yace mata itama zata iya kula mashi da ayaana amma ina haryau bai taba kulata akan suggestion din datake kawo masa akan rayuwar ayaana ba. dataga kmr ta hakan bazata samu shiga ba kawai ta fara matsawa akan islamiya sabida yanzu haka tasan bazatakai wani cikakken 2yrs a nigeria ba, dan she is sure a kasar waje zatay duk wani sauran karatun dake gabanta ryt frm degree uptil level of PHD. dan sungama shiryawa da babanta cewa she is going to become a business icon, with a grade one major professorshp ryt frm (fin.tech, msc inta kuma a enterprise risk management, phd in financial economics) duka kuma a columbia univesity na manhattan dake birnin new york zatayi, is her best top ivy leaque unversities na duniya datake mutuwar son taga ta kasance acikinsa all her academic life wanda in few months zata fara shirye shirye.

mai bawa babanta shawara yace tafara rubutu essays da exam na TOEFL dinta tana submitting tun yanxu sabida koda bata ci a farko ba ta samu daman sake rubutawa kafin ta gama scndry schl inta tunda tazo kurkusa.

da duk wann bayanin ta dinga damun ibaad da yawan kira da zuwa gidan akai akai har saida amminshi ta masa fada akan kawai ya amince mata tunda  dakanta take cewa zatay karatun addini yanzu. shide sharadin tan ne kwata kwata bai masa ba, cos he cant
take care of ayaana snn ya kula da wata agefe ga nashi, karatun.

dakyar ya shawo kan amminshi ta barshi yace ma zainab din zaina kawo wani malami har gidansu yana mata karatun atleast 3 times a week
wednes, thur nd sunday. jin yace har gidansu zaina kawo malamin yasa ta amince atleast she get to see him 3 times a week da wuri wuri ta amince taje ta gayawa babanta har wani falo na musmn aka shirya mata na karatun agidansu the following week batare da bata lokci ba ibaad ya kawo malam jameel har gidan prof ana biyansa 200k a month yana koyawa zainab arifah karatun islama agidan wanda duk iyayen ta sun dauka abun bazai taɓa daurewa ba sabida sun san yarsu da sakalci da tsabar kwyuwa, da abun mamaki kuwa sai gashi har anci wata uku da wani abu zainab arifah tana zama tay karatu muddin ibaad ne zai kawo malami, kai wasu abubuwan ma da iyayen basa iya saka ta sai ga shine kawai zai ce mata tay kuma sai suga tay.

wanda memakon hakan yasa sudinjajin dadi aransu sai yana cusa musu tsananin  baqin ciki da fargaba,hajy hamida kullum zargin su bappa zaidu sukeyi akan sun tsafe ibaad ne shiyasa yarsu ta haukace akansa dan yagama musu da yarsu da soyayya sai su kasheta suhau kan gadon ubanta, she belive son da zainab arifah take ma ibaad  ba ordinary ba ne kullum tana wajen malamai  tana bayarda bincike haryau kuma anace mata ba aga komi ba.

shikuma prof yafi bada himma akan kashe masa yarsa kawai ake so ayi dan antsanesa
daga familysa kullum yana saka ido, duk abunda ibaad yake yi kuma haryau bai gama aminta sosai dashi ba duk dama ibaad bai taɓa ko awasa ya tambaye abun hnnunsa
ko ya nemi taimakon sa ba. sumtimes sai yace girman kai ne, wani bin komi yace munafurcine.

ata fannin ayaana kuwa duk dama ta saka kanta akan karatunta sosai saidai abubuwan da ya soma canzawa tsaknin ibaad da zainab arifah kuma tanaji kullum hajiya mairo sai tay ta hiran abun a falo, tayi ta fadin maganganu, tana cewa aiko rokon ibaad zasuy ya aure zainab sabida rayuwarta ya gyaru, ita batamasan meye ake ji a soyayya bare aure amma sai taji gabaki  bata kaunar ana hada ibaad da zainab arifah musmn akan batun aure

most of the time she looks normal amma daga ta ga zainab arifa tana rawan kai tana bada labarin islamiyta da ibaad sai tanajin rashin nitsuwa, this week suka fara exams a schll kuma tay karatunta sosai amma most of them bata san metake yawn rubutawa ba, har suka gama aka basu hutu, kwata kwata 3 weeks holidays sukayi agida sakamakonsu ya fitovkowa yana tsammnin ayaana zata yi gaba tana kara dubawa taga
4th din ta sake zamowa ranar kuka ta dingai a daki safiya kuwa ta rinka mata dariya kai kamar zata tashi sama tsabar dariyar mugunta..

dakyar ayaana tazo ta gane cewa kmr yawan jin labarin zainab arifah da yaa ibaad da hajya take damunsu dashi kmr fa shine yafara dauke mata hankli. kowa yay mata jaje, still taga ibaad baice mata komi ba..koda ta kai masa result din yace mata bazai gani ba har sai ta ci first. uncle moh km ko ajikinsa haka ya kara jajibo mata gifts ya bata sabida jss class zata shiga. duk ta shiga damuwa...ranar tana zaune a falo tay tagumi mujaheed yazo, da kyar ya lallameta ta gaya masa subject din da duk bataci ba, yace mata babu damuwa da daddare inbata komi tanazuwa wajensa a falon zaina koya mata iya wanda suke bata wahalan tunda tana lessons. kamr da wasa ayaanah taji dadin wnn maganan ranar monday suna komawa schl aka mata promotion zuwa side din manya jss da new uniform, duk ranar da babu lesson ta kan zo  ta same mujaheed yana koya mata extra lesson wanda sosai yajanye mind inta daga zuwa wajen hajiya tana jiyo abubuwan dake dama mata tunani

the funy thing was she cant even explain it, kawai dai bata so taji ana cewa yayanta zai auri anty zainab arifah ne, she doenst knw why but it alwys felt intensed in her small hrt

rayuwa yafara canzawa sosai da taimakon mujaheed wnn karon ayaana tazo na biyu
shima bata wani ji dadi ba duk dama ibaad ya dauki sabon wayar iphone13 me kyau ya bata sabida kowa acikin yaran gidan daya ya shiga scndry ake basu waya sabida saukaka cmuncation da asigments dake ma ana mugun saka musu ido, ya bata wayar nan baiko saka lambarsa aciki ba su mujaheed da sauran yan gidan suka karba suka  sasska nasu aciki sai can daga baya ta dauki lambar gogan awayan amminsa tay saving, shikansa bai sani ba saidaya ga ammin sa ta turo masa tex da wayar, murnan ayaanah daya da harynxu islamiya haryau itace take zuwa na daya sabida tuno da addanta datake yawan yi intana karatun qur'ani cos karatun addini was the best part of inayah's life tana da memries dinsu na hakan sosai saiyana sata tana tunata duk sanda take koyan karatu. bokon datake mutuwarso ne kuma ynxu yafara bata tsoro sosai, dan saida tay term kamr uku kafin nan finally Allah ya bata ikon cin nasarar zuwa na daya, ranar kam bakaramin murna tay ba, gashi a tsakiyar sati ne ibaad baizo gidan ba
uncle moh da tuntuni yake boye kishinsa na ganin ibaad ne yafara saya mata waya bashi ba, yau anace mai ayaana tazo first baizo gidan ba saida yay oder wata tsaddyar apple detachble tablet me dan karan kyau da tsada it cost almost 1.4 million sabida limited edition ne.

agidan kusan babu wanda baisha mamakin wann kyautar ba, ayayinda yara still thinks is very normal, anty safeera kuwa atake tasoma jin kamar kalamansa akan ayaana wnn karon yafara mata nauyi..

cos he alwys say things
agabansu kamar irin “Ayanah ba ‘ordinary’ bace. ko yace maata wai kowanne abu da ya fito daga wajen ayana yana so ya zama abin da zan iya alfahari da shi....har ta fara tunanin ko zai amshi ayanan ne gabaki daya ahannun su ammi karama da bappa zaidu da ibaad shi ya zame mata tamkr uba sai kuma tarasa da wanne kalma zata saka magann ya zama daidai
ahaka dai hartazo ta share abun aranta


tun wednesday uncle moh ya bata wann girgicaccen kyautar she spend much time da mujaheed da kulthum suna koya mata yadda ake amfani dashi, tsabar kyan tablet din yasa the more suna using the more har hanklin kulthum ya fara dawowa kai taji kmr itama tanason a siya mata.

washe gari koda ta gaya ma uncle mohd itama ya siya mata irinna ayaanah da mamaki taga ya haura mata da fada sosai har yace mata wai tafara kishin yar uwarta ne kawai bawai ta rasa abun duniya agidan ba,

bai taɓa mata tsawa ba dan haka taje daki tay ta kuka wanda hakan still ya kara dagawa anty safeera hanklinta sosai.

babu yadda anty safeera batay wajen tuhumarsa dalilin yima kulthum wann uban tsawar ba sai yace sam sam lefinta ne ai kishi da ayaanan take so ta koya shikuma bayason wnn halin. dakyar ta lallemesu duka tacewa ko bai saya mata ita zata siya mata tukun nan maganann yazo ya kare batare da kowa yaji ba.

ranar friday bayan an dawo daga schl ayana tay wanka ta saka hadadden custard yellow atampa peplum nd strght skirt ne daya kama dirin jikinta tsaf tsaf, tsabar dikin ya  mata kyau haka yauma anty safeera ta musu light juma'a make up
suka zauna a falonta suna video da pictures

da yamma liss ta dawo sashen ammi karama unxpectldy ta same yaa maheer da wasu friend dinsa guda biyu sunzo

har kasa da ladabi ta gaishe su, tana Allah Allah ta tashi sabida tasan dolene da ibaad sukazo da batagansa anan ba tasan yana dakinsa, zucyr yarinta ya debata tay maza taje ta dauko result din taje room dinsa ta same yana waya, ta jira har ya gama snn ta gaishe shi ta miƙa masa ya gani she had all flat As yace
tay kkri, snn ta masa tex da duk abubuwan datakeso zai siya mata anjima da dare amma sai gobe in sunzo wknds zai kawo matasu.

wani dadi taji tana ta murmushi just as  she was planning to  tell him uncle moh ya siya mata expensive tablet wayarta ya fara ringing...ibaad ya kure ta da ido, tana ganin sunan dake jiki taji tay wani irin freezing dan har ga Allah batasan yaushe tasa wnn sunan ma altho banda hjy mairo da da ruthy, da sultana da yaa ibaad sauran kusan kowa shiyay saving nasa dakansa. tarasa waye  yasaka mata.."BIG DADDY"kuma da capital letter...hannunta taji ya fara mata nauyi tana shirin daukawa ibaad ya fixge wayar calmly ya kalle screen din ya kyabe baki bai jira ko scnds daya ba ya saka hands free lokcin ji tay kmr kirjinta zai fashe

muryan uncle mohd sukaji" hello, ayaanah dear. yaya kike. baima jira ta amsa ba yace
"karki manta i promised u an ice cream spree after those gifts bansan ko zaki tuna ba dear, so yanxu zan fita, amma bayan isha idan na dawo zamuje tare ko?yay murmushi, toh saiki gayawa amminki zamu fita anjima tare karsuzo suna nemanki.

ahnkli ayaanah ta sauke kanta kasa

uncle moh yaji shuru yafara hello hello, ibaad baice komi ba a hello na ukun ya katse wayar ya wani irin watsa mata mugayen kallo yanaji kamr zai hadiyeta cikin lunshe ido da budewa yace hmm..snn ya mata jefa da wayar ajikinta ransa a bace kusan dakyar ma ta cabe kafin ta dago tagansa yay sauri zai fita, da gudu ta tsaresa muryan ta na raw a rawa tace "yaa ibaad, pls wait...da wani irin bacin rai a fuskarsa ya juyo yace wait nd do "What??? numfashinta atake ya tsinke ta dan matsa baya da sanyin murya me cike da rauni tace "i dint save his number like this..

ransa a bace yace
...i dint ask u abt that.

shiru tay hawayenta masu tsananin zafi da tsoro me yawa suka fara zubowa kmr an kunnasu

dahar yay zuciya zai fita ya kara dawowa kanta ya tsaya yace "gifts? since when?? dakyar ta dago ta kalleshi tace "since..since ...tun ranar da aka fara bamu result ne fa ya bani wasu abubuwa..sai ranar, sai shekranjiya.. nd " i was about to tell you now...

nade hannunsa yay a kirji yace really okay, go on tell me...

wani irin rawa jikinta yafaray tsoro ya rike mata zuciya ahnkli ta share hawayenta kanta na kallon kasa tafara masa bayanin duk abunda uncle moh ya bata wanda bata gaya masa ba..

wani irin dan uban masifa yakeson yaga ya mata amma kukan datakey a mugun tsorace kuma araunace yasa bai iyayin masifar ba.

cikin hadiye tulin fushinsa a kirji yace "he bot u all those expnsive gifts kuma bai saya ma yaransa ba kuma kika karba? ke kadaice kika ci first agidan nan ko? kulthum is always coming first tunda take bata taba zuwa 2nd ko 4th ba meyasa bai bata tablet ba wato sai kece marar tarbiya ko zaki na karban abu anyhow ko toh ai yamiki kyau...give me your phone ryt now..

hawaye na kan sauka a idonta ta mika masa har tagama cire rai akai, ta dauka tafiya da abun sa zaiyi, duddubawa yay kirjinsa har yana bugawa da karfi dayaga baiga wani abu aciki ba ya shiga contact dinta ya ya canza sunan daga big dady, ya dawo mata dashi uncle muhammad. ya canza na mujaheed ba ya sa mata yaa mujaheed..

ya koma call logs dinta yaga daga sultana sai wata schl mate inta Aisha suke yawan waya, danna kan layin uncle moh yay ya saka a blocked. snn ya kashe wayar me gabaki daya da tsananin fushin da baisan yana dashi ba ya kalleta yace"...no calls today,..kije ynxun nan kiyi sallah kiy bacci. bazan ce miki kidena karban wayann abubwn awajensa ba aikinsan babu kyaune shiyasa kika ki gayamin tun farko but since ure hiding it ,continue. yana gama furta hakan ya damka mata wayar ahannunta ya fita cikin sauri..

#
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025