Kamar da wasa pg 3
by @mrsomar
KAMAR DA WASA 💘
Fatima Isah
(Mrs. Umar)
Page 3
Muryar ta na rawa hawaye na bin fuskarta ta shiga cewa.
"Alhaji Jamilah babu ita ta mutu Dadansu munyi rash.."
Salati duka falon ya ɗauka mafi yawanci sun girgiza da wannan mutuwa wanda ta kasance tamkar almara, abu kamar wasa. Ƙaramar magana ta zama babba.
Ubbah ne ya yi jarumta, ya yi kundun bala ya fice da saurin ya isa jikin ambulance É—in, yana rike S. Y. Shatima dake layi, kamar zai faÉ—i.
"Ya Salam, yi a hankali,kada ka faÉ—i!"
Sai da aka zaunar da shi cikin gaggawa, kodayake zuciyarsa na tsananin zafi yana jin zuciyar sa tana bugawa da sauri. Kowanni motsi yana sa jikinsa yin nauyi. Kamar lokacin duk duniya ta tsaya, amma wani abu mai girma ya faru cikin zuciyar sa.
"A'a, Jamilah! Wannan ba zai zama karshenmu ba..."
Yana cewa a cikin zuciyarsa, yana ƙoƙarin ƙarfafa kansa. Saboda wannan, zuciyarsa ta yi tsalle kamar tana ƙoƙarin jure wannan rashin mai tsanani. Amma idanun sa sun buɗe. A cikin mummunan yanayi da ke tattare da shi.
Har aka shiga da gawar Jamilah cikin parlour Dada ba tare daya sani ba sam baya cikin natsuwa yana dab da rasa duk wani kwarin gwiwa nashi.
Kafin ace maka me duka falon ya cika da jama'a gidan daya kasance shashe hudu ne a ciki. Na mahaifiyar sa sai na aunty Amarya matar ubansa sai na Yapendo kakarsu kenan sai na Uncle Musa kanin mahaifinsu sai nashi daya kasance cikin shashen da Dada take yake ciki duk lokacin da suka zo hutu nan suke sauka.
Sai da aka giceta kafi masu kiran waya suka cigaba da kiran waya kafin ace maka me labari har ya yaɗu kafaffen sada zumunta matar "brig.gen Shamsuddeen Yusuf Shattima. Ɗa a wajen Yusuf Adamu Shattima mai Company aminci Nigeria limited. Saboda 'yan Yola su samu zana'ida yasa aka barta sai bayan la'asar duk da S Y Shattima bai so haka ba amma haka Ubbah da Uncle Musa suka fi ƙarfin sa. Da yake lokacin a wannan zamanin ba wani wuya ne dashi ba karfe hudu da minti 5 aka fita da ita aka yi mata sallah dama abinka da jirgi karfe 3 yan Yola rabi da kwata sun iso. S Y Shattima shi da kansa ya yiwa matarsa wanka tare da mata sutura.
Tun bayan kai Jamilah gidanta na gaskiya da suka dawo S Y Shattima ya nufo cikin gida ganin haka yasa Ubbah biyo shi suka yada zango a parlour Dada na sama wanda suke zaune da Ammie sai Naana suna jimamin wannan lamari.
Kan sofa ya kai zaune tare da dafa kanshi ya yi shiru yana nazari.
Ya ɗauki wasu yan mintina kafin S.Y. Shattima ya sauki numfashi mai ƙarfi, yana kallon fuskar kowa a cikin falon. Yana jin nauyin zuciyarsa yana ƙara taruwa, amma bai nuna alamar cewa yana jin rauni ba. A hankali, ya daga kai yana kallon Dada, Ubbah, Naana, da Ammie.
"Na gode da goyon bayanku,"
ya fara magana cikin muryar da take cike da rauni.
"Amma akwai wani abu da nake ji a zuciyata. Jamilah tana da hakuri sosai, kuma ba zan bari wannan tafiyar tata ta tafi ba tare da sanin gaskiyar abin da ya faru ba."
Dada ta sanya hannunta a kan idonta taÉ—an shafa kaÉ—an, tana kallonshi da ido mai cike da tausayi. "Modibbo(haka Dada take kiransa saboda sunan É—an fari) ka fahimci cewa wani abu sai an danne zuciya, A wada munyal,a anda Allah 6uri amin yidugo mo hanko hosi hunde mako. Nasan kai mai hakuri ne ka qara a kan wanda kake"
"Humm ninnon Dada amma jonta kam mi jodata mi lara be mema am debbo be bikkon. Saboda ido dana saka a duk wani lamarina shi yasa ake min abin har yakai zuciyata matakin karshe nake ji bazan iya saka ido ina kallo ba"
Ubba ya gyara zamansa a cikin kujerarsa, yana kallon É—an nasa da kyau.
"Ta viyu ninnon a wada doa tan ankam,Allah hoinu . Zan iya fahimtar yanayin da kake ciki, amma za mu bukaci shawarwari,za mu tafi tare da yin bincike mai zurfi."
Ammie na zaune a gefe, tana jinjina kai.
"Hamma Sam akwai wani abu mai muhimmanci da yakamata mu fahimta a wannan lokacin. Yaran nan suna buƙatar kulawar ka. Kada ka bari su rasa jagoranci, saboda sun san soyayya da kulawar da kake ba su."
Naana ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta miƙe tsaye daga kujerar. "Ni dai ina cewa, ya kamata mu haɗa hannu, mu bincika abin da ya faru, kuma mu tabbatar da cewa Jamilah ta sami kyakkyawar makoma a cikin zuciyarmu."
S.Y. Shattima ya kalli dukkan su.
"Na gode da kulawarku, amma har yanzu ban ji cewa na fahimci komai ba. Ina jin cewa akwai wani babban abu da ke faruwa a cikin wannan lamari, kuma ina son sanin gaskiya. Na san cewa yarana suna buƙatata yanzu fiye da kowanne lokaci."
Dada ta sauke numfashi, tana jin tsoron yadda zuciyar É—anta ke tafarfasa.
"Modibbo ka yarda da ni, akwai abubuwa da ba za a iya gane su ba. Amma tare da goyon bayan juna, za mu iya magance kowanne irin matsala."
S.Y. Shattima ya lumshe ido yana jin kamar yana ɗaukar nauyi na dukkan al'amarin. A cikin zuciyarsa, yana fahimtar cewa wannan ba zai zama abin da zai shige ba, amma ya kasance babban al'amari da zai buƙaci kulawa sosai.
Cike da kwarin gwiwa Ubbah ya ce
"Za mu ci gaba da bincike,mun tabbatar da cewa wannan ba wani abu mai sauƙi ba ne.baza mu yi hanzari ba, amma zan duba kowane sashe na wannan lamarin."
Ammie sai yanzu ta magantu
. "Moddibo! (Kamar yanda yar uwarta ke kiranshi haka take kiramshi ita É—in uwace ga Jamilah da kuma Naana) ka yi hakuri, mu na tare da kai. Zamu taimaka maka wajen gano gaskiyar wannan abu."
S.Y. Shattima ya jinjina kai cikin rashin tabbas, yana jin wani ƙarfin hali a zuciyarsa.
Ganin S. Y. Shattima bai ga yaran sa ba yasa shi tashi ya nufi shashensa yana zuwa É—akin yaran ya nufa. Cikin sa'a kuwa ya samesu zaune cikin wani yanayi,a hankali ya kai zaune yana kallon su É—aya bayan É—aya.
Tashin hankali bai fiye yi wa yaran zafi irin na rashin uwa ba. Minal ta kasance ƙarama mai wayau, amma rashin Jamilah ya gigita tunaninta. Tana zaune gefen kujera, tana kallon fitilar da ke kan bango, zuciyarta na yawo tamkar tana nema.
Iman kuwa, 'yar shekara shida da 'yar watanni, ta ƙi cin abinci tun safe. Ko ruwa bata sha ba. Ta zura ido tana kallon ƙasa kamar tana karanta wani rubutu da duniya ta rubuta mata, wanda bata iya karantawa ba.
"Sister Minal,"
ta furta a hankali,
"Wai ni... Miemie ta koma ina ne?"
Iman ta girgiza kai, muryarta na rawa.
"Sun ce miemie ta mutu.. amma ni zuciyata ta kasa aminta"
Sai ta juyo ta kalli mahaifinta da ke gefe yana kallonsu, hawaye a idanuwansa. Fuskar S. Y. Shattima cike take da wata irin sanyin rai da tausayin da ya kai ga durƙushewa. A cikin duka abinda ya faru, halin da yaran ke ciki shi ne ke karawa zuciyarsa nauyi fiye da komai.
Ya nufi inda yaran suke, ya durƙusa har ƙasa, ya ce da Iman.
"Iman! ki tuna da abin da Miemie take faÉ—a? Ta ce ke jaruma ce, ko?"
Iman ta É—aga kai a hankali, hawaye na bin fuskarta.
"Eh... amma na manta."
Shattima ya matse bakin sa, yana kokarin boye kukansa. Ya É—ago Minal da hannunsa guda, ya zauna da su a cinyarsa.
"Ku saurara... mi huli Allah..miyidi Miemie Amma Allah hosi miemie dilli Allah yidi miemie"
Minal ta dafa kafadar mahaifinta tana kuka. Iman ta gyara zama a jikin sa, ta ce da karamin murya.
"Mi yidi Abie... mi yidi Miemie..."
Daga gefe, Dada na goge idonta da yatsunta, tana kallon su da tausayi. Ta ce a hankali:
"Yara da ƙaramin lokaci su ke buƙatar sabon karfi. Moddibo, ka zama hasken su. Wannan lokacin, ka fi zama uba da uwa a lokaci guda."
Shattima ya gyada kai. Cikin zuciyarsa, ya ɗauki alwashin ba zai sake barin yaran nan su ji rashin gata ba. Zai tsaya musu. Zai riƙe su Ko da suna cikin kuka, zai ƙarfafa su da ƙauna da gaskiya.
#SON ZUCIYA
#SOYAYYA
#MAKIRCI
#YAUDARA