33
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE💫.
arewabooks@surayyahms.
as usual, extra-ordinary beautiful nd hilarious comments nd hypes from different angles.thank you my kind readers❤️uncle moh loves u more soyayyar karfi dayaji..duk wanda yaji haushi munsani, dan bamu cemai dear ko mun siya masa ice cream bane toh babu yadda aka iya damu. #team uncle moh #big zaddy khaalidina feeha abadan🤣🤝.
⏯️3️⃣3️⃣
kallon kofar da ibaad ya rufen tadingayi tana hawaye masu sanyi daga tsaye, wani irin sanyi jiiknta yay duk sai taji karamin zuciyarta ya bala'in rikicewa a lkci guda, zama tay a bakin gadonsa hawaye na zuba a idonta, ta rasa meke mata dadi, tajima anan cikin dakinsan bata fita ba har saida taji alamar sunfita sallan isha kafin nan itama ta fito
ammi karama dake tattara falon tabi ta da kallo ganin irin sanyin da jikinta yay da kalan jan zuciya datakey sai batace mata komi ba dan tasan bazai wuce case ne tsakaninta da ibaad ba, ayaaana bata gane komi ba har taje room dinsu
tay alwala tazo tay sallahn magrib, nan inda tay sallan tazauna tana karatun qur'ani har akayi isha'i ta tashi tayi
Tana cikin sallah ta kara jin surutunsu a falo da alaman sun dawo yaa maheer da abokasan da yaa ibaad din suna cin abinci they are all gisting about football anata hayya hayya akan E football nd most of maheer's frend basu san wai ammi karama ba mamansa na asali bane dan all this time gani suke kamar ma duk duniya yafi sakewa a rayuwarsa da ita bai taba kai abokai gidansu can ba saboda yasan mahaifyrsa ammi babba ta bala'in tsanan ganin baqi.
ayaanah tana idar da sallanhta akan sallayan ta zauna tareda cigaba da nitsuwa tanamai rero karatun qur'ani haddanta take ta nanatawa dan ya zauna mata dakyau a kwkwalwa, ita dadi ma taji da suka kasance a falon basu tafi da wuri ba ita kanta saida ibaad yay mata fada tafara gane kamar abunda ya fadin gaskiya ne kawai it will only be better in zaina siya musu abu da yaransa atare amma ba yana wareta yana bata abubuwa masu shegen tsada ba.
daga falon kuwa irin wajajen 9:30pm abokan maheer har sun fara tunanin tafiya gida ibaad ya biyo ammi har cikin dakinta da maganan
duk dama ya nuna mata cewa baison wann abun gifts da outings da uncle moh yake son farayi sa ayaanah ammi bata wani bashi fuska akai sosai ba.
tace masa ya kwantar da hanklinsa bazata taɓa barin ayaana ta fita agidan da dare ba, but der is nothing wrong with gifts..kawai saidai in ace uncle moh din yana daurewa ya musu da yaransa tare, sabida ko ayaanan ma ai bazatana jin dadi ana wareta ba, amma in sukace uncle moh kwata kwata yadena bawa ayaana abu zai dawo musu babban case agidan harma agaban hajiya tunda yarinyan nan dai respnsibtyn gidan sun ne gabaki daya...
ganin kamar ibaad bai wani qamsu ba tafara masa fada tace batason ya jawo mata abun magana kawai yasaka ido akan ayaana amma kar yace zaihana wani agidan muamala da ita bare ma uncle moh ai kawunsa ne, yana da yaran da suka girme ayaana dan haka bazai cutar da ita saidai ayi masa gyara kawai..
bada son ransa ba yabar maganan, sun fito daga kitchen dn kenan saiga mujaheed ya shigo, ya gaishe da ammi da ladabi, snn suka gaisa da ibaad kai tsaye yace ammi ayaana fah? tace"ohh yanzu dai na leka dakinsu naga tana kan haddanta a daki amma bari na duba maka hala ta gama tay bacci naga goma saura..
yace okay, dama babanmu ne yace inbatay bacci ba tazo ynxu..wani irin dauke wuta ibaad yay atake yace "kaje kace masa tay bacci. its late!
mujaheed ya juya atake ya kallesa, ganin inda ya mugun hade rai sai baice komi yace "okay, ammi sai goben inta farka sai ki gaya mata wai her phone is still off ..da kai ta amsa masa yana barin wajen ta juyo da kallon tuhuma ta kalle ibaad tace meye hakane kam rayyan?ayaana is awake
meyasa zakace masa haka
hade ransa yay bai amsa ba sai can ahnkli snn yace amma ammi ai dare yayi, its almost 10, yakamata ma ai kisa musu light out mana pls ammi
....10ck sai karsu bar dakinsu suje koina they are still kids ynxu ne suke bukar bacci...
tace rayyan i know what ur problem is, kuma nace maka zan masa magana. but this isnt a boarding house bazaka hana yaran nan fa walwala ba, amma tunda kace light out ne aishikenan, amma bazan dai hanata zuwa sashen safeera akan wann maganan ba,..gobe kuma zan samu muhammad din, i will talk to him abt the gifts, dan naga kmr kai baka yarda da kowa bane ko?? shiru yay baice komi ba, muryanta kasa kasa tace" kasan ya riga yasaka aransa cewa kana da raini shiyasa jinin ku bai hadu sosai ba tun kana karami, ni wallah gaskiya banason wani hayaniya ya shiga tsakanin ka dashi akan ayaanah, i dont have energy for all this family feuds rayyan pls ka rufamin asiri..i promise u ayaana will be fine innaga wani abu da zai cutar da ita i wll even solve it myself. zai magana cikin dakatar dashi tace " ya isa haka babana muje kawai gobe in kazo wknds zakaji komi.
gyada mata kai yay a ladabce har suka shigo cikin sauran mutanen dake falon ammi duk tay sallama da abokan maheer within few minutes suka watse gidan ya dauka da wani irin shiru....
washe gari da safe ranar asabar ayaanah tana idar da sallah ta fito sanye da hijabin datay sallahn ajikinta ta wuce dakin ammi karama da sanyin ladabi ta tsuguna tace mata "ina kwana ammi" ammi dake zaune akan sallaya da mrmshi tace "lafiya kalau ayaana har antashi? how was ur night tace fine alhamdullh. "toh yanxu dai kije kiyi wanka jiya uncle dinku ya aiko a kiraki da dare ina dai ba wani barna kuka masa acan bako?ambaton hakan da ammi tay yasa ayaanah ta dago kai da mamaki tace"a'a..ban masa komi ba. sounding curious ahnkli ammi tace" jiya akace min kin kashe wayarki ne ma shiyasa bai sameki acan ba, ayaana, kifadamin gaskiya karkiji tsoron kowa kinga bana son dan yana baki kyauta yaje ya dawo miki wani abun tashin hankali da yan uwanki ko a gidan nan in akwai wani abu dake faruwa bansani ba ki gayamin kawai ynxu..
kan ayanaah na kallon kasa tace" Ammi babu komi, dama jiya ne kawai ya kira awaya kuma sai yake cewa wai na fito zai kaini wajen ice cream wai bayan ishai sai yaa ibaad yaji wayar sai yaji haushi ya kashe wayar gabaki daya..amma wallh ammi bani nace masa inason haka ba. nifa babu ruwana bance yana bani abu ba.
ammi karama ta dan yi shiru tace "its okay, nasan ban taba gaya muku ba amma once is 6:ockpm henceforth babu fita agidan nan. duk wani ice cream ko wani ciye ciye da zakuyi duk ayishi da rana banda dare 10pm kuma naga kowa acikin dakinsa, snn dik abunda ya baki ki tabbata kin gaya mana sabida kar wata rana azo wani matsala yataso akanki ace bamu sani ba kinaji na ko?
ahnkli tace eh inaji ammi
tace good toh kije kiyi wanka, bansan meyasa yake nemanki ba amma in kin gama sai kije ki gaishesu saikiji ki dawo maza ynxun nan.. tace toh. ammi karama ta sallemeta ta fita, tana komawa dakinsu wankan safiyar tay ta canza kaya tasaka riga da skirt da mini hijab ta wata danlop sleeper akafarta ta fito
kai tsaye ta wuce sashen anty safeera bata tare da tasaka komi aranta face fargaba da rudewar tunani
Har ta isa Allah Allah take taga koda mujaheed ne amma ina wajen gabaki daya is silent kamar babu mutane aciki, sai taji tsoro ya kamata bazata iya zuwa dakinsa ita daya ba, kai tsaye ta wuce zataje kofar kulthum tana kama handle tun bata bude ba taji anyi gyaran murya ata bayanta adan tsorace ta juyo caraf suka hade da uncle moh wani irin murmushi taga ya mata daga can nesa yace ayaana dear karaso nan mana..ai jiya na aika a kiramin ke aka ce mi kinyi bacci.
kamar wacce kwai ya fashe mata ajiki ta sake kofar kulthum din ta dawo ta wajensan tana tafiya ahankli ahankli kamar bazatyi ba harta karaso kuwa bai daga idanunsa akanta ba
yarinya datake jss 1 kam gani yake girmanta bazaiyi wuya ba within few years to come ne kawai zata zama ready sexually, physically nd mentally, sann ya aureta ta zamo nashi, bama sai takai 18 ba tunda hatta ammii karama ma yasani sarai batakai 18 din da ake fada ba aka aurota agidan nan so ba akansa za'a fara auren karamar yarinya agidan ba.
daf da wajen hadadden coridorn sashensa inda yake tsayen ta tsuguna cikin ladabi da fargaba tace ina kwana uncle.. da wani irin murya yace haba tashi mana dear karki rusuna min haka, wayarki ya baci ne ko? jiya na kira ki sai naji kamar bakiji na har na dawo gidan kuma ina kira naji akashe..
girgiza masa kanta tay ahnkli tace "a'a bai baci ba, ina karatu ne,.. da safe ne ammi tace min wai ya mujaheed yazo yace kana kirana shine nazo... ganin yadda tay saurin saukaka mgnn nervously yasa yaji arnsa kmr ko tsoronsa takeji yasa bataso ta sake jiki dashi
..cikin kame kansa yace okay, dama ice cream dinki ne nakawo miki toh muje dakina nabaki yana fridge saiki karba ki koma kije kiyi baccin ki dan naga kamr bacin bai sake ki ba..
batace masa komi ba kanta na kallon kasa yana wucewa gaba ta tsaya cak daga bakin kofar dakin har ya shiga ciki ciki ya dauko katon ice cream bags guda uku manya daga cikin fridge dinsa daga waje ya daga ido ya kalleta yace"dont stand dere my dear karaso ciki mana ki karbi abunki.
..tunkafin ta amsa ya wani taho da sauri yajawo hannunta ciki gani datay yana kkrin kmr zai mannata da jikinsa danya shafata yasa tay saurin fixge jikintan anashi muryan ta na rawa rawa sosai tace" uhmm uncle ammi tace na dawo yanxun nan, zan iya sha dani da su kulthum dasu safiya ko
ganin kmr she is starting to get scared of him sai yay maza ya dawo cikin senses dinsa cikin dedeta nitsuwarsa da normal voice nasa yace "toh toh badamuwa kije to kusha tare mana ai naki ne nidai nacika miki alkwari ne kurum..
kanta na kallon kasa tace nagode uncle..
kansa adan daure da yanayin ta yace its okay dear dama shikenan u can leave.. yana gama furta hakan ta gyada masa kai da mugun sauri ta fice a dakin tanamai jin tsananin fargaba.
shidakansa kuma daya zauna abakin gadonsa ya sauke ajiyan zuciya yafarajin kmr abunda yakeyin is bit off nd shameful. duk dama babban abokinsa alhaj Amir ne yake yawan bashi wnn tabbataciyar shawarar na akan cewa ya dage akan ayanah, kar ya zuba ido yay shiru yace saita girma ne zai sako kai, tun yanxu ne da ayaanan bata dawayo zai jawota jikinsa sosai, ya dinga bata gifts, snnan yana kyautata mata akai akai sabida kowani zuciya yana son me kyautata masa, snn ya dinga spending time da ita sosai yana dan janta da harmless physical touch, uwa uba yana spoiiling inta da ababen kwadayi sosai, Alhaj ameer ya tabbatar masa cewa inhar yayi hakan, tamkar yana trainer zuciyar ayaana ne da sonshi kuma ahaka ta girma, natural love ne zai ginu aranta akansa, snn koda wata matsala zai taso agaba da matarsa safeera by then sunyi shakuwa da ayaana da bazata taɓa iya rabuwa dashi ba.
shawarar sosai tay making sense amma sai gashi nan yafara aiwatar abun yana masa wani irin gashi kmr ayaana tafara jin tsoronsa.. doguwar tunani yayi akan haka kafin ya mike ya shiga wajen wanka.
dakin kulthum ayaana ta shiga ta sameta a nannade acikin bargo kanta namata ciwo da alaman period dinta ya fara sako kai, da mmki ta dago ta kalle ayaana ganin jikinta na rawa rawa har ta zauna kusa da ita suka gaisa tace "sis what happen meye wann kikazo dashi a leda...ayanaa ta tattaro nitsuwarta dakyar tace "abbanku ne ya siya mana abu dukanmu dani dake safiya shine kawai na kawo ki aje mana..ni kinga dama yaa ibaad yace min karna sha abu me sanyi da sasassfe sai kawai kusha abunku. mikewa kulthum tay tace toh mugani.. da sauri taga ayaana ta mika mata, ta karba ta bude tace wow..toh thanks, kinsan wani abu sis? mama na tace zata siya min irin tablet dinki gobe, cikin gwalo ido ayaana tace alhamdullh dama ji nake kamar in baki nawa kyauta
..suka fara dariya.."kinsan ai baba yahanako? kawai ki rike abunki..in nima mama ta saya min sai muna koya abu aciki..
ayanah ta gyada kai tana murna...hira kadan sukayi me sanyi sann ta kama hanyarta ta dawo sashen ammi karama batare da ice cream din ba, koda ammi ta tuhumeta batun kiran bata boye mata ta gaya mata komi dayace mata saidai bata san ya zata fadi abun a sigar da zaisaka ammi taga abun kamar yana damunta ba,...
...haka akay taron wknd din kowa ya hallara saidai sam hanklin ayana baiya jikinta saboda daure mata fuska dataga ibaad yay ranar sosai wanda yasa ta dadajin ta damu atake kuma tsoron karban abun hannun uncle moh din yafara kama zuciyarta, duk da ammi karama taxo ta samesa a mutunce ta tuhumesa aka batun ware sauran yaran da gifts, saidai dake ya raina age dinta yana ganin kamr ko shinan ya girmeta, dama can da irin rainin kanin mijin nan aransa kuma gani yake kmr ba asalin age dinta su hajy mairo suke fada a fili ba, kuma he is very very sure yama girmeta sai bai wani bata kwakwkarn amsa ba ya shanshantar yace ai shirmen yara ne dan haka akyalesa zaiyi duk abunda yay niyya ma ayaana
tun tadaga haka tasan ba fahimtar ta zai yi ba, sosai ta rike alkwari ma ibaad she make sure ta saka ido, duk sanda ya kira ayaana gefe sai ta kuma tambaye ayaana ya sukayi.
bai kuma fasa kawo abubuwa time to time yana bata ita daya ba, har yasa ayaana tafara fitowa fili ta nuna masa alaman bataso, ya zamana kullum kota kashe wayarta kota ki zuwa sashen nasu gabaki daya musmn in aikowa yay taje.
bayan faruwan hakan da kamar sati uku komi ya fara lafawa su ayana suka koma 2nd term insu na jss1 ibaad kuma yana kkrin shiga 2nd smtr na level two dinsa a medicine.
wann satin ne suka samo wani babban cigaba a gidan, inda da wasa da wasa mahaifin anty safeera dake matsayin tsohon ministe da sukaje wani confernce ya saka hannu awani takarda har aka budewa uncle mohammed wani babbn intl connection ya samu wata contract da wata construction firm na larabawa, ita kuma hajiy mairo mai tuwo babban shagonta ya samu state award na fastest growing traditional restaurant a kano haka akay taro yan kasuwa kala kala suka kawo investmnt akan zasu adada wajen ana so ajonashi ayi prof. catering school na koyarda abincin zamani dana gargajiya...
satin gabaki daya ayaana sai taji sakat sabida hanklin uncle moh ya koma ga shirye shiryensa na tafiya kasar dubai zaije yay kamr 1 month kafin ya dawo.ranar alhamis da safe wajajen karfe 10.00am saura ibaad ne kawai baije schl ranar ba sbd abubuwa da suka masa yawa, kuma hrga Allah yafi gane advanced private club lesson dinsu akan normal schl lectures dinsu ynxu sai gabaki daya yau ya dauki karamin hutu da zai harhada ppr works da assigment dinsa na club dan sunyi nisa sosai a field, ga vsiting doctors turawa wasu larabawan egypt din nan duk ana turowa suxo sumusu practicals da lectures on a short visit, school lectures dinsan gabaki daya kmr masa revision ne. past exams result dinsa was incredibly awesome shine wide margin topper a ajinsu sede abun baya darashi sam kuma haryau bai yi aboki ko abokiya a ajin ba, shide bazaka taɓa gane masa ba dan ko mahaifyrsa baiya son nuna mata result in yaci saidai suji ana yabon kkrin dansun a bakin professor ciroma dake abokin bappa zaidu ne.
ibaad will alwys keep his successes private nd his problems even more quieter, asalinsa baison yawan samun attention ko yabon kowa da kowa ko kadan kawai abunda ke gabansa yakeyi most time.
tun daya dawo daga sallan fajr yake kan calculations da su drawings da sauran lissafe lisafen chem. compounds acikin dakin sa. yana gamawa kenan ya shiga ya fito wayarsa ya fara kara bappa zaidu ya kirasa tareda umartansa kawai yay akan tunda yana nan yaje fmily house ya dauko ma hjya mairo me tuwo wani envelope a dakin ta yakai mata shago ynxun nan. tun da ya gama wayar daukar lokcinsa yay me kyau ya shirya kansa kamr wanda zaije wani waje mai muhimmaci.
he wore a complte set of gentle men set data masa mayen kyau, this clean white short-sleeve polo me aji da wata Light grey chinos, paired with Clean white sneakers and a simple brown leather wrist watch hade da Fresh haircut dinsa dat look brushed neatly. snn ya shafa hadadden turarensa na naxos. ya dauki wallet dinsa da wayarsa it took him 30min snn ya fita ya dauko baqar lexus din bappa zaidu dake parke a tsakiyar gidan ya taho family house dashi.
gidan was quiet yara duk sunje schll ammi karama taje aikinta ya rage anty safeera ne kawai ta aje komi nata danta taya mijinta shiryawa
da safe ne but they have this wonderful intimate sex kafin ta shiryasa tsaf ta rakosa har waje kagan shakuwa da irin soyayyarsu bakata taɓa tsammanin uncle moh zai daga ido ya kalle wata ya mace a duniyar nan ba.
suna fitowa gaban motarsa sai ga ibaad harya dauko file din a hannunsa zai wuce yana sauri anty safeera ta kwala masa kira ya dawo ta wajen sun ya gaishesu...
uncle moh dama ya jima yanaji aransa ibaad baida ladabi sosai atake ya fasa shiga nasa motar yace tunda ibaad fita zaiyi da babban mota kawai shi yakaisa aiport din ya saukesa. duk yadda ibaad yay dan ya doje haka yaki sam yace he cant drive nd make calls kawai suje ya bawa hajiy aikan ya kaisa aiport. ibaad ya hakura baice komi ba ya amshi jakarsan yasaka masa a booth har yaje ya zauna a driver seat uncle mohd bai gama tsotsar bakin matarsa ba duk dama yasan ibaad yana iya kallonsu ta madubin mota. saida ya gama duk iskancinsa da zaiyi sann ya zo ya bude motar ya wani hakimce a owners coner yana zama ya fara zabga kiraye kiraye yana hira da wasu aboknsa yana kyakywtawa da dariya kamr wani drivernsa ya daukosa har suka isa shagon hajy mairon ibaad baice masa komi ba,yay parking ya sauka yakai mata aika yana dawo wai sai a sann uncle moh ya sauka shima yaje, ibaad try his best not to react dan yasan uncle moh is alwys trying to provock him to anger, dan sam sam baya treating maheer haka wani bin ma kamr frnd yake daukar maheer amma shi sam jininsu bai gama haduwa ba.
after like 10 min of waiting ya dawo yana shiga motar ya cigaba da wayarsa banda tadin sirrikan aurensu dana yan matansu awaje babu abunda yakey da abokansa..
wht seem like a few minutes jouney bcome endless for ibaad sabida surutun banza da uncle moh yake yi a baya, 11:30am suka kawo aiport, haka yaki sam ya rike troly ko ya bayar a dauka mai a moving vehcle yace sam sai ibaad ya sauko ya bishi dashi ciki, suna tafiya ciki yanakan wayarsa kamar bazai gama ba. he is busy bragging na yadda zai kara samun kudi dat will make him do what ever the hell he want in his life. ibaad yay baya baya dashi yabarsa yay gaba shi yana tahowa daga karshe, tun suna cikin harabar arivals idonsa ya sauka akan wata dattijuwar mata wacce daga ganin shigarta kasa msulmace she is walking alone nd slow, da tsadadden hand woven gucci bag a hannunta bana kananan masu kudi ba,saidai abun da ya fara dauke masa hankali da yanayinta shine wannan shortness of breath din daya hango atattare da ita
she was heading for her luggage nd exit he tot to himself she will be fine tunda arival ne, sai ya dauke idonsa har suka iso inda uncle moh zai tsaya ahnkli ya aje masa bags dinsa yakama hanyarsa ya tafi baiko cemai sai anjima ba.
Da sauri ya shiga mota dan ya koma gida, dan da yamma can yana so yaje shi gym, maheer barely have time now sabida karatunsa yay zafi sosai. yana kama hanya dede gate din fita daga cikin aiport wata katuwar jeep ta tsare masa gabansa tana tuki ahankli ita bata matsa gefe ba kuma bata bashi space din wucewa har suka hau kan hanya yana horn amma mai motar bai bashi hanya ko ya matsa ba, tun yana iya dabara yana kkrin over taking har yaji ransa ya fara baci da matukin motar. sundau mintina suna tafiya a slow har saida suka danyi nisa kafin hanya yay fadi ya samu ya kara wuta ya wuco gaba caraf kuwa idonsa ya sauka akan wann matar da dazu ya gani, she was driving very very slowly nd shaky kamr wata me blurry vision can kuma yaga tafara breathing fast like she can’t catch air tadanyi Resting dayn hannunta akan chest dinta while trying to breathe,
kasa wuceta yay ya sauke windonsa yafara mata horn saida yay kamar sau biyar kafin yaga dakyar ta juyo ta kallesa yana shirin mata alaman ta tsaya yaga da sauri ta sauka akan shoulder ta tsaya da motar dake shirin kwacewa a hannunta a mugun girkice take nishi kmr wacce heart attack yke neman kamata atake.
agaggauce yay parking ya sauƙa ya iso gaban motar ya tsaya yafara kwankwasa mata windon yanacewa "excuse
me ma'am are u okay?...tana numfashi sama sama ta bude kofa suna hade ido tace dan samari ...pls.. help me," help me karna mutu na bar yaro na pls help me..kafin yace wani abu tafara kkrin dago wayarta zata bashi tana jan nmfashinta dakyar tana cewa" i will call my doctor..pls help me ta..lk ..to him.. kusan duk wani symptom na heart attack atake ya fara bayyana ajikinta all this cold sweat, visible Chest discomfort ga wani irin shortness of breath mai dauke da Chest pressure sai yaga kmr jaw dinta yana mata ciwo shima.
his insticnt was almost driving him crazy bai san sanda ya bude motar ba, yana budewa yay turning off ignition ya bar kofar motartan a bude, ya maida seat dinta baya, ya cire mata seat belt dan ta zama she is lying down flat godiyan Allah ma dayaga she is still uncoucious hannun ta na rawa tana mika mai wayar yafara magana da doctorn ta, docton yace masa maza maza kafin tafara loosing counsiouness ya kawota asibitinsu na rahama international private hospital yanxu he wll send emergncyy on the way too,.
ibaad yana daga wayar a kunne ya ga doc har ya turo location...ya koma car dinsa da sauri saurii ya kulle, snn ya dawo ya samu matar is still very much councious nd breathing, saidai the more tanayi the more yana raguwa the more suna bata lkci the more lamarin yana kara lalacewa baiyi wata wata ba ya shiga motar yafara janta yana tukin yana mata magana just to keep her awake ita kuma sai rokonsa take akan yay hqri ko sunje asbitin kar ya kyaleta har sai yaronta yazo, snn duk tsiya kar ya bari wani ya shiga inda aka kaita in ba mutumin sunan shi jamal ba, har suka karyo kwanan shiga gari bai gama gane nufinta ba, wanda tun basu karasa asibitin ba motar paramedics na asibitin suka tardasu a take atake aka dauketa aka kwantar da ita flat aka bata nitroglycerin bcos she is still very much coucious snn aka sa mata oxygen mask
within few minute suka iso rahma intenational hospital aka wuce ciki da ita aka fara bata taimakon gaggawa.
yana asibitin ya tura tex ma mujaheed ya masa kwatance inda spare key yake dan ya dauka yaje ya dauko masa car
daya bari a hanya dazu.
saida har yaga mujaheed ya amsa shi da okay snn yaji hanklinsa ya kwanta kamr yadda matar ta rokesa haka nan ya zauna for almost 2hrs har aka kira azhr ya samu wani security yay tipping insa snn ya ce masa kar yabar kowa ya shiga ciki inba wani me suna jamal ba.
after few minute ibaad ya idar da sallah ya dawo kenan ya hadu da securityn da ya bashi gadi awaje suna hade ido yace masa ai matar ta farka tana nemansa haryace mata yaje sallah so zai iya shiga ciki..
cikin sauke ajiyan zuciya tare da yin hamdala dan dama a dame yake ya koma gida ya doshi dakin.
tun a kofar yake jin sautin magangnu kmr ba ita daya bace aciki, saida ya dan kwankwasa kofar snn yay sallama kusan atare suka amsa shi ya shigo ciki cikin nitsuwa, inda atake suka hade ido da wani hadadden cute guy dat look handsome nd exctly brazillian sabida skin colour da dark red lips dinsa da wani irin baqin suma.
ya saka suit baki me dan karan tsada wanda a ido kawai dao bazaka ce kusan age mate na ibaad bane, sabida sense of responsiblty da maturity dake lullube a fuskar yaro...kallom juna sukayi na dakikan lkci kafin murmushin matan ya katsesu tace dan samari shigo mana ya ka tsaya daga kofa
ibaad baice komi ba ya karaso daf da ita yace "how ur feeling maam ya jiki...da hawaye a idonta tace nagode Allah "Alhamdullh, Allah ya maka albarka. nagode yaro na. you are a god sent you saved my life kumaka rike min alkwari.. what is your name? yace "Ibaad" ..tace "masha Allah ibaad, i am hajiya maryam moriki. mutane sun fi kiran da lady Diana. this is my only son jamal moriki.
atake jamal din ya mika ma ibaad hannu har ynxu jikin sa yana rawa rawa muryansa kamr nawanda zaiy kuka yace"..thanks men. thanks for saving my mother's life it means alot.. pls how can we repair you can ask for anything
...karamin scof ne ya kufce ma ibaad yace "no. pls..i just did what i tot is ryt.. Allah ya bata lafiya. gayen ya gyada kai with so much gratitude in his eyes yace "Ameen"..ibaad ya kalle matan da karamin murmushi yace can i call u lady?tay dariya kadan tace ye.. yace" okay lady, i think i will leave you two now..Allah ya baki lfya
card dinta ta ciro ta mika masa da hawaye a idonta tace "pls dont say no my dear..call me anytime aikoda baka buktr komi awajena zamu iya gaisawa bcos ure a very kind person.. bai musa mata ya karbi card in ya kalli jamal sukay sallama suka dinga masa godiya sosai.
yana ficewa a dakin ko titi baikai ba yaji ana kwala masa kira ata bayansa yana juyowa sa mamaki yaga jamal ne ke biyosa yana riskansa, ibaad yace hey, i hope everything is okay? jamal yana haki yace "yeah yeah..na manta ne ban karbi contact dinka. ibaad yace is der really need for that..
..jamal ya kalli cikin kwayar idonsa yace u did not only save my mum frm dying u waited for her nd protected her...pls let me be ur pal or wat eva, by the way i am new in nigeria, taki jirana na nw gama meeting tazo ita daya, jirgi na kuma yazo 1nd half hour bfr hers..aiko gaisawa zamuna yi maybe we cud even hang out sumtimes..
cikin kyabe baki ibaad yace
"alryt, gayen ne ya fara ciro wayarsa wata golden plated iphone tana shining wanda saida ibaad ya mata kallo biyu, irin customise phones din nan ne sa ake saka musu highly encrypted security codes, ibaad ya saka masa numbers atake yay saving ya masa flashing ,ibaad yay saving numbarsa snn suka rabu.
Bayan faruwar haka sa kamar wata guda bai kara ji daga wajen su jamal ba, kuma shima bai sake nemansu ba kowa yafada harkan rayuwarsa
uncle moh ya dawo nigeria daga dubai gabaki daya harkalla ya balain bude masa kudade da budi tazo masa atakota ina
wani irin sabuwar salo yazo dashi mai ban mamaki, giyar kudin daya karayin na balain debarsa, yanxu ya dawo kusan kowani karshen sati saiya bawa ayaanah kudin kashewa ko tana so ko bataso, harhada tactics dinsa yakeyi da hajiya mairo me tuwo dan kawai ayaana tana karban abun duniya a hannunsa, lamarin da gabaki daya ya jawo mata rashin nitsuwa sabida yadda ibaad yake yawan fushi da komi dake faruwa...
dakyar uncle moh yazo ya fara yana hadawa da sauran yaran a kyautatwarsa, but still sai yay ma ayaana wani abu na daban, ko ya bata nata kyautar yafi na kowa ko ya saya mata nata kalar daban.
banda ammi karama data hana sam ayana tana fita daga zarar mgrib yay ko side in anty safeeran bata kyaleta taje da dare yanxu.
kafin ayana suyi exam na shiga jss 2, wani irin silent war ne ya dinga gudana tsakanin uncle moh da mutanen gidan musammn ma ibaad
dan uncle moh nuna musu yakey shi babba ne, kuma yasan me yakeyi, wani bai isa ya dakatar masa ba, nd he is always manipulating anty safeera with big big gift, ya canza mata cars and soo much money koda kuwa sunyi magana akan wasu abubuwan dayake bawa ayana sai yace sam ba haka bane sai kaga kuma ta yarda dashi, ga hajiya mairo ita kam bata gane komi ita duk daukawa tay danta muhammadu yana da tausayine kawai sosai
kan kace wani abu ayanah tana da exotic watches, abaya na dubai, da expensive bags da kuma expensive jewerie kala kala daya siya mata duk wai tsarabar dubai duk sanda yaje koda na kwana uku ne sai ya kawo tsaraba na ayana kuma me shegen tsada yake kawowa.
silent war dake tashi atsakanin ibaad da uncle moh din yasaka ayaana a wutar tsakiya, ibaad ya dawo yana mata tsauri, akan tsafta, bacci, ko ana kallo zaizo ya koreta acikin yan uwanta ya hade rai yace taje bacci, dole tay karatu hadda zai takurata wani bin tanayi bakinta na bari. duk sai ya zamo bata samun sauki face wajen mujaheed.
har karya takeyi ma uncle moh dan karta karbe abun hannunsa dan ta samu sakin fuska awajen ibaad koda rana dayane amma sam sam yaki shidakansa saiyaje ya bawa hajy mairo yace ai abu kazan nan na ayaanah ne a ajiye mata ita kuma da zuciya daya take daukar abun haka zata kira ayana tasata karba dan dolenta babu yadda ta iya msmn ma da yanzu yafara hadawa da yaransa yana siya musu duk dama baikai wanda yake bawa ayaanah a idonsu, da kuma bayan idonsu ba.
abubuwan dake faruwa sunyi affecting din ibaad sosai,
musmn daya gane cewa wann ƙarin daukaka da sabon budin da uncle moh ya samu na kudaden larabawa shine ya saka izgilinsa ya karu sosai yake yin abunda yagadama
,ynxu duk gidan babu wanda ya isa ya hanasa yay abunda yaga dama koda sau nawa ammi karama zata masa magana baya daukar maganan ta da mutunci a idonsa bare kuma matarsa da tunda ya samu karin daukakar yake balain manipulating inta da soyayya yana baza mata bakin aljihunsa busines dinta tana wasa da kudinsa aciki duk ya rudeta ta zama koda taga abu marar kyau bata wani daukar abun serious kuma daga yay mata bayani kadan sai ta shashantar. hakan sosai ya kashe ma ammi karama gwiwa, ita kadanta tasan cewa ayaana kwata kwata batason komi dayake faruwa tskaninta da uncle moh, amma ganin ya rufe ma matarsa da yaransan ido duk basu korafi tarasa ya zatay, gashi alkwari tay bazata kyale ibaad ya tunkare case din ba, dan tasan duk randa tabarsa yay magana akan ayaaana bala'in da uncle mohd zai kunce agidan basu san karshensa ba...sam sam bataso ibaad yay fada da uncle dinsa musmn akan ayaana gani take kamr zaiy affcting abubuwa dayawa agidan.
ibaad ya shiga wani yanayi wanda har yakany amusing din zainab arifa, wani bi, she enjoys the bully da takurin dayake ma ayaana,dan duk sanda taga ayaana tana takure ko tana kuka sanadiyar masifar ibaad bakaramin dadi hakan yake mata aranta ba.
within 2 months it became so clear that uncle moh yana opressing din lamarin ne da kudi, dan yasan ata nan ne kawai ibaad ko wani agidan bazai iya taka mai burki ba.
business din da ibaad yake cewa saiya gama 2nd semester dinsa ne zaiyi sai yaji yafara shiga ransa cos he feel he had to do sumting to get ayaanah out of that complicated situation da uncle moh yake kkrin cusata aciki
yana cikin wann nazarin suna daf da fara shirin exam zainab arifah ma tafara nata makircin, inta zo gidan taga ayaanah atakure tana karatu ita daya ko an hanata fita sashen su anty safera sai tadinga cewa ai ayaana tana bata tausayi, haka zata bita har daki tana pity petting inta, wann wkdn din ana zuwa tazo ta same ibaad da kinibibi tafara ce masa yadda take takura ma rayuwar ayaana ynxu tana bata tausayi dan haka tana so ya bata permission zasu je shopping hala ta samo mata farinciki acan" he was so pissed wai har da ce masa tausayi yarinyar take bata..yace atleast she is grounded. zainab tace but she is just so vulberable i kind of pitying her. yace you dont pity urself da everything u want weda good or bad u must get it? tace excuse me how is dat a bad thing?
yace mata abar tausayi ai itace wanda aka traineta batasan darajar kanta ba. maganan ya mata zafi sosai ranar da fushi ta koma gida. ranar gabaki daya ransa a mugun bace yake, ayaana tana lura dahshi yau ko abinci baici ba...wani tunani tay, can da yamma bayan ishai kafin su wuce gida, taje kitchen ta debo abincin ta kawo masa har dakinsa, wanda dakyar da wahala ya kulata. haquri ta dinga bashi ita kanta bata san asali meyasa take bashi hakurin ba. dayaga tay masa kuka sosai kuma yasan hanklinta sam ba akwance yake kwana biyun nan ba sai ya hakura ya sauko sun jima a dakin nasa yana mata nasiha cewa kwata kwata tadena amshar wani abu awajen wani namiji koda shine yake bata abu excessively haka kartana karba sabida one day wnnan abun zai zamo mata trap ko wani abun gori. har ransa baiso da ya gaya mata hakan a fili ba duba da age inta, amma ji yake kamr uncle moh ba tsakani da Allah yake mata wasu abubuwan ba. kuma yana amfani ne da matsayinsa akansu yake yin abunda yaga dama dan yasan yana da bakin da zai iya magana hajiya mairo ta amince dashi kai tsaye.
kusan ma akan uncle moh ya mata fada amma da wayo kuma sosai ta fahimce shi duk da ma bai ambace suna ba. since that day datay shagwaba ta rarrashe yayanta suka dawo dede ya dena fushi, a satin gabaki daya sai ta fara wani irin silent rashin kunya, daga zaran uncle moh ya saya mata abu kai tsaye sai tace masa atambaye yaa ibaad in yanaso ta karba...
tunda tafara masa haka na daya na biyu dayaga abun nata dagaske ne tuni yaji ya fara mugun hatsala, ranar jumaa da sassafe ana fita a sallan fajr ya kada jallabiyarsa ya wuce sashen hjy mairo da zimman kai karar ibaad game da wann magana da ayaanah take furtawa....
# atattauna monday in sha Allah zamu tashi da zafin tsiya.....💋❤️
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025