Page-2
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By
*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page2️⃣
Inna na zaune bisa kujera a tsakar gida, jin sallamar da ake ne yasa ta juyowa ta dube ni a wulaƙance ka na ta ce, "jira ki ke sai na ce ki je ki duba su waye ke sallama?" Ban bari ta kai ƙarshen maganar ba na tashi da sauri tare da jan mayafina na nufi ƙofar gida.
Subhanallahi!!! Ina fita me kuwa zan gani? mutane rike da Annur jina-jina da jini. Ban san lokacin da na riƙe numfashina ba, zuciyata ta fara bugu da saurin cike da fargaba, hannayena su ka ɗau kyarma ina shirin ɗagasu, sai kuma na sa gudu cikin tashin hankali ina nufan inda Annur ya ke tare da fashewa da kuka.
"Na shiga uku! Annur me ya same ka? ka buɗe ido, yi min magana!" Kalaman da na ke furtawa kenan cikin matsanancin kuka ina jijjiga Annur da ke hannun wani mutumi, ganin yadda na ke kuka ya ƙara ba mutanen tausayi, nan suka fara ba ni baki.
Ɗaya daga cikinsu ya yi dauriyar cewa, "ƴata yi haƙuri kin ji? Je ki kira mana mahaifin ku" da ƙyar na iya dakatar da kukan da na ke na ba shi amsa, "Abba baya nan" "Mahaifiyar ku fa? Ko ita ne kira ta" ya ƙara faɗi, da gudu na kuma yin cikin gida ba tare da na daina kuka ba, duk da Inna ta ji hayaniyar amma ko motsawa daga inda take ba ta yi ba, ina zuwa inda take na fara cewa "Inna ance, ance kizo, Inna jikin Annur duk jini!" na faɗi ina kuma fashewa da wani kukan.
"Ke rufamin baki! za ki wani ce jikin Annur jini, ni na aike shi yin wasa har ya ji ciwo a hanyan ko me? Sai da na yi masa gargaɗi kafin ya fita, to bari ki ji ba inda za ni! Sai ki je ki sanarwa ubannki a wurin sana'arsa inyaso shi ya zo, haba wannan takura har ina? Ba ni na haifa ba amma an dawo min jaraba" tana kai ƙarshen maganar ta juya gun Halima da ke gefenta tana bina da harara tun ɗazu ta ce, "Halimatuna kawon ruwa insha kin ji?" A shogwaɓe Halima ta miƙe har da tura baki, don so ta yi ace ni inkawo ba ita ba. Ni kuwa ban kuma à sanyaye na juya ina fita, va abun da na ke sai sheshsheƙan kuka na ke ta faman yi.
Bayan na fita mutanen su ka ƙara tambayata, wai ina Umman ta mu? Ban iya ba su amsa ba sai ma wurin Annur da na yi wanda banga alamar ko motsi daga garesa ba. Ana haka sai ga Abba ya iso, yana ƙoƙarin tambayar lafiya? Ganin dandazon mutane a ƙofar gidansa, maganar sa ta tsaya ganin Annur da ya yi, da sauri ya ƙaraso cikin tashin hankalin ganin ɗansa kamar gawa, baki na rawa ya fara cewa, "me ya samu ɗana? me ya same shi?".
Ɗaya daga cikin mutanen ya ce, "muna zaune a bakin titi, mu ka ga yaron nan na ƙoƙarin tsallake titi, yunƙurinsa da wuya wata mota ta kaɗe shi, ko tsayawa mai motan bai yi ba".
Kar in kai ku da ni sa. A wannan ranar Annur ya amsa kiran Mahaliccinsa, mutuwar sa ba ƙaramin taɓa ni ya yi ba, ƙanina shi ne kaɗai wanda na ke zaunawa da shi inyi hira tun bayan rasuwar Umma, amma sai ga shi shima ya tafi ya barni. A raina ina jin cewa tabbas Inna Jummai ce sila, amma tunawa da maganar Ummana da na yi ne yasa na bar wannan tunanin.
Bayan rasuwar Annur ƙaddarata ta cigaba da tafiya cikin tsanani da damuwa, wahala da takura, farin ciki ya gama ƙaurace min, har ina ganin kamar a haka zan dawwama cikin baƙin ciki har abada, duk na bi na ƙara ramewa, wanda mahaifina ya ke alaƙanta hakan da mutuwar Annur. Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min har zuwa wani lokaci.
GARI YA WAYE.
Kamar kullum na fara aikace-aikacen gida, ina cikin yin wanke-wanke Halima ta zo ta tsaya a kaina, na kusa ba ta shekara da wani abu, amma ba abin da ya ke haɗa ta dani illa baƙin hali da sharri, ban ce da ita komai ba akan tsayen da tai min ba ina ci gaba da aikina, sai jin muryarta na yi tana cewa, "wahalalliya kawai! Ni ki dai yi sauri ki gama ki zo ki yi mana girki yunwa na ke ji" ta faɗi tana ɗaura hannu a kwan-kwaso.
"Ni za ki cewa wahalalliya?" Na faɗa tare da juyowa ina kallonta. Murmushin da van fahimta ba tai min, ta ke ta sa ihu har da kuka, da mamaki na bi ta da kallo da tunanin yau kuma wani sharrin za ta ƙa ƙaba min? "Ya yah ya yah? Me akai miki?" Cewar Inna bayan ta fito daga ɗaki, sai da Halima ta langwaɓe murya ta fara cewa, "wai don na ce ta yi mana girki inta gama shine ta mare ni Inna, kuma ma har tana faɗin baza tai ba" "iyyee! Yaushe ki kai ƙwari haka da za ki maran min 'ya Nuriyyah?" Inna ta yi maganar tana ƙuramin ido.
Cikin muryar tausayi na ce "Inna wallahi ni ban mare ta ba, hasalima ita ce ta zage ni da kalmar wahalalliya, amma ban mata komai b..." cikin masifa Inna ta katse ni da cewa "Allah Nuriyyah? To yo dama wacece ke inba wahalalliyar ba?" Tana kaiwa ƙarshe ta rufeni da duka, har sai da ta yi mai isan ta, sannan ta rabu da ni tana fitar da numfashi ta kuma cewa, "kuma ki gama ɗin, ki zo ki yi mana girkin, munafuka kawai!".
Tana faɗi ta wuce, sai da Halima ta yi min gwalo ka na ta wuce, da ƙyar na iya haɗiye kukan da na ke ina share hawaye da su ke zubar min kamar fanfo, domin babu amfanin da hakan zai yi min, idan na ɓata lokaci ban kammala da wuri ba, to fa wani abun ne na daban da Inna za ta kuma ɗaura min.
Bayan na gama na ɗaura girki shima na kammala, Inna Jummai ta fito ta ɗibi abincin ita da 'yarta su ka shige ɗaka. Yunwa ya dame ni sosai, hakan yasa na yanke shawarar inje in tambayi Innar ko za ta bani abincin?.
Zuwa na yi ƙofan ɗakin na tsugunna, kan na kai ga yin wata magana Inna ta ce, "ke mayya me ki ke min a bakin ƙofa!?" sunkuyar da kai na yi cikin muryar fargaba na ce, "daman... Am daman yunwa ne ke damuna Inna, shsh shine na ce ko zan samu, samu abincin da zanci?" Inna Jummai ta maimaita maganar da na ce cikin musguna, "daman yunwa ke damuna. Munafuka kawai! To sai ki jira in mun rage kyaci ai, sai shegen iyayi irin na uwarki! Kin wani zo kin taren iskar shaƙa, ni tashi min a bakin ƙyaure!" ta yi maganar kamar ta san mahaifiyata, wanda ina da tabbacin ko hotonta ma ba ta taɓa gani ba.
Tashi na yi simi-simi kamar munafukar da ta ce, ina nufan wurin tukunya don in kankare ƙanzon ciki, saboda in kashe yunwar da ke nuƙurƙusata. Hakan yake faruwa ako da yaushe, in sun rage inci, in ba su rage ba kuma in ƙa re a ƙanzon tukunya, ko kuma wata rana Inna ta dubeni ta ɗiba min kamar abincin da jariri zai ci, Abba in ya fita tun safe sai yamma ko dare yake dawo wa.
Ina cikin kan-karewa na ji saukar ruwa cikin tukunyar, da hanzari na ɗaga ido na sama don inga mara imanin da baya so na da alkhairi, akan Halima idona ya sauka, yayin da ita kuma ta ke bina da murrmushin baƙin hali sannan ta ce, "ashe dai kin tabbata munafukar!" Ɗaga hannu na yi da niyyar mari saboda haushin kalmar da ta faɗa mun, da kuma ruwan da ta zuba min cikin ƙanzo.
Last page
___________________________________________________
Annur ya rasu🥺 kuma Inna Jummai ce sila, ga shi ta cigaba da gasa Nuriyyah ita da Halima, ko me zai faru gaba?
Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_