AMRAH

AMRAH PART 05

by @hussainyusuf

AMRAH

<<PART 05>>

Shamaki yana tsaka da birgima, sai aka hango Malam Buba yana nufo fadar riƙe da hannun Amrah, matarsa Ladidi tana biye da su a baya. Da mutane suka hango su, sai suka fara zamewa ɗaya bayan ɗaya, suna barin fadar a guje. Kafin su Malam Buba su ƙaraso, gaba ɗaya jama’ar wajen sun tarwatse, sai Maigari da tsirarun fadawansa ne kawai suka rage.

Shi kuwa Shamaki, tun da ya ji ana cewa "Ga ta nan!" kuma ya ƙyallara ido ya hango su, sai ya rarrafa ya koma bayan kujerar Maigari, ya labe ya yi shiru, kamar ba shi ne ya gama birgima ba. Da ya ga dai sun nufo fadar kai tsaye, kuma ya ga babu wata mafita, nan take ya arce, bai sanar da Maigari ba.

Zuciyar Malam Buba ta yi zafi ƙwarai, ganin yadda mutane ke ta gudu kamar sun ga wata mummunar annoba. Lokacin da suka ƙarasa fadar Maigari, har da fadawan nasa sun gudu, ya rage daga Maigari sai Liman kaɗai a zaune. Cikin damuwa, Malam Buba ya durƙusa a gaban Maigari ya gaishe shi. Maigari ya amsa gaisuwar a tsorace. Ko kaɗan bai yarda ya kalli inda Amrah take zaune ba, gani yake idan ya kalle ta, to ƙarshensa ya zo.

Maigari ya kalli Liman ya ce, "A yi mana addu’ar neman tsari." Liman ya fara karanto addu’a. Su Malam Buba, Maigari, Ladidi, har da Amrah suna amsawa da Amin.

Ana shafa addu’ar, Maigari ya ɗago kansa zai kalli Malam Buba, amma karaf idanunsa suka sarƙe a cikin idanun Amrah. Nan take, sai ya ga idanun nata suna jujjuyawa, suka canza launi zuwa kore shar! Gashin kanta ya miƙe ya yi tsayi, ya canza launi daga baƙi zuwa kalar kore shar! Kuma kan macizai suka bayyana a jikin gashin!

Duk yadda Maigari ya so ya kawar da kansa daga kallon Amrah, ya kasa. A hankali, kan macizan ya gama bayyana a jikin gashin kanta da ya miƙe. Gaba ɗayansu suka kai wa Maigari sara a lokaci guda!

Saboda tsananin firgita, bai san lokacin da ya faɗo daga kan kujerarsa ba, ya kwalla ihu da ƙarfi. Yana waiwayawa, sai ya ga macizan suna miƙo wuya za su cije shi. Ya fara ihu yana cewa a zo a taimake shi, Amrah za ta kashe shi!

Mutane suna jin ihunsa daga cikin gidajensu, amma babu wanda ya yi gangancin fitowa ya kawo masa agaji. Su Malam Buba da Ladidi suna zaune a wuri guda, suna kallon duk abin da ke faruwa. Shi kuwa Liman, tun da ya kalli Amrah sau ɗaya, ya ji gabansa ya faɗi, sai ya ɗauki takalmansa a sume, ya bar kan tabarmar da suke zaune. Yana ɗan yin nisa da fadar, ya kwasa a guje yana waiwaye, kamar wani ne yake binsa a baya.

A hankali, Maigari ya ci gaba da ja da baya, yana ba Amrah haƙuri, "Amratu, ki dubi girman Allah ki yi min rai! Ki bar ni da raina! Wallahi babu abin da na ce a kanki, wallahi ban ce komai a kanki ba!"

Mamaki ne ya kama su Malam Buba da Ladidi. Su dai sun ga Amrah a zaune take a wuri guda kusa da su, amma sun ga Maigari sai faman ba ta haƙuri yake yi.

Hankalin Maigari ya ƙara tashi lokacin da ya ga kan Amrah ya rikiɗe gaba ɗaya ya koma kan maciji, ta nufo shi kai tsaye za ta sare shi! Aikuwa, ya kwasa a guje. Yana gudu, iska tana baza babbar rigarsa, kuma yana ta ihu. Duk lokacin da ya waigo bayansa, sai ya ga Amrah tana biye da shi, sai ya ƙarawa gudun nasa ƙaimi.

Yana zuwa ƙofar gidansa, ya sa ƙafa ya hankaɗa ƙyauren gidan ya shige. Ya fara kiran sunan matarsa cikin tsananin tashin hankali, "Jummala! Kina ina? Ki buɗe min ƙofar nan kafin aljanar yarinyar nan ta yi ajalina!" Da rarrafe ya ƙarasa ƙofar ɗakin, ya hau buga ƙyauren da ƙarfi, amma tsoro ya hana matarsa Jummala buɗewa.

Zaune Maigari ya yi a ƙasa, yana ihu shi kaɗai. Kwatsam, ba zato ba tsammani, ya ga Amrah mai kan maciji tana leƙo shi ta katanga! Kafin ya yi wani yunƙuri, ya ga ta bayyana tsulum a gabansa! Aikuwa, nan take ya saki fitsari a wando. Amma duk da haka, ba ta bar shi ba, ta kawo masa wawan sara a goshinsa. Saboda tsananin firgita, ya baje a wajen sumamme.

Da Malam Buba ya ga fadar Maigarin ta tarwatse, sai ya ce wa Ladidi su tafi gida kawai. Suna tafiya a hanyarsu ta komawa gida, ba su haɗu da kowa a hanya ba. Kowane gida idan ka kalle shi a rufe yake. Misalin sha biyu na rana ne, amma garin ya yi shiru, kamar babu sauran mutane a ciki, saboda tsananin tsoron Amrah da ya shiga ransu.

Yinin ranar, babu mahaluƙin da ya leƙo waje. Sallah ma, kowa a gida ya yi tasa, saboda Liman shi ma kasa fitowa ya ja sallar ya yi. Sai bayan sallar la'asar, mutane suka ɗan firfito, su ma a gaggauce suka gabatar da uzururrakinsu. Da suka ga magariba ta kusa, suka sake komawa gida suka kulle.

Washe gari da sassafe, Maigari ya tashi Shamaki ya aika shi wani ƙauye da ke kusa da su, domin ya gayyato wasu manyan Bokaye biyar da ake matuƙar ji da su a harkar tsafi. A kan su zo su yi maganin hatsabibiya Amrah.

Malam Buba da Ladidi suna zaune sun zuba tagumi, abin duniya duk ya ishe su. Amrah kuwa tana kwance a kan tabarma. Tana son fita ta ɗan zagaya gari, amma Baffa ya hana ta fita ko ƙofar gida.

Ita dai Amrah, duk abin da ke faruwa a ƙauyen, kamar ba ta sani ba. Abin yana matuƙar bai wa iyayenta mamaki, kuma yana ɗaure musu kai. Su kansu sun ga wani gagarumin canji a tattare da ita. A iya jiya zuwa yau, ta zama haka, ga shi nan kowa gudunta yake yi a ƙauyen, ko ta ƙofar gidansu ba a bi. Dama gidan zagaye yake da manyan bishiyoyin kuka da na tsamiya, kodayake ai duk kusan su ne suka zagaye ƙauyen.

Hussain Yusuf✍️