FreeArewaPen original
AMRAH
- 1views
- 28chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Alƙalami ya fi takobi🖊️📝
Sample · Dandano
Bayan Kamal ya fita sai Zeenatu ta fito tare da jaririyarta a hannunta tana yi mata wasa, cikin jin dadi da walwala. Kafin Zeenatu ta zauna kira ya shigo wayarta, ta damƙawa Jawad jaririyar ta shiga cikin ɗaki da sauri don ta ɗaga wayar..Jawad yana tsaka da yi wa jaririyar wasa, sai ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. A zatonsa ma Kamal ne ya dawo. Ajiye jaririyar ya yi a kan kujera ya je ya buɗe ƙyauren. Sai ya ga wayam babu kowa a ƙofar.Mamaki ya kama shi, amma sai ya basar, saboda yana zaton kunnuwansa ne suka jiyo masa ba daidai ba. Rufe ƙofar ya yi ya dawo cikin falon, sai ya tarar babu jaririyar a inda ya ajiye ta.Gabansa ya yanke ya faɗi. Sai ya kalli ƙofar ɗakin da Zeenatu ta shiga, sai ya yi zaton ko ita ce ta fito ta ɗauki jaririyar. Gabansa ya tsananta faɗuwa, ya ci gaba da kallon ƙofar ɗakin Zeenatu yana jiran ta fito ya gani ko ita ce ta ɗauki babyn nata.Yana nan tsaye Zeenatu ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.