AMRAH PART 06
AMRAH
<<PART 06>>
Su Malam Buba suna zaune, sai suka ji sallama a ƙofar gida. Yana fita, ya tarar da fadawan Maigari guda biyar a tsaye. Bayan sun gaisa, suka ce masa ya zo fada nan take Maigari yana son ganinsa da gaggawa, amma idan zai tafi, ya je shi kaɗai. Suna faɗa masa, suka juya da sauri suka bar ƙofar gidan. Malam Buba ya canza riga kawai, ya saka takalmansa, ya nufi gidan Maigari.
Yana isa, ya tarar da fadar ta cika da manyan garin. Sannan ga wani babban boka a zaune gaban Maigari. Babu komai a jikin bokan sai warki da ya rufe al’aurarsa. Amma gaba ɗaya jikinsa cike yake da guraye da layu na tsafi. Haka kuma, a damtsen hannunsa na hagu, ya saka wani ƙaton kambun tsafi. Malam Buba yana ganin sa, gabansa ya faɗi, ya sha jinin jikinsa.
Yana cire takalminsa zai zauna a kan tabarma, sai wannan hamshaƙin bokan ya daka masa tsawa, ya ce, "Ja da baya! Kai gagarumin mai laifi ne!"
Malam Buba ya ja baya da sauri, yana mamakin wane laifi kuma ya aikata har aka haɗa irin wannan taron a kansa?
Boka Durwas (Shi ne sunan bokan) ya kalli Malam Buba ya ce, "Dole ne ƴarka Amratu ta fuskanci hukunci a wajen manyan bokaye na wannan yanki. Saboda ta aikata babban kuskuren da zai iya jawo mu kifar da garin nan. Don haka, idan ba ka so mu hallaka mutanen ƙauyen nan naku, to dole ne ka ba ni ƴarka Amrah na tafi da ita, domin ta girbi abin da ta shuka."
Wani kallo na rashin hankali Malam Buba ya watsa wa Boka Durwas, cikin rashin tsoro ya ce, "Ai har yanzu ban ji ka faɗa min laifin da ta yi ba."
Maigari ya tari numfashin Boka Durwas ya ce, "Haba Buba, me kake faɗa ne haka? Kaf ƙauyen nan babu wanda bai san cewa ƴarka Amratu ce ta kashe hatsabibin Boka Rubbas ba? Saboda haka, ina umartar ka salin-alin ka damƙa musu wannan yarinyar su tafi da ita. Su yi mata duk hukuncin da ya dace da ita. Mu ma sai mu huta da fargaba, mu jefar da ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda."
Malam Buba ya tashi tsaye ya ce, "Wallahi, ko sama da ƙasa za su haɗe, babu mahaluƙin da ya isa ya tafi da ƴata wani wuri don ya hukunta ta! Sai inda ƙarfina ya ƙare." Nan fa hayaniya ta ɓarke tsakanin mutanen garin da Malam Buba. Shi yana cewa ba za a iya tafiya da Amrah ba, su kuma suna cewa dole ne a tafi da ita su ma su huta da fargaba.
Boka Durwas ya ɗaga hannu, kowa ya yi shiru. Sannan ya ce, "Ko iyayenta suna so ko ba sa so, sai na tafi da ita da ƙarfin tsafina. Don haka, ku kwantar da hankalinku, ku bar ni na yi aikina."
Nan take kowa ya yi shiru. Boka Durwas ya fito da jakar tsafinsa, ya zazzage kayan tsafin a kan tabarma. Sannan ya hau zagaya su, yana karanta wasu ɗalasimai yana ambatar sunan Amrah. Kowa ya zuba masa ido. Ya daɗe yana karanta ɗalasiman, sannan ya zauna ya dubi Maigari ya ce, "Ku kalli hanya."
Da sauri mutane suka kalli hanyar, sai suka hango Amrah tana gudu! Mahaifiyarta tana biye da ita a baya tana kiran sunanta. Ita kuwa Amrah, sai faman gudu take tana cewa sai ta bi Boka Durwas garinsu.
Boka Durwas yana ganin haka, sai ya bushe da wata mahaukaciyar dariya. Sai da ya yi mai isarsa, sannan ya dubi Maigari ya ce, "Ranka ya daɗe, ya ka ga aiki da cikawa?" Maigari ya amsa da "Uhmm," idanunsa a kan Amrah. Cikin ransa, ya rinƙa tuno yadda ta wahalar da shi jiya. Kwana ya yi yana zawo saboda muguwar tsoratar da ya yi. Yanzu ma, sai yake ganin kamar za ta sake yi masa abin da ta yi masa jiya. Ba don da Boka Durwas a kusa ba, da tuni ya gudu gida.
Amrah tana ƙarasowa, ta faɗa jikin Boka Durwas. Shi kuma ya riƙe hannunta suka tafi.
Cikin fushi, Malam Buba ya yunƙura da nufin ya bi bayansu, sai ya ji kamar an saka sarƙa mai ƙarfi an ɗaure masa ƙafafu, ya kasa motsawa ko kaɗan. A ɓangaren Ladidi ma haka ta ji. Suna ji suna gani, Boka Durwas ya tafi da ƴarsu ƙwaya ɗaya da suke matuƙar so. Ba su san me zai yi mata ba idan ya tafi da ita.
Kuka sosai Ladidi take yi, tana kiran sunan Amrah tana cewa ta dawo, amma sai Amrah ta ce, "A'a Inna, Boka Durwas zai kula da ni." Haka Malam Buba ya rinƙa kuka kamar ƙaramin yaro. Tun suna iya hangensu, har suka shige cikin daji, suka daina ganinsu, sun ɓace ɓat.
Daga nan, su Malam Buba suka ji an saki ƙafafunsu. Suka rinƙa birgima suna kuka tare da kiran sunan Amrah. Mutane kuwa, me za su yi idan ba dariya ba? Wasu kuwa, murna ce ta cika ransu, an raba su da alaƙaƙai.
Bayan Kamal ya yi wanka yana niyyar fita ofis, ya fito falo, bai ga Zeenatu ba. Don haka, ya koma stairs don ya duba ko tana lafiya. Yana zuwa ɗakin, ya tarar da ita a kwance ta lulluɓa da bargo, tana nishi ƙasa-ƙasa. Da sauri ya ƙarasa kusa da ita yana kiran sunanta, "Zeenatu, me yake damunki?" Da ƙyar ta iya ba shi amsa.
Ya buɗe wardrobe ɗinta, ya ɗauko mata doguwar riga, ya ce ta saka su tafi asibiti. Da ƙyar ta iya tashi da taimakon Kamal ta saka rigar. Ya riƙo hannunta suka sauka ƙasa. Shi yake taimaka mata har suka shiga mota, sannan ya ja suka tafi.
Bayan an yi ƴan gwaje-gwaje, likita ya tabbatar wa Kamal cewa matarsa tana ɗauke da juna biyu ɗan wata huɗu. Murna a wajen Kamal ba ta faɗuwa, ya ɗaga hannu sama yana miƙa godiyarsa ga Allah. Ita kuwa Zeenatu, duk da ba wannan ne cikinta na farko ba, sai ta ji kunya ta rufe ta.
Tun daga asibitin, Kamal ya fara tarairayarta, ita kuwa sai zuba masa shagwaba take. Da Kamal ya ɗauko wayarsa, mutum na farko da ya fara yi wa wannan albishir shi ne babban amininsa tun yarinta, wato Jawad.
Lokacin da ya faɗa masa cewa matarsa Zeenatu ta sake samun juna biyu har ya yi wata huɗu, Jawad ya ji daɗi sosai, ya rinƙa zuba masa addu’a a kan Allah Ya sauke ta lafiya.
Lokacin, Jawad yana tare da Hamrah. Da ya faɗa mata, ita ma ta nuna farin ciki sosai, ta ce, "Allah Sarki Anty Zeena! Wannan shi ne cikinta na uku. Sauran duk ɓarinsa take yi. Allah Ya sa wannan ya zama rabonsu." Cikin jin daɗi, Jawad ya amsa da Amin, yana ƙara jin soyayyarta tana ratsa jinin jikinsa.
Haƙiƙa, kullum godiya yake yi wa Allah da ya haɗa shi da Hamrah. Kamun kanta, natsuwarta, iya magana, uwa uba, tsananin kyawun da take da shi, sune suka fi jan hankalin Jawad game da Hamrah. Duk da yarinya ce, sosai tana da hankali da natsuwa.
Ya tashi tsaye ya ce da ita, "In an jima ki shirya, zan zo na ɗauke ki ki raka ni na yi wa abokina Kamal murna da samun wannan ƙaruwa." Hamrah ta mayar masa da murmushi ta ce, "To, amma idan Umma ba ta bar ni ba, sai dai ka yi haƙuri. Ba zan iya tsallake umarninta ba."
Jawad ya ce, "Ba matsala, balle ma na san Umma ba za ta hana ki ba, in dai kin ce ni ne." Hamrah ta yi murmushi ta ce, "To baby, sai anjima ɗin idan ka zo." Da kanta ta buɗe masa mota ya shiga. Ta rufe, ta rinƙa ɗaga masa hannu har ya fita daga layin nasu.
Hussain Yusuf✍️