ABUNDA KE 'BOYE...

34

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.


⏯️3️⃣4️⃣
Tun gari bai gama wani washewa ba uncle moh ya karaso cikin sashen hajiya mairo, lkcin ita kadaine azaune acikin sashntan tamike sawun kafafunta akan wata lallausar sallaya, tafin kafar nan ya gama jin bakin lalle asalin na gagajiya sai sheqi yake yi,cikin sashen banda qamshin turaren sandal balls babu abunda ke tashi koina ya dau tsafta da qamshi

lazimi take bugawa da katon carbi a hannunta tana Allah Allah tagama tajawo wann hadadden herbal tea dake tashin kayan qamshi gabanta da surkuwnta fatima ta kawo mata a flask yanxun nan, tana cikin wann yanayin taji an doka mata sallama..

"salama alaikum

jin muryan autarta ne yasa maza ta gyara zama tun bai karaso ba tace"muhammadu??

sai da har ya shigo da baqin jallarbiyrsa snn yace naam hajiya nan take ya zube kasa ya zauna da ladabi yace "hjy an tashi lafiya? tanata kallon murdadn fuskansa tace "kalau, mohammadu yaya kake, yaya kuma yan jikokina? tun be amsa ba cikin kyabe baki tace jiya anan nan yarka kulthum tazo ta shanye min madara na kuma nace mata bata isa ba wallah saita biyani, wai haka kuka rainesu ne in zasu sha conflaks sai sun zuba kusan rabin kwankwanin madara a kofi? yara basu san maleji ba, basu gaida me maleji, hm yyl haka kawai ana zaman kalau bazaku turo yaranku suna kassara ni bazai saku ba

..cikin karkadai tare da katseta ahnkli yace "wai har kayan madarar taki ya kare ne mama? tace o,o nifa bance maka yakare ba wnn tsakanina da jikokina ne kasan dai fada baya karewa amma dai ya kamata ku koyawa yarku kulthum maleji wani shegen namijin ne ynxu zataje gidansa tana masa irin wann barnan madaran baikoroto ba hmmm..

yaja ajiyan zuciya cike da ji dakansa yace koma yaya ne zuwa anjima zansaka akara stocking miki kayan shayi tunda ke da jikokin naki kike sha, mama in kulthum bata sha madara yanxu sai yaushe zata sha? ..kyabe bakinta tay tace toh toh shikenan, ai yarka ce banawa ba. kudai dake barnan kudi dama baya muku wuya..ohhh ni mairo Allah na tuba yaushe ma aka kawo wnn din baifi sati biyu ba inbanda shegen kwadayin yara inama nake da lkcin shan wayanann abubuwa,.. hmm toh ya aikin naka kuma ince dai komi lafya?

fuskarsa ba asake sosai ba yace lafya kalau hajiya...bari na zuba miki shayin ki kisha dan wata magana nake tafe da shi kuma sauri nake zanje na shirya naje aiki .

cikin kwalo ido game da dafe kirji tace tohhhh..ince dai ba wani aure zaka jajibo mana ba muhammadu..ku fa maza ba dama kuga matayenku sunyi bulbul suna walwala agida caraf saiku kawo batun mata kishiya..yaushe ma safeeran ta gama haifa maka yaya da har zaka fara batun dankara mata kishiya kai jama'a..

jawo flask din yay yanakan zuba mata shayin a cup a nitse yace "hjy bance miki fa aure zanyi ba dan Allah karki kaini gaba..

tace amma ai zakayin ko? nifa uwarka ce duk naga take taken ka wallah..

dan karamin murmushi yay yace ehh tohh idan zaku bani mata agidan nan ba..

dan dariya tay tace "mata agidan nan? kaji wani maganan banza yo safiya yar cikinka zaka aura,.. ko kuma waye kagani ya dace dakai agidan nan, zaidu dai ya rigaka furtamin sunan fatima..kai da Allah gayamin meke tafe dakai kawai bana son shashanci.

sauke ajiyan zuciya yay ya kalleta with serious face snn yace "hajiya bawani abun tashin hankalii bane..kawai dai yadda abubuwa suke tafiya agidan nan ne basu min dadi, kar nay magana ace na tsane wani yaro wani ina fifita shi Dan haka gaskiya ni zan gaya miki abunda ake min agidan nan bana jin dadinsa dan na lura kamr yaran nan gabaki daya basa ganin girmana kuma iyayensu mata ne ke daure musu gindi...inba haka ba harnine za'a dinga min gadara agidan nan,wai ace na bada yarinyarnn kyautar abu sai taki karba tace wai sai wani wawan yaro agidan nan ya bata izini akan shi waye ne? zaman aure ne a tsakaninsu ko kuma shine ubanta, ni sam bana so na ja wata magana, amma tun da yarinyar nan dai jikarki ne, kece zakiyi masa magana dan duk gidan nan wallh babu wanda zai iya dukana acikin yaran nan, dan haka banaso akaini bango na harzuka na ci uban yaro acikinsu babu wanda yafi karfin duka wajena.

aje kofin shayi tay cikin
katsesa tace kai kai kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun haba haba haba muhammadu..wai kai da waye haka kake wann masifa da boye boye, banason mita kmr matar mamaci kawai fito fili, waye ya rainaka? waye kuma tantirin marar kunyar acikin yaran nan da suka hada meeting sukace zasu bugeka suna hauka ne da zasuce maka zasu casaka? wai waye yay maganan nan gaya min nikaina saina ci ubansa

cikin harde ransa yace hajiya aikinsan waye ne basai nakama suna ba amma inhar kinaso na kama sunan shikenan akan ibaad da ayaanah nake magana.

rike baki tay cikin sassauto da murya  tace tohh shikuma rayyanun meyay maka muhammadu Allah sarki naga bayama shiga harkan ka meye hadinsa dakai kuma

adan hatsale uncle moh yace" a'a..hajiya dakata min, dan Allah karki wani fara bin bayansa da wann irin pretence din dan ko ke nan kinsan anjima ana nuna min ban isa da yarinyar da kika kawota gidan nan ba, yakaiga maman safiya saitana tsare ni dawasu irin maganganun banza kamar tamaidani yaro bansan menakeyi ba dan ina bawa ayaana kyautuka ya zama ana kallona kamar mutumin banza, duk sabida ke nake yin hakuri na shareta sann ina bata girmanta kasncewarta ex matar yayana amma bafa tsoronta nakeji,  bana son raini, bazan kuma lamunci raini musmmn daga wajen marar kunyar Ɗanta dake neman shiga harkata akan yarinyar nan ba..wai tukunma ma ni a'ansa ne? gaskiya hajiya kija masa burki, ya kyale yarinyar nan tunda shi ba ubanta bane kuma ba aurene tsakanin su ba..kar ya kara hanata karban abu awajena idan ba haka ba wallah agaban yarinyar saina ci masa mutuncin da bzai kara iya daga ido ya kalleta ba bare ni...

cikin hade fuska tace  kai subhanallah toh ya isa haka
..shi rayyanun ne yace ma ayaana tadena karban abu awajenka baki da baki  ya gaya maka haka?

yace "aa baifada min baki da baki ba,amma ai kullum nabata abu sai tacemin wai inje intambayesa kenan shine yahanata karba, nifa wallah munafurci ne banaso...a fito fili mana, inkema bakisone in saka hannuna akan yarinya ne akigaya min saina san anware ni, saina bar muku yarku dama ai gwaninta ni bai karbeni ba, wani abun da akeyi agidan nan na rainin wayo ai ba isa ayi ma yaa zaidu ko yaa zayyanu ba saini da aka raina ma wayo

juyowa tay ta kallesa tace kai muhammadu wallah kafiye fadin rai abu kadan saika fara hada kanka da yayunka shi zayyanu ma ina ruwansa shidaya tsine ma uwarsa? zaidu kuma kasan baya mita girma ya kamashi kaine dai kake halinku na yan auta haryanxu..

...shikenan kaje, naji korafinka bari shi rayyanun yazo ni da shi zamuyi magana kaima sai akai zuciya nesa. banason ayi abun kunya yadda rayyanu yake zuwa gidan koyan dambe (gym) yana dada buduwa yana kato kowani rana, ai da kuyi abun kunya dashi gara duka kawai ahakura da rainon abarmin yarinya kawai zan maidata ma zaidu sai shiya riketa agidan sa, dan wallh haka kawai bazaka kama dambe da yaran cikinka ba..Allah na tuba wallah dukanka rayyanu zaiyi kaine dai baka kallesa da kyau ba  toh wallh ahirrrrr dinku nahana wnn magana, wanda yake zuwa gidan dambe kam bazaimin asarar haihuwa ba gara shi uwarsa bata tsufa ba koyau tay aure zata iya sake haihuwa.

da dan bacin rai a fuskan uncle moh yace "Allah ya kiyaye ya dake ni, ohh ashe dama tsoron sa kikeji kenan ko hajiya? zatay masa magana a zafafe yace toh wallh ba'a isa dai akan dan wnn maganan a daga yarinyar nan agidan nan ba..kawai ki masa magana inba wai tsoronsa kikeji ba..ko so kike ki gwada ma duniya maganan da ake fada game da ke akan uwarsa fatima ya tabbata gaskiya, dama ance kwata kwata baki kaunar lefin fatima kusan kowa ya san da haka
..toh wallah bazaiyu ba, akan shi waye...?

cikin daga mai hannu tace "toh naji. yanxun nan zan kirashi zaizo zan masa magana kuma koma miyene zakaji ayi hakuri akai zuciya nesa.

daga haka suka karkare maganan bayan ya dan zauna da ita na wani lkci ya ciro cheque na kudi wanda ya shirya tun jiya ya bata yace toh ga goron jumaa hajiya"..daukar cheque din tay tagani kudi ne meyawa tana murna tafara saka mai Albarka daga nan ya tashi yakoma sashensa domin ya karya ya shirya ya fita.

Tun bayan haka hajiya bata sake dago wnn maganan ba, har saida taje shago ta zauna kafin ta dinga kiran ibaad awaya yanata ringing bai dauka ba karshenta basu hadu ba sai har washe gari ranan asabar, kowa ya taho, su ibaad ne farko farkon zuwa gaisheta aka gaisa lafiya ana zama kenan tafara dago maganan acikin mutane. ga bappa zaidu, gasu maheer da mujaheed da su anty safeera, kananan yaran ne kawai basu nan

kamar maganan arxiki tafara nasiha cewa tana alfahari da kokarin kowanne acikinsu, sai kuma ta murda zancen ta dawo cewa ita bata dauke ma wani kyautatawa ko kulawa da jikarta ayaanah ba, dan haka karda hakan ya zamo silar da wani zaiy gadara ma wani. tay dogon wa'azi akan kyautatawa..tunda ta fara maganan ibaad kallonta kawai yake da mamaki..

dan yagama lura da cikin gidan gabaki daya, bama hajy mairo ba, kusan gani suke kamar tsaurin da yake ma yaran akan tarbiya da karatu kawai takurawa ne da mugunta. kowa ya tofa awajen shi baice komi ba

hajiya tace wai a saukake ma jikokinta su more zama agidan adena tsorata su bakowani dispcline bane akeyi da zafi da tsauri, bataso taji ana yawan duka, ko ana hanasu hutu, tunda duk suna kokari snn duk abu na kyautatawa da nuna gata indai agidan nan za'a basu kyauta ba nawaje ba kar ana hanasu tunda gidan nan duk ba cutar dasu za'a yi ba.

yanajin yadda uncle moh yay maza ya haura kan maganan harcewa yake su ibaad din ma ai tarbiya da nitsuwa bai gama ishensu ba dan haka basuyi girman da suma zasu takura ma na kasa dasu ba...

kusan kowa ya tofa albarkacin bakinsa atakaice dai hjiya mairo da uncle moh suka justifying komi which sunhow make sense to odas, sabida kowa gani yake toh meye lefin da ana bada ayaana ko wata yarinya kyautuka agidan nan, ibaad yay shiru ransa ya gama bashi cewa uncle moh ne yakai kararsa wajen hajya sai bai tanka kowa ba har aka sallamesu dukansu uku suka fita..

maheer yay kmr zai fahimce abun amma kuma sam ibaad yaki ya bashi fuska suyi maganan, mujaheed ne ma yaso shima yay korafi da dabiar baban nasa, saidai sanadiyar maganan nan sai shima ya dada zulmuwa yafara ganin abun as normal tunda dai gidane kuma babu cutarwa acikin kyautatawa.

kin cewa komi da ibaad yay yasaka maganan yay sanyi kowa ya cigaba da abunda ke gabansa har yamma yay, da zasu wuce gida hajy mairo ta kirasa uwar dakinta tafara masa magana privtly shikadai akan maganan rayuwar ayaanah

she din't even ask him what is hapening kai tsaye tay assuming cewa murdadden halinsa yasa yake so lallai ayaanah tadena karban abu daga wajen yayanta...sai cewa take inda muhammad ba dan cikina bane da sai nace kareta kakeyi, toh yaushe kuma alheri ya zama mugunta? ynxu inba shi ba waye agidan nan yake saya mata kayan gayu. wallh har tausayi muhammadu yake bani ka dubafa yadda yake nuna ma ayaana so da gata, harma fiye da yayan cikinsa, wnn ma ai abun alfahari ne garemu, kuma haka Allah yake son mutum yaso dan wani kamr yadda zaiso nasa toh ahir dinka rayyanu da nemansa da fitina nide bana son tsugudidi da tashin hankli...kaji na gaya maka kenan

tunda tafara maganan latsa wayarsa yakeyi idonsa na kallon wayar har ta gama baice mata uffan ba kuma bai dago ya kalleta ba. har saida
tay shiru ya miƙe tsaye ahnkli cikin danne abun aransa yace "toh, hajiya kiyi hakuri..inkin gama ni zan wuce gida kaina na min ciwo!

yanayinta wani iri tana kallon daurarren fuskarsa tace ahhh dakata min, wai yanaga kana wani daure fuska kana amsa ni daddaya rayyanu? wato kai badama amaka mgna kenan sai kay fushi? toh bari inazuwa ka jira ni anan..tun be amsa ba ta fita fuuu bada jimawa ba saigata nan ta dawo da ammi karama tana cewa hajy lafya? harsaida ta kawo ta ciki sann tace"fatima ga danki nan, wai daga namasa magana akan abunda yakey marar kyau shiknan fa ya fara kumbura.
....fisabililllah ynx meye laifin muhammadu dan yana nuna ma ayaana gata... shin ita ba mutum bace da zaina daure fuskansa yana hanawa?

cikin lumshe ido da budewa while stilll maintaining his temper yace "Hajiya cewa fa nayi kiyi hakuri ai banmiki wani musu ba, tunda naji maganarki shikenan..kuma na baki haquri kusan akaro na biyu kenan saidai kuma inkinaso shima naje na bashi hakurin ne toh..

hawaye tafara saukewa cikin raki tace fatuma kinjishi ko?

ahkli ammi tace hajiya dan Allah kiyi hakuri..tunda yace yaji in sha Allah koma miyene ya wuce.

tace aah ah fatima kin haife rayyanu amma ashe kekam ma bakisan ainihin halinsa ba, ai ni gwammaci yamini masifa akan dayamin shiru, hakafa anan ya barni inata magana baice uffan ba wai sai cemin yay inyi hakuri kamar wani na zalunceshi? yo meye laifina anan dan nagaya masa gaskiya, yarinyar nan fa ba uba ne da ita agidan nan ba..meye ne aciki idan muhammdu yana bata gata na uba da zaina hanawa ni gaskiya bangane ma rayyanu mutum sai kace kafurin farko?

cikin lallashi ammi karama tace yi hakuri hajiya.  maganan ya wuce haka i am sure ya ji. kuma in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba. dama fa yana maganan ne sabida kar abun yay yawa tazo ta lalace ko
kuma yan uwanta da ba amusu irinnata abun yay affecting dinsu, aike kinsan yadda yara suke tunani amma bawai ya hana bane Allah ya huce zuciyarki mama

tsabar ransa ya baci baisan sanda idonsa yay jaaa awajen ba..yarasa ma me zaice caraf kuwa sai wayarsa yafara ringing baiko daga yaga waye bane muryansa kasa kasa yace ammi zan wuce inaga maheer ne yake kirana suna jirana zamu wuce gida dare yayi.

gyada masa kai tay da tausayinsa a idonta cikin taushin murya tace "toh, inka isa gidan saika kirani..har zai wuce tace rayyan toh kay ma hajy saida safe mana..fuskrsa a daure yace"...hajiya sai da safe' baijira ta amsa ba agaggauce yabar sashen yanajin ransa na wani irin tafasa...

ringing biyu wayarsa yay ya dauke bai duba ba har saida ya shiga mota ya same maheer yana dubawa kuwa da mamaki yaga kiran jamal ne baibi kirar ba dan kusan tafiyar kurmaye sukayi a motar sabida in ransa na bace bai fiye son yin wata magana..

har suka kai gida kowa ya nufi dakinsa ransa na dagule dan gabaki daya abunda ya faru ayau yay masa zafi sosai saidai bai bata lkcinsa wajen yanke hukunci koyin wani tunani meyawa akai ba
kayan jikinsa yacire kai tsaye ya shiga bathrum ya kunna cold shower ruwan sanyi yana sauka a duka ilahirin jikinsa yajima ahaka kafin yaji ya dawo cikin hayyacinsa bacin ran yay sanyi, wrpping towel yay around his waist, snn yay brush a agaban sink, yana gamawa yay alwala yadawo room dinsa yay yan shafe shafensa ya shirya kansa cikin wata clean short marar nauyi bai saka riga ajikinsa ba ya dau ruwan gora ya zauna daga bakin gadon sa yanasha cikin lumshe ido da budewa yaji duk abubuwan da su hajiyan suke fada nadawo masa kansa, at some point yafara jin ya gaji dakomi dake faruwa, he even started to blame himself for caring, sai kuma ya tuna ita ayaana babu ruwanta, she is just a naive little girl yasan dai duk wann maganan banzan bazai wuce uncle moh bane ya tada shi, yay tunani duniyan nan na yadda zai kyale musu ita yayi abunda ke gabansa


saidai wani bangaren ransa kuma gabaki daya yaqi sam ya amince masa da batun fita sha'anin ayaana msmn inya tuna content din dake cikin wasiqar mahaifyarta, ji yake kmr idan yayi sake rayuwar ayaana ya lalace tmkar yaci amanar mamanta ne data rokesa with all the emotion i  her heart cewa yasaka mata ido sosai akan rayuwar yarta ayaanah sabida mahaifinta juma ya riga yamusu mmunan baki bataso yarta tazo binni ta lalace. idanunsa a lumshe yana cikin lisafin yadda zaiyi ya warware wasu abubuwan, wayarsa ya kara katseta da kara, da sauri ya bude lumashen idonsa duk ya dauka ko jamal din ne yana dagawa saikuma yaga mahaifyarsa ce

cikin sauke ajiyan zcya me sanyi yadauka tun beyi magana ba da sanyin murya tace rayyan nima fushin kayi dani ko?dazu nace kana isa gida ka kirana shine har yanxu shiru..

dan karamin numfashi ya saki ahnlki yace "kiy hakuri ammi wanka nay yanzun nan nake shirin innagama saina kiraki

tace its okay..kun isa lafya? yace alhamdullh kai tsaye tace "rayyan, pls dont take all this to heart. i knw it pains alot to be misunderstood kuma dama abunda nake ta guje maka kenan shiyasa bana son ka dauki zafi akan lamarin ayaanah..dan Allah nide karkace zakay fushi da ita da kuma sauran yaran nan. sumtimes hajy tana magana ne in favour of her son's emotions, kasan dai ita uwace, dama bazataga kusukuren danta haka kawai ba. amma tunda sunce maka kabari toh kwata kwata kadena shiga harkansa.

cikin katseta yace ammi nifa bance ma yarinyar nan tay masa komi ba. kawai nasiha na mata akan yawan karban abubuwan masu tsada da takeyi a hannunsa, .anyways, nide maganan nan ya kare
kuma ba fushi nayi ba, nide in ina takura ma yaranku kuyi haquri i will amend my ways.

dan shiru tay muryanta wani iri tace rayyan pls nide karka yanke wani danyen hukunci dat will make you to abandon ur sisters, inba dan kai ba bansan yazanyi da safiya ba. i truly truly understand you. dont blame urself for anything kaji?? kawai dai shi kawun ka muhammad din ne nakeso kafita a harkansa....

a nitse yace toh ammi..kema ki kwantar da hanklinki i am okay..wani kira yana shigowa wayata can we call it a night?

tace okay ayi bacci lafya. karamin murmushi yay mata yace u too maa.

tana katse wayar ya ga jamal ne cikin sauri ya dauka dan karya yanke da calm voice dinsa yay sallama, suka gaisa..
yace kwana biyu..nan da nan jamal yafara bashi haquri yace urgent meeting ya maidani U.S i cudnt call you men i am so sory..ibaad yace babi komi nima i was pretty much occupied, toh yajikin mum dinka, da fara'a jamal yace alhamdullah ta warware sosai
..hira kadan sukayi jamal ya fara sugesting ko dazasu hadu acikin sati su gaisa tunda shima ya dawo kanon yanzu kuma zaiyi kamar hutun wata biyu yanan nan

ranar wednesday da yamma suka yanke zasu hadu kafin suka karkare kowa yay bacci

washe gari sunday tun bayan sallahn fajr ibaad yakashe wayarsa gabaki daya sassafen suka fita gym shida maheer basu dawo ba sai wajajen 10pm sukay wanka suka ci abinci dats packed with healthy protein, maheer ya wuce wajen harkan secret investment ventures dinsa da already yanzu ya farayin karfi dan ya jima da fara abunsa a boye.

wani irin baccin huta gajiya ibaad yayi duk jikinsa saida ya samu nitsuwa, but with what is happening arnd him yaga kamr shima is high time kawai yay puting business tots insa into action tunda yana da kudin nan, ga uban gadon filaye da millions of naira da babansa ya bar masa me yawa dake babansa surgeon ne amma kuma yay running Big rice farming business ya tara silent arxikin nan saidai shi humble and simple life yay baya show off kwata kwata bakamar na prof ba  dama kuma maheer yasha matsa masa akan yafara kafa source of income insa da wuri basai karatun sa ya rikesa sosai ba. he tot abt it for while, sai kuma ya rasa ta ina zaifara sabida baida wasu kwakkwaran circle na abokai inba frends circle na maheer da mujaheed ba, besides, mujaheed  is a sport nd tech guy kuma shine karaminsu a mazan gidan sai gabaki daya baifiye son shigewa jikinsu sosai ba sabida field of interest dinsu yay hannun riga in bawai suna gida duka atare ba.

Da wannan tunanin aransa yake zama har ranar  wednssday yay suka hadu da jamal moriki a wani waje da shikansa bai taba sanin akwai irin wajen a kano ba.


THE BLACK MINARET

inside wani huge walled villa acikin nasarawa GRA blacl minaret yana dauke da wata matte-black metal gate with the emblem of a small eight-point star. Only members na wajen sukasan address snn ba a iya shiga saidai wani dan wajen ya kawoka ciki.

special waje ne da boyayyun Business magnates, young heirs of wealthy families,Oil & real estate families, crown princes, nd Private bankers da
many Diaspora billionaires suke zuwa when they’re in kano town.

Jamal ne dakansa ya fita waje ya jawo ibaad ciki, just few members wanda kowa abunda ke gabansa yakeyi ne awajen

waje is god damn private nd breathtaking, All-black marble floors Gold trims, silent lounge with dim amber lighting ga lumtsa lumtsan Leather chairs, da private conference room da kuma babban library with only business and philosophy books sai cocktail bar da suke cema Mirage Counter...

duk wayewar ibaad saida yajishi kamar ba a kano state yake ba, sai kuma ya tuna taken garin wai koda me kazo an fika nd na today he don confirm dat statement.

wani hali guda daya jamal moriki yake dashi wanda shine yake balain tafiya da ra'ayin ibaad wato humbleness da bala'in saukin kai ga iwa uba aji da yin magana acikin nitsuwa bada jiji dakai ba.

jamal ba irin gayun nan bane wanda arxiki da daukakrsu ke rufe musu ido su raina wani ko suyi girman kai ko show off, kyakkwan tarbiya ce mai rai da lafya ajikin yaron he is calm, jovial and classy..

royal blue suit yasa me balain tsada amma bamai hayaniyan design ba,tunda ibaad yazo suka zauna su biyu a mirage counter suna shan mocktail, anan yafara introducing kansa properly ma ibaad

jamal moriki yaro ne ga wani shahasharen me kudi da ya rasu kwanan nan, bada jimawa ba. he is the only son of his mother lady diana, after suffering in court da kawunsa akan arxikin babansa daya rasu shine harya samu aka
damka masa ya hau kai at this young age dan da wata biyu kawai yagirme ibaad a shekaru

saidai yanayin yadda yake maganansa da tulin kamiya da kuma nitsuwa tareda ilimi u cant just deny his early maturity aura.

a yale uversity dake U.S yake kan karatunsa, while still tryng to run his fathers business conglomerate in the U.S and Dubai. maman sa ne kawai take saka masa ido akan komi shiyasa baya son ya rasata dake tana da boyayyen ciwon zuciya wanda a sanadiyar mutuwar babansa ne akasan ma tana dashi
....sunxo kano ne sabida anan ne shima aka haifesa asali ma anan ya fara tasowa a family house din maman sa gidan mahaifinsa ne kawai yake abuja.

wasa wasa suka sha hira dan ibaad  baiwani sha wahalan bayyana masa kansa ba dan yana ambatar sunan familynsu na almansur jamal ya cankosu  yace masa ai tun suna yara sukasan kawunsa prof zayyanu sabida ta hannun prof din marigayi baban jamal alhaj moriki yake samun wasu intnl contract da kudadensa ta sauki.

it became so easy for them to trust each oda at first manly date dinsu,..daga haka jamal yay requesting ko zasu dawo abokai sabida baisan kowa a kano ba kuma bazai iya trusting cousins na jikinsa ba duba da suna nuna maitarsu akan arzikin da aka daurasa akai yanxu..


ibaad baiwani bashi fuska a farko sosai ba, harsaida suka dan dau lokaci suna yawan hanging out tare suna hira suna dada fahimtr juna within 3 weeks ibaad ya fara sakan jiki dashi musm ma da har cikin family saida jamal ya kaisa, nd jinin mum din jamal din bakaramin haduwa yay da na ibaad ba, wnn sanyin aji da yadda yake kame kansa yasa ta jima da ganewa tabbas ba karamin tarbiya aka bashi ba hala bazai cutar da danta ba.

dama shi sabo ga maza
bawani abu ne mai daukar lokaci ba nez musmmn irin nasu na yaran masu shi, they are always talking about bigger things, educations, cool adventures, da abunda duniya ke ciki..busines jamal yake karantawa. most time zaizo gidan bappa zaidu da yamma ya jira ibaad a masallaci, ko ibaad ya same sa acikin black magnet a regular hangout dinsu....
#DONT BE SHY FINE GEH OYA POST UR COMENT SABIDA DA DARE A SAMU BONUS


idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025