SADAUKARWAR SO.

02

by @jamilaumarjanafty

SADAUKARWAR SO..!!

(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)

Wattpad:@Jamilaumar315

Mallakar:Jamilaumar(Janafty)

Page2️⃣

Kullum Maryama Tana Hanyar Zuwa Ririwai ganin Mastur wanda Tuni Baba Jibo yayi mai Huduba da sunan da Maryama ta Zabamai kowa ya sani Zabin Maryama Shine Zabin Habibu.

Har sai da akayi suna kana Ta Zauna agida anyi Shagali Daidai Gwargwado na masu karamin Karfi an yankama Mastur katon Ragon Sunansa wanda Maryama ita ta Kiyawata Ragon a Chan Maruka Daman Tun Samuwar Cikin Hajarah Din Tace Ragon da akuyarta ta Haifa na Sunan Abunda Hajara ta Haifa ne kaunar Dake Tsakanin Habibu da Maryama Wata kaunace da Allah ne kadai yasan Yawanta.

Inna Hasiya ce ta Cigaba da kulawa da Hajara da Mastur,Ayya ma Sai dai ta Leko su Inno kuma Bata zo ba Tana yi ma Inna Hasiya kara da kuma Ayyah Kuma Alhamdulillah Hajara Tana samun Dukkan kula Bata komai Inna Hasiya Ke Duka ayyukan Gidan Hajara ko Tace Zatayi sai Ta Hanata Gefe Daya Habibu na Tsaye da Duka Kafafunsa na ganin ya Yalwata Ahalinsa Gabadaya Duk da Baba Jibo Karfinsa ya Fara karewa ammh Karfin Noman na nan Tare Dashi,Baya barin Habibu Ya Tafi Gona Shi kadai Koda bazai yi wani aiki ba sukan Tafi Tare Domin ya Taimakamai suna Noma koda ba Damuna ba sukan Noma Irin su Tumatir da Sauransu kafin Damina Ta zo.

Koda Hajara Tayi arba"in da Haihuwa sai wanda ya ganta tayi Kiba ita da Mastur kamar ba su ba sun samu kulawa Sosai kuma suna cin abinci mai Gina Jiki Sai kuma akayi Sa"a Nonon Hajara mai kyau ne Tuni Mastur sai Kiba yake Maryama kuwa Duk sati sai Tazo Garin kawai Domin Taga Mastur wanda Soyayyar Datake yi mai Tun yana Ciki ne Har yazo Gidan Duniya.

Sai Hajara Da kanta takai ma Inno Mastur Ta gansa ta Daukesa Ta sakamai albarka Tare da Fatan Rayuwa mai albarka Chan ta wuni Tare Dasu Suna ta ina suka saka da ita ita da Mastur irin Soyayyar da Kowa ke Nuna mata ita da Abunda ta Haifa na sakata kuka Habibu Kullim ya Dawo Haka Zai Dauki Mastur ya Dinga mai wasa Tun yaron baya ganewa Har ya Fara gane mai kula Dashi Sosai Wani Lokacin Hajara ita yar kallo ce Domin Daga Inna Hasiya Har Baba Jibo Suna Rawan Jiki wajen Daukan Mastur yaron ya Shiga Ran kowa Saboda Nasabarsa da Kyansa Tun yana Jaririnsa.

TUSHE..

"JIBRIL Baba Jibo da Inna Hasiya sune Asalin iyayen Habibu da Maryama su din Dukkansu Haifffun Garin Doguwa Local Goverment Dake garin kanon Dabo awata anguwa mai Suna Ririwai.

Tsakanin Inna Hasiya da Baba Jibo auran Zumunci ne Tunda Abokan wasa suke da Juna iyayansu Tun suna da rai suka Hadasu Zama waje Daya saboda ganin Dacewarsu,Tun iyaye da kakanin Sana"ar iyayen Su Baba Jibo Noma ce da Kiwo kuma ita suka gada Dayake alokacin Ilimin Zamanin nan bai wani yawaita ba Sai karatun allo Daka Sauke Zaka Fara Noma Domin itace Sana"a Lokacin Da kowa yasan iyayenmu Musamman ma na kauye Dashi.

Tun bayan Auran Baba Jibo da Inna Hasiya Allah ya Dauki Ran Iyayan Baba Jibo Daman Inna Hasiya Iyayan Baba Jibon suka Riketa Ta rasa nata iyayan Tun Tana karama sai ya zamanto sun Rumgumi Maraicin su Dagasu sai Daidai kun yan"uwa da suka Rage wasu duk sun Tsallake Zuwa wasu garuruwan Domin neman nakai kuma Tunda suka Tafi basu Dawo ba.

Inna Hasiya itama ta Dade bata samu Haihuwa ba Domin sai da suka Fitar da Ransu kana Allah ya basu Habibu wanda Haihuwarsu yazo musu da wani Budi a Shekarar Amfanin Gona yayi kyau Baba Jibo Da abokinsa Mallam Yahaya sun samu Alheri sosai Shiyasa Tun Lokaci Baba Jibo Ke Kiran Habibi Jarumi kuma Gwarzo.

Tun Haihuwansa suke matukar sonsa Haka Habibu ya Taso Cikin Gatan Duka iyayansa Gefe Daya kuma ga Aminin Mahaifinsa Baba Yahaya da Inno da Ayya suma ba"a barsu abaya ba wajen kula Dashi Dayake Zumunta ne na Makota ka wanda alokacin Bayan Makocinka Shine Babban Amininka kuma Dan"uwanka Abokin Shawaranka.

Habibu ya taso Shi kadai ne agaban Inna Hasiya kuma Shi mutum ne mai kulafuncin Yan"uwa sai dai Allah bai bashi ba Tun yana ma Inna Hasiya kukan ta sama mai kanwa Har ya Gaji Lokacin da aka Haifi Maryama Habibu nada Shekara Tara a Duniya ne Lokacin yana Makarantar Allo ya Hada karatunsa na Izifi Talatin,Alokacin ko su inna Hasiya sun Cire ransu da samun wani karuwa sai gashi Allah ya basu Maryama Farincikin da Habibu yayi ko Inna Hasiya da Baba Jibo basu yi shi ba Haihuwan ta kasance shi akayi mawa.

Domin Tun da Maryama Tazo Duniya alhakin kula da ita ya koma Wuyan Habibu MKarantar allo Kadai yake iya Tafiya yabar Maryama Bayanan kuwa Yana Gida Tare da ita Tun Tana Wata Hudu a Duniya Da Rigima da komai Yake sakawa Inna Hasiya na goyamai Maryama Da karfi da yaji ya koya mata zama Komai ya samu Baya iya Cinsa shi kadai Sai ya Rage ma Maryama Tun kafin Maryama ta isa Fara cin Abinci Habibu ya Fara bama Maryama kayan kwalama Batare da Sanin su Inna ba sai Dai kawai suka ga Maryama Bakinta ya Bude da Cin Abu komai aka bata.

Maryama da Habibu ta Fara Bude Ido a Duniya,Tun Tana Shekara Daya a Duniya Ta Fara Tafiya Ko"ina kuma Habibu Zai saka Kafa Bata yarda sai ta Bishi In ko yamata wayau ya Tafi makarantar Allo bata da ita ba In ta Fara kuka sai ya Dawo Taji Muryansa Ya Dauketa ya Lallasheta ya bata Sweet din Daya Siyo mata take yin Shuru Ko Inna Hasiya ko Baba Jibo Bata yarda da kowa sai Habibu Mutane suna mamaki da Jinjina ma Wannan kaunar Dake Tsakanin Maryama da Habibu.

Tun awannan Shekarun nata Habibu ke Daukanta yana Zuwa Allo da ita Saboda In bai je da ita ba Ta Rika kuka kenan akwai Ranar ma Data Fakaici Ido Tabi Bayansa sai dai Tsinto ta akayi Tabi Hanya Tunda Ranar Bai kara yarda ya Tafi ya barta ba Duk inda Zashi da ita yake Tafiya Tun Alarammah na Fada har ya Daina Saboda Maryama Bata yarda da kowa sai Yayanta Habibu Kaunace Daga Allah data kuma Fara Tun Tasowarsu.

Haka Rayuwarsu Ta Cigaba da Gudana Cikin kaunar Juna Har Habibu ya Sauke alqurani aka yayeshi sai ya zamana Maryama kadai ke zuwa makaranta Shima ssi da aka sha Daga Domin Da Farko tace bazata kara zuwa makarantar ba sai da yayanta Habibu Shi kuma Lokacin ya Fara Bin Baba Jibo Gona sai yamma suke Dawowa Maryama wuni take kuka Kamar Wata wacce Za"a yanka In Ta Dawo Daga allo Bata ga Yayanta ba Inna Hasiya tagaji da Lallashi ta Fita Batunta Sai ya Dawo ya Lallasheta Take yin shiru Dole ta Hakura Tunda Inna Hasiya tacr Tana mace baza ta Rika Bin su Gona ba ta zauna agida.

Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Tafiya Cikin Soyayya da kaunar Juna Daya baya son bacin Ran Daya musamman ma Habibu Da baya kaunar bacin ran maryama ko kukanta itama Haka Sai dai kuma Duk da wannan Kaunar Dake Tsakaninsu Bai Hana Maryama ta Girmama Habibu a mtsayinshi na yayanta Datake matukar Ji dashi.

Tana da Shekara 14 aduniya ta Sauke Qur"ani Akayi Walimar Saukarsu a makarantar allonsu Wanda Habibu yayi mata rawan Gani Sosai wajen Walimar Saukarta Wanda ya saka Maryama farinciki sosai Zuwa Lokacin kuma sai Manema Daga Ko"ina suka yi ma Maryama chaa Tunda alokacin Yara mata basa wuce Sa"anninta ake Aurar dasu Tunda ba karatun Boko suke yi ba.

Duk cikin manemanta Mutum Daya ta yarda Take kulawa Sule wanda yake Mutumin Maruka ne Shagon kayan Kwalliyan mata gareshi anan cikin kasuwar Ririwai,Maraya ne Mahaifinsa ya Rasu sai dai Yayyinsa Maza Suna Saune a Famiy House dinsu ne gidan Gado Shi da Mahaifiyarsu Da suke Kira Goggo Sule Shine karaminsu yana da Yayyi mata Da Maza Dukkansu su Biyar ne wajen Goggo Mata Biyu Maza uku.

Ganin Maryama Ta fi Son Sule yasa Baba Jibo da Mallam yahaya suka yi Bincike akansa kuma suka samesa da Nagarta Hallaye nan da nan suka bashi Izinin Turo mgabatansa Lokaci Habibu nada shekara 24 aduniya ya zama Matashin Saurayi,Cikin Lokaci Kadan Sule ya Turo mgabatansa aka Gudanar da Neman aure aka Saka Rana Har acikin Ran Habibu bai so Maryama Tayi Aure Nesa Dasu ba yaso Kusa da Gida Saboda ya Shaku da ita Zai ji ba Dadi in Tayi mai Nisa Sai Dai kuma bashi da tacewa ganin Maryama na kaunar Sulen kuma ya Tabbata in ya Furta Baya son ta aureshi Ko Maryama na Mutuwar son Sule ya Tabbata Saboda Farimcikinsa Zata Fasa Shi kuma Bazai so ya zama Sanadin Ruguza Farincikin Yar"uwansa ba kuma Tilon kanwarsa ba.

Haka akayi Auran Maryama aka kaita Maruka sun sha kukan Rabuwa ita da Habibu,Maryama Tayi kuka sosai Kuma Ta makale ma Habibun Sai da yaje dashi aka kaita Chan Maruka Gidan su Sule Inda zai zauna a Babban Gidansu Tun Wannan Zuwan Mahaifiyar Sule ta Fara yada mgana kan Wani Sabon Salo ne Za"a kawo amarya Harda Kato ana mata Bayani Yayanta ne, Bata ma Tsaya Saurara ba Domin Har acikinta Ranta Bataso Auran Sule da Maryama din ba an dai fi karfinta ne.

Tun da Maryama Ta auri Sule Take Cikin Mtsala Da goggonsa Mace ce mara Hakuri gata Fitinanniyar Bata kaunar Maryama Ko kadan kuma Sun Hada kai da matan ya"yanta yayyin Sule suna Muzguna mata Sai dai Tsiranta Daya Mijinta yana Matukar sonta Burinsa ya kyautata mata Saboda Habibu ya Jadaddamai ya Rike mai kanwarsa Amana Domin Duk Duniya ita kadai garesaa kuma baya son wani abu ya sameta bama Domin haka ba Yana Tsananin kaunar Maryama Tun baya Fahimtar Halin Dayake Ciki Har ya Fara Fahimta sai yaji ya kara Sonta Domin bata Taba gayamai Tana Fuskanta wata mtsala ba ballatana Kuma in taje ta gayamasu Inna Hasiya wani Abu Koda sun Tambayeta ya Zaman ta da Dangin Mijinta sai tace Komai Lafiya bata Taba Bude baki ta Fadi wata mgana Saboda bataso su Shiga Cikin Damuwa Saboda ita ba.

Habibu Shi ya Fara karantar Halin da Maryama ke Ciki..Domin Daman Duk Sati yana Hanyan zuwa Gidan Maryama Din Dauke da kayan kwalaman Dayake Siya mata na Tsaraba Duk Abunda yasan Tana so in ya samu kudi zai Adanasu baya Tsinana ma kansa komai sai Maryama,Tun yana zuwa yana Tambayanta me ke sakata Rama tana cewa bakomai Har dai Ranar yaje Gidan ya iske Goggo Ta tasata Tana Zaginta Maryama na Duke Tana kuka Ranar Duka Gidan sun ga Kalan Fushi da Bacin Ran Habibu Bai tsaya Jin ba"asi ba ganin Maryama na kuka yace ta Hado kayanta Su Tafi Gida Bata da yarda Zatayi Haka ta Hada Ta Bishi ita kanta Goggo sai Ta Raina kanta Daga baya.

Sai dai su Baba Jibo suka Gansu kwatsam,nan Habibu yake Maida musu abunda yafaru Inna Hasiya ta Fara Fada Tana Fadin bai kyauta ba Taya zai Dauko ta batare da Izinin mijinta ba Haka ta Dinga Fada Tana Nuna Bacin Ranta,Shi dai Habibu Bai ce komai ba Baba Jibo ma bai yi mgana ba Saboda Inna Hasiya ta Rigatayi mgana kuma Bayaso Habibun yayi wani Tunani Tunda Maryama kanwar sa ne ko suna da rai Shi mai Tsayawa kan mganar Maryama ne.

Adaran Sule ya zo Ririwai yana Rokon su Baba jibo suyi Hakuri su bashi Maryama su koma,Baba Jibo yace basu zai bama Hakuri ba Habibu zai bama Hakuri mgana na Hannunsa Dole ya Duka yana Rikon Habibu Shi kuma yace Zai Tafi da Maryama ammh Da Sharadin wlh ko kallon Banza aka kara mata ba Zagi ba sai ta bar Gidansa Ba Dole ba wai Basu sonta bane suka Aura mai ba kuma ba Jaka suka kai mai ya Dai ja mai kunni Daga karshe Sule yayi alkawarin Insha Haka bazata kara Faruwa ba,Cikin Girmamawa Sule ya Dauki Maryama suka koma Washegari kuma yayi Tsiya agidan ya kuma Tsoratar da Goggo Cewa in aka kara Takura ma Maryama Wlh zai Dauketa su bar garin Jin haka yasa ta koma Tayi Lambo Sanin Halinsa gashi kuma Auta ne tana Matukar Ji Dashi Bata son yayi mata Nisa.

Dalilin Faruwar haka yasa Maryama ta samu yanci Duk da Dai anayin ammh ba kamar baya ba Sai ta samu kwanciyar Hankali Ta maida Jikinta Har Aran Habibu yake jin Dadin ganin Maryama Cikin Farinciki Sai dai me Shekaran Maryama Biyu da Aure bata Taba ko batan wata ba Dalilin Daya saka Goggo Ta kara yunkurowa kenan Tana Fadin Maryama Juya ce bata Haihuwa,Tun abun baya Damun Maryama har ya Fara Damunta Itama Tana so ta Haihuwa ammh kana naka Allah na Nashi ne har ta kwarari Shekara Biyar Gidan Sule Bata Taba ko da Batan Wata ba zuwa Lokacin abubuwa sun Riga sun gama Rikicewa Goggo Ta Daka Tsalle tace sai Sule ya kara aure shi kuma yace bazai yi ba,Tun Maryam Din bata saka baki ba Har tazo ta Fara Rokon Sule Daya ji mganar Goggo ya kara Aure ko Zata samu Sassauci Daga Goronta mata da gorin Mutanen Gidan.

Daga bangaransu Baba Jibo basu da yarda zasu yi da Halin da Maryama ke ciki Sai dai suna Tayata addu"an Allah ya bata Haihuwa Tunda shi ne mai badawa Habibu kuwa Duka Salolinsa Maryama yake sakaawa Yana Rokon Allah ya bata Haihuwa sadaka kullum sai yayi Domin Farincikin Maryama Shine nashi Cikin wannan Halin Goggo ta matsa Sai da Sule ya kara aure da yar Aminyarta Zainabu kuma Ta tare nan kusa da Dakin Maryama din.

Auran Sule da Wata Biyar Habibu ya auri Hajara Diyar Mallam Yahaya wanda Hadin na Baba Jibo ne,Habibu yaro ne mai Biyayyah bai taba ma Iyayansa Gaddama ba Ballatana Hajara Data kasance yarinya mai kunya mai Hakuri alokacin Tana da Shekara 16 ne akayi musu auran Suka Tare nan Gidan Inda Baba Jibon da shi Habibun suka Gida Dakuna Biyu Dake Barayin Inda Habibun ke Zaune Ginin Jar kasa da mai yaben ganye aka Shafeshi da Farin Fentin Farar kasa na Mutanen kauye

Lokacin Maryama ta koma Maruka Bayan Tazo Bikin Yayanta Habibu ta iske Zainabu Nada Ciki Lokacin Gori da Habaice Habaice duk ya Tashi Sai Dai maryama ta koma Daki Tana kuka Domin Da Zarar ta Fito sunanta Juya Bata samun wani Jin Dadi sai Sule ya Dawo wanda Daman Goggo Tuntuni Take Fadin Ta asirceshi ne baya ji baya gani sai akanta.

Haka Zainabu ta Haifi yarta Mace Maryama na cikin Halin Tsagwama da Bakinciki Ko yar ma ba"a bataa ta Dauka ba,wai kada ta kasheta saboda bakincikinta Ranar tayi kuka kamar Ranta zai Fita sai dai Da Sule ya Dawo yaji Labari sai ya kara musu yace sunan yarsa Maryama aikuwa kan Haka sai da Goggo Ta mareshi Shi kuma yace bazai Sauya ba Maryaama Ta Riga ta sani Sule na Sonta kuma Har Abada bazai Taba Juya mata baya ba Shiyasa Koda Tana Cikin Damuwa da Zarar ya Dawo sai ta Kirkiro Fara"a da Annushuwa ta Dora saman Fuskarta aranta Bata Fatan Taga Damuwa akan Fuskar wadanda baza sukuni in suka ganta Cikin Damuwa Wato Yayanta Habibu da Megidanta Sule.

Daga Barayin Hajara ma Shuru ne ba wani Labari Su basu Damu ba Tunda sun yarda Allah ne bai bayarwa ammh Kuma Habibu Shima yana son Haihuwa Kodomin ya mallaka ma Maryama Abunda ya Haifa ta Daina kukan Rashin Haihuwa aduniya sai kuma Allah bai bashi Haihuwan da Wuri ba, ammh bai gaji ba yana gayama Allah akoda yaushe

Bayan Auransu Ba Dadewa Allah ya Dauki Ran Mallam Yahaya Hajarah Inno da Ayyah sai yayarta karime kadai suka Rage mata Sauran kaneenta yara ne itace Babbansu sai dai Bata da wani Damuwa Habibu dasu Baba Jibo sun kasance mata tamkar wasu garkuwa gareta Maryama kuma Ta kasance Kamar wata yayarta Shiyasa ma take kiranta Adda Maryama.

Kwantashi ba wuya awajen Allah har Zainabu ta kara Haihuwan Yarta Mace taci Sunan Goggo Mardiya,Maryama Shuru wanda ba Domin sule na kaunarta ba Tuni Goggo Da Zainabu sun yi Sanadiyar da Ta koma Gida Sai dai sun yi sun yi sun gaji Maryama ta Zame musu Ciwin ido basu yarda zasu yi da ita acikin wannan Halin ne Ciki ya Bulla Jikin Hajara Murna ba"a mgana Tun Daga Lokacin Maryama Take Shirin Tarban Abunda Hajara zata Haifa Cikin Kiwonta Ta Dauki Rago Daya ta wareshi na Sunan Abunda Hajara Zata Haifa Ko Habibu Baya Dawainiya da Hajara yadda Maryama take yi Ko bazata zo ba in Sule zai zo Zata aikosa da su Goriba aya da Sauransu aka wo ma Hajara Su Baba Jibo suna mamakin wannan kaunar Dake Tsakanin Maryama da Abunda ke Cikin Hajarah.

Haka Hajara Tayi ta Ronin Cikinta Da Taimakon Inna Asiya da Habibu Da Maryama Har Cikinta ya isa Haihuwa ta Haifi Mastur kamar yadda Maryama ta Zabamai suna da kanta Wanda Maryama bata iya Runtsswa ba Tun bayan da Habibu ya Kirata yace Hajara na kan gwiwa kuma Farinciki bai Saketa ba sanda ya kirata yace mata ta Sauka Ta gode ma Allah kuma Taji kaso mafi yawa Daga Damuwar Rashin Haihuwanta ya Ragu Tunda yau Taga Da"an Dan"uwanta Datake matukar so kuma Take ji Dashi.

Wannan kenan..!

*****

Haka Rayuwa ta Cigaba da Gungaruwa Cikin Koshin Lafiya da Tsarawan Ubangiji,Hajara na Cigaba da kulawa da Mastur haka ma su Inna Hasiya ba"a barsu abaya ba Balle sun samu Jika Lokacin da karfinsu ya Fara karewa

Bangaran Habibu ma ba"a barsa a baya ba ga Maryama wacce kusan kullum tana Hanyan zuwa ganin Mastur wanda yaron ya Shiga Ranta Kamar ta Daukesa Sai dai bata da yarda Zatayi Tunda bata da Nonon da Zata bashi,Abunda bata sani ba Habibu yayi ma kansa alkawarin Ko iya Mastur kadai zai Haifa zai mallakama Maryama Shi kuma ya Zauna Haka ya gwammace ya Cigaba da ganinta Cikin Farinciki Har Abada Daya ganta Cikin kunci Da Damuwa Shi kadai ya yanke ma kansa Hajara na yaye Mastur zai Damkama Maryama Shi Halas malak.