SADAUKARWAR SO.

03

by @jamilaumarjanafty

[12/23, 6:59 PM] Janafty: SADAUKARWAR SO..!!

(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)

Wattpad:@Jamilaumar315

Mallakar:Jamilaumar(Janafty)

Page3️⃣

Mastur nada wata goma sha takwas Hajara ta yayeshi a kuma lokacin ne Habibu ya bayyana ma Iyayansa da ita kanta Hajara Alkawarin Daya Dauka na Mallakama Maryama Mastur har Abada.

Dukkansu sun Nuna amincewarsu Hajara kuma Daman ita mai Biyayyah ce ga Lamarin Habibu sai dai Inna Hasiya Ta ce baza"a bama Maryama Mastur yanzu ba yayi kankanta abari yakai ko Shekara Biyar ne ammh ayanzu akwai Cutarwa Araba uwa da D'anta a irin wannan Lokacin Jin haka yasa Baba Jibo ya mara mata baya Dole Habibu ya yarda da Shawaransu sai sukayi Shuru da bakinsu basu Gayana maryama din ba.

Sai dai Tana jin an yaye Mastur Ta Shiryo tazo kan zata Tafi Dashi Chan Maruka ta yayeshi Habibu ko Hajara ba wanda yayi mata gaddama Suka Hada mata kayan Mastur suka Dankamata Daman ya saba da ita ganin itace yasa bai ma yi Rigima ba Duk da Tun yana jaririnsa bai da yawan Rigima da yawan kuka Maryama Taji Dadi Harda kuka Sulaiman yazo ya Dauketa suka koma Goggo Dataga Maryama Tazo da Mastur Sai da Tadinga mgangunu Tana Fadin Sai dai Taga ana Haihuwa ita kam Juya ce Harta Zainabu ta gama Raina Maryama sai dai Saboda Sule yasa bata tankasu Ta Cigaba da Sabgarta na kula da Mastur Datake Jinsa kamar Dan Da tahaifa acikin cikinta.

Mastur bai dawo gida ba sai da ya Shafe wajen wata Biyu a wajen Maryama kana ta Dawo Dashi Wanda kamar kada ta Dawo Dashi Saboda yadda suka saba Da juna Harta Sule sai da yaji kewa komai ita kemai Bata Gajiya Watarana Har Hawaye Sule yake mata a Boye yana Fatan Allah ya bama Maryama Haihuwa itama Taga kwanta Aduniya Lokacin Data Dawo da Mastur ba Domin mganarsu Inna Hasiya ba, da Tuni ya ce Maryama ta koma da Mastur Ya bata Shi ta Rikeshi sai bazai iya ja da Abunda iyayansa suka ce ba, Shiyasa yayi Shuru da bakinsa ammh Tsausayin kanwarsa na nan Damkam aransa wanda Ko Barci baya Barinsa yanayi Cikakke.

Haka Rayuwa ta Cigaba da Tafiya da Dadi ba Dadi,Acikin Hakane Allah yayi ma Mahaifiyar Hajara Rasuwa Inno Sakamakon amai da gudawa Kafin Safe ta Cika Sosai Hajara da Habibu suka ji mutuwarta Inna Hasiya da ayya sunyi kuka sosai na Rashin Inno Baba Jibo Shi ya kasance kamar wani Shakiki Har akayi Sadakar bakwai aka waste Hajara ta koma Marainiya sai da Habibu bai barta ta kara kukan Maraici ba ya Tare mata Dukkan Gaban da Zataji yau Bata da iyaye.

Mastur Nada Shekara Hudu a Duniya Hajara ta kara Samun wani Cikin sai dai bai zauna ba Tayi Barinshi Haka Allah ya Tsara ammh Habibu yaji Ciwon Rasa Gudan Jininsa Sosai Fiye da Tunani Domin bai Dora ma kansa Kulafuncin Mastur ba Domin Maryama zai bama Shi Halak Malak.

Cikin Gudurin Allah Hajara ta kara samun wani Cikin Sai dai wannan karon Kusan Lokaci Daya Suka samu Ciki da Maryama Allahu akbar bawa Kada ya Cire rai da Rahamar Ubangiji..

Maryama Tayi kuka Kamar Zata Shide Saboda Murna Sule kam Kamar ya Zuba Ruwa akasa yasha Haka Habibu wanda ya bar Murnan Cikin Hajara ya koma Murnan Samuwar Gudan Jinin Maryamaa,Chan gidansu Sule kuwa Goggo da Zainabu kamar Bakinciki Zai kashesu Domin alokacin ma zainabu na Shayar da karamin Danta mai Suna Auwal Goggo Bata so Maryama ta Haihu ba Har Abada sai dai Kana naka ne Allah na nashi..Na Allah kuma Shine Daidai.

Sai kuma Tunda Maryama ta samu Cikin nan Lafiya yayi mata karanci Yau Lafiya Gobe Ciwo Cikin yana da Laulayi Sosai ta kwanta asibiti yafi Sau Uku Saboda Rashin karfin Jiki Bata samu Zaman lafiya ba sai da Cikinta yakai Wata 6 alokacin ne kuma Hajara Itama ta Sake Barin Cikinta wanda Tasha Wahala kamar bazatayi rai ba Saboda cikin ya zama Gudun Jini Dakyar ta Rayu Wanda Har su Habibu sun Fidda Rai da Hajara sai dai Rai mai alfarma sai gata tashi ammh fa an kashe kudi Tunda Har sai da aka Dangana da Asibitin General na Garin Doguwa,achan ne likitoci suke gaya musu Da wahala Hajara ta kara Haihuwa Saboda Mahaifiyarta Tana da Rauni ba Lalle bane in ta samu Ciki Ya zauna Har ta Haifeshi Saboda Raunin Mahaifan Dake Tare da ita wannan Labarin ya sanyayama su Inna Hasiya Jiki Suna ganin Tayaya Za"a Raba Hajara da Mastur alhalin kuma ba lalle bane ta kara Haihuwa sai dai jin Dadinsu Daya Cikin da Maryama ke Dauke Dashi Kila zai Tada wannan alkawarin da Habibu yayi Tsakaninsa da Ubangijinsa.

Lokacin da Hajara Taji Abunda Likitoci sukace bata Damu ba ta Fauwalama Allah Lamarinsa,Sai dai akasan Ranta Taji ba Dadi Ko bakomai Tana so Ta kara Haihuwa ko Saboda Habibu da Taga ya Damu Tun Lokacin Datayi barinta na Farko. ammh bata da yarda Zatayi Tunda Haka Allah ya Tasara mata Sai dai Tana yi ma Maryama Fatan Allah ya Sauketa Lafiya.

Tunda Maryama ta Shiga watan Haihuwanta sai Lafiya taki ta Kullum Cikin Ciwon kai da Jiri Ashe Tana da Hawan Jini iyayenta ko Habibu basu sani ba Daga ita sai Mijinta ganin Haka yasa Habibu yayi ma Sule mgana kan yana so Maryama ta Dawo gaban Inna Hasiya Saboda Ta samu mai kula da ita Tunda agidan sai dai Sule ya Taimaka mata ba dai Goggo Ko Zainabu Sule bai yi Gaddama ba ya Amince sai dai Goggo Taso Ta Hana Habibu bai tsayama Sauratanta ba Ya samu Tashar Mota sukaje har Gidan ya Dauko Maryama da Duka kayanta Dana Haihuwanta Data Tara Zuwa Gida sai dai su Inna Hasiya suka gansu kwatsam Hakika kuma Taji Dadi Domin Tana Tunanin yadda Maryama Zatayi Haihuwan Fari achan ba wani nata akusa Har Tana Tunani  Tayi ma Ayya mgana Taje Chan Maruka har Maryama din ta Haihu sai gashi ma Habibu ya gama mgana.

Nan Dakin Dake kusa da na su Habibu aka gyara ma Maryama Take Zaune Jiran Haihuwa kowa kula yake da ita ba Ba Baba jibo ba Inna Hasiya ba ba Ya Habibu ba ba Hajara ba Mastur kuwa murna ta kamashi Sai Tsalle yake Goggo Maryama ta Dawo Gidansu da Zama Tunda ta Dawo ya koma Dakinta da kwana ance yaro ma yasan mai Nuna masa kauna Shiyasa Tun yara yaronsa ya Shaida kaunar da Goggonsa kemasa.

Kullum Sule kafin ya Tafi Gida sai ya Biyo ya ga Maryama ya kawo mata tsire ko Nama bata ma wani ci Sai dai Mastur Da su Inna Hasiya Kwanan Maryama Goma agida Ranar Jumma"a da yammah ta Fara Naguda,Nagudan Data Dauketa Har Washegarin asabar bata Haihuwa ba,an kira anguwan zoman Gida sun kasa Kuma gashi ba wanda yasan Tana da Hawan Jini Habibu bai kwana agida ba agarin Doguwa ya kwana yaje siyar da Hatsi Daya Dawo ne yaga Halin Datake Ciki ya Fara Fada yana Ta ma Sule Fada tunda Tun da Maryama ta Fara Nagudan aka Kiraahi aka gayamai Inna Hasiya ne da Ayya keta Shiga da FitaHajara na waje Rumgume da Mastur Dake kuka ganin Halin da Maryama ke Ciki..

Habibu ko Hutawa bai yi ba ya je ya samo Mota suje asibiti kafin ya Dawo Maryama ta Haifi Danta Namiji sai dai kuma me Tuni Jini ya yanke Mata Sai kuma ta Fara Jijjiga Tana Datse Bakinta da Harshenta Cikin Tashin Hamkali Ayyah ta Fito Tana kuka Da Neman Taimako Gabadayansu suka Shiga Dakin Har da Baba Jibo da Hajara da Mastur da Sule ganin Halin da Maryama ke Ciki yasa sule ya Duka da Jinin da komai ya Rumgumeta yana Kiran sunanta Inna Hasiya ita ta Dauki Jaririn Dake kuka ta yanke mai Cibi Ta nadeshi Cikin wani Zani Tana Tsaye Tana kallon Maryaman ta kakkafewa kawai sai ta Juya baya Tana Sharan kwallah Hajarama kuka Take Mastur kuwa Duk da yana karami ne ammh ya Fahimci wani abu mara kyau na Faruwa Baba Jibo ne ya karisa kusa da ita yana Tofa mata addu"a yana Kiran sunanta.

Habibu Dayaje ya samo Mota Da Gudu ya Shigo Gidan kamar zai Kifa sai dai yana Sawo kansa Dakin Mala"ikun Daukan rai suka Karisa Zare Ran Maryama Allahu akbar Kullu Nafsin Zaki"katul maut kowani Rai sai ya Dandani zafin mutuwa,Tun daga Bakin Kofar ya Tsaya Cak ganin Inna Hasiya na Hawaye Sule na kuka Baba Jibo na Sharan kwallah Hajara da Ayya na kuka Mastur ma haka sai yaji Kafafunsa sun Daina Daukansa Maryama ya kura ma Ido ganin ta Kwance Jikin Sule idanuwanta sun kafe sama bata Numfashi Tuni yaji wani Dum..! Dam..! Bai san ya akayi ba sai dai yaji Duhu ya mamayesa Lokacin Dayake neman karisawa ga gawar Maryama Yaji Salatin su Inna Hasiya Daganan bai kara sanin Inda kansa yake ba sai bayan Awa Daya da ya Farfado ya gansa kan Jikin Baba a tsakar Gida Ga Gida ya Cika da mata sai Koke koke akeyi sai komai ya Dawo mai Sabo Cikin Mutuwar Jiki da kunar Zuciya ya Mike Zaune yanabin Kowa da kallo kamar yadda suke masa kallon Tsausayi Idanuwansa ya Sauke kan Hajara Dake sanye da Hijabi Tayi kuka Har tabama uku Lada Mastur na Jikinta Shima Duk Hawaye sun Bushemai Gabansa ya kara wani Rugu Rugu bai Samu Zarafin mgana ba wani makocinsu ya shigo Dauke da Likafini da Turare da ganye magarya ya mikama Baba Jibo Batare da yayi mgana ba shi kuma ya Mike ya isa ga Kofar Dakin Maryama ya Kira Ayyah wacce ta Fito Tana goge kwallah ya Mikamata ya juyo Sai matan Dake waje suka Fara Fadin"Allah ya Jikan Maryama..! Allah yasa aljannah ce makota..Tayi Shahada ta Haihu Ko abunda ta Haifa bata gani ba Allah yayi mata Cikawa.."

.mganar haka ta Rika mai Amsa kuwa acikin kunnuwansa Yanzu Shikensn kanwarsa Maryama ta rasu..? Innalillahi wa'inna illaihirraju"un..Allah gareka muke kuma gareka zamu koma..Allah ya jikanki Maryama Allah ya sadaki da mala"ikun Rahma.

Yake yake ta Fada acikin ransa Mikewa yayi ya Fice matan suka Bisa da kallon Tsausayi.

Waje ya Fita yaga Mutane Dayawa a kofar gidan Duk sun yi Jigum Jigum Ga Sule agefe Shi da yayyinsa Yana ta Sharban kuka Suna bashi Hakura Habibu na Fitowa kowa ya Bisa da kallo ganin babu Hawaye ko Daya a idanuwansa Baba Jibo ya Nufa Dake Tsaye Cikin Sanyin Murya da wani Juriya yace"Baba ina gawan Maryama..?

Baba Jibo yace"Tana ciki iyayenka na shiryata.."Kai Habibu ya Kada kafin yace"Allah ya jikanta..Ina Abunda ta Haifa..? Baba jibo ya Dafa shi yana Fadin"Ameen Habibu kayi Hakuri kaji .? Abunda Ta Haifa Ayya tace Namiji ne ya na nan da Ransa.."Shi dai Habibu Gefe kawai ya koma ya Tsugunna yana Kiran sunan Allah acikin Ransa ya ma Nemi Hawaye ko Kuka ya rasa yana nan Tsugunne sai ga mata da yawa daga gidan su Sule Harda goggonsa da Matarsa Zainabu sukayi musu gaisuwa suka Shiga Gidan ba Dadewa Aka leko aka Kira Baba Jibo yana Shiga ba Dadewa yazo ya Kira Habibu da Sule yace suzo suyi ma gawa Sallama An gama gyarata.

Shidai Habibu Baba Jibo ke Jansa Har Zuwa gaban gawan maryama da aka Hadata Cikin Likkafani an sakata Cikin makara Shidai Habibu Durkusawa kawai yayi yana kallon Fuskar maryama da Sule ya saka Hannu ya yaye Zanin da"a Ka rufe ta da shi,Wani irin yake ji acikin Jikinsa kamar bashi da Lafiya yana jin kamar karya ne..? Maryama bata mutu ba Zata tashi Inna Hasiya Kasa Zama Tayi ta Fice Tana Sharan kwallah Sule ne ke ta ma Maryama addu"a yana Sharan kwallah Habibu kuma ko motsi ya kasa yi ganin Haka yasa Baba Jibo ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Kayi Hakuri Habibu..Kayi mata addu"a Yanzu Maryama ba Shirunka Take Bukata Ba addu"an ka take Bukata.."Baba Jibo na mgana ya Runtse Cikin Kunar rai dana Zuciya ya Kura ma Fuskar Maryama Ido yana Fadin"Allah ya yi miki Rahma Maryama..Halinki na gari ya Biki..Allah ya karbi Shahadanki.."Daganan kawai ya Mike ya Fice Daga Dakin yana jin kamar Bashi ba kamar karyane Maryama nada Ranta Wata Duniya ce Ta Dabam yashigo Ko Daukan gawan ma Kasawa yayi Baba jibo da Sauran Mutane suka Shiga suka Fito da gawan yana jin kukan Mata Daga Cikin Gida Baba Jibo Shi ya ke rike da Hannunsa harzuwa cikin makabarta Daman Tuni an haka kabarin.

Habibu yana ganin Abun kamar a mafarki wai yau maryama ta bar gidan Duniya,Yana ji yana gani suka Sakata a kabarinta shi da Baba Jibo da Sule suka kuma maida kasa suka tula Tunda ya Durkusa gaban kabarin yana Mata addu"a yaji Hawaye sun Cikamai ido,ammh sun kasa Zubowa Saboda Juriya yana ta dai yi mata addu"a har Mutane suka watse bai sani ba Daga shi sai Baba Jibo Sule ma yan"uwansa sun jasa yana kuka.

Kafadansa Baba Jibo ya Tabo ya Mikamar Dashi yana Fadin"Tashi Muje Habibu...Maryama tatafi ta barmu..Sai dai muyi mata Fatan Allah ya karbi Bakuncinta.."Bai iya cema Baba Jibo komai ba ya wuce bayan ya kara waiwaya ya kalli Kabarin Wani Katako ya gani nan gefe kila na masu hakan kabari ne,ya Dauko Katakon Da Sauri ya Kafashi gaban Kabarin Maryama yana kara kallon Kabarin yana ji kamar Maryama bata mutu ba Tana Ciki Tana Kiran sunansa ganin haka yasa Baba Jibo ya Riko Hannunsa suka bar makabarta ya san yayi Rashin Ya ammh Habibu ne yayi Rashin Kanwarsa Masu Soyuwa garesa.

Har suka Dawo Gida nan waje suka yada Zango inda aka Shinfida Manyan Tabarmu ana karban gaisuwan Shidai Gashi nan ne yana zaune yayi Zuru Kamar wani gaula in ance ya Hakuri Habibu sai ya Daga kai yace Hakuri namu ne Duka.."Allah ya jikan Maryama Allah ya raya Abunda ta bari..Sai ya samu kansa da Saurin amsawa da Ameen yana jin wani Nauyi Daga saman Kirjinsa Baba Jibo na Lura Dashi bayason Rashin Fitar Hawayen nan Habibu yafi so yayi kuka ya Fitar da Abunda ke Ransa kada wata Cutar Zuciyar ta kamashi..

Acikin Gida kuwa Mata sai Koke koke suke Barin ma Hajara Tayi kuka Kamar Idanuwanta Zasu Daina gani Haka ma Mastur Duk da yana yaro ya Fahimci Tabbas Goggonsa Bata agidan nan yaga su Baba sun Fita da ita Inna Hasiya kuwa bata kuka sai dai Lokaci bayan Lokaci Tana Sharan kwallah Ayya ita ta wanke Jaririn nan tas aka Sakamai kaya kamar ya san maraicin Daya sameshi Tun Zuwansa Duniya bai yi kuka ba yana Hannun Hajara ta kamkameshi Tare da Maatur Tana kuka Dangin Sule suna Daga gefe Goggo Da Zainabu kamar ma Murna suke da Rasuwar Maryama da Bakincikin Abunda ta Haifa kafin Ta rasu suna dai Gefe suna kallon Kowa Daya bayan Daya bama wanda yabi takansu Zafin Mutuwar Maryama mai Radadi ce ga ahalinsu...

Haka akayi ta karban gaisuwan har Ranar uku..Ranar da Jaririn da Maryama ta bari ya kwana yana kuka Daman Daga Ruwa Sai Ruwa ake basa in ya fara kuka ganin haka yasa Habibu Daya zama wani Shuru Shuru ya Dauki Hajara da Jaririn Suka Tafi General Hospital na garin Doguwa aka Dubashi Bayan ya Shigar da bayanin Mahaifiyar shi Ta Rasu Lokscin Data Haifeshi likitan nata Fadan meyasa ba"a bashi madara akayi ta Bashi Ruwa yunwa ce ta kamashi kuma in son samu ne a samu wacce Zata Shayar Dashi Saboda ba lalle ne Madara ta Rikesa har ya Rayu ba Shi Nono Tamkar wani Sinadarin Jariri ne yana karaminsa da haka suka baro asibitin bayan Habibu ya kashe Sauran kudadensa Duka an Duba yaron Komai lafiya an Rubuta musu madaran da zasu Dinga bashi,Daganan gida ya maida su Hajara ya wuce kasuwa yaje ya siyo madaran ya kawo nan da nan Hajara ta Hada da Ruwan Zafi ta fara bashi sai gashi yasha da yawa Daganan sai barci Tsausayinsa da kaunarsa ya kamata Allah Sarki Yazo Duniya Lokacin da zai ji Dumin mahaifiyarsa mai Rabawa Tazo ta Rabasu.

Ranar da akayi bakwai da Rasuwar Maryama ranar Habibu yayi ma jariri Hakika kuma ya sanya mai Suna MANSUR.! Batare daya Jira Sule wanda sai dai yaji abun Daga sama Bai Damu ba Domin yasan Habibun Haushinsa Yake ji Tun bayan Daya gayamai Maryama nada Hawan Jini Tuni Ran Habibu ya baci yana ganin kamar Harda Sakacin Sulen ya Rasa Tilon kanwarsa Maryama.

Aranar kowa ya watse Gida ya Rage Daga Inna Hasiya sai Hajara da Baba Jibo da Habibu da Mastur sai Ayya Dake nan Tana Taimakama Hajara kula da Mansur Daman su goggo Tun Ranar uku suka koma Sule din ne ya zauna Har akayi bakwai Habibu bai samu Sararin kuka ba sai Ranar da aka watse chan kuryan Dakin Hajara ya shiga ya kwanta akan gado ya Fara kuka kuka mai Cike da Tsausayi da wani kewar na Rashin Maryama ba wanda ya Hanashi Domin kukan ne kadai zai saka ya samu Saukin Komai acikin Ransa.

Ya Dauki Mansur yana kallo ba inda ya Baro Maryama sai da ya kwaso Duhun Fuskar Babansa Tunda Maryama Fara ce kamar yadda Habibu yake Fari Tunda kakarsu wacce ta Haifi Inna Hasiya Mutuniyar Maiduguri ne irin Fararan Kanurin din nan ga kyau ga gashi Ita Inna Hasiya ta Dauko suma sai suka Dauko Farinta ta Duk da Shima Baba Jibon Yana Da Haskensa.

Habibu yaji Duk duniya Mansur ne kadai ya Rage mai wanda Zai kallah ya Tuna da Maryama Wacce Kullum yake kuka da Rashinta,Sai ya Dage Damtse Duk Gidan ba wanda yakai Shi kula da Mansur wanda ko Sule bai sami Damar mgana kan Mansur din ba ganin yadda Habibun ya Cika komai kuma Uwa Uba kwarjini garesa In ya Hade ran nan bamai iya ja Dashi.,Madaransa kuwa Duk Sati yake Hanyan Zuwa Siyowa Acikin Ransa kuma yana Wani Tunani Dole ya Nema ma Mansur wacce Zata Shayar Dashi ta zame mai Uwa.

Hatta Mastur Dake karami ji da Mansur yake haka zai zauna yayi ta kallonsa yana mai wasa Daukansa Kuwa in Hajara ta Hanashi kuka zai Tayi Dakyar yake yin Shuru Shi adole sai ya Daukesa kuma bazai iya ba Habibu ya yanke Shawaran Hajara Zata Shayar da Mansur kuma Daya Tuntube Hajara dasu Baba Jibo Tuni suka amince Domin Habibu yace bazai Taba Bama Sule Mansur ba ganin irin yadda Maryama ta Rayu agidansu baya Fata Mansur ma yayi irin wannan Rayuwar Dukkansu sun yi Na"am da wannan mganar ta Habibu.

Ranar da Maryama Tayi arba"in Ranar aka Raba komai Daga abunda Maryama ta bari na awakai ne na kiwonta Sai wasu yan kaya da aka Raba Sule ya samu nashi Sauran kuma na Mansur ne awajen ne Sule ya nuna yana son Karban Mansur wanda Goggo ce ta tada Bala"in sai ya karbosa Shi bashi da Ra"ayin Haka Tunda ya Rasa Maryama Yaji Duniyan Ta Juya mai Baya,nan take Habibu yace bazai Taba bashi Mansur ba Hajara Zata Shayar dashi Shi kuma zai zame mai Uba Har abada Mganar data kawo Hayaniya Yayyin Sule suka Shiga mganar kan sai sun karbi Mansur Shi kuma Habibu yace Wlh Ya Rantse bazai Taba basu Mansur ba Haka aka tashi Ranar Zuciyoyo ba Dadi Baba Jibo Shima wannan karon ya Goyi Bayan Habibu Domin bazai so ya Rasa Dan Maryama ba Akaro na Biyu ba kamar yadda ya Rasata ba Shi Sule yayi Shuru karfinsa akaci.

Wannan Dalilin yasa Goggo Mahaifiyarsa Sule tace suje su Rike Mansur ammh Gadon Mansur bazasu bada ba su Zasu Rike Habibu bai Damu ba Domin Basa gabansa Suka Tattara suka bar musu komai kayan Dakin Maryama ne kadai Ayya da Hajara suka je suka kwaso aka Saka Dakin Inna Hasiya Hajara kuma asibiti suka koma amtsayin wacce Zata Shayar da Mansur aka bata mgangunan da Zasu Kawo Ruwan Nono Tazo Gida Tana sha kuma Inna Hasiya na Hada mata da wasu gayyayyaki na gargajiya Cikin Sati Daya Nonuwa suka Shiga Taf Suka Fara Zuban Ruwa cikin Farimciki Hajara ta Fara Shayar da Mansur Wanda Daga ita Har Habibu Suke mai Son da basu son Meyasa ba ammh Suna Jinsa Aransu kamar Dansu Mastur Barin ma ita Dake Shayar Dashi..Wata kauna ce Daga Allah sai dai Mutuwar Maryama Har yau har Gobe ta saka barin Zukatansu barin ma Habibu Da koda yaushe sai yayi kukan Rashin Kanwarsa Dayafi so Fiye da kowa aduniya,Baya kwana Biyu bai Ziyarci kabarinta ba Har sai da Baba Jibo ya Dakatar dashi ganin Rashin Maryama din yana Neman Taba Habibun Sosai...!

Allah ya jikan Maryama da Rahma Allah yasa ta Huta..Allah ya karbi Shahadanta Ameen ya Allah..Tafiyar mai Nisan Zango ce yanzu muke kan Shimfida bamu isa Mafarin ba..