04
(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)
Wattpad:@Jamilaumar315
Mallakar:Jamilaumar(Janafty)
Page4️⃣
Bayan Shekaru Biyu..
"Bayan Shekaru biyu da suka Gabata Da Rasuwar Maryama Da kuma Rikon Mansur Daya Dawo hannun Hajara.
Itace Madadin Uwa garesa Habibu kuma Uba ne garesa Mastur kuma ya kasance yaya garesa kuma Dan"uwansa Wanda yake Shekara ta bakwai Alokacin ya Fara girma an sakashi makarantan allo.
Girma da kuma Halin Rayuwa ya kara Kama Baba Jibo Ya Fadi a gona Sakamakon Jiri Daya kwasheshi yasa yake gida bai da Lafiya ciwon baya sai dai yakan Fita zuwa masallaci dake kusa baya Doguwar Tafi sai al'amuran suka koma Hannun Habibu Bayan kula da gonakin Mahaifinsa sai ya Fara Kiwo anan Cikin Gidan kama Daga awakai da Shanaye kuma Allah ya saka ma Abun albarka Dayake Inna Hasiya Tana Tsaye da Kafafunta Tana kula da komai.
Mansur Tun yana da wata Goma sha Biyar aduniya ya fara Tafiyansa ba inda baya zuwa Tun yana karaminsa yake kama da Mahaifiyarsa Shiyasa Lokaci Bayan Lokaci In suka kalli Mansur suke Tunawa da Maryama Saboda ba inda ya barta Hajara da Habibu sun fi Nuna Kaunar Zahiri Ga Mansur Fiye da Mastur wanda bai Damu ba Dayake Tun yana yaronsa Miskili ne mara Hayaniya da son mgana Sai dai Yana Bala"in son D'an goggonsa wanda Hajara Ta Fadamai Tun Mansur na Jariri ta gayamai Yaron da Maryama ta Haifa kafin ta Rasu Mansur kenan yaro, da rike abu ya rike komai acikinsa kansa Har yau har gobe bazai manta da Ranar da aka Fita da ita cikin wani Farin kyalle ba,Wanda Abun ya kasa bacemai acikin Kwakwalwarsa.
Tare suke Taruwa wajen kula da Mansur wanda Habibu kemai komai na Rayuwa Hajara kuma taci kashinsa Taci Fitsarinsa kuma Ta shayar dashi Shiyasa Take Jinsa ajikinta Kamar itace ta Haifesa,bangaran sule kuwa Koda yaushe yana Hanyan zuwa Ririwai ganin Mansur kuma ba laifi yana kawo Hidimansa a matsayinsa na uba da Farko har Habibu ya hana akarba sai Baba Jibo ya Dakatar Dashi yace Ya kyalesa ko bakomai Sule uba yake ga Mansur kuma Akwai Hakkinsa a Kansa Tunda yana Raye da wannan Dalilin Habibu yaja bakinsa ya Tsuke Ya zura ido Kawai Sai dai Bayan Sule Ba wanda ya kara Tako Kafarssa Daga Dangin Sule Harta kuwa da Goggo Mahaifiyarsa Suma basu wani Damu ba Shima kuma Sulen bai Taba Gigin cewa Zai Dauki Mansur ya Tafi Dashi Chan maruka ba Tunda yasan ba wani mai kaunar Abunda Maryama din ta bari,Duk da Mansur yaro ne ammh yawan zuwan Sule gidan yasa ya saba Dashi Sosai in ya gansa ya Fara Zillo kenan yana gaurancinsu na yara alamin yaga wanda ya sani ballatana Sulen baya zuwa Hannu Rabbana yan Minti da alawan yara yakan Riko musu shi da Mastur din wanda shi bai ma cika sha ba sai ya Tattara ma Mansur din shi da yake Sarkin Shan Zagi ne.
Haka Rayuwa ta Rika gangarawa Da Dadi ba Dadi Mansur nada Shekara Uku aduniya Wani Ifila"i da kaddaran Allah Daya baya wuce musulmi ya Fado musu Cikin Dare Gobara da ba"a san Daga Ina Take ba ko Daga ina ta Fara ba,Tatashi a Shashen su Inna Hasiya wanda Daga ita Har Baba Jibo sun kone aciki Koda aka Samu Nasaran Ceto su sun Riga sun Shaki Hayaki Sun Kone Daga wasu sassan na Jikinsu Allahu akbar Inna Hasiya da Baba Jibo sun amsa kiran Mahallacinsu alokaci Daya.
Wannan abunda ya Faru ya Girgiza Habibu Da Duka al"ummar Ririwai mutuwa Farar Daya kuma lokaci Daya,Hajara tayi kuka Mansur da Mastur su kansu sun san anyi Rashi Domin sun matukar sabawa da kakanin nasu barin ma Mastur Da ya fara Girma da wayau Habibu yasamu Jarabtan Mutuwan iyayansa alokaci Daya bai Nuna gazawa ba Yayi kukan Zucci ya Fauwala ma Allah komai ganin yana da Mata ga Ya"yansa Guda Biyu Daya kasance Shine garkuwansu Dole ya zama mai Juriya da kuma Jajircewa Domin inganta Rayuwar Mastur da Mansur.
Tun Rasuwar su Inna Hasiya garin Ririwai ya Fita kansa ya Fara Tunanin Sauya wata Rayuwar,Daman bayan Rasuwar su Inna Hasiya sai ya Dauko Ayya tana zama da Hajara Saboda ta Debe mata kewa Domin mutuwar ta Girgiza ta sosai Ta kasa Daina kukan Rashin su Inna gani take kamar kullum kwannan Duniya in ta Tashi Zata Iya Bude ido Ta gansu ta saka yardan ma kanta Cewa sun barsu acikin Duniyan su kuma sun Tafi Gidansu na gaskiya.
Batare da Habibu yayi Shawara da kowa ba ya Fara Shirinsa Gadonsa na Gonaki na wajen Baba Jibo da suka zama gadonsa Duk ya Hada ya Tattara ya Saida Tare da Duka Dabbobinsa Batare da yayi Shawara da kowa ba Shi kadai acikin Zuciyarsa ya yanke ma kansa Shawaran zai yi Nisa da garin kano Domin samun wani Waje da zai je ya gina wata Sabuwar Rayuwa Shi da Matarsa da ya"yansa Guda Biyu wadanda yake Fata da Muradin Da kuma Burin Inganta Rayuwarsu Ta zama wata aba mai ban Sha"awa anan gaba.
Su dai su Hajara sun ga dai an kwashe Dabobbi an Tafi Dasu kuma Habibu bai ce musu komai ba Ayya ce ma ta Tambaya Shine yace zai musu bayani Daga baya sai da yagama Hada Duka kudadensa Da Shawaran inda zasu koma kana ya samu Ayya da Hajara da mganar Sun yi kuka sosai na ganin Zasu bar Mahaifansu sai dai basu yi Gaddama da Habibu ba Tabbas yaga Rashi da maraici yana Bukatar Nesa da garin Doguwa Gabadaya nan dai suka Bashi Goyon baya kuma nan take yace su Fara shiri suyi sallama da Makota Nan da Sati Daya zasu Koma ZARIA..!
Kuma ya sanar dasu bazai Saida wannan Gidan ba Ko Domin gaba Watarana zasu iya zuwa Ko bayan Ransa ko su Mansur bazasu Rasa wajen sauka ba Sai da zai saka wasu Amintattun da zasu kula da Gidan ba sai sun Biya ko asin su ba Ayyah Tayi Na"am sosai da wannan mganar Nan da kuma suka Fara shiri Bayan sun gayama Makota da yan"uwa da abokan Arziki cewa Zasu bar garin Doguwa Gabadaya dama Jahar kano Kowa yaji sai yaji bai ji Dadi ba sai dai Kowa yasan a irin wannan Rashin da Habibu ya Fuskata bazai Taba iya zaman garin ba Nisa da garin Kila zai sa ya Rumgumi Duka Kaddaransa.
Habibu Mijin Karimatu Yayar Hajara ya yi ma mganar su zo Gidan su sai su Zauna Tunda in da yake Zaune gidan gado ne awajen ba yalwa yana jin haka yafi Kowa Murna yadinga ma Habibu Godiya kamar zai kwantamai yace bakomai,Karima Tayi Bakinciki Rashin yar"uwata alokaci Daya da Ayyah sai dai in ma Tace Ayya ta zauna kada ta Bisu bata da karfin RiketaTana ji Tana gani Ranar wata Asabar Habibu ya samo Babbar Mota ya kwashe musu Dan Tarkacan kayan sawansu Basu Dauki Komai ba Bayan Haka Sule yana nan suka bar garin Doguwa Gabadaya Domin Habibun ya gayamai Zasu bar garin bashi da ta cewa Saboda yasan Ko Giyan wake yasha Habibu bazai bashi Rikon Mansur sai dai yaji Dadi dayayi mai alkawarin da Zarar sun isa suka samu Muhalli Zai Kirasa Da haka suka Rabu Suka kuma yi bankwana da garin Tare da Rakiyan yan"uwa da abokan Arzuka Mansur Nata Murna Sun Shiga Mota zasu yi Tafiya Mastur Dake da Wayau alokacin Sai Jikinsa yayi sanyi Jin Hajara ta gayamai Zasu bar garin Doguwa ne zuwa waje mai Nisa Shiyasa sai Jikinsa Duk yayi sanyi ya koma Gefe ya Rabe wani Lokaci yana Jin Sha"awar Mansur ganinsa yaro ne ba Ruwansa yayi ta Harkokinsa Sabanin Shi da sam Hayaniya ke Damunsa.
Habibu na gaban Motan da suke Ciki yana Sharan kwallah Na Kewa da kuma Alhiinin Yau zai bar Mahaifansa ba Inna Hasiya ba Baba Jibo ba Kuma maryama Allah Sarki Rayuwa kenan acikin Zuciyarsa yayi musu addu"an Allah yayi musu Rahma Gabadaya Daga Hajara Har Ayya sun yi shuru Jikinsu Duk yayi sanyi Mastur ma haka Mansur dai ke ta Burumtunsa Daga Jikin Hajara zuwa na Ayya ko na Mastur babu abunda yayi mai dadi..Yarinta mai Dadi.
*******
Sun sauka agarin Zaria Karamar Hukumar Dake kaduna garin gwammah ashe akwai wanda ke jiransu atasha da Waya da kwatance da Habibu ke yi suka yada Zango a kwangila Dake Zaria suka Hadu da wani Mutumin wani Fari gajere wanda bai wuce Sa"an Habibun ba suka gaisa dashi a Mutumce Kana ya Shiga Motar ya Dinga Nuna ma Direban Hanya sai gasu Cikin Hanwar Fulani Dake Wajen Kwangila anan Cikin garin Zaria.
Anguwa ce mai Cike da Gine Gine da zamani Daga Chan gefe kuma akwai Bukkan Fulani Yanzu ne da Gari ya Fara cika Gine gine ya fara yawaita Daga gani Sabuwar anguwa ce Domin wasu Gidajen yanzu ake ginasu ba"a gama ba Tuni Ayya da Hajara da Mastur suka Saki ido da baki suna bin Garin Zaria sa kallo suna mamakin Lalle kallo na Birni Sosai Sudai ana ta Tafiya suka ga an Tsaya kofar wani Dan Madaidaicin Gidan Bulo wanda yaji Shafen Filista da Fenti Mai Ruwan Kasa yayi kyau da Kofar gidan mai kyau nan suka tsaya Habibu yace su Fito kuma a sauke musu kayansu sudai sai bin Ko"ina da kallo suke gidan yana Tsakiyan Gine ginen manya manya ne na masu Kudi Hatta Jikin Gidan nasu wani katon Gida ne ake Ginawa ma"aikata sai kai da kawo suke.
Mutumin shi ya bama Habibu key din Gidan Daman gidan yana Bude ne, yace su Hajara su Shigo Yana Rike da Hannayensu Mansur Yara kuma Dake waje suka Taimaka musu da Shigowa da kayan suna Shiga suka ga Tsakar Gidan yasha Siminti Daga gani Sabon Gidane mai Dauke da Daakuna uku Reras abun mamaki Wata Mata ce ta Fito Tana Musu Maraba Ta karbi kayan Hannun yara Zuwa ciki Tana Faman yi musu sannu da Zuwa suka amsa suna kare ma Gidan kallo Harda Rijiya da makeyi nan Har Guda biyu Gidan dai yayi kyau sosai Ko"ina an Shafe shi da Fenti.
Har Dakin suka Bi matam katon Daki Ciki da Falo ne Dakin ba Komai sai katuwar Tabarman da aka Shimfida sai kololin abinci nan ta ce su Zauna suka zauna Tana ta yi musu Fara"a suna Binta da kallon Rashin Sani Ruwan Ta Fara basu wanda Ta mika musu mai Sanyi Cikin kwanon Sha,suka Sha sukayi Godiya Habibi suna waje sai da suka gama Zagaya Gidan kana suka Shigo Matar ta gaishe da Habibu Tana yi ma su Mastur wasa wanda Mansur ya tafi wajenta da Gudu Banda Mastur da bai sabo da Mutane.
Sai Lokacin Habibu yayi ma su Hajara Bayani sunan wannam Mutumin Usmanu Kuma wannan Da suka gani Matarsa ce Balaraba basu Taba Haihuwa ba suma baki ne Daga Rano Ta kano suka Dawo nan da zama saboda kasuwancin Sai da Hatsi da Usman din ya Fara sai ya Saida gidansa na chan yazo nan ya Siya gida ya Dawo Shi da Iyalansa Habibu yace yasan Usman a kasuwar Garin Doguwa ne in yaje saida Hatsi,Anan suka san juna suka kulla abota Duka Rashin da akayi Mishi ya zo mai gaisuwa Shi kadai ya gayama Burinsa na son barin Garin Doguwa Shi kuma ya bashi Shawaran ya saida Duka Gonakin sa ya kawo Kudi ya siya masa karamin Gida In suka Dawo Sauran kudin sai ya ja Jali ko irin Sana"arsa ya Fara Wanda yake Gudanar da ita akasuwar Zaria Dake Cikin Zaria City.
Ya gayamasu Shine bayan ya Saida Komai yazo suka Hadu ya bashi Kudaden shine ya Siyamai wannan gidan Sauran kudin kuma zai siya musu Kayan Zaman cikin Gida sauran kuma sai yaja Jali Daashi Mamaki ya kamasu jin wanman Gidan na Habibu ne Lalle Dayake Baba Jibo ya bar Manyan Gonaki Sosai shiyasa kudin sukayi auki Sosai nan Ayya Tayi ta ma Usman Godiya yace bakomai an zama Daya.
Nan suka Fita suka bar su da Balaraba Bayan ta saka musu Abincin Data yo Daga gida suka ci sukayi sallar suka zauna suna kara Hutawa Balaraba akwai baki sai Hira take musu Ayya ce mai Biye mata Hajara Shuru kawai tayi kewa na Damunta Tuni Mansur ya ware sai waasansa yake Mastur ne ke rakube ajikinta Shima ya kasa Sakin Jikinsa Balaraba Sai wajen yammah Tayi musu sallama ta koma Gida ta yi musu Tuwo ta kawo musu da Filo da Wata Tabarman sai Zanin gado suna ta yi mata Godiya su Dukkansu suka kwana anan Dakin Habibu kuma ya kwana Adayan Dakin bayan sun bashi Tarbama da Filo.
Washegari kuma Tun Safe Usman ya raka Habibu Kasuwa yayo musu Siyayyah,Ya siyo Kafita Babba Guda Daya sai Karama Guda Biyu Daya nasu Sauran kuma na Ayya da Su Mastur Tunda ya"ya Maza ne sai Ledan Daki da Tabarma da Filluka da Sauransu sai kayan girki da kayan abinci gabadaya abunda Zasu Bukata duk sai da ya Siyo musi Har sai da ma ya Shiga Cikin kudinsa Daya ijiye zai ja jari sai dai bai Damu ba Usman yace a Hankali sai ya Siya komai Ranar ma Balaraba ta basu abinci Domin sai yammah su Habibu suka Dawo da Kayayyaki Balaraba Ta taya su suka Jera komai Dayan Dakin aka sakama Ayya Katifarta da Katifarsu Mansur,da Ledan Daki Dayan Dakin kuma sai aka saka Kayan abinci da kayan Girki Tunda ba kowa Dakin Farko kuma nan ne Dakin Hajara nan aka saka babar Katifaan.
Sai Dare Usman da Balaraba suka Tafi Bayan tafiyarta Habibu ya Fita ya siyo musu Ruwan Zafi Da Buredi suka sha suka kwanta Da safe kuma suka Mike da aiki Hajara ta Fara Kokarin Sarrafa Girki Tun Safe Balaraba ta aiko mata Da icce da Murhu Tuni Ta Dora ta Dama musu Koko Tunda Har Kullin kamun sai da Balaraba ta aiko musu Dashi Shiyasa Tsskaninsu sai dai Godiya Dayake basu da wani Nisa Sai dai Gidajensu ba"a jere suke ba Nasu na dagachan gefe ne ma"ana Suna kallon kallo.
Kafin a Rufe Sati Daya da Dawowarsu Zaria Tuni Usman ya Samar ma Habibu Gurbin Zama a kusa dashi a kasuwar Zaria inda yake saida Hatsi su Shinkafa,wake Masara, Dawa,da Sauransu kafin Habibun ya samu Shago,Sai ya Rabashi da Izinin Wakilan kasuwan Shima ya Saro Hatsin Ammh Shi Har dasu Barkonu da Su mangyada da Sauransu da yakinin Allah zai saka ma abun albarka Domin yana da Burin ya sakasu Mastur a makaranta Boko su samu ilimin Zamani,Saboda kudaden Hannunsa Duka sun kare Allah ne ma ya Rufamai asiri Komai ya Tafi kamar yadda yake Fata.
Allah yasa ma Fatan Habibu albarka bai Rufe shekara Daya da Fara sana"ar saida Hatsi ba komai ya Sauya Daga Rayuwarsu Allah yasa ma abun albarka komai na Bukatun Gida ya gama Siyan musu ya saka Mastur a makaranta Lokacin yana da Shekara 8 kenan aduniya firamari 1 aka sakashi ganin yayi girma wata makarantan Fimarin gwannati ce,Ya kuma Siya yar kekensa Dayake Zuwa kasuwa da ita akai yake Daukan Mastur yana Kaisa makaranta in zai wuce kasuwa,In kuma an tashi Mastur din ya Dawo da kansa Wanda sai da aka sha Daga da Mansur ya hakura da yace shima sai an sakashi Kuma Habibu yace sai ya cika Shekara Biyar zai sakasa Boko ammh Islamiyar da aka saka Mastur An saka Mansur din suna zuwa Tare,Zumunci Tsakaninsu da Balaraba da Usman Sai abunda yayi gaba sun Rike juna kamar yan"uwa.
Zuwa Lokacin Sule yasan Mazauninsu Domin yazo wajen sau Biyu ma,yana ganin Mansur Daya koma yana bama Goggo Labarin Cigaban da Habibu ya samu sai ta gwalesa Domin bata kaunar sake jin Sunan wani ahalin Maryama,jin haka yasa ya Yi shuru da bakinsa Ammah acikin Ransa yasan Son Dayake ma Mansur acikin ya"yansa Dabam ne.
****
BAYAN SHEKARA BIYAR..
"A zuwan wannan Lokaci Komai na Rayuwarsu ya gama Daidaita ba Dai za'a kirasu masu kudi ba ammh Suna da Rufin asiri Tunda Yanzu haka Habibu ya mallaki Shagon kansa Na Hatsi a kasuwar Zaria Yafi ma Usmanu Habakan arziki da Costumer,daman haka Allah yake al"amarinsa.
Tuni an saka Mansur makaranta Inda yake da Shekara 9 a duniya Mastur kuma yana da Shekara 13 aduniya ne yaana aji Shida a primary ayayin da Mansur na primary 3 alokacin Suna zuwa Islamiya da yammah asabar da Lahadi kuma suna zuwa Hadda Na Safe Basu da kowa sai su Balaraba wacce suke kira da Inna Balaraba Hajara kuma Mansur ke kiranta da Hajja Tun yana yaro sai sunan ya Bita Harta da Mastur shima Hajja yake Kiranta Habibu kuma Daya Zama Magidanci yanzu Baba suke Kiransa Zuwa Lokacin Sule na yawan zuwa yana Duba Mansur ganin haka yasa Habibu ya gayamai Shine Mahaifinsa Saboda ya Girma Koda watarana Bashi da Rai yace bai san wannan ba Hatta da Suna a makaranta ma Mansur Sulaiman Doguwa yake amfani Dashi Sabanin Mastur Dayake amfani da Mastur Habib Doguwa Tun alokacin Akwai yarinta atare da Mansur so bai wani Damu ba ya Shiga Sabgarsa.
Tun alokacin Hallayarsu Ta Fara Bambamta Tun suna da kankanin Shekaru Mastur Miskilin Mutun ne wanda mgana bata Damunsa Shi dai barsa da karatu ina zaka Karatu ina ka Fito karatu bashi da yalwar Fara"a Ballatana Sakin Jiki da wanda bai sani ba yana da wuyar sabo da kuma Wuyar Mu"amala,Sabanin Mansur Dayake Tun yana karaminsa mai Fara"A mai Surutu mai yawan waasa da Sakin Jiki da Mutame Shiyasa Mastur yake mai Fada in kaga Mansur na Tura baki Mastur ne ya Tasa shi gaba sai yayi Karatu Shi yafi maida Hankalinsa kan wasa Fiye da Karatu,Ko a makaranta Haka yake da wasa kamar me baya maida Hankali In Mastur yayi mgana Hajja tace yarinta ke Damun Mansur zai bari saboda bata son ana Takuramai Habibu kuwa kullum sai yayi ma Mansur Fadan ya Tsaya yayi karatu ya natsu Tamkar yayansa ammh Ina akace Hallita wani abu ne Wasa da Rashin maida hankali ga Abu ajinin Mansur yake sabanin Mastur da sai ya wuni bai yi mgana ba Shi dai karatu Domin yana da Burin Yayi ilimi mai Zurfi Domin Cika Burinsa na ganinsa Sanye da Kakin D'AN SANDA..!
Wannan kenan..