08
[12/23, 6:59 PM] Janafty: SADAUKARWAR SO..!!
(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)
Wattpad:@Jamilaumar315
Mallakar:Jamilaumar(Janafty)
Page8️⃣
Bayan wasu shekaru..
The Nagerian Divisional Headquater
Porthercourt
"Wani babban Headquater ne na Gamayar yan sanda Dake Jahar Parthercourt,Babban waje ne,Da akan bama yan Sanda Horo sosai Kuma Babban Headquater ne mai Dauke da Yan Sanda Shashe Shashe Bayan Haka kuma akwai Gidaje Quaters na mallakan manyan ma"ikatan wajen da ma wasu Daga Cikin kananun.
Daga yammah ne ginin Police Station din yake,Wanda yaji ginin Zanani mai farin Dutse Daga gaban wajen Motocin yan sanda ne da mashina gasunan Fake a parking Space sai kuma Kaida kawon wasu Daga cikin Mutane da kuma Sargents din Dake wajen.
Da Misalin karfe 8:30am na Safe ne Ana Zirga zirga awajen Cikin hakane wata Bakar Mota Prado,Mai kyau da Daukan ido,ta Shigo wajen cikin Slow Driving,cikin Hankali ma mallakin Motar ya karisa Faka Motar kuma ya zauna aciki yaki Fitowa kamar kiftawa kuma sai ga wani Sargent ya Fito sanye da kayan yan sandansa Bakake ya Tsaya Wajen Kofar Motar sai da ya Sara kana ya saka Hannu ya Bude Murfin Motan Lokaci Daya kuma ya koma ya kame Yana Raba Idanuwa kamar wanda yayi karya.
Sai da aka bata wajen Mintina uku kafin ma mallakin Motan ya Zuro kafarsa Guda Daya waje wanda Take cikin wani Bakin Takalmi Sawu Ciki mai Tsada na Fatar Damisa,ayayinda Kafarsa Take Fara mai Cike da gargarsa,an Dauki Lokaci kafin ya zuro Da dayan kafan sai dai wannan karon Cikin Zafin nama ya bayyana Gabadaya awaje.
Wani Muradden Matashin Namiji ne Dogo mai ingarman Jiki da mazantaka mai kwarjini mai Haiba da Dattako,yana da Haske ammh Ba Fari ba sosai Sai dai Fatarsa yafi kama da Kalan yan Moroco,Yana da Fadin Kirji mai nuna Zallar Jarumta da Sadaukantaka atsaye yake Daga ganinsa kaga Cikakken Namiji Sosai Damtsen Hannayensa Muscle dinsa Duka Sun Bayyana Tsabar karfi da kuma Nuna Jarumta,Doguwar Fuskarsa Tana Dauke da Dogon Hancinsa da bakinsa Dan Daidai sai Sajensa Daya Zagaye Bakinsa Dake karamai kyau da kwarjini yana da Idanuwansa Daidai Misali masu Dauke da wani Sirri,Gashin kansa a Nannade yake kamar na Fulani Sai Gashin Idanuwansa da suke wani Zara zara Dasu Idanuwansa ya Toshe su da wani Bakin glass,Jikinsa Sanye da Kayan yan Sanda Bakin wando da Riga mai Ruwan Blue ya saka Belt ya matse kugunsa Dashi,Daga yammah Da Kafadarsa Anininsa na igiyan matsayinsa,sai Daga Dama wajen aljihu wani Dan gold ne makale awajen an Rubuta DCP M.B DOGUWA.. Daga saman kansa kuma Hularsu ne na yan Sanda kafe akansa wacce ta karamai wani Sirrin kyau kamar don shi akayi Hulan da Uniform din gabadaya.
Sargent din Dake Tsaye ya Kara saramai yana Fadin"Gud Mrning Sir.."yana Tsaye yana kallonsa Lokaci Daya yana saka Hannu acikin Aljihun wandonsa bai mai mgana ba kai kawai ya gyada mai kafin naga ya Dagamai Hannu Cikin Sassarafa da Takun Jarumta yayi gaba Lokaci Daya yana Duba agogon Dake hannunsa na kamfanin Rado.
Shi kuwa Sargent din jiki na rawa ya Sunkuya cikin Motan ya kwaso System sai wasu Tarkardu da wayoyinsa Guda Biyu,Sauri Sauri ya Rufe Motar Lokaci Daya ya saka Key din Motar ya kulleta yabi bayansa Da Gudu Gudu Sauri.
Yana Shiga wajen aka Fara kamewa ana mai sannu da Zuwa Ko Daga kai baiyi ba Sai dai yana Kallonsu Daya bayan Daya ta Cikin Bakin glasa dinsa Sanin Daman ba mgana zai yi ba basu Damuba kamar zai Tsaya sai kuma ya Cigaba da Tafiya Har zai Shige Koridon da Zai sadashi da Office dinsa Sai kuma ya Juyo Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Where is Sargent Alotuwa..? Gabadayansu suka kame atsaye kafin wani in yamurin Dan sanda yace"He is not well Sir.."Shuru yayi kafin ya kada kai bai ce komai ba ya Juya ya Fara Tafiya Cikin kasaita wannan Sargent din na Bin bayansa da kayansa Daya kwaso mai amota sai da suka ga Basa ganinsa kana kowa ya Sauke Hannuwansa suna Sakin Numfashi Sargent Bala Dayake Bayarbene yace"Kai Sir fa akwai Kwarjini..In ya kalleni Har Hanjina nake jin suna Kadawa.."
Dayan Sargent din mai Suna Sargent Gashuwa,Ba Musulmi bane ya karbe da Fadin"Shiyasa yake saka Glass yasan Idanuwansa na Tsorata Mutane..He is Hausa man Buh I recpect Him sosai He Know his work sosai sosai fa."Gabadayansu kai suka gyada Domin Shekara Biyu da Fara Aikin sa anan wajen Wlh suna Jin Dadin sa sai dai Wanda baya son gaskiya ne bazai yabe sa ba ammh Mutum ne nagari mai gaskiya da Amana sai dai Illarsa Daya Miskilin Dan Sanda ne Baya son Hayaniya Ballatana Doguwar magana ko su Da Suke karkashinsa bazasu Taba Kirga mganarsa Dasu ba mganarsa ko Ta bangaran aiki ne baya wuce Daya Biyu Zuwa uku..Ko kuma wani Lokacin ya gwammace ya Rubuta a takarda ya bama wani Sargent ya Karanta musu Saboda baya son Doguwar mgana Hakan kamar Takurace Garesa Da Farko suna mai wani kallon mai girman kai da Wulakanci sai da Tafiya Tayi Tafiya suka Fahimci Haka Halinsa yake Yawan mgana Ko Hayaniya Tamkar sune abokan gabansa.
Kafin ka isa ga Office din nashi Sai ga wuce wasu kananan ofishoshi Kamar guda Uku haka kafin ka Hango wani Dan Korido wanda kana Binsa zai kai bakin wannan Babban Ofishin,Wanda Daga bakin Kofar an saka wani Dan Anini da aka Rubuta DCP MASTUR HABIB DOGUWA..
Kafin ya saka Hannu ya Bude Office din Sargent Inuwa Dake bayansa yayi saurin Taran gabansa ya saka Hannu Daya ya Bude mai Kofar Office din Daya Sha gyara wanda Daga gani Duk Safiya ana Tsabtacesa Domin ga kamshin nan na Tashi na Turaran wuta Domin kowa yasan DCP Mastur Habib Doguwa akwai Tsabta kuma baya Shiri da kazamai Shiyaaa in masu Shara suka zo kafin su Fara Tsabtace ko"ina Office dinsa ne na Farko wajen gyrawa da Tsabacesa Baya African Time 8:30pm Daidai yake Shigowa Cikin police Station din.
Cikin Takunsa na Jarumta mai Cike da Sanyinsa ya Saka kansa Office din bayan Daga Labbansa yayi Sallama,Sargent Inuwa na Binsa abaya kamar Jela,Kan Kujeransa ta Zama ya zauna Lokaci Daya yana Kiran Sunan Allah sargent Inuwa kuwa sai da ya kame kana ya Sauke kayan Dake Hannunaa Saman Babban Teburin Dake gaban Yallabai Cikin kwarewa ya sake Saramai ya kame Lokaci Daya bai Dago kansa ba yace cikin Wata Murya mai cike da Umarni"Ka kawomin Fayel din nan na Case din old man din nan da yaransa.."Yafada Cikin Harshen Turanci Lokaci Daya yana Jawo System din gabansa ya kunna Ta Dagani Gani aiki mai Muhimmanci zai gudanar Cikin Saramai yace"Ok sir.."Daga haka ya Juya ya Fita bayan ya Rufomai Kofar Office din.
Abunda zai baka mamaki Shine ganin irin Tsaruwan Ofishin Domin Daga ciki akwai wasu Kujeru Guda Hudu na zamani da sukayi ma Office din kwanya Harda Karamin Center Table Atsakiya, sai Daga Chan Kuma Babban Tuburu ne mai Dauke da Manyan Takardu da kuma System Sai Kujeran mai zama Daga Mai kallonsa kuma Kujeru Biyu ne na maraba da baki,Akwai Hotunan Shugabanin Nageria da wasu manya Da ke jagoranta Bataliyan yan sandan Gabadaya,Daga Gefe kuma karamin Daki ne shima na Hutawa Domin Har da karamin gado akwai aciki sai karamin Bandaki Domin Kama ruwa ko wani Lalura in ta kama Mutum
Daga Gefensa Zamansa kuma karamin Fridge na Bukatar ma mallakin wajen In hakan tataso.
Sargent Inuwa bai Dade da Fita ba sai gashi ya Dawo bayan yayi Knooking Daga ciki yayi gyaran Murya kana ya Shiga ya Ijiye Fayel din Saman Tuberin ya Juya ya Fita Ko Kansa bai Dago ba yana ta aiki kan System din gabansa Ammh Idanuwansa sun nan Danne Cikin Bakin Glass dinsa wanda ke karamai kyau da kwarjini Bantaba ganin wanda kayan sanda yayi ma kyau da saka Tsabar Haiba ba irin Mastur Domin Daya kara Girma sai ya zama kamar Mallam Habibu yayi kaki ne Harta Da yanayin Mirmishin su Iri Dayane Tamkar Yana Matashinsa Lokacin Suna Doguwa sai dai wannan Mai kama da Habibun Na yanzu Ilimi da waye da kuma Rayuwa sun Dabaibaye Rayuwarsa Sosai wanda suka kawo Babban Chanji mai yawa da kana gani Zaka Fahimci Hakan.
Ya Zurfi Cikin aikinsa Karar wayarsa ta dawo Dashi Daga Duniyar Daya tafi wanda in ya Shigo Office dinsa ya fara aiki baya kaunar wani abu ya tsaidashi,Karamin Tsaki yaja ya na Zare Glass din Dake Fuskarsa A kasalance ya Jawo Wayoyinsa Duka Biyu A inda Sargent Inuwa ya Ijiye mai Duka Wayoyin Manya ne Kirar Kamfanin Samsung.
Idanuwansa ya lumshe Lokaci Daya yana kara Bude su ganin Sunan mai Kira SIS RUMANA lokaci Daya kuma da Faskeken Hotonta Daya bayyana a kan Scrren din wayar nashi Wata kyakyawan Farar Matashiyar yarinya,wacce a Shakaru bazata wuce Shekaru 25 aduniya ba Sai dai yanayin Jikinta ya Boye Hakan Tana da Tsawo ammah ba Sosai ba Daga samanta Har kasa Tana Cike ne,Fuskarta yar Doguwa ce mai Dauke da Dogon Hancinta sai Dan bakinta mai Fadi haka da Kumatunta Turbarkallah masha Ba laifi Tana da Kiban Murjewa da Jin Dadi Tana da Manyan idanuwan da Matsaikatan Gashin Ido Dana Gira, a kallon Farko in kayi mata sai kaji kana so ka kara Domin duk inda ake neman mace mai kyau da aji Da Ilimi Rumana ta wuce nan Daga ganinta Ilimi Ya gama Ratsata Ajikin Hoton ma kamar acikin makaranta aka Dauketa Tana tsaye bakin wani Aji,Tana Sanye da Doguwar Rigarta Baka sai tayi Rolling da Jan Vail Hakama Jakarta Ja ce da Takalmin kafarta Hill wanda ke kara mata Tsawo,Tarin Littafan karatu ne taRumgume a Hannunta Sai Idanuwanta Dake Cikin wani Farin Siririn Gilashi mai kyau Daga ganinsa na kara karfib gani ne na masu karatu Gabadaya Hakoranta suna waje ne har Wushiryanta mai kara mata kyau da kwarjini suka Bayyana cikin Jerun Fararan Hakoranta masu Haske da Daukan Ido Daga gani Duk wata takan Ziyarci Dental Domin Tsabtan Hakorin nata.
Kura mata Hotonta ido yayi yana kallo Har Kiran ya Katse bai Daga ba kansa ya Dafe Lokaci Daya yana wani yamutsa Fuska kamar irin ya gaji Sosai Bayansa ya koma ya Jingina da Kujeran kafin ya Fara Lalubanta Cikin Sanyi Tabbas yasan bai kyauta ba Domin shi yayi mata alkawarin zai kirata din yau da Safe ammh kuma sam ayyuka sun sha mai kai ya manta Yanaji Wayar ta Fara Ringing sai kawai ya Sakata a Speaker ya ijiyeta nan saman Tuburin ya koma ya Jingina da kujeran yana Kara Lumshe Idanuwansa masu Kama da na Mage.
Cikin Sirriyar Muryanta da kuma Natsuwarta Daya santa Dashi Yaji ta Daga wayar tana Fadin"Nayi Fushi Yaya Mastur.."Tafada Cikin yanayin yar Shagwaba Bai Bude Idanuwansa ba ya muskuta yana Fadin"Afuwan kanwata..Ina kwana.."Jin ya gaisheta sai taji kunya Tafara DariyaTana gaishesa ya amsa mata Cikin Muryansa a Dake Tambayan aikinsa Tayi yace Mata Alhamdulillah Sanin Halinsa na Rashin Hayaniya yasa Daga nan Tayi Shuru bata kara mgana ba Sai shine Dakyar ya samu Damar ce mata"Ya karatu..?
Tayi Mirmishi kafin tace"Lafiya kalau..Mungode ma Allah.."Ya Dade bai yi mgana sai chan Taji yace"Allah ya taimaka..Ki maida Hankali Kinji ko..?
Har acikin Ranta Taji Dadi Cikin Karya Murya tacce"Insha Allahu..Ka kularmin da kanka kaji..? Bai bata amsa ba Illah Taji Sautin Motsinsa sai kuma Taji Sanda ya yanke wayar Kurama wayar ido Tayi Tana kallon kyakyawan Hotonsa da kayam yan sanda Wanda aka Daukesa sanda IG na kasa ke basa mikamin Dcp,Tana son Hoton Saboda Kaunar Hoton Datake yi ne yasa ta Sakashi a Wallpaper dinta na Wayarta Saboda Ta Rika ganinsa Duk Lokaci Data Dauki Wayarta.
Haka Allah ya So da bayinsa kuma haka Allah yake Tsara Lamarinsa Ita kanta bata san yaushe bane ko wani Lokaci ne ta wayi Gari taji Zuciyarta na Cike da Kaunar Mastur,Ammh Ta Lakanta Hakan da Wannan Soyayyar ta Faro asali ne tun Zamansa Da yayi agidansu da Koyamata Karatu Dayake yasa ta Shaku Dashi Taji yana Burgeta bata sani ba Har ya Rikide ya koma Soyayyah Wanda Tana Kokarin Boye Abunda acikin Ranta ammh Da Zarar Taji Muryansa Sai Taji ta Rasa Duk Natsuwarta.
Kiran Sunanta da akayi Shiya Dawo Da ita Daga Hayyacinta Tayi Saurin Mikewa Tana gyara zaman Lapcoart Din Dake Jikinta,Suna Tsaka da aiki na taTsaigata ta Kirashi Domin indai Abunda ya Shafi Mastur din bata Hadashi da kowa Wayarta ta saka Cikin Jaka Ta Fice Daga karamin office din lokaci Daya Tana kara gyara zaman Rolling din Vail din Dake Jikinta.
Shi kuwa Mastur bayan ya kashe Wayar sai kuma Jikinsa ya Mutu ya kasa Cigaba da ayyukan Dake gabansa Sai kawai ya Kara gyara zama yana kara Maida Idanuwansa ya Lumshesu kamar mai Barci Lokaci Daya yana Tirayo Wasu abubuwan da suka Gabata da ira iran kulawan Rumana akansa Gabansa ne ya Fadi baya so Ace yau Rumana ta kamu Da Sonsa Domin bai Taba Sonta ba Kallon Kanwarsa yake mata Shi Tuni Zuciyarsa da Duka mafarkinsa suna ga Mace Daya kwara daya Tak Daya bama Dukkan Zuciyarsa da Gangan jikinsa Shi kansa bazai fadi yaushe ne..?ko kuma Wata Rana ne ya kamu da Sonta ba sai Dai kawai ya wayi Gari ne Cikin Soyayyarta mai karfi Wacce Ta Dade acikin Zuciyarsa Tana Yabanya da Rassa.
Ashekarun da suka Gabata abubuwa na Cigaba Dadama sun Faru Dashi da iyalansa Ya Faro Rayuwarsa tun Saurayin Jami"a Dayake ta Fafutukar Neman ilimi wanda ya Zauna agidansu Rumana Har ya kamallah Digree dinsa,sai Yaje Service dinsa ya Dawo Daddy Alhaji Sunusi Tureta da suke Kira Daddy ya shiga ya Fita har ya samu Gurbi a police staff Colloge Acadamy Dake Jos chan yaje yayi Short Service dinsa Ya Fito a matsayin ASP,yayi aiki A bambamtan wurare kamar Kaduna,Zamfara,Kano Lokaci Bayan Lokaci kuma kwazonsa na sawa yana samun karin Girma Shekaru Biyu da suka Gabata ne ya samu Mikamin DCP lokaci Daya kuma ayi Posting Dinsa zuwa wannan Babban Headquater din na Parthercourt,Lokaci Daya suka Bashi Quaters Din ma"aikata inda anan yake Zaune ya mallaki Motan Hawa da kudade da baisa iyakarsu ba da Kudin albashinsa Duk da yayi ma iyayansa Hidima kuma yana kan yi musu Har yau har Gobe bai Gaza ba.
Rumana yarinyar da Har yau har gobe Yake Girmama Muradinta da Burinta na Son karatu da Zama Wata Mace abun Alfaharin Iyayanta Wata Rana ayanzu Haka Rumana Tana University of Lagos Tana Shekarta ta Karshe ne A medicine Alokacin Data Fadamai Ambition dinta bai kalleta a mtsayin wacce Zatayi ba sai gashi ta bashi mamaki yau tana ma Shekararta Ta Karshe ne,Jaruma ce kuma Jajirtattace kan Abunda ta sakama Gaba Mayyar karatu ce ko shi Wani Lokacin yana Sara mata Sai dai Duk yadda yaso Diza ta kasance irin Rumana Burinsa bai Cika ba Tunda ba Ra"ayinta bane,Diza tundaga Secondary Bata Cigaba da makaranta ba Duk kuwa da Kudin Mahaifinta bai zai cega wani Abu na Cigaba da Diza ta samu Bayan Shudewar wannan Shekarun ba abu Daya zai yi Tunawa Shine Bata zauna Haka ba Tashiga makaranta Koyon Sanks Na Shekara Daya Tayi Training har ta kware Sai kuma ta shiga Makarantan Koyar daMakeup Har ta kware ta zama makeupartics,Yanzu haka Ta Bude Classes din a Online na Kiyar da Snaks,Tana Odar ko'ina kake so a Fadin Nageria Ashekaran Daya gabata Daddy ya Gina mata katon Waje Inda akayi Lonching din Bude wajen mai Suna DIZA SNAKS AND MAKEUP CENTER.. anan Zaria dogara Dake cikin zaria,anyi Lonching din ammh bai Hallarta ba Sai dai Daga Dizan Har Uban Gayyar Mansur sun Turomai Hotonan su Aranar da akayi Murnan Bude wajen.
Banda wannan Abubuwan Guda Biyu bai hango ma Diza wani Cigaba data samu ba,Ammh a wajenta Tana ganin Hakan ma babban Cigabane gareta Domin Ta samu Abunda Take Nema kuma Burinta ya Cika Daga Daddy Har Mommy ba wanda ya Takura mata kan sai Tayi karatu Domin suna Bin Ra"ayinta ne kan Abunda take so ne,Bangaran Uban gayyar Kuwa Zai iya cewa Duka Burinkansa Allah ya Cikamai a yanzu Haka Mansur Ya shiga Siyasa Tsudum Tun Kuruciyarsa yana Da Shekara 25 aduniya ya Nemi Kujeran Kansilan Yankinsu na Zaria Daddy ya goyamai baya kuma ya samu Nasara ayanzu Haka Mansur yafishi kudi da samun Abun Duniya ya mallaki Gidaje Da Motocin Hawa,yakai Hajja da Baba makka da Aiya Sun Hada Hannu Shi da Mastur sun Buge Gidansu sun Sauyamai Fasali ZUWA na zamanii kuma sun Fadadama Ma Babansu kasuwancinsa Yanzu Baba Habibu sai yaga Dama zai je Kasuwa Shagunansa na Hatsi ba su adadi Duka ya saka yara Har yazo ma yau Usmanu awajensa yake cin arziki Tunda shi Jalin nashi yana Tarawa ne suna karewa.
Son Siyasar Mansur ajininsa Take Da kuma Biye ma Muradin Diza Tun bayan kamallah Secondary ya samu nasarar Fadawa Jami"ar ABU dake Zaria inda ya karanci Political Sceince,Kuma Shigarsa makarantan Yazo mai da Nasarori masu yawa Domin Tun yana aji Daya ya Fara Siyasan makaranta,Har takai Suna aji 3, ya rike Mukamin President na Daliban ABU Gabadaya,Bayan Kamallawansa kuma Daddy ya Takamai Baya ya Fada Siyasa,ka"in da Na"in Alokacin Baba Habibu yaso ya nuna Rashin Amincewarsa Mastur ya yi mgana Dashi kan ya barsa yayi Ra"ayinsa Toh in kace abu nan ne Zakaci abinci Cikin Lokaci Kadan Sunan Mansur Sulaiman Doguwa ya Zagaye Zaria da kaduna Gabadaya alokacin Zaben kasililon ya samu Barazana ganinsa yaro kuma bashi da mata ammh kuma Daddy ya Shige mai gaba komai har ya samu kujeran Kansilan Shiyar Zaria,Bayan sun Gama Shekara Biyunsu sun sauka Yanzu Haka Neman Kujeran Chairman yake yi Domin yace sai ya Cikama Diza da Hajja Burinsa sai ya zama gwamna Watarana,Ayanzu Haka Mansur Dake da Kimamin Shekara 29 aduniya ammh kudi da Nasaran Rayuwa sun Lullubesa ya sauya kamar bashi ba kuma Har yau gobe Duk inda ya saka Kafa nan Diza take sakawa sai dai bata zuwa Taronsu na Siyasa ammh Ta karan Rakashi Taronsu na Partynsu Duk wanda yasan Honourable Mansur Doguwa yasan Lady Diza Sunusi Tureta mai mallakin Wajen yin Snaks da kuma Kwalliya mai kayatarwa Ayanzu da Girma ya kamasu akwai Cigaban Rayuwa sosai atare dasu.
Ajiyar rai kawai ya Sauke lokaci Daya ya Bude Dara Daran Idanuwansa kafin ya Dago da kansa yana Mikewa alamun gajiya agogon Hannunsa ya Duba 12:40pm na Rana kansa ya Dafe Lokaci Daya yana Mikewa ganin yadda ya bata Lokaci yana wasu Tunane tunane ko Daya bai yi aikin gabansa ba,Karamin Tsaki yaja kafin ya Ture kujeran Dayake kai ya Mike bai Dauki Komai ba Daga wayoyinsa Har System din nan ya barsu ya Shige karamin Dakin Lokaci Daya yana Balle Botirin Hannun Rigansa bai Dauki Lokaci ba sai gashi ya Fito Fuskarsa da Ruwa alamun alwala yayi Hulan kansa ya ijiye kan Tebur din kafin Ya Tura Kofar Office din ya Fice Domin Zuwa Dan karamin masallacin Dake Cikin Headquater Domin Gudanar da Salla,Dayake Gari ne Daya Hada Mutane Dabam Dabam akwai ma"aikatan da ba Musulmai ba Ko acikin Yan Sanda basu da yawa Shiyasa Inda suke Gudanar da Ibadansu wani Kebenttacen Wajene da suka samar dashi da kansu.
Yanzu ne muka Shiga Mafarin Gudarin Labarin....Ku cigaba da Bibiyata na Tabbata bazaku yi Nadama ba..