10
SADAUKARWAR SO..!!
(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)
Wattpad:@Jamilaumar315
Mallakar:Jamilaumar(Janafty)
Page1️⃣0️⃣
SOKOTO
Area:Sama Road
"Misalin karfe 7:50am na Safiyar Ranar Asabar ce Garin yayi sanyi Dayake an kwana ana Ruwa jiya Da Daddre Dayake Lokacine na Damuna sai aka wayi Gari cikin Sanyi Sanyi da Ni"ima mai Dadi.
Mai adaidata ne ya sauketa Adaidai Kofar wani katon Gida mai Bakin get,Tana Daga Cikin adaidatan ta Sauko Waje Tana Laluban karamar Jakarta Dake Rataye a Kafadanta ta Ciro Kudi Dubu Daya ta bama mai adaidaitan yana Shirin bata Chanji Tace ya barsa nan da nan ya Fara mata Godiya,Fitowa yayi ya taimaka mata Ya Fito mata da Manyan akwatunta guda Biyu Har Zuwa Gaban get din Gidansu Godiya tamai yace bakomai Kafin ya koma yaja adaidaitansa ya kara Gaba.
Tsaye Take bakin get din bayan ta saka Hannunta ta Buga Lokaci Daya tana gyara zaman karamin Hijabin Jikinta Ta gaji matuka sai wani lumshe ido Take Gasu sun Dan kumbura Saboda Rashin Barci Pakiatan ne Riga da wando ajikinta Sai ta Saka Karamin Hijabi a saman kanta Saboda Zafi Tun karfe Shida na yammah Jiya ta Hawo Motar Express din masu Zuwa arewa Daga Lagos Kawai Tana so Tayi Tafiyar Mota,Hakan na Burgeta,Sun samu Break ne na Sati Biyu Kafin su Fara Final Exam dinsu taso ta zauna Cikin makaranta Tayi karatu sai kuma Kewar Gida ya kamata Shiyasa ta yanke Shawaran Tahowa ko Sati Daya Tayi ta koma Bata Kira Kowa ba Daga Abba Har Umma basusan da zuwanta ba sai dai su ganta kwatsam Tana son ta basu Big Suprise ne.
Lokacin da Megadi ya Bude karamar Kofar yaga Rumana Shima kansa yayi mamaki sai ya Shanye ya Fara mata Sannu da Zuwa,ta amsa Cikin Fara"arta Tana gaishesa Shi ya Daukan mata Akwatunan nata Zuwa Cikin Gidan bayan ya Bude karamar Kofar.
Tunda Taga Babu Motar Abba Tasan ya Fita ammh Duk da haka sai ta kalli megadin Tana Fadin"Abba na ya fita ne..? Cikin Girmamawa yace"Eh bai Dade da Fita ba karamar Hajiya.."Dama haka yake Kiranta kai ta gyada Cikin mamakin Fitan Abba yau da wuri haka sai tayi Tunanin kila wani Uzuri ne ya taso mai da Gaggawa Haka Suna Tafe har suka Shiga Babban Falon Gidan Megadin ne agaba Tana Binsa da Abaya.
Ba kowa afalon sai karan Talabijin din Dayake ta Faman Ruru ita kadai,Bude Murya Rumana Tayi ta kwada Sallama Tana Fadin"Umma..Gani na Dawo..Goggo Jummai kina ina..?
Take Fada Tana Bin Hanyar Kitchen din Megadi kuma nan Tsakiyar Falon ya ijiye mata akwatunan ya Fice,Wata Yar Dattijuwa ce ta Fito Daga Cikin Bakinta Kamar zai yage Saboda Farinciki cikin Murna Take Fadin"Muryan wa nake ji kamar ta Diyata Rumana..?
Bata idasa Rufe baki ba Rumana ta Fada Jikinta Tana Murnan ganinta Itama Goggon Jumman Rumgumeta Tayi Tana Fadin"A"a Bakin Ikko..Da Safe haka..?barka da zuwa.."Dagowa Rumana Tayi Tana Fadin"Daman Surprise nake son baku..Ina Umma Megadi yace min Abbana ya Fita..?..
Goggo Jummai tace"Umman ki Tana sama Abban eh ya Fita Tun Safe ko karyawa ma bai Tsaya yayi ba..Rumana Kin Rame ko Duk karatun Bokon nan da kuka sama Ranku ne..? Rumana na Dariya Fararan Hakoranta suka Bayyana Ta Lumshe ido Tana Fadin"Bakomai Goggo Jummai watarana sai Labari. baki son Kiji ana Kirana Dr.Rumana ne..?
Goggo Jummai ta Shafa kanta Tana Fadin"Sosai ma..Ina son Diyata ta zama Likita Watarana Ko Bana Raye Ta zama abun alharin kasarta.."Rumana Tace"Kina ma Raye Goggo Jummai kinsam bana son irin wannan mganar ko..? Kina so mu Fara Fada Daga Dawowata ko.?
Kafin Tayimgana wata Matashiyar bakar yarinya Ta Fito Daga Cikin Kitchen Din Tana Fadin"Sannu da Dawowa karamar Hajiya.."Tafada Harda Rankwafawa Amsawa Tayi Tana kallonta Kafin Tace"Juma Daman kina Nan..? Kai ta gyada Tana Fadin"Eh ina Ciki ne ina aiki.."Goggo Jummai tace"Kina dai Shiriritarki ta Fama Juma..Maza kwashi kayan Ruma ki kaimata Cikin Dakinta Kamar Umma ta san kina Tafe Shekarajiya tace ma Juma ta Shiga Dakin ki ta gyara Miki yayi kura.."
Rumana Tayi Mirmishi Tana Fadin"Shiyasa nake son Ummata.."Tafada Tana Shafa Jikinta,Lokaci Daya tana wani Yamutsa Fuska Tana Fadin"Goggo Jummai yunwa nake ji Wlh..Rabona da abinci Tun Jiya.."Ta Fada Daidai Lokacin da Juma ta kwashi Akwatunan Rumana Ta Haura Dashi Upstair inda Dakin Ruman yake Dagachan gefe yammah Daga Inda na Iyayanta yake.
Goggo Jummai Ta Juya tana Fadin"Jeki wanka ki Sauya kaya Kafin Lokaci na Hauro Miki Da kayan karyawan naki Sama.."Kai ta Girgiza Tana Fadin"A"a Bazan saka Kakata aiki ba..Keda baki da lafiyan kafa Sai ki Hau Bene da Kaya ahannunki.? Salon ki kara Turdemin yar kafan taki a rika Kirana kakar Rumana mai Karyayyiyar kafa..? Ta karishe Fada Tana Dariya Goggo Jummai tace"Ai Diyata Likita ce bani da Damuwa.."Juyawa Rumana Tayi Tana Fadin"Nidai kada ki Hauro Dashi..Zan sauki na karya Tare daku Goggo..Umma kuma Ko Ta Fito kada kice mata na Dawo so nake ta ganni kamar Daga sama.."
Cikin Kaunar Rumana Har Cikin Ranta Tace"Shikenan Diyata Afito Lafiya.."Daga haka ta juya Tana Tafiya sannu Sannu ta Shiga Kitchen ita kuma Rumana ta Fara Haura step Zuwa saman Bene Tana Shiga Dakinta Taga Juma gaban Madubi Tana ta kallon kanta Rumana ta Dade Tana kallonta Tana Dariya kasa kasa Halin Juma sai ita.
Gyaran Murya Tayi Tana Fadin"Juma Sarkin kallon madubi An fara kenan ko .? Jin muryan Ruma yasa ta waigo da Sauri Tana Sosa keya Tace"Ayi Hakuri karamar Hajiya.."Bata ce mata komai Har ta Fice Tana wani Sunne kai Binta Tayi da kallo kafin tace"Juma Bansan yaushe Zata Gane ta zama yanmata ba..
Tafada Lokaci Daya Tana Ijiye Jakarta Saman gado,Kafin ta Fada kan gadon Lokaci Daya Tana Fadin"I miss My Bed.."Take Fada Tana Dariya Ta Dade kafin Ta Mike Karamin Hijabinta ta Cire Ta Tura Kofar Tiolet din ,Ta Shiga Bata wuce Minti Talatin ba sai gata Ta Fito Dauke da Rigan wanka ajikinta kanta Ta nannadeshi da karamin Towel.
Kan Madubi Ta Nufa Ta ja karamar Kujeran Dake wajen ta Zauna Ta Fara Shafa Lotion dinta na Man Olive,Har ta gama batayi wani kwalliya ba ko Hoda bata Shafa ba,Ta Mike ta isa Gaban makeken wardrope dinta Ta Bude ta Dauko Wata Doguwar Rigar Atamfa,Ta Saka Bayan ta Zare Rigar Wankan Dake Jikinta da Towel din,Dankwalin Atamfan ta Daura a saman kanta Ta Dauki Rigan wanka Ta maida Tiolet bayan ta Shanyasu Cikin wata karamar Igiya Ta Fito kenan Taji karae Bude Kofa Tana Dagowa suka Hada Ido Hudu da Umma Waro Ido Tayi Tana Fadin"Ummata.."
Tafada Cikin Murna Da Farinciki Lokaci Daya ta isa Gareta Ta fada Jikinta suka Rungume juna Hajiya Farida na Dariyan Farincikin ganin Yarta kwara Daya aduniya ta kara Riketa Tana Fadin"Ai ni Fushi nake dake Ruma..ace ki Dawo gidanan bansani ba.."Dagowa Rumana Tayi Ta Shagwabe Tana Fadin"Waya gaya Miki..? Nafa cema Goggo Jummai is a Suprise"
Umma na Dariya tace"Juma ta Gayamin..Ai kinsan Goggonki bazata Fadamin ba Tunda bakin ku Daya.."Rumana ta Tura Baki Tana Fadin"Kai Bakin Juma kamar Sikat ba"a Sirri da ita.."Umma na Dariya ta Shafa kumatunta Tana Fadin"Ruma ta ta Rame sosai.."Tafada Tana Taba Wuyanta Cikin Shagwaba Rumana ta kara Rungumeta Tama Fadin"Umma na Karatu ne..Dole na Rame bama ssamun Hutu sosai..kuma ba Jirgi na Biyo ba Jiya na Taso kwana mukai Tafiya Doguwar Motar nan ta Express na Shigo ."
Umma Ta Zaro Ido Tana Dagota Daga Jikinta Tana Fadin"Mota..? Baki da Hankali ne Ruma..?yadda Kasar nan ta lalace ba Tsoro da wani abu ya Faru Dake fa..? Ta Fada Cikin Bacin Rai ganin yasa ta Kama kunnuwanta Duka Biyu Tana Fadin"Ba gashi na iso Lafiya ba Umma..? Kiyi hakuri bazan Kara ba.."Bata iya Fushi da yar nata Sai Ta Cire mata Hannunta a kunnuwan Tana Fadin"Shikenan ya wuce..Muje kasa ki karya Na kira Abban ki na gayamai kin Dawo yana ta Murna wai kun samu Hutu ne..?
Rumana Ta juya Tana Fadin"Umma bari na Dauko Wayata..Eh..Mun samu Breaks ne na Sati Biyu Zamu Fara Final Exam dinmu Shine nace Bari nazo nayi ko Sati Daya ne Sai na koma kewarku keda Abba Duk ta Isheni bata barina ma Cin Abinci.."Tafada Bayan ta Dauko Wayar nata Daga Cikin Jakar Data Dawo da ita Ta zo Gaban Umman,Wacce ta Rike Hannunta suka Fice Daga Dakin Tana Fadin"Muma muna kewarki..Bamu da yarda Zamu yi ai Karatun yazo karshe..Sai Service ko..?
Tafada Tana kallinta suna Saukowa Daga Upstair kamar wasu yaya da kanwa Ruma Tace"No Umma sai munyi Intenship na Shekara Daya kana zamu Tafi Service.."Kai ta gyada Tana Fadin"Kuma..? Allah ya Taimaka achan zaki Intenship din...?
Tafada suna Zama kan Daya Daga Cikin kujerun Falon,kai Rumana ta Girgiza mata Tana Fadin"A"a Umma..Arewata zan Dawo..Nan Uduth zan yi in na samu Insha Allahu..'"Umma tace"Allah ya Tabbatar mana da alheri.."Daga haka suka Cigaba da Hiransu Sama sama Rumana da latsa wayarta Lambarsa ta Kira ammh kuma bai Daga ba Sunfi Sati basu mgana Dashi ba Karatu ya sha mata kai Shi kuma bai Kirata ba sako Ta turamai Ta gayamai sun samu Hutu Tazo Gida da kuma Rokon Addun"a Zasu Fara Final Exams dinsu.
Juma ce ta Gabatar musu da Breakafast Saboda Ruma yasa Umma tasaka ta Shimfida Babbar Darduma Saboda in Tana Gida Bata son cin Abinci Saman Dining tafi son Ci kam Darduma a kasa,Nan aka Baje musu komai Rumana ta matsa Tace Tare da Juma da Goggo Jummai Zasu karya Umma bata Damu ba sanin Halin Rumanan Goggon jummai ce ke Baya Baya Juma dai ba Ruwanta Shirishirintanma ya Isheta Yan Garinsu Abbanta ne Daga Wamako Abba ya Dauko Goggo Jummai Domin ta Taimakama Umma Tun Tana da Karfinta Tazo Gidan Tun Ruma na karama akwai Shakuwa Sosai Tsskaninsu Kuma Ruman tana Daukanta kamar kakarta Ita ta sakaa mata ma sunan Goggo Jummai,Lokacin da karfinta ya kare ciwon kafa da Ciwon Baya sai Umma Dataji Dadin Zama da ita tace ta Dauko mata Daya Daga Cikin Jikokinta sai su Zauna Tare ita ta rika yin aiki,goggo Jummai Taji Dadin karamincin Su Umma Juma Jikarta ce Diyarta ta Fari ta Haifeta ta Rasu,ita Dauki yar Shekara 15 aduniya suna Zaune Tare Duk da Ciwon kafan Datake Fama Dashi Bata zama Haka batayi aiki ba komai na Bukatar Rayuwa Umma da Abba suna yi musu a yan"uwansu suka Daukesu ba masu aiki ba.
Tare Dukkansu suka karya Suna Hira suna Raha bayan sun gama Juma ta kwashe komai Zuwa Kitchen Goggo Jummai Tatafi Dakinta ta Dan kwanta ta huta suka bar Ruma da Umma anan Falon suna Hira Har wajen Azahar sai da aka Kira Sallar azahar kana kowacce Tayi Dakinta Ta gabatar da Salla,Rumana Barci ne a Idonta Sai kawai Tabi Lafiyan gado Ta kwanta Domin jiya Batayi barci ba kasawa tayi,Tana kwanciya Barci ya kwasheta Cike da Tunanin Mastur acikinsa.
Sai Bayan La"asar TaTashi Shima Sai da Umma ta Shigo ta Tasheta Tayi sallah Kana tatashi Tayi wanka ta Sauya kaya Zuwa Riga da wando na pakistan Daman yawancin kayanta kenan Bayan ta idar da Salla ne ta Bude akwatunanta Dama Daya na kayan sawanta ne Daya kuma na Littafan karatunta sai System dinta,System din ta Dauka Littafan kuma ta Xube su Kan gadonta Domin karatu Zatayi kamar Hauka irin karatun da masu wasa bane,Earphone dinta Ta Dauko ta Saka a wayarta Bayan ta saka Karatun alqur"ani ta Toshe kunnuwanta Ta Bude System dinta ta Fara Karatu bayan ta saka Sirrin Gilshinta mai kara Mata karfin gani Umma ta Lekota ganin tana Karatu yasa ta Kyaketa Ta yi Karatunta Rumana Bata Tashi Daga Karatunta ba sai da aka Kira Mangariba kana Tatashi ta Fada Tiolet ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Ta Zauna Tana azkar Umma ta leko Tana gayamata Dawowar Abbanta Ko Hijabin Jikinta Bata Cire ba tabi Bayanta Tana Murna.
Afalon Sama ta gansa Rumgumeshi Tayi Tana Murnan ganinsa Shima Riketa yayi Cikin Farinciki,Yana Shafa kanta Gefensa ya Zaunar da ita yana Fadin"Rumana ya karatu..?
Shagwabe Fuska Tayi Tana Fadin"Ba Dadi Abba..Wlh Kamar zamu Haukace fa..Yanzu fa Bayan mun bar asibitin Cikin makaranta ne aka bamu Sati Biyu muyi Karatu kafin mu Fara Jarabawar Karshe.."Yana Shafa kanta yace"Masha Allah..I know my Dota..Zata iya da yardam Allah..Allah ya bada Sa"a Dr Rumana Muhammed wamako.."kanta yayi Girma da Kirarin Abban nata ta Washe Baki Tana Fadin"Nagode Abbana..Ina alfahari Dakai sosai kaida Umma.."Shima Mirmishin yayi mata yana Dafa kanta yace"Muma muna alfahari Dake Rumana.."Umma ce Dake jeramai abinci nan gabansa Take Mirmishi Nam Abba ya Sauko Da Rumana da Umma suka Hadu sukayi Dinner a sama Bayan sun gama Ruma ta kwashe komai Zuwa Falon kasa Juma ta karba Zuwa Kitchen Dakin Goggo Jummai ta Leka ta gaisheta,Ta isleta Tana kan Sallaya Tana Lazimi Bata wani Jima ba ta Koma Dakin Umman nata ta Zauna Gefensa suna Hiran su Sama sama Tana sska musu baki Cikin Farinciki yau gata ga iyayanta Masu Soyuwa Gareta.
Suna Cikin Hiran ne Wayar Abba ta Dauki kara Ya Dauko Ta Daga Cikin aljihunsa yana Ganin mai Kiran ya saki Mirmishi yana Fadin"D'anki Farida Mastur.."Umma ta Washe Baki Tana Fadin"AllH Sarki DCP zakace min Nima da Safe ya kirani ya gaisheni Yaron nan Wlh bantaba ganin mai Datttako irinsa ba Kamar wani Babba.."
Abba yace"Bari..Bari Farida..Yafada Lokaci Daya yana Daga Wayar Cikin Sallama Rumana Dake gefe Tayi Lambo ajikin Abba kamar bata jinsu nan kuwa Gabanta ne ke Fadi Kiran sunan Mastur kadai da Abba yayi yasa Jikinta ya saki Ta Tuna Ta Turamai sako ammh Bai Kirata ba Daman baya Kiranta sai in ita ta Kirashi baya Daga Kiranta zai bari ta yanke ya Biyo baya Tana ji suna mgana da Abba yana gayamai ta Dawo Gida Daganan aka Bama Umma suka gaisa sai kuma Sukayi sallama.
Umma ta kada kai Tana Fadin"Iyayensa sun yi Dacen D"a..Wlh Ina Sha"awarsa..Babu Ruwansa akwai Hankali da Tarbiyan gashi dai bashi da yawan mgana Ga shi ba wani Babba ba sai Halin Girma.."Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Ai Alhaji Sunusi yace Sak Hallsyansa Ubansa ne..Haka Mahaifinsa yake Baba Habibu.."Umma tace"Ai har Mahaifiyar tasa..Hajja ai akwai kawaici da Halin Girma.."duka Hiran nasu na Yabon Mastur ne Tana Jinsu Batace komai ba Sai da Abban ya kalleta yana Fadin"Rumana kinyi Shiru baki ce komai ba..? Kina kiran yayan naki kuna gaisuwa kuwa..?
Kai ta gyada Tana Fadin"Eh Abba.."Mirmishi yayi yana Fadin"Allah yayi miki albarka..Babanki na Zaria nata Cigiyanki yaushe zaki mai Hutu ki kwana Biyu.."Rumana Ta muskuta Tana Fadin"Abba sai na Gama Exams na Dawo Gida kafin na Fara Intenship.'Umma tace"Yadai kamata kam Ruma..Hajiya Asiya ma Tagaji Da min Magiyan yaushe Ruman Zataje Suna Daga Kafa ne saboda Karatunta.."
Abba yace"Zataje Tayi Musu Hutu Insha Allahu Koma kije Chan Asibitin ABU Kiyi Intenship Dinki ko Service dinki.."Rumana ta Dago kanta Tana Fadin"Abba sai inda na Samu fa..Sai anyi Exam duka zan je nayi in na samu Shikenan.."Umma tace"Zama ki Samu..ko nan Sokoto ko Chan Zaria Duk inda kika samu duk Gidane..'Rumana bata kara mgana ba Abba ne yace"Kuna waya ko da yar"uwanki Diza..? Kinsan Ta Bude Wajen Makeup da Snaks,..?
Rumana Tace"Eh Abba...muna Taba Chart da ita sama sama..Ina kuma Following dinta Duka Social medianta Ina ganin posting din abubuwanta na Tayata Murna Abba sai dai Why Taki Karatu..?
Umma tace"Bata Ra"ayi ne Rumana..Ba gashi kuma Allah yasa ma Abun albarka Hajiya Asiya na gayamin irin Ficen da Dizan Tayi a Chan Zaria da kaduna.."Abba yace"Sosai ma..Kowa fa da hanyar Cin Abinsa baka ga Mansur ba Dan Wajen Shi Habibun Daya ke Riko .Kamar waasa Siyasa Ta zama Hanyar Cin Abincinsa.."Umma tayi Dariya Tana Fadin"Honourable kenam..Shi kuma ai dan Barkwanci ne ko Wasa da Dariyansa yaci a Zabesa...Abokin Diza kenan Tun na yarinta.."
Rumana Duk Tana jinsu Bata ce komai ba Ganin Ta gundura da yin Hiran yasa ta Tashi Tana Fadin"Umma Da Abba..Sai da Safe Zanje nayi karatu na kwanta.."Sukayi mata sai da Safe Kana ta Fice Zuwa Dakinta suka Bita da kallon Sha"awa.
Wanka ta sakeyi tayi Sallar Isha"i kana ta saka Kayan Barci Tazo ta Hau gado Duk yadda Taso Tayi Karatin ta kasa Saboda Tunaninsa,Shiyasa wani Lokacin bata so Tunaninsa yazo mata Sai ya Hanata Sukuni wani Lokaci sai ta maida kanta Kullum Cikin karatu Saboda kaucema Tunaninsa Sai dai yau yaci karfinta Kowa yabonsa yake..Kowa Sonsa yake saboda kyawawan Hallayansa Ture Littafan gabanta Tayi ta Jawo Wayarta Ta Lalubo Lambarsa Data sakama Emoji na Zuciya da makulli ta Dokamai kira.
******
Fitowarsa Daga wanka kenan Daure da Towel a kugunnsa Jikinsa Duk yana Digan Ruwa Daga kan gadon da wayoyinsa ke Zube yaga Babbar Tana Haske a Silent ya sakata kafin ya Shiga wanka.
Karisawa yayi kusa da wayar ganin Sunan Rumana yasa ya Dafe kansa bai Daga Kiran ba Sai da ta katse kana ya Dauko Wayar ya Shiga wajen Sako ya Fara Mata Rubutu.
Me kike yi baki kwanta ba Har yanzu Rumana..? Akwai Exams agabanki..ya kamata by Now kin kwanta saboda kwalkwawarki ta zama Fressh Abunda kika Karanta ya zauna Miki..Kada ki Damu ki kwanta u Took in d Mrning Gud Night..
Daga Haka ya Tura mata Lokaci Daya ya Maida wayar saman gado ya isa gaban Madubin Dake Dakin ya Fara shafa Lotion,sai da ya gama kana ya isa gaban wardrope din Dake Dakin Cikin Hanger ya Dauki Jallabiya ya saka yunwa yake ji Silafas dinsa ya Zura ya Fita Zuwa Kitchen ya manta bai yo Takeway ba kafin ya Shigo Gida kuma ya Kira Wani Sargent din Kamar Shiga Hakki ne.
Kitchen din Dake Cikin Apartmemt din da gwannati ta bashi yake zaune ya Shiga gas ya kunna ya Dora karamar Tunkunya ya saka Ruwan Zafi Yana Zafi ya kashe Gas dim ya Fito Falon Dayake Babba yaji kujerun alfarma wajen Dinning ya Nufa inda kayan Tea suke ya Hada nan ya Zauna yasha kadan bada yawa ba ya Ture kofin ya Mike Zuwa Falom kan Daya Daga Cikin Kujerin Falon ya Zauna ya Dauki Remot yana Sarrafa Tibin Dake kunne Tun Fitowarsa..
Tashar NTA Ya kamo yana kallon Labarai Cikin Harshem Turanci kansa ya maida Saman kujeran ya Jingina Lokaci Daya yana Dora kafa Daya kan Center Table din Dake Tsakiyar Falon ya Rage ma Idanuwansa Karfi Kamar mai jin Barci nan kuwa Duka Hankalinsa na kan Abunda yake kallo ne.