AMRAH PART 07
AMRAH
<<PART 07>>
Boka Durwas yana tafe a gaba, Amrah tana biye da shi a baya, kamar raƙumi da akala. Duk inda ya shiga sai ta bi shi. Sun yi tafiya mai ɗan nisa, kuma ranar ta yi zafi sosai. Amrah ta gaji, ƙafafunta sun fara harhaɗewa, don haka ta koma tafiya da sassarfa. Amma saboda rashin imani, Boka Durwas sai ya rinƙa hankaɗa ta yana ɗura mata muguwar ashar. Haka ta daure, ta ci gaba da tafiya. Jikinta duk ya yi laushi, bakinta ya bushe, ga yunwa da take nuƙurƙusar cikinta.
Yayin da suka zo dai-dai wata ƙatuwar bishiyar kaɗanya, Boka Durwas ya ja hannunta zuwa ƙarƙashin bishiyar suka zauna. Ya buɗe jakarsa ya ɗauko wani busashen nama wanda ko soya shi ba a yi ba, ya hau ci yana korawa da ruwa.
Ya jefo wa Amrah ma, ya ce ta ɗauka ta ci. A yatsine ta kalli naman, ta girgiza kai alamar ba za ta ci ba.
Dariya Boka Durwas ya yi ya ce, "Yarinya gara ma ki ɗauka ki ci, don idan muka ƙarasa, ko minti biyar ba za ki ƙara yi a raye ba. Iyalan Boka Rubbas da kika kashe, sun shirya tsaf domin ɗaukar fansa a kanki."
Amrah ta ce, "Ni ba zan iya cin wannan abincin naka ba, gara na mutu da yunwa."
Girgiza kai Boka Durwas ya yi, ya ɗauko salkar ruwansa ya kwankwaɗa, ya yi wata ƙatuwar gyatsa, sannan ya baje a ƙasa. Sanyin inuwa ya kwashe shi, bacci mai nauyi ya ɗauke shi.
Amrah tana ganin haka, sai ta tashi tsaye, ta yi girgiza, ta rikiɗe zuwa siffar wani ƙaton gizo-gizo. Jikin gizo-gizon gaba ɗaya wani irin gashi ne mai tsini kamar allura. Nan take, ya fara canza launi daga baƙi zuwa fari tas, zuwa ruwan ganye, zuwa ruwan ɗorawa.
Wata baƙar yana mai tsinin gaske kamar mashi ya feso daga bakinsa. Yanar ta tafi da gudu, ta soki Boka Durwas a goshinsa. A firgice ya farka yana waige-waige. Karaf idanunsa suka sauka a kan Amrah da ta rikiɗe zuwa mummunar siffar gizo-gizo.
Da sauri ya ɗan ja da baya, yana neman jakar tsafinsa. Can gefe ya hango ta tana ci da wuta! Ya laluba gurayen tsafin da suke jikinsa, nan ma ya ji babu ko ɗaya.
Cikin tsananin tashin hankali da firgici, ya takarkare ya kwarara wani uban ihu wanda ya cika dajin gaba ɗaya. Shekarun da ya ɓata, da wahalhalun da ya sha kamar zai rasa ransa wajen tattara ilimin wannan tsafin, su suka fi ɗaga masa hankali. Ga shi a lokaci ɗaya, Amrah ta lalata masa komai.
Wata wuƙa ya zaro daga ƙugunsa, ya nufo gizo-gizon cikin baƙin nufi. Tun kafin ya ƙaraso, gizo-gizon ya feso masa yana mai kama da net, ta lulluɓe gaba ɗaya jikinsa. Ta yi masa ɗaurin goro yadda bai isa ya iya motsa ko da yatsansa ba.
Tana gama ɗaure shi da yana, sai ta rikiɗa ta koma Amrah ta asali. Ta bushe da dariya ta ce wa Boka Durwas, "Yanzu ina tsafin naka? Kar ka yi tunanin ka samu nasarar tahowa da ni ne da ƙarfin tsafinka. Na biyo ka ne don ba na so na yi maka mummunan kisa a gaban jama’ar da suke matuƙar jin tsoronka, saboda ba na so su tsorata da yawa. Kai ma yanzu zan gama da kai, kamar yadda na gama da shugabanka Boka Rubbas."
Cikin ƙarfin hali, Boka Durwas ya ce, "Ƙarya ki ke yarinya, ba ki isa ki yi nasara a kaina ba..."
Tun kafin ya gama ɓaɓatunsa, Amrah ta busa masa iskar bakinta. Iskar ta rikiɗe zuwa baƙin hayaƙi ya zagaye jikin Boka Durwas. Sannan ya rikiɗe zuwa kunamai masu yawan gaske! Suka yanyame jikinsa, suna cizonsa. Yana ihu da kururuwa. Amrah tana tsaye a wuri guda tana kallonsa tana dariya.
Gaba ɗaya jikinsa ɗaure yake da yana, babu damar ya motsa. Yana ji yana gani, kunaman suka rinƙa fincikar naman jikinsa suna jefarwa. A haka har ransa ya rabu da gangar jikinsa, ya daina motsi.
Hussain Yusuf✍️