Kuncin zuci
by @bintuuu
Zaune suke a falon suna hira banda Laila da ta wani bata fuska tana jin ranta duk a dagule, wayanta ne riqe a hannunta tana sake trying line na Ahmad for the 50th times baya tafiya, ta sake buga tsuka tana jin kamar tayi ihu ko zataji dadi, Anty Murja ce ta kalleta tace "Ke kuma ke da wa? meye hakan muna zaune zaki rinqa mana tsuka" adan fusace Laila tace "Babu ruwanki dani" Anty Murja zatayi magana Mummy ta dakatar da ita dalilin daga mata hannun da tayi, shiru Murja tayi ta kama hararan Lailan... sai Mummy ta juya tana kallon Lailan tace "Wayan nasa bai shiga bane Auta" Laila tayi cilli da wayan anan kan kujera tace "Mummy da alamu blocking dina yayi, kuma wallahi zai san ni yayi blocking" Anty Murja ta buga wani tsukan itama tace "Banza wahalalliya, an fada miki namijin da baya yinki zai taba sauraronki ne, kin tsaya kina batawa kanki lokaci kamar wata mayya, may be yanacan ya samu wata ma bata ke yake ba" Nan Laila ta miqe ta fara masifa idonta rufe tana cewa "Nifa ki fita harkata kar in karta miki rashin mutunci..kuma wallahi kinji na rantse ko za'a hada sama da qasa sai Ahmad ya aureni, ni kadai dinnan zaki gani" Mummy dake kallonta tace "To wayace daman bazai aureki ba Auta, ai hanyar da kikaqi tun farkon ita zamu bi yanzu, cikin sauqi ze shigo hannunki" Anty Murja tace "Barta Mummy ta tsaya nan, anfada miki zamanin yanzu ko da namiji yana sonka basai ka hada da dan dabarbarun layoyin nan ba sannan a zauna lafiya, balle ke naki ma a fili kowa yasan Ahmad baida lokacin ki"
Laila ta koma ta zauna tana hucin takaici tace "Dama lokaci nabasa ai Mummy, a tunani na zai dubi kulawata a garesa amma gaskiya ni yanzu ko me za'ayi masa ma ayi, kuma wannan karon a hada da wannan sadaka yallan da tazo gidansu Nafisa, kin tunata ai" Anty Murja tace "Wace kuma haka?" Laila ta amsa da "Wata shegiya ce tana zama agidansu Nafisa ta debo fari kamar wadda jini ya qare mata a jiki, ni tun ganina da ita na farko daman batamin ba" Anty Murja na sauraronta ta sake cewa "Meya hadaku to?" sai Laila ta fara bata labarin abunda ya faru ranan da Ahmad yaje daukansu Anty Amnah gidan Salma da kuma abunda ya faru a Airport ta qara da cewa "Ina tsaye Ahmad ya rinqa kakkama yarinyar nan a gabana Anty Murja" sai Murja da wangale baki ta kalli Mummy dake sauraron Lailan for the second time itama, dan tun ranan da abun yafaru Lailan ta fada mata.
Can Mummy ta sauqe numfashi cikin isa tace "Duk me sauqi ne wannan Auta, ita wannan yarinyar qaramin issue ce, shi Ahmad din zamu bullowa da farko" Laila ta matsa kusa da mummyn ta kwanta a jikinta tace "Wallahi kuma duk sai na rama shariya da wulaqancin da yayi min bayan aure, se ya gane kuransa" Mummy da Anty Murja suka fara dariya Mummy na shafa kan lailan tace "Tsaf ma kuwa Auta har fin hakan".....
Ranan talata sunje makaranta gurin supervisors dinsu, Ahmad ya kira Na'iman a lokacin da ta fito daga office din malamin, dauka tayi tafara gaisheshi, a nutse ya amsa mata sannan yace "Where are you?" ta daga kai tana duban sunan arean da taken a rubuce saman ginin gurin, fado masa sunan wajen tayi sai yace mata "Supervisor'n ya ganki?" ta amsa da "Eh" sai shima ya fada mata inda yake nan wani car park da ake kiran gurin da Westgate, tace "Okay, bari na kira Nafisa ko ta gama abunda takeyi itama" Ya amsa da "Okay" sannan ya kashe wayan, kiran Nafisa tayi daga can bangaren tace "Kinganni yanzu ma fitowa nayi daga office din dan amsa kiran, ki dan bani mintunan kadan sai mu tafin" sai Na'ima tafada mata inda zata samotan inta gama sannan ta kashe wayan ta nufi car park din..
Tsaye ta hangosa a jikin motansa yau kuma har da glass din sa a fuska, ta nufesa idonta na kansa ganin yanda baqin glass din ya qara masa wani masifaffen aji, bata kai da qarasawa gurinsa ba taga wani guy ya fito daga mota nan kusa da ita yace "Na'ima" tsayawa tayi da fara'a tace "Yaya Umar" sai ya rufe cab din motan ya dan taho gurinta yana murmushi yace "Idonki kenan a qasar nan, Ina Nafisa?" Na'ima tace "Kayi hakuri ai mun zata ma ka bar England gaba daya" ya girgiza kai tareda cewa "Inanan" gaishesa tayi ya amsa sai kuma ya fara tambayanta ya karatu, Na'ima ta daga kai ta hango Ahmad tsaye yana facing dinsu at the same time yana kallonsu, juyawa tayi tana bada amsa a guy din akan wata tambaya daya mata na ko sun kusa gamawa, tana cikin magana ta hango Ahmad din ya taho gurin nasu sai ta cigaba da kallonsa har ya qaraso nan ya tsaya kusa da ita yana facing guy din, dan daburcewa Umar din yayi sai ya miqa masa hannu da nufin suyi musabaha, Ahmad ya zare glass din fuskan nasa yana kallon cikin idonsa sannan ya miqa nasa hannun suka gaisa yana amsawa babu yabo babu fallasa, rasa abunda zai sake fada Umar yayi sai ya kalli Na'ima yace "Toh Na'ima sai anjima, ki gaishe da Nafisa please" sai Na'ima ta gyada kai tana murmushi tace "Zataji in Sha Allah, nagode" ya juya ya nufi gurin motansa Ahmad yabi bayansa da kallo, Na'ima ta dan dago kanta ta kallesa ganin irin kallon da yabi Umar din dashi, cikin sanyin murya tace "Meya faru" Ahmad bai dena kallon bayan Umar din ba ya wani hade fuska yace "Sai wani kallon cikin idanunki yake yi while he was talking" Na'ima ta dan ware idanu tafara yar dariya tace "Tun daga can din ka hango haka?" ya juyo yana kallonta "Eh mana, he kept staring at you" Na'ima na murmushi tace "Ni dai ban gani ba" sai ya sake cewa "But who is he? Your ex?" tayi saurin jijjaga kai tace "A'a, abokin Yaya Faruk ne da ya hadamu dashi farkon zuwanmu school" Ahmad ya gyada kai yace "Kallonshi yayi yawa, daya cigaba kawai cire idon zanyi in huta" Na'ima batasan lokacin da tafara dariya ba Ahmad na murmushin shima ya tsaya kallonta baya ko kifta ido, sai da ta tsaya da dariyan yayi qasa da murya yace "I'm serious Na'eemah, for a moment ji nayi kamar in hankadesa" dena dariyan tayi ta tsaya kallonsa cikin Ido tanajin zuciyarta na chanja bugu nan take, cikin kwantar da murya ya qara matsowa kusada ita ya sake cewa "I really want to be your first, kicemin baki taba saurayi ba please Babe" ai nan take Na'ima taji kaman an zuba mata ruwan qanqara aduk jikinta, duk wani annushuwa dake zuciyanta ya bace gaba daya, kauda fuskanta tayi batace komai ba
Ahmad ya sake cewa "Babe" taqi kallonsa ma, zai matso kusada ita tadanyi baya tareda cewa "Please stop" sai ya tsaya din bai kuma dena kallonta ba, ganin yanayinta yasa a hankali yace "Muje mota toh", jerawa sukayi suna tafiyan ba wanda yace komai cikinsu..
Suna isa gurin motan kenan Na'ima ta hango Nafisa sai tace masa "Ga Nafisan can ma" shima ya juya gurin Nafisan wadda take tahowa fuskanta da fara'a, tana isowa tace "Yaya kuyi hakuri na bata muku lokaci ko" yace "A'a Nafisa badamuwa" ta gaishesa ya amsa sannan ta sake cewa "Wallahi riqeni supervisor din yayi and he kept talking in circle, sai je ka dawo yake tayi a maganan bana gane komai, wai nan gyara yakemin a papers din" sai sannan Na'ima tayi murmushi, Ahmad yadan kalleta yana jin ransa na sakewa ganin ta sake fuska...
Yau ma nafisa baya ta shige tabar Na'ima da shiga gaban motan, cikin shiru sukayi tafiyan Ahmad na kallon gefen Na'ima jefi jefi ganin ta juya kanta tana kallon window, sai ya kunna qira'an Qur'ani a motan gashi basu wani tsaya ba kasancewan yau yanada isasshen mai a motan..
Ganin atmosphere din cikin motan ne yasa Ahmad nayin parking a kofar gidan Anty Amnah Nafisa tayi saurin fita, Na'ima da jikin ta yayi sanyi ganin yanda yanayinsa ya koma ne yasa ta juyo tana kallonsa, kuma sai ta rasa me zatace masa ma, shima kallonta yake ahankali yace "I'm going to California tomorrow, wani aiki ya taso min" sai Na'ima ta sakejin jikinta ya qara wani sanyin takasa magana, ganin yanayinta yasa Ahmad yadan duqo cikin kwantar da murya yace "Babe..bawani dadewa zanyi ba, it's just a few weeks away" Na'ima ta gyada kai, ya sake cewa "zaki yarda mu rinqa yin video call din in na tafi?" ta dago idanunta ta kallesa, sai ya sake yin qasa da murya yace "Please" itama ta sake gyada kai, sai a sannan tace "Allah ya kaika lafiya" Ahmad yaji addu'an nata har cikin zuciyarsa, yana murmushi yace "Amin Na'eemah"...da haka suka rabu zuciyarsu na kewan juna tun ba'aje ko Ina ba.....
Bayan tafiyan Ahmad California sai ya kasance wayan nasu ba sosai suke yi ba saboda yanda ayyuka suka sha masa kai, dan tafiyar tasa tanada alaqa da expansion din oil and gas company din nasu wanda suke cuku cukun launching anan Los Angeles, Adam ma acan ya samesa suke aikin tare..dalilin banbancin dogon awannin da yake tsakanin qasashe biyun yasa basa samun yin waya akai akai, Dan kafin dare yayi yasamu nutsuwa ita kuma by then tsakar dare ne tayi bacci, sai dai yakan hana kansa bacci watarana in bai gaji sosai ba ya jira har safiyar garin London tayi sannan ya kirata wanda acan kuma shine tsakar darensu.. video call din ma baifi sau biyu sukayi ba shima lokacin ya dan samu sararawa ne within lokacin aikin..
Haka dai Na'ima suka maida hankali itada Nafisa kan dissertation dinsu da sukeyi dan sunzo wani fage ne a karatun da ake kira da (Trinity term) ana nufin karshen karatun kenan wanda a wannan lokacin kawai dissertation din akeyi kuma shi yafi exams a fagen wahala, project ne babba kuma dogo da ake daukan lokaci gurin qaddamar dashi, research akan research akeyi kafin a kammalasa...
Ahmad bai dawo ba saida ya kwashe tsawon kwanaki ashirin da biyar acan wanda jinsu yayi kamar yayi watanni baiga Na'ima ba,
Ranan da zai dawo sunyi waya da ita amma bai fada mata zai dawo din ba, dan lokacin ma yana Airport sai Na'ima tayi tsammanin yana gurin da akwai hayaniya ne bata kawo airport a ranta ba, shi kadai ya dawo London din, dan ya bar Adam acan shima daga can din zai wuce Nigeria saboda akwai pending ayyukan da Ahmad yabari acan Lagos zaije ya qarasa su..
Isarsa qasar ko gidansa bai wuce ba ya dira gidan Anty Amnah
Na'ima na zaune da Anty'n su kadai a falon dan Nafisa ta fice gurin Lauren a lokacin, ganin Ahmad kwatsam yasa Anty Amnah dan ware ido tace "Son.. sauqan yaushe haka" Na'ima dake sanye cikin wani yellow boubou na kamfala tafara ware dankwalin zata yafa a kanta duk idon Ahmad na kanta, zama yayi a kujera alamun gajiya duk a tattare dashi yafara gaisawa da Anty Amnah tana tambayansa hanya, miqewa Na'ima tayi ta tafi kitchen ta debo masa snacks da drinks takawo, nan gabansa ta sunkuya ta ajiye a kan glass table din yana bin ta da kallo, komawa tayi ta zauna ta gaishesa ya amsa tareda cewa "Ya karatu" tace "Alhamdulillah".. casually suka gaisa wanda in ba fada maka akayi ba bazaka taba cewa there's something going on between them ba..
Magana sukadan farayi jefi jefi shi da Anty Amnah sai Na'ima taga ya ciro wayarsa daga aljihu yafara dannawa, wayanta dake hannunta ne taji yayi vibration, ta dan dago tana kallo ganin message ya tura mata me dauke da saqon haka..
'Gosh..i missed you'
Dago kanta tayi suka hada ido tayi saurin kauda kanta tana dan murmushi, bata sake kallon bangaren sa ba har saida taga ya miqe yana yiwa Anty Amnah sallama akan zai wuce sai tace ya tsaya yaci abinci ana kanyi ne, yace "A'a Anty zanje in huta tukunna" tace "Allah bazaka tsaya ba son, saura kadan fa" ya sake cewa "Bakomai Anty, sai anjima" fita yayi Na'ima na nan zaune ta bi bayansa da kallo, sai kuma taji wani message din ya sake shigowa wayanta kamar haka..
'Babe, bazaki fito in ganki me kyau ba?'
Sai kawai tayi murmushi ta tura masa emoji me kada kai da kuma gwalo, hakanan Ahmad dake tsaye jikin motan sa ya hakura ya tafi batareda ta fitan ba dan ita saitaji wani kunyan kallon idonsa takeyi ma kodan sun kwana biyu basu hadu bane oho. Da Nafisa tadawo ma Na'ima batayi gigin fada mata dawowan Ahmad din ba.
Da dare suna kwance itada Nafisan a gado kiransa ya shigo wayanta, dan juyawa tayi taga Nafisa na kallo a iphad dinta nan kwance sannan ta daga kiran, daga can bangaren Ahmad yana zaune a babban falon gidansa ya miqe kafafunsa kan glass table dake gabansa yana kallon movie a Netflix, shiru sukayi bayan Na'ima ta daga kiran sai kuma taji yace "Fushi nakeyi kuma baki ma san inayi ba Babe" tayi wani murmushi me dan sauti tace "I'm sorry" Ahmad yayi sipping tea dinda ke riqe a hannunsa sannan yace "Dagaske nayi fushi kuma bazan miki magana ba" sai ta dan yi dariya tace "Yanzun me mukeyi" shima yana murmushin yace "I mean from now on" kawai murmushi tayi batace komai ba tanajin duk wani qofa dake zuciyanta yana budewa cikin annushuwa, daren ranan sunsha hira ba laifi wanda mafi yawan hiran shiru yafi yawa, in sukayi magana daya zuwa biyu zasuyi shiru kamar ba waya suke ba, Nafisa dake gefen Na'ima har sannan, sau tari sai ta dauka ko sun gama wayan ne sai kuma taga an cigaba da magana, jijjaga kai kawai tayi tana murmushi ta gyara duvet dinta tayi baccinta..
Washegari suna cikin yin breakfast ne Anty Amnah tace da Nafisa "Jiya yayanku yadawo bakyanan" sai Nafisa ta juya tana kallon Na'ima with suprise sannan tace "Anty wai jiya jiyan nan?" Anty Amnah tace "Haka nace fa Nafisa"
Nafisa na dan dariya tace "Yi hakuri Anty, nadanyi mamaki ne aikuwa anjima zamu je gidansa, dan inata masa alkawarin zamu kai masa ziyara kuma bamuje ba" Anty Amnah tace "Ya kamata dai, yana qoqari akanku, kuje ku gaishesa na musamman" Nafisa tace "in Sha Allah" ganin haka yasa Na'iman cewa "Toh" itama..
A motan Anty Amnah suka tafi, Na'ima na bin green forest din da kallo ganin ashe haka unguwarsa ke da nisa kuma yake zuwa gurinsu akai akai, Nafisa tace "Bobo baki fa fadamin meya hadaku ba daf da zeyi tafiyan nan" Na'ima ta juyo tana kallonta tace "Bamuyi fada ba sis, me kika gani?" Nafisa tace "Shikenan, I thought wani abu ya faru ne a lokacin, sai kuma naji baki min maganan ba" Na'ima tayi shiru kaman bazatace komai ba, sai kuma can tace "Nafisa i think i should tell...." bata qarasa maganan ba kira ya shigo wayanta, ta dago wayan tana kallon sunan Faruk dake kiran, dagawa tayi suka gaisa daga can bangaren Faruk yace "Habibtin Mami kin manta da Yayanki ko" tayi dariya tace "A'a Yaya, kayi hakuri school work ne ya riqemu" Yace "Shine babu kira Na'ima" tace "Kayi hakuri" shiru yayi baice komai ba at first, sai kuma ya sauqe numfashi yace "It's Okay dear, Ina Nafisa?" miqawa Nafisa wayan tayi itama suka gaisa sannan tace "Ka ganmu nan a hanyar zuwa gidan Yaya Ahmad" da dan mamaki yace "Wai har yanzu yana England daman?" Nafisa tayi dariya tace "Kaima kayi mamaki ko yaya" sai ta juya ta kalli Na'ima da hankalinta ke kan titi...
Wani unguwa sukaje me shiru bakajin qaran komai sai kukan tsuntsaye dan tsakanin gida da gida ma wani forest ne, Nafisa ta faka a daidai mashigar wani baqin gate me raga raga Wanda kana iya hango farin babban ginin dake cikin compound din, dan miqo hannu Nafisa tayi ta danna wani madanni dake jikin gini a gefen gate din, ba'a dauki lokaci ba gate din ya budu suka shiga, nan compound din tayi parking suka fito Na'ima na bin flower garden din gurin da kallo, ta gefe kuma motocinsa ne a jere kusan guda hudu, sai Nafisa ta zagayo gefenta tana kallon motocin tace "Yau sai na dauki makullin dayar can" ta qarasa tana nuna baqar Wrangler jeep din da yazo daukansu da ita rannan, murmushi Na'ima tayi dan ita hankalinta yafi kaiwa kan flowers din da tagani..gaba Nafisa tayi Na'ima na biye da ita suka qarasa main entrance din gidan, basu kai ga tura grand door din ba suka ga ta budu da kanta, idonsu ne yafada cikin na Ahmad dake kallonsu with suprise, sanye yake cikin baqaqen kaya na 3quater da T-shirt, sai Na'ima taga farin fatarsa ya sake fitowa sosai...Dan yin baya yayi sannan yafara musu iso fuskansa da dan murmushi sai suka bishi cikin babban falon da komai na cikinsa ya zamo fari da baqi, idon Na'ima na duqe suka zauna kan kujeru, Ahmad dake kallonta shima ya zauna a kujeran da ke facing dinta sannan ya kalli Nafisa yace "I thought bazaki gane gurin ba ai" Nafisa tayi murmushi tace "Haba dai Yaya" gaisheshi Nafisa tayi ya amsa sai a sannan itama Na'ima ta kallesa tace "Ina kwana" kallonta ya dinga yi not minding Nafisa dake gurin, Sai kuma ya miqe ya tafi wani corridor dake nan downstairs din, Nafisa tace "Ehem Ehem" dan juyowa Na'ima tayi tana kallonta, ganin irin kallon da Nafisan ke mata yasa ta dauke kai tana murmushi.
Bai dade ba ya dawo hannunsa riqe da refreshment ya ajiye nan kan table sannan ya zauna, Nafisa tace "Yaya amma ka chanja interior na gidan?" ya dan bi falon da kallo yace "Eh Nafisa" tace "Yayi kyau sosai, can i take a tour?" Ya gyada kai "Sure, go ahead" sai ta miqe ta nufi stairs tafara hawa sai kuma ta juyo fuskanta da fara'a tace "Yaya yau inason mutafi da jeep dinnan please" ya sake cewa "Ba damuwa, key din yana cikin bedside drawer na" ta gyada kai sannan ta cigaba da hawa stairs din zuwa sama.
Juyowa yayi ya kalli Na'ima dake zaune har sannan batace komai ba, sai ya miqe yadawo nan gefenta a hankali yace "Yau ma bazaki kulani ba" itama cikin sanyin murya tace "Mun gaisa fa" sai ya rinqa kallon ta fuskansa da murmushi baice komai, ganin haka sai ta fara wasa da bakin gyalenta, jin beyi magana ba tace "Me kakason ince to?" yace "Tell me how you missed me Na'eemah" dago kai tayi tana kallonsa shima haka sai taji idanunsa sun mata nauyi nan da nan ta kauda kai tana dan gyaran murya tace "Ka daina kallona irin haka" sai yayi dan dariya yace "Fadamin ya nake kallon naki?" batace komai ba sunanan zaune Nafisa tadawo falon hannunta riqe da key tace "Yaya wannan ne ba" ya daga kai yana kallon key din yace "Eh shine" zama tayi ta zuba musu juice din da yakawo musu dazun ta miqawa Na'ima sannan suka fara hira itada Ahmad din jefi jefi, kiransa akayi a waya ya miqe yana cewa "Sorry i have to take this" sannan yayi hanyar fita waje.
Juyawa tayi ta cewa Na'ima "Bobo muje sama in nuna miki wani abu" sai Na'ima ta girgiza kai tace "A'a Nafee"
Nafisa ta taso tafara Jan hannunta tace "Dan Allah kizo muje, kawai wani abu zaki gani sai mu dawo" haka Nafisa ta jata suka je side dinsa da ke nan saman, sai taga sun wuce falo da study room dinsa Nafisan zata jata wani daki tace "Nafisa is not proper in shiga masa daki dai" tace "Meye wani proper, da'alla kizo mu shiga" shigansu dakin Nafisa ta jata gurin master bed, itadai Na'ima sai bin gadon da kallo ganin girmanshi, sai da suka tsaya daidai setin gadon sannan Nafisa ta kamo kafadunta ta juyar da ita suka kalli ginin dake facing gadon.
Hannu Na'ima takai bakinta tsabar mamaki tana kallon katon hoton ta da akayi framing anan jikin ginin, hoton ya kusa cinye gurin dan girma, dariya takeyi acikin hoton bazata manta ba ranar da sukaje gurin sport dinnan ne domin kayan ne ajikinta cikin hoton..sunanan tsaye Nafisa bakinta kamar ze yanke dan murmushi tace "Yaya Ahmad is Finished" sai kuma tayi dariya tace "Na'ima..I'm truly happy for you, for all of you..this is clean" itadai Na'ima takasa cewa komai sai hawayen da ya kawo idonta tunani iri iri a ranta, janta Nafisa ta sakeyi suka koma falon qasa nan suka samu Ahmad kishingide a sofa yana danna wayarsa, dagowa yayi yana kallonsu Nafisa tace "Yaya zamu tafi" yace "So soon?" Na'ima sai kallonsa take tana jin zuciyarta wani iri, Nafisa ta sake cewa "Eh Yaya, yauwa yanzu ya zamuyi da motan Anty Amnah, inason mu koma acikin taka" ya danyi murmushi yace "Ba damuwa Nafisa, zan aika mata anjima" sai ya sake cewa "I've ordered food, ku tsaya akawo tukunna" Nafisa tace "A'a Yaya a qoshe muke mukam" jakansu dake nan kan kujera Nafisa ta dauka suka fara nufan hanyan fita, shima miqewa yayi yabi bayansu har nan parking space, bakin Nafisa yaqi rufuwa dan itadai Allah yasa mata son motan, duk yanda yaso Na'ima ta kallesa taqi gashi kuma taqiyin magana, shigewa motan tayi itama Nafisa ta tada suka fice yananan tsaye....Ranan da dare da ya kirata ma baigane kanta ba duk tayi wani irin sanyi, haka dai yayi ta magana tana amsawa sama sama, ita jin ranta takeyi duk a hargitse ma tarasa me zata fara tunani guda daya, what if yazo ya san ta taba aure? , what if yasan tushenta? , what if yasan su waye mutanen da ta rayu cikinsu?.. dakyar bacci ya kwasheta daren ranan tsabar tunani..
Ranan wata laraba sun wayi gari da shirin zasu kai project papers dinsu gurin supervisors dinsu, da wuri suka shirya ko breakfast ma basuyi ba dan zuwan wuri sukeson suyi, bayan sunyi sallama da Anty Amnah suka fice , fitowan su kofar gidan zasu nufi gurin motan Ahmad dake nan fake sukaga wata Uber tayi parking dan nesa dasu,
Tsayawa kallon Laila data fito daga bayan motan sukayi dukansu, drivern ya fito yafara ciro mata akwatin ta daga bayan motan..Nafisa da ke gefen Na'ima tace "A'uzubillahi minash shaidanir'rajim..ji wani mummunan gani da farar safiyar nan" duk yanda Na'ima takai da Jin ranta babu dadi saida ta kusa fashewa da dariya.
Sunanan tsaye babu wanda yayi gigin tayata kama akwatin data ke ja da kyar, dan tsayawa Laila tayi tana kallon motan Ahmad dake fake a kofar gidan sannan ta qaraso gurin su Nafisan.
Nafisa tace "Ke kuma sauqan yaushe da safiyar nan" Laila na mata kallon banza tace "Ban sani ba" Nafisa tace "Hattara dai Laila, babu wanda nake shakka kaf London, da dutse zan miki gugan baki wallahi" sai Laila tayi wani tsuka me qarfi tana hararan Na'ima da taqi kallonta, wucewa tayi har tana dan bangaje kafadan Na'iman tayi cikin gidan Anty Amnah'n janye da akwati suna binta da kallo, sai kuma Nafisa ta daga hannu sama afili tace "Allah ka yafemun zanyin abunda uwata ta haneni da yi"..
A hanyarsu na tafiyan ne Na'ima ta juya ta kalli Nafisa tace "Sis ko zamu koma namu apartment din tunda kin samu sauqi" Nafisa ta dan harareta tace "Wa? Akan Laila tazo kenan, wallahi bazamu bar gidan ba saidai ita ta bari, tsoronta ma mukeji kenan" Na'ima ta girgiza kai tace "Banason tashin hankali Nafee" Nafisa tace "babu abunda zai faru dai sis, kema kinsan Anty Amnah ai, bazata dauki nonsense ba" shiru Na'ima tayi batace komai ba sai Nafisa tasake cewa "Ki kwantar da hankalinki dan Allah, ba wani abu"...
Na'ima ce zaune akan wani rest bench cikin school premises din itada zarah hannunsu riqe da ice coffee, hira sukeyi kiran Ahmad ya shigo wayanta, bayan sun gaisa a nutse ya tambayeta "Babe where are you?" Ta amsa da "Ina school" ya sake cewa "I'm on my way now" sanin daga London ya kamo hanya yasata cewa "Allah ya kawoka lafiya" ya amsa da Amin sannan ta sake cewa "Zanje apartment dinmu dauko mana wasu kayan" daga can bangaren Ahmad ya amsa da "Okay zanje can din daukanki" sannan sukayi sallama ya kashe wayan, tashi tayi sannan tayi sallama da zarahn akan zata tafi, saida ta tari cab anan bustling street na bakin makarantan sannan ta shiga suka wuce, a hanya ta kira Nafisa bata dauki kiran ba kawai ta maida wayan jaka...
Isarta apartment din nasu ta fito daga elevator anan corridor din nasu taga wani kamar delivery man a tsaye a bakin kofan dake gefen nasu apartment din, wuce sa tayi bata ga fuskansa ba dan sanye yake da facing cap har da face mask, saida ta tsaya daidai kofar su ta saka door pin din ta bude zata shiga taji an hankadota da karfin gaske ta fada cikin gidan nasu, kifewa tayi anan falon zuciyarta yayi wani bugawa da qarfi har tanajin bugawan a kunnuwanta sanin mutum daya ne zai iya mata haka a kaf duniya, ta juyo daga kwance tana kallon sa, rufo kofan yayi yacire face mask din yana kallonta cikin wani irin kallo dayake kada 'ya'yan hajinta tun fi azal, fari ne guy din kamar Na'ima amma babu ta inda suke kama da juna sannan yanada dan kakkauran jiki, qarasowa yayi falon cikin muryansa me kaifi yace "Yaushe na fara wasa dake Na'ima" baya tafarayi tana dan jijjaga kai, isowarsa gurinta beyi wata wata yakai mata hari da kafansa akan cikinta, Na'ima tayi wani qara tana kama cikin nata, sai da yayi mata harbin sau uku cikin tsawa yana cewa "Tell me...yaushe na fara wasa dake" sai ta fara rarrafawa tana dosan gurin kujera tana hawaye ya kamo gashinta ta bata ya dagota, hannu takai tana kama gashin nata da ya riqe tafara wani irin kuka, dagota yayi ya bugata nan jikin kujeran ta sakeyin wani ihu, yana huci yace "Har zan bada saqo gurin banzar kawarki sannan kiqi complying, who are you Na'ima?" kuka take bata ce komai ba har sannan, sai ta miqe zaune tana kallon cikin idonsa, yana kallonta shima ya sake cewa "I warned you haduwan mu bazatayi kyau, dan haka ki tashi ki wuce daki ki debo kayanki mu tafi gida, and i mean NOW before i wound you"
Na'ima dake kallonsa tanajin zuciyarta tana bushewa for the first time, a hankali tace "Bazanje ba" tsayawa kallonta Bilal yayi with shock written all over his face.. tana kallonsa idonta na zuban hawaye ta sake cewa "Bazanje ko ina ba Bilal" ta qarasa maganan itama tana mamakin irin qarfin gwiwan data samu a karo na farko na tsawon rayuwanta tareda Bilal, tunda ta mallaki hankalin kanta a rayuwa take tsoron Bilal da duk abunda ya shafesa..
Miqewa tayi still yana kallonta tace "Wallahi ko zaka kash.." bata qarasa ba ya dauke ta da mari bata farfado ba ya sake kai mata wani, baya tayi zata gudu ya kamota ya bugata da bango tana ihu, yana huci yace "Maimaita abunda kikace" ta fara jijjaga kai zata kwace kanta kawai ya hau kai mata mari tana tarewa da hannunta, burinta daya a wannan lokacin shine takai ga zuwa kitchen ko zata samu wuqa, dakyar ta kwace ta nufi hanyar kitchen din ya kamota ya sake bugata da kofan dakinta, Jin kofa a bayanta yasa ta bugawa ta fada dakin yana biye da ita, hannu takai ta daki mirror da karfi ya tarwatse a nan dakin ta dauki babban yanka guda daya ta juyo tana nuna Bilal din dashi, jikinta na rawa tace "Ko ka fita ko muyi mutuwar kasko" yana kallonta bai motsa ba ta sake matsowa tana taka fasassun mirro'n daya zube nan qasan dakin, cikin ihu tace "Ka fita Bilal, ko in kasheka nima in kashe kaina"
Bilal ya shiga shock sosai a wannan lokacin ganin yanda Na'iman daya sani ta rikide ta koma wata daban, sai yayi qasa da murya yace "Na'ima you've tasted freedom, is this really you?" Ta fara dosowa gurinsa yadanyi baya ganin da gasken zata iya caka masa, tace "Wallahi ko ka fita daga gidan nan ko in kasheka" baya yafari suka fito daga dakin yace "Na'ima listen to m.." cikin ihu tace "I'm done, I'm done Bilal" sai kuka yazo mata kuma, tasake cewa "Ka barni nayi rayuwata, kabarni hakanan" Ya daga hannun sa alamun surrender yace "Alright zan fita, ki ajiye abun hannun naki tukunna" ta girgiza kai gashinta duk yayi daddaya tana zare masa idanu ta cigaba da doso sa da mirro'n hannunta yana jini, da baya da baya Bilal ya fita daga kofan, tana ganin ya fitan ta jawo kofan ta rufe da qarfi ta jingina bayanta nan jikin kofan tana fashewa da kuka me karfi, yardar da abun hannun nata tayi ta tsugunna nan bakin kofan ta cigaba kuka tana dafe hannunta a setin zuciyanta...
Qarar wayarta ta Jiyo anan kan sofa ta miqe dakyar ta isa gurin, sunan Ahmad tagani rubuce a fuskan wayan, sai lokacin ta tuna ashe ya fada mata zaizo daukanta, daukan wayan tayi bata daga kiran ba sai ta nufi gurin balcony tadan leqa kanta..
Numfashinta ne taji ta tsaya a wannan lokacin ganin Ahmad a tsaye jikin motansa waya a kare kunnensa, daga gefensa a nan street din kuma Bilal ne tsaye shima da alamun yana jiran abun hawa, dukansu kusa suke tsaye da juna batareda daya yasan daya ba.. Na'ima ta dago wayan tana kallo ganin Ahmad ya sake mata wani kiran, kallon su ta rinqa yi tananan tsaye in idonta ya kalli Ahmad sai ta kalli Bilal shima dake nan gefe........
Shin wai wacece Na'ima?, Menene asalin alaqarta da Bilal?, Shin ya kuke ganin wannan lamarin zai qare a tsakanin wa'innan mutane?..
Kudai ku biyoni dan Jin labarin Na'ima da abubuwan da rayuwarta ya qunsa ......
Follow my account please.