Kamar da wasa pg 5
by @mrsomar
KAMAR DA WASA 💘
Fatima Isah(Mrs Umar)
Page 5
ABUJA, Nigeria
"Wallahi Anisa, a wannan karon ba zan sake ba! Bazan sake bari a cuce ni ba. You know I love Hamma Sham, and I won’t allow anyone to ruin this chance for me again," Yusura ta faɗa tana tafasar zuciya, idanunta cike da ƙiyayya da takaici.
Anisa ta gyara zama a gadon su, tana kallon Yusura da mamaki da shakku. a hankali ta ce.
"Anya Yusura, wannan zargin da nake maki. Kin tabbatar ba ke kika saka hannu a mutuwar Jamilah ba? Kada fa soyayya ta rufe miki ido."
Yusura ta bushe da dariyar takaici, ta ce
"Please Anisa, don’t even go there. Jamilah ta mutu ne saboda kaddara, not because of me. Amma kuma wallahi wannan ƙaryar da ake yayatawa wai za a aura mashi yar'uwarta sai na hana! What nonsense?!"
"To Yusura, ki kiyaye. Kada soyayyar da kike yi wa Hamma Sham ta kai ki ga aikata abin da zai jawo miki la’ana. Kin san kowane lokaci za a iya gano gaskiya you no who is Hamma Sham zai iya yin komi saboda ahalinshi dan haka ki kama kanki."
Yusura ta miƙe tsaye, tana gyara ɗan kwalin kanta tare da ɗaukar mayafi da jikarta. Tana tafiya da ƙarfi, kamar wacce aka kona mata zuciya.
"Idan da akwai gaskiya a cikin wannan ƙasar, to wallahi ni ce wacce ta fi cancanta da Hamma Sham. In ba ni ba, to babu wata!"
Anisa ta bita da kallo mai cike da damuwa, zuciyarta na bugawa da tambayoyi marasa amsa. A ranta, ta furta:
“Allah Ka kare Hamma Sham daga duk wani sharri da aka boye masa a cikin soyayya...”
Yusura na fita kai tsaye shashen Yapendo ta nufa dan dama a shashen su Anisa take yanzu shashen Uncle Musa kenan.
Tana fitowa kamar abin haɗin baki da S.Y. Shattima taci karo ya raka bakin da suka zo mashi gaisuwa, abinda zai baka mamaki duk jama'ar dake gidan yan zaman gaisuwa Yusura bata duɓe suba ta iso wajan S.Y. Shattima tana wani karairaya tamkar zata karye ga rigar jikinta duk tabi mata jiki sai kace ba ɗiyar fulani ba da aka sani da kunya.
Duk da P.A Khalid na tare dashi yana nuna mashi wani abu a ipad haka ta tsaya a wajan cikin shake murya da wani karya harshe ta ce.
"Hamma sham jamban duna"
Ko kallon inda take bai yi ba yaci gaba da duba abinda P.A ke nuna mashi. Sai da ya gama yana shirin barin wajan kafin P.A ya ce.
"Sir ana gaisheka"
"Jam"
Ya ce daga haka bai ce komi ba ya ƙara gaba abinshi.
Wannan bakin ciki yasa Yusura sakin kuka ba tare da ta yi tunanin jama'ar wajan ba ta nufi shashen yapendo zuciyarta tamkar zata fasa ƙirjinta. Kafin ace maka me idanunta sunyi jajir.
****
Zaune suke a babban falo, wanda aka ƙawata da kujeru da tagogi masu curtains na alfarma. Dukkanin gine-ginen gidan na nuna matsayin babban dangi gida na manya.
Gwaggo Hakima na zaune akan sofa mai ɗan tsawo, tana karanta jarida da cup din shayi a gabanta. Yapendo tana gefe, ta ɗaura mayafi a kafaɗa, amma idanunta na kan Yusura tun da ta shigo da hawaye a fuskar ta da ido ja.
Yusura ta ajiye jaka da sauri, ta nufi Gwaggo, ta faɗa mata a jiki, tana cewa da murya mai sanyi cike da ciwo:
"Mom! wallahi bana iya jurewa. Ni ce Yusura. Wannan zafin kishin da nake ji game da Hamma Sham zai kashe ni."
Gwaggo ta sa hannu tana shafa kanta, tana daidaita numfashinta, ta ce a hankali:
"Toh my baby, ke da zaki zama uwar gida, ke da jinin Shatiima ke kwance a zuciyarki, me zai dame ki?"
Yusura ta ɗan matsa gaba, hawaye na gangaro mata.
"Bana jin yana sona Gwaggo. Ina jin kamar ba zai taɓa kallona da idon da nake so ba. Tun rasuwar Jamilah, nake ji a zuciyata kamar na samu wata dama duniya. Sai dai ina lamarin ya wuce duk yadda kuke tunani. Kuma yanzu ana cece-kuce wai zai auri Naanah, yar'uwar matarsa...!"
Yapendo ta ƙware baki, ta tabe leɓe ta ce:
"Yusura Ko da ance za’a aura mashi ita, she can never be you. You are the real one. Shi Shamsu yana buƙatar mace kamar ke da hankali, da iya zama. Ba yarinya mai bin umarnin Amina ba."
Gwaggo ta gyara zama, ta ce a harshen Fulfulde cikin nutsuwa:
"To debbo mari munyal no duniyaru wuli pat o nyamai risku, ta damu jonta Shamsu jema on."
(Idan mace tana da hakuri, duk duniya zata kira ta. Ki nistu ki tsaya a hankali, Hamma Sham naki ne.)"
Yusura ta fashe da kuka, kanta na kan cinyar Gwaggo.
"I’m tired of fighting for love. I just want to be enough for once..."
Gwaggo ta ɗaga kai, ta ce da karfi:
"Ke ki yi shiru kin ji Yusura? Wannan faɗa ba naki bane ke ɗaya muna tare dake. Wannan gidan, wannan family, ke kike da damar zama uwar gidansa. Ba Naana ba"
Yapendo ta ƙara da cewa
"Mu dai zamu shirya. We'll find a way to make him see you. Koda da lallami, koda da dabaru. Wannan karon sai dai su Amina su bita da idanu. Ke ce matarshi."
Gwaggo ta juyo da kyau, ta kamo hannun Yusura
"Yusura... ki tsaya da ni. I have a plan. Wata rana sai kin ce, ai dama Gwaggo ta faɗa. Shamsu zai dawo gare ki by force or by love."
Yusura ta share hawayenta, ta ce a hankali:
"Nagode Mom. Nagode Yapendo. I'm ready. I'm no longer afraid."
**
Waje ɗaya na cikin gidan, Nanah na tsaye a jikin tagar sashensu tana kallon falo.Tana jin komai. Da suke tattaunawa dan tazo ɗaukar abu ne ta jikin wajan taji maganar su shine ta tsaya tana ji. Murmushin ta saki mai faɗi ta ce
"Ina jiran ku. ku zo da shirin ku amma ni ma ba na wasa Hamma Sham ba na wasa yara ba ne."
****
A lokacin da Yusura taga S.Y. Shatiima a tsaye a lokacin P.A Khalid na tsaye ne yana nuna mashi abinda yaci karo dashi ne yana faɗi.
S.Y. Shatiima yana kallon allon iPad da P.A Khalid ya miƙa masa, fuskar sa a daure kamar kullum, sai ƙamshi da ƙasaita ke fita daga jikinsa. Duk da ƙarfin halin da yake nunawa, akwai wani nauyi da ya lulluɓe zuciyarsa na rashin Jamilah da har yanzu jikinsa ke jin dumi.
P.A Khalid da tausayi a muryarsa ya ce
"Sir, congratulations… sabon posting ne ya fito yanzu. Na gani a cikin group, an saka sunanka zaka je a matsayin Commander a 17 Brigade, Natsinta Army Barrack, Katsina."
S.Y. Shatiima ya ɗan ja numfashi, ya amshi iPad ɗin ya duba. Bakin sa bai motsa ba, amma idanunsa sun bayyana ƙwaƙƙwaran tunani.
"Kwana bakwai bai cika ba tun rasuwar Jamilah kuma suna neman na tashi yanzu na koma wani wajan?"
P.A Khalid cike da girmamawa ya ce
"Sir umarni ne daga sama. Amma zaka iya neman delay na ƴan kwanaki, in ka ga ya dace."
"A’a. Soja ba ya zaɓar lokacin da za a kira shi. Ka shirya min komai. Zan koma Lagos, amma tafiya ba za ta wuce cikin kwanaki biyu ba. Har yanzu gaisuwa nake karɓa, kuma ba zan bar su Iman da Minal a nan ba kamar yanda na ɗaukarwa Jamila alkawari."
"Na fahimta, Sir. Zan tsara jadawalin gaisuwa da kuma yiwuwar tafiyar bayan kammala kwana bakwai."
S.Y. Shatiima jinjina kai yayi tare da cewa
"Kai samo min bayanin dakarun da ke Katsina. Ina buƙatar sanin abin da zan fuskanta tun kafin na isa."
Kai P.A Khalid ya jinjina mashi kawai.
A lokacin yusura ta iso kun gane ko?
***
Abinda ya ɗaurewa Naana kai shine batun aurenta da S.Y Shattima babu wanda yasan da maganar daga Dada sai Ammie shima Dada ta kawo shawara dan a tunaninta Naana ce kawai zata iya rike yaran Jamilah ba tare da wata matsala ba.
Amma ga magana har taje wajan su dan ko Ubbah bai san da batun ba dan yau Dada ke shirin tunkararshi da maganar..
#son zuciya
# makirci
#yaudara
#soyayya
#Bemty's Kitchen