MAKAUNIYAR HANYA

DAGA KALLO D'AYA

by @ayshnur

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

MAKAUNIYAR HANYA......

Daga alk'alamin Ayshnurpyar

Wannan labarin ban yi shi dan cin fuska ga wani ko wata ba, idan har yazo dai-dai da rayuwar ki/ka akasi aka samu. Ina rokon Allah yanda na fara lafiya yasa na gama sa lafiya. Allah yabani ikon rubuta abinda yake alkhairi.

Dedicated to my mentor Lubabatu Sani Maitafsir

Jinjina ta musamman ga Meemi Bashir (queen)

              Page (1)

   DAGA KALLO D'AYA...!

TWO MONTHS EARLIER

Sassanyar yammaci ne mai d'auke da iskar damina, yanayin iskar garin cike yake da ni'imar dake sanya nutsuwa a zukatan mutane musamman wad'an da suka kasance masoya.

Amma a bangaren ta akasin hakan ne ya kasance, duk da dad'i da yanayin da garin yake ciki, tafe take tana jimami cikin zuciyarta.

'Wannan wace irin rayuwa ce haka ta same ni! Ace ba kada 'yancin zama bisa inuwar wani?'

Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

A wasu 'yan shekaru baya kad'an da suka shud'e, tana d'aukar kanta cikin jerin Mata masu tsananin nasara da cikakken sa'a a rayuwa, amma sai gashi lokaci guda d'aya tak! Ya zamo sanadin sauya saitin agogon rayuwarta gaba d'aya.

Lokacin da yafi komai tsada a gareta. Ya janyo sanadin kasancewarta tamkar mujiya, musamman wajen mutanen da watanni kad'an baya suke d'aukarta a matsayin wata fitila wacce zata zamo mai haska birnin zukatan su!.

K'uuuuuuuu.. ..... K'arar birkin daya taka ne da k'arfin tsiya, gami da horn shine yayi sanadiyar dawo da Zuciyarta daga kogin tunanin da ta kasance ciki dak'ik'u kad'an baya, wanda suke barazanar aikawa da ita garin da ba a dawowa.

Sai dai Koda ta farka daga duniyar tunanin data fad'a hakan bai sanya ta iya k'ara ko da taku d'aya ne daga inda take tsaye, wanda zai iya kai rayuwarta ga matsera.

Cikin izza ya fito daga motar tasa, ganin matashiyar yarinyar da a kallon sura na zahiri ba tayi kama da mai tab'in hankali ba, amma gata akan tsakiyar hanya tana tafiya, ba tare da tayi duba ga gudun fad'ama ababen hawan dake ta zirga-zirga bisa kan hanyar ba.

"Baiwar Allah lafiyar ki kuwa kike tafiya bisa tsakiyar titi ba kya gani sosai ne!?"

Kyawawan fararen idanunwanta ne suka samar wa kansu masauk'i cikin nasa idanun, wanda nan take hakan yayi sanadiyar kunna wani hasken wuta cikin zuciyar natsattsen matashin saurayin dake tsaye gabanta.

"Tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan kayakkyawar halittar".

Bai san maganar tasa a fili yayi ba, gabaki d'aya zuciyarsa ta shagaltu ga kallon kyakkyawan yarinyar dake tsaye gabansa. Da alamu shima ya shafa'a da cewa a tsakiyar hanya suke.

Wani k'arar horn din ne ya sake karad'e kunnuwansu, sai dai a wannan karon da alama masu tab'in hankalin su biyu ne bisa tsakiyar titi.

Ganin ba ta da wata alama ta motsawa daga inda take tsaye, yasa shi janyo ta daga kan hanyar.

Hak'uri ya koma yana bawa mutanen da suka soma hayaniya a wurin, kasantuwar motar sa daya bari rabi da rabi kan hanya, ya yi sanadiyyar had'a d'an matsak'aicin hold up a gun.

Kafin ya gama fakin d'in motar nasa inda ya dace, ya hango wannan yarinyar ta ci gaba da tafiya da alama jiri take gani, cikin hanzari ya fito daga motarsa, amma kafin ya isa gareta hangowa yayi ta yanke jiki ta fad'i k'asa.

Cikin bugawar zuciya wanda tun sa'ar da suka kalli juna ido cikin ido da yarinyar yake jin bugun zuciyarsa da sauri da sauri, ya kuma rasa menene mak'asudin hakan, ya k'arasa wurin da take.

Da taimakon wasu mutane suka sanya ta cikin motarsa, Medicity hospital dake G.R.A malali ya nufa da ita.

***** **** *****

Yana kwance a kan shimfid'arsa na bacci tunanin yarinyar nan daya ci karo da ita kawai yake, yanayin da ya ganta ciki ya jefa zuciyar sa, cikin kogin tunani, muhimmin abinda yafi damun sa shine rashin Sanin hak'ik'anin wacece ita, bata dawo cikin hayyacinta ba har ya baro asibitin, gashi ba waya a tareda ita balle yasan a ina yan uwanta suke.

Haka yayi ta faman birgima da tunane-tunane kafin b'arawo barci ya sace shi

A zahiri kuma tunda ya koma gida duk lokacin da tunanin ta ya fado masa, sai ya rinka jin fad'uwar gaba.

Bai fad'awa Mahaifiyar sa wani labari dangane da had'uwarsa da yarinyar ba, ya d'an jira tukunna domin akwai hadafin da yake da a kanta, mai yuwawa ita ce silar samun mafitar sa!.

Wata k'anwar abokinsa ya nemi alfarma ya kaita can asibitin ta zauna da yarinyar, domin k'anwarshi Saudat tayi tafiya, kuma ko da tana nan ma bai so su san da batun yarinyar tukun.

2DAYS LATER

Yau kwana biyu kenan da kai matashiyar yarinyar nan asibiti amma har zuwa yanzu bata farfad'o ba. Sai dai a yau likita ya bashi tabbacin cewa ana sa ran zata iya farkawa a kowane lokaci.

Shigowar sa gida kenan daga asibitin yake, bayan sun gaisa da Mahaifiyarsa Hajiya Aisha, ya doshi matakalar benen da zai sada shi zuwa d'akinsa.

"Irfan!"

Hajiya Ayshat ce ta kira sunan d'an nata.

Cike da damuwa shinfid'e bisa fuskar tasa ya waigo, inkiya ta mai da idanunta alamar ya dawo gareta, jiki a sanyaye ya k'arasa kusa da inda take zaune bisa kujera, a k'asan lallausan kafet d'in dake malale cikin d'akin ya zauna, domin nuna girmamawa gareta yace

"Gani Mommy".

"Akwai abinda yake damun ka kwana biyun nan ina lura da kai, ko sharad'in da Abban ku ya maka ne?".

Ya gyad'a Kai alamar A'a.

"Amma kuma nayi dogon nazari akan ka na gano wasu sabbin canji a tare da kai, dan harta da yanayin shigowar ka da fitar ka gidan nan duka sun canza.

In har yarinyar ce ka samu to menene kuma ya kawo damuwa da rashin walwala, ina son jin dalilin damuwar ka?".

Soshe-soshen k'eya ya fara da 'yan kame-kame.

Domin a zahirin gaskiya bai san ta ina ma zai fara ba.

Yace mata ya samo yarinyar da zai aura alhali yarinyar bata ma san inda kanta yake ba?

Yarinyar da bata san ko wanene shi ba, bai da tabbacin ma shin za ta amshi tayin soyayyar da zai yi mata.......

"Ka samo yarinyar ne nace ka yi shiru!

Shin 'yar gidan wanene kuma a ina take, tambayar ka nake?".

"Uhm..uhmm..........Mommy dama....dama ban.......".

dakatar dashi tayi da hannunta.

"Bana bukatar b'oyo ka fito fili kawai kamin bayanin abinda na tambayeka, shin ka sami yarinyar, Eh! Ko A'a!?".

" Eh! Na same ta".

Ya tsinci kanshi da furta kalamomin da bai san daga ina harshen sa ya lalubo su ba, har suka kai ga k'ok'arin fitowa daga bakinsa.

Har ga Allah ba abinda yayi niyar fad'a ba kenan amma dama 'baki shi ke yanka wuya....'

"To 'yar gidan wanene, a ina suke da zama 'yar nan garin ce ko ko?"

Kalamanta suka yanke mai zancen zucin da yake yi.

"Ban san ko 'yar gidan wanene ba Mommy, kuma yanzu haka ma maganar da muke yi tana asibiti".

"Asibiti! Meya Kai ta asibiti kuma?

Itace ba lafiya ko wani ne dai...?".

Bayi da wani zab'in daya wuce ya fayyace mata komai.

Nan dai ya zauna ya zayyane mata abubuwan da suka faru tun daga farko har karshe, bai so sanar da ita halin da yarinyar take ciki ba a yanzu, ba tareda ta farfado ba, yaso sai ya fara sanin ko ita Wacece, daga inda ta fito, ya kuma ji ra'yinta akansa, dan yau kwana biyu da tsintarta da yayi, amma ya na jin zuciyarsa dumu-dumu cikin soyayyarta!.

Sannan gashi yanzu ya na gabatar da ita gun mahaifiyarsa, a matsayin wacce zai Aura!.

'Lallai wannan shine riga malam masallaci'.

Ya fad'a cikin zuciyar sa.