2
**********Daƙyar ta samu ta tashi ta yi wanka ta shirya daƙyar sai lumshe ido take yi, so take ta koma bacci kamar yarda ta ga wasu na yi wasu har takalminsu suka sa suka kwanta abinsu sai mita take yi a ran ta tana tsine musu mutanene suka tasheta itakam bata da niyyar tashi aka tasheta sun karfe biyu da rabi ga ba ruwa sai da suka je suka ɗebo shima ga layi sam bata san lokaci ya ƙure haka ba sai da ta zo kwanciya irin ta janyo wayarta ta duba taga ƙarfe huɗu da hamsin kafin kuma ta ji an fara busa musu a fito. Wani irin ware ido ta yi, kafin da sauri ta shiga zuba biscuits da lemu a jakarta ta sa wayarta ta diro tana sa takalminta a gaggauce. Ta fita ta yi masallaci akwai hijabilan Sallah a masallacin hakan yasa bata zo da na ta ba. Suna idarwa aka sake busawa su fito. Ganin tsayuwar bata ƙare ba ce yasa ta shimfiɗa dardumarta ta zauna tana turo baki. Sai da gari ya ɗan fara haske sannan Murad da take gabansa ya kalle ta a zaune sai gyangyadi take yi.
"Hey! Zunaira...
Ya faɗa zai dafa ta.
"Heyy get up!
Aka faɗa mata tare da wata shegiyar tsawa ana zungurinta da sanda. A wani irin zabure ta tashi tsaye tare da dardumarta ta cukuikuyeta, tana ƙifta ido. Musamman da taga Rayyan ne.
"Good morning Sir".
Ta faɗa a ɗare muryarta na rawa. Be amsa ba sai harara da ya zuba mata kawai yana yin gaba.
"Ɗan muguwa...
Kallan da ya mata yana dawowa ne yasa ta tsuke baki tana yin ƙasa da kan ta gabanta na faɗuwa. Allah yasa be ji ba abinda ya faɗa yanzun nan ya kai ta guardroom ɗin da ta ji suna cewa suna da shi can suke ladafta mutum.
Murad kawai kallanta yake yi ganin ta yi rolling ɗin ta tsaf ta sa skin tight daga cikinta gajeran wandon ta sa safa ta sa sleeve a binta. Kayan sun yi mata kyau ba su wani matseta ba. Duk da ta da ƙugu amma sun yi mata daidai. Ba kuma su fito da shape na jikinta ba.
"Good morning".
Ya faɗa mata daidai tana kaiwa biscuits bakinta a kuma dai-dai kunnenta. Da sauri ta juyo ta ga shine hakan yasa ta sakin masa murmushi tana ambatar Morning too.
"Bismillah".
Ta faɗa tana miƙa masa, ɗan murmushi ya yi mata yana girgiza kan sa alamar a'a. Bata musa ba ta mayar da abinda side bag ɗin ta ta cigaba da cin na ta. Sosai ta ji ta gaji kawai so take ma ta kwanta itakam. Wannan ai masifa ce, wallahi Buddy ya cuceta kawai ya gama da ita da yanzu tana can tana kwance tana bacci abinta.
Waiwayawa ta yi taga babu kowa a wurin sa suke hakan yasa ta tsugunnawa tana turo baki gaba cike da tsantsan sangarci da Shagwaɓa, ta fara kulle idan ta kenan ta ji ana taɓa ta da sanda, ana taɓa mata takalmi, hakan yasa ta buɗe idan ta tana tsuke baki. Ganin wani soja na mata murmushi yasa ta tashi tsaye.
"Tired already abi?
Ya faɗa mata yana mata ɗan dariya jinjina masa kai ta yi tare da gaida shi.
"Manage".
Ya faɗa mata yana ɗan bubbuga kafaɗarta kafin ya yi gaba. Yana yin gaba ta sake tsugunnawa.
"Kawai shikenan a hanani bacci, ni ba soja ba ba komai ba. Allah zai saka mun Buddy".
"Heyy!
A wani irin firgice ta zubara jin Muryar Rayyan a kan ta. Tashi ta sake yi tana ƙifta ido tare da gunguni.
"Buddy wallahi na yi ma Allah ya isa sai ta bika...
"Ni zaki yiwa Allah ya isa?
Ware ido ta yi sosai tana kallan Murad, kafin ta yi saurin girgiza kan ta sosai.
"Ni zaki yiwa Allah ya isa?
Sai ta kasa magana tsabar yarda tagan shi daf da ita, tuni ta yi baya ta riƙe hannun Murad ta jingina da jikinshi sosai tana ƙifta ido.
"Sir am not talking...
"Shut up! My friend!
Ya ɗan daka mata tsawar da bazata janyo hankalin mutane ba zuwa gare su sosai sai de wanda ke platoon ɗin su suma ba duka ba.
"Oya come".
"Sir...
Ta sake ƙanƙame hannun Murad sosai, kafin ta fara ƙwalla. Yanzun aka ce gama ce musu
Obey first, complain when the mission is done. Murad ya ce mata.
"Don't argue".
Hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana sakin masa hannu hawaye zirr ya zuba a idan ta. Suna ganin tana binshi a baya yuuuu sojojin nan suka biyo su, suna zuwa guard room aka fara sa tsallen kwaɗo batare da wani duka ba ko wani abu, ta kai ta dawo ta kai da dawo sai da jima sosai tana yi har aka sallame 7;30 aka kada musu abinci sannan aka barta ake tambayarta kuma wai me ta yi masa? Dan shi tunda ya kawo ta nan bata ga ƙeyar shi ba. Kuma tambayar irin ta cike da kulawa ce irin, to ke da me kika masa? Bayan sun gama cin ubanta sun gama sa ta tsallen kwaɗon za su zo ce mata wani abu?
Tana kuka de ta sanar da su abinda ya faru yau ɗin.
"Sir. Rayyan anan wurin ya fi kowa ɓacin rai da bin doka a duk cikin mu, dan haka ki bishi a sannu. Kar ya sake maki magana ki yi masa abinda ki ka yi. Idan ba haka ba, mu kammu ba zamu iya cetar ki ba".
"Sunana Oga Kamal".
Ya faɗa mata calmly yana miƙa mata hannu suka gaisa.
"Daga wanne state ki ka zo?
Ya faɗa mata yana miƙa mata jakarta, tissue ta ɗauka tana share hawayenta, ta kasa tashi, hakan yasa shi taimaka mata ta tashi tsaye.
"Abuja".
Jinjina kai ya yi be ce da ita bakomai ba. Ta zo fitowa suka haɗu da Rayyan shi kuma zai shiga. Wata uwar harara ta zuba masa a kaikace tana turo baki. Kallan da ya yi mata ne yasa ta saurin durƙusawa tana cewa.
"Good morning Sir".
Ta faɗa tana share gumtuwar ƙwallarta. Be ce da ita komai ba, dan ya lura yarinyar akwai rashin kunya. Sai de ya ƙi ya matsa daga inda yake ɗin ya bata hanya, ita kuma ta ƙi ta ce masa zata wuce.
"Sirrr".
Sai kuma ta yi shiru tana ɗan matsowa tana ƙifta ido, dagaske tsoron yi masa magana take yi. Shi kuma kiran da Oga Kamal ya yi masa ne yasa shi barin hanyar yana barin abinda yake yi na duba file akan hanyar dan kawai ya ƙi ya bata hanya ta wuce. Tunda jununta bata da kunya.
"Malicious...
Juyowar da zata yi ne yasa ta suka haɗa ido tana zuba masa harara zata furta abinda zata furta tuni ta mayar da abinda zata furta zuwa ga 'Thank you Sir' tana sakar masa yaƙe. Tare da saurin yin gaba tana sauke ajiyar zuciya..
***********"Tashin hankali mema za'a yi da wannan mutumin?
"Wayyooooo Nanna".
Ta faɗa tana zubewa a ƙasana bishiya sai kuma ta fashe da kuka tana zaro wayarta ta fara kira.
"Hey!
Ta ji Ahmad ya faɗa daga cikin wayar. Sake rushe masa ta yi da wani kukan tana yi tana kallan sa dake videon call ne. Har ya shirya zai tafi wurin aiki abinsa yana ɗaura agogo.
"Cutest wannan kukan fa? Ba zaki yi shiru ba ?
Tana turo baki sosai ta fara share hawayenta cike da tsantsan taɓara da sakalci ta ce.
"Ina other Half".
Agogon ya ƙarasa ɗaurawa kafin ya ce.
"Me ya faru?
"Ni ka bani ita".
Ta faɗa masa da Shagwaɓa tana kumbura baki.
"Good morning".
Ya faɗa mata cike da tsantsan kulawa. Tana sake turo masa baki gaba tana share hawaye ta amsa da morning. Fita ya yi yana mata magana da cike da kulawa yana lallashinta har ta fito babban parlourn su inda kowa ke zaune yana cin abincin sa da'alama fita kowa zai yi. Wayar ya ajje inda kowa zai iya ganinta itama zata iya ganin su. Kawai ta rushe musu da kuka.
Kyakkyawan dattijon dake wurin wanda suke cewa Nanna shine ya fara lallashinta kafin Samha da Buddy su ɗaura, daƙyar ta samu ta yi shiru ta basu labarin Rayyan.
"Wallahi mugu ne mutumin nan, sam baya da adalci a rayuwarsa, kunga uban wahalar da aka sani?
Buddy ya ce,"Wallahi Cutie laifin ki ne, baki da aiki sai rashin kunya, gobe ma dan Allah ki sake".
"Nanna ka shiga tsakanina da Buddy, tun farko shine mutumin da ya sani na zo wannan wurin".
Mammy ta ce, "A'a laifin ki Zunaira...
Sai kuka jin abinda Mammy da Buddy ke faɗa a kan ta.
Samha ta ce, "Zunairah please ki yi haƙuri".
Tana wani turo baki sosai ta gyaɗa kai tana hararan Buddy.
Ya ce, "Ni fa bance ki je ba...
Nanna ya ce, "A'a Mahmud kar ka sauya magana mana, anan ka zo ka ke cewa akwai daɗi".
Yana dariya sosai ya ce,"Amma ai bance ta je ba ko? Kuma na ce mata akwai rashin bacci...
Ahmad ya ce, "Waye ya je sanda ya faɗa?
Mammy ta ce, "Ni de na ji, sanda yake faɗa mana ko Babyna?
Ta faɗa tana kallan Mahmud da sauri ya gyaɗa kai sosai yana murmushi.
"Ni de kawai ka cuceni ka gama dani...
Muryar Dadda suka ji a bayansu tana dogara sanda tana masifa hakan yasa Zunaira kashe wayar ta kawai dam bata san ciwon kan wannan tsohuwar da burinta kawai ta ga sun yi aure kamar sune kawai yara a duniya.
"Saboda ban isa da kowa ba a cikin gidan nan. Saboda ban kai ba, banda daraja, saboda baku bani daraja ta ba yasa ba wanda ya zo yau ya gaida ni ko? Ga shalelem gida bata nan ko? Gata gida ko?
Mahmud ya ce, "Walalhi a gidan nan, da ke da Cutie Pie kune jinyar gidan nan".
"Baku da aiki da surutu".
Tana samu waje a cikin parlourn ta zauna tana faman zuba masa harara daga inda yake zaune yana cin abincin.
"Gwara mu muna da surutu wasu ko kisa za'a yi a gidan nan ba za su ɗaga ido su kalla mutume ba. Kuma da ba'a zo an gaida ni ba. Ban mutu ba, da ba'a zo an duba lafiya ta bama, ras na tashi gashi de da ƙwarina kuma da jini na a jiki sosai.. kamar de yarda aka ga na tashi lafiya. Ba kuma zan mutu ba sai ubanku da uwarku sun aurar min da ku duka".
"Saboda ba'a son auren shine aka tura wata yarinya garin arna su je can su yi yaƙi, ita kuma wannan aka ce wai sai mijjn nata ya kammala karatu tsabar iskanci da rena min hankali. Wanne irin karatu ne za'a ce mutum sai ya kammala shi tukunna".
"Yoo nawa aka haɗa aure da karatu?
Samha a hankali ta tashi tana yiwa Mammy peck, Ahmad ya riƙo hannunta yana kallanta, gently ta sakar masa shima peck ɗin a kuncinta, kafin shima ya sakar mata a hannunta, haka ma Buddy shima cike da kulawa ya mata peck, Nanna ne kawai ya gyaɗa mata kai tare da sanya mata albarka yana sakin mata murmushi sosai kafin ya yi mata waving. Har inda Dadda take tana faman taɓe baki ta zo har ƙasa ta gaisheta.
"Bani amsawa, na ce bani amsawa. Munafukar yarinya, kin fi kowa munafurci a cikin gidan nan, saboda baki magana. Kuma Wallahi tallahi ki ji na faɗa maki, tare da ƴar uwarki za'a haɗa ki aure, ko kin kawo miji ko baki kawo ba".
"Ya Ilahi".
Ahmad ya faɗa yana kallan Dadda kafin ya kalla Samha yace,"wai Dadda meye haka?
Mahmud ya ce, "Oya wuce ki tafi kar ki makara, ki ka biye wannan matar ba zaki je ko ina ba".
"Daman da kai da Zuneraa kun renani Mamuda a gidan nan".
"To shikenan baki da aiki sai surutu da yiwa mutane faɗa".
Ya faɗa yana tashi shima ya ajje cup ɗin sa haka ma Ahmad daga tsaye ya gaida ta ya fice. Ahmad ne ya ɗan tsugunna ya gaisheta shima yana tashi ya fice. Mammy bata jira ba ta wuce itama ta fita sai Nanna ne ya zo inda take ya zauna a ƙasa cike da ladabi sosai ya russuna ya sake gaisheta.....