5
***********Sai yamma lis ta tashi daga baccin da take yi. Sosai ta ji jikinta, zazzaɓin ma ya sauka sai de ciwon cinyar da ta yi mata tsami sosai. A hankali ta sauko daga kan gadon, ta fito daga ɗakin kawai taga Rayyan a zaune ana treating masa ƙafarsa. Da'alama gurɗewa ce ya yi. Amma yarda yake massaging ƙafar bafa zaka ce wani mahaluƙi ake taɓawa ba. Ita kuma nurse ɗin sai wani iyayi take yi, wai ita corper, dan duka corpers ne a clinic ɗin, sune suke aikin, ma'aikatan kawai suna zaune ne abinsu.
Kallansa ta sake yi, taga hankalinsa be wurin wayarsa ma yake ɗan dannawa abinsa. Kafin ta sake kallan nurse ɗin, yarda take yi tana wani jan hankalin sa, da'alama de ta yaba. Wayancin matan ƴan iskan wannan corpers ɗin sai wani kallansa suke yi suna shafa shi suna ce masa sorry sir. Ita sai abin ma ya so ya bata dariya. Haka de ta daure ta matso tana ɗan jan ƙafarta wai ma fa ya gani, kar ya ce zai sa ta parade ciwon ƙafa take yi.
Karo na farko da yarinyar da ta taɓa bashi dariya kenan, ya fa ganta sanda ta fito ras, har ƙarewa kowa kallo da ta yi duka yana sane da ita, amma bata tashin nuna bata da lafiyar ba sai yanzu da zata wuce.
"Hey fine girl kin tashi?
Ta ji wata ta faɗa mata tana tasowa ta shafi fuskarta cike da kulawa. Ɗan gyaɗa kai kawai ta yi.
"Ba zazzaɓin ma ko?
Ta sake faɗa mata. Nan ma gyaɗa mata kai ta yi.
"Ina so na yi sallah".
"Ohk, use this toilet".
Ta faɗa tana nuna mata toilet ɗin. Shi kuma yana ƙofar wurin, dole sai ya matsa zata wuce. A hankali ta turo baki kafin ta ƙarasa kusa da shi tana kasa yi masa magana
"Sir! Please zata wuce".
Ta ji wannan ɗayar ta faɗa masa.
"Mtsw!
Ya sake tsaki kaɗan, kafin ya ajje wayar sa yana kallan yarinyar dake masa iyayi wai tana ce masa da zafi ne? Tsaki ya sake ja a kawo na uku kafin ya sauke ƙafarsa daga kan table din da aka ɗaura take ce masa ai ba'a gama massaging ɗin ba. Likitan da ya dubata Ahmed shine ya zo yana duba ƙafar nasa. Dake sun ɗan saba da shi ɗazun da ta zo da kuma sanda ta sake dawowa, har ta ji yana Yaren Ebira hakan yasa ta cewa.
"Ka yi masa da zafi, yarda zai cika asibitin nan da ihu".
Ta faɗa da gurbataccen yarenta da bata gama iyawa ba. Dariya ya yi mata ya ce.
"Ba ruwana toh".
"Dagaske nake yi maka, baka san halin sa ba ne ba. Mugune sosai, baka san abinda ya min ba. Ya iya mugunta".
"Yanzu fa ya barni na wuce ya ƙi bani hanya tsabar mugunta".
Murmushi kawai ya yi yana cewa, "Sir! Dawo nan, sai ka fi zama comfortable akan wannan kujerar".
Bece komai ba ya tashi ya koma inda aka ce.
"Dole abi umarnin likita".
Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana wucewa kuma sarai ya ji ta sai de bata iya haɗa ido da shi ba. Dan wallahi dagaske tsoronsa kuma take ji dam ɗazun nan idan sa fa har kaɗewa ya yi ya koma ja sosai. Har ta fito ba'a gama masa ba, sai de yanzu kam dake namiji ne ke yi dole akwai zafi, amma be wani nuna ba. Kawai de kallan ƙafar nasa yake yi. Dardumar Ahmed ya bata wannan nurse ɗin ta bata hijabi ta yi sallah. Sai anan ma ta san musulma ce dan sam bata kala da musulman ba. Sai ga ƴan Platoon na su, da yawansu wasu daga cikin su sun zo wai duba shi.
"Kaii wannan mutane da shisshigi suke, mutumin da ba wani kirki ne da shi ba uban me kuka zo ku yi masa?
Ta cewa Murad tana kallansa.
"Ke na zo dubawa. Nagani if you are still sleeping na tasheki.. wannan baccin ya isa haka".
"Kuma na ji daɗin baccin sosai".
"Daman shine damuwar ta ki ba?
Jinjina masa kai ta yi alamar eh.
"Ina ganin Oga Kamal ya wuce da ke mun fita Saed ai".
Ɗan murmushi ta yi kawai. Suna fitowa ya ce, "Yau za'a yi welcoming party".
"Ohhh! Ka ce zaka yi rawa".
Yana dariya ya ce, "Kawai sai na fara rawa?
"Hey! Fine girl".
Ta ji Ezekiel ya faɗa a bayan ta yana haɗa yatsun sa biyu alamar fairy clap.
"How are you? How your body?
Ɗan ajiyar zuciya ta sauke tana masa wani banzan kallo kafin ta yi masa yaƙe tana furta.
"am fine".
Ta yi gaba kawai abinta. Mami ta je ta ci abinci sannan ta wuce masallaci ana yin Sallahr Magriba ta kwanta ta yi bacci sosai har Isha sannan ta tashi ta sake yin alwala ta yi sallah. Har aka fara korar a fito sannan ta fito, clinic ta koma sai de aka ce baza'a yi attending kowa ba hakan yasa ta fitowa ta zauna a waje kawai kafin ta ɗauko wayarta. Taga tarin Missed calls na ƴan gidan su. Zata kira su kenan kiran Mahmud ya sake shigowa wayarta.
"Hey! Fine girl".
Ya faɗa mata, tsaki ta ja kawai tana turo baki..
"Me ya faru kuma? Ko ba wanda ya taba ce maki fine girl har yanzu? Kin san fa a camp kowa ma mai kyau ne babu mummuna".
"Wai kasan me ya faru?
Ta shiga bashi labarin abinda Ezekiel ya yi mata, sai kuma ta kashe wayar ta kira video call tana sa Bluetooth a kunnenta. Ta cigaba da basu labarin abinda ya faru a yau ɗin gaba ɗaya na rayuwarta da abinda ya sameta, tana yi tana zubar musu da ƙwalla, ba abinda da bata faɗa musu ba har kalar abincinsa da yau ta ci a Mami sai da ta faɗa musu. Da targaden da Oga Rayyan ya yi shine ta tuntsire da dariya. Murad na gefen ta daga nesa dan bata ma sanda zuwan sa ba,. Kawai yana kallon ikon Allah. Kowa da irin gidan su, ita kam yaga alamar wannan ƴar hutu zalla, an kuma mugun Shagwaɓata a gidan su. Sannan ga dukkan alamu akwai shaƙuwa mai ƙarfi sosai a tsakaninsu. Na su gidan ya tuno, taab daga Baban har Maman na su babu sauki kowa da irin faɗan sa. Ba'a zama da su ayi zance lafiya a ƙare lafiya ana farawa za su fara sauya maka magana musamman Mama.
Ɗan murmushi kawai ya yi yana jin kewar nasa a halin shima, kafin a hankali ya ciro wayarsa ya danna musu shima video call, ya san yanzu Baba yana gida shine kawai kullum datar sa a buɗe take. Yana kira kuwa Momma ta ɗauka.
"Meye haka ɗin? Ita wanna uwar hular har dare tana kan ku?
Yana murmushi a hankali ya ce, "Ehh Momma, ina yini".
"Ni qalau nake, hasko mun naga kowa da kowa".
Juya cameran ya yi ya hasko mata Mutanen dake waje da kuma wasu dake ciki.
"Kai me yasa ba zaka shiga ka yi rawar ba, ka ke zaune a waje?
"Momma kin san ni...
"Uban nasan kai? Yoo ni yarda nake da yarana? Taab. Yanzu haka kana nan kana holewa da ƴan mata, ka yi mata sun fi kala ɗari".
Ta faɗa tana zama a parlourn su ɗan madaidaici shi ba wani babba ba. Da gudu sauran yaran suka taho suna leƙa shi.
Ayyan ya ce, "Wallahi Ya Murad, ka yi ƴan mata abinka. Ka morewa rayuwar ka. Allahu gafurrahim ne a koda yaushe ne. It's only comes once in your life...
"Ayyan? Agaban ido na ka ke cewa ya yi abinda yake so? Ka ke cewa ya kwanta da mace, ya yi zina?
Ware ido Ayyan ya yi yace, "Yanzu Mommy yaushe na faɗa haka dan Allah?
Amrah ta ce, "Mommy wai ke sai kina juya mana maganarmu...
Amal ta ce, "Ya faɗa,ai abinda ka ke nufi kenan".
"Shegiya munafuka, mugulmaciya annamimiya wallahi wutar ki daban take a lahira shegiya".
Ƙulewa ta yi bata ce masa komai ba, yanzu bata da lokacin sa, tashi kawai ta miƙa musu wayar suka cigaba da zance sa su. Shi kuma yana murmushi sai tambayar sa suke yana amsa su.
"Amma de ka yi abokai ko?
"A friend".
Ya bashi masa yana tasowa daga inda yake ya dawo kusa da Zunairah ganin ta gama wayar da ta kwashe tsayin lokaci suna yi da ƴan gidan su.
"Meet my siblings".
Ya faɗa yana miƙa mata wayar.
"Hiii I'm Amal".
"Amrah".
"Ayyan".
Duka kowa ya faɗa mata sunansa.
"Zunairu, nice to meet you guys".
"Nice to meet you too".
"Are you Hausa?
Ayyan ya faɗa yana kallanta, sai ta gyaɗa masa kai.
"You looks so familiar Amma na rasa inda san ki".
"Maybe supermarket or hospital".
Ta bashi amsa. Kafin ta sake cewa, "Samzun Super Market".
"Yessss anan ne ma na taɓa ganin ki".
Ya faɗa so excited murmushi ta yi masa kawai tana jinjina masa kai. Nan fa suka fara hira da ita da Amrah da Ayyaan dan duka za su yi sa'anni kamar da can sun san juna, ga su da shegen surutu. Murad kawai gefe ya koma yana kallan ikon Allah. A cikin lokaci ƙankani sun san junansu har ba'a cewa komai har address na gidan su ta bayar da cewar zata yi ordern abinda Amrah ke yi su kaiwa Samha as a surprise gift ɗin ranar birthday ɗin su, su tuna mata ita mantawa take yi dan haka early in the morning su je su kai idan time ɗin ya yi a take a wurin ta yi payment ɗin komai da ake yi....
***********Tun daga wannan ranar wani abu be sake shiga tsakaninsu da Oga Rayyan ba. Idan sun haɗu de zata gaishe shi, idan yaga dama ya amsa idan be gani ba kuma ya yi shiru. Babu wanda take mu'amala dashi idan ya wuce gaisuwar a meditation ground shine kawai suka saba da zarar sun tafi ma bata sake ganin kowa. Parade kuwa tuni aka cire su team ɗin da ya fi kowanne iyawa ya ɗauka ya dena ɓata lokacin sa akan su. Sauran kuma sai ya raba su, zuwa games ɗin da za'a yi mata volleyball wasu basket ball da hand ball, wasu kuma tennis haka ma maza wasu chass wasu kuma foot ball. Gaba ɗaya ancire su a duka games ɗin banda volleyball ma ba'a cire su ba, kuma ya san tana so ne shiyasa take yi ɗin dan a yarda ya lura da ita da bata so ko me za'a yi bazata yi ba. Haka ya bi ya raba su. Kowa tsoron sa yake yi, Platoon officer ɗin na su ba ruwan sa Bama ya yawan zuwa, ganin haka yasa Rayyan zagewa sosai akan su domin ganin sun cimma abinda ake so daga ƙarshen wannan tafiyar. Har su miss beauty da miss NYSC aka ware, da su mr. Corperate da mr. Mancho. Suka ware shike kula da komai dan haka be bari kowa ya zaɓa ba, shine da kan sa ya zaɓa abinsa. A miss beauty da miss NYSC ne Murad yace a sa Zunairah suka ce wai bata da wani tsayin kirki. Kuma sanan bata da tsayin da ake buƙata. Sosai suka fara haɗa kan su sai de wariywar da ake nunawa musulmi ta yi yawa kam. Abubuwa da dama sai an sa su sau a cire, saboda wai basu iya ba, haka aka sa Murad a debate aka cire shi, wai he's not interesting bayan kuma shine da kan sa yace he's interesting ɗin. Daga Murad har Zunairah basa shiga cikin su, idan ka ga sun yi magana to su biyu ne suka keɓe, dan bata taɓa ɗaukan renin su, idan sun yi mata magana su gaisa idan ba su yi ba kuma Shikenan su je can, bata san hauka da rashin hankalin nan na su, su ka fara rungume mutum.
Da safe yau ɗin aka yi announcing sun ci volleyball sun zo na ɗaya za su buga da wanda suka yi semi final sannan su yi da final. Wani irin tsalle suka yi dan ba wanda ya yi tunanin za su ci ɗin. Dan anyi rufa rufa ajiyan da yamma suka ji haushi. Shi kan sa Rayyan ɗin be yi tunanin za su ciba. Zunairah harda kukan ta na baƙin ciki shine ma ya bata haƙuri tare lallashinta. Ana faɗa kuwa ya bi su ɗaya bayan ɗaya suna gaisawa. Yana sakin musu ɗan murmushi a hankali. Har ya zo kan ta ita ce ta karshe. Kafin ta sakin masa sassanyar murmushi tana miƙa masa hannu. Wani irin sassanyar sihiritaccen kallo ya yi mata, kafin a hankali ya miƙa hannun nasa suka gaisa sai kuma ya bata wani irin slight side hug yana ɗan bubbuga kafaɗarta Sannan ya wuce yana sake sakin mata murmushi, veil ɗin ta ta taɓa ta ji ƙamshin sa sosai. Murmushi ta saki sosai tana kallansa.....