ABUNDA KE 'BOYE...

34

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.

⏯️3️⃣5️⃣

Graduation day:

Wayewar gari ce mai sanyi iska tana kadawa ahankali kamar ana masa umarni ya nutsu yaurana kokadan bata fito ba tukuna amma dakin Zainab Arifah ya riga yayi wani irin haske da grandier decorations tareda tsadadn fitilu da kyawawan akwatunan kyautuka da aka jera mata a dakin tun jiya da daddare ayayinda take bacci batama sani ba.White nd gold boxes, ga manyan bouquets ga su sabbin bags, heels, sets na jewelries,har ma da wani babban frame da aka rubuta OUR PRIDE, OUR STAR. Congratulations on your Graduation zainab Arifah al-mansur.”Duk dakin ya dauka da sheƙi kamar gift room na royal palace.

yau Waking Moment dinta ma daban ne hajiya hamida ne tazo da dakanga da wani irin expenisve botle of champaing da sassafe cikin tsananin farinciki tay poping fasss a sama tace baby girl… wake up. its ur day!!! Da tsananin farin ciki Zainab tabude idonta a hankali ta tsaya cakkk ta yi blinking sau dyawa saboda dakin nata ya canza tamkar magic land with all the light, dolls, and gift boxes sorrounding her, atake Tsigar jikinta ya tashi ta mike zaune cikin wani irin sautin murna tace "yeeeyy...finally, i am a graduate! awn nd dis is All for me?hajy hamida tay dariya softly tadan shafa kanta tace yess Everything for you, my daughter. You earned it. Today is your special day.”

tun bata amsa ba sai gan nan prof zayyanu ya shigo cikin dakin sanye da farar jallabiya yana murmushin farin cikin wanda bai iya boyewa,with this strong i am proud of u energy yace heyy "look..my princess is up! top of her class,best in the whole set Zainab Arifah Ina alfahari dake sosai, Wannan ba ƙaramin abu ne, zamu iya yi komi don nuna miki yadda mukeji princesss u can name anything in this world today nd i prmise u it will be yours..

da tsananin murna ta dora kanta akan kirjinsa ta dada rungumesa sosai tana jin wani irin sinadarin sonshi yana lulluɓe ta. da wani irin shauqi a muryanta tace i love u dad

...you are best man in this whole world. zan iyayin komi dan nasaka farinciki..dad..all this success is dedicated to u ...

idonsa kamar zai zubar da hawaye yace "Thats my girl.. i love u too my princess..ure my world. ta kara kankamesa ssai hajiya hamida ta dinga kallonsu feeling sober tanata murmushi sosai

jim kadan manya manyan kawayenta su Nala da Rukky suka iso gidan suka kawaye ta yadda ake ji da zainab din kowa ma zama yay sunai mata kallo kamar wata real princess.

professional yan kwalliya su biyu ne suka mata special makeover aka saka mata Wani shimmering italian pinkish gown da gold shoes, kayan ya kwanta a jikinta tamkar anzana ne ajikinta her Hair was styled neatly, aka mata subtle make up mai kyau irin nasu na masu shi, kawarta Rukky tana tsaye a gefe tana tahowa kasa da excitement. tun daga can tace “Nalaaaaa, yaufa akwai bura uba anyah kuwa arifah bazata makantar da yaran makaranta yau ba? Nala ta ce, we run d town remeber? Wallahi the whole school will bow for her today, Dukansu suka yi dariya.

at arnd 9.30 am aka gama duk wani shiri suka fito tare da ita iyayenta da kawayenta dukansu suka sakota a tsakiya suna masu yagalgalata, a cikin wata exotic convoy na mercedez bunker Jeeps guda hudu suka nufi wajen hidima cikinsu babu wanda bai tsokalo wankan kyau na fitan hankli ba.

Wajajen karfe tara da rabi suka isa babban conference hall inda venue graduation in yake security ne kaca kaca a school din har da surveillance drone

tun daga waje manyan motoci keta hayaniyar parking sabida ingancin karatun da ake samu awajen yasaka wasu masu kudin marasa girman kai suka kawo yaransu schl din duk dama basufi daidaiku ba.

Drivers suna gama parking ahalin prof sauka suka karasa ciki her family arrival was chaotic dan kafin ma su iso cikin aka fara zunde ana nunasu saiji kake ana ambatar the almansurs, ihun rans dinta kakeji "O.M.G its zainab Arifah almansur"top student! she broke the school record! kusn kowa idonsa nakanta suna takowa hannunta makale dana babanta tana wani irin yngatcn murmushi ana musu confetti har inda zasu zauna lokcin zuciyarta acike yake da farin ciki danji take kmr wa ita kadai akay shirya wann taron bama sauran dalibai ba.

decoration din wajen yayi balain kyau yaran masu kudin nan are all dressed like met Gala red carpet event, basu saka wani graduation gown ba kawai sai aka rabawa kowa expensiv silk graduation banner kowa yamakala wuya like a parade prince nd princeses.

Bangaren su hajiya mairo kuwa dake yau asabar ne tun jiyan ta dinga jadadda ma kowa fitowa da wuri dan zuwa wajen hidimar nan dan bawai zainab Arifah zataje ta gani kadai ba harda ma zumudin son taga zayyanu duk dama ya raba kansa da ita amma still akasar ranta tanaso koda fuskansa ta gani. haka tasaka aka tashi sassafe, tun 6 am aka hau shiri, dama kuma anyi odern abinci da kayan snacks anyi packaging insu in d best way possble duk na kaiwa graduation ground domin taya zainab arifah murnan gama makaranta.

kulthum da sultana suka saka designer gowns dake ynxu sunyi tsayi duk angirma sai bakaramin kwalliya me aji suka sha ba classy french gown ne ajikinsu amma na sultana mint green, na kulthum kuma calm champainge gold da duk wani matching accesories bakaramin kyau suka yi ba...

ayanaah ce kawai taki sakin jiki ta shiga ribibin hidima dan tafi dmuwa da abunda zai je ya faru acan,haka kawai takejin kwata kwata bata son tana ganin yayanta da anty zainab arifah, kuma wann intense feeling din sosai yake ginuwa acikin zuciyarta bana wasa ba. kowa na zumudin zuwa amma banda ita dan normal make up inta tay ta shafa kajol, tay lining lips dinta ta bishi da shiny lipgloss sai kuma yakara sakawa tay masifar kyau din harma fiye da wanda suka tsaya cancade make up tashirya tsaf cikin atampa exclusive green da pattern din yellow da baki, dinkin yayi mata kyau sosai, skirt ne with peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns din atamfar aka yi mata aiki dashi, dan kunne kawai ta saka bata sa sark'a ba, agogon gucci ta dauka ta mak'ala a hannunta tay dauri me push back kadan snn ta yafa veil me sharara tagama shirinta ta fito.

ayaanah tayi wani irin kyau, gashi tay tsayi zaka rantse su sultanan ma age mate nata ne, karfe tara da rabi kulthum suka fito daga dakin sukayi dakin anty safeerah, tana ganinsu tace "Masha Allah sisters dina kunyi kyau" kulthum na murmushi tace "not as much as you, sultana tace aikece beauty queen a dan shashance ayaana tay dariya kasa suka sauko suna jiran mujaheed mai kaisu yazo dan Already hajiya mairo da su ammi sun fara yin gaba, daga su yaran sai anty safeera ne ynxu agidan dake maheer akace ya tukasu su hajiy kowa yasan aransa ibaad ma yana tare dasu..jerowa sukayi awaje harabar gidan sunata daukar hotona da selfies da wayoyinsu.

agaggauce anty safeerah ta kulle dakinta wayar ta a kunne tana cewa haba mujaheed yanxu da kabisu maheer din uban waye kake so ya kawo yaran nan bayan ni anbarmin aikin tahowa da abinci

..maganan datake y kenan har ta sauko tana fitowa babban falo tana jan tsaki daga can kasa ta hango ibaad daga stairs har ya canja kayan dake jikinsa ya saka casual ralph lauren shirt da sweat pant ajikinsa kafanshi sanye da slippers din Fenty, babu ma alamar zaijeshi wani waje, hanyan waje taga yabi zai fita ba tare da ya kalli palon ba rike da makullin motar da wani irin sauri tace "ibaad, don Allah ga su kulthum nan ko zaka ajiyesu a awajen su hajiya tunda kai ma fita zaka yi pls dan Allah kawaye na ne har sun iso babu wani space a motar kuma bana so suyi driving da kansu, bai juyo ba saida yaji ta gama cikin ransa yace hmm wato dai yau shi yazama driver wa yaran nan,cewa kawai yayi "toh" snn ya sa kai ya fita. anty safeerah ta sauke ajiyan zuciya dan batay tsammanin ma zai amince da wuri haka ba.

hasken rana daya fara fita ya haska fuskar ayaanah dago kanshi yayi zai duba ko sun fito idanunshi suka sauka kanta tsayawa yayi yana kallonta da gashinta da yasha gyara da yadda take murmushi ahankli. wani abu me karfi kamr sihiri yaji yana fizgarsa, cikin sauri ya dauke kai basu ma lura dashi ba saida ya shiga motar ya danna horn da karfi.

sultana ce ta farga ta fara zuwa kafin kulthum tabi bayanta ta shiga suka zauna a gidan baya da ido suka dinga ma alama ma aayana signal akan ta zauna agaba dan karma yace sun maidashi drivernsu ganin babu yadda ayaanah ta iyane yasa ta shiga gaban har zai tada mota jin dadin turarenta ya bugoshi ya dakata ya dubesu su biyun abaya ya daka masu tsawa yace "ina kuke tunanin zan kaiku haka da gashi a bude kmr wasu dolaye ku fice min a mota kuje ku rufe kanku da kyau kuma kar wacce ta ɓata min lokaci...da wani irin speed suka sauko suka wuce cikin gidan da sauri fargaba yasa ayaanah jin kmr itama ta sauka ta bisu tana kama handle din motar ya kwace ya rufe kirjin ta taji ya buga idonsu sakale dana juna yace "where did u think ure going to? muryanta a rarrabe tace "kace...muje...cikn katseta yace "not you..suda bantaba gaya musu bane nace suje ke ai nasha gayamiki kidena tula kwalliya a fuskarki bakiji ba..u wanted me to see it ryt? toh nagani! cikin matsanancin jin nauyinsa ta sunkuyar dakai kasa muryanta na fita ahnkali tace "nifa ba kwalliya nayi ba, amma bari zanje na canza toh.

...dan dauke kansa yay cikin basarwa yace"i dont have that time.. just use ur veil nd cover it up banason irin wann dresing in da zai nuna wani part na jikin ki awaje.. jan veil din ajikinta tay ahankli ta kara rufe jikinta dashi, yana kallonta da wutsiyar ido yace "not like this, sake hade ido sukayi dashi ya mika mata hannu idonsa nakan veil din ajikin sanyin kunya ta zare veil din ajikinta ta mika masa ya rike duk qamshin ta ya buleshi

cikin lumshe ido da budewa ya kare ma jikinta takaitaccen kallo snn ya tattaro makansa nitsuwa carefully yay placing veil din above her head, ya dan rufe mata sama sama daga inda sumanta yake nunawa ta gaba she look abit matured now tamkr wata matar aure

kanta na kallon kasa har ya gama kafin ta dago ta kalleshi da sanyin murya tace "nagode"..ido ya zuba mata baice komi ba, taga ya daga wayarsa yana latsawa ko minti daya bai gamayi da wayar ba sai ga su sultana sun dawo babu dandanin gashinsu da ke nunawa a fili.

suna gama shiga ya kunna motar, ya saka karatun qur'ani at medium yadda babu daman suyi magana da juna. har cikin makarntr su zainab arifahn ya kaisu spot din da familynsan suke yana ajesu suka sauka yana kkrin juyawa kenan hjiy mairo ta hangosa ta karaso wajen tafara masa masifa akan dalilin dayasa shima bai shirya yaxo nan din ba aikuwa ko kulata baiyi ba yaja motarsa yay cikin gari. haka nan ta dinga surutu dakyar da wahala tasaka ammi karama ta kirasa awaya harsaida ya amsa cewa zaizo tukun hanklin hjy mairo ya kwanta..

daga gefe kuwa kulthum da sultana banda tsokanar ayaana babu abunda sukeyi kowa nace mata tay kama da matar aure duk dama wasa ne she keep wondering why xai saka mata veil dinta ahakan..

can anty safeera taxo tare da kawayenta su biyu sai ruthy da hajy mairo tace axo da ita zata na rabawa jama'a abubuwan souverniers da sukazo dashi..

kusan kowa ya hallara face bappa zaidu dan shi baidama lkcin wann shirmen banxan, uncle moh ma daga baya ana daf xaa shiga yaxo aka basu speacial seat a VIP zainab arifah dake can sama wajen graduant kamr xata hadiye ranta ko ta tada aljanu data gan kowa yana wajen face ibaad.

gashi har camera me tsada na msmn tazo dashi wanda zata dauke zallan memories din graduation inta dashi, wanda intaje U.S ta dinga kallo tana tunawa da wnn ranar a matsayi ranar farincikin da bazata taba iya mantawa dashi ba

Shiru hall in yayi ana sauraron speech in da Principal keyi da ta gama ne sauran members in High table suma suka karba mic suna yiwa graduating students in Nasiha game da sabuwar rayuwansu wanda zasu fara a university sai da aka gama speech ne aka fara presenting dinsu short litreture drama professional band perfomance da wasu abubuwan na nishadi da al'adu.

Ana gamawa aka fara kiran best graduating students domin su karbi certificates dinsu Mc na cewa Zainab arifah hall in ya cika da ihu fa tafi bayan ta mike masoyan ta ne ke ihun kai hatta malamai sai da sukay mata tafi cos she was such an excellent student duk da tarin chaos din datake jawowa na nuna classims acikin dalibai.

ihun da aka sane ya sa ayaanahn jan tsaki mai tsayi a hankali batare da tasan ma tay ba

zainab arifah ta sauƙa daga kan kujeran da take ta karasa stage ta karbi certificate inta daga hannun principal a hankali tace mata " Thank you maam" bayan yan hotuna da aka dukesu da ita ta koma inda sauran mates dinta ke tsaye lkcin kawai ibaad ne a mind inta tafarajin wani irin baqin ciki atake kar ruwan idonta yafara canzawa..

haka aka ci gaba da kiran sunayensu har sai da aka kira duka students din sannan aka yi musu standing ovation tareda tafa musu dukansu a kan stage in kowannensu ya tapping bannersa suka sa ihu ana musu hutu, bayan nan kowa kujeranshi ya koma bayan nan, lokacin ne aka fara presenting beautiful prizes for the best overall graduating students lkcin kirjin kowa na bugawa da fargaba.

Itadai rashin zuwan ibaad kawai takeji aranta dan taso ace yana nan xa'a kirata sama a karramata haryanxu batasan wani irin baqinciki zataji acikin zucyarta ba in ibaad baizo ba.

Principal ce dakanta ta taso ta tsaya tana kallon Zainab Arifahn kamar shining diamond cike da alfahari ta amshi mike tace “Ladies and gentlemen…presenting our exceptional star… the one nd only pride of this honourable Academy… Zainab Arifah Almansur.”

memakon taji farinciki duk ta tuna ibaad baya nan sai ta fashe da kuka saida babanta ya tashi yaxo ya rike mata hannu,.tahowa yayi da ita zuwa stage Gown dinta yana sharar kasa gashin kantan nan dayaji gyara yana baza kyalle wajen duk ya kaure da tafi kuma kowa ya mike tsaye aka bata Standing ovation.

Ayayinda zuciyarta ya cike da duhu wann rana na farinciki yadawo mata na kuka babu wanda yasan akan ibaad take kuka an dauka ko kukan murna ne da nuna godiya

Daga nan aka karanta achievements nata Best Overall Student, Winner of School Math Olympiad, Honorary Award for Leadership, Outstanding Academic xcellence...Principal ta dauko award plaques masu kyau har guda biyar duka ya mika wa prof zayyanu sai kuma muryar announcer kawai.“By the request of her parents, family, and the school board, Zainab Arifah almansur is presented with the Elite Scholar Crown, the award given once in ten years...raf raf aka fara tafi..tsabar kuka taki sam ta karbi awards din.. wa baban nata aka mikawa crown dn yasa mata akanta lokacin tafi da kuma camera flash ne ke haskawa ta kota ina

duk da kukan da zainab takeyi still prof yanaji ne kamar duk duniya shine kawai ya haifi ƴa me ilimi, hajy hamida kuwa har tana zubda hawaye, har sai bayan angama snn Zainab ta mike a hankali ta kama mic for her speech kusan kowa yasan ta tsaurin ido amma yau sabida absence din ibaad muryanta na rawa rawa hartana jan majina tace “Today… is more than graduation to me. It is proof that no background, no doubt, no challenge can stop a girl who sees herself as capable to win..“Thank you soo much dad. Thank you to every single person who believed in me nd who care to come..dede nan ta kara fashewa da kuka me zafi dakyar tay controlling kanta tace"I promise… this is only the beginning..

Wani irin tafi aka mata kafin nan Music ya fara cike wajen kawayenta su Nala ta daga ta sama tana ihu, zainab “ZAINAAB!!! Zainab Arifah became the name the whole school will never forget amma awajenta is almost the worst day ever tunda ibaad baixo mata ba.

haka aka ci gaba da bawa sauran dalibai prizes, but asif today is her day alone har gifts na most most obedient,

uwa uba itace neatest, punctual..snn akaba dukka prefect kyauta

Dj ne ya kunna ma zainab din wakan champion mates dinta sunata mata murna suna zagayeta dan kuwa tafi kowa karban prizes a wajen Kowa na admiring dinta koma wacece ita Masha Allah tayi kokari sosai.

haka aka ci gaba da bidirin daga karshe aka rufe da addu'a,tun suna ciki suka fara daukar hotuna da yan ajinsu har suka fito waje,all eyes was on her kowa ma hirarta yakeyi sabida karramawar data sassamu da kuma irin kukan dataci.

Daga nan Kowa wajen family members dnshi ya wuce hajiya mairon ta fara rungumewa ta kara fashewa da kuka tun kafin tafara complain hajiya tace mata zainabu Allah yasanya Albarka,Allah ya taimakeki yasa kifi haka",tace Amen hjy amma meyasa bakice ma ibaad yazo ba gaskya hajy bakimin adalci ba. baki bude hajiya tace ikon Allah dama ba kukan farinciki kike yi makanki ba akansa kike wann uban kuka toh wallah ki koyi gode ma Allah zainabu kaji min yar goguwa wato namiji ne ma aranki ko?

Daidai lkcin prof yake karasowa tawajen tare da su hajy hamida da wasu friends dinta..

suna xuwa hajy mairo ta dauke wuta tay tsinin baki, murya kasa kasa hjya hamida da frnds intan suka tsunguna ta gaida hajiya mairo, itama ta amsa ta a dakile. sabida idon mutane yasa prof ya karaso gabanta yafara gaisheta, jin yanace mata mama mamaki abun yake bata..kallon idonsa tadingay da fushi bata amsashi ba har ya tashi ya bata waje....zainab Arifah ta dawo kamar wacce aka mata mutuwa koina taje ta tsaya saita tambaya mesa ibaad baizo ba duk saida tasa iyayenta suka damu, prof ya dinga kiransa layinsa a kashe. maheer yana tare da kulthum, ita kuma tabi ta nanike ma mujaheed da question har ya rasa abunda zai ce mata.

can can bayan har angama gaishe gaishe anata rarraba abinci snn ibaad ya karaso

ahakan ma disturbing text message din daya gani a dayan layinsa da amminshi ne kawai tasani yasaka yabar abunda yake yay wanka yasaka black kaftan da hula ya taho.

yana sauka a mota out of emotions zainab arifah ta wani je da gudu ta rungumesa saida tasa yaji kunya idon mutane sosai, it was hard for him to maintain his face yayo saurin raba jikinta dashi fuskrsa a dore yace "ke lfyarki kuwa ya zaki wani cakumo ni cikin mutane kamr wata babban mahaukaciya are u insane?? cikin kufula ta kallesa zatai magana cikin katseta yace" ke da Allah matsamin karko sake min haka..am not ur mate" dan turata gefe kadan yay ya wuce wajen su amminshi tay saurin biyosa abaya da fargabn kar ace mutane sunga abunda ya faru

she kept following him duk inda ya tsaya within few minute ta dawo dede tadena kuka sai kuma ta bude chapter kinibibi...bata ma bari babanta ko su hajiya sun tuhumesa ba sai tana karsehi tunda dai yazo shikenan...dacan ayaana tana zaune da su anty safeerah da su sultana ne saidai tunda aka kafa chapter zainab arifah taga kowa yana cewa ai kukan datakey sabida ibaad baixo bane bla bla bla tunda yanxu ta gama schl kawai ayi kkri amusu aure karta shiga wani hali kowa yana kawo dfrent opinion hanklin yaana sai ya fara tashi sosai..

she was watching duk yadda zainab rifah ta makalkaleshi batajin kunyar idon kowa kamr wutsiya take binshi tama mance batun iyayenta agefe

ga hajiya sai hirarsu take

ma uncle moh itama maganan kenan ayi ayi musu aure..

ruthy ne kawai tagano cewa ayaana ba kalau ba, Agindin wani bishiya ruthyn taja hannun ayaanah suka zauna ta inda ba'a kallonsu, tun kan tace mata komi taga ayaanah tana hawaye tafara rarrashin ta tana bata hakri har sanda taji nauyin dake kan zuciyarta yay sauki snn Ta tambayeta meye ne damuwarta?

Dacan tay shiru kmr batasan mema zata fara furtawa sai can kuma Ahankali ta sauke ajiyar zuciya saboda fargaba da tashin hankalin da zuciyarta ke ciki wani tsiririn numfashi taja hade dayin kasa kasa da kanta dan sam bazata iya kallon kwayar idanun ruthy a wannan lokacin snn tay mata karya ba.

Ahankali tasoma magana muryanta kasa kasa cikin sanyin jiki tace"yaya na ne" daga nan shiru ta danyi tana fidgeting fingers dinta kanta asunkuye take idanunta suka kara tara wasu sabbin ruwan hawaye tanajin wani sabuwar feeling din tsananin tsoro dake dabaibayeta,a cikin shagwabbiyar yanayi tanamai takune fusknta da sakalci tace,'..toh Bashi ba ne saiyana ta fadomin acikin raina kuma ynx kowa yana cewa zai auri anty zainab..

...shiru ta kumayi tana dago kanta sai zirrrrr hawaye masu rauni suka sauko mata bisa kuncinta, kara fashewa da kuka tay mai tsanani cikin kukan take cewa "ni wallhy bana son ya aureta..kawai bata dace dashi ba..kuma baice zaiy aure ba. Jawota jikinta ruthy tay ta rungumeta ganin kukan nata yafarayin yawa tace kai ayaanah kiyi hakri dan Allah...kinga za'ay ta kallon ki kina kuka anan wajen...kiyi shiru kinji?

Da kyar ta dena kukan ta dago kai tanajan shesheka ruthy tana dan shashare mata fusktanta cikin sigar lallami har sanda ta danne kukan tas snn ta riko hannayen ta suna fuskntar juna da sanyin murya tace "i knw how u feel..hajiya tace min he is ur quardian, wai shiya kawoki nan garin ko? its natural for u to feel attached to him nasan duk inda yake ai shima hanklin sa nakanki

..koda bansani ba ai alama ya nuna yarinyar nan ce take sonshi..kimasa uzuri kinsan idan mace tanason namiji irin wann bazaki iya gane komi ba.

Ta dafa gefen fuskarta acikin nitsuwa tace ki kwantar da hanklinki ki karkisa damuwarta aranki if she is not good for him zakiga bazai aureta ba kinsan mata masu throwing kansu ma namiji maza basu daukarsu da daraja i assure u he is not going to fall into her traps

jiki a sanyaye ayaanah tace haka ne, sai kuma tay karamin murmushi tace "i dont even knw why it bothers me. sai inaji kamr i am intimadetad by her. i mean, ruthy look at her she is a rich princess, classy nd intelligent..kuma tana sonshi sosai..sai naga kamr dai with time zakiga zata aure shi din dan banga wani abu data rasa ba.

cikin dafata ruthy tace 'ayaanah amma kinga kanki kuwa har kike hada kanki da wancan kucakar...ayaana tace what?ruthy tace yes kinjini gayyar kudi ne da kyale kyale

amma wallah ko kusa dake bata kai ba. if da ace kece a matsaynta ma da ba haka ba. besides, kema me kika rasa? iyaka ta nuna miki bude ido kema da kinaso da tuni na nuna miki hanyar zamowa big girl dede da yayanki..

da mamaki ayaana tace bude ido as how?? cikin rage murya ruth tace "like getting to knw alot of big girls stuff mana. kmr yadda wancan din takeyi. she have her gang, fashion taste, nd can drive cars. halama tazaga duniya tay socializing ke fa zama kawai kike a waje guda kuma yadda kike kyakyawan nan koshi yayankin yaga kina leveling up bazai kalle wata zainab arifah ba.

shiruuu ayaana tay for a while kafin can tace " i dont knw what to say..amma zan miki magana innayi tunani akai..

karamin dariya ruthy tay tace " its just leveling up babe. wai bakiga yadda na dawo bane? just to knw how things work.. what attract men..no matter what dai dik macen da bata san kanta ba bazata iya mulki a duniyar namiji ba. itama wann din da tana da aji da tuni yafara sonta...cikin katseta ayaana tace its okay...zan kiraki amma bari nagama ss1 dinnan dai cos i dont want to be lagging behind..

ruthy tace anythime kika shirya kawai kizo wokers estate ko mu hadu a shago i wll teach u some things..

da fargaba aran ayaanah tace okay...daga haka suka bar hiran, bayan ayaana ta gyara fuskarta sukazo wajen daukar hoto.

Tunda akay na family tay dasu sultana da kulthum sai bata kara shiga wani ba dan yadda zainab arifah take makalkale a inuwar ibaad yana balain bata haushi

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025