ABUNDA KE 'BOYE...

36

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.

⏯️3️⃣6️⃣

Neman waje tay ta zauna akan wani chair bata jima da zaman ba cikinta yafara murdawa which explains the sudden mood swing da anxiety datake fama dashi saiyanxu ta gane ashema period ne yake shiriin xuwa mata shiyasa ita kanta ta gane kanta..

tunkan ciwon ciki yay nisa ta mike cikn sauri zataje wajen mujaheed ta rokesa suje gida tunda anma gama komi tana dosowa sai kuma tagansa tare da xainab arifah suna magana portrait juyawa tay da ssuri bata karasa wajen ba, agefe kuma kwata kwata bataga su kulthum da sultana da yaa maheer ba da alaman sunje can ta wajen prof xayyanu tare da anty safeerah da uncle moh ana gaggaisawa batamasan meyake gaya musu acan ba

tana juyi ta hango hajiy mairo tana zaune da ruthy tana sharo kwana zata zo wajensu taji inuwar mutum ata bayanta kirjinta taji yana bugawa da balain karfi tana juyawa kuwa suka hade idanunsa waje guda

...ganin yadda idonta yay wani irin jaaa ahnkli yace ina zaki je? muryanta na fita da sanyi kafin ta amsa shi taga ya kamo hannunta "come lets sit over der nima nagaji..kafin tace wani abu taga ya jawo hannunta ahankli take binsa abaya har suka isa gaban wani chair a garden suka zauna inda babu hayaniyar mutane sosai

suna zama ta sauke ajiyan xuciya ya xuba mata ido fuska ba yabo ba fallasa yace "are u okay? hawayen da batasan da su ba ya ciko idanunta da sauri

ta girgiza kai ya hade rai "toh mesa kikaje can kika xauna da wata kina mata kuka? da mamakin jin hakan daya furta ta kallesa cikin sanyi tace

cikina ne dama yake min ciwo.

.".dan shiru yay kdan yana kallonta cikin kyabe baki yace

"nd u dint tell me? toh toh ince ta baki drugs awajen kinsha

...hawayenta datake dannewa ya fara zuba ta girgixa kai ahnkli tace lokcin ai kana tare da mutane ne ni bazan iya zuwa nagaya maka ba

yace ni bana tare da kowa its just zainab ko bakisan ta bane...cikin turo baki da shagwaba tace but she is talking to u all the time shiyasa.

..yace shiyasa me? u have no businss with her talking to me da zakiy fushi..cikin makale wuya tace "ni ba fushi nayi ba..da wutsiyar idonsa yadan harareta yace i dont believe you sau nawa kina ciwon ciki bakaiy kuka ba saida kika ganni da mace..kara tuluwa hawayenta yay tace nifa ba haka bane i dont want to cut u ppl off kuna magana kartaji haushi ai naji ana cewa ita zaka aura kuma..

karamin dariyar bazata yay yace.."aure? ninace miki haka..zatay magana yace look..in abunda ke damunki kenan why wont u do sumting abt it..go nd tell xainab dat ure once my wife shikenan zata kyale miki ni hala. hawayen tafara sharewa ahnkli kafin ta san amsar da zata bashi sai ga zainab din tana tahowa ta wajensu da sauri ganin yadda suke zaune kurkusa da juna kuma akebence da wani irin hararar kasan ido ta kalle ayanaah tace 'ashe kinzo? ai ban ganki ba..dakyar ayaana ta amsa tace ehh..shide mamaki take bashi. zainab ta dawo da idonta kansa tace hey, ynxu photographer da zai mana portrait zaizo just give me 5min dan Allah zan je na dan kimtsa fuska na zo nace mai ya same mu anan...tana fadin hakan batajira jinshi ba ta juya da sauri ta bi kawayenta dan agyara mata fuska cos she want a very big portrait of them wanda zatay masa enlargement ta aje a dakinta

tana barin wajen bada jimawa ba kuwa photograper yazo

irin professional din nan to kowa yana jiransa shikuma baisan waye zainab arifah ba he tot ko ayaanah ce..yana zuwa yafara cewa small madam kidan kara matsawa kusa dashi..sir can u place ur hands around her, yawaa..bai bata lokci ba ya daudauka musu hotona masi shegen kyau..yana barin wajen ibaad yace tashi muje gida tunda cikin ki namiki ciwo kar yay tsanani..batace komi ba ta miƙe tsaye ta fara binsa batare da kowa ya lura da su ba ya bude mata gaban motar dayaxo dashi ta shiga ta zauna snn ya zagayo yana shiga ya tukasu suka bar schll din suka nufi gida.

yana sauketa ya juya ya koma gaban wata eatery ya shiga, nan ita kuma ta wuce daki dan tay wanka ta saka pad, ta gama har ta fito kenan tazo taga ya aje mata ledoji guda biyu, daya na drugs daya kuma kayan cime cime ne aciki..tun bata bude ba taji qamshi na bugata bari tay ta kimtsa kanta ta saka simple riga da wando marar nauyi ta zauna ta jawo ledan ta ciro fruit salad na ciki ta sha saida taji daidai snn ta fara cin su plaitain eggs da su pper chicken dake ciki...katon ice cream dake ciki tasha kadan ta aje sauran a fridge at around 2pm ta tura masa text snn ta kwanta nan wani bacci me nauyi yay awon gaba da ita..

bata kara jin meya faru ba sai can wajajen 4 data farka takeji labari abakin kulthum yadda zainab arifah ta dinga ma photographer hauka a fili...in short the whole graduation dat was suppose to be joyous was just a grand mess kowa saida ya wuce gida da gulmanta a makaranta.

bayan komi ya lafa 2 days bayan graduation din aka kawo ma zainab arifah pictures insu har gida ta gaggani bayan ta yayyaga nasu ibaad din tasa wuta ta ƙonasu kurmus, gashi tun jiya tay tay ta rokonsa ta text message akan su sakeyin hoto baiko kulata ba harynxu..

dakyar ta cire batun hoton aranta ta dukufa shirin zuwa karatu duk wani abu na yar gata an mata har saida ya rage kwana biyu kafin ta wuce snn tazo gidan ta musu sallama, kowa a shashensa. anan ta nace musu wai saidai ayaanah ta karbi wayarta ta mata hoto

ita da ibaad, ayaana kuwa ta karba ta musu pictures guda biyu, zama tay awajen tana editing din hoto dan ya kara kyau bayan ta gama ganin ita daya ne anan ta miƙe kai tsaye ta shiga room dinsa bataga kowa aciki ba har da zata juya kuwa sai caraf taga hotona guda uku half opened acikin envelope akan table dinsa da sauri ta bude taga the same pictures ne nashi da ayaanah data yayyaga sune anan batama san ya akayi ya samu copies dinsu ba..

kirjinta atake ya fara mata zafi tay sauri ta fara cusa su a envelope din da alama zata dauke taje ta konasu agida har tagama tattarawa zata saka a jaka kenan taji mutum akanta tana dagowa taga ayaana ta kura mata ido fuskarta ba asake ba tace "anty zainab in kin gama gani kibani yayana ne yace inkawo masa pictures din zai tafi dashi gida kuma sauri yakeyi...

ranta bai so ba ta miƙa mata..

ayaana ta bude hotonan tana kalla agaban zainab arifah tana murmushi basuce ma juna uffan ba, har ayana ta gama ta juya wani dan uban tsaki zainab arifah din taja ta fito batace ma kowa komi ba ta wuce wajensa sai taje ta same ayaanah still tana tsaye ajikin motarsa suna magana bata san me suke fada ba

haushi yasa kawai ta shiga nata motar ta daka ma driverta tsawa basu ma lura da ta bar gidan ba. koda da taje gida sosai haushin ayana ya kara tuluwa aranta tana jin kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamr yarinyar nan ynx

bata daddara ba ranar da zata tafi haka tasa babanta ya kirashi wai shi zai kaita airpot duk da hakan ya faru har ta wuce U.S hanklinta a tashe yake akan alaqar sa da ayaanah. gashi sunyi da babanta cewa bazatana dawowa gida ba sai once in a while bayan ta samu dogon hutu, tun a jirgi kuma tafarajin inaaa hakan bazai taba yuwa ba, tun bayan graduation innan she bacome so insecured abt ayaanah sai ta fara jin dole ne ma tana dawowa gida akai akai sabida bazata sake yarinyar tagama kwace mata ibaad ita tana can tana karatu ba

tana isa gidanta a manhattan sukay waya da kawayenta iyaka maganan datake musu kenan sai kuma taji duk sun bi bayanta akan tana dawowar kawai in tana zargin ayaanah acewar rukky ai ayaanah tafita komi da komi is only fair if she marked her territory.

bayan kamar wata biyu da wucewar zainab arifah kasar waje daga nan nija kuwa ayaana tafara sauya kalar rayuwarta gabaki daya

schdules na karatun ta da skin care da skills inta na girki duk ta kara kaimi akansu bana wasa ba. dacan bata fiye kashe kashen kudin da uncle moh yake bata ba but the more ruthy tana gaya mata yadda rayuwa take a america the more tana gogewa anan itama. ruthy tana harka da wasu gang ne ita kanta batasan a ina ruthy ta samesu ba they know almost everything abt life kullum tazo shago anan suke haduwa, haka zasuje wajen hair dressing, latest designer da ake dinkin zamani da sauran abubuwa na gyaran jiki na mata tana daf xata y final exams na ss1 aka fara shirin graduation din su kulthum da sultana ranar da suka gama su final exams dinsu aka musu hadadden walima a ranar ne kuma kulthum ta gaya musu cewa yaa maheer yace mata zai aureta but she dont knw what to tell him yace dai taje tay tunani..they kept it as secret basu gaya ma kowa ba saidai su bata shawara, har maheer yay passing bar dinsa yay register nysc.

acikin yan kwanakin nan ibaad yafara batun exams insa na 500lvl yafara clinicals daga lkcin ne kuma ya lura da sudden canzawar da ayaanah tay sosai wanda harshima yasha mamaki irin seriouness da karatu da kuma yadda take bala'in yin wayo tana wayewa harma kamr zata fi su sultana sanin rayuwr kwalisa da kwalliya yanxu. while uncle moh is busy faving ways yana spoiling dinta with gifts dan wata rana har schll dinsu yake zuwa mata da suprise, tuni ruthy ta fara gaya mata cewa ai uncle moh sonta yake yi,ita kuma duk bata dauki abun seriius ba damuwarta yadda zata dawo macen kanta ne ta dan kwace ibaaad a hannun zainab arifah.

first time da zainab ta fara zuwa hutu iyayenta basu so ba amma ta nuna masa bazata iya zama acan haka ba babu yadda suka iya suka kyaleta, kullum tazo gidan she will only provock the situatuon na wann silent jealousy war dake tsakanin ta da ayaanah, zainab tana ji dakanta cewa tana da komi na duniya, ayaana kuwa tana amfani da wann daman tana dada shaping brain da sense of fashion inta.

kafin ayaana takai ss2 maheer ya gama nysc da zai wuce karatunsa aka hada harda hidimar birthdaynsa akayi masa home walima me dadi ranar haka sultana da ayaanah suka zuga kulthum har saida ta amshi batun aurensa yabata kyautar axurfa ring me shegen tsada few weeks after that ita da sultana suka fara level one a bayero university shikuma ya wuce canada karatu...

rayuwa ya zamana basa wani haduwa sosai da ayaana inba agida ko wkends ba wanda yasa ynxu ayaana tafi shakuwa da ruthy sosai sabida suna spending much time insu atare a shago da kuma cikin kawayen ruthyn da suke nuna ma ayaana wani duniyar yan matanci da batasan dashi ba.

she is almost 16 amma sosai jikinta ya habaka silent rival competition dinsu da zainab arifah har sai ya baka dariya

musmn da zainab taxo ta fara jin kamar kanta zai kunce idan ta dawo taga canji ajikin ayanah,kmr yadda akata ririta ilimnta haka taji ana ririta na ayaanah, nd nala is alwys trying to copy ayaanah's fashion sense. gashi dai normal laces da atampa take sawa amma yadda take zagewa tay styling dinsu da dinkin zamani yabi jikinta yasa suka fara kishi da ita sosai

ya zamana ko zainab tana school a can america amma

hanklinta sam baya kwanciya, she was so intimadated da ayaana, professional gym din datake zuwa acan U.S tana gyara shape na jikinta duk sai taji ya fara kasa mata, yadda take ganin jikin ayana yana transforming into hour glass shape dake itama suna fita gym din time to time haka da su ruthy. ita kuma tay tay nata ya canza amma inaaa.. she started to think abt cosmetic surgeries. inda zata biya millions of naira agyara mata shape inta ya dawo me kyau fiye da na ayaanah, still duk wnn bai isheta ba har gidan su tasaka mum dinta hajiya hamida akan lallai ta kirawo mum ramlat collection itama aka siya mata atampopi da leshuna irinna ayaanah. babu abunda basu siya ba aka bawa fashion profesionals suka mata dinkunan zamani yet still duk hanklinta bai kwanta ba.

within dis time business din su ibaad yay flourishing sabida they are well connected and highy marketed by strong business routes he bot his first personal cars ayayinda yake kan kkrin shiga final year yana xuba kudi me yayiwa ma mum dinsa hidima snn ya kuma bude ma ayaanah clothing line online business tana saida imported gowns wanda ko ammi karama ma bata gayawa mata komi da komi akai ba dan harga Allah bataso uncle moh yaji labari bare yay wani abu akai, kanwarsa safiya kuma ya bata kudade itama tanayin nata beaded bag business din agida.

hanklin uncle moh ya fara karkata sosai wajen batun fayyace ma ayaana sirrin dake zuciyarsa da zimman next year tana gama secndry school sai aurensu, haka kawai ya tsira nunawa anty safeerah wata kalar soyayya me ratsa zuciya kudinsa yake zuba mata har kamr baisonsu trying to trap her dan kar yazo ya kawo batun aure ta kawo masa matsala dan ji yake babu amount of borin da zata masa da zaicanja shi ya fasa auren ayanah musmn ma yanxu dayaga ta bude ido ta wayewa sosai

the same week ayaana tafara lura da wasu dabiun ruthy da bata gane musu ba, dan dacan dai ta dauka kasancewarta ba musulma ba yasa take harka da maza but now is becming totally difenrt wasu irin mata da gayu take harka dasu kmr yan cult, nd it feels like she is sleeping with both of them. saidai abune da ta kasa samun wani evidence akansu dan ruthy bata sakewa ayaanah tazo dakinta ga tana aikata wasu abubuwa da ba daidai ba. ita ta koya ma ayaana abubuwa da da wuyane akoya mata su a gida kmr su amfanin saka jigida, full nd elaborated explanation of what female libido is, vaginal care,art of seduction da sexual feelings,har yadda ake aski na maza, she will alwys tell ayana ai intay aure wyann abubuwan zasu mata amfani musmn ma da ynxu da iyawa matan bariki suke kwace zuciyar mazajen wasu, ruthy ta jima tana so ayaanah ta fito fili ta bata labarin alaqarta da uncle moh in aurensa zatay dagaske saita nuna mata hanyar da zatay handling babban mutum dan tunda suke da ita ta lura kmr shine yake yawan bata kayan duniya da kudi amma kuma haryau sai taga ayaanan kmr hanklin ta ma bai kasan gabaki daya.

ayaana bata wani jin maganan kowa inba na ibaad ba, ruthy ta kasa gane mata sam gani take kamar game dinta agefe amma kuma tafi damuwa da wani daban wanda yake da budurwansa da zai aura.

Har ila yau, Rayuwa sosai ta sauyin bazata wa ayaanah. wanda ya santa a shekaru biyu da suka shude bazai taba yarda da cewa ita din bace yanzu cikin sauki dan kuwa wayewar da tay ynx ya bala'in amsar tsarin jikinta ya saka mata kamiya da nitsuwa da kwanciyar hankali, ko fatar jikinta ma dayaji isashhen kulawa, motsa jiki hutu,da ingantaccun Abinci tuni jikinta ya warware ya dau wani irin haske da kyalli kibane kawai batayi sosai ba amma babu wani abu ajikinta na girma da bayyana ba

Wani irin tsabar kyaunta na tun usuli shiya soma hargowan fallasa kansa a fili kamar wanda dama a matse yake daya fito sarari,ba aufi tun tana ss2 din tan tasoma dawowa babban mace cikin cikakkiyar hanklinta Dadin karawa da yanzu ta cire tunanin komi da kowa aranta takuma dora dammaran kai rayuwarta gaba shikenan taji rayuwa yana mata sauki,bayan tallafawar tarbiyansu ammi karama karatun novels din da takeyi shima ya balai'n taka rawa sosai wajen cire ma zuciyarta tsoron tunkarar rayuwarta na nan gaba duk dama Labarin novels baicika zamtowa gaskiya ba amma yana taimka mata wajen social nd mental awarenesss da samun ilimi game da wasu rudaddiyar matsalar dake addabar rayuwar ya mace koma na wani daban na kusa dashi, Hatta kulthum saida ta komo baya tana shan mamakin irin tarin ilimin ayaanah yarinyar a mugun nitse take,kuma tana kkrin perceving knowledge dinta in a very sensible and matured manner sam sam batada ragon azanci, wanda za'a iya alakanta yiyuwar hakan,a sababin challenges din da tacikaro dasu masu nauyi da wuyar dauka a rayuwa. ko ita dakanta batayi tsammanin zata kai wayann shekarun batare da taga mamanta ko addanta ba.

kwance tashi babu wuya karatu ya fara rike zainab arifah sosai yawan dawowarta nigeria duba ibaad sai ya ragu sosai, dan akwaita da son taga tafi kowa ilimi kuma can columbia university na manhattan kusan makarant ce da ake ji da ita a duniya mostly geniuses da gifted student ne kawai ke iya zuwa can dan haka kusan dolene yasata nitsu danta faranta ma babanta ransa kamr kullum

...all this time tun bayan graduation din xainab sau daya tall prof xayyanu yaje shago ya gaida hajiya mairo wanda rabi hayaniya kawai suka kare dashi, koda ta masa maganan yan uwansa da shiga dangi sai yace mata ita ta wareshi kuma yan uwansa dama arxkin sa suke so bashi ba, duk nasihar da zata masa ahaka maganan nasu yake karewa, shine me lefin amma yafita playing victim card da kyar da wahala ya turo hajiya hamida tazo ran juma'a da goma na arziki ta gaishe da hajy mairo agida wanda tun daga ranar basu kara dawowa gidan ko sun kirata awaya ba.

rayuwa ya cigaba da haka ibaad yana kammala exam yafara batun housamnship ayaana tana kkrin zuwa ss3 saiya bude personal business dinsa a kasar waje him nd his friends are lowkey conjuring 400+ millions every month his life had completely changed u cant even recognise him ryt now, wasu harkan ma ta wajen connectiomn dinsa yake samar wa bappansa upper hand a international business.

it was miracolous how life can completely change with the ryt ppl, ryt netwking, nd ryt connections batare da ansha wahala sosai ba. kudi yake dashi ynxu wanda shikansa bai nitsu yasan nawa ya tara ba

da shi da abokansa sun dawo wasu kala na daban irin hot gentle guys dinnan da zakama ji tsoron hada hanya da su, farhan yay gemu all over his face yana kuma kitso shima yana managing wani branch na bank in babansa acan sydney yanxu, prince hassan kuma shima this year zaiy aure yana tech business personally ya bude kamfani fin tech, jamal is already running companies nd fathering a 1yr old baby boy da matar sa mufeeda ta haifa masa. ibaad had this upgraded john abrahams body structure not too big and not close to skinny kuma shi yana da tsayi, he is a bit muscular and very strong shi baiya tara gemu me yawa kamr na farhan saidai sajensa is alwys neatly caved, kansa a low cut yake bari. his skin is as smooth nd clean like a baby. duk ranar dayazo gidan haka kulthum da sultana zasuyi ta hot body crushing akansa while ayaanah had deeply fallen in love with him..

duk dama babu wanda yake kulawa da rayuwarta kamr shi, ita dai haryau bata cire tsoro da fargaban zata iya rasashi wa zainab arifah ba..

kwance tashi ayana da sultana da kulthum suka dawo hadaddun yan mata kuma haryau safiya bata sakewa ta hada hanyarta dasu, soyayya me sanyi da dadi kulthum sukey da maheer d distance make them addicted to each oda on phone, video calls, chat, kuma duk abunda takeso yana tura mata sultana tafara kula saurayinta ahmed waziri sama sama wanda a schl ne ma kadai suke haduwa.

this year zasu shiga 200 level, ayaana kuma tana first term ss3 ranar asabar anzo wknds kwasam bappa zaidu ya shigo ma hajy da su uncle moh da maganan auren kulthum da maheer kai tsaye tunda bazai jima ba zai dawo dan yasamu ma wani aiki a malaysia already

..kamar da wasa aka fara maganan uncle moh bai damu ba da murna yace in har kulthum ta amince toh shima ya amince dan yafi aminta ma da maheer sosai...

cikin kankanin lokaci su anty safeerah suka ji ta bakin kulthum har saida aka gamsu da komi snn aka fara batun aure, it was like the smoothest weding proposal agidan kowa is okay with it dan hannu biyu ammi babba ta amince sanin cewa anty safera da uncle moh suna dashi, kuma kulthum din yar gata ce she have noting to loose kwata kwata wata uku su bappa suka saka rana nan aka fara shirye shirye, kawayen amarya su ukunsu sukayi meeting aka bawa sultana babban kawa ayaana kuma itace incharge na girls bridal shower event da zasu hada as usual ruthy ta kira tana tayata siye siyen kayan bridal shower da kayan da zasu saka, while sultana suna shirye shiyen kayann amarya na dinner, kamu da su dinki da su anko da sazu saka a hidiman biki...

Tunda aka fara ma amarya shiri ta koma yawancin zamanta tare da hajiya mairo a nan family house, in ana zaune kullum cewa take gidan zaidu yafara fin karfinta dan tunda aka saka ranar auren maheer ammi babba ta kunce ma bappa zaidu salo salo na shafin hauka, kullu yaumin sai tay zage zage ta kirasa munafuki, kai hatta maheer dinma zagin shi takeyi tana cewa ana munafurtan ta, badon komi sai gani datay kusan rabin shirin auren da ammi karama akeyin komi, ita kuma ko kadan batason fatima ta shiga mata hidimar auren danta, shikuma maheer yasan ammi babba sam bata iya muamala da jama'a ba baison ranar aurensa yaji kunya shiyasa ya nace dole dole sai ammi fatima ta shige masa gaba, koda tazo taji labarin cewa ma da shawara ammi karama maheer zaiy auren nan bakaramin zage zage tay ba..

iya bakin kkri hajy mairo tay wajen sasanta su amma ina haryau ammi babba a haukace take tana jin haushin kowa dan haka tace lallai lallai itace za'a barmata batun hada akwatunan aure

haka ta tara gang din kawayenta su hajy ramatu haka maheer ya siya boxes dinsa snn yafara turo mata kudi tana sayan abubuwa wasu abubuwan oder yakeyi ya saidai taga an kawo. tsabar zugin kawaye wani irin kayan fitar hankli suka dinga sawa sabida kar ace fatima tafita ko ita bata dashi..haryau bata gama warkewa da dumbin baqin cikin datake shaka awajen bappa zaidu ba cos she knew shine yake sponsoring din rayuwar fatima da kudadensa ta rasa wani irin asiri fatima tay ma mijinta dan ko ita baiya kashe mata kudaden dayake kashewa fatima a boye.

hajiy mairo dataga bazata iya solving wann case din ba yasa ta tattaro ta dawo family house domin shirya amarya Saidai shirin tasu ba irin tamu ta zamani bane,irin shirintasu ce ta al'ada ta yadda za'abi salo salo wajen kakkabo da ni'imar ya mace wanda basai an shashsha wani wahalar banza wajen shaye shayen maganin mata ba.

Tun cikin wnn watar farkon acikin watannni ukun nan da ya kama hajy mairo ta sauya ma kulthum routine din cin abincinta,yanzu kaff abin cinta sun dawo na asalin fresh fresh ganyayyaki da kayan marmari da hadaddun kunun daƙa asalin dakan tsakar gida na turmi,vgero,waken suya,gyada mai yaya, Ridi,alkama da makamantan su kala kala masu nunnuƙe da kayan yaji kanun fari masoro,kajiji harda busasshen dankwalin hausa, domin hade jikin mace,da tsassafo da ni'ima da kuma bulbulo da komi najikinta ciki da waje.

yanzu kusan awajen hajya mairo kulthum ta take wuni safe da rana wani bin bacci ne kawai ke kawo ta cikin gida

anty safeera batace musu komi sabida ta lura wann ba huruminta ba ne haryau da akwai wnn kunyan bata son ta wuce iyakarta akai. Gefe kawai tay itama tana nata shirye shiryen ata gefen ta kyale kulthum da hajiya mairo

Babban aminiyar hajy mairo wato hajy hajara wanda kusan kullum tana zuwa gidan suyi budurin su akan kulthum atare babbar mace ce datasan ilimin al'ada irin tsoffin matan nan ne da anga jiya anga yau..ansan komi.

Dan tunma kafin su fara shirya amarya ita tasoma kawo shawararin cewa abi da yarinya a sassafa sassafa acewarta takurawar da akeyi ma ƴa mace inzata gidan aure a dura mata wann abata wann shine babban makasudin dayake jawo mata matsala acikin zamantakewar auren ta a nan gaba musamman ma wann zamani da yawancin kayan gyaran na emrgency ne bana din din din ba,in yay ne yayi lasting zuwa wata uku wata shida,ko shekara guda amma daga an haihu kuma shikenan komi ya lalace kenan sai anyi dagaske asake dawowa zam zam Kafin nan kuma sai kaga yarinya har ta shiga damuwar ganin sauyawa atattare da mijinta Batare da yin la'akari da cewa shidan adam in ya samu dadi, anan gaba na wanda yafi dadin da ya samu abaya zai nema ba.

Hakan yasaka amfani da magungunan mata batare da karato hikima da basira aciki ba yake da mummunan hatsari ga rayuwar ya mace

daga zarar miji yaji zaƙinki tun kina amarya, bazai karayin la'akari da yau da gobe ba a kullum bukatarsa shine kirika kara masa zaki yau yajiki fiye da jiya gobe ma yajiki fiye da nau wann shine burin kowani da namiji.

Dan haka yasa suka dauki hanyar bida jikin kulthum ta hanyar da baza akai ga wann matakin ba,babu wani maganin mata da suka siya face yan tarkacen hade haden su na wanke infection,da dumama cikin jiki da farji da kuma duk wani matakin da zai kauda zubar ruwan gaba

Sirrintaccen hadinta na furen tumfafiya da aka wankeshi tas aka dakashi da mazrkwala masu kyau kamar falle

Guda biyu,sai dabino shima mai kyau kamr rabin gwangwani haka da kaninfari maiqamshi cokali guda da citttan ta daidai misali Duka wannan hadin aka dakesu lugwi suka dawo gari. In za'tay mata amfani dashi sai an gurza kwakwa snn a jika a ruwa ta jiku sosai snn sai tace ruwan kwakwar a kofi,toh da hadin wannn garin da ruwan kwakwar za'a tafasu daga ya dan huce kadan sai bata ta sha.

Wnnan hadin mai tasirine mai saka mace taji tana hadewa tana matsewa taciki,yana matukar kakkabo da sha'awa da niima shiyasa Bai wuce sau daya sau biyu suke mata acikin sati ba.

Sai yan tarkacen markaddan kankana dabino da gwanda da zuma,ko markaddden ayaba a zubamai zuma aciki abata tasha.

Ta hada kayan sauko da ni'ima da kara dadin wajen daban wanda dama hade haden yayan itacuwa na fruits su suka taka muhimmayar rawa aciki sede wasu fruits din ba kasafai aka cika samun su ba saita sha wahalan aikawa a jos ko can ta wajen inyamurai sannan sukanyi excises din jikin ta sosai,sai yan daidai kun supplements kamr su sweet root of peruvian viagra da asalin tsumin goron tula.

To Tasan yarinyarta virgin ce duk dama da sauran sit bath da hajiya hajara ta riga ta bayar wanda tasan zasu matseta amma anan hajy mairo saita ragesu wasu abubuwan xuwa nan gaba Aganin ta in kulthum ta matse sosai abunfa bazai zo ya musu kyau ba dan haka kayan matsi basuda da yawa acikin kayan gyaran ta.

..kuma duk wani abu na amfanin mata me kyau na zamani duk ta dan siya mata na tsuguno na wanka duk ta sata agaba, Shirin datake mata irin wanda za'aji tane zam zam bakamar ko wacce mace ba. sauran kuma aka dan tarkata aka mata guzuri dasu.

mujaheed was so busy a ranakun yana taya mamansa abubuwan shirye shiryen biki

kusan ibaad ne yake yin komi gameda fannin ango duk wani hidiman kayan sawa and all what is needed na ango shi kadansa yakey tareda shi da prince hassan zarko dake sukadaine ynxu a nigeria farhan da jamal kuma suna kasar waje sai lkcin biki zasu taho.

ata fannin kawayen amarya kuwa abubuwa basuyi ma ayaana tsauri ba dake tana tare da ruthy suna aiwatar da kominsu atare wata rana har kwana sukeyi atare agidan ko taje ta jima a dakin ruthy.

ana shigowa month din bikin shiri yay nisa amincewa da shakuwa yafara shiga tsakanin sultana da saurayinta ahmad waziri yadda taga ana ma kulthum yasa itama tafara jin kamar bazata wani jima ba zatace masa yes kawai ya turo itama tay auren nan. he is very calm and loyal to her, duk wani yawace yawace da saya sayen biki yana makale da ita duk dama yaa ibaad ya saka mata ido ya hanata hirar dare ko yawo da sauri a mota anyhow yawanci abu sai taje school suke samun daman yinsa hankali kwance.

Burnt Orange da,Chocolate Brown da,Gold aka fitar kalolin biki dana anko dana komi ba kawaye ne zasu daka burnt orange da golden head, iyaye kuma zasu saka golden attires da chokolate brown head, maza da sauran tarkacen famiy kuma they stand btwn gold nd chokolate brown....

3 weeks to the weding ne birthdayn saurayin sultana yace mata kaninsa usman ne zai shirya masa cake cutting party kyma yana so ta halarci wajen koda na 5 minutes ne a farko bata amince ba amma dataga ya nace sai kawai ta amince masa cewa sai ta tambaye gida in anbarta taje kwana a wekdns family house zata iya fita da dare batare da kowa ya sani ba..

sabida aminta da son datake ma ahmad ta roka bappa zaidu ya barta akan zata kwna takai ranar sunday a family house, sartuday night ne birthday partyn daga kulthum sai ayaana kawai ta gayawa gaskiyar inda zataje..

bayan anzo wkends an watse around 8pm sultana ta shirya zuwa birthday ayaana da kulthum suka rakata waje batare da anganosu ba...30 min kawai tace musu zatay by 9.30-10 dai suka saka ran zata nemesu suzo su shigo da ita amma inaaa

9.30 ya wuce 10 yay har ya wuce akazo kan 11 ayaanah ta dinga kirar layin sultana yana ringing amma ba adauka ba hanklinsu in yay dubu ya tashi suka rasa abunda yake musu dadi, tana kira kulthum tana kira wasa wasa har 2pm na dare basu ga sultana ba karshe ma sukaji wayarta akashe tsabar sun damu har kuka sai da sukasha subiyunsu a daki tsoro ya gama cika zuciyarsu...da har sun yanke hukuncin cewa kafin asubah zasu fito su gayawa ya mjaheed sai caraf suga text message dinta na cewa tana waje...da wani irin speed suka fito cikin sanda hanklnsu bai kara tashi ba saida su ganta babu takalmi babu dan kwali daga ita sai wayarta jikinta na rawa sosai. kafin su iso dakin gabansu ya gama faduwa, saida sultana tasha kuka snn ta fara basu labarin cewa ai set up ne, kaninshi faisal ya saka musu kwaya a drink ya dauke hotonan su akan gado half naked awaya yana threatning dinsu akan zai watsasu..

how they both wake up confuse tayita kuka harta fasa masa kai da flower verse ta zazzgeshi shima yayita kuka... she told them how he confront his bro har ya masa duka agabanta saishi kuma ya fadi gaskiya cewa ai mum dinsa ne tace ya lalata masa rayuwa sabida kar azo a bashi sarauta

...she was recording cos she was shocked of the betrayal yadda ahamd din ya saka yaron aransa sosai

iya abunda yasa su ayaana jin relieve kenan but they are scared, angry nd confused. ta basu labari har inda ahmad ya rakota waje yana bata hakri yana mata bayani and how she regret trusting him while he let his family problem push him to black mail her kawai ita bata son ta sake gann fusknsa, she came home cold nd crying she even played the audio recoding for them. sukayi ta kuka then she demand they kept it as secret har saita samu mafita satin gabaki daya basa cikin hayyancinsu dan har vaginity test sun rakata tayi.

kullum ahmd zai kira ta amma bata daukawa, he came one time ana daf da bikin kulthum, dakyr suka roqeta ta kulashi nd he told her yayi bincike akan magana anma kama mum din faisal tana zuba asiri ma sarki she is custody now..nd he want to ask for her permission ko zai iya fadan abunda ya faru tsakaninsu ma sarki koda baza abashi aurenta ba he want to get justice for her since his bro is trying to expose them to get his mom out..

yace gara ace shiya fara kai maganan da kaninsa yakai yadai kalallameta she was just crying, then later told him koda yakai karar tan will it be enuf to save her dignity? baya tunanin idan iyayenta suka sani, ko yayunta sukaji ta fita da dare taje wajensa zasu kasheta, she put her self at risk ne sabida ta yarda dashi nd she loved him so much...kamar xai kuka yale amsata with more intense love duk agabansu ayaana akayi suma suna hawaye yadda ahamd din ya dinga rokon sultana yana bata haquri

sai can ayana ta jawota sukayi magana agefe suka tattauna posble out come nd plans. then they decide akan tace masa zuwa anjima she wll make her decison nd call him

bayan tagaya masa yana tafiya sukaje daki suka karasa tattaunawa, then da dare ta tura masa text saiya kirata tace tana da solution da zata basa na kare kansa daga sharrin faisal bro din, amma sai ya mata alkwarin cewa he wll only use that to keep him silent..amma bawai ya tona musu asiri ba..he beg nd gave her his word....dacan ma harta fasa sabida tsoro daga baya kuma da safe saita tura masa recording audio da video..she blocked him a chat din ryt away, yakira ma bata daukawa but he still send her text every day da kyar su ayaana suka ta rokonta akan tabashi snd chance musmmn ma since the plan was succesfl kuma faisal da mum dinsa ma ansaketa an kulleta shikuma yabar kasa. dakyar sultana ta iya yafe maganan ya rufu and ever since shima ya fara batun zai turo asan dashi agida tace masa bayanxu ba sai angama auren yayanta tukuna...

case din daya dauke musu hankli a satin kenan basu ma san da cewa zainab arifah itama ta dawo nigeria domin halattar biki ba

dacan anata cewa baza'a tara jama'a kafin kace wani abu satin biki anfara cika musu gida dan Acikin mutanen da anty safeera ta sanar da su iya wanda suke close da itane sosai,sai relations yan uwanta na nesa da kusa da kuma few colleques dinta na wajen aiki da suke kud da kud

hajiya mairoce dai ta taro mutanen ta birni da kauye,dan wasu na kusa da itan ma a sashen ta suka tare tun ana saura sati daya hidima ana shirye shiryen bidirin biki.

Tun abu na kamar wasa saida yan uwan anty safeera sukazo sukasaka shirye shiryen ya wuce tunanin jama'a abu yana nema ya dawo wani babban hidima dan kuwa bakaramin naira ake ta narkawa awajen tsare tsaren hidindimon da za'ayi ba.

Programes kala uku wanda ba'aza somayin su ba sai ana saura kwana uku da zuwan ango nigeria,dan hakama yasa aka buga invitation card tun wuri aka babbawa wanda ake son su hallici wajen taron wanda mafi akasari mata ne

,mazajen da aka gayyata basufi a kirga ba yawanci ma abokan mahaifinsa ne da wanda ake mutunci dasu sosai.

Day one na budirin bikin da wankan amarya aka fara tradional bridal wash colour of the moments was brown nd gold, akayi decorating cikin gidan aka kawata shi da ado irin na al'adun indiyawa ga tabarman alfarma masu shegen kyau Inda sisters da anties din anty safeera kowa ya dauki nashi sashen hidiman da zai kula dashi.

Ranar wankan amarya aka gayyato tradional beauty nd spa artist dinta tundaga ƙasar sudan saidai ita irin asalinta yar buzuwa ce din nan, hadin gambizar niger da kuma ƙasar sudan din,itama da mukrabbanta tazo gidan aka tara mata ana yan raye raye na al'ada akayi ma amarya traditional spa,waxing etc,snn aka mata wankan madara da caramel dilka, da wani irin kwabin skin mask Bayan an gama wanka har 12 dare aka kai ana mata tsumi da kayan qamshi.

Tun ba aje ko ina ba jikin kulthum da kawayenta ya fara fidda wasu irin rikitattun qamshin turaruka tun daga tsakar kanta qamshi hartafin kafafunta qamshi ne mai tsananin dadi yake fitarwa.

Washe gari sassafe haka aka sake taron bridal sitting inda aka tsantsara ma amarya lallen heena ja da baki a hannu da kafafu masu mugun daukar hankli, duk wanda yazo wajen shima saida aka zana masa nasa a hannunsa..

Tun daga rana na biyu manyan mata da antys suka fara ma amarya nasiha da hudubar zaman aure da wani dan karamin Al'adan su da sukeyi kamar budan kai,wanda saida yammacan akayiwa mata kwalliya ta saka golden chantilly lace dinta mai matching color design na amina muaddi heel cover shoes da purse dinshi,an mata kwalliyarta nude kamar dai yadda take so mai daukar numfashi taji gwalagwalen nan wuya da hannu bakaramin kyau tayi ba.

Wani babban mayafi mai sharara dogo aka mata rufi dashi duk inda tabi qamshine mai ratsa zuciya yake ragowa awajen,few schl mates dinta data gayyata wanda basufi su uku ba su suka dan tssattsaya mata akayi program din kamar budan kai.

Yan uwan miji bayan sun mammana mata kudi suka kawo mata kyautuka Snn aka bude fuskanta a sarari kowa ya kalla.

daren ranar maheer ya dawo suka zauna a wani babban hotel, both his freinds and ibaad's friends su goma cass

aka kwana tare.

Washe gari Ranar juma'a ne randa aka saka ranar daurin aure, da dare kuma sai dinner early morning 11:30 saturday za'ayo budan kai snn akai amarya.

yauma bakaramin kyau amarya tayi ba makeup artist sun tsantsara mata wani nude nd breathtaking kwalliya bakinta na wani irin shining da lipsgloss, ta saka wani tsadadden white lacy flowing weding gown mai cuts nd ruffle neck da dogon hannu

,kayan is so decent nd damn classy mayafinshi shima transparent ne har kasa yakeja yana sharar kasa,bayan nan komi na jikinta da akayi pairing silver colour ne...

angwaye suka saka grizzly sand colour shaddoji amma gare dukansu suka dinka ango ne kawai yasaka pure white ana gama daurin aure sukayo wata gawutacciyar liyafa acikin wani babban hall inda duk wasu mazajen da uncle moh ya gayyato suka hallara aka ci aka sha aka babba da souviernies wa baki

can angwaye suka rako shi gida yazo yay gaisuwa kafin nan aka fito da amarya da kawayenta sunsha kyau bana kadan ba,ayaana da kulthum sukasa chokolate brown colour aka musu nasiha bayan manya sun fita aka barsu duk wani surutun ango da amarya da akayi ayaanah bata dago kai ba hakama ibaad baice uffan ba har suka gama suka fita, he was just noticing yadda mujaheed yake ta daukar hoto da ayaanah, lkcin abokansa duka suna falon hajiy mairo anata surutu zainab arifah tazo ta zauna acikinsu dan bata taba ganin abokan ibaad ba sai yau and she is dying for him to introduce her to them to shikadaine bayanan anan, yana can sashen amminsa shikadai a daki ya cire garensa yana business call, yana gama kammala wayar cikin sauke ajiyan zuciya ya rubuta text ya tura ma ayaana akan ta kawo masa abinci daki yanxun nan.

ganin text din yasa ta raba kanta da fitinar mujaheed tace masa ana kiranta aciki, tajuya zata koma ciki kenan cikin sauri sai ga safiya suna hade ido tace " ke..uncle moh yana kiranki acan falonsa waikije yanzu nan yana tare da abokansa acan...

Tun safiya bata gama rufe baki ba ayaanah tace kije jice masa baki ganni ba tana fadin haka tay sauri ta wuce cikin gida,

sashen Ammi karama ta nufa tana tafiya tana gyara zaman veil dinta dan irin dinkin me fallen neck dinnan aka mata mekyau batasaka komi a wuyarta ba

wani irin shiru sashen ya dauka dake ammi tana tare da sauran jama'u a sashen hajya mairo ga frend in ibaad dana maheer an cika wajen da surutu zainab arifah ce kadai acikinsu kafin mujaheed shima ya jonasu...

jin shirun yay yawa kai tsaye ta nufi dakinsa dan ta duba shi, ahnkli ta turo kofar kirjinta na bugawa ahnkki ta tsaya cak daga kofa tana hango fara kal din singlet dinsa ya kwanta adan rigingine dagashi sai singlet din sai doguwar wandon shaddansa na daurin aure da bai cire ba.

kai tsaye wannn qamshin jikinsa me ratsa zuciya ya danne nata qamshin duk dama jiya wuni sukayi ana musu turare cikin daidatu makanta nitsuwa tay sallama me sanyi ahnkli taga ya juyo suna hade ido irin sihirtaccen kallo daya bita dashi yasa tabi ta sunkuyar dakanta kasa da sauri...ya amsa sallamar

ya zuba mata ido gabanta na faduwa ahnkli ta karaso gaban gadon har zata tsuguna yabi ya saka hannunsa ya fixgota bazata tajita azaune kusa daf dashi...

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025