KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Tushe Gandun Labari..

Asalin Na'ima Yusuf Dabo......

Na'ima jika ce a cikin Ahalin Malam Hamisu Dabo dake cikin garin Mayo-Belwa, Adamawa state, Malam Hamisu ya taso cikin nema sosai na sana'ar gwari kuma da ita Allah ya rufa masa asiri yake daukan nauyin 'yan'uwa da kuma iyalinsa, Matar sa daya mai suna Habiba wadda ta kasance bahaushiya yar garin kano suna rayuwa cikin rufin asiri, haihuwar Habiba biyar suna komawa babu rai wanda hakan ba qaramin tashin hankali yake sa musu ba, Habiba tasha tsangwana gurin dangin hamisu wanda har 'yan uwanta sun shaida hakan, rigima akayi sosai tsakanin danginta da na hamisu saboda har maita sun jingina mata akan hakan, 'yan uwanta sun shigo cikin lamarin gurin neman magani har daga qarshe suka rugumi dangana da hakuri, kuma sai Allah ya dubesu da rahama ya bawa Habiba wani cikin wanda ya kasance na shida kenan, cikin ikon Allah ta haifo danta namiji ranar suna yaro yaci Abdullahi, Hamisu sun raini dansu na tsahon shekara kafin Habiba ta koma ga Allah, sanadin ciwon jeji da yayi mata mummunan kamu, mutuwanta ya jijjaga Malam Hamisu da 'yan'uwanta sosai amma haka suka rungumi kaddara sukayi hakuri, ranar da 'yan'uwan habiba suka tashi komawa bayan zaman makokin ita Habiban, sun nemi abasu Abdullahi su koma garinsu dashi amma Malam Hamisu Sam yace "A'a" abar masa dansa zai kula dashi, danginsa da ba wani son Habiban suke ba tun can asali, basu nuna damuwarsu akan hakan ba, dakyar Malam ya yarda wata qanwar Habiba dake zama anan garin kano ta karbi Abdullahi dan itama a lokacin tana kan renon danta qarami wanda zeyi sa'an Abdullahi shima..
An dauki shekaru kafin Malam Hamisu ya sake wani aure, Kuma wani ragon azanci sai be bibiyi bayan dansa ba 'ance dan Adam ajizi' , daga baya ya auri wata ana kiranta lantana me kai musu tallan nono gurin sana'arsa, sunyi zaman lafiya da lantana kuma a wannan karon sun samu haihuwa har yara hudu, babban cikin sunansa Ayuba, Nasiru, Yusuf sannan lubabatu data kasance kurma, acikin yaran Malam Hamisu babu wanda bai kama sana'ar gwarin ba, amma sai yazamo Yusuf ya hada tasa sana'ar da boko...
Yusuf ya taso daban cikin 'yan'uwansa tayanda daga kan halayyarsa har zuwa hazaqarsa daban take, ga nutsuwa da rashin hayaniya, babu yanda Malam Hamisu beyi dashi akan ya kama sana'ar sa kawai ya ajiye boko ba amma abun yaci tura, su Ayuba da Nasiru kam dama 'ina zakuje? Kudi.. daga Ina kuke? Kudi.....' sai zafin neman kudi, kuma sunqi taruwa kamar wa'inda akayiwa baki, ta bangaren Yusuf kuma Allah ya rufa masa asiri daidai gwargwado, a iya karatun secondary din da yayi ya samu aka daukesa aiki anan makarantar primary na gwamnati dake cikin garinsu, 
Ana tafe bayan wasu shekaru kowa yakai ga gacin aure acikinsu, Lubabatu ce tafara aure aka miqata wani qauye dake nan kusada garin nasu, Ayuba da Nasiru kusan tare ma sukayi nasu auren, zuwa wannan lokacin sunyi neman kudin har fita ci rani zuwa manyan gari sunyi amma kudi sunqi zuwa kaman abun masifa...
A lokacin da Yusuf ya tashi aure shikuma yadanyi kwari a fannin aikinsa da kuma sana'arsa dayake tabawa, wata yar maqotansu yagani yanaso sunanta Binta wadda afarko dai kyawunta ne abunda yafara rinjayarsa gareta, asannu asannu suka kuma daidaita ganin halayenta abunso, gashi mahaifiyarsa tana sonta, Binta ta taso gaban kakarta ne tareda qanwarta Halima, iyayensu sun rasu sai zama ya dawo dasu itada qanwar tata gurin kakarsu ta wajen Uba kuma se ya kasance ba wani dangin azo agani garesu ba, Allah ne gatansu sai kakarsu da ta tsaya musu akan komai nasu..Aure akayi na so da qauna tsakanin Yusuf da Binta yarinya mai hakuri da kawaici, sai ta hadu da Yusuf shima mara hayaniya da kuma nutsuwa, anan cikin unguwa Yusuf ya fulaste gidansa daya siya me dauke da daki biyu aka kai masa Bintarsa..Zama sukayi na so da tattalin juna, Yusuf na matuqar son Matarsa, Binta bata rufa shekara ba ciki ya bayyana jikinta, murna wajen Yusuf ba'a cewa komai, haka suka rinqa tattalin cikin tare gwanin sha'awa har Allah ya kawo ranan haihuwar Binta suka samu diyarsu mace inda taci suna NA'IMA, yarinya son kowa gurin kyau da haiba, gashi Allah ya zubawa Yusuf son 'yarsa kamar ya maidata ciki, bini bini yake yawo da abarsa akan keke, abu kuma indai Na'ima tace tanaso a gidan nan to sai an mata shi, dayawan lokuta hakan baya yiwa Binta dadi sanin me rayuwa ta qunsa yau mune gobe ba muba, Yusuf yakance "Tunda muna rayen, kuma Allah ya bamu iko sai muyi mata" Binta takan jijjaga kai kawai sanin kome zata ce masa bazai fahimta ba saboda son 'yarsa ya rufe masa ido, 'yan'uwa da dangi kowa ya shaida Yusuf yana son 'yarsa Na'ima dan baya iya boye hakan agaban kowa..
Na'ima na datawa mahaifinta ya sakata nan makarantar da yake koyarwa, aka sakata a primary, tare suke tafiya da mahaifin nata kuma tare suke dawowa gida a kekensa, kuma har zuwa lokacin Allah bai qara basu wata haihuwan ba, hakan kuma bai taba damun Yusuf ba sanin cewa komai na Allah ne, Binta ce ma mai saka damuwan hakan a ranta wani sa'in..
Babu dalilin hawa balle na sauqa kawu Ayuba ya fara mitan wai Yusuf ya saka 'yarsa a makarantar boko nan Nasiru ma ya karba dan dama ko menene Ayuba zeyi to bakinsa hade da shi Nasirun , haduwa sukayi su biyu suka yiwa Yusuf caaa, saida Malam Hamisu ya shiga maganar tukunna suka kama kansu, itadai mahaifiyarsu irin matan nan ne masu sanyin bala'i, sai abunda 'ya'ya suka aiwatar kawai tana gani babu tsawatarwa sosai....
Kwanci tashi Na'ima nada shekara 8 a duniya Allah yabawa Binta wani cikin, Sunyi murna har ba'a magana, Yusuf kamar ya maida Binta ciki saboda murna, a wannan lokacin ne kuma Allah yayiwa Malam Hamisu da kakar Bintan rasuwa, bi da bi kowanne ya koma ga Allah banbancin kwanaki uku, abun ya taru ya hade musu guri daya tun ba ma Binta ba, ga ciki ga mutuwa, qanwarta da itama zuwa lokacin tayi nata auren a garin yola ce tazo suka hadu sukasha kukansu, su Yusuf sunji mutuwar mahaifin nasu sosai suma, ahaka dai akayi zaman makoki kowa ya sake runguman kaddara, yazamto Malam Hamisu da kaka sunzamo tarihi saidai abisu da addua..

Ina labarin Abdullahi?...'yan'uwan mahaifiyarsa basuyi riqo da amana ba, basu dubi zaman so da amincin da Malam Hamisu yayi da Habiba ba lokacin da take raye, tunaninsu a koda yaushe shine wannan sabanin da aka samu tsakanin 'yar'uwarsu da dangin mijinta, wanda har hakan yasa qanwar maman Abdullahi bata zamo uwata tagari me sashi akan hanyar da zai nemi 'yan'uwansa ba, kasancewar mijin Hajiya Babba (ayanda suke kiranta kenan) ya na da rufin asiri sai Abdullahi yasamu kula da ilimi daidai gwargwado a gidan, ya taso cikin nema a fannin kasuwancin da mijin Hajiya Babba yakeyi, asannu asannu Hajiya Babba take sa Abdullahi bin mijinta kasuwa yana ayyuka har shima Allah ya hore masa yayi nasa shagon, a wannan lokacin ne kuma ya waiwayi gidan, babu yanda Hajiya ta iya haka ya dan tattaro guntun chanjinsa yazo duba mahaifinsa, su Ayuba sai a sannan suka sanshi, Yusuf bai hadu dashi ba dan baya gari ma lokacin da Abdullahin yazo, ganin jikinsa da alamun maiqo ne yasa Ayuba da Nasiru suka rinqa yin nan nan dashi kamar su maidashi ciki, Abdullahi bai wani dade ba ya koma kano gurin aikinsa...
Bai sake waiwayansu ba saida Malam yayi kwana arba'in da mutuwa ya dira garin, rana tsaka ya zo musu da wata mota mai dumi ya faka ta nan qofar gidan Malam, lokacin duk su Ayuba suna gurin aiki, goggo Mahaifiyarsu Yusuf dince ta sauqe shi sannan ta tura ayi mata kiransu su Ayuba dake nan kasuwar da ba nisa tsakaninsu, Yusuf dai qin barin aikinsa yayi, dan duk wata martaba ta Abdullahi kuma ya daina gani tunda har mahaifinsu zai mutu ace har ayi taro a watse babu alamunsa, sudai Ayuba da Nasiru cikin mazari suka kada kafarsu suka tafi, hankalinsu bai sake tashi ba saida suka ga motan da Abdullahi yazo da ita nan kofar gidan, Yanda kasan fir'auna da bayinsa haka suka rinqa tsugunnawa yayan nasu kamar su goya shi, babu wani batun baizo mutuwar ubansu ba, wannan bayanin ya kau kuma tunda yazo musu da chanji..ganin irin yanayin 'yan'uwan nasa ne yasa Abdullahi yi musu rabon kudi suna godiya kamar bakinsu zai yage, sai yammaci Yusuf ya baro gurin aikinsa, gidan mahaifiyarsa ya nufa dan gaisheta kafin ya wuce gida gurin iyalinsa, yayi mamakin ganin motan Abdullahi har sannan bai tafi ba, shima Abdullahin ganin Yusuf din sai yaji ya kama kansa, gashi dai ko da wasa Yusuf bai kaishi a shekaru ba amma yaqi sake masa kamar yanda su Ayuba sukayi, kuma cikin wani ikon Allah sai nan da nan Abdullahi yaji yanason Yusuf din, babu yabo babu fallasa Yusuf ya gaisa da yayan nasa sannan yace zai shiga cikin gidan ya gaisheda goggo, gyada kai Abdullahi yayi ya bayansa da kallo, Ayuba dake nan tsaye kusada Abdullahin ne yace "Kasan ai da'aka je kiran namun baya nan shiyasa baka ganmu tare ba" Abdullahi bai ce komai yana kallon bayan Yusuf din..Da yammacin ranann Abdullahi ya juya bai kwana garin ba...

Lokacin da Haihuwar Binta yazo sai abun yazo mata da matsala sosai, yau ciwo gobe lafiya, Hankalin Yusuf duk ya tashi sai mahaifiyarsa ce me dan saka hannu a lamuran nasa dan 'yan'uwansa dai kowa ta kansa yake, kar ma azo zancen Ayuba, dan shi idan bazaka qareshi da kudi ba to kai da banza ma duk daya, ta yanda hatta mutan gari sun san halinsa , kudinka mutuncinka a gurinsa dan kome kace yayi maka indai zaka bashi kudi to tsaf zeyi..

Ahaka dai binta tayi ta fama da jinya 'yan kudaden Yusuf duk suka tafi wajen neman magani, a satin da haihuwan ta fara tasowa gadan gadan wani irin sanyi Binta tayi har hakan yana baiwa Yusuf din tsoro, Na'ima dake Shirin shiga shekara na 9 a duniya ma saida ta fahimci wani abun na damun mahaifiyarta duk itama sai tazama shiru, makarantar ma bata son zuwa dan Yusuf daman tunda rashin lafiyan Binta ya tsananta ya maida zuwa aikin nasa sama sama..
Ranar da naquda ya tashi daman da asuba Yusuf ya nufi wajen mahaifiyarsa suka taho gidan nashi tare tashiga dakin wajen Binta daketa salati da juyi, Yusuf nanan tsaye bakin gadon mahaifiyarsa tace ya dauko kaya su kaita asibiti wanda shi sai a lokacin ma hakan yazo masa kai tsabar birkicewa, riqo hannunsa Binta tayi tace ya matso kusa tanason suyi magana, anan ne kuma tashin hankalinsu yafara linkuwa, dan Binta wasiya tafara bashi akan Na'ima, ta nemi ya kula da ita sannan ta fara neman yafiya, damqe hannunta Yusuf yayi ya fara kuka kamar qaramin yaro yana gyada kai tareda da tabbatar mata zata samu lafiya, Na'ima da tashinta kenan daga bacci, ta shigo dakin mahaifiyar tata itama, kuka ta farayi goggo ta dauketa suka fice, Kafin tadawo dakin Binta tace ga garinku nan, ta koma ga Allah da cikin da bata haifeshi ba kenan....
Hasbunallah...ranar Yusuf kowa ya shaida gigicewarsa, magana yake yana kauce layi, duk wanda yaga yanayinsa sai ya tausaya masa ainun, saboda wani irin tashin hankali ya shiga na rashin abokiyar rayuwan tashi da ba'a iya misaltawa, Na'ima babu baki sai kuka, in ta juya nan da can taga tarin mutane a gidan nasu kuma babu ummanta sai kuka, kuka kam sunyi shi ita mahaifinta har akayi sadakar bakwai basu dawo daidai ba, da qanwar maman Na'ima dake yola tace zata dauke ta Yusuf atake daman yace babu wannan zancen, zai riqe 'yarsa abar masa abunsa,ga kuma mahaifiyarsa tana raye zata tayasa kula da Na'iman, haka ta haqura bayan zaman makoki takoma gidan mijinta babu Na'ima..
Haka rayuwansu ta cigaba me cike da gibi babba, in sun tashi da safe daman tsaf ze wanke 'yarsa ya shiryata, tare zasuje siyo abun karyawan su dawo, sai ya tabbatar ta qoshi sannan ya zuba mata na tafiya wanda zataci a lokacin break, dorata yake bisa Keke su tafi makaranta, a lokacin break daman tun fil azal ma gurinshi take cin abinci, da zaran an tashi kuma ba gida yake maida ita ba, can gurin goggo yake kaita sannan ya wuce gurin sana'arsa a kasuwa,daga gurin goggon ne kuma zata sake shiryawa ta tafi islamiya, sai ya dawo kuma ya sake daukanta su wuce gida wanda babu yanda ita goggon batayi dashi akan ya bar mata Na'iman ba amma abun yaci tura, shidai be fito fili yace A'a ba, amma bini bini in 'yarsa na gidan to ko ya dawo anan zai kai har dare, har se goggon tace ya tafi, da fari yana tafiya gida ya kwana shi kadai amma daga baya sai yayi shinfidi nan bakin kofar goggon yace nan zai kwana, da ta tambayesa dalili yace "Goggo gidan yana sakamin kunci arai kullum na shigesa" ganin haka yasa tafara barinsa ya tafi da Na'iman in yaso in sun taso daga makaranta sai ya kawota, dan lamarin Yusuf babu alamun qara aure nan kusa kuma....
Ina labarin Ayuba da dan'uwansa Nasiru? dan lubabatu tayi nata auren da da dadewa daman har da yaranta manya anan qauyen dake kusa da garin, shi dama Ayuba mata biyu garesa ta farko Jummai sunanta yara na kiranta Umma, sannan ta biyu mai suna Abida ana kiranta Anty Amarya, shikuma Nasiru Matarsa mai suna Laraba yara na kiranta da Umma Laraba har 'ya'yanta ma haka suke kiranta, 
Ta fannin gidan Ayuba dai Allah ya hadasa da guda daya shima, dan jarabar Umma har shi Ayuban tsotsewa take balle Anty Amarya, irin fitinannun matan nan ne wanda su a rayuwa kar a zauna lafiya ga son abun duniya, cikin 'ya'yanta mata babu wanda bata dorawa tallan abinci kuma ko nawa za'a kawo mata ko da akwai qari akan kudin baruwanta itadai lafiya lafiya, A lokacin da Binta ta rasu bayan an kwana biyu tisa Ayuba tayi a gaba sai ya dauko mata Na'ima, yarinya ga kyau ba qaramin kudi zata kawo mata ba, to sai aka samu akasin shi Yusuf ba irin mutanen nan bane masu saka saka da lamura, yayun nasa ma tun sa'in da ya fahimci irin rayuwar da suka daukowa kansu , ya rage shiga sabgoginsu, haka duk suka zubawa Yusuf idanu yana kula da 'yarsa tare da tallafin goggo....

Ranan Na'ima suna kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta ita da mahaifinta, ya tsaya nan wani kanti ya siya mata biscuits da sweets tanata murna, saida ya bare mata ya bata tafara ci sannan ya hau keken suka qarasa gidan Goggo, sun sameta zaune nan kan taburma a tsakar dakinta hannunta riqe da tasbaha tana zikr, bayan Yusuf ya gaishe ta, Na'ima ta miqo mata ledan biscuit din tana murmushi tace "Goggo gashi kici kema" ta qarasa maganan cikin muryanta me sanyi hadeda yarinta, murmushi Goggon tayi itama tace "Kici abunki Na'ima, Allah yayi albarka" Na'ima ta gyada kai ta zauna nan kan taburman, miqa hannu Goggo tayi qasan gadon karfenta ta ciro musu kwanon abincinsu da take ajiyewa kullum kafin su dawo, miqawa Yusuf tayi yananan zaune, Na'ima ta miqe ta debo musu ruwan wanke hannu, tare suka ci abincin anan dakin goggon suna hira jefi jefi har suka gama, sai da Yusuf ya miqe zai wuce kasuwa goggo tace "Zan aika yarinyar nan taje gidan kawunanta su gaisa anjima tunda babu islamiya" Yusuf yace "Toh goggo can din zanje daukanta kenan" Goggo ta girgiza kai tace "Ai ba wani dadewa zatayi ba" ya gyada kai sannan sukayi sallama ya shafa kan Na'ima dake yi masa murmushin sannan ya fice.
Bayan fitarsa ne Goggo tace da Na'iman "Maza yi sallah sai kiyi wanka ga kayanki nan na fitar miki, kije gidan kawunki ki gaishesu" gyada kai Na'ima tayi tace "Gurin Anty Amarya?" Goggo tace "A'a har Umma ma duk zaki gaisar in kinje" ta amsa da "Toh" sannan tafara yin abunda aka sata..
Bayan Na'ima ta shirya Goggo tace ta dauki biscuits din nata taje, dayake gidan kawu Ayuban anan unguwar yake kuma tasani sai nan da nan ta isa, shiganta gidan da sallama tasamesu nan tsakar gida, Umma ta girke nan kan kujera hannunta riqe da muciya tana juya marden alala dake cikin kafulas a gabanta, yarta me suna salame zaune gefenta tana murza manja a ledojin da zasu qulla, bin Na'ima sukayi da kallo dukansu har sauran yaran, Umma sai kallon kayan dake jikin Na'ima take ganin yarinyar fes da ita ga uban ya gyara mata gashinta gwanin sha'awa, gaishe da umma Na'ima tayi, bata daina kallonta ba tace "Lafiya autar babanta" sai Na'ima tarasa me zata sake cewa gashi duk suna kallonta, tananan tsaye yaron umman me suna Salim ya fizge biscuit din hannunta, ta daga kai tana kallonsa batace komai ba, Salame ce tace "Toh da kika tsaya mana aka din bazaki zauna bane, zo ki bude mana leda" da sauri Na'ima ta gyada kai ta zauna nan aka fara aikin alalan da ita, sai da suka gama kulla alalen nan tas da ita sai gumi take na rashin sabo, bayan sun gama ta kalli umma a hankali tace "Umma zanje gurin Anty Amarya" Salame ta sake cewa "Wani ya hanaki ne" miqewa tayi tafara karkade riganta ta nufi dakin Anty Amarya da ke nan gefen na umma, a kwance ta sameta kasancewar tana fama da laulayin sabon ciki, Anty Amarya na ganinta tafara murmushi tace "Wace wannan kaman Na'iman Abbanta?" sai Na'ima ta fara dariya dan tanason Anty Amarya kaf gidan ita kadai take mata fara'a har ta bata abu in tazo, Anty Amarya ta sauqo daga kan gadon nata dakyar ta kama hannunta tana tambayanta ya makaranta, sai lokacin Na'ima ta sake tafara magana, data fita debo ruwa ma Anty amaryan Umma tace tazo ta zauna ayi gyaran shinkafah da ita, komawa gidan Goggon da bata yi ba kenan sai nan gidan kawu Ayuban babanta yazo ya dauke ta a kekensa suka wuce gida, da daren ranan Na'ima na zaune da mahaifin nata anan veranda na qofar dakinsu tace "Abba" ya dago kai yace "Na'am 'yar Abba" tace "dazu Salim ya kwacemin biskit dina" yayi murmushi tareda kai hannunsa ya shafa kanta yace "Sharing is caring daughter, kinga kin 'yammasa kenan" sai Na'ima ta jijjiga kai tace "Toh zaka siyamin wani?" Ya sake gyada kai tareda cewa "Gobe ma" cikin son kawar da zancen yace ta fara fado masa karatun da sukeyi a islamiya, nan tafara yana kallonta fuskarsa cike da walwala, ganinta a ko yaushe na tuna masa da Binta sosai wanda tun hakan yana sosa zuciyarsa har ya saba, sai kallonta yake tana magana aransa yana roqon Allah...yabashi tsawon rai su rayu tare da 'yarsa har girmanta.

But, if wishes were horses......

Wayewar washegari Na'ima ta riga mahaifinta tashi, dama anan dakinsa take bacci shi a qasa ita akan gadon, sauqa tayi takai hannu tadan tabasa, jin kamar yana bacci yasa ta fita abunta dan dama a matse da uzurin fitsari ta tashi, har taje tayi ta dawo bai tashi ba, ta zauna tana jiran ya tashi suyi alwalan tare shiru bai tashi ba, sake taboshi tayi tace "Abba" shiru kamar me bacci gashinan idonsa a rufe, fita tayi tayo alwalan sannan tadawo tafara sallah, har gari ya waye bataga Abbanta ya tashi ba, daga qarshe ta miqe ta fita daga gidan, gidan Goggon ta nufa tana sauri, isarta gidan tasamu kawu Ayuban yazo gaishe da goggon sunanan zaune a daki, ganin Na'ima ita kadai da sassafe yasa goggo tadanji hankalinta ya tashi ta fara tambayanta meya faru, fada musu tayi Abban ta yana bacci tayi tayi ya tashi kuma shiru, Ai atare Goggo da Ayuba suka miqe,fita sukayi a gigice basu tsaya ko Ina ba sai gidan Yusuf suka shiga har cikin dakinsa nan suka samesa kwance kamar yanda Na'iman ta barshi, Ayuba ya jijjaga shi goggo ma ta matso tana kallonsa hankali tashe, a sannan ne suka gane rai yayi halinsa..
Yusuf ya koma ga Allah acikin baccinsa......