ZAKIYYA Matashiya mai juyayyiyar Kaddara
4
by @sadiyanasir
A daren ranar Zakiyya bata samu baccin kirki ba. Duk lokacin da ta rufe ido kalmomin Aliyu da hoton Mahmod suna suke mata yawo a kwakwalwa.
Washe gari kamar kullum haka ta ajiye ma Aliyu kosai amma har lokacin shigarta gida bai zo ba, ganin har kusan Azahar yasa tayi sadaka ma Yara. Karfe hud'u ta shirya cikin shiga ta kamala ta sallami Mama Rakiya akan zata kasuwa, amma a zahirin gaskiya gidan Kawu Isma'il za taje su tattauna da Aunty Amina akan zancen Aliyu. Da sallama ta shiga gidan ckin sa'a kuwa ta samu Aunty Amina kad'ai Yaran da Kawu duk basu nan. Yanayin da Aunty Amina taga Zakiyya ya tabbatar mata akwai damuwa. "Lafiya kuwa Zakiyya meke damunki?". Tayi maganar bayan sun gaisa. Ajiyar zuciya mai karfi Zakiyya ta sauk'e ta mai da hankalinta gun Aunty Amina. "Lafiya kalau Aunty yar matsala ce dani shine nazo gareki ki bani shawara?". "Ina jinki ". Tayi maganar tana kallon Zakiyya. Nan Zakiyya ta kwashe yanda su kayi da Aliyu da irin zaman ukubu da take a gidan Mahaifinta. Nisawa sosai Aunty Amina tayi zuciyarta na zafi tace. "Wallahi Rakiya azzaluma ce Matar nan bata da Imani Zakiyya, rashin gatan ki bai kai ace wai sai kinyi kosai da kunu kafin ki samu abinda za kici ki rufa ma kanki asiri ba, ya zama dole wannan karo Kawun ki yayi wani abu kai, sannan maganar gaskiya in har Aliyu da gaske yake kuma anyi bin cike bashi da wani mummunar hali ki amince dashi sannan ki mika lamarinki gun Allah kiga abin mamaki, Mahmod Allah ya karb'i abinsa ki yarda da Kaddara haka Allah ya tsara rayuwarki dashi kalilan ce, kuma tabbas abinda Zahra ta fad'a miki gaskiya ce Malam harda damuwar ganin halin da kike ciki yasa ciwo yake nemar rayuwarsa, kice Aliyu ya baki kwana biyu ki nutsu kiyi Addu'a, idan kinji nutsuwa a zuciyarki to kiyi hakuri ki amsa mishi Koda baki kaunarsa, a hankali watarana zaki so shi". Murmushin takaici Zakiyya tayi. "Zan iya amincewa na Aure sa amma batun soyayya babu Aunty, ban san haka nake kaunar Mahmod ba sai da ya bar duniya, bana jin zuciyata zata amince da wani a matsayin masoyi". Murmushi Aunty Amin tayi. "Shikenan Hajiya Zakiyya naji ki Aure shi ba don kina son shi ba sai don cancanta". "Umm yauwa Aunty don Allah kiyi hakuri karki sanar da Kawu zancen nan, wallahi hakan ba k'aramar matsala zata haifar min ba, kin san halin Mama Rakiya Sarai, kuma kin san rubutun da akayi a kotu akan saka baki da Kawu yake cikin hidimata, kawai kicigaba dayi min Addu'a in sha Allah watarana sai labari". "Shikenan Zakiyya". Aunty Amina ta ambata tana jin zafi a ranta.
Sai kusan karfe shida kafin Zakiyya tayi mata sallama tana mai jin dad'in shawarar da Aunty Amina ta bata, a gaggauce ta k'arasa kasuwa ta saya abinda zata saya ta wuce gida, Allah ya taimaketa Mama Rakiya ta fita bare tayi mata fad'an kaiwa yamma. Malam ta samu zaune a tabarmar ta isa garesa ta zauna ta gaishesa a ladabce. "Zakiyya kin dawo?". "Eh Baba ya jikin dai?". "Uhumm da sauk'i Zakiyya amma gaskiya bana jin dad'i". "To ni Baba meyasa ba za'a kaika asibiti ba? Tunda ka fara ciwon nan a gida kake jinya fa, sai dai aje chemis a sayo magani amma har yanzu baka san meke damun ka ba?". "Hakane Zakiyya kin san hidimar asibiti sai da kud'i kuma ai alhmdullah jikin da sauk'i ba kamar farkon ciwon ba, in sha Allah nan da wani lokaci har Kasuwa zan fita". "Allah ya amsa Baba ya baka lafiya". "Ameen ya rabbi Ubangiji ya miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya". "Ameen ya rabbi". Zakiyya ta amsa ta mike tana jin dad'in Addu'ar Mahaifinta.
*****
Abu kamar wasa kwana uku kenan Aliyu bai zo amsar kosai ba, kullum Zakiyya sai ta ajiye amma shuru har abin ya soma damunta, a ranar wajen karfe na dare suna kwance a tabarma a tsakar gida da Zahra suna hira saboda zafi da ake sako ya shigo daga lambar da bata da suna. dauka tayi tana kallon rubutun “Amincin Allah ya sameki a duk inda kike mar'atus saliha, ina miki fatan alkairi, zaki iya bani amsar maganar mu gobe? Ina jiran ki, ko menene kika zaɓa? Daga Aliyu.” Zuciyarta taji ya buga da karfi tayi murmushi mai rauni.
“Gobe…”
ta maimaita a hankali. Tsintar kanta tayi da rubuta "Shikenan Allah ya kaimu gobe". Ta mike tayi d'aki ta jingina da bango ta rufe ido zuciyarta na binta da tambaya. “Shin meke shirin faruwa da nine? Ko wani sabon jarabawa zan shiga?” Ta jima a haka kafin ta sauk'e ajiyar zuciya ta fito tayi alola ta koma ta kwanta tana sake sake har bacci ya d'auke ta.
Washegari da asuba Zakiyya ta tashi da wani irin sanyi a zuciyarta wanda bata san dalili ba, amma kalmar “gobe” da ta fada jiya ta tsaya mata a rai. Gobe ce yau, kuma yau ce Aliyu yake jiran amsar da zata iya canza duk rayuwarta.
Ta yi sallah ta dade tana addu’a.
“Ya Allah ka bani alkairin da ya dace da ni…”
Haka ta maimaita har zuciyarta ta dan lafa.
A waje, rana bata fito sosai ba, amma zuciyarta ta fi ko wanne dare ciki duhu. Ta fara hada kunu amma yau hannunta yana rawa tamkar marar lafiya, hatta kunu da take damawa tamkar ba laka a jikinta. "Ke! Me ya same ki ne yau?” Muryar Mama Rakiya ta katse tunaninta. "Ko baki da lafiya ne?". "Lafiya kalau Mama". Tsaki Mama Rakiya tayi bata sake cewa komaiba. Shuru Zakiyya tayi tacigaba da aiki kamar yadda ta saba. Babu wani abu daya dameta yake nukurkusar zuciyarta kamar da abinda ke cikin ranta.
Kamar yadda take tunani Aliyu ya bayyana da sassafe. Amma yau bai zo da murmushin nan nasa ba. Fuskar shi na cikin damuwa, kamar mutumin da ba ya son takura amma yana a cikin halin da ya fara takura kansa. Jawo dutsen dake gefe yayi ya zauna kusa da ita.
“Ina kwana Zakiyya?” ya fada a hankali. “Lafiya kalau Alhmdullah, kwana biyu shuru?.” Ta amsa idonta na kasa. Idon sa akanta na dan lokaci yana kare ma kyakkyawar fuskarta kallo na dan lokaci kafin ya ce. "Na san za kiyi Mamakin ganina, watakila kice ni Mutum ne mai naci da son cusa kaina in da ba'a so, ban zo don na matsa miki ba, sannan ba zanyi miki dole ba, amma ki sani ina jin al'amari mai girma akan ki Zakiyya, nasan yau ita ce ranar da zaki yanke hukuncin alakar dake tsakanina dake, karki damu da halin da zan shiga ina so ki fad'a min gaskiyar abinda ke zuciyarki game dani, nayi Imani da Allah sannan na yarda da kaddara ki fada min kinji?.” Ya k'arasa maganar a rauna ce. Runtse ido Zakiyya tayi zuciyarta na bugawa saboda tashin hankali, muryarta na rawa tace
“Ban san inda zuciyata take so ba, Ina jin tsoron kaina, sannan ina tsoron rayuwa, ina jin fad'uwar gaba sosai Aliyu, ban tab'a tunanin zan rasa Mahmod a k'ank'anin lokaci ba, ina tsoron sake jefa kaina cikin soyayya saboda banji da dad'i ba.” Shiru Aliyu yayi yana k'ara karantar yanayin Zakiyya. Cikin natsuwa yace "Tsoro ba laifi bane Zakiyya. Mutum da yake da rai, yake jin ciwo, yake da tabbaci da rashin tabbaci shi ne yake jin tsoro. Idan da kin ce ba kya jin komai ma, to da shi ne abin damuwa.”
Kalmar tasa ta dan taba zuciyarta ta dago a hankali ta ce:
“Aliyu… yanzu ba zan iya yanke hukunci akan Alakarmu ba, ka sake bani lokaci don jin amsa ta, A yanzu zuciyata tana da rauni, bazan so ka shigo rayuwata sannan na zubar da kaunar da kake bani saboda rashin shiri ba.” Cize leb'e yayi sannan yayi murmushi mai ciwo. "Na amince zan jira ki, Amma ki sani, ni ba zan daina yi miki addu’a ba.” Ya mike har ya juya zai tafi sai ya sake waiwayowa:
“Idan akwai wani abu da kike bukata ki fada min kina da number ta.” Yana gama fad'in haka ya bar wajen cikin nutsuwa.
Da ido Zakiyya ta bishi zuciyarta ta tsaya cak, haka dai a daddafe cikin rashin nutsuwa ta k'arasa sana'arta ta shiga gida. Wunin ranar a wani irin yanayi tayi shi, da dare bayan kowa ya kwanta, Zakiyya ta zauna zaman kadaici, tunanin hirarsu da Aliyu ta sake dawo mata. Mikewa tayi ta d'auro alola ta gabatar da Nafila raka'a biyu ta bishi
da doguwar addu’a, ta bude zuciyarta a gaban Ubangiji. Ta d'auki tsawon lokaci kafin ta koma ta kwanta tana jin wani abu na motsa mata a cikin zuciya game da Aliyu, ba soyayya ba, ba tsana ba, amma kamar karamin haske bayan duhu. A wannan daren ta dauki shawara ta farko a sabuwar rayuwarta. Zata rufe zuciyarta ta nemi nutsuwa kafin ta amsa kowa.
Ba mafita tsakaninta da Aliyu ba.
Ba zaman rashin gata da
Mama Rakiya ba.
Ba kuma maganar mutane ba.
Zabin Allah da kwanciyar hankalin zuciyarta. murmushi tayi ta rufe ido ta fada bacci.
***
Aliyu kuwa duk da bai tsammaci haka daga gun Zakiyya ba, hakan bai sa son da yake mata ya samu rauni ba, sai ma sake jin sabon al'amari akanta. Jidda Matarsa ta fahimci Mijin nata baya cikin nutsuwa, haka ta bar abin cikin zuciyarta har lokacin bacci, shigewa jikinsa tayi yatsunta na wasa cikin gashin kansa. "Abban Farrah meke damunka don Allah? Yau tun dawowarka na fahimci akwai abinda ke damunka? Don Allah ka sanar dani ko zan samu sukuni a zuciya?". Ajiyar zuciya ya sauk'e ya k'ara jawota jikin sa. "Bakomai Jidda kawai yanayin aiki ne, kin san mutane yau da gobe". "Hakane don Allah ka rage damuwa dasu, kacigaba da Addu'a in sha Allah watarana sai sunyi nadamar abinda suke maka". "Wannan hakane, Allah ya miki albarka". "Ameen ya rabbi Alamina Mijina, sai da safe". Ta gyara kwanciya tuni bacci ya d'auketa. Kallonta Aliyu yayi tausayin Jidda na shiga zuciyarsa, a tsari na rayuwarsa babu zama da Mata biyu, amma had'uwa da Zakiyya ya ruguza komai na rayuwar shi, ji yake idan ya rasa Zakiyya zai iya rasa rayuwarsa. Da wannan tunanin shima bacci ya d'auke sa...